ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 1

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 1

Da ka doso garin Giwa gidan 

za ka fara hanga daga gabas masu kudu na garin, tangamemen gida da aka yiwa jan rufi na zamani mai zagaye da girgijejen gate na bakin karfe 

da aka fi kira da Mahdi-ka-ture. Dauke yake da (estate) guda wanda ya hadiye gidaje na zamani (flat) guda goma sha biyar. 

Idan ka daga kanka sama, rubutu ne da aka yi da ruwan gwal mai sheki an rubuta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ESTATE. Gidaje ne reras (dispersed) masu sanyin gani a ido da _ fenti ruwan gwaiduwar kwai. Gida daya ne ya bambanta da wadannan gidaje guda goma sha hudu wato gida na farko. 

Gida na farko ya fi duka gidajen girma, kuma shi kadai ne mai hawan_ bene. Mamallakiyar wannan babban __ gida tsohuwa ce ‘yar kimanin shekaru saba’in da biyar mai amsa sunan HAJIYA HADIZA GIWA, wadda ‘ya’ya_ da jikokinta ke kira da HAJJAH. 

Za ka yi mamaki idan ka ji cewa, duk girman gidan nan ita kadai ta yi rayuwa a cikinsa a matsayin matar gida, haka duka 

‘ya’yayen nan goma sha biyar ita ta haife abinta daya bayan daya, babu dan miji babu dan kishiya a ciki. 

Wannan ya faru ne a cewar al’ummar garin Giwa a sabili da kaunar da marigayin mijinta Abubakar Bamalli Giwa ke mata, da kuma _ kyawawan_ halayenta’ da kyakkyawar mu’amala da kowa. 

Don haka ne bayan rasuwar A.B Giwa ‘ya’yansa ba suyi maraici mai yawa ba. Hajja ta zamo bango abar jinginarsu, wannan kuma baya nufin cewa sakar musu take yi, a’a, akwai tarbiyyar sannan akwai (discipline) ga duk wani da ko jikan Hajjah. 

Babu wanda za ta sakawa kara ya tsallake, babu wanda za ta cewa eh, ya ce mata a’ah. Babu wanda zai zartar da wani hukunci a kan gaban kansa ko iyalinsa ba tare da izininta ba. 

Mace ce mai kyakkyawan tunani tare da kaifin basira, ta yadda duk wani motsi da ‘ya’yanta ko jikokinta suka yi ta san me suke nufi. Mutum ce kaifi daya ba ta zance ta canza. 

Haka duk kaunar da take gwadawa ‘yan 

jikokinta ba za ta taba yarda karami ya kawowa babba raini ba. Jikokinta suna kaunarta sosai fiye da iyayen da suka haife su. Yawanci da daya da daya suka zame kayansu suka dawo nan (Babban gida kamar yadda suke cewa) wurin Hajja. Don a cewarsu, sun fi jin dadi gidan Hajja, abinci kala-kala kala-kala sai wanda suka zaba,tana kuma basu labaran hikaya da tatsuniyoyi na dabarun zaman duniya, tana rungume su komai girmansu ta rarrashe su ta ji abin da ya dame su idan iyayensu sun bata musu rai. Amma hakan ba ya nufin idan ka yi laifi ta sanya Baban Giwa ya hukunta ka, don dai ita dai ba ta iya dukan jikokinta in ba da mahuci ko rankwashi ba. 

Haka nan bayan ran A.B Hajiya Hadiza ta tsaya tsayin daka_ wajen _ tarbiyyar zuriyarsa, tare da kiyaye auratayya tsakanin jininshi. Har yau, har gobe Haj. Hadiza na bisa kudurin mijinta A.B Giwa na gama auratayya tsakanin jininshi, suna so ko basa so, in yaso daga baya su suke sanin yadda suke yi su shirya su so juna a bisa dole har su zo suna gode mata. 

Hakan ne ya haifar da yaduwa da fadada 

hadi da watsuwar zuri’ar A.B Giwa cikin garin Giwa da wajenta, inda kuma duk suka shiga dole a gane su, saboda kamanninsu da tsagin Mallancinsu dake gefe da gefen fuskar kowannensu, wanda wanzamin gidansu ke yiwa kowane yaro da kowacce yarinya ranar radin sunansa. Duk da cewa sun kebe kansu cikin Estate dinsu, sana’ar neman abinci ko aikin gwamnati na fiddasu cikin garin Kaduna ko Zaria 

A cikin gidan A.B Giwa, bayan jikokinta akwai dangin mijinta mai rasuwa, ‘ya’ yan ‘yan’ uwanta Kaltume da Kubra, dukkansu zawara ne. Kuma da yake sun manyanta sai suka zamo masu jibantar ayyukan gyaran gidan da harkar dahuwar abinci, duk da akwai wadatar masu aiki a gidan. Bangaren ‘ya’ ya maza (Boys quaters) shi Hajja ta ware daga farkon gidan wadanda ga gidajen iyayensu amma sun gudo sun tare mata har girmansu. Sauran jikokinta ‘yammata da suka tasa duk ta aurar dasu a nan cikin Giwa ko Zaria da jininsu, mafi yawa na cikin Zaria, ‘ya’yan Hajja goma sha hudu ne, maza goma mata hudu. 

Abubakar Bamalli Giwa hamshakin mai arziki ne na da can-can shekaru aru-aru da suka wuce. Asalinshi Bamalle ne na garin Giwa, iyaye da kakanni, sana’arshi noma ne na kayan abinci (crops production) su masara, gero, achcha, dawa, alkama, shinkafa, dankali, doya da kayan miya, su yake nomawa duk shekara a loda a DafDaf zuwa kasuwannin garuruwa masu bukata. 

Ya mallaki tafka-tafkan gonaki sama da goma a cikin garin Giwa, wadanda shima gadarsu ya yi. Gidajen haya bila adadin a cikin Giwa da Kaduna, har ma da Zaria. 

A duk shekara ya kan nome amfanin gona mai yawan gaske, a nan ake loda su a buhunhuna zuwa kasuwannin garuruwa 

daban-daban. 

Zai yi tsayi in fayyace ko in lissafo sunayen zuri’ar Abubakar Giwa daya bayan daya, amma babban su shine Alh. Mukhtar Abubakar Bamalli wanda ke jagorantar reshen BAMALLI FOOD CROPS AND CASH CROPS PRODUCTION na Kaduna, wato wakilin kasuwancin kayan gonarsu na reshen jihar 

Kaduna baki daya, don haka zaman shi da iyalinshi ya fi yawa cikin kaduna, duk da gidansa na nan cikin A.B Bamalli Estate, in sun zo Sallah ko biki budewa kawai suke yi su share su shiga. 

Sai Ahmadu A.B Proffesor ne a jami’ar Ahmadu Bello a tsangayar harkokin noma da kiwo, gidansa na nan cikin jerin gidajen malamai na A.B.U Zaria, kamar Baban Kaduna (Alh. Mukhtar) shima gidansa ne na biyu a A.B Bamalli Estate. Yadda Alh. Mukhtar ke zuwa da _ iyalinshi suyi kwanaki ko sha’ani, haka yake zuwa da nashi. 

Alh. Na’ibi Abubakar Bamalli ke bi mashi, gidanshi na nan cikin Estate shi ke kula da gonakinsu. Sai Ibrahim A.B, mai kula da gidajen hayarsu na cikin Kaduna. Barau A.B shine ke kula da Distribution (rarraba) amfanin gonakinsu) zuwa garuruwa, shima cikin Estate yake shi da iyalinsa. Sani A.B, Sadi A.B da Salisu A.B, kowanne da bangaren da _ yake jagoranta cikin hanyar neman abincinsu. 

Sai Aunty Hauwa wadda ke auren dan aminin marigayi A.B wai shi Alh. Sabi’u 

Kwangila da ‘ya’yanta biyar, suna nan cikin Kaduna a unguwar Malali. Yaya Ladidi ke bi mata, ita kuma Zaria take aure unguwar Tudun Wada. Sai Yaya Hafsatu dake aure nan cikin Giwa. Aunty Rabi (autar Hajjah) ita ce kadai mai karancin shekaru a cikinsu. ‘Yar kimanin shekaru ashirin da bakwai, shekarar baya ne aka yi auren ta da Yaya Muftahu dan kanin A.B wanda aiki ya hulla shi Kano, yana aiki da gidan wayar Zain. 

Kwari irin na Hajiya Hadiza wannan ba zai rasa nasaba da jin dadin da take samu wurin ‘ya’yanta ba, domin a kulli yaumin kamar ana kara mata kwari da kuruciya ne, ba za ka yarda da tarin shekarun da take dasu ba a fuska da yanayin jiki. Ita kanta ba dukiya kadan ta mallaka_ wwurin marigayin miujinta ba, iyayenta § da kakanninta ‘yan asalin Zaria ne tushen unguwar Tukur-Tukur. 

Marigayin mijinta Alh. A.B Giwa shine dan garin Giwa ba ita ba, ita aure ya kawo ta. Haka bayan ranshi ba ta tsallake ta bar wannan muhallin da suke ciki ba ita da 

‘ya’yanta. Tana kokarin hada kansu ba tare 

da sun yiwa mahaifinsu nisa ba, don kara killace zumuncin su. Basu aure mace ko namiji sai cikin zuri’ar su (jinin su).

Wannan ne ya sanya suke kama da juna, inda duk ka gansu in ka san daya daga cikinsu za ka gane su. Farare tas-tas masu dogon hanci da yalwar idanu da garin jiki (girma da tsayi). Da an gansu an san su, in ba ta tsagin ba ta kamannin, in ba ta kamannin ba ta jin kai da yanga, daga matansu har mazansu.

Mutane da yawa kan ce zuri’ar A.B sun fiya girman kai da dagawa, amma a zahiri nutsuwa ce kawai da Allah ya haliccesu da ita da tsabar sanin ciwon kansu, domin dukkaninsu ilimi na Muhammadiyya da na zamani ya wadaci kwanyar su.Har kullum arzikin A.B karuwa yake, domin basa wasa da hakkin Allah cikin dukiyoyinsu (Zakkah).

Har zuwa inda yau ke motsi tun bayan ran marigayi A.B, ba a ko taba kwatanta auren bare cikin zuriyar sa ba, don a ganinsu auren bare zai bata musu family,

Zai jawo rarrabuwar kamanni, ya rarraba musu kan ‘ya’ya, kuma ya haifar da sauyin kamanni cikinsu. 

Hajjah duk da kasancewar mace ce mai fada a yawancin lokuta, amma fa in ka iyawa halinta ka fahimci likes and dislikes dinta, to ta fi ruwan sha saukin sha. To haka gaba daya ‘ya’yanta suke lallaba ta, suke faranta mata, ba ta da ciwuwwukan da tsofaffi ke fama da shi ko daya irin su sukari, ciwon kafa, hawan jini ko rikicewar girma. Musamman babban danta Alh. Mukhtar ya fi kowa iya zama da ita da tattalinta da yi mata biyayya a bisa dukkan umarninta. 

A cikin Estate din akwai babban masallacin da suke haduwa suyi dukkan salloli biyar a kan lokaci, bangaren maza daban, an sanya labule tsakaninsa da bangaren mata. Yaransu da manyansu da wuya ka ga suna sallah a cikin gida in ba da wata babbar lalura ba. 

An hore su da sallah da kula da lokacin yin ta. Da zarar Baba Barau (Limamin A.B Mosque) ya yi kiran sallah kowa zai aje 

da sun yiwa mahaifinsu nisa ba, don kara killace zumuncin su. Basu aure mace ko namiji sai cikin zuri’ar su (jinin su).

Wannan ne ya sanya suke kama da juna, inda duk ka gansu in ka san daya daga cikinsu za ka gane su. Farare tas-tas masu dogon hanci da yalwar idanu da garin jiki (girma da tsayi). Da an gansu an san su, in ba ta tsagin ba ta kamannin, in ba ta kamannin ba ta jin kai da yanga, daga matansu har mazansu.

Mutane da yawa kan ce zuri’ar A.B sun fiya girman kai da dagawa, amma a zahiri nutsuwa ce kawai da Allah ya haliccesu da ita da tsabar sanin ciwon kansu, domin dukkaninsu ilimi na Muhammadiyya da na zamani ya wadaci kwanyar su.Har kullum arzikin A.B karuwa yake, domin basa wasa da hakkin Allah cikin dukiyoyinsu (Zakkah).

Har zuwa inda yau ke motsi tun bayan ran marigayi A.B, ba a ko taba kwatanta auren bare cikin zuriyar sa ba, don a ganinsu auren bare zai bata musu family,

gidansa ko a kan iyalinsa face da sanin ta, da amincewarta. Haka igiyoyin auren da take kukkullawa a tsakaninsu basa ganin bekenta, domin duk wanda ya bi ko ba da son ransa ba, daga baya sai ya ga amfaninsa. Don haka duk cikin samarin da ‘yammatan da suka tasa babu mai tunanin yin budurwa ko nuna ga wanda yake so, sai wanda Hajjah ta ga ya yi mata dai-dai ta hada su. 

A halin yanzu dai yara uku ne mata a gabanta da basu haura shekaru_ bakwai zuwa takwas ba, duka jikoki ne, Ummi, Zanirah da Fa’iza. Samarin maza ‘yan sakandire da na jami’a sune Allah ya yi yawa dasu a gidan. Duk sun baro gidajen iyayensu sun tare a baskwata din Hajjah. 

Ba ta nuna damuwa sam, kamar yadda ba ta takura da zaman su, ita dadi ma take ji duk inda ta juya ta gansu, tana bari-bari ko suna hirarsu ta jika da kaka cike da kauna da fahimtar juna. 

Dadi take ji ta ga jikokin nan nata sun zagayeta, wannan ya tsokani wannan, wancan ya tsokani wancan, ta yi ta shari’a, 

ta yi ta bari-bari ko ta kai musu duka da mafici. 

Sai dai Hajjah ta raini jikokinta da kyakkyawar tarbiyya ta yadda babu yadda za ayi ka ga karami ya kawowa babba raini, ko ka ga da wuya macen da ta tasa ta zauna kusa da mazan ko kokaye-kokaye, haka nan duk motsin da dayansu zai yi, to a kan idonta ne. 

Yanzu kam hankalinta duka yana kan ‘yan matasan jikokin nan nata mata guda uku da suka saura a gabanta ta dage wurin tarbiyyar damu. Wato ni, Ummi (Khadija) da Zanirah. 

FA’IZ, Da ne ga babban dan Hajja Alh. Mukhtar, kuma rayuwarshi ta dawo gidan Hajja ne tun daga shekarun yaye ba kamar mu ba. Kaunar Hajjah da Fa’iz daban ce da duk sauran jikokinta, saboda shi kadai ne me sunan marigayi A.B wato (Abubakar), kuma a cewar ta kullum Yaya Fa’iz shine photocopy na A.B Giwa, daga kamanni har halayya. 

Fa’iz ya shiga ran Hajja fiye da duk ‘ya’ya da jikokinta. A cewar Hajjah, Fa’iz 

yaro ne mai shiga rai, kuma mai nuna mata kulawa fiye da kowa a zuri’ar. Komi Fa’iz ya samu na Hajjah ne, baya kyashin kadar da komai nasa wayjen faranta mata, musamman kasancewarta ma’abociyar cin farin goro da mu’amala da man zaitun, habbatus-sauda da turaren miski a jiki da 

tufafinta. 

Tun yana karami ya san yadda yake samar dasu gare ta baya bari ta neme su bayan sun kare sai dai wani ya tadda wani, daga Abubakar-Fa’iz da take kira (Hafizi), kasancewar shi mahaddacin Alkur’ani a shekaru na goma sha biyar. Zai kuma iya karya harshe ya karanta shi tiryan-tiryan da dukkan kira’ar Hafizan da muke dasu a Saudiyyah, irin su Abdur-Rahaman Sudaith, Jabir da Abdur-Rahaman Bn Marwan Al-Juhainy da Khusairi. 

Fa’iz ne kadai ya yi karatun sakandire a birnin Madinah Al-Munawwarah, daga aljihun Gwamnati. Yana da shekara goma ya yi musabakar izfi talatin daga jihar Kaduna ya samu sponsorship zuwa wata sakandire a Madinah. 

Ya dawo gida yana da shekaru goma sha 

bakwai, ya kuma zabi gidan Hajjah a matsayin gidan zamansa maimakon gidan mahaifinsa Alh. Mukhtar a cikin Kaduna. Daki guda Hajjah ta ware ma mijinta Fa’iz a Boys Quaters da duk abin da zai bukata, sannan 1n ta ji shi shiru kullum kafarta na hanyar dakinsa don ganin “ko lafiya Hafizi baka shigo ba?” 

Sai ya ce, “Akwai abin da nake yi ne Hajja, zan shigo anjima kadan”. Haka suke a kullum. 

Zanirah kanwa ce ga Fa’iz, wato ita ma diyar Baba Mukhtari ce, zamanta gidan Hajjah ya samo asali ne tun wata tafiya da mahaifiyarta Mama ta yi aikin Hajji tana Shekara hudu ta kawowa Hajja ita. Bayan dawowar Mama kiri-kiri Zanirah ta ki gidansu. Ita da Jabi Road sai hutu, shi din ma ba kowanne ba, sai wanda ta ga dama. 

Babban Yayansu shine Bashir wanda ke karatu a matakin farko na jami’ar Ahmadu Bello, sai Fa’iz wanda a bana ne ya kammala sakandire, Abdulhakim ke bin Fa’iz, sannan Shu’ aib, Yahaya, sai Zanirah da autansu Abbas da muke kira (Junior). 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *