AHUMAGGAH. CHAPTER 6
Bayan kusan kwanakin wata guda junnut ta kammala jarabawan ta na gaba da primary.+ Anan suka sata agaba da huduba marasa amfani,domin kuwa babu ta inda kalaman su yake karkata taje face rudin duniya Jahan khatun ce ta dada zurma zuciyan junnut har ta amince cewa ita dib mace ce mai tsananin daraja da mulki dan haka bazata ta cika sauke kanta Kamar sauran mata ba Musamman da akan nuna mata hoton khaldun sa’ood ake kuma jaddada mata cewa nan gaba shine fa mijin ta. Doka ne junnut in taje america bazata yi saurayi ba dan haka kudin sosai aka sake mata wanda shi kadai ma ya isa ya dauke mata duk wani sha’awan rayuwa da wani wanda bai kai ta ba dukiya. Toh A Washe gari da asubahin fari jirgi ya tafi da ita xuwa chan united states. Bangarena kuwa tun ranar da nagama waec jahan Aarah ta gama min bayanin komai a nitse. Big sis subaya is all excited cewa zan koma zama da su amma sabida mijin ta sadaat sai kwata kwata bana jin wani dadi Dadin karawa ban taba tunanin son da jahan Aarah take nuna min zai yi tasiri a zuciya ta ba sai da muka shiga jirgi muka taho gidan big sis subaya a saudi arabia. Gaba daya sai naji ni cikin shaukin rabuwa da ita I was quiet for sometime,bana fiye motsawa kamar ba yau na fara zuwa kasar waje a rayuwa ta ba. Duk wani zumudi da jjc yaki zuwa min,big sis ce take ta famar jana ko ina tana nuna min wurare. Saudi arabia its a perfect place but i just cant wait to go to my new school in london. Zaman sati guda danayi da su sai da naji nagaji sosai,sadat is alwys on my nerve ga big sis gaba daya bata da gane abu,abun nata ma sai gaba gaba yake yi. Yanzu gashi har ya tursasa ta muna cin abinci tare har dashi a tsakiyan mu. Haka zaiyi ta jefo min silly looks,ba dama na dan kware da ruwa sai yafi kowa daga hankali awajen yi min jaje. har naji nagaji nafara ina shiga kitchen ina taya mai aikin su girki,toh daya gane hakan ba karamin masifa big sis ta sha a hanun sa. Big sis sai tace min ki daina yawan wahal dakanki tunda kinsan darling sam baya son bacin ranki And i also do not want to see you suffering,” Ni kuma wanann ba irin kalar rayuwar da zan iya bane tun ina ma big sis bayani har na dawo inta na min maganan sadaat yace kaza akaina saii dai in yi shiru ina jin ta. I just wonder when she wll realised all this. Washe gari da aka ce zan tafi london ji nayi kamar an saka zuciya ta a kankara Here comes my freedom,Atleast zanci abinci,nayi yawo nayi duk abunda nake so batare da sa idon wannan mijin big sis din ba,araina har na fara harsashen hala idan yaga bana nan zai fi bada hankalin sa akan big sis bani ba. Da safen da jirgi na zai tashi tare da su duka muka je london din,ga wani uban shoping din da suka mun,tsaban abun takaici sadaat har da kokarin sa wajen siya min inners.3 A hakan kuma duk big sis bata dauke sa wani abu ba. Babban universityn dake london din aka saka ni,inda zan karance full 3 +1yrs nutrition course! Im just 15;16 dan haka aka damka ni wajen university maiden,don fir naki shawaran sadaat na cewa akama min hotel ko apartment ba hostel ba. Bansan nufin sa ba amma Har kuka sanda nayi ma big sis sannan ta dan tsaya min har ya amince aka barni na zauna a hostel din.2 Besides bansan komai game da london ba,and i need my space. So nake na bude idanuna dakaina na batare da sa idon kowa ba ko dan domin nasan abunda ke min zafi Kwana biyu big sis sukayi min kafin suka koma saudia,a hakan ma bata gamsu ba sai da ta nemo min student mate dina musulmai daya daga nigeria sunan ta Khadija daya kuma daga instanbul frm turkey sunan ta jasmin itama duk musulmar ce. Kafin su tafi a cikin tarairaya big sis take cemin idan akwai matsala na kira mijin ta ko ma na kira ta In babu kuma sai hutu zasu zo su dauko ni Nace mata toh kuma A haka mukarabu. Daki na na koma nayi kwanciya ta na dada lumshe ido dan Har Wani sanyin iskan freedom ke bin jinin jikina. I miss my big sis amma idan na tuno Ayanxu there is No more sadaat sai naji dadi Dan shikadai ne abun daya takura ma rayuwa ta. Bangaren junnut kuwa a wani tangamemen condimonium na yayan manyan kasar aka kama mata. Dogon Gidan sama ne mai hawa shida,site din ta na hawana karshe. Sai ya kasance Ni ina kasar london,junnut Dina tana kasar America We both exist in 2 different location batare da mun kawo tunanin hakan ba. And My first day in college was full of abun mamaki. ,sabbin kawaye na da big sis ta jona mu, wato khadija da jasmine gaba dayan su babu tayan baya Na lura wato shi dan nigeria ko aina yake zaka samu he is naturally upgraded suna da saurin wayewa ga wayo da iya bi da mutane3 Khadija yoruba girl ce tana da jikin girma kuma farin fatar ta dan dai daine,jiya da muka fito lecturs naga yadda ta ware tana takun ta hankali kwance tana muamala da kowa tamkar wanda ta san london din kawai abun sai ya bani mamaki. Nikam ban wani sake jiki na ba,am shy and quiet,toh tunda dija ta gane hakan ta fara sani agaba tun bana so har na fara bin ta ina warwarewa She has been encouraging to chill,tace ki mance fa nan london ne ai kalar fatar nasu baifi namu ba,and you see this big girls da suka fimu jiki da tsayi duk sa’oin mu,turawa ai girman buredi ne dasu ..3 Nikuma na lura da suna da rainin wayo musamman yan first year ace sunga kai ba kalar fatar su ba. But still some of them are cool,wasun su ma basu magana da kowa harkan gaban su kawai sukeyi. And jasmine,ita kuma yar kinibibi ce ga shegen iya masifa da kadadi Shiyasa ma tun a satin mu na biyu aka fara sanin mu a ajin mu,duk wanda ya gaya mana baki sai ta fada masa jaja zir. Sau biyu tana tada hargitsi acikin filin aji1 Nice dai shirun acikin su,amma sabida ina da kyau sosai kuma na fisu tsarin jiki wasu students ma sabida ni suka fiye shiga harkan mu. Nidai Abunda ya sa na dada jin dadib tarayyar mu shine dukan su suna da kwakwalwa da kaifin tarbiya,ban taba jin sunce muje adult party ba,barin ma jasmine akwai ta da rike addini ita kuma khadija ta ta kere mu a a ilimi da baiwar gane karatu. After six weeks aka raba mu a activites,sai kowa ya koma yin asalin abunda ya kawo shi,amma da shike same level ne kusan tare muke fitowa sai mu hada hanya nu dawo dormetry. Su suka sa ni na dan ji dai dai,dan bamu komawa hostel wani bin sai munje yawo iri da iri acikin gari. A haka Har muka saba sosai aka fahimci juna. Dan idan nayi waya da jahan kuma suna kusa sai kaga sun karba sun gaishe ta. Bangaren junnut kuwa rayuwar ta is private,ita kadai ce a apartment din ta dan haka babu mai shiga harkan ta. At her age anan america sai bata fara tuka kanta ba,driver aka kawo na musamman wanda idan zata fita shi zai na janta ko ina. Haka take zuwa class ta zauna,high level girl babu ruwan ta da magana da kowa,ga wani irin shegun dreses masu dan uban tsada data ke sawa,she is alwys on 5inchs rock stud,ko designer sandal hills. Uwa uba heavy make up sai dai tana dan rufe gashin kanta da scarf. A schl din su sai ya zamto babu wanda take muamala dashi,sai da aka kai kusan 4 month kafin ta hadu da wata princess yar japan. Sunan ta princess hildah,sosai halayen su ya zo kusan daya Gashi itama yar gidan masu shine,dan bayan hildan,junnut ita kadaice student din da ake kawo ta school da exotic sport cars kamar su jaguar,aventador,benz sport,wani bin zakaga hilda harda tuko lamboghini. Toh Da ita kawai junnut ke fita Shan iska,da haka har suka dawo close allies Basu zuwa wani waje in wajen bai cika sunan sa na manya bane! Hilda it ta fara koya ma junnut dabiun saka tsadaddun manicure and pedicure irin su black and white diamond nails Dogayen atachement na human hair da clothing fashion styles na zamani kala kala,suna deban wankan su just like real American celebritys Kafin kace kobo,junnut ta aje al’adan ta gaba daya ta dawo wankan damammun jeans and trousers,hot lingeries,spectacles,natural gashin kanta kuwa wani bin sai taci rabin season bata ma sanda shi ban Da ita Hilda gaba daya saida suka haukata college din su musamman da yan mata da samari suka sa ido sosai akan su kowa yana son su san dashi. Junnut har application of friendship ake rubuta musu,daga nan sai ta koyo iya maganan banza da saurin kaskantar da dan adam,hilda kam A ce dama. Domin kuwa babu marabar halayen hilda da zarah mj a wani hausa novel na surayyahms da nake karantawa mai suna sakamako.3 Da first session ya kare junnut da hilda basu je hutu gida ba,wani extra institution na business enterpneship na yayan masu kudi sukayo registan kansu suna zuwa ana damawa da su Jahan khatun dataji hakan kamar zata kashe kanta dan murna. **** Nikuwa da naje hutu sai na yi gamo da rashin saa,ina zuwa saudi arabia kwana biyu kawai big sis tayi tace wai zataje califonia meeting zata dawo in 1week. Nace zan bita,haka taki fir tace ai daga schl na dawo kawai ma huta2 Haka dai na daure na zauna I have to live with that sadat mu biyu kawai a gidan A rana na farko da ya dawo daga aiki,na fito na gaishe sa zanje dauko abunci yana ta kallo na ban kula shi ba Dana kawo abincin zan ajiye,kawai sai naji ya kama min hannu na ya ruko a nashi har yana kokarin murzawa a tsorace na dago zan fauce Sai naji Yace…bahi?..ban amsa ba nayi kokarin kwacewa Sai ya bini da wani shuumin murmushi,wai ke ya rayuwan ki haka ne? Sai Na share shi Nace here is ur food. .ni na koshi zan juya kenan sai ba ji charaff ya mike ya chapko ni,”ke zo nan ki fada min labarin london”sai ya dangwala ni akan cinyar sa da karfi dukan hannun sa sun matse ni sosai”1 Wani bugun da kirji na yayi alokacin bansan sanda raina yayi mumunan bacin da sai da hawaye suka ciko min ido na ba Blurting hurtful word na so nayi ko zanji dai dai But Am still respecting him sabida bai taba furta min komai ba,duk dama duk wata mace mai tunani zata gane mummunan nufin sa akaina Sai na fauce jikina a zafafe na tura sa na mike tsaye na bata raina na hade rai bance uffan ba..shima tsayen ya mike Kamar bai san inayi ba,ya kika min shiru ina tanbayar ki,.na kau da kaina gefe tsaki ne ya kufce min,ban hankara ba kawai sai naga mutum ya dada matsowa. Ni kam tsoro da haushi ya gama ma hatsala ni “Wani kuka mai sauti na fashe masa da shi,yace meye akayi miki…wont you tell me?labari kawai zaki.. Tun bai karasa ba ya shiga mika hannun sa zai shafo fuska ta,turawa nayi na furta Ni dai Bana so!!!cikin tsawa kuma a zafafe naja zuciya ina kuka, sai da ya dan ja yana kallo na cikin mamaki. Magana yake min amma Ban kula ba,Da sauri nabi gefen sa na haura sama bayan na shiga na kulle da key har jam locks Har dare ya tsaga inata juye juye ni kadai Tsaban takaicin sa dake ci na sai nake jin kawai na fito fili na fada ma big sis subaya abunda ke raina game da sadatt ko hala inna fada zata fara lura.+ I know he did all this on purpose ya daura ni kan cinyar sa domin ya gwada ya gani ko zan bashi fuska sai ya cika burin sa akaina. Cikin raina nace karyan ka ta sha karya,nikam namar wuta ce kuma har ka mutu bazaka ci ba.Haka na gama shiryawa akan zan gaya ma big sis komai washe gari. Da mamaki na yau da safe na fito da mug din tea a hannu na ina saukowa kasa charaf sai gashi nan shima ya shirya cikin black suits Yana haurowa alaman zaizo dakina. Tun daga dan nesa na dakatar da shi da wani kallon raini,shima ya bini da murdadden murmshin kau da kaina nayi a slow not withstanding nace mishi ina kwana? Yace lpya,nan ya fara bani hakuri kamar da gaske harda ce min shi bawai ya kama ni don raina ya baci bane Kawai ya dauka ai shima babban yaya ne,zai iya min wasa. Duk dama inajin nauyin sa amma haka na daure na cire kunyar na ce mashi bana son irin wasan. Sai yace min toh yamin alkwari bazai sake ba. Lpya lpya muka karya,big sis ce ma ta kira shi a lokacin sukayi magana sai ya bani wayar ina amsawa. A yadda naji tana ta zuga mijin ta da safen nan i just lost the caurage to tell her again. Big Sis subaya ta yarda da mijin ta sadat irin mummunan yardan nan Duba da yace ma bazai sake rike ni hakan ba sai na share maganan har yamin sallama ya fita. Zama na yi ina waya muna chating da su dijja,kuma har yau junnut na makale da zuciya ta a dukan social media acct na duba ta amma da shike she is very private sai ban same ta ba 8pm na dare sadat bai dawo ba kuma mai aiki ta gama girki xama nayi serving kaina inaci ina tuno da rayuwa ta musamman wanda nayi da khaldun sa’ood a nigeria,shin yaushe idanuwa ta zata sake ganin shi? Wani Lumshe ido nayi tsamm ina mai jinginar da kaina jikin chairs na tsawon minti goma sannan na mike na wuce daki nayi kwanciya ta Ina idda adduar bacci na dan rufe feets dina daga nan Bansan sanda bacci ya dauke ni ba.. Chan cikin dare sai naji kamar inuwar mutum akaina sai ban bude ido ba dai na dan gyara kwanciya ta3 Sai chan na dada jin kamar bargo na ya motsa,sai na farka amma ban bude ido ba,kamad wanda yake jira na ja jiki charaf sai naji an kama feets dina ana shafa min Wani uban tumble nayi na hada karfi na kwace kafata na sauka daga gadon a firgice Murya na rawa nace Waye wannan!! Yana shiru yana kallo na,gashi wutar is dim bana wani gani sosai..nayi sauri kenan zan kai hannu kan bedside lantern sai naji Sadaat ya kamo ni,ihu na fasa kamar bansan shidin bane ina cewa ka sake ni,i hate it ni kabarni Bai ko kulani ba sanda ya sake aje ni kan cinyar sa ya matso ni da hannayen sa, Kuka na fashe da shi mai sauti na shiga zamewa da karfi ina fifficikewa Da kamar shiru zaimin sai kuma naji ya ce ke!! Wahts wrong with you, A zafafe Na juyo na tofa masa yawu a ido sai da ya sauke ni kasa amma bai sake min hannu ba Are you mad..ya fada yana mutsula ido yana tswatar min ina shiru in kan sheka kuka Dan Masifa ya shiga min wai na masa shiru,nace ni bazan yi ba kawai ya fita min a daki Ko yanzun nan na hada shi da big sis Salon wasa da hankali na Yace what! me akayi miki? Ko da na shigo na miki wani abu ne Cikin kuka Nace masa eeh,kana taba ni ne kuma bana so. Da mamaki sai naga yayi wata busashyar dariya Ya ma dada matso hannu arogantly Raina ne ya dada baci na shiga jajjan hannun da balain karfi daga nashi amma nakasa faucewa Tsoro ne tam cikin raina A rude nake cewa nika sake ni ai kace bazaka sake ba i told u bana so Yace shusshhh If u keep blabering sai na daura ki akan gadon nan,u know what i mean? Ya karashe yana cusa min marasa kunyar idanun sa anawa Wani diffff kirji na ya buga,a hankali na furta na shiga uku Jajeyan idanuna na kalle shi da shi,cikin tsananin fargaba da tsoro nace to kasake ni pls ..big br…bai bari na karasa kiran suna shi ba ya wani daga min hannu,cikin shuumammen murya yace dont call me that Yace kice min sadaat..zanfi jin dadi Nikuwa na dada fashe masa da kuka nace bazan fada ba Daya lura naji tsoro sosai,sai ya fara dariyar hauka shikadai har sanda na dena sauti ina ta jan shessheka. Rangwafar da wuya yayi yana kallo na anoyingly kamar irin ya tausaya min din nan,jin zai sake dago ni zuwa kan cinyar sa yasa na dannna wata makahuwar ihu mai shegen kara Tsaban na firgita shi Sai ya dada ja na a haukace yana neman toshe min baki da karfi,na fincike nima da karfin ban hankara ba naji saukar mari tasss akan fuska ta…. Tura ni yayi kasa da duka karfin sa alaman yaji haushin abunda nake yi, nikuwa dana sabule na zube kasan wani dada karkacewa nayi ina shirin sake danna masa ihun dayafi wanda nayi firgitarwa Hannun shi yasa ya ya finciko ni tsaye,a tsorace na fara bashi hakuri baki na na rawa,bai sake ni ba sanda ya manne ni da wall yana kare min kallo Keep quiet! Ya daka min tsawan da bansan sanda na dauke sauti chak ba Yace ashe baki da hankali bahiyya ai na dauka ke wayayyice karar me kikeyi?hawaye ke zabo min bance uffan ba Sai yayi tsaki,yace ohhh na tuna its tru that u can take the girl out of the village but you can neva take the village out of the girl. Me kake so dani? Na furta azafafe, pls leave me alone,daga cewa bana son kana rike ni!ai bana so ne pls let me beeee Na tsawatar akan fuskan sa with much courage Dan shiru yayi yana kare min kallo kafin yace,kin tsane ni u hate me ko? Ai na lura dake tun tuni nasan baki kaunata u disliked Me since back then. Ban jira ba Nace eehhh,why wud i like you?ana son mutum dole ne,ni ka sake ni na dada turasa a wulakance shima sai ya dada matse ni Numfashin sa yake watso min akan fuska,yana kallo na Listen ‘i like you bahiyya! Ina son ki sosai har cikin zuciyata babu karya. Kuma nasan kin gane hakan tun a nigeria,wai meyasa kike abu kamar karamar yarinya ne. I swear ban taba jin wata y mace kamar yadda nake jin ki ba Meyasa zaki rufe idanun ki?oh cant u see.. Kaina na saukar dan Wasu zafafan hawaye ne suka saukar da kansu daga idanuna dan Ko mamakin abunda yace din banyi ba,sai na kau da kai na gefe na dada hada raina sosai,na share abunda yace nace ka sake ni. Baiyi hakan ba ya shiga marairaice min Please say somthing! Meyasa kika tsane ni?ko tsoro kike ji? Isit subaya,orrr khaldun..Look baby kar ki damu da su i will take care of you Ban ma bari ya kara kalma ba Cikin hatsala na wani kalle shi a gigice.. Daddagewa nayi na tofa masa yawu a fuska,cikin kuka mai nuna mugun tsanan sa nace just let me go, Kuma wallhy saina fada ma big sis. Ure a coward..i hate you. ..wani dariyar takaici ya fashe dashi har ya sake ni amma bai dena ba. Da sauri na ja jiki zan bude kofa na bar masa dakin a zuciye,sai naji ya daka min tsawa Yace min gaskiya na fada makii ina son ki bahiyyah ,amma in kina tunanin zaki fada ma matar na kije kofa a bude take saidai kisani bazata taba yarda da ke ba. Harda cemin ina nayi wasa sai ya hada min sharri awajen big sis. He is talking to me like a real infidel, Da tafin hannun na dan share tears dina dan sosai Tsoro ya kama ni,sai Nace mishi oho nidai sai nafada,kuma bana son shi na tsane shi har abada daga nan na ja tsaki na fita na banging masa dooor. Kasa zama nayi dan Acikin daren na nemi big sis a waya ban same ta ba,haka nayi ta jigila tsaban kuka ko bacci ban iyayi ba Washe gari da sassaafe na fita na bar masa gidan nayi tafiya ta baima sani ba. A Chan wani restaurant kusa da gidan na je na zauna anan naci abinci nakai 2hrs Ina zaune nikadai ina tryng big sis amma shiru. Around 9 na tashi zan bar wajen kenan sai ga kiran ta,jiki na har na rawa na saka kirar a kunne nace hello big sis…bata jira me zance ba ta fara min tambayoyi wai ina naje da safe ai yanzun cook ta kira tace mata basu ganni ba Kuma sadaat yace mata bai kwana a gida jiya. Cike da mamaki nake jin ta”sadat Bai kwana agida jiya ba?Araina nace what?murya na na rawa kadan nace Big sis nifa banje ko ina ba ina the punts restaurant ne,..ta tsari numfashi na tace ok just go home now,a dan rude nace no big sis listen akwai abunda zan fad…sai ta dan yi ajiyan zuciya tace ok talk later bahii im really busy sai kyat naji wayar ya off tsaban sauri a hargitse na dada danna dial sai kuu kuuu baima shiga, Da fushin haka na tafi gidan Tsakar gidan babu kowa dan haka Daki na na wuce straight,chan abun ya dame ni sai na tura ta tex ta email Nace idan ta samu netwk ta kira ni,akwai maganan da zan gaya mata akan mijin ta sadaat And its very urgent Daga nan Almost 10hrs nayi babu reply din ta sai kawai na hakura na cigaba da zama na a sama batare da ina saukowa ba, kuma duk sanda nake daki gam gam nake kulle kaina Dan Cereals da chokolate buns kawai nake jikawa da madara na sha In har anga nafito to na tabbata irin odd hrs din nan ne da babu kowa a tsakar gidan Sai naxo nayi wani fast food ki indomie haka dakaina na koma daki,sosai nasha mamakin yadda bana samun big sis a waya kuma itama bata kira na Sai ranan dana fito Cook din mu take gaya min ai dama idan taje california akwai refugee camp din da suke zuwa na wanda girgizam kasa ya taba rayuwar su so wajen babu netwk sai anci saa Dana gane hakan sai na dena damuwa Haka dai na dinga dodging sadat ban sake bari mun hadu da shi ba Har sai da akace min big sis ta hau jirgin zata dawo saudi anjima. Dana fito da safe da shi muka fara haduwa yana zaune a babban palon gidan,ya dora hannayen sa akan computer sa yana latsawa Ko in sake duban inda yake na hade raina sosai zan wuce shi sai yace kin gama boye boyen naki? Nayi masa shiru,yana mikewa tsaye zai matso kusa dani sai naja da baya Zan gudu Da sauri Ya kamo hannu na,nikuwa take naji ido a sun cika da hawaye sai ya sa hannu kan lips dinsa ya ware min idanun shi yace shusshhh..dont you dare call anyones attention ko yanzun nan na miki abunda bazaki so ba Bandamu ba Nace ni ka sake ni… Yace ohhhh rashin kunya zakiyi min,dan kinga na barki kwana biyu har kin dauka kina da wayo ko? Ya tabe baki..just be careful Sai ya sake ni Araina nace yau kam ba abunda xai hana ni fada ma big sis waye kai Mugu kawai macucin banza. Ashe ma ya fito a afili. Sai naji yayi dariya ya rufe system din,kallo na yayi yace ure free to do anything..ya wuce ya haura sama. Tsaki nayi na wuce nima na cigaba da abunda ke gabana. Tsakanina da shi babu mai cewa wani uffan,sai chan da yamma lokacin na idar da sallah a daki na kenan,na fito zanbi kitchen sai na fara jiyo sautin surutu akasa. Dana leko kadan sai naga big sis wani dadi ne ya mamaye ni,cikin raina nace alhmdullh ban damu ba na sauko aguje. Banzan kuwa yana tare da ita haka na zo na bi gefen sa na rungume ta. Wani kankame ni itama tayi,tana dan bubbuga baya na da hannun ta Cike da fara’ar ta shiga tambaya na tana cewa How you princess Na dago zan mata magana da muka hade ido sai naji hawaye sun ciko min ido na sosai Gaba daya zuciyata ta dau zafin abunda ya faru tsakanina da sadaat,sai nayi shiru ban sani ba Big sis tana ta kallo na,ina sauke boyayyen nishi zan sauke kai kasa sai ta tallafo fiska ta Da Wani sanyin kallo ta bini da shi wanda ya dada hassasa kukan dake so ya kufce min,da sanyi muryan ta mai saurin nuna damuwa tace ahhh Whats wrong? Yau kuma kin dawo baby ne daga oyoyo sai kuka…har na dago kai zan yi magana Charaf sadat yace Ya bazatayi miki kuka ba,she misses you and you know Bahiyya ai dake kawai ta saba Sai ya dan jawo ta jikin sa suka jeru suna kallo na yace,ko ba haka bane bahi?na tsime kamar bada ni yake ba Naki ma daga kaina na hade rai kuma bance komai ba Yace u see Babe I told you,kinga tinda kika tafi bahiyya has not been her self,fushi ma takeyi da kowa Sis tace awwwnn Im so sorry,sai ta riko hannun na!tana dan matsewa a mata gently Gaba daya haushi ya rufe min ido Tana kokarin daga fuska ta,bansan sanda ba sake hawayena va,tace what?Wai meye hakanTa dan kalle ni ta kuma kalle sadat din adame,azuciyar sa yana ta tsoron abunda zan yi amma sai ya fuske kamar baisan komai ba,hannu na nasa na yarfe tears dina ina faman taro karfin magana,big sis itama ta shiga share min ta jawo ni na zauna akan cushion kallo na take yi cikin nitsuwa..bahiyyah whats wrong,Ta furta a hankali Ko na maki wani abu ne? Na girgiza kai,cikin rawan murya mai dauke da shagwaba nace ive been calling you sis baki sako na ba? Hankali adan tashe Tace noo,wani sako sai Tayi kicin kicin zata kawo hand bag din ta dauki wayar ta Sadat Duk Yana lura da mu duka am sure ranshi yayi fari da big sis tace bata ga wayar ba na daki Tace min minene a tex din naki,did you need anything meyasa baki fada ma sadaat ba Zan yi magana Sai naga ya taho daf kamar zai zauna kusa dani dayaga na dan tsorata sai ya sauya salon taku ya dawo gefen ta,yace Comn subaya kinayi kamar bakisan bahiyya ba Ai nagaya maki bahiyya taki sakewa ne kawai da baki nan musamman da ba asamun ki a waya. Tace ohhhh am so sorry netwk ne baida kyau Nace noo big sis i …i. I want to tel… Big sis bata tsaya jina ba tayi murmushi ta ja cheeks dina tace bari na kimtsa to sai naxo kiyi min shagwaba Ai kuwa kamar jira yake ta mike yayi saurin janta ya riko hannun ta Tsaban takaici Da sanyin jiki nace ok har suka haura sama ban bar wajen ba I dont know what happen big sis bata sake fitowa ba,washe gari wajen cin abinci sai tace min ita bataga text dina ba I knew it must be the work of this devil,hala shi ya goge bata sani ba Kassh ai da ban fada a fili ba ma Nayi ta jin haushin abun araina Big sis kuwa bata ma san menake ba kuma haka yaki firr ya barta mukebe tare,just for that moment ya fara makale mata yana yi yana bin ta agindi kamar wani sabon ango Har nagaji nayi shiru ina ta jiran perfect timing. Wasa wasa har big sis ta cika four days da dawowa amma sabida sadat sai bata saurareni ba,toh ranar da dare naji tace sadaat din zaiyi tafiya Allah Allah nake yi ya tafi na samu space din fada mata komai Toh da safen ni da shi ne akan dining table,dan tana zama ya aike ta daki da gangan wai ta dauko masa wristwach Ko uffan bance masa ba,shima bai kula ni ba sai kokarin zuba abinci yake yi a plate. Alaman da na shi ne dana big sis Tana dawo wa muka fara cin abinci suna dan hira Fada naji big sis tana min,tana cewa wa nasani anan saudia da zan na ficewa agida anyhow I dont know how sai naji tace ai security ne yace mata taja min kunne ya dena yawan yawon dare Cikin tsananin mamaki Nace wallhy bana fita amma haka big sis taki ji na sam The more i defend myself the more inajin salon munafurcin da ake ta kulla min agidan Wato har an hada baki da masu aikin gida ana so abata ni awajen big sis ko Tsaban abun ya caga min kwalwawa sai na hade rai naki bata hakuri dan nasan ba mai min wannan abun sai sadat.. Harara kam ya shata wajena haka kuma na bar table din ban sake cewa komai ba. Daki na naje ina kuka,sai chan anjima na wanke fuska na sauko kasa Ai yau kam babu abunda zai dakatar dani daga fayyace mata gaskiya Hanyar dakin ta na nufa gaba gadi Daf zan murda door knob sai wayar hannu na ya dau kara,bakuwar number ce dan haka na daga Bai jira na aje munfashi Daga nan muryan sadat ne ya doki kunne na yace Min baki sanni waye bane da tuni kin saukaka kanki kin mika min wuya .yace min shi ya sa masu aikin gida suka fada ma subaya ina fita yawo anyhow Kuma aikata ire iren haka ba komai bane a wajen sa. Wani tsaki mai sauti ne ya kufce min cikin bacin rai nace toh sai me,,Allah ya kiyaye ni…kuma bari yaji ina daf da tona masa asiri yanzu Wani Dariyar mugun ta ya fashe min dashi,yana kuma cewa bai damu ba naje na fada mana in har ina so na kashe subaya yanzun A zafafe nace shine zai kashe ta bani ba mugu maci amana. Ko ajikin sa,sai na hatsala na bangaje kofar big sis na shigo,a zafafe na shiga kwalla sunan ta nace big sis..sai na kuma tsaya durus,cos dan hangota ko motsi banga tanayi ba, ai da sauri na jefar da wayar na zube jikin ta..big sis..big sis..na shiga jijjiga ta ina tattaba ta sai shiru gashi jikin ta yayi sanyo har ya sake Ihu na tsala ina kiran sunan ta ina salati bansan sanda na fashe da wani matsanncim kukan tsoro ba Mancewa nayi muna fada da sadatt sai na raromu wayar a haukace cikin kuka na shiga gaya masa yadda na same ta. I tot he was listening Ashe jira yake nakai karshen aya sannan ya fada min ai shi ya bata poison drink Wanda zai wahalar da ita dan nagani Jiki na na bari na mike tsaye da wayar nace what? Hankali kwance Yace yeah.and i wll do worst idan kika sake yunkurin cewa xaki gaya mata wani abu game dani A wannan lokacin ji nayi na loosing duk respect din da ke tsakanina dashi Ciikin tsawartawa mai zafi Nace masa bai isa ba Ni Zan kaita asibiti kuma wallhy sai na fada Wani dariyar yamin,yace shikenan ki kaita mana,im every where my darling,ashe kauyancin ki zaisa ki rasa big sis dinki yau ma kuwa…and I will surely come for the burial. Kinga kin saukaka mana maganan auren mu Nace stop it, Shima daka min tsawar yayi cikin barazana yace muddin nace zan cigaba da taurin kai sai ya koya min hankali ta inda bazan manta ba Yace min shi baya neman abu a hanashi ..nima dan dole saina so shi Kuma wai shi dama ba son big sis yakeyi ba idan ta mutu ba damuwar sa bane har da cewa,idan na yarda ina son ta rayu a duniya kuma cikkn farincikin to kar na yadda na kure shi. Kukan haushi takaici mamaki da tsinkewar zuciya kawai nakeyi bance mishi komai ba ma katse wayar na koma jikin big sis inata cigaba da kukan cikin kona rai. Da kyar na mike na kira ambulance aka fitar ta da ita,wani familiar doct ne ya duba ta of couse ya dada tabbatar min food poison ne. Duk dama nasan ba yi na bane na birkice but I was seriously regreting meya sa ban yi recording last call din mu ban daddara ba na same doctor I asked him for proof ko zan iya amfani da shi nayi ma big sis bayani amma sai ya shiga min bayanan karya yace min ai normal allergy ne kar na damu. …i dint even know that bakin su daya da sadaat. Sanda big sis tawarware muka koma gida,sai nayi shiru ban dago wani magana ba sabida bani da proof mai karfi ga tsoro na duk ya koma kan yanayin jikin nata Amma washe garin ranar da ta gaya min ai doctorn ma nashi ne sai na fahimci duk bakin su daya. Kawai sai na fara takatsantsan,ban ce komai ba kam amma har yanzu ban saduda akan sanar da big sis ba. But the more i try the more mugayen halayen sadaat masu ban tsoro ke bayya min,he is a devil Sam sam mutumin baida mutunci Cikin kwanaki gaba daya nasan sirrin sa har da dalilin sa na auren big sis,kaina y dda daukar zafi tabbataccen proof ko wani shaida nake nema har yanzu amma Allah bai bani sa’a ba. Har kowa ya dena gane min acikin gidan kuma tsaban tsanan sadat na dena saukowa cin abinci duk wani walwla na yanke ma kowa I stay disconected harta fannin bigsis ko hira take min bancika amsawa ba,dan tausayin ta saura kiris yasa zuciya ta ta buga Gaba daya tsoron maza sai ya shiga raina,lallai SO kan iya zamowa MAKAMIN CUTA. Idan muka rabu a daki ko kitchen Kullum sai naje daki nayi ta kuka cos i pity her alot. Kullum innayi zuciya zan fada anyhow Sai na rasa ta yadda zan bullo mata,har big sis ta soma damuwa akan sauyin data ke gani a tattarre dani I started looking pale kamar wacce take da cikin fari Idan tace zata fada ma jahan sai nace mata ah’ah Kawai banajin dadi ne Big sis ta kaini asibiti yakai sau hudu ana ce mata lpyta kalau End of holiday yazo zan tafi london,sai tace zasu bi ni,banyi musu ba sabida naga yadda ta damu dani sosai. muna isa hotel muka kwana akan washe gari zanje hostel,na fito kenan ina dada tattara kaya na sai naji sadaat yana ce ma big sis gidan yayi kyau kawai su kaini yanzu. Araina Nace what? I know he wanted me out of the hostel dan ya samu hanyar xuwa a sace har yana tsora ta ni har ya samu galaba akaina Hawaye ne suka sauko min sai na share ina dada tabbatar da hakan daga cikin zancen su Ai ina ji yanace ma Big sis sign… Da sauri Nafito a hargitse cikin kakarin sautin kuka nace big sis.. Sai duka suka dago suka kalle ni,she noticed how i squaze my face kamar mai shirin yi kuka Dan haka Tsaye ta mike cikin masifa tace wai meye ne matsalan kike ta damun kanki bazakai fada kowa na??? Nace gida zaki kama min? Tare da sauke ajiyan zuciya Tace eh Big sis dan Allah kiyi hakuri Ni dai wallhy bazan zauna ko ina basai hostel Tace mene? No dear u have to sai ta taho tana magana tana kokarin kawomin catalog din gidan hannu na take shirin kamawa tace kinga gidan kuwa yana da kyau zaki ji dadi U wll be very comfotable u see! Ta damka min Nikuwa ko duba banyi ba nayi jefa da shi na dada fashewa da kuka” ni dai bana so..hostel nake so A dame ta riko ni tace bahiiya lpya kuwa talk to me? bance komai ba na fada Jikin ta ina shishgewa cikin salon naci da shagwaba ” ni dai hostel nake so big sis,inayi har ina bubuga kafa ta da kasa Haushi kamar zai kashe sadat Sai ga gogan ya dalla mata harara yana mata alaman irin ai ita ta bata ni dan haka ta tsawatar min Ita kuwa big sis tausayi na take ji gaba daya kanta ya fara daurewa da strange behaviours dina Ga sadaat ya sata agaba da mugun kallon alaman dole kawai ta sa ni na amince Karshe dai big sis ta dago ni tana rarrashi na tamkar jaririyar da batasan bakin nonon uwa ba har nayi sanyi na dena sheshekar a nitse tace baahhi..pls ki zauna anan din kinga har munyi booking. Inyaso next year sai ki koma hostel dinki Tun kan ta gama na kwace jiki na anata nace nooo big sis In sai na fita hostel to Ni wallhy acire ni a schl din,haka kawai na tsinci kaina na da mata bori da kukkuni Cike da taurin kai ba turje,naki sam Har sadaat ya ja mata tsaki ya fice. Yin haka dayayi sai ta rude Nan ita ma tafara min surutu tana cewa kingani ko Yau har kin bata ma sadaat rai wai meke damun ki Nace nidai bana so,keep quiet tadaka min wani tsawar for the first time sanda na razana Tace bazaki zauna a hostel ba thats final,..zai lklhata tace min kimin shiru ko da wasa..yyaa ina maki magana kina min musu..just go park ur things im taking u there.. Righg now ta dasa zare min ido Wani kukan na fashe mata dashi murya na rawa har naji na tunxira zan gaya mata dalila na Ina nacewa bigg sis….ta jawo ni cikin fushi da karfi kuma rai abace tace right now bahi. Inda ta damke nin har na min zafi,Dauke kai nayi cikin kuka na shiga dakin na sa lock,na sulale bakin door na cigaba da kuka na Duk tana jina cos sosai nadaga mata hankali Almost 1hr tayi tana buga wa na futo amma sam naki ranar Ni banji dadi ba itama haka Nidai Ban taba mata rashin kunyar da nayi mata yau ba Haka har tayi fushi suka bar london ban kula ta ba,sai da nayi two weeks naji ance ta zo wani city kusa da mu Ko da na tashi zuwa wajen ta sai na dauki su khadija da jasmine muka je,sabida su big sis ta kulani na kuma lura cewa sosai sadat ya zuga sis subaya akan abunda nayi mata ranar. Nadai bata hakuri amma bata sake min fuska ba har muka rabu na nadawo hostel zuciyata bai min dadi ba I love big sis very much,amma cikin kwanakin sadat sosai ya nuna mata cewa tayi kuskuren sakalta ni da kulawar ta. Semester gaba daya banda jahan Aarah dake kira na banajin dadin kowa Sai Ana daf zan dawo hutu sai gogan ya kirani cikin dare Yana cewa muddin ban amince na fita hostel don yana xuwa waje na ba sai ya sa subaya ta tsane ni na har abada,tun in mayar masa har fargaba ya fi karfin zuciya ta Kuka nake tayi da wayar akunne na hade da yadda sis subaya ta dauke min wuta kwana biyun sai barazanan sa sosai ya taba ni khadija ce ta raba ni da wayan ta rungume ni tana rareashi ban iya gaya musu komai ba sai washe gari. Toh Duk iya dabaru da tunani suma sunyi amma sai dai sharrin sadat gaba daya ya fi karfin mu Duj inda muka billi yana nan,tamkar wanda yake kallon duk abunda nakeyi atv Haka naje hutun da zimman zamu shirya da big sis Sai dai hakan baiyu ba sakamakon big sis bata da wani buri face na amsa ma mijin ta sadat cewazan bar hostel zuwa inda ta zaba min. Nikuma nasan muddin na amince tawa ta kare babu abunda zai hana shi raping dina and i can neva risk it. Shidai bai cika sa baki in tana min magana ba amma idan suka je daki,har kuka yakan sata tsaban bakaken maganan. Sai daya sa ta yarda cewa ina da taurin kai da raini,ga wani sabon kalaman dayake ce mata Wai na samu waje ne shiyasa nake bude mata ido Achan kuma Da muka binciki gidan a london dasu dija mun tabbatar da cewa gidan ma na wani tsohon abokin sa ne dan iskan gaske kuma duk ya san masu lura da wajen. Basai am fada min ba nasan tarko mai girma zai shirya min muddin nace zan koma gidan da zama and i just cant risk it. Hutu na sam bai min dadi ba, i have to choose between faranta ma big sis rai and her husbands evil desires towards me .. Finally ranar da zan koma second session big sis har 16thbirday party ta hada min tmna kexe raini duk dan na saduda na ce na amince zan bar hostel Ba don naso ba na bata kunya. Haka muka rabu this time basu ma raka ni ba. Daga nan Time to time zata kira ko na kira ta,sadat da yaga dai ina da taurin kai alaman bazan saduda ba sai ya sa karfi wajen bata ni a zuciyar big sis yanzu Sai ya nuna cewa ai yana bincakawa yaga silar taurarewa na shi yana zargin a schl din ake zuga ni To Dan fitar da muke yi shoping da shakatawa da su jasmine duk yabi ya hada mata cewa ai angaya masa maza kawai muka sa agaba and he alwys manipulate her with lies and proofs Tun lokacin Kusan kowani wayar da zamuyi da big sis sai ta min fada sosai Har abun ya fara affecting dina Ba tantama big sis tafi yarda da maganan sadat akan na kowa arayuwar ta,hakan kuwa yana dada kashe min kwarin giwan tona masa asiri awajen ta To this time da naga khadija ta bude dan karamin eatry lounge mai dauke da coffe shop tana saida nigerian dishes dasauran su sai nima nace zan dena zuwa hutu saudi arabia kwata kwata1 Ban neme su shawara ba I have to call jahan direct dan na samu cikakken permision mai karfi kafin na samu daman zama da khadijan sosai Abun yayi ma big sis zafi aranta,bawai dan aikin danake so din na ,damuwar ta shine wai har nice zanyi tunanin yin 8months ban dawo gidan ta ba. Hakan kuwa rayuwar mu ta cigaba,yanzu big sis gani take na waye ne bata isa ta gaya min naji ba And then she was Regreting why she was too cool at first. Nikuwa wani bin har kuka nake yi tsaban yadda nake jin kewar ta A raina. Amma Haka na daure na fita sha’anin su Duk rayuwa ta a london na fara yin shi bana zuwa ko ina hutu Na koyi abubuwa dayawa awajeja daban daban Musamman al’adun yan nigeria da irie iren abincin su har da tsarin rayuwr su, A Sanadiyar dija nasan wasu yan mata da yan maza dayawa daga nan Bayan su jasmine da dijan kuma Ina da abokai daban daban acikin turawa both side of my life Alhamdullhi. A Yanzu ina daf da shiga 17yrs Idona ya bude sosai,babu abunda ban sani ba game da rayuwa. Wani abun idan aka min sai na hada da radadin rashin iyaye na nayi ta kuka har sai naji sauki But that dosnt stop me from living my life! Bangaren junnut kuwa tun lokacin da kaamil ya sanar da cewa khaldun sa’ood zai dawo apartment dinsa na America hankalin ta ya fita ajikin ta a kullum bata da aikin yi sai na jiran tsammani.5 Gashi Dama jahan khatun ta bata umarni cewa yana dawowa maza tana zuwa wajen sa akai akai dan su saba da shi sosai Dan haka ba tare da bata lokaci ba ta fara karkata hankalin ta wannan hanyar, Bayan ya dawo da kwana biyu kaamil ne ya fara zuwa mashi. So itama ranar da suka shirya kai masa ziyara ita da kawar ta hilda Kaamil din ne ya bata adress dib gidan Babban flat din khaldun is quiet far from asalin main cityn america dan kuwa acahn baya yake kusa da wani sharbaben wood island One feet floor sleek apartment mai glass coverings ta ko ina komai na gidan is All white banda yelwataccen shukoki da flowers. Tuki suke suna kare ma enviroment din kallo irin na ya kece raini Cikin wata kerarriyar mota kirar dodge fara sol a harabar gidan su kayi parking Banda military watch men da chefs Babu wani tarin mutane a cikin gidan dan haka koda suka shiga ciki sai da suka yi tsayuwar minti 30 a falon sa suna aike aiken a sanar masa isowar su.. kowa haka zaije ya dawo yace musu yayi knocking amma oga baida izinin shiga room dinsa da kyar mutum daya yace musu ya isar da sakon nasu yace sujira yana zuwa.. Dukan su riga da wando bakake suka sa suna zuba qamshin turaren lacoste amo desigenr su kuma jimmy choo ce up and down kansu ya sha gyaran long and curl platinum hair dress kowacce da hair style dinta. Bisa tsarin wayayyu kuma haddadun yan mata suka zauna akan white cushin kowacce ta wurga kafa daya akan daya sun kura ma kyakkwar tsarin falon ido.. Shikuwa khal dama bacci yakeyi dan kaamil ya sanar da shi zuwan nasu amma sai ya manta Da aikan sun ya iso ya riske shi sai ya farka,anan ma sai da ya shiga gym yayi 10minutes warm up ya dawo ya shiga wanka yayi sallah ya shirya kansa cikin kannan kaya sannan ya fara tunanin saukowa. Hilda tayi tsaki har ta fara fifita sabida babu abunda yafi cin mata rai kamar aja mata lokaci Sun fi awa guda suna jira a falon Amma da iska ya buso wani uban qamshin turare wanda ya zo ya doki hancin su ya kuma canzawa atmospher wajen gaba dayan tsari,sai da suka juyo bazata suna kallon takun san babu shiri…8 Slightly Quick and majestic kwarjinin sa ya fito kamar zarrah.4 Ko da ya matso kusa yana dan duban inda suke “Wani karin kaimin son shi Junnut ke ji aranta zuciyan ta cike da zumudi kamar zata tsinke. Ita kuwa hilda ta riga ta sume ma haduwar sa,sai yau ta dada yarda da surutan junnut akan sa,he is extremely hot aganin ta..ko da ace shi ba soja bane aganin ta ya cika ta duk inda namiji zai kai. Shikuwa bai wani bata lokacin sa wajen sake musu kallo na biyu ba Bayan ya musu takaitaccen sallama Akan kujeran dayafi nesa da su ya zauna inda Su biyun suke fuskantar sa. Hilda ta dauka ko junnut zata iya tuhumar sa akan aje su dayayi suna ta jiran sa for hrs amma sai taga kamar ma junnut bata samu fuskan ba He remain queit kuma bai ce akowa musu komai ba Junnut ce ta dan yi gyaran murya tace Mashi ga kawarta hilda bla bla bla…little introduction amma “ok”nice” good” sune iya abunda yake iya furtawa. Zaman su a falon sun kodi azaban jan aji mulki da kasaita daga wajen sa amma dolaye kamar wanda kare ya lashe zuciyar su haka suka yi ta nace mashi da surutai wasu ma baiya amsawa.3 Tsaban nuna bai ma san sunayi ba after 40 minutes ya mike ya haura sama. Shi bai ce musu yana zuwa ba, bai ce musu kuma sai anjima ba Haka sukayi ta zama, da Hilda taga bazata iya ba tace ma junnut pls ki haura kije ki same shi,am sick of all this waitings.. Junnut sai da ta mike sannan ta dab dafa kafadun hilda alaman bada hakuri,cos looking at yadda ta ke yatsine tan tsaki kasan sam bata saba da wulakanci ba daurewa kawai takeyi Toh ta hauran ma amma bata san wani daki yake ba. Four rooms ne ajere side by side biyu na kallon biyu Dukan rooms din Irin kofofin nan ne masu noise proof activator so she is not sure ko in tayi knocking ma za’a jita. She stood there for a while,dan ko masu aiki basu da ikon wulgawa ta nan saida babban dalili. Karshe dai Dakan su suka gaji suka tafi. Bayan kwana biyu toh dama in sunje shakatawa sukan yi hiran khaldun da hilda,. ITace ta shiga zugata akan,duk rashin sabo ne,amma in tana zuwa gidan akai akai zasu saba ita kuwa junnut tuni ta hau kan wannan maganan ta zauna. To kusan kowanni wekend ta kanje gidan taci zama Tana hidimonin ta kusan ita kadai dan bai taba kulata ba….. Atleast ta sa kanta sabawa da doors,kitchen etc din gidan so tasan inda zata bude ta same ruwan sha ko abin tabawa3 Daki biyu spare bedrooms ne na ukun ne nashi daya kuma empty ne amma da joint cushions aciki Gashi Masu aikin Ba’su bari ana shigan dakin baccin sa amma junnut saida tasan inda dakin yake kuma har closet dinsa tana marking. Shidai bai taba ce mata baiya son komai daga gare ta ba,kuma bai fito ya mata wani direct wulakanci ba Amma aranta ta yarda cewa kamar har yanzu bata samu waje aransa bane, dan aganin ta babu namijin da zai na ganin kyakkwar mace mai yawan kwalliya da aji irin ta Yace baiji ya fara sauke mata kansa ba. Toh ranar data zo da safe ne unxpected laundry man yana shirya kayan sa zai kai masa closet da kinibin ta sai ta tsayar da shi ta amshe kayan ta shiga dakin nasa daya hana shiga wai tana gyara wa. Dama Waya yake amsawa ta bayan saman bene dawowar sa kenan daya hange abun data keyi Abun ya bashi haushi matuka. A fusace ya juya dan bata masan ya shigo har ya fita ba, Loundry man din ya kwalla wa kira yana tahowa kuwa baima san sanda ya zage ya balbale shi da da masifan kar ya sake bata kayan sa ba Yace infact akira masa duka ma’aikatan gidan duk zai kora su Kowa yayi tsuru tsuru,sunyi jungum ana bada hakuri Wani uban warning ya kashe musu cewar sa Kar su sake bari wani ya shigo min gidana batare da cikakken izinin na ba And as for his room directly ya ce kar a sake bada wata ya mace dama ta shigar masa har abada. Junnut Ta gama jera kayan kenan as She was about coming ta tsaya cikin bacin rai da mamakin guts dinsa Tana jin duk abunda yake fada Tsaki kawai tayi,dan kuwa abun nasa bawai baya damun ta ba, kawai tasan ta zabi ta rufe idon ta akan son sa ne Har nice zai kafa dokan kar abani daman shiga dakin sa? Arent we supose to be fiances naga dai bayi da wata matar zama saini? Haushi da takaicin sa ya sa ta fice agidan bata sake dawo ba shima kuma bai neme ta har tsawon wata guda. Chan data huce ta cigaba da zuwa this time normal gaisawa suke yi amma kuma sai ya samu saran tana zuwa shikuma zai barta agidan ya fice bazai dawo ba sai ta gama zaman ta ta tafi Abun na mugun mata daci Intayi korafin ta gaji to jahan khatun ne agaban wajen bata labarin cewa ai haka nan halayen sa suke kawai ta daure su saba. Abun ya dade ya na bata mamaki aganin ta ashe babu wacce zata iya zama da shi. he is soo mean and stern tunda aka hada su har yau Ko sau daya bai taba yin abunda ya nuna damuwar sa akan abunda ke tsakanin ta da shi ba Haka dai suka cigaba within the months,ranar ma tasha wankan kece raini ta tazo wajen shi sun kuma hade ido tub daga sama tasan yagan ta sarai amma data aika sai yace ace mata baya jin zai iya saukowa. Abun ya ishe ta tana fita agidan straight sai ta kai karan sa wajen kaamil Magana take yi azafefe har tana bari,she was soo bitter Cikin furucin ta har take cewa Ai bani nace ina son shi ba da zai dinga wulakantani Ga maza nan iri iri?idan yasan ba aure na zaiyi ba sai yaje ya gaya ma grand ma dilshad asan nayi cos am very sick of him and his super egoistic attitudes.. Wato yaga ina bin shi ko…hmmmm cikin bacin rai take kada kafafu tana kukkuni Abun gaba daya ya dame kaamil dan bai masan tana yawan zuwa wajen sa’ood din ba Yace toh kinsan ya za’ayi?let me call him right now sai muji mai zaice Ta ce to nidai kasa a handsfree dan kaima ba gaskiya kake fada min Kallon ta yakeyu don Abun nata kamar zai bashi dariya amma kuma fuskanta bai yi kaman haka ba dan haka ya dailling call number khaldun Bugu daya kuwa sai gashi an dauka. Khaldun din ne ya fara magana cikin murya mai alaman bacci Yace kaamil, Brother… Wani nitsetsan murmushi kaamil yayi cikin kamiya yace bacci kakeyi? Toh let me call you leta kenan ko!…. A lokacin wani mugun harara junnuta ta banka masa,tunn kafin ya daga idon sa Sai gashi khaldun din yace nooo ba bacci nake yi ba..wannan da naga kiran ka da tsakar ranan nan Any prblem? Dan gyaran murya kaamil yayi yace not realy,dama dai ina so muyi wata magana ne,kai tsaye yace masa its about junnut… Wani 2min silence khal yayi dan zai iya yuwa ma bai wani rike sunan ta akansa amma dai ya gane meya ke nufi2 Bai daice komai yace r u coming now? Gaskiya bazan iya magana a waya ba,kaamil im really lonely!..ya dan marairace murya Kamil sai yayi murmushi”need some brothers love? Dariyar gefen baki khal yayi yana yunkurin tashi Yeah,..Come let me spoil u on the road…ya furta a sakalce yana mikewa akan gadon sa. A tare Duka suka yi murmushi mai sauti Dan tseren mota shine abu mafi sanya su nishadi a rayuwar su. Agefe kuwa ran junnut ne ya dada harzuka ya dada konewa wani zafi kirjin ta ya shigayi,ohh ya ilahi So he is lonely, amma baya bukatar macen da zai aura a kusa da shi sai namiji dan uwansa. Haka kawai ta fara bori tana masifa cewar ta zata je kawai tace a warware alkwarin ita tagaji da wulkanci. 2 Kaamil Tun yana lallabata yana ce mata “ai karatu kikeyi,khal baya so yana takura ki ne” har ya gaji ya dawo banda dariyar ta babu abunda yake1 Ita kam Har da guntun hawayen ta Dan kuwa Tana son khal yanzu sosai,sai ta dinga complain barkate harda laifin karyan da kaamil yake mata Na cewa khal na kulawa Tace kaamil na lura sam ba so na keke ba,ure my quardian amma babu ruwan ka da damuwa ta Kana dai gani yana azabtar da ni amma ko ajikin ka dan kaima baka son ganin laifinshi Wato warayya kake nuna min dan ni ba sister ka bako? Gaba daya junnut ta haura ba sauki haka dai kaamil Yayi ta bata baki Har suka shirya zuwa fuskantan khaldun tare. All black Armless shirt and rubber short,yabar suman kansa carefree,ya gama shiryawa car racing dinsa yana ta jiran bro dinsa charaf sai ga kaamil ya taho masa da junnut Tsaki yayi aransa amma Sai yayi kamar bai girgiza ba ita kuwa Kamar mayya ta noke tayi shiru batace uffan ba,Tana ji suka gama gaisuwan su1 Hannun sa sanye da black racing mask Yace ma kaamil din shall we! nan kaamil ya dan riko sa yana yake yace bro baga ka bakuwar ka bane? Naga kamar baku gaisa ba Khal Sai yayi shiru yana kallon kamil din,Da idanun su suka maida ma juna zance khal yana masa alaman to inna naganta sai me zanyi mata? Kuma yasan Tsaff ta gane komai Kan sun hankara junnut ta zuciya zata bar wajen kamil sai yayi saurin riko hannun ta yana cewa ke wai ina zakije! A dan fusace ta juya”Idanun ta har sun ciko tace Ni tafiya zanyi,bayace baiya son gani na ba ai yace ya gaji dani…sai tsirrrr hawaye suka sauko mata ta shiga sharewa.. Kaamil yayi shiru baice komai ba a karo na farko khal yaji bai kyauta mata ba dan sosai ya lura da fushin da yake dawainiya da ita7 Amma sam shi baisan ma me xaiyi mata ba1 Har kaamil zaiyi mata magana sai ya masa alaman yayi shiru ya sake ta ta tafi kawai. Ita kuwa dataga hakan sai ta dada tunzira Kamar zata fashe ta fincike hannun ta , Tana sa kafa zata bar wajen khak ya dan juya ya kalle ta bayabo ba fallasa yace ma keyar ta Sorry”.. Toh Kafin ma ta juya ta ya ja hannun kaamil kamar zasu sakai Data ga hakan Sai ta ja tsaki mai sauti hawayen ta ne suka fara zuba babu control ta shiga gogewa tana cigaba da tafiya a fusace Zuciyan kaamil sam bai gamsu ba,sai yace Bro pls Stop dan Allah ka tsaya kasaurare ta we can play after that ko! Kaamil ya roke shi cikin nuna damuwar sa Dan shiru yayi kafin yace masa Ok..amma baiyi yinkuri ba Can i call her back? Kaamil ya tambaya Sai ya gyada mashi kai shikuwa a gurguje yabi bayan ta baice mata uffan ba ya jawo hannun ta suka dawo duk dama tana jajjan sa alaman tayi zuciya ita bata so… Da suka iso gaban khaldun,sai ta fara fincikewa “Just let me be..ta tura hannun sa ta harde ranta ta kau da kai Kammil ya tabe baki…”Ke baki da hakuri junnut, wai fushin me haka?kawai wai dan mutum yace ya gaji toh waye baya gajiya?…she hates when he alwys side with his bro dan haka ta banka masa wani harare Tace toh ina ruwan ka ai shiyasa nace zan tafi u stay with ur holy brother Abun nasu har mamaki yake bada khal daya tsura musu idanu yana binsu da kallo kamar masoya biyu sun kawo masa kara1 Har Sai da sukayi shiru,kafin ya dago ya kalle ta Daurewa yayi Yace Meke damun ki?… Bata amsa ba taja dogon tsaki Wani mugun hada rai yayi ya shanye Kaamil yace junnut ke fa bakijin magana,memakon ki nitsu a schl kiyi jacking kinzo kina haura ma mutane da masifa,Whats wrong with you har ta dago azafefe zata amsa muryan khaldun ya dakatr da ita Hey its ok … Sai Ya juya ya kalle kaamil ka barta kawai We can play together. Sai ya juya,..i really hate noise ya kada kanshi yana maganan cikin wuya kamar bada su yake ba Junnut Ji tayi kamar zata nitse kasa adena ganin ta a duniyan nan tsaban takaici wai itace namiji yake kaskantar da ita haka?yau ta dada gane cewa ashe kuwa da tayi kuskurren auren sa cikin gaggawa da hawan jini da bakin cikin sa zai iya kashe ta . Cike da dauriya ta dage tace thanks but I dint come to play Kaamil pls lets go in baka tafiya ni zan tafi.. Wani lumshe ido Kaamil din yayi yace pls dan Allah kibari, Khal nawajen amma yadda ya dauke kansa kasan yayi banza da sune Sai da Kaamil ya jawo ta kusa dashi sai ya juyo. Kamil yace pls lets setll dis now. Duka basu ce masa uffan ba Anan ya fara magana na fahimta, har yayi kokarin bursting asalin case din cikin mayar ma khaldun duk abunda yake yi wanda junnut bata so at same time yana kokarin shan bakin dan uwan sa Dan ya gama lura da cewa kwata kwata junnut ba type din khaldun bane. Ita kuwa junnut da kaamil ya fayyace laifin kowa sai taji dan dama dama ranta Dan shiru khaldun yayi daga bisani yace mata “am sorry…kafin ta daga ido ta dube shi sai yace..if u feel that way… sai ta yi shiru tana nazari,”sorry if i feel that way?? Ohh that means baima yarda hakan dayake min laifi bane? Atake jikin ta yayi sanyi tanajin wani karyewan ziciya, To amma tunda har ya furta sorry whats the points?sai tace mashi its ok.. ta dan juya kanta gefe tayi shiru Dan dariya kaamil yayi musu aransa Sai suka barta a farfajiyan cikin gidan tana tsaye su suka shiga fitowa da racing cars dinsu Sport cars ne na benz da bmw anyi personalising jikin su da kalolin khakin asalin sojoji daya kuma khakin marine corps. Kaamil yace mata tazo suje ta kalle race din su,wani tunani tayi sai tace suje su dawo zata jira su agidan,ba wanda yayi mata musu Har suka fice suka tafi abunsu,zuciyan ta har iyanzu bai wani sauko ba,ruwa tasha tasa aka dafa mata noodles taci sai chan tayi amfani da wayar ta tayi odering kayan sakawa da make up 25 minutes delivery ya ruske ta Cikin daya daga spare rooms acikin dakunan gidan,anan dama ta aje kolin ta har tayi wanka ta kimtsa, normal table gown A shape tasa ta dada gyara suman kanta bata wani dade ba sai gasu sun dawo. Tsayuwa tayi tun daga window tana kallon su suna ta surutu thy look soo cute together Amma halin khaldun har yanzu shiya fi jefa ta cikin nazari,wato shi Namijin da ya fiye bada wahala ma zuciya mace kuma tafi nace wa ma sonshi3 Ta so ace yadda take gani yake nuna kulawa akan kaamil haka itama zai nuna mata. Ita ko bai kai haka ba in zai na kulata toh babu damuwa arayuwar ta. Anan kuma bayan sunyi parking suka shiga sukayo sallah tare, toh khaldun yana idarwa ya nufi dakin sa shikadai ,fitowar sa daga wanka kenan sai ga kaamil ya biyo bayan sa Waje ya aamu ya zauna…yana ta kallon sa,Kaamil Yana so suyi magana na fahimtar juna akan junnut amma khaldun yaki sam..iya kaci yace masa junnut ai karamar yarinya ce meta sani? Ko yace Shi sam baya son shirme Kaamil dai yasan ba iya dalilin bake nan amma sai ya hakura ya share Da kyar ya matsa masa ya amince akan idan zasu tafi gida ya biya sukai junnut din shoping…