YAR ALMAJIRA CHAPTER A
Umma! umma!! umma!!! “kitashi karki mutu kibarmu a cikin wannan rayuwa me cike da tarin bakinciki da kuncin zuciya dan Allah umma kiyi hakuri ki bude idanunki” kuka sosai takeyi me cin zuciya, tana jijjiga ummanta dake kwanta akan wani tsamurarren katifa, ganin dai har yanzu umman taki motsawa yasa ta fita waje dan neman agaji, abun mamaki tana fitowa naga wani hadadden gida agefe me cike da abubuwan ban mamaki da al-ajabi, sake kallon ta nayi sannan na kalli d’akin data fito aciki, tunani nafarayi kodai 6angaren yan aiki ne ko kuma d’akin matar me gadi ne toh koma dai miye bari zan binciko mana daga baya.+
Wani me adaidaita ta tsayar sannan ta rokeshi akan ya taimaka mata su d’auko mahaifiyarta daga ciki, dafarko yak’i yarda saboda tsoron irin hali na d’an adam awannan zamanin daga baya kuma ya amince suka shiga suka fito da ita, basu tsaya ko inaba se government hospital dake cikin garin bama, kasancewar weekend ne asibitin shuru ba hayaniya ba kuma mutane dayawa, bayan anshigar da ita ta biya kudin me adaidaita sannan ta shiga dan biyan kudin ganin likita, wani kudi naga tafito dashi kamar tsumma duk ya kod’e ya sha lik’i kallon kudin ta tsayayi tana hawaye kamar bazata mik’a ba, ganin haka yasa account din taji tausayinta tace tabari zata biya ai dari biyar ne ba komai insha Allahu baze gagara ba, godiya tayi mata bayan ta karb’i reciept sannan takoma gefen emergency inda aka kwantar da umma, tana zuwa likitan yafito yana share zufa kallonta yayi kafin yace “kibiyoni office dina”.
Bayan sun shiga ya nuna mata gurin zama sannan ya bukaci reciept kafin ya fara magana kamar haka “agaskiya mahaifiyarki tana shan wahala, shawara daya ce kufitar da Ita waje ko kuma ku rasata domin tana bukatar wannan aikin da gaggawa”.
Kallonshi tayi tana hawaye kafin tace “likita banida yanda zanyi domin banda wanda ze taimakamin ni nake bara nake aikin dako nake ciyarda mu dani da kannena biyar da kuma mahaifiyarmu, da ace inada hanyar da zan iya taimakon mahaifiyata afitar da ita danayi, ko kuma da ace inada kudin biyan aikin dana bada nawa ansanya mata domin bamuda kowa se ita” takare maganan tana kara sautin kukanta.
♣🌹♣☘♣🌻♣
Agida kuwa Amina,Habiba da Nusaiba sunata sharban kuka domin sun tausaya wa umma sosai ayanayin datake ciki, tabbas suna ganin rayuwa da jarabobi kala kala, umma itace gatansu yanzu kuma tana cikin halin rayuwa ko mutuwa domin kuwa indai bawani ikon Allah ba sunsan ayanda aka fitar da umma daker tadawo musu, suna cikin haka hauwa’u da Khadija suka dawo daga kasuwa gurin da Fateemah take wanke wanke awata me saida abinci kasancewar ciwon umma ya tashi da dare shiyasa sukaje domin ta basu ranchen kudi sukai umma asibiti, suna dawowa sukaji abunda ke faruwa nan suna suka bud’e shafin kuka kamar ance musu ta mutun.
Umma wato (Maheeda) d’iya ce ga marigayi alhaji aliyu bomoi, mahaifinta shahararren malamine kuma hamshak’in mai kudi, mahaifiyarta ta rasu tun aranar da aka haifeta, umma yar gata ce gaba da baya kuma yar sarauta domin mahaifiyarta d’iyar sarki ce mahaifinta kuwa na rike da mukamin hakimin gari, umma su biyar ne a gun mahaifinsu, hud’un yaran yadikkon ta ne wato matar babanta, mahaifiyarta itace ta biyu agun mahaifinta, kasancewar ta me sunan mahaifiyar babanta yasa take samun soyayya fiye da sauran yaran sannan kuma gata marainiya tausayin ta ya karu azuciyar mahaifinta, hakan yasa yadikkonta salame ta tsaneta kuma take kishi da ita domin tasan yanda mai gidan ke son marigayiya, gashi kuma son ya shafi d’iyarta har ake nuna banbanci tsakanin ta da yaranta injita da fada, haka rayuwa ya cigaba da tafiya musu har tayi aure tabar musu gidan inda matar babanta tayi sanadiyar mutuwar mahaifita dan taci gado sannan kuma ta raba ta da danginta aka manta da ita kuma tayi sanadin rushewar rayuwar aurenta….
Ni sunana fateemah ana kirana da Noor kasancewar naci sunan kakarmu ta wajen uwa, mun tashi cikin gata irin wanda ko wani ‘dan adam ke son kasancewa aciki, mahaifin mu babban attajirine wato Dr muhammad Nura, mu shida ne agun iyayenmu, nice babba shekarata goma sha-shida se Nusaibah me shekara goma sha-hudu sannan Hawwau me goma sha biyu, Habeeba nada shekara goma, Aminatu yar shekara takwas da autarmu khadijah mimi me shekara bakwai wacce taci sunan mahaifiyar babanmu, kuma tsakanin su da Aminatu ba nisa mun kasance yan gata kowa nason mu kota wani 6angare kwasam se wani abu yafaru wanda yasan yamu cikin wani haki na kuncin rayuwa mun rasa mahaifin mu alhali yana raye mun rasa dangin mu na kowani 6angare alhali suna raye sannan gashi wacce muke gani muji dadi tana cikin wani hali .
♣🌹♣☘♣🌻♣
Se guraren karfe biyu umma ta farfado daga doguwar sumar da tayi, farinciki ne ya cika zuciyar Noor, zuwa tayi ta rungumi umma tanayi mata sannu sannan taje ta d’auko ruwa da roba ta wanke mata baki bayan ta gama ta bata abinci seda taga ta koshi kafin ta bata ruwan da likita ya sayo musu sannan ta gyara gurin tafita waje dan wanke kular.
Bata dade da fita ba ta dawo tana sauri sauri dan kar umma ta bukaci wani abu, office din likita ta fara shiga ta ajiye mishi kular ta sake yi mishi godiya sannan ta koma dak’i gurin umma, se da suka kara awa daya sannan likita ya sallame su tare da basu magunguna kyauta da kuma kudin adaidaita, albarka kam likita yasha agurin umma dan se godiya suke mishi mara adadi suna fitowa harabar asibitin suka samu napep, kwatancen unguwar suka mishi sannan suka shiga, suna isa suka bashi kudinshi kafin suka shiga ciki.
“oyoyo umma oyoyo umma, wayyo Allah mun gode daka dawo mana da umman mu lafiya cikin koshin lafiya” shine abunda yaran ke fad’a da sukaga umman tashigo da kafafunta batare da taimakon wani ba, haka suka zauna suka zagaye ta suna hira suna mata adduar samun lafiya me d’orewa da kuma kudin da za’ayi mata aiki.
Horn din da sukaji ne yasa duk duka tashi suka nufi gurin taga, kod’add’en labulen tagar suka d’aga suka kallon me shigowa, atare naga duk suna share hawaye ashe kuka suke ni banma sani ba, kallon umma nayi naga tayi saurin goge nata hawayen tana cewa “hayya alal salah, duk muje muyi alwala gashi ankira sallah” tafada tana janyo Mimi daga jikin tagar, itama Noor ta rike hannun sauran kannenta suka kama hanyar waje dan yin alwala.
Komawa nayi waje dan ganin abunda ya sanya su kuka gaba dayansu harda umma amma kash na makara dan kuwa banga kowa ba se motocin dake ajiye a haraban gidan da kuma karnuka dake ta kaiwa da komowa.