BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir

Daidai lokacin da Safah ta fito daga toilet tana daure da tawul iya cinyoyinta. A rayuwarta ba ta make up (kwalliyar janbaki, shafe-shafe, su eye shadow da su mascara). Sai dai ta shafa lotion wanda ta tabbatar is a dermatologically tested, zai kara mata taushin fata ne kawai, irin su Olay, E45 lotion, Norwegian formular, Nibea ko Abeeno. Ba wanda zai kara mata haske ko kankani ba. Babban sirrin kwalliyar Dr. Safah shine, Armpit Sprays, tana using designer body sprays da dama masu sanyin kamshin da ba za ka so ta matsa daga kusa da kai ba. 

Ta tsaya tana kallon ‘yar’uwarta, “Ke lafiya kike fiddo min da kaya? Ce miki na yi kwalliya zan yi? Office fa za ni”. 

Ta ce, “Ki saka dai, Mami ta ce in fiddo miki don kar a bata lokaci, baki muka yi’. 

Cikin takaici ta ce, “Amma kin san ranar aiki ce ko? Ina ruwana da wasu bak”. 

Ta ce, “Ai wajenki suka zo”. 

“Wajena?” Sai kuma ta yi shiru kawai, ta karbi rigar ta sanya ta rufe tulin gashin kanta da dankwalin rigar suka fito. 

Marwa ba ta sake ta ba, haka ta yi ta janta har kofar dakin baki. Wani kamshi ne da ta sani a kwanakin nan ya doki hancinta a lokacin da suka isa kofar dakin bakin. 

Amma ta kasa tuno inda ta san kamshin chromelegend, sai da Marwa ta yaye labulen idonta yai arba da Dan Abdulkareem Numan, wanda ta kwana, ta kuma wayi gari zuciyarta cike taf da soyayyarsa maras misali. 

Ko idonta ne ke mata gizo? Anya shine? Kada dai da asubah ya dauko hanya saboda maganganun da Marwah ta fada mishi a waya? 

To in shine ya a kai ya san gidansu? Haka ta yi ta tambayar kanta silly kuestions (to silly mana?). Wane ne bai san Dan Kasa a Kaduna ba balle har sanin gidansa ya gagara? 

Kallon shi kawai take cike da mamaki da wani irin dadi cikin ranta, sai dai kuma ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarsa yake ba. 

Bayan rashin barcin da ya kumbura mishi manyan idanunsa, ya bambanta da dan gayen nan na kwanaki biyu da suka wuce, domin ya bar lallausar kasumba ta cika gefen fuskarshi, fuskarshi ta fada sosai. 

Jeans da farar T. Shirt ne kawai a jikinsa, sumar kanshi ta kanannade alamar yau ko ruwa ba ta gani ba balle kumbing, sai hakan ya mai da shi tamkar Balaraben Madina. 

Daga kai ya yi a hankali yana kallon ‘ya’yan Dan Kasa da ya dade yana jin labari, fara da baka ‘yan biyu, wadanda sam basa kama da juna, kowacce da irin kyanta, da irin kwarjininta, da irin kasaitarta ta manyan kwalayen zuzzurfan ilimin boko. 

Daya da tsohon ciki, daya single. Yarinyar farko da ta taba hana shi barci a rayuwarsa, ta hana shi zuwa office, ta mantar da shi yiwa Danejo sallama. Ya kamo hanya shi da direba da dukudukun asubahi. Ko escourt babu. 

“Barka da zuwa” Marwah ta fadi tana murmushi. A hankali ya dago. “Barka kadai, If I guess it 

right, ina tare da Mrs. Engr. Zahraddeeni Maitama, kuma Hussainarmu. I appreciate your jobialness….. In ban bata ba, ke kika amsa wayata daren jiya, don na tabbata in don wannan Doctorn ce bani da wannan matsayin”. 

Ya fada yana nuna Safah da bakinsa. Dariya ta yi ta ja hannun Safah har kujerar dake kallon tasa, sannan ta ce, “A’a, Safah ce da kanta”’. 

Shima ya ce, “Ba zan yarda dake ba”. 

Shigowar Zahraddeen tasa suka katse jayayyar, hannu suka sake yi shi da Lamido, ya ce, “Zamu wuce Zaria yanzu, wish you all the best my brother”. 

“Allah ya kai ku lafiya”. 

In ji Lamidon. 

Suka yi musayen complementary card, ya ja hannun matarsa suka tafi. Takun tafiyar ma kamar ya yi mata saboda tsabar kulawa. 

Daga shi har Safah din suka bisu da kallo. Ko kai ka gansu sai sun baka sha’awa. 

“What a lobing couple”. In ji Lamido da zuciyarsa ta kasa boye sha’ awar da suka bashin. 

Ya mai da duban shi ga Safah wadda ke zaune kamar an dasa ta saboda tunanin kunyar da Marwah ta bata, wane bayani zata yi masa ya yarda cewa ba it ace ta fada ba? Ba ita ta amsa wayar ba bayan sautin su iri daya ne, ya sakko daga kujerar shi ya tsugunna a gabanta tamkar ya kwantar da kai a kafafunta. Amma bai yi hakan ba. Maimakon hakan durkuso ya yi sosai kamar bawa a gaban uwargijiyarsa. 

“Barka da safiya amaryar abdulkarim Naseer. A 

yau gani durkushe gabanki a gidanku, rokonki nake da kwanon barata a hannu, I’m begging for your hands in marriage. Zan samu Dr. Safah? Ba don na isa ba, ba don ina so in nuna isar ba. Sai don so da kauna na gaskiya, wanda babu sirki a cikinsa. 

Sunana Nasir Abdulkarim, a gida ana kirana Lamido. Ni mutumin Taraba ne, iyaye da kakanni. Nine da na farko a gidanmu, kuma ma’ aikaci ne. 

Matata Dijah kanwa ce a gareni, domin diya ce ga kanwar mahaifiyata, muna da yara biyu duk maza. Shin am I accepted? 

Aure ko gobe a daura shi, ba samartaka na zo ba, neman aure na zo na so da kauna. Idan har anyi duk wani bincike da ya kamata ayi a kaina……. kin karbe ni Safah?” 

Kalma kuma ta kare masa, domin wannan miskilar ba ta ce da shi komai ba. 

“To shi kenan Doctor Safah ……. wallahi in baki bude baki kin amsa min ba yau na hakura. Idan na tafi ba zan sake dawowa ba…….’ 

Idanunshi sun kada sun yi jajir a lokacin da yake wannan furuci. 

Ta tabbatar da gaske yake, mugun faduwa gabanta yake yi. Tsigogin jikinta ke tashi da azababbiyar soyayya, amma bakin ya kasa furtawa. Mikewa ya yi ya zura hannunshi a aljihun bayan wandon shi, ya fiddo wayarshi dake ta ruri ya am

“Kinga bana son kwarmato, ni yaro ne da zan bata a Abuja ko ya ya? Yanzu haka ma ni a 

Kaduna nake, amma a yau zan dawo ba kwana zan yi ba insha Allah”. 

Bai saurari komai ba ya kashe wayar ya tasamma kofa, ya barta daskare cikin kujera ta rasa abin da yake mata dadi. 

Juyowa ya yi ya yi mata wani irin kallo wanda ya samu damar yin shi kai tsaye cikin kwayar idanunta. 

Ita ta yi hobbasar russunar da idanunta, domin sun Zama masu rauni cikin nasa. Ya kada kai, sai kuma ya yi wani lallausan murmushi ya sa kai ya fita. 

Ji ta yi kamar ta bishi ta kamo shi, ko ta samu sassaucin soyayyar da ta yi mata dabaibayi, baki ya kasa furta ta. 

Wani zubin miskilancinta ita kanta yana burgeta, amma yanzu ta yarda wani lokacin yana cutar 

Ta tuno kalamansa. Ai sai ta yi hanzarin mikewa ta hada da sauri, gudu-gudu don ta cimmasa. 

Wayyo! Sai kurar da motar ‘Ferrari’ ta tayar, suka fice daga harabar gidansu. 

Ji ta yi tamkar ta yi ihu ta ce, ““Wayyo Allah!” Ko kuma ta sheka da gudu ta kirawo shi. 

Duka cikin biyun babu na zabi, abin nufi idan ta yi na farkon ko da cikin hayyacinta take kamar yadda ta tabbatar, za a lika mata hauka ne. 

Na biyun kuma karshen zubewar ajin diya mace kenan, musamman da yake ba shi kadai bane. Sai 

ta yi cikin gida da sassarfarta, ta dauki wayarta don ta kira shi. 

Nan ma ta ga duka cikin zubewar aji ne, don haka ta aje wayar gefe a kasalance da rashin sauran idea, ban da suyar zuci. Da cizon dan yatsa 

Abu na gaba da ya zo ranta kuma shine, ta kira Marwah tunda da alamar shiri a tsakaninsu ta gaya mata komai. 

Sai kuma ta tuno baranbarama irin ta Marwah, za ta yi sulhun ne beyond the limit. Sai kawai ta hakura. 

Kwana daya, biyu, har uku babu Nasir babu wayarsa. Ba ta fasa komai na hidimar rayuwarta ba, amma fa ramewa take a tsaye, zazzabi take a tafe. Wuni take hadiyar paracetamol amma kuzari da karsashinta babu shi. 

Da aka kwana bakwai ba ta ji daga Nasir din ba, gaba daya sai ta sukurkuce a daka, ta bar zuwa office don gudun kada ta turawa wani hakori a makogaro tunda ba ta da lissafi. 

A rana ta tara sai ga Dr. Safah, Dr. Garba ya daura mata karin ruwa a ofishinta, saboda rashin cin abinci, kuma ba ta so Mami ta sani shi yasa ta zo Office ya saka mata. Washegari ma haka. Amma a rana ta uku Dr. Garba ya ce ba zai kara saka mata ba, sai dai ya gayawa Mami ta daina cin abinci sai dai ta yi karin ruwa. 

Ta san shi sarai mutumin Mami ne, kuma a haife ya haifi sa’arta. Duk da kasancewar shi a karkashinta kamar Yaya yake a gare ta. 

Safah ta yi kuka har ta gode Allah, a rana ta goma da Nasir bai neme ta ba, ta ce, “Ni kuma haka Al

lah ya kaddaro min rayuwa, sakacina da miskilancina ke korar wadanda nakeso, duk wadanda nake so bana samun su, sai dai su barni da kunar zuci. Bayan sun kimsa mini soyayyarsu. 

Na so Zahraddeen na rasa, na so Imam na rasa. Yanzu ma kuma na rasa Lamido! Wanda nake da hope mai kyau a kanshi, ya koyawa zuciyata yadda za ta so shi sannan ya gudu ya barni. Ya ya zan yi da dimbin soyayyarsa da ta kankane a zuciya ta?” 

28 OK KK 

Tun Mami na zuba ido ta ji wata magana muhimmiya a kan Lamido Nasir, har ta hakura. Abinda ta kawo a ranta gaskiya ne wato miskilancin Safah ya kore shi, don ta ji komai a bakin Marwah, da dalilin da yasa ma har ya taso ya tako da asubah ya zo gidan. 

Wato dadin kalaman da ta gaya mishi a waya a zuwan Safah ce. Ta kare da cewa, “Wallahi ni na tabbatar tana son shi Mami, son da bata yiwa Zahraddeen ba. 

Amma ba za ta iya furtawa ba, ko ta nuna alama. Ba kowa ne zai iya fahimtar Safah ba, don haka ne masu sonta ke tafiya su barta. 

Saboda su a ganinsu wulakanci ne da rashin so, miskilancin ta da zurfin cikinta ya zarce misali. Amma ki bar komi a hannuna tunda Zahraddeen na da no. wayarsa”’. 

Mami ta ce, “Nima ban goyi bayan ki neme shi ba, ki zuba musu ido, in har yana sonta saboda Allah na tabbata zai dawo komai daren dadewa”’. 

Sai Marwah ta ga hangen mahafiyarsu gaskiya ne. 

Mami ta maida kanta kawa ga Safah, ta koma janta a jiki, da yawan zama tare da ita. Duk don son ta ji abin da ya kori Nasir Lamido. 

Daman dai ita ba wai son wannan aikin asibitin da take zuwa take yi ba, don haka ba ta takura mata sai ta koma ba, aure take so ta yi don yana gaba da komai. 

Don haka ta dora komai a kan Doctor Garba, tsohon likitan hakorin da yayo dukkan karatun shi a (Moscow). 

Ita kuma ta ji da ‘yarta wadda ta tabbata soyayya ce ke dawainiya da ita, wane soyayyar da aka yiwa Zahraddeen. 

Kamar kullum, to yau ma haka ta yi sallama dakin Safah, hannunta rike da plate shake da nunannen inibi jawur da shi, da tuffah ita ma bula-bula jawur da ita. 

Gefen gado ta zauna, a ya yin da Safan ke kwance da carbin dan yatsa makale a yatsanta na dama tana ta istigfari, don tana ganin alhakin Imam ne duk ya jawo mata al’amarin dake faruwa da ita. 

Mami ta zauna bakin gadon ta ajiye mata farantin a kan dan karamin teburin gilashi dake gefe. Ramammiya (in lobe) din ta muskuta ta mike zaune. ‘Mami ko na ci babu appetite babu taste a bakina”. 

“Hakan za ki daure ki ci, magana zamu yi mai muhimmanci. Amma sai kin cinye gaba daya kayan itacen nan tukunna”. In ji Mami. 

Ta dan fiddo jemammun idanunta? 

“Duka Mami? Ina laifin kuater?” 

Mami ta girgiza kai, “To ci rabi’. 

Ta hau durawa tana zubda kwallo, idanunta narainarai kamar ta saki kuka. 

Sai da ta ci yadda Mamin ta gamsu sannan ta kyale ta. Ita kanta sai ta ji dadin bakinta da cikinta wanda ke ta kugi, ko ruwan bunu ba a tarfa masa ba tun safe. 

Ta ji taste din dandanon harshenta ya dawo. Sai ta mika hannu cikin dan firjinta na bakin gado ta dauko madarar Hollandia (strawberry) ta cika tumbinta da ita. 

Cikin dan lokaci ta ji ta dawo hayyacinta, idanuwanta sun bude sosai. 

Ta yi murmushi, 

“Mami Allah Ya bar min ke!”. 

Murmushi ta yi, “Idan ke kina addu’ar Allah Ya bar miki ni, ni bakya yi min fatan Allah ya bar min ku, marayuna hudu, sanyin idaniyata. 

A’a, ke so kike kema ki tafi lahira ki barni da kewa, tun ban ga ‘ya’yanki ba”. Ta share idonta da gefen mayafinta, amma hawaye basu bar ambaliya ba. 

Kololuwar tashi hankalin Safah ya yi, ta yi azamar rungume mahaifiyarta. 

1““Me na yi Mami? Me na yi miki?” 

Ta ce, “Meye baki min ba? Kina son kashe ranki ta hanyar tunani, damuwa, da rashin cin abinci. Allah ya baki miji na arziki kin kore shi. 

Safah so kike ki tsufa baki yi aure ba? Meye laifin EFCC Abdulkarim Nasir? Wanne irin miji 

kuma kike hari bayan shi? Kada ki ce min har yanzu jiran Imam kike? 

To wallahi zan fita sabgar ki, idan baki tsai da mijin aure ba. Saboda ke ne har yanzu ban yi aure ba, don ba zan iya tafiya gidan auren wani in barki cikin gidan nan ba. 

Me kika yiwa Nasir? Ki gaya min gaskiya, me kika yi masa ya janye neman auren ki?” 

Kuka take sosai. “Ni Mami wallahi ban kore shi ba, ina son shi sosai Mami (ta yi subul da baka). Shi ya tafi da kansa, ya yi fushi kan dan abin da bai kai ya kawo ba”. 

Duk da hawaye ne a idon Mamin ba ta san sanda ta kama dariya ba. Abin da take son ji kawai kenan wato tana son Nasir ko ba ta son sa? 

“To mene ne abin da bai kai ya kawo din ba? Ke fa kullum a komai sai kin nuna ke ‘yar fari ce, maza yanzu lallaba su ake, balle ZARATAN cikinsu. 

Babbar asara ce a garemu rasa masoyi irin Lamido a wannan marrar. Cire miskilanci da kunya da ji da kai ki kwantar da murya ki ba shi hakuri, koma a kan mene ne ban takura in ji ba, in dai har bai kaucewa addini ba. 

Ba kuma zan tashi daga wajen nan ba sai kin kira shi a kan idona…….. ” 

Ta zaro ido sosai alamar razana. Mami ta gyada mata kai, sai kin kira shi zan fita daga dakin nan”’. Ba yadda ta iya, don ta ga Mami da gaske take. Sai ta ce, “In yi mishi tedt Mami?” 

Ta ce, ‘“‘A’a, kira bakida -bakv’. 

Ba ta doguwar jayayya da Mami, ba tun yau ba, 

tun ranar da ta sha mari a kan Zahraddeen. 

A hankali yatsun ta suka lalubo sunan LAMIDO NASEERR ….. suka kira. 

Ringing sosai wayar ta yi ta yi ba a daga ba. A karo na biyu da ta yi redialling ba ta jima tana kukan ba aka katseta. 

Ta ce, “To kin gani ko Mami ya katse”. 

Ta ce, “Kin fita a wajena ko babu sabulu, sauran lamari ki barwa Allah ki sa ido. Ba abin da ya gagare shi”. 

Mami ba ta idasa rufe bakinta ba sai ga sako (tedt) ya shigo daga Lamido Naseer, mai cewa. “Yau kin tuna dani ne?” 

“Kullum ma ina tunaka”. 

“Uhm! Kina tuna ni da me ne Safah?’ 

“Da SO da KAUNA, yarda da aminci”. 

Imagine! Ai a take sai ga kiranshi ya shigo, don nauyin Mami sai ta kasa dagawa. Mami mikewa ta yi ta fita tana yiwa Allah godiya cikin ranta, wanda ya sulhunta sha’anin aure, Allah kadai Ya san ladan da ya tanadar masa. A nan ina so in ja hankalin ‘yan’uwana iyaye mata, yawan alkunya tsakanin ki da diyarki mace ba naki bane, musamman wadda ta tasa. Hakkinmu ne mu ja su a jiki, mu zama kawayensu ta yadda za su saki jiki su dinga gaya mana halin da suke ciki mu dora su a kan tartibiyar hanya, maimakon mu barsu da kai matsalarsu ga kawaye wadanda ba lallai ne su basu shawara ta gari ba. Yawanci ma sai dai su dulmiyar dasu da gur

guwar shawara saboda kyashi da hassada. Nuna halin ko in kula ga ‘ya’yanki wai don kina ganin sun girma, sun yi ilimi, wallahi ba yi bane. Komin girman mutum a wajen iyayenshi yaro ne danye (Takori). 

Zan so na nado muku muhimmiyar hirar da ta gudana a tsakanin wadannan masoya a yau, to amma ta fi karfin takarda da biro su rubuta. 

Hira ce ta masu ilmi wadanda suka san abinda suke yi, ba ‘yan I lobe you……. I need u ba. Ta wani bangaren kuma, hira ce mai ratsa zukata, su kara aminta da juna, domin kowannensu a yau ajiye miskilancin nashi yai a gefe da ajin da mukamin, ya bayyanawa dan’uwansa sirrin zuciyarsa. 

Sun yarda sun amince da zama karkashin inuwar aure har gaba da abada, in akwai. A duniya da lahira, har a Aljannah suna fatan su rayu tare, su fadi tare sannan su tashi tare. Fatan ALHERI Safah da Lamido. Takori 

2K OK 

Daga dukkan bangarorin biyu, wato Taraba da Chikun, ba a samu tangarda ba. Haka binciken da Kawu Sufyan ya yi a kan EFCC Lamido, it probed positibe, ta fannin halaye, asali da sana’a. Shekarunsa goma da matarsa ta fari, ba’a taba jin kansu ba. 

Sai ma wajen binciken ne alamu suka nuna Nasir da Safah ‘yan’ uwan juna ne na jini. 

Hakan ya faru ne ranar daurin aure, daurin auren har biyu a kayi, wato Safah da Shahidah, wadda 

aka fara daurawa auren da angonta Ministan yada labarai Hafizu Ingawa, matarshi ta dade da rasuwa wajen haihuwar dansu na fari, yana nan dan shekaru biyar (Muhsin). 

Baffa Sufyan ne ya shigo da iyayen ango wadanda suka zo daga Taraba domin su gaisa da Mami da Hajiya Maama. 

Ai kuwa dagowar nan da Malam Abdulkarim ya yi sai idonsa cikin na ‘yarsa Mami. Ya ce, “Zaynaba nake gani ne ko kama ce?” 

Mami ta hau salati, “Baffan Taraba ashe ka san Lamido?” 

Sai ya yi dariya ya ce, “Iko sai Allah, to kenan ke ‘yar’’uwar amarya ce ko rashin zumuncin naki damu don kar mu raba ki da gidan marigayi mu tilasta ki kiyi aure yasa kike boye ‘ya’ yanki. Don dai na san ‘Yan Biyu na dade da sanin anyi musu aure”’. 

Mami dariya kawai take zuciyarta kamar madara don farin ciki, ta kasa ba da amsa sai Hajiya Maama ce take mishi bayani. 

“Ai ita Safah ba ta je gidan mijin ba suka rabu, tana ta karatun likitanci tsayin lokacin sai yanzu Allah ya kawo auren”. 

Sai ya fiddo waya ya kira Lamido ya ce maza ya ZO. 

Haka ya tsallake bankwanan da suke da jama’arsa ya zaro jiki ya shigo, amma mai tsaron lafiyarshi na biye da shi, inda duk ya cire kafa nan yake mayar da tasa. 

Yana shigowa falon bakinsa dauke da sallamar girmamawa, a nutsensa yake tsaf, babu abin da ke 

firgita shi a rayuwa. Mutum ne mai karfin zuciya da karfin imani. 

Wannan ne ke sayo mishi kwarjini na musamman a duk inda ya shiga. Ita kanta Mami sai da ta firgita da BABBAN GORON da diyarta ta samo. Sai dai firgicin nata bai yi tasirin da ya bayyana a fuskarta ba, ‘yarta ma BABBAN GORO ce, lallai da ake cewa “Babban Goro sai magogin karfe”. (Takori). 

Har kasa ya kai gwiwoyinshi yana gai da Mami da Hajiya, ba sai an gaya masa ba, kallon farko ya ga fuskar Marwah cikin fuskarta. Sai ya kara kwanciya sosai kamar zai yi mata sujjada saboda kauna da girmamawa. 

Mal. Abdulkarim yana murmushi ya ce, “Ka ganta nan Yayarka ce, da kakanta da kakana na wajen uwa, uwa daya uba daya suke. 

An dade da aurenta da Aliko sun zo bikin wata ‘yar’uwarmu da ta yi aure a Chikun, a can ya ganta ya bita gida Yola ya aure ta. 

Abin da yasa baka santa ba tuntuni, Aliko baya kaita Yola. Bayan rasuwarsa kuma babu yadda bamu yi da ita ba kan ta koma gida ta sake aure ta ki, da ta ga an takura mata ma sai ta yanke zumunci da kowa, ko ‘yan Yola sun zo sai ta ki yarda ayi maganar komawarta, ka ji dalilin da yasa baka santa ba”. 

Cike da farin ciki Lamido ya dago ya sake matsawa jikin Mami kamar ya rungume ta, sai ta daura hannunta a kan kafadunshi ta ce. 

“Wai Lamidon Hajiya Nadeeya da ka kai karatu Legas shine ya zama mijin Safah? Ni duk zuwan 

da yake bamu taba gaisawa ba, amma na rasa dalilin da yasa zuciyata ta karbe shi tun ba ta ganshi ba”. 

Haka dai aka yi ta hirar zumunci da tuna baya, duk yadda Malam ya so su koma Taraba a ranar hakan bai yiwu ba, Mami ta ki, tasa aka share (guest-room) na Daddy suka kwana a can. Washegari suka yi asubanci Taraba ta diba. 

Ranar ta kasance ranar wunin biki, a nan harabar gidan aka yi. 

Washegari walima ce itama ta mata zalla Mami ta shirya. Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi ita ta wa’azanci mata a ranar, a kan darajar aure da wajibtakar sa a Musulunci. 

Ta kawo darajojin da Allah ya yiwa matar aure da daukakar ibadarta a kan ta mara aure. Me maza na gari ke so a mace? Meye basa so. 

Lacca ce ta yi sabon salo irin wadda ke cakude da ilimin musulunci mai tafiya da zamani. Wanda yawanci ta zakulo su ne daga rubutun (Aisha Lemu). 

Banda wannan Mami ba ta yarda da kowane program ba. Ta ce albarka ake nema ba bidi’a mara amfani da almubazzaranci ba. 

Sai dai shima angon ‘yan office dinsa sun shirya liyafar cin abincin dare a hotel din NICON wanda za a gudanar bayan an kai amarya Abuja. 

A karo na biyu Mami ta yiwa amarya nasihar zaman aure tana kuka tana rokonta ta jure ta zauna a gidan aure, wannan ne kadai kwanciyar hankalinta, da dadi da babu dadi ta horeta da hakuri sakamakon kananun maganganun da ta soma ji 

daga bakin ‘yan’uwanta na Yola a kan Danejo, suna cewa ma wai kwata-kwata ba ta san anyi auren ba. 

Motoci ne in an anbiable-array (a jere reras) har guda goma bakake sidik firda-firda daga Kaduna har Abuja. 

Tankareren bungalow na amaryar na nan a unguwar Asokoro. Wani irin American Billa tamkar kana cikin daya daga flats din New York. Tsayawa fasalta tsarin gidan ma sai ya zama bata lokaci, dan haka babu abin da babu, babun ce kurum babu in ji Malam Bahaushe. Yayin da aka wuce da Aunty Shahida nata gidan a Ministershill. 

Suna isowa ko zama basu yi ba, sallar magariba suka fara yi zuwa isha suka yi wanka aka sake shir1 aka kwashe su zuwa Nicon – Noga, a can ne angon ya tari amaryar da kansa, don shi ya bude mata kofar mota da kansa ya rungume ta ya sumbaci goshinta, ya rada mata cikin kunnuwanta. “Welcome to the new and wonderful life, full of lobe and happiness”. (Ina miki maraba da shigowa sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki da so da kauna). 

Ina rokon Allah Ya bani ikon rike ki da amana, da soyayyar da bata yin rauni, sai ranar da na bar duniya”. 

Dago fararen idanunta ta yi ta dube shi, kwayar idanunta narai-narai da hawaye, kwayar idanunsa ta tabbatar mata da abinda ya fada, haka yake har zuciyarsa. 

Ita kanta ta yarda ta shigo sabuwar rayuwa, wal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *