UMM ADIYYAH CHAPTER 86 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
gaza yarda za ta zo ta yi shi da TJ. Ne
suka ji sa makulli, sai ga sallamar Zaid ya
shigo.
Cikin fara’a suka yi musabaha da TJ. Sannan
ya ce “Madam, sannunku da zuwa.”
Jakar kwamfutarsa ya ajiye da kwat dinsa, san-
nan ya dawo ya zauna a kujerar da
Umm Adiyya take zaune da Minaal a han-
nunta, idan ka gansu sunyi dagwas dasu
kamar ka sace, take TJ. Ya ji wani abu ya
murda masa, amma ya yi murmushi
kawai.
Saboda ya san mutum baya taba wuce rabonsa,
kuma Umm Adiyya da Zaid an yi su
ne domin juna ko yadda suka dace, yadda koo
wane motsinta akan idanun Zaid,
yadda suke yiwa Minaal wasa, daga gani ba
abinda suke so irin yara dukansu biyu.
Suna da wani gamayya na jini da kai na gefe,
idan ka zauna da su dole ka ji abin ya
ratsa ka.
To mun gaisheku, za mu wuce, magariba ta
kawo jiki.” TJ. Ya fada yana yunkurin
**************
Bayan kwana biyu ne ya zo ya dauketa saboda su
tafi yin VISA (Biza), sai a lokacin
ta fahimci inda za su je. kasar Jamus ne.
Daga nan kuma suka fara shirin tafiya, ba
kama hannun yaro. Wani aikin ne zai kai
shi daga nan kuma za su dan zagaya, sai su
dawo, tafiyar ta kwana goma ce.
Nan da nan ko Umm Adiyya ta yi masu shiri,
ana gobe za su tafi, ya kai ta gidan Anti
A’isha da gidan Abba ta yi masu sallama, san-
nan suka kama hanya. Aikin sa a cikin
Hamburg ne. Don haka nan suka fara yada
zango, har ma suka kaiwa Masdook da
Mihjanaa ziyara, sai da ya kammala abinda ya
kawo shi. Sannan ya wuce da ita
garin Göttingen.
*************
Tun safe ta gaza zaune ta gaza tsaye, ga shi Zaid
ya fita, duk ta rasa abinda ya ke
mata dadi, tana ta sake-sake a ranta. Ji take yi
kamar abubuwa suna mata yawo a
kuka ba.