FUSKA UKU COMPLETE

 FUSKA UKU COMPLETE

Zaune take saman k'aramar kujera irin wanda mata ke amfani dashi a madafi...  Yanda ta rafka uban tagumi ga buta ijiye gabanta zai tabbatar maka cewa cikin damuwa take,  da alama alwala take shirin yi amma ko gizau da butan gabanta bata yi ba, tayi nisa matuk'a cikin duniyar tunani.... 

A haka ya fito daga makewayi ya kuwa hangeta yanda ya barta nan duk'ufe gaban buta...  Girgiza kansa kurum yayi ba tareda ya furta koda kalma kafin ya k'arasa gaban k'aramar randar da kansa ya d'ibi ruwa ya tada nasa alwalan...  Abin mamaki har yakai ga ida alwalansa wannan baiwar Allah sam batako motsa daga tagumin da tayi ba...

Cikin tsanaki ya warware hannun rigarsa kafin ya d'au karan goge bakinsa ya saka cikin bakinsa,  lokaci guda ya k'araso yanda take a zaune....

"Bilkisu..!"  Shiru bata amsa ba...  D'an bud'e muryarsa ya kuma yi a karo na biyu

"Bilkisu..!" 

Sai a sannan taji kiran nata da yake yi....

Saida ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya had'i da muskutawa kana tace "Malam wai har an sauk'o daga masallacin ne...?"

Yanda ta masa tambayar yaso basa dariya amma ya d'an gimste yace "Kiyi alwala kiyi sallah idan na dawo sai muyi maganar kinji koh...  Amma wllhi wllhi kinji na rantse maki ban yarda ki tafi bariki neman d'anki ba,  wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa tunda shi bamu da daraja bamuda mutunci a idanunsa,  na tabbata akwai ranar da zai nememu da kansa basai kin tafi nemansa ba,..."

Baikai aya ba murya na rawa ta katse sa da fad'in "Malam wllhi ni nasan ba laifin d'ana bane tsinanniyar matar nan tasa ita ta shiga tsakaninmu dashi,  wllhi nasan yana son zuwa gida amma bazai iya ba sabida ta jik'a ta basa yasha,  kasan matan bariki sunfi maciji guba... Malam don Allah ka min izini na fita na nemo shi, yau fah kusan shekara kenan tim rabonmu dashi...."

Shiru Malam yayi tamkar mai nazari had'i da yin gajeren murmushi kafin ya girgiza kai yace "Mata kenan,  akan 'ya'yayenku zakuyi komai kuma zaku d'aura laifi kan 'ya'yan wasu ku wanke naku 'ya'yan... Shin kin tab'a sanin kalan matar tasa?  Kinsan yaya akayi aka nema auren,  kinsan wanda ya tura a matsayin wakili....?  Duk baki sani ba,  rana guda ya shigo tsakar gidan nan ya sanar damu yayi aure kuma bai buk'aci albarkan ko guda daga cikin mu ba...  Sanin kanki ne tunda muka gama d'awainiyar karatunsa ya girma ya zama mutum ya tsallake k'afafu ya rabu damu,... Toh ina mai tabbatar maki kada ki kuskura ki d'aura laifi kan koma wacece ita matar nasa,  wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa..  Laifina guda gata da na nuna masa da yawa, cikin sa'anninsa da suka taso tare a garin nan shi kad'ai ne ya tafi makarantar kwana na yaran hamshak'ai,  kai tun daga alimantari d'insa karatu mai inganci na basa,  idan baki mance ba har gona ta da shanayena na gado duk na sayar a dalilin na inganta rayuwar yaron nan amma ga sakayyan da yayi min, kar dai ki mance mahimmacin shanayen gado wajen bafillace....  Tabbas sai yanzu nake hango maganganun su Malam Dalha,  shi yaro ba'a masa haka,  yanda ka tarbiyartar dashi toh kuwa haka nan zai tashi maka,  baisan babu ba tun tasowarsa shiyasa ya girma yana jin nauyin ya nunamu yace ga iyayen sa,  na masa mai wuya tunda na turasa har k'asar waje yayi karatu ya sami abin yi....  Babu komai yajesa duniya ce tafi gabaruwa iya jima, bazan masa baki ba sannan bazan saka damuwarsa cikin zuciyata ya dameni ba,  kuma kema ina shawartar ki da ki cire tunaninsa cikin zuciyarki domin hakan ne kurum zaifi maki sauk'i, mu zuba wa sarautar Allah idanu, rayuwarsa ce yayi yanda yaso da ita,  duk yanda yaje yazo nan dai shine cibiyarsa kuma mahaifarsa....  Na wuce masallaci kinji liman har ya tada ik'ama, maza kema kar na dawo na sameki wajen nan...."  Bai jira cewarta ba ya fice cikin sassarfa...
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *