KUDIRI CHAPTER 2

KUDIRI





CHAPTER 2




Yauwa, gwara da Allah Ya san a gan ku tare. Angwayen ne suka zo tare da matan da zasu dauki amarya. Duk da dai Azare za a kai ta, sun bukaci a yi komai da wuri a kan lokaci. Na yi bayani wa Gwaggonku Tambaya, yadda za a bayar da garar bikin.” +

Asiya ta gyada kan ta, alamar ta fahimta. Ta fi kowa sanin yadda Dada ta sha wahalar tara garar Maree. A hidimar wannan biki kadai sai da ta sayar da shanun ta biyu hade da gonar da ta ke sa a noma mata gero da damina. Ta yi hakan ne don kar a ga gazawar su. Duk da ma Mudassir ya hana a sayi kayan daki. A cewar sa , ya tanada ma ta komai na kece raini. 2

Ku san duk matan garin a nan kowacce za ta ci ta gyatse sannan ta kai wa bataliyan ta gida idan ta tashi komawa. Haka al’adar garin su ya ke idan a na biki. Asiya abin haushi ya ke bata. A yi ta wahalar daurawa a sauke ba kakkautawa. Da a ce tana da iko, da lokacin auren ta in ya zo babu wani tuwon da za a yi.

Kawai garin za a kukkula da kuka, a raba wa kowacce mata, idan ta je gidan ta girka. Muhibbat ta sha dariyar wannan ra’ayi na ta. Oho dai. Allah Ya gani, da gaske ta ke yi idan za ta samu halin yin hakan. 3

Haka ta fita ta shiga shirin tara kan kawayen su da ma wadan da za su kai amaryar dakin ta. Ba ta kaunar ta sake bata wa Dada ran ta.

Motoci hudu ne kanana, hade da bus-bus manya guda biyu suka je diban jama’a. Mata kuwa suka cika tab don kuwa babu wacce ta ke son a bata labari. An gama bikin gidan su amarya, sauran na gidan ango.

An bar garin a na wake-wake cikin jerin gwano:
A yau rana na hazo,
A yau rana na hazo
A yau rana na durum durum
Rana na hazo
A yau Maree ta na fushi, Mudassir sai murna ya ke mata
Rana na hazo

Sun isa garin Azare misalin karfe bakwai na dare. Kasancewar an takura cikin motar, kowa sai hamdala take yi, don za su samu su huta. An kai su kofar wani gida a ka tsayar da su, ko kofar ba a bude ba.

Mata suka rika alla-alla a bude su shiga don akwai ma su laluri, wasu kuma yaran sun a ta fitina a motar. Abin da a ka fara da wake ya koma damuwa.

Wahalar dai bata kare ba, don sai a ka sake daukar kan motocin, a ka kuma nausawa wa ta unguwar, bayan abokan angon sun fita sun yi magana a tsakanin su. Sun koma dai suka rika ba da hakuri, kan cewa sun yi batan kai ne.

Wasa gaske, a ka rika yawo da su a gari, a na kewayawa, amma ba su kai wannan gida ba har suka kai misalin karfe tara. 1

“Kai, wai abokin ango, wannan wacce irin wahala ce da ukuba? Wannan gida kamar ya bace mu ku a doron kasa? Sai ka ce za mu kai ta karshen Nijeriya?”

Direban da ke tuka motar da suke cikin ta, wanda ita ma Maree ke ciki tare da Asiya, ya yi murmushi cikin neman afuwa, ya ce, “Ki yi hakuri Baba. Gidan Angon ne na nan garin ba mu san shi sosai ba. mun fi sanin gidan sa na Bauchi, shi yasa kika ga muna yawo.” 1

“Yo wannan ai da ma Bauchin kawai ku ka kai mu, mu san mun kwashi hanya. Amma yawon nan har jiri ya fara saka min da ciwon kai.”

Direban ya ce, “Ki kara hakuri dai Baba. Gidan Bauchin ne ba a gama ginawa ba, gefe daya ne ya gyara sauran ukun bai karasa gyarawa ba. To yadda bikin ya zo ma sa cikin gaggawa ya sa shi yanke shawarar ya zauna a nan din kawai. To kun ga dare ya yi, ga shi ba mu san garin sosai ba. Angon ne fa da kan sa ya ke ma na kwatancen gidan da kan sa a waya.”

Rufe bakin sa ke da wuya, wayar sa ta dauki kara. Sau takwas ke nan, Asiya ta na kirgawa. Ya sake tsayar da motar sannan ya fita daga cikin ta don ya amsa. Gwaggo kuwaa ta ci gaba da sababi, wai bai amsawa a gaban su sai ka ce munafiki? 4

Sauran direbobin ma suka fita suka tarar da shi. Suka koma gefe suna Magana kasa-kasa. Ai kuwa Gwaggo Tambai ta fita ta same su cikin masifa, “Anya, kun kulla gaskiyaa kuwa? Tun dazu kuke ta yawo damu harm un haddace hanyoyin garin ma. Sannan motsi kadan sai ku tsaya mitin sai ka ce ma’aikatan gwamnati. Ko dai ku din ‘yan yankan kai ne?” 5

STORY CONTINUES BELOW


Suka fashe da dariya gaba dayan su, “Ah haba Baba. Koma ki zauna don yanzu kam mun gane kwatancen. Kwantar da hankalin ki. Za mu tafi yanzu.”

Bayan ta zauna, kowane direba ya koma motar da ya fito tare da albishir din sun gane gidan. Kowacce mata ta shiga hamdala, tana alla-alla a isa gidan.

Asiya na zaune a gidan gaba, ba ta ce uffan ba. direban da ke motar su ya sauke muryar sa ta yadda su biyu suke iya jin sautin muryar sa, y ace, “Ran ki ya dade, mun samu gidan fa. Ko murmushi ai sai ki yi. Ga shi tun da ki ka shiga ban ji kin ce komai ba.”

Ba ta kula shi ba, don tun shigar su motar ta lura ya na neman shige ma ta. Musamman ma ya dage kai da fata, kan sai dai ta shiga motar ta sa ta zauna a gaba

Motar kowa yayi tsit, hakan ya sa ta jin takura har suka kai ga wani lungun da ya kai su ga wani katafaren gida mai farin fenti da bakin get. Sun dan tsaya kafin a ka kai makullan gidan sannan a ka bude.

Gwagggo Tambai dai ta yi ta mita, ta na cewa a she gidan ma ba wani boyayye ba ne suka wahalar da su a Karin banza. Gidan kawatacce ne, ta kowane yanayi a ka duba. Cikin kuwa ya shan kwalliya da kayan alatu na zamani, kama daga kujeru, kayan kicin da kayan daki.

Da gaske ne, Mudassir yayi tanadi wa Mareensa don ta more rayuwa. Asiya sai da ta yaba hakan. Kayan sun burge ta, kama daga launin su, zuwa tsarin su, duk da cewar bas u kai na gidan Dokta Yusuf da ta shiga ba. ta tsayar da kan ta. Me ya hada ta da shi kuma, da har tunanin sa zai fado mata? Sa kai a uku mana, wai takabar suriki. 4

Kasancewar kowa ya gaji ga kuma yunwa, babu wadda ta nemi komai. Kawai kwanciyar su suka yi, aka bar ma su yara da nema mu su abin tabawa. A ganin Muhibbat, ma su son gulma ne, don kuwa su da ke neman abinci, me ya kais u zagaye gidan gaba daya?

Da gari yawaye, ‘yar tsame a ka kai musu hade da burodi da ruwan shayi na karyawar safe. Bai kai kan su ba, sai da suka kira abokan ango, wadan da suka hado mu su da soyayyiyar doya da kwai mai hijabi suka kara. 5

Sun yi ta ba su hakuri ne, kan cewar an bayar da dafa abincin wa Destination Hotel da ke garin Azaren, amma sun kwafsa mu su ne. da rana kam sun yi alkwarin samun canjin yanayi.

Da gaske kuwa, zuwa hantsi, sai ga gasasshen rago dungurungum mai maiko nyas, nyas, nyas, sai kamshi ya ke yi. Ga kuma soyayyun kaji mai fefe sur langa. A ka hado mu su da taliya mai miya da dafa-dukan shinkafa.

Akwai soyayyun kifi karfasa, da kuma ganda mai romon yaji yaji. An bankare musu zabbi sun gasu, kan cewa idan za su koma su yi tsaraba. 11

Kowacce kuma ta washe, a ka shiga danasha a na goge wuya. Ba kula da taliyar ba ma, an mayar da hankali wajen burosh da makilin kawai. Ruwa da jus-jus ba a cewa komai. Sai diba su ke suna kora wa don maganin zafin garin Azaren nan. 2

Muhibbat kuwa kada kan ta kawai take yi, tana cewa za a yi ta waajen zawayi da gudawa idan suka koma gida. Kowa kawai diba take cikin cikin ta da ma leda, ana jinjina wa mijin Yalwaji-Mariya kan wannan hidima. Ta san za a koma a samu na yi tsawon kwananki.

Bayan azahar, abokan ango suka bayyana, sannan suka kwashe ma su biki, a ka bar kawaye tsiraru kawai. Wasu sun koma ne, suka bar sallahun idan an ba da kudin sallama to a kai musu Kason su can Dagauda.

Maree dai tun daren da suka je ta ke cike da farin ciki da annashuwa. Sai zagaya gidan ta ke, bayan an waste, tana jin nishadi. Hakika mafarkin ta ya zamto gaskiya. A wannan rana ta samu yadda ta ke so. Ta yi aure cikin daula, kuma wanda take so ne ta aura. 2

Asiya ta yi mata farin ciki kwarai da gaske. Ta rika tunanin da a ce ta yi abin da ya sa a ka fasa wannan aure da tayi wa Maree hasara.

Kuma Maree ba zata taba yafe ma ta ba. Wata kila ma rabon zama ne ya kai Mareen, don haka ta yi alkawarin bin su da du’s kawai. Aure hakika, rufin asiri ne.

STORY CONTINUES BELOW


Maree ta rika zumudin zaben dakin ta na kwana a gidan, cikin dakuna biyar din da ke gidan. Kowanne kawatacce ne, amma sai ta zabi na kusa da wanda ta ga kayan Mudassir a cikin sa. Duk da dai ba ta da niyyar raba daki da shi, gwara dai ta zaabi na kusa da shi din.

Lokacin da ta shiga kicin sai ta kara rudewa, saboda ko a mafarki ba ta tsammanin mallakar irin kayan da ke ciki ba. deep freezer, firij, abin dafa abinci na iskar gas da na wuta, har ma da kabet na jera filet. Ga wajen cin aabinci da aka tanadar ma sa tebur babba, shi ma da na sa kabet din a gefen sa.

“Gaskiya Maree, kin samu aljannar duniya.” In ji Muhibbat. “Kin samu yadda kowace yarinya ke burin samu. Kin yi sa’ar aure.”

Maree ta wulkita idanu, ta na jin kanta kamar ta tashi sama cikin shawagi. Ta ce, “Wannan ma kadan ki ke ji. Domin Mudan ya yi min alkawarin cewar da zarar na tare, to zai mallaka min mota.” 8

“Mota? Kai Masha Allah! Allah Ya saka mu a danshin ki.” Muhibbat da wasu kawaye suka furta a lokaci guda.

Wata cikin su ta kara da cewa, “Ai ni da zan samu gida irin nakin nan, to da wallahi na huta. Sai ko na nemi lahira, amma duniya kam na samu.”

Maree ta gyara zama ta da kyau, ta ce, “Dube ni da kyau Kursiyy, ruwa ba sa’an kwando ba ne, kuma ko da jijjiga kurna ta fi magarya. Na fi karfin ki raina min hankali, kin ji ko? Na fi karfin ki wallahi.”
Kursiyy ta kalle ta, “Me ya kawo wannan magana kuma?”

Maree ta Harare ta, “Ga ni na yi za ki rena min hankali. Ki dube ni, ki ga wurin da nake. Wallahi duk Dagauda babu wacce za ta samu gata irin tawa. Don haka idan mafarki ki ke yi to ki farka, ehe!” 10

Kursiyy ta ce, “Komai nisan gari fa akwai wani a gaban sa. Har ke wacece za ki ce duk garin mu babu wadda za ta samu abin da kika samu? Dabarar ki ce ko wayon ki? Kuma dai na gani gidan uban ki bai fi na ubana ba.”

Maree ta ce, “Yarinya fi ni da gidan uba, ni kuma na fi ki da gidan miji!”

Da kyar su Muhibbat suka kasha wutar wannan sa-in-san. Kowa ya san Maree wajen ji da kan ta, da son nuna ta fi karfin kowa. A kullum nunawa ta ke babu wacce za ta kai matsayin ta, tun da babu waccee ta kai kyaunta. 2

Sai da Asiya ta fidda da ta daga dakin, sannan ta ce, “Haba Maree, ke da yau ranar farin ciki ne gare ki, me zai saa ki rika cacar baki da kawar ki kuma?”

“Mun raba gari da ita wallahi, ‘yar rainin hankali kawai.” Ta fada tare da murguda bakin ta.

“Kar ki ce haka. Kowa da ki ka gan ta nan za ku rabu ba da dadewa ba.” Maree za ta sake magana ta katse ta, “Ya isa haka don Allah. Yanzu za a shigo sayen baki. Me kike so abokan angon su ce?”

Rufe bakin ta ke da wuya su ka ji karar ham da shigar motoci harabar gidan. Maree ta yi murmushi, “Ina ga fa sun iso.” 2

Su ka koma dakin kamar ba abin da ya faru a lokacin. Abokan ango suka shiga ciki tare da sallama, kowanne cikin su ya sha shadda, sai kamshi ke tashi.

Daya daga cikin su ya ce, “Kun gani, ashe nan wajen suka boye.”

Wani ma ya ce, “to gas hi kun zauna kan gado, ba ma da wajen zama.”

Muhibbat ta ce, “Ba ga kafet ba? ai sai ku zauna hankalin ku kwance.” 1

“A kasa kuma? Duk kwalliyar nan ta mu?”

Wata mai suna Larai ta ce, “To ko wurin ya yi mu ku girma ne? Kun san fa yau amarya ke mulkin ta na isa da sarauta. Don haka tilas ta zauna a sama.”

“To ai ba ita kadai ke mulkin ba yau. Shi ma angon sarki ne a yau.”

Muhibbat ta ce, “Bismillah, idan kun ga za ku iya ba sai ku zauna cikin mu ba.”

Duka su ka bushe da dariya, “A’ah, amarya kina jin abin da su ke cewa ko? Kin yarda a bar angonki ya tsaya sai kkace ya hadiye tabarya?”

Dukan su kawayen suka ce,“A’a, mun ki wayon. Amarya ba za ta yi magana ba sai ango ya saya.”

Abokai suka yi saranda, “To ai gani na yi kun hade baki ne, shine na ce na san dole amarya ta goya wa angon na ta baya. Ko bah aka ba amarya?”

Babu wadda ta kula su. Ganin hakan ya sa suka kuskusta a tsakanin su, sannan suka fuskanci kawaye, “To mun ji. Nawa ne ango zai biya don amaryar sa ta yi masa magana don fa ya kosa.”

Daga nan fa a ka yi jayayya kan kudin har aka tsaya kan dubu talatin. Ango biya nan take. Su ka ce, “To amarya sai ki yi wa angon naki murmushi, tun da ya nuna kosawa a kan hakan.”

Maree ta dan yi murmushi sannan ta hade kai da gwiwa don kunya. Su kuwa suka rika dariya. Muhibbat ta ce, “Ah, yaya haka? Kun biya kudin magana kuma ku ce a mu ku murmushi? Kun san fa murmushi ya fi tasiri a kan kalamai.”

Wani abokin ango ya ce, “Kai, ke kam ba dama. Sai ku fadi kudin murmushin, za mu biya.”

Wani daban ya ce, “Ba haka ba.” Ya nu na Asiya, sannan ya ce, “Ita kuma wannan nawa zan biya don sayen na ta bakin?”

Gaba daya a ka mayar da hankali a kan su. Kallo daya Asiya ta yi ma sa, sannan ta kawar da kan ta. A halin yanzu ta kara tsanar jinsin maza, saboda yaudarar da Yusuf-au Khalid yayi wa Maree.

Maree. Shin mijin ta ya san halin da take ciki kuwa? Idan ya sani me zai faru nan gaba? Ta yaya za ta yi rayuwar aure a haka? Ta kalle su daidai. Gaskiya Muhi ce. Murna ya kamata ta taya sub a yawan tunani ba. 2

“Wannan kanwar amarya ce.” Ta jiyo muryar Muhibbat ta na bayani.

“Ai fa, ga kammani na gani kuwa. Ko shiyasa ita ma take na ta mulkin ne. domin tun jiya na yi nayi tayi min Magana amma ta yi biris.”

Muhibbat ta ce,“Ai sai ka jira ka aure ta tukunna ka yi maganar sayen baki, idan har ta na rabon ka ke nan.”

Ya yi ‘yar dariya, “Ki ka sani ko a yi da ni?”

Nan Asiya ta sake daga kan ta ta kalle shi. Ba kyakyawa ba ne cancan, amma ya na da kwarjini da fara’a. Duk cikin abokan shi ya fi walwala da sakin fuska. Ga shi ya sha jamfar sa ta shadda mai ruwan toka, ya na haskawa.

“Amarya, tun da bakin ki ya bude, za ki ban kanwar nan ta kin a aura? Don wallahi ta yi min.”

Asiya ta kalle shi kawai, a yayin da ta ji zuciyar ta ta buga, amma ba ta tanka mu su ba. Ta mike tare da barin cikin dakin, ta na jin lokacin da Maree ke ce ma sa, “Ka same ta ku daidaita kawai idan da gaske ka ke yi.”

Lokacin da ta koma, wata mai suna Sa’ade ta ce mata, “Su Laminde a na ja wa bawan Allah rai. Kar fa ki ja da yawa ya tsinke.”

Ba ta kula su ba, don kuwa ba lallai ne ta fada mu su cewar namiji ba gaban ta ya ke a lokacin. Maza sun aba ta tsoro fiye da dajin Falgore, idan ma ta san wurin da dajin ya ke ke nan. Ita dai ta sha jin labarin dajin, cewa ya na kunshe da abubwan almara kala kala. 2

Muhubbat ta ce, “Ki ba da kai kawai bori ya hau Minde, kin ga sai mu je mu sha biki a Kano. Kin zama matar Rabi’u Gwammaja, ‘yar babban birni.” 1

Maree ta murgude bakin ta ce, “Ke Muhi, da ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? An ce mi ki Laminde za ta amince ne? Ai ita ba za ta bar Dagauda ba, can za ta yi aure ta zauna.” 5

Ba bu wacce ba ta fahimci gatsen da maganganun Maree ke dauke da shi. Asiya ta ci gaba da kimtsawar ta. Ta dade da sanin cewar a rayuwa, Maree ba ta kaunar a ce ta fita, ta kowane bangare ne kuwa. Ba ta damu ba, don ta san komai na Allah ne.Assalamu alaikum.”
Muhibbat ta yi sallama tare da shiga tsakar gidan su Asiya. Ta tsuguna ta gaida Dadan.
“Oh, ‘yar halak kin yi Ambato. Yanzu na ke shirin tura Laminde gidan ku ta kira min ke. Sai ga ki da kan ki ma.”

Muhibbat tayi murmushi, “Ni ma tun jiya na ke son zuwa amma Allah bai yi ba sai yanzu.”

“Allah Sarki. Yaya Iya? Sauran mutanen gida lafiya?”

“Lafiya kalau Dada. Su na ce na gaishe ki.” Ta ja kujerar da ke gefen Dadar sannan ta zauna a kan ta, ta ci gaba da cewa, “Da ma tun jiya da dare mu ka yi waya da Maree, ta ce don Allah na gaishe ku, in kuma ce da ku ta na nan lafiya.”

Jin hakan ya fiddo Asiya daga cikin dakin su, wurin da ta shiga yin sallar la’asar. Tun kwanaki take yawan damun Muhibbat, kan ta yi waya don su gaisa da Mareen amma ba ta samu dama ba.

Dada ta yi murmushi mai fadi, “Allah Sarki. Dalilin kiran da zan miki ke nan. Da ma gani na yi tun da suka koma gidan sun a Bauchi, babu wanda ya je ya dubo su. Shine na ke shirin tura Laminde. Amma na san kin fi ta sanin wajen na ta. Ko za ki iya yi ma ta kwatancen?”

Asiya ta saki murmushin jin dadi. Tun bayan dawowar ta daga Bauchi, Dada ba ta yarda ta yi nesa da ita ba, musamman ma da ta ji sun koma Bauchi.

Komawar ta su ma ya kasance ba a sani ba a gidan su. Ta shi ne ya tashi, kamar yadda Mareen ta fada, cewa mahaifyar mijin ta ta bukaci ya mayar da ita can, don ta na son su zauna tare.

A ranar Maree ta samu watanni biyar ke nan da aure, sannan watan ta uku a Bauchin. Shi yasa ma Dada ta yi tanadin garin kuka, kubaiwa busasshiya, daddawa, manshanu galan guda da sauran wasu tarkacen da Asiya ba ta san kan su ba.

“Ai kuwa ni ma ina ta son na je Bauchin don karbar wasu kayyayakin da aka sayo min daga ta Habuja. Gobe ne amma tafiyar in Allah Ya kai mu.”

“Kin ga faduwa ta zo daidai da zama ke nan. Ita ma Laminden sai ta shirya ku je tare goben idan Allah Ya kai mu.”

Bayan tafiyar Muhibbat, Asiya ta rika jin hankoron son ganin ‘yar uwar ta. Ta kagara gari yaw aye. Da, a tunanin ta wani abin zai faru, amma ko da ta ga har a yanzu babu komai, sai ta kwantar da hankalin ta. Ai lafiya c eke buya, ko kuwa? 5

Da sassafe suka shiga motar Sani kwatambe ya kais u har tashar mota da ke kasuwar central a Bauchi. Kasancewar sa mai kaunar Muhibbat, bai karbi kudin su ba. su ka yi ma sa godiya. 2

“Muhi, yaushe ne za ki kira mu, mu sha bikin ki da Sani?”

Muhibbat ta harare ta, “Jiya.” 2

Asiya ta fashe da dariya. Ta san Muhibbat ba mai zaben maza ba ce, amma ta fannin Sani kwatambe kam, iska ce ke wahal da mai kayan kara. Ya na ta cusa kan sa, ita kuwa bai dame ta ba, don bay a gaban ta.

“Me da wukar. Daga tambaya?”

Muhibbat ta bude jakar da ta rataye mai launin ruwan kasa, wanda ya shiga sosai da atamfar ta na Diamond. Asiya kuwa doguwar riga ta saka na wani yadin material mai kyaun gaske.

“Ya kamata mu kira Maree, ko za ta sa a turo motar gidan ta a dauke mu. Kin san zuwan ba-zata mu ka yi.”

Ta na magana tana latsa lambar. Da ma tun can ita ke da lambar. Ita kuwa Asiya ko wayar ma ba ta mallaka ba. lokacin da Maree ke gida ne ta kan dauki na ta ta amfani idan ta na bukata. Ko da tayi aure ba ta bar ma ta ba. ta dai yi mata alkawarin aiko ma ta da wannan kwance da zarar Mudassir ya saya mata sabuwa, babba.

STORY CONTINUES BELOW


Muhibbat ta kara wayar a kunnen ta, ba da dadewa ba ta saki murmushi, “Hello, mutuniyar. Kin san a ina muke ni da Minde a yanzun nan? To mu na kasuwar central…..na Bauchi mana….don Allah ki turo da mota a dauke mu, don mu na jira.”

Asiya ta kara jin zakuwar son ganin Maree. Ta tabbata Mareen ma za ta dimauce don ganin su. Tun da suke ba su taba rabuwa na tsawon wannan lokaci ba. Lallai, yau akwai labari, ba ta yi tsammanin za su runtsa ba. Alhaji Mudassir kam sai dai ya yi hakuri, don za su dauke ma sa mata na dare daya.

Ganin canjin yanayin fuskar Muhibbat ya sa ta tsayar da hankalin ta a kan ta. Ta ji ta na cewa, “Ke don Allah ki bar wasa. Dada ce fa ta turo mu duban daki.” Ta na maganar fuskarta a daure.

Asiya ta shiga tunanin akwai matsala. Bayan Muhibbat ta ajiye wayar ne ta kalle ta, “Kin ji fa wai ba sa gari. Jiya jiyan nan su ka tafi Legas. Kuma wai gidan na su babu kowa.” 1

Gaba daya ran Asiya ya baci. Kash! Da sun sani ma su sanar tun farko. Shi yasa ziyara a birni yake da wuyar sha’ani. Ta kalli Muhibbat, “Ta fada miki lokacin da za su dawo ne?”

“Ta ce za su kai wata guda kafin su dawo. Wai tun dawowar su nan garin ma bas u zauna ba. yau suna Kaduna, gobe Habuja, jibi Yola. Kin san manya.” 1

Duka suka yi murmushi, “Ba laifi kam, wai an yi duka wa ‘yan biki har an karya kafar uwar amarya.” 4

Muhibbat ta yi dariya, “Minde, ba ki dama. Yanzu dai karfe biyu saura kwata, kuma ban san ke ba, amma yunwa tana kwakular cikina wallahi.”

Asiya ta ce, “Ni ma haka. Ga gajiya.”

Tun safe ba ta sa hatsi cikin bakin ta ba, tsabar zumudin son ganin Maree. Amma gas hi bas u yi sa’a ba. ga babu wanda su ka sani a garin. Ya zama tilas ke nan su koma, duk wa ta fata ta zube a kasa.

Wani mai Keke Napep ya tsaya a gefen su, “Yaya Hajiya, tafiya ne?” ko da ya kalli Asiya sosai, ya yi murmushi, “Ikon Allah! Hajiya, yau Allah Ya sake hada mu.”

Asiya ba ta gane shi ba, ba ta tsammanin ma ta san shi. Amma sai ya kara yi ma ta bayani, “Ni ne na dauke ki kwanaki can da dadewa na kai ki asibitin Sauki da gidan Dokta.”

Mamaki ya kusa cinye harshen ta. “Kwarai kuwa, an yi hakan. Ta yaya a ka yi ka gane ni?” Ita kan ta ko hanyar ma ba za ta iya tunawa ba, balle wanda ya dauke ta ya kai ta.

Ya dan sosa keyar sa, “Ai fuskar ki ba mai saurin bacewa wa mutum ba ne.”

Asiya ta lura Muhibbat ta kawar da kan ta gefe a kokarin ta na danne dariyar da ta kwace ma ta. A bayyane ne, mutumin ya kyasa ma ta. Ita ma ta cije, sannan suka gaisa da direba.

“Yau ma asibitn kuka kara zuwa?”

Ta girgiza kanta, a yayin da surar Dokta Yusuf ya gifta a zuciyar ta da idanu. A duk lokacin da aka ambaci asibiti ko ma Bauchi to sai ya fado mata a rai. Ba ta son hakan, don bai kamata ba. Amma ba ta da yadda ta iya. Idan ya kutso sai ta mayar da shi, a zauna lafiya.

Kawai kamar daga sama, ta ji Muhibbat ta tambaye shi, “Ka san Musaba Motors?”

Ya gyada kan sa, ita kuwa Asiya ta tsaya kallon ta. “Nan ne zan kai ku? Ina ce wanda ke wajen hanyar zuwa Zango?” Muhibbat ta ce, “Ina mu ka sani. Mu dai ka kai mu kawai.”

Asiya ta taba Muhibbat a lokacin da ta ke kokarin shiga cikin keken, ta ce, “Me kike shirin yi ne haka?”

“Me ki ke tsammani? Ta yaya za a yi mu juya yanzu mu koma Dagauda? Me za mu je mu fada wa Dada? Sannan a gaban ki Baban ya aike ni wajen Mudassir. Me zan je in fada masa?”

Asiya ta ji lokacin da mahaifin su ya ce da Muhibbat ta je ta yi wa Mudassir tunin gyaran gidan sa da yayi alkawarin yi masa, don an kwaye dakin sa tun wata daya da auren su kamar yadda ya umurta, amma har a lokacin a cikin sito ya ke kwana. Sannan idan ya na da wasu kudade ya aika ma sa, don ya ga wani babban fili har sun yi ciniki, ya na son ya saya. Duk ta ji, amma ba wai ran ta da ma ya so ba ne. 5

STORY CONTINUES BELOW


“Mu je mu ce musu ba sa gari mana.”

“Amma dai ba yau ba. Zuwa za mu yi wajen sayar da motocin sa, in ya so a kai mu gidan su. Kar ki manta, shi fa dan gari ne sannane. Dole ba za a rasa wanda zai kai mu gidan iyayen sa ba. Ko can sai su ba mu masauki.”

Muhibbat ta shiga ta zauna ciki sannan ta make. Fuskar ta ta nuna alamar da gaske ta ke kan kudirin ta. Ba yadda ta iya, a bisa dole ita ma ta shiga ta zauna, sannan mai keke ya ja su suka fara tafiya.

Ba wai lokacin damina ba ne, amma Allah Ya kiyaye su bata. Ga shi yanayin garin Bauchin ne sa a hankali. Sun sha jin labarin yadda mutane ke bata, sai ka ce kwabo.

Musaba Motors wajen sayar da motoci ne mai girma da fadi. Harabar wurin ya na cike tab da motoci iya ganin ka, kala kala.

Akwai manya da kanana, sabbi fil da kuma tsoffi. Akwai masallaci a gefe guda kusa da wani babban tankin ruwa na robar da a ke yayi, sannan wani ginin da a ka tsammani ofisoshin ma’aikata ne.

Muhibbat ce ta fara sauka, sannan Asiya. Amma sun yi direba magana kan cewa ya jira su, don za su iya bukatar aikin sa. Ya amince, ya gyara zaman keken sa. 2

Sun tarar da wasu mazaje biyu ma su shigar alfarma, suna jingine jikin wata kasaitacciyar mota fara sol, suna hirar su. Kai tsaye Muhibbat ta yi mu su sallama, Ita kuwa Asiya uwar jin tsoro, ta na makale a gefen ta. Tun da ta zo wancan karon ta fuskanci dokta, ta koma matsoraciya. Wannan karfin halin na ta duk ya zube.

Bayan sun amsa cikin fara’arsu da komai, sai Muhibbat ta ce, “Don Allah, mu na neman wanda ya san gidan Alhaji Mudassir Dan-Ali ne.”

Suka kalli junan su, sannan su Asiya, “Alhaji Mudassir kuma? A ina yake aiki to?”

Su Asiya kan su ya kulle, “Alhaji Mudassir, mai wannan kamfanin. Mun zo ne daga Dagauda, mu ‘yan uwan matar sa Mariya ne.”

Daya daga cikin su ya ce, “Ku zo mu je na hada ku da shugaban mu. Babu mamaki zai fi ganewa.” 2

Su na biye da jagoran su har zuwa cikin wani ofis matsakaici amma kawatacce. Wani mutum ya na zaune kan kujerar alfarmar mai juyawa ta ma’aikata, ya na rubuce-rubuce.

Ko da ya dago ya kalle su, jagoran na su ya ma sa sallama, sannan y ace da su Asiya, “Wannan ne babban manajan mu a nan. Sai ku yi ma sa tambaya game da wanda kuke son gani.”

Manajan ba wani babba ba ne, matashi ne wanda ke sanye cikin kananan kaya na koriyar shat da wando launin ruwan kasa. Fuskar sa dauke da fara’a, wand aba mamaki yanayin hulda da jama’a ce a fannin kasuwancin sa ta koya ma sa.

“Barka dai.” Muhibbat ta gaishe shi. Asiya kam sai tsoro ta ke ji. Gani ta ke yi zai iya far mu su a lokacin. Ta mayar da hankalin ta kan yanayin tagogi da kuma kofar shiga ofis din. Idan har ya kama su ranta a na kare ne, to su san na yi.

“Wajen Alhaji Mudassir mu ka zo, shugaban kamfanin nan.”

Da farko dai fuskar sa ta nuna alamar zautattu ne a gaban sa, daga baya kuma ya kalli wanda ya kai su din ya ce, “Bala, ka je ma na ka kira shi. Kar ka bar su suna jira.”

Muhibbat ta shiga hamdala, amma Asiya ta tsinci sautin gatse cikin muryar sa. Ko kuwa dai zagin kunne ne. ko ma dai kawai don ta gaji ne? Amma duk da hakan, sai da ta yi wa kanta tambayoyi.

Me ya sa ba a ce su je ofis din sa ba a matsayin san a shugaba, sai a ka zabi a kira shi? Ko dai ofis din na sa ne wannan manajan ke aiki a ciki kafin ya dawo? Me ya sa Mariya ta ce sun yi tafiya tare da shi, alhali kuma yanzu an ce a je a kira shi? Ko kuma dai ba shi din ba ne, an samu akasi ne. bari dai ya je su fahimci komai. 1

Bala ya dawo, “Ga shi nan Yallabai.”

Dukan su biyu suka kalli kofar a daidai lokacin da manaja ke cewa, “Alhaji Mudassir, shugaban kamfani, ka yi baki.”

Idanuwan su suka karo da Mudassir, amma kwanyar su ta kadu ainun. Ga shi dai fuskar ta sa ce, amma kayan da ke jikin sa irin na….me ya ke yi cikin kayan sarki wato inifom na ma su gadi kuma? 23

Sun gane kayan ne don lokacin shigowar su harabar sun ga mai irin ta. Kuma kofa ya ke budewa ta shiga ya kuma rufe ta.

Yayi murmushin taraddadi a lokacin da dukan su biyu babu wacce ta iya furta komai. “Sannun ku da zuwa….ashe yau ku ke tafe?”

Wata murya ta kutsa kwanyar Asiya, ta na jijjiga ta kan cewa taa farka daga mummunar mafarkin da ta ke cikin ta. Ta kara lumshe idanunta da karfi sannan ta bude, wai ko da a ce zagin ido ne. amma ya na nan tsaye, murmushin nan da ya saba yin sa cike da fuskar sa.

Muhibbat ce ta furta, “Yaro da kudi ke nan wannan? Lahaula wala quwwaati illa billah! Ko dai kammani ne? amma wannan kamar ta baci.”

Ai kuwa mutanen da ke gewaye da su suka tintsire da dariya. Shi kuwa ya sunkuyar da kan sa cikin tsananin jin kunya. Wai shin an sauke shi ne daga mukamin shugaba, ko kuwa dama tun can maigadi ne?

Bala ya ce, “Lallai Mudassir ka shahara wajen karya. Watakila kudin kamfani ne da ka kwashe ka yi ta hidima abin ka. Mu kuwa k ace an shigo ne an sace.”

Kan Asiya ya kara bugawa. Shin me take kara shirin ji? Mudassir da ma ashe makaryaci ne, wanda ya yi ta cika su da burga kan arzikin karya? Muhibbat ce ke ta doka salati, Asiya kuwa ji ta yi kamar ta aka tsalle ta cafko wuyan sa ta shake, in ya so yam utu kowa ma ya huta. 3

“Ina Mariya?” Ta tambaye shi. Ita wacce ta damu da ita ke nan, ba abin kunyar sa ba.

“Yallabai, wace ce kuma Mariya?” Manaja ya tambaya cikin gatse da dariya.

“Mariya mata ta ce, wadannan din kuma ‘yan uwan ta ne. don Allah Yallabai, ina neman a ba ni damar da zan kai su gida, in ya so sai na dawo bakin aiki.”

Manaja ya kalle su kamar wanda ke tausaya wa rayuwar su, ya ce, “Zan baka awa daya, ka je ka dawo ko kuwa za ka yi bayani.”

“Godiya na ke.” Ya kalli su Asiya, “Mu je ko?”

Suna yunkurin fita Asiya ta na jin kamar ba ta da kafa. Ba ta san yadda ta ke iya mika kafafuwa daya gaba ba. Kawai tafiyar take yi.

Ta jiyo muryar manaja ya na cewa, “Mtsw. Allah Ya sawwake. Duk wanda ya ce ba zai zauna a matsayin da Allah Ya masa ba, to ya na tare da wahala. Ina amfanin karyar da ka je ka tafka, ga shi an tsile ka kana tsilli-tsilli da idanu kamar ka ci kudin aika.” 4

A cikin keken da su ka je duk suka dugunzuma zuwa wurin da suke zaton gidan sa ne. suna tafe kamar wadan da ruwa ya cinye su, kaduwa ta baibaye kwanyar su. Lallai ne Mudassir, lallai wannan ai cin amana ce da yaudara. Wannan ai zalunci ne da rashin mutunci.

Wadannan kalaman Asiya ta ke son furta ma sa, amma ta gagara tsinto muryar ta. Damuwarta dai ‘yar uwarta ce. Ko wane irin hali take ciki?

Wani lungu suka shiga mai cike da tsoffin gidaje na laka irin na gargajiya. Hakan bai ba su mamaki ba. Ba su ma yi tsammanin akwai abin da zai kara ba su mamaki ko kada su ba har sai da suka shiga daya daga cikin sassan gidan. Tsayawa cak suka yi dalilin da abin da idanun su ya gane mu su. Asiya ta ji numfashin ta ya dauke, iska kawai ta ke iya shaka, ba ta san wacce iri ba ce.

“Maree!?” Muhibbat ce kawai ta iya furucin. Ita ma ta dafe kirjin ta ne, idanuwan ta tamkar su bulluko daga mazaunin su, su fadi a kasa.Mariya ta kalle su cikin mamaki, sannan kunya ta biyo baya. Maimakon ta yi musu maraba da murnar ganin su, sai ta yake hakoranta.

Ta na daure da zani kodadden gaske, kan ta da hula amma gashin kan ta a tsettsefe, ya na nunawa ta kasan hular. Ta riko buta a hannun ta na hagu, ga alama daga bandaki ta fito. Ga ciki rusheshe, ya fito fili.
3

“Muhi, Laminde, sannun ku da zuwa.” Ta na magana muryar ta na kadawa. “Ku zo mu je daki.”

Gidan irin na gadon nan ne, mai sassa daban daban. Suna wucewa kowa sai kallon su yak e yi. Mata ne da yara cike tab, fututu da su. Wasu yaran suna warwaso kan faten tsaki, uwayen su kuwa suna ihun ce musu idan ba su ci a hankali ba to ba za su samu kari ba. Ba wai ba su taba ganin irin gidan ba ne. 1

Irin sa ma a Dagauda akwai. Amma ganin Maree a ciki ya jijjiga su. Ita da ko gidan mahafin su ma mitar zama cikin sa ta rika yi kafin auren ta.

Mudassir ya gabatar da su ga matan gidan, su kuma suka rika yi mu su maraba lale. A hakan ne har suka isa sashen da suka hangi Mareen da shigar su. Asiya ta tsaya ta kalli sashen. Duk da cewar a birni ne, jinkar ciyawa ce a saman dakin Mareen…idan an kira shi daki ke nan. 2

Cikin sanyin jiki Maree ta canja zuwa wata doguwar riga mai kamar buhu, sannan ta dan yi mu su murmushi, alamar ba ta so su gan ta cikin yanayin da suka yi ba. 2

Dakin babu girma, in an bar Asiya, za ta ce akurkin kaji ne. Akwai tabarma guda da ke shimfide kan tsohon kafet din da ke baje, a gefe guda wata ‘yar katifar da ba ta wuce waya goma ba ke shimfide. Dakin a hargitse ya ke kamar ba mutane ke kwana a cikin sa ba. Hakika ya yi na sabani da wanda suka bar ta cikin sa a Azare.

Asiya ta gagara magana, kuka kawai ta ke son yi amma ya ki zuwa ma ta. Wannan wacce irin masifa ce haka? Ina aljannar duniyar da ta samu? Wallahi, da wannan ukuba gwara ma da auren Buba saurayinta na farko ta yi, da ya fi mata. 1

Buba ya so Maree tun sun a saurayi da budurwa, amma karatun da ta saka a gaba ya hana ya aure ta da farko. Kaddara ta saka ya auri Rumana.

Amma duk da hakan bayan ta kamala sakandare ya koma. Sai dai ita Maree ta hani kanta da auren talaka. Sai ga shi an ki kare wajen tsuguno an dauko biri. 4

Zafin yanayi ya rufe su. Watakila don tafiyar da suka sha ne kuma dakin babu fanka. Ko kuma tsananin kaduwar da suka yi. A ganin Asiya dukkan su ne. don kuwa ta san ba za ta taba mancewaa da wannan rana ba, har mutuwar ta.

         *        *       *


Asiya ta yi zugum kamar yadda Muhibbat ta yi, suna sauraron Maree kawai, wacce ke bayanin halin da ta shiga ciki. Bayani ne ta rika yi babu boye boye. Ga alama ta dade tana neman wurin da zata amayar da cikin nata ko zata ji sanyi.

Ciki. Hankalin Asiya ya tsaya kan cikin Maree, da yadda ya fito sosai. A gaskiya, fiye da rabin bayanin na ta,ba saurare ta ke yi ba. Tausaya wa ‘yar uwar tata kawai ta ke yi.

Ta na jin Muhibbat ta tambaye ta, “Haba Maree, me zai sa ki zauna cikin yanayin yaudarar na da wulakanci hade da zalunci? Ki duba ki ga irin karyar da ya rika cika ki da su a can garinmu? Wannan zai iya kashe ki ya boye wukar.” 2

Maree ta yi wata dariyar da babu armashi, ta ce, “Na bar komai a hannun Allah.”

Asiya ta sake kallon tumbin Maree. Ita ma ta kasance mai yaudarar mijin nata ne tare da munafurtar sa. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ta yi shiru. Shi da kuma gudun kar a mata dariya, ta sha kunya idan asirin ta ya tonu. Don kuwa a Dagauda, zata zama abar kwatance.

STORY CONTINUES BELOW


Cikin takaici Muhibbat ta ce, “Kaico! Allah Ya sawwake.” Sannan ta kara gyara zaman ta kan tabarmar da Mudassir din ta shimfida mu su, taambaye ta, “To gidan ku na Azare fa?”

Maree tayi dariyar takaici, “Ba ki ji abin da na fada muku tuntuni? Hmmm, wannan gida na yayan abokin sa ne, wanda ya gina ya bar wa kanin say a rika lura ma sa da shi. Shi kuma a Amurka ya ke da zama. Shi ne Mudassir din yayi hanya hanya, ya karbi aron gidan na tsawon wata biyu. Rana daya mai gida yayi waya kan cewa zai dawo da iyalan sa da zama gaba daya.”

Ta ci gaba da cewa, “Farko ya ce da ni mu dawo nan ne don iyayen sa suna son mu zauna kusa da su. Da ya kawo ni nan, ya ce zan zauna ne kafin ya gama gyaran gidan namu. Ya nuna bukatar ganin na yi cudanya da ‘yan uwan sa don mu saba. Yau watanni uku ke nan har da kari. Tun ina kuka har na saba, na hakura. 2

“Da farko dai na ki cudanyar da su domin ina ganin sub a ajina ba ne. su kuma ashe kallon sakarya su ke min, don da magana ta fito, sai gulmata a ke yi. Ga haushina da suke ji, kan cewar lokacin da Mudassir ya samu kudi, maimakon ya musu abin arziki da su, sai ya kashe min duka.

“Kudin daga baya aka san tushen su. A wajen aikin sa ne a ka ajiye miliyan biyar, kasancewar an yi cinikin yamma ne a lokacin bankuna sun rufe. Sai maigidansu ya boye kudin, a lokacin shi kadan sa ne. Bai san Mudan ya gan shi ba. cikin dare ya lallaba ya sace kudin, shine ya shiga bushasha da su.

“Bayan an gano shi ya dauka, an samu babu ko sisi. An daure shi a gidan kaso na tsawon sati biyu. Sai da Baban say a sayar da filayen da yak e da su ya hada da shanun sa uku tukunna ya bayar da abin da ya samu. Sauran mai kamfanin ya rike shi ya rika ma sa aiki babu albashi har sai ya biya kudin gaba daya.” 2

Bayan ta dan tsaya ta yi kwalla, ta ci gaba da cewa, “Ni na jawo wa kaina. Ni na cuci kaina ba kowa ba. naje wajen neman gira na rasa ido. Tukunyar tuwon gidan nan kadai zai karya bayan mutum, bayan ya haukata shi. Kirjina ciwo ya ke min.” 6

Ta na magana kamar za ta na share kwalla. Haushin ta Asiya ta shiga ji. Shikenan sai ta zauna Mudassir ya yi ta raina mata hankali? Ina Mareen ta ke ne, wadda ba ta daukan irin wannan?

Mudassir ya doka sallamar shiga cikin dakin. Wani abu ya tokare musu wuya. Musamman Asiya, ko ganin sa ba ta kauna. Kimar sa ta zube a idanun ta.

Ta wani bangaren kuma so take yi ta gan shi, ta ga yadda idanun sa zasu kasance bayan irin abubuwan kunyar da ya tafka. Abu sai ka ce a cikin fim?

Ya shiga dakin, hannun sa dauke da kooler na abinci, “Mariya ga wannan a ba wa bakin mu.” Ya dan kalle su, “Tuwon gidan namu ne tuwon gandu. Na san ba za ku iya ci ba ne ya san a sayo muku shinkafa.”

Muhibbat ta ce, “Ai ba komai, mu kowanne muna ci, ba mu saba karyar arziki ba.” 2

Muhibbat ke iya magana da shi. Ita Asiya ji take kamar ta rufe shi da duka kar ta tsaya, kamar Allah ne Ya aiko ta!

Mudassir ya yi ‘yar dariya, ya ci gaba da Magana kamar bai ji gatsen Muhibbat ba, “Akwai taliyar da zan aiko, don na san shi ne abin marmari.” Ya ajiye bakin leda, “Wannan piya-wata(pure water) ne mai sanyi, maganin zafin yanayi.” 7

Suka bi shi da kallo, ko a jikin sa. Ko bai gatsen ba ko kuma bai fahimta ba. Ko ma bai dame shi ba gaba daya. Maree ta bukaci su sha ruwan sanyin sannan su ci abinci kafin su yi sallah. Taliyar mai manja da yaji ya aiko mu su, dafa-dukar shinkafar ma babu fasali. Daga ruwa sai manja da kafi-zabo radau! 5

Maree ta shiga gabtara har ta na santi. Kwalla suka ciko da idanun Asiya. Oh, wai duniya juyi juyi, kwado ya fada cikin ruwan zafi. A lokacin da Maree ke gida kafin auren su, duk lokacin da Mudassir ya je zance sai tukunyar su ta shaida.

STORY CONTINUES BELOW


Musamman ya kan sayi rago ko tunkiya a yanka, a yi ta ci a na morewa tsawon kwanakin da zai yi. Ban da kaji da kifi. 4

Yau ga abincin gidan sa. Tuwon ma da facalolin Maree suka ba su kamar dutsen garin su. Hakika duk wanda a ka jefe shi da shi sai an dinke ma sa wajen, don babu abin da zai hana shi jin ciwo. Miyar ma gwara a yi shiru, don sun kasa gane kuka ce, kubaiwa ko me? 12

Tsawon dare da kyar ta runtsa, ta na tunanin yadda wannan abu ke faruwa kamar a mafarki. A tunanin ta, idan ta bude idanun ta za ta farka taga ba gaskiya bane. Ta shiga alla-alla gari yaw aye ta bar gidan. Ba zata iya ci gaba da ganin wannan takaicin ba.

Washegari da sassafe Asiya ta gama kimtsawa don su koma. Amma Muhibbat ta shawarce ta kan ta hakura sai washegari, gudun kar mutanen gidan su zaci akwai matsala. Asiya ta san da hakan, amma ba ta jin kara zama a wannan gidan muddin tana son kanta ya zauna daidai.

Tuwon da ba su ci bane na dare Maree ta shiga kicin ta duma mu su tare da taimakon wata a cikin matan gidan mai suna ladiyo. Suna mutunci sosai da Maree, ta na kuma tausaya mata halin da take ciki.

Sauran matan gidan suka dan sako musu dan abin da suke jauron su, kama daga danwake, awara, kosai da koko. Asiya ganin irin gidan ta gagara cin komai. Rijiya daya ce a gidan. A nan suke wanke-wanke, wanki har ma da wankan yaran su. Ga poo din yara kaca-kaca kusa da wurin. A na kuma hidima hankali kwance. 2

Sun zaga gai da matan gidan daidai, sun kuma yi musu maraba. Duk wurin da suka shiga sai an musu tayin koko da dumame. Idan Asiya ta ga fuskokin yaran su babu alamar an wanke tun bayan tashi daga barci, ga wasu majina cike a hancin su. Amai ta rika ji amma ta daure. 4

Kan hanyar su doyi ya cike hancin su. Wata fankaceciyar tukunyar da suka gani da ke gefen wajen wanke wanke ya kara bas u tsoro. Tausayin Maree ya kara kama su. A ce tuwo sai ta tuke shi cikin wannan tukunyar da mata uku ne za su iya tuke shi? To gaskiya dole ta sha wahalar ciwon baya. Ga ta da ciki…ba sa tausayin ta ne?
2

“Ke Maree, ina akwatinan auren ki ne?” Muhibbat ta tambaye ta. A lokacin sun karya sannan Asiya ta share mata dakin tsaf. Ita ma kan ta tambayar ta gifta a ran ta, ba ta so yi bane kar ta ji abin da ya fi karfin ta.

Maree ta fi dakika talatin bakin ta bai bude ba. idanun ta kuwa sai tsananin kunci suka nuna. Can ta amsa, “Bayan da kuka kai min kayana a can Azare, sai ya hanani dinka kayan a can. A cewar sa, telolin can ba su iya fitar da dinkunan da yake so ba. satin mu uku a can ya taho da akwatinan nan garin da sunan ba wa tela. Karshen ganina da su ke nan. Daga baya ne nake jin cewa ya sayar da su ne don biyan kudaden da ke kan sa. Ba na da kayan saka wa sai idan an bani kwancen sa.”

Maree idanun ta tab da kwalla amma tayi karfin hali ba ta zubar ba. Muhibbat sai salati da sallalami, ta na cewa, “Gaskiya wannan cin fuska yayi yawa Maree. Dole ki dauki mataki a kai.”

“Wallahi ba don lalurar da na ke tare da ita ba, da na tayar ma sa da hankali ya sake ni. In ya so a kira ni bazawara b azan damu ba.”

Hankalin Asiya ya sake komawa kan cikin. Tsawon zaman da Maree ta yi da shi babu tanadin haihuwar da suka yin a jariri. A yadda cikin ya girman nan idan haihuwa ta zo ma ta fa? Ta na tsoron ranar da asirin da suke rufewa zai tonu.

Ta kakkabe wannan cikin zuciyar ta. Ba ta ma son ta sani. Allah dai Ya kara rufa mu su asiri.

Bayan sallar la’asar, Muhibbat ta kammala shirin zuwa karbar sautun ta a kasuwar central, wanda a ka yi ma ta daga Abuja. “Zan sayi yadudduka ma idan na same su da sauki. Na dai fi son sayen kaya a can Kano gaskiya.”

Asiya ta kalle ta, “Ashe da kudin ki a marar ki, kika hana bawan Allah Sani kwatambe ko?”

“Kun ji Laminde da neman Mmgana, wai an ce da gwauro yaya iyali. Sanin ne wani bawan Allah? Bar wahalalle, mu je zuwa, mahukaci yah au kura. Ko tausayi ba ya bani ki ji in gaya miki.”

STORY CONTINUES BELOW


Suka dan yi dariya, Maree ta ce, “Mutuniyar ki na wuta fa, a na bin ki da fetur.”

Muhibbat ta gyara rigar ta na shadda mai ruwan zuma, ya sha aikin wuya, ta ce, “Kin san fa mazan ne sai a hankali. Dole ka tantance don gudun yin zaben tumun dare.” 4

Wajen yayi tsit a yayin da maganar ke shawagi a iska. Asiya ta lura Muhibbat ta yi nadamar furucinta a gaban Maree.ba a son ranta bane, amma ta riga ta furta. Kamar a zuba gishiri ne kan gyambo. +

Asiya ce karshe ta mike, ta ce, “Ya kamata mu je ko? Ko ba komai za a jefa min cile.”

Lokacin ne suka sake. Muhibbat ta ce, “Kya ma taya ni zaben kaloli ma su kyau.”

“Ba ruwana da zaben kaloli. Zan je na ji kudin su, don idan na zo saye a wajen ki kar ki tsuga min tsada.”

Muhibbat ta harare ta, “Kin ji min yarinyar nan ko Maree? Wasa-gaske fa kina surutun tsiya.”

“Ke dai fito mu je, don sai kin saya min alawa tsinke, leda guda ladan rakiya.”

“Ni ma ladan tafiya nake nema, don ba zan ki alawar ba.”

                         *          *          *

Dokta Yusuf Haruna ya fita daga dakin tiyatar da ke asibitin Sauki, wurin da ya cire wa wani marar lafiya makoko. Ya matukar gajiya, don tun safe ya ke ta fama da aiki tukuru. 2

Ya nufi ofishin sa, ya ki kallon jerin mutanen da ke jiran ganin sa a layi. Hutu ya ke bukata. Ya yanke shawarar komawa gidan sa don ya ci abinci ya kuma huta. In ya so ya koma. Amma kafin nan ya yi wa Hadi da wani abon likita mai suna Dokta Rufa’i magana, kan ya kula ma sa da marasa lafiyar da ke kan layin ganin na sa.

Bayan ya shiga kewaye ya wanke hannayen sa tsaf, sai ya canja zuwa kwat din sa. Amma bai saka na wajen ba, ya sakala shi ne a hannun na sa, sannan ya gyara zaman nektayel din sa. 3

Wajen sakatariyar sa ya tsaya, ya sanar mata canjin da a ka samu, shi kuma ya nufi gidan sa.

Ya iske Umma a falo, ya gaishe ta. Ta amsa cikin fara’a, sannan ta tabaye shi aiki. “Aiki Alhamdulillahi. Yaya na ki jikin?”

Umma ta yi murmushi, “Dan auta, yau ka tambayeni jikin nan sau goma ke nan. Da yawan tambayoyin ka ne waraka ai da na rabu da sake ciwo ke nan a duniya.”

Ya fadada murmushin sa, ya ce, “Umma dole ne na damu, don idan ba kya da lafiya ba kya son nunawa. Ai kuwa dole hankalina ya gagara kwanciya.”

Akwai kulawa sosai cikin muryar sa. Ta ce, “Kar ka damu, na samu sauki. Jirin ne kawai ke damuna, amma ba can ba.”

“Kin sha magani kuwa?”

“Na sha. Amma ba mai kashe jikin nan da sa barci ba. ban a son wannan, ka canja min shi.”

Ya nuna rashin jin dadin sa, “Zan canja miki, amma ki daure ki sha wannan din zuwa an jima. Magani a na shan sa ne ba don dadi ba Umma. Na baki wannan din bisa dalili ne.”  ita ma ta bata na ta fuskar, “Daga yau ni ma ba zan sake bin maganar ka ba, tun da ka ki bin nawa.”

Yusuf ya nisa. Labarin gizo ba ya wuce na koki. Ya sauke muryar sa cikin ladabi, “Umma kin san ban a kin maganar ki. Ina rokon ki da ki kara hakuri ki kuma kara min lokaci.”

Umma ta nisa, ta ce, “Dan auta, ba so nake na rika takura maka ba. a ganina don na nemi ka yi aure ai ba aibu bane. Ka na da dukiya da kuma lafiya, me zai s aka ci gaba da zama gwauro?”

Ta kalli gewayen ta, ta ci gaba da cewa, “Ka kalli wannan makeken gidan nan, kukan kadaici yak e yi. Dakunan cikin gidan nan sn kagu da son jin takun ‘yan kananan kafofi. Ni kaina na kagu da na fara wasa da jikokina idan Allah Ya bani su. Me yasa kake neman tauye min wannan farin cikin da zaan samu?”

STORY CONTINUES BELOW


Yusuf ya fashe da dariya. Umma ta harare shi, “Au dariya ma na baka ko?” Na zama rediyo ke nan?” 

Ya tsagaita dariyar, “A’a, ba haka be ne. Ji na yi kin karo wasu sabbin abu ne cikin sharhohin kin a kullum.” Duk da cewa ya bar yin dariyar, idanun sa bas u bar kyalli ba.an auta, ka mayar da ni kakar ka ko? To zancen yin aure ba zan fasa yi maka ba, ehee!” 2

A hankali ya durkusa a gabanta, ya ce, “Umma ta ki kara bani lokaci. A kullum na tuno da maganar auren nan sai na shiga zullumin kar na kawo wadda za ta shigo ta raina min ke, ta rika ci mi ki mutunci.

Sannan ta nemi rusa kyakkyawar tubulin da ki ka dasa cikin gidan nan ba. Ba zan iya daukan hakan ba gaskiya. Amma da zarar na samu, finkico ta zan yi sai gaban ki. Aure kai tsaye.”

Ta yi murmushi, ya ji dadi matuka, “Hmm ka na magana sai k ace bad an Adam ba? Waye ya cika goma? Kowa fa tara ne. ni dai ka yi ka kawo min surka ta kafin na mutu.”

Dokta ya girgiza kan sa. Umma ta kan yi ma sa irin wannan kalar tausayin ne idan ta na neman tilasta ma say a yi wani abu cikin dabara. Emotional blackmail ke nan.

Ya nisa, “To Umma. Gobe da yamma idan Allah Ya kai mu zan je nag a diyar kawar nan ta ki, wadda ki ke son na gani tuntunin.”

Ta nuna zumudin ta a fili, “Gobe kuma? Me kake yi yanzu? Sai ka shirya kawai mu je ka gan ta. Shi aikin alheri ba a jinkirta shi.”

“Umma, ki yi hakuri na ci abnci sannan na yi sallah. In ya so sai mu je duk wurin da kike son mu je din.”

Umma ta yi murmushi, “Allah Yam aka albarka. Bari ma na kira Hajiya Asaben na sanar mata. Amma kafin nan, ina son ka kai ni asibiti koyarwa, don akwai ‘yar wajen Hajiya Gambo da ta ke kwance a dakin ‘yan hatsari. Ka tuna cewa mashin ne ya buge ta a titin unguwar su? Ina ga an kusa sallamar su. Balle ma kuma ni kadai ce a gida kamar wata mayya. Kar ciwo nay a sake tashi ba kowa kusa. Ka san hawan jinni yadda ya ke.”

Ya kara fadada murmushin sa. kwarai, Ummar sa ta kware wajen siyasa. Dolen sa ya fita da ita, sannan dolen ne ya je ganin wannan yarinyar da ta ke son ya je ya gani. Yaya ma sunan ta? Ba rike ba. Sannan Umma ta bas hi lambar wayar ta har sau biyu amma ba zai iya cewar ga wurin da ya jefar ba.

“To Umma. Ki shirya mu je na sauke ki a can, in ya so ni sai na wuce wajen wannan yarinyar.”

“Sahla sunan ta. Ya kamata ka rike sunan ta tun za ku daidaita da juna.”

Ya mike tsaye, “Sahla, ba zan manta ba daga yanzu in shaa Allah.”

Ya san ba wani jimawa za ta yi a asibitin za ta yi ba. Da zarar sun je za ta ce bari ta karasa wajen kawar tata, don ta tabbata ya je ya samu..Sahla. Bai manta ba. Ko ya manta ma Umma za ta ci gaba da tuna ma sa.

Ya yi wanka sannan yayi sallar la’asar. Jamfa ya zaba ya saka, wani launin ruwan toka. Tun da zai je wajen budurwa dole a gan shi cikin kaya manya don a dauke shi da muhimmanci. Sannan ya san Umm aba yarda za ta yi ya je da kananan kayan ba ma.

Ya kalli kan sa a madubi da kyau. Wannan satin bai aske sajen da ya bari a fuskar sa ba. Hakan ya kara ma sa duhuwa. Bai san lokacin da zai bar jin bugun zuciya ba a duk lokacin da a ka ma sa maganar aure ba.

Soyayyar Abida ta bar ma sat abo ma girma a zuciyar sa. ta shata wani tambarin da bayan ita babu wacce ta iya kutsawa ciki.

Abida. Ya ji zuciyar sa ta shiga kuna. Me ya sa ta tafi ta bar shi? Ya san dai babu wanda ya isa ya wuce ranar sa. Amma alkawari ta yi ma sa, na cewa za ta kasance tare da shi har abada. Sai gas hi ranar da aka daura mu su aure ta mutu, ta bar shi da kewa. 12

Ba zai taba mancewa da wannan ran aba. Shi yasa baya tunanin Kalmar aure ko kadan. Baya kaunar ganin kowacce mace a duniya. Ya yi sallama da soyayya. Zai yi wani auren ne kawai don Umma ta matsa, don kuma ya faranta mata rai.

Bai yi aune bay a ji kwalla ta zubo ma sa. Ya yi sauri ya goge. Shi namiji ne, bai kamata ya bari tunani ya na masa nisa haka ba. Dolen say a daure, ya bude zuciyar sa, ko zai ga farin cikin mahaifiyar sa.

Yamma lis suka bar gidan sai asibitin. Kamar yadda suka tsara ne, Umma zai ajiye sannan ya wuce. Sai da ya tsaya ya sayi su maltina da kayan marmari a hanya don a kai.

Ko da shigar su, suka hadu da su cikin motar su an sallame su za su koma. Da ma Hajiyar ta na shirin za ta kira Umman ta fada mata ke nan sais u ka hadu.

Bayan sun gaisa sama-sama, sai suka yi a kan su Umman za su bi bayan su har gidan. In ya so Umma ta sauka shi kuma ya wuce zuwa wajen hirar ta sa. ba bu musu, motar su Hajiya Gambo ya na gaba, su kuma suna biye da su.

Yusuf ya karya kwanar da za ta fitar da shi daga asibiti, ya ji Umma na cewa, “Wannan ban san ta ba kuwa? Tsaya ….tsaya dan auta.”

Ya tsaya a gefen hanyar, kan sa a kulle. “Yi baya kadan.” Ta umurce shi.

Shin wa ta gani kuma? Bai wuce wata kawar tata b ace ita ma. Ya dai yi ribas a hankali. Umma ta ce, “Yauwa, tsaya nan.”

Sai a lokacin ya ga wadda Umman ta say a tsaya domin ta. A birkice ta ke, kallo daya mutum zai mata ya san ta na cikin matsala.Asiya, ina kika fito haka?” umma ta tambaye ta. +

Sai a lokacin ta fukance su sannan ta gaida Umma, sannan ta dan tsaya nazari, kafin ta gaishe shi shima. Ya amsa ta nuna alamar gyada kan sa, sannan ya mayar gaban sa , yana jiran lokacin da Umman za ta ce ya ja motar su tafi.

Tun bayan rabuwar su a can Dagauda a ranar da ta fi9ncike su, bai kara ido byu da it aba. Haka nan bay a son ganin ta, don a tunanin sa, duk wurin da ta je to za a samu matsala.

Har yau mamaki yak e ji, kan cewa yarinya karama kamar ta har za ta iya fuskantar sa. A je, ya san kuskure ne da akasin da aka samu ne ya sa hakan, amma da a ce da gaske ne shi ya aikata laifin hakan za ta tsile shi?

Ya girgiza kai a kokarin san a kakkabe wannan tunani daga ran sa. Amma fa dole ya sara mata, yarinyar akwai karfin hali, sannan akwai wauta. 2

“Babu. Ina neman Dada ne a waya amma kudin sai yak are. Shine zan je bakin get na saya.” Ta ba da amsa.

“Amma lafiya dai in ce ko?”

“Ah, lafiya kalau Umma.” Sannan ta saki murmushi.

Bai san dalili ba, amma ya tsinci wani abin da muryarta, wanda ya kasance sabanin amsar ta. Akwai abin da ta ke boyewa amma ba zai so Umma ta tambaye ta. Alla-alla ya ke yi su bar wajen.

“Yaya Mariya? Na ji an yi bikin ta ko?”

Yusuf ya lura da yadda ta yi saurin amsawa tare da gyada kai irin na kadangare, “Eh an yi. Ita ma ta na nan lafiya.”

Kwarai. Akwai abin da ta ke boyewa. Wata budurwa ta bayyana tare da kiran Asiyar, “Laminde, kin samu yin wayar kuwa?”

Asiya ta girgiza kan ta “A’a, mu je can dn kawai in ya so sai mu yi tare.” Ta shiga kokarin jan ta su tafi.

Budurwar ta ki motsawa, ta mika wa Asyar hannu, “A’a, kawo wayar nan ki je Maree ta farfado tana son neman ki.”

Umma ta tambaye su cikin kulawa, “Da ma Mary ace ba lafya?”

“Eh.” Waccan ta amsa. Asiya ba ta ce uffan ba. Kasancewar gaban sa yake kallo bai san yaya yanayin fuskar tata take ba. Ya san da ma akwai abin da ta ke boyewa. Amma bai yi tsammanin kunnuwan sa za su jiye ma sa babban abu ba.

“Me ya same ta?”

“Yau kwanan ta uku ke nan da haihuwa.”

A lokacin ne ya dan kalle su, hankalin sa a wajen su. Umma ta dafe kirjin ta, “Ta haihu?”

“Eh. Ta samu ‘ya mace, amma yarinyar ba ta da lafiya. Likita ya ce ta na da shawara (jaundice). An saka ta cikin kwalba. Mareen ma an kara mata jinni don ta zubar da shi sosai wajen haihuwa.

“Subhanallahi.” Umma ta furta, sannan ta kalle shi. 2

Ya nisa, ya ce, “Su shiga mu je su kai mu wajen ta.”

Ya dade da iya karantar zuciyar Umma ko da motsin jiki kawai ta yi. Ya san tana tunanin kar ta takura ma sa ne ko bata ma sa lokaci. Shi ma kan say a na son ganin wannan jaririya. Duk da dai sun yanke dukkan alaka, ba bu laifi idan sun gan ta sannan su wuce.

                                 *         *            *

Asiya ta na tafiya ne, nauyin da ke zuciyar ta na sauka kafafuwanta. Don haka ne ta fara takun ta a hankali. Tana iya ganin Muhibbat tare da Umma suna tafiya a gaban ta. Ba za ta iya ba.

STORY CONTINUES BELOW


Ba zata iya shiga ciki ta fuskanci Maree ba. A kalla ba a lokacin ba. Ta na bukatar karfin jikin ta, da ma na zuciya kan hakan, ko da za ta kara mata karfin gwiwa.

Jiri ya dibe ta zai watsar. Kawai ji kan ta tayi luuuuu za ta fadi. Allah Ya tamake ta wata Nas na biye a bayan ta. Da ta tallafe ta, suka yi kasa tare ta na tambayar ta ko lafiya. A lokaci guda kuma ta kwala kira wa abokan aikin ta, kan su kawo agaji.

Mutum daya Asiya ta gani, ya tsuguna a gefen ta, muryar sa a natse, kasa kasa sannan cike da damuwa ya tambaye ta, “Are you alright?”

Ba ta amsa ba. Iska kawai take shaka, mai cike da kamshin turaren sa. Ba ta iya ganin komai sai fuskar sa. ta gyada ma sa kai, ta yi yunkurin mikewa tare da taimakon Nas. Ta na jin idanun sa a kanta, ta ki kallon wajen da ya ke. Tun farko ma ta yi mamakin ganin sa a asibiti. Eh, ta san likita ne kuma wurin da take asibiti ne. Amma dai ba ta yi zaton hanyoyin su za su ratsa ba. 2

Tsayuwar ta ke da wuya ta sake jin kafafuwan ta sun yi sanyi, kamar wacce ke cikin kankara. Da kan ta ta nemi wuri a gefen baranda ta zauna. A lokacin Muhibbat ta dawo cikin sauri, ta na tambayar ta, “Lafiya Laminde?” me ya faru?”

Mutane suka fara taruwa kowannen sun a son sanin abin da ya same ta. Wasu ma kawai son ganin kwakwaf ne kawai. Dokta ya umurci wannan Nas da ta tallafa ma ta su shiga. Su ka yi sa’ar samun wani daki wanda babu kowa. 2

Duk girman damuwar ta a lokacin ya sauka mata. Takaicin da ya samu Maree, yanayin da take ciki, sannan da wannan nay au kuma. Ba ta gama fita daga wahalar da ta sha na farko ba, sai yanzu kuma ga wannan. Shin yaushe ne matsala za ta kare mu su?

“Muhi, ba zan iya ba. Abubuwa sun fi karfina. Yaya zan yi?”

Muhibbat ta shiga yi mata fada, “Haba Minde, idan ba ki yi karfin hali ba yaya kike son Maree ta yi? Daurewa fa za ki yi, don a jikin ki Maree za ta samu kwarin gwiwa.”

Asiya ta kada kanta, zuciyar ta na tafarfasa. Idan bata mayar da hankali ba hawan jinni zai kamata. Ta gagara Magana, kwalla cike tab cikin idanun ta. Ga shi suna ta kokarin neman Dada a can Dagauda amma bas u same ta ba.  Da a ce ta na nan ne ma abubuwa za su zo musu da sauki.

Sallamar da Dokta yayi ne ya sa ta saurin goge fuskar ta, amma ba ta daga kai ta kale shi ba ma balle ta amsa. Muhibbat ce ta amsa. Ya mika ma ta gorar ruwa da katin magani, “Ga wannan a ba ta ta sha. Zai taimaka wajen kawo mata natsuwa.”

Muhibbat ta karba cikin godiya sannan ta balle kwayar mai kalar fari da ruwan dorawa ta bata. Ba ta yi jayayya ba, ta karba ta sha. Lokacin ne ta kale shi. Ya na tsaye ne cikin kyaun diri da na halitta. Ya kura ma ta idanu kamar wanda ke iya ganin hanjin ta. Fuskar sa fayau. 2

A zaton ta, juyawa zai yi yayi tafiyar sa, ba ta dauka zai kula su ba ma.

“Na gode.” Ta furta gare shi, ta tabbatar da muryar ta ta dauki sakon hakan.

Umma ta shiga ta na tambayar ta abin da ke faruwa. Ta amsa mata da cewar ciwon kai ne ya matsa mata lamba tun jiya, shine ya kawo mata wannan jiri.

Muhibbat ta yi caraf, ta ce, “Ba ciwon kai ke damun ta ba, matsalolin Maree ta runguma, tana neman ta kasha kanta.” 2

“Me ya samu Mariyar? Ina ce ta haihu lafiya?”

Asiya ta kalli Muhibbat, idanun ta suna rokon ta kan kar ta fadi komai sannan ta sunkuyar da kanta. Wadan nan mutane ne da a watannin baya suka girgiza a dalilin ganin ta. Ta birkita mu su rayuwar su, ta jijjiga mu su duniyar su.

A halin yanzu ba ta kaunar su sake shiga damuwa ta dalilinta. Don haka ba zata ce da su komai ba. Barin su za ta yi su yi tafiyar su, tare da fatan kar Allah Ya sake hada fuskokin su.

STORY CONTINUES BELOW


Muhibbat ta ce, “Za ta ce mi ki babu komai, amma akwai. Kuma nib a zan bari ta kasha kan ta ba.”

Ta yi biris da rokon ta ido da Asiya ta yi mata, ta ci gaba da cewa, “Yau kwanakin mu hudu ke nan a nan garin, a matsayin bakin Maree. To tun shekaranjiya mu ka so komawa, amma ganin cewar ta fara ciwon mara ya sa muka dan jira don mu ga yadda za ta kaya.
“To tun jiya daga gida jini ya ballo ma ta, yake ta zuba har muka kawo ta nan. Allah Ya taimake mu ta haihu lafiya. Daga baya kuma jinin ya sake ballo mata. Tun da dangin mijin nata suka kyalla ido suka ga jaririyar nan, na san za a samu matsala. Mahaifiyar sa ba ta boye abin da ke zuciyar ta ba. Ta ce babu yadda za a ce auren su wata biyar ke nan, amma ta haifi ‘yar wata tara? A takaice dai, jiya da safe, a lokacin da a ke fafutukar neman jinin da za a saka mata, Mudassir ya shigo ya mika mata takardar sakin da yayi har sau uku. Ya kuma ce ba zai saka hannun sa a kan jaririyar ba, kuma mahaifiyar sa ta ce ba ta kaunar ta sake ganin ta. Don ma kar mu bi ta gidan sa wajen daukar kaya, da kan sa ya kwaso kayan ta da namu ya kawo ma na nan, don wulakanci.” 4

“Inna lillahi wa inna ilayhir raji’un!” umma ta furta tare da salati. Ta ci gaba da cewa, “Ni ban taba ganin rashin Imani da mutunci irin wannan ba. A ce mace ta na kwance rai a hannun Allah, amma ko a jikin mijin ta?”

Muhibbat ta ce, “Wallahi tun jiya ba a gane kan ta ba sai dazu ta farfado. Ga jaririyar ba lafiya, sannan ita ma uwar ta na kwance, babu namiji ko ma mace babba a cikin mu. Wayar da mu ke ta kokarin yi wa Dada ta gagara shiga. Komai fay a mana cak ne.”

Umma ta nisa, “Hakika, dole ku rasa yadda za ku yi, ku kuma shiga wani hali. Don kuwa ku yara ne, ba za ku iya ba. Amma tun da na zo, ina son ku kwantar da hankain ku gaba daya, ku bar komai a hannun mu.”

Asiya ta yi yunkurin magana, “Umma, wannan dawainiya…”

Umma ta daga mata hannu, alamar ta shanye duk wani abin da ta yi niyyar furtawa. “Na ce ki bar mana komai. Yanzu kid an kwanta ki samu isasshen hutu. Ni da dan auta zamu je wani waje mu dawo.”

A lokacin ta sake kallon Dokta, wanda tun bayar da maganin da yayi, bai sake cewa uffan ba. Suka fita, su ka bar ta da Muhibbat, wadda kamar ta san abin da Asiya ke tunani, ta ja gwauron numfashi, sannan ta yi hamdala. Ita ma godiyar ta yi, domin ta san Allah ne Ya turo mu su su Umma don su taimake su, su sama mu su sauki.

Allah Ya sani, duk da cewar ba ta so dora mu su wahala ba, ta na matukar bukatar su. A kalla, kafin su sake komawa kauyen su, wurin da suka fi wayo, ba za su kara haduwa da sub a.

Washegari da sassafe Umma ta kai mu su ziyara. Ta na sanye ne cikin leshi mai launin makuba, ta yafa gyale fari sol. Kunnen ta da ‘yan kunnen daham, amma ba ta saka sarka ba. Kamshin ta ya hade da na Dettol da izal, ya garwaye dakin baki daya.

Gadaje guda goma sha hudu ne a cikin babban dakin, suna jere a bangare dama da haunin dakin, suna fuskantar juna. Gadon da Maree ta ke mai lamba shida ne, don haka a ta farko farko a ke samun ta.

A gefen gadon na su akwai tabarmar da mijin Marren ya saya tun farkon zuwan na su asibiti, kafin ya sake ta ke nan. Sai filas dan karami, wanda Muhibbat ta sayo mu su shayi a cikin sa dazu sanyin safiya.

Filas din Muhibbat ce ta saya bayan haihuwar Mareen don bukatar da zai iya tasowa. Sai gorar Fanta, wanda Muhibbar ce ta sha. Asiya kam, in ban da maganin da likita ya bayar kan a bata, ba ta kai komai baki ba. A lokacin ma Karin jiri da ciwon kai take ji. Ta san ba za su rasa nasaba da yunwar da ke kwakular ta ba.

Umma ta kai mu su abinci a manyan kooler guda biyu, dayan soyayyen dankali ne da kwai a gefe, dayan kuma ferfesun kaji ne. a cikin wani filas kuma an zuba mu su kunun tsamiya ne lafiyayye. Ta hada da babban gidan maltina, ruwan madarar gwangwani na peak da kuma jusa-jusai irin su Fanta da sprite. Sannan ta kai ruwan zafi na daban cikin wani babban filas din daban tare da bokitin roba. 2

STORY CONTINUES BELOW


Ta bukaci su zuba wa Mareen ruwan dumi ta dan watsa a jikin ta, ko zata dan ji dama dama, ta warware. Nan take suka cika umurnin ta. Maree ta mike ta shiga bandakin bayan Muhibbat ta kai ma ta ruwan.

Bayan Mareen ta fito daga wanka, Umma ta ba ta riga da zani sabbi ta daura. Kayan na wata kanwar Dokta ce, wadda ba ta sa fiye da sau biyu ba. Bayan ta shafa mai ta saka kayan kuma, sai ga Maree ta yi fes abin ta. Daga nan Umman ta tilasta ma ta shan ruwan shayi mai kaurin gaske, bayan ta ba ta maltina da madara. Daga nan ne sai Umma ta fita ta dan ba su wuri.

Abincin ya cike wurin da kamshi. Cikin asiya ya dauki ruri, amma bakinta na nauyin karba ta ci. Sai da Muhibbat ta yi ta surutu tukunna ta kurbi kunun, ta dan kai kwan cikin baki. Damuwar ta, sun samu Dadar a waya jiya, kuma muryar ta ta yi sanyi matuka, jin abin da ya faru. Ta yi alkawarin zuwa a ranar, don haka zumudin ganin ta ba zai bari ta ci abincin ba.

Misalin karfe goma sha biyu na rana ne Dada ta iso asibitin tare da Sani kwatambe. Yanayin fuskar ta a natse ne, amma idanuwanta sun nuna shaidar birkicewar da ta yi, da kuma tashin hankali tun bayan sanar da ita halin da a ke ciki. 2

Tun da ta samu kujerar roba ta zauna a kai, ba ta furta komai ba illa amsa mu su gaisuwar da suka yi mata. Ta doka tagumi a kan habar ta, Allah kadai Ya san abin da ta ke tunani.

Nan ne kuma Asiya ta kara jintashin hankali. Wane hali mahaifan su ke ciki a yanzu? Wane hali za su fuskanta nan gaba? Hakika, za a iya dagewa a ce aure ya ba wa Mudassir wannan diyar, amma yaya za a yi da kwaye dakin mahaifin su da a ka yi? Ga shi ya gama bazawa a gari cewar za a gyara ma sa gidan sa ya koma na zamani. Yanzu ba suriki, ba bu gyaran dakin sannan ga jikar sa ta fito duniya. 2

Lallai ne, Asiya ta san fuskantar mahaifin su shi ya fi sauki, a kan fuskantar garin Dagauda gaba daya. Abin da ita Asiya ta guje wa faruwan sa ke nan. Sai dai dolen su ne, domin kaddara ta riga fata.

Da yammacin wannan rana Dokta Yusuf ya sa a ka kais u zuwa asibitin sauki, don a can za a bas u daki babba su kadai, sannan jaririyar zata fi samun kulawa daga wajen sa. gado daya ne a dakin, amma an mu su shimfidar kafet musamman, don su samu wajen zama ba tare da takura ba.

Sun samu kimanin kwanaki biyu a nan asibitin  suna samun kulawa ta musamman, har uwa da diya sun fara murmurewa. Babyn a kan fitar da ita waje ne don ta rika samun rana bayan an tube kayan jikin ta an kuma rufe idanun ta da wani kyalle, gudun kar hasken ranar ya mata illa.

Umma ta kasance tare da su a kullum. Kusan a nan ta ke yini, ta na kuma kula da jaririyar. Dokta kuwa tun bayan zuwan su nan, sau daya ya shiga ya duba Maree. A kullum sai dai Nas ta kai ma sa babyn ya duba ta, ya ga yanayin samun saukin ta. Daga nan a mayar da ita wajen uwar ta.

Maree ba ta fiye son magana bat un bayan haihuwar ta. Asiya zata iya kidaya lokutan da ta dauki jaririyar ta a hannun ta. Sai an dage da fada da surutu da sauran su, tukkuna ta ke ba ta nono. Ba ta ce umm, balle umm umm.

“Gobe zan koma gida Dagauda.” Muhibbat ta sanar wa Asiya, a lokacin suna zaune cikin lambun asibitin, sun bar Umma da Dada tare da Maree cikin dakin.

Asiya ta ji gaba daya hankalin ta ya kara tashi, “Na fahimta.”

Muhibbat ta kalli kasa, ta na tunanin kalaman da zata furta. Yanayi ne da Asiya ba ta taba gani ba. A ce Muhibbat ta kasa magana. 2

Ba kuma laifin ta bane. A ranar da safe ta ji lokacin da take waya da mahaifin ta, ya na cewa lallai ta koma gida, ko kuwa ta hadu da fushin sa.

Ba abin da zai sa ta bata rant aba ne. ta san labara ya bazu a can, Allah kadai ya san abin da a ke cewa, na karya da gaskiya. Idan a ce ita ce a matsayim Muhibbat, mahaifin su zai kira ta koma gida shi ma.
Amma dai Muhibbat din ta boye mu su ne, ba ta kuma san Asiyar ta jib a. ta shiga kame-kame, “Kin san akwai kudaden mutane a hannuna. Akwai wadan a suka ban sautun saya musu kaya, ba zai kyautu su yi jira ba.”

Asiya ta dan yi murmushi, “Ya yi, hajiyar bizines. Allah ya koro ciniki.”

Muhibbat ta dan yi murmushi, “Hmmm ke dai akwai ki da zolaya.”
“Ai gaskiya na fada.”

Ta kara sunkuyar  da kanta, ta ce, “Ban so barin ku ba Laminde…”

“Kar ki ce zaki daga wa kan ki hankali. Watakila a sallame mu a goben ma mu koma tare gaba daya.”

Su ka yi shiri na dan lokaci. Dukan su abu daya suke tunani. Yadda za su yi idan sun koma can din. Can Asiya ta nisa. Akwai yadda suka iya ne da kaddara? Za su bar ma su magana su yi ta yin ta, komi ya yi farko tilas ya yi karshe. A hakan har watarana komai ya zama labari.


Asubar farko Asiya ta farka kamar yadda ta saba. Ta yi niyyar yin alwala tare da yi nafilfili kafin a kira assalatu. Ta lura da kofar dakin su a wangame. Kanta ya daure, ta na mamakin yadda a ka yi hakan. Waye ya mu su wannan gangancin kuma?

Ta tura kofar ta rufe a hankali, gudun kar ta tashi sauran, musammam jariryar Maree. Duk dai ficicuya ce, wannan yarinya akwai iya rambada kuka, musamman idan aka ce karfe goma na dare yayi. A lokacin ne za ta ce gari yaw aye.

Wani abu ya tilasta ma ta dubawa don ta tabbatar barcin ta take yi bata farka ba. ta na barcin ta ne abin ta, don kuwa Dada ba ta dade da kwantar da it aba. Nan ta lura Maree ba ta kwance a kan gadon ta. 8

Ta nisa sannan ta zauna bakin gadon. Bai wuce ta na bandaki ba. Za ta jira fitowar ta kawai. Ta rika sake sake, tana kallon su Dada, wadan da ke kwance a kan dardumar da ke shimfide na sallah. Muhibbat kuwa tana kwance ne kan kafet din da ita ma ta tashi daga kai, ko motsi ba ta yi.

Ta bata tausayi, sannan ta taimaka kwari da gaske. Ba don it aba, bata san yada zata yi ba da wannan hali da suka tsinci kan su ciki.

Ba don ita ma ba da watakila ma bas u san halin da Mareen ta tsinci kan ta ba. hmm, wai har fait ace ke hana ta a da, ta nemi su juya su koma Dagauda kawai. Sai gas hi ashe Allah ne ya turo su kawai su fidda Maree daga wannan kangin.

Shiru, shiru, Maree ba ta fito daga bandakin ba har aka fara kiran assalatu. Dada ta farka, ta gan ta a zaune a hakan. Ta tambayi dalili, ita kuma ta amsa da, “Ina jiran Maree ta fito daga bandaki.”

Cikin idanun barci Dada ta yi hamma, sannan ta ce, “Ohhh. Tun yaushe ta shiga?”

“Ni ma dai ban sani ba. amma na dade ina jiranta.”
Kamar wadda aka sanar wa cewar hira a ke, jaririyar nan ta motsa, ta fara mita, zata fara kuka. Dada ta dan yi tsaki, 
“Wannan  yarinya akwai fitinar tsiya! Kira Mareen ta fito ta dauke ta don ni kam sallah zan yi.”

Jinjira ta shiga bare bakin ta, zata hana kowa sakat. Asiya ta je ta yi ta kiran Maree kan ta yi sauri ta fito. Jin ta shiru ya sa ta taba kofar, ta na tunanin anya kuwa, lafiya?

Kofar ta bude ba tare da wani shamaki ba. mamaki ya kama Asiya. Yo, ashe ma kofar a bude take tuntuni ta zauna zaman jira a wofi? Ta tura kofar a lokacin da ta ji yarinyar ta kara sautin kukan ta. A bisa dole Ddada ta sake daukar ta,

“Laminde, ki ce tayi sauri ta gama abin da take yi ta fito ta karbe ta”

Sai dai lokacin da ta shiga bandakin, bata ga alamar Maree ba, balle Mareen kan ta.Dokta Yusuf Haruna ya zauna a kan kujerarsa ta ofis, ya na juyawa a hankali. Ya kishingida jikin kujerar, sannan ya mayar da kansa ta baya, idanun sa a lumshe. Ya yi kyakkyawar nisawa. +

Kwanaki hudu da suka gabata sun kasance mafi tashin hankali gare shi. Da farko an Haifa mu su sabuwar halitta cikin zuri’ar su, ga matsalolin da uwar wannan baby ta samu kan ta. Ya yi bakin kokarin san a yin abin da ya dace. A ganin sa komai na tafiya daidai. A yanzu kuma sai ga wannan.

Shin ina a ka taba samun uwar da zata haifi diyar ta, sannan ta gudu ta bar ta? Ya gyara zaman sa, tare da sabon nisawa. Shi likita ne, ya fi kowa sanin hakan ya na faruwa a fadin duniyar nan. Kawai bai yi tsammanin hakan zai faru da sub a ne.

Amma bai so yadda ta gudu ta bar ‘yar uwar ta da mahaifiyar ta cikin mummunar hali ba. Shi kan sa ma ta jefa shi cikin damuwa. Bacewar ta daga asibitin sauki ya nuna gazawar tsaro da kulawa, wanda bai dace a ce an samu a asibitin ba.

Wannan labara zai jawo hayaniya mutane, da shisshigin ‘yan jarida da hadamar jami’an tsaro. Karin matsalar ma, bayan tafiyar Mariya, mahaifin su ya je asibitin da kan sa, ya kara girman matsalar.

Ya bukaci mahaifiyar Mariya da kanwar ta su bi shi gida can Dagauda, ba tare da jariryar ba. An buga wajen neman ya canja ra’ayin sa amma ya ki fir.

Duk ma da an nuna masa cewa yin hakan kece hakki ne da ma doka. Ya tattara su da dokar ya watsar gefe guda. Doka ko rashin ta, duk duniyar nan bai ga wanda zai hana shi zartas da hukunci kan iyalin sa ba.

Ya sake nisawa. Ya bar wajen su da safiyar nan, mahaifiyar ta yarda ta bi shi, kanwar Mariyar ce…ya ya ma sunan ta? Asiya. Ita kam ta zauna. A kalla a yanzu ne, bai san gaba ba. Ya fahimci dalilin guduwar Maree, a kalla ta wani bangare. 2

Amma mahaifin ta? Me ya sa shi yin hakan? Kawai don baya kaunar a ce an haifa ma sa shege a zuri’a? Shin hakan zai canja wani abu daga abin da ya faru ne? Ba zai hukunta shi ba, amma tilas, shi ma yana da laifi a kan halin da Mariya ta shiga ciki.

Bai so ganin yadda jaririyar nan ta shiga wannan yanayi ba. Tun a farkon kwanakin rayuwar ta mahaifan ta sun mayar da ita marainiyar dole. Fiye da laifin kowa, Yusuf dole ya karbi na kanin sa, wanda ya fara lalata rayuwar wannan yarinya Mariya tun farko.

A ranar da ya tuhume shi kan zancen bayan komawar su daga Dagauda, ba kunya ko tsoro, Khali ya ce da shi, “Wallahi Yusuf, da ka san yadda na tsane ka, da abin ya baka mamaki.” 2

“Idan ka tsaneni, wannan tsakaninmu ne. Amma me zai sa ka lalata rayuwar ‘yar mutane?”

A lokacin khalid ya yi masa kallon da ya soki zuciyar sa, amma sai bai nu na ba. ya ce, “Idan ka lura, ba rayuwar ta kadai na lalata ba, har da taka, dan lelen Alhaji. Nan ba da dadewa ba labarin abin da na aikata a matsayin kai zai baza duniya, mutane zasu la’ance ka, su ta kwatance da kai. Asibitin ka zai zama kufai, rayuwar ka za ta shiga cikin tsanani har sai ka bar garin nan cikin dare da tocilan da kafafuwan ka. Sai na jijjiga rayuwar ka Dan auta, sai na rugurguza ka.” 4

Ya sake nisawa. Maganar sa ta soke shi, ba wai don ya yarda dda barazanar sa bane. Hasali ma tausayin sa ya ji. Wannan irin tsana baya da kyau wa lafiyar dan Adam. Shi likita ne, ya sani. 2

“Jaaps!”

Sunan da Hadi da Sadi suka saba kiran junan su ke nan tun suna makaranta. Ya bude idanun sa , yayi ido hudu da Dokta Hadi, babban aminin sa.

“Ka yi nisa mutumina. Na yi ta sallama amma baka jib a.relax, kar ka daga wa kan ka hankali, domin ‘yan sanda sun bazu wajen neman ta. Za a same ta in shaa Allah, don kuwa na san ba zata yi nisa ba.”

STORY CONTINUES BELOW


Cikin kololon zuciyar sa, Yusuf yayi fatan hakan, don kuwa ya san Mariya bata gama warkewa ba, ga ba karfin jiki. Ba zai yiwu ta yi nisa ba. Amma ya danganci lokacin da ta fita daga asibiti.

Ya karkata akalar tunanin sa zuwa ga jaririya. Ba ta da lafiya, ga kuma rashin uwa. Ta na bukatar uwar ta, wadda Allah kadai ya san duniyar da ta shiga. Dole ya dage wajen kulawa da ita.

Dokta ya ce, “I hope so, ina fatan hakan.”

Babu abin da zai ce da sun a kalmar godiya. Tun faruwar wannan abu, sun kasance tare da shi tare da cikakken goya ma sa baya. A yau ma ganin faruwar hakan ya sa suka janye duk wasu marasa lafiya ma su son ganin sa don kawai ya samu natsuwa.

Dokta Hadi ya zauna, ya na fuskantar abokin sa, “Duniya ke nan. Ka ga yadda wasu suka haifi da, amma suka jefar. Wasu kuwa suna nema ba su samu ba.”

Yusuf ya ji abin ya tsaya ma sa a wuya. Ya san Hadi ba so ya ke ya kara tone ma sa matsalar ba, damuwar sa ce ta kan sa ta sa shi yin wannan furucin.

Shekarun sa bakwai ke nan da auren san a farko, amma har yau bai samu haihuwa ba. Shi tun suna jami’a ya auri Suhaima, daga baya ya kara da Kausar, amma kowacce ba ta haihu ba. dole ne hakan ya sosa ma sa zuciya.

Dokta Hadi ya ci gaba da cewa, “Ka san tun da na fada wa Suhaima abin da ya faru sai ta buga min waya kowane bayan minti talatin don ta ji yadda a ke ciki game da yarinyar. Har cewa take wai idan mun rasa mai reno za ta zo ta mana a kyauta, ba sai mun biya ta ba.”

Dukan su suka yi murmushi. Yusuf ya san Hadi ya sako barkwanci ne kawai, amma can kasar zuciyar sa, da gaske yake yi. Tabbas, da za a bashi babyn zai karba.

Sai dai ba zai iya yin hakan ba. ba zai iya ganin jinin sa ta girma tare da bare ba, alhali yana nan a raye. Ko da Khalid zai watsar da ita, komai tsanar da yake masa, tilas ya karbe ta ya bata kulawa. Nauyin sa ne, hakan ne kuma ya dace. Ya tabbata da mahaifin su yana raye, zai amince ma sa da hakan.

A hakikanin gaskiya, ba zai kara barin wannan yarinya ta shiga wani halin da take ciki ba. ba ta da laifi ko guda, don haka bai dace a mata horo irin wannan ba. sam bata cancanci hakan ba. don haka zai gyara, yayi alwashi, zai gyara. Wannan kudiri ya kulla a ransa, zai kuma aiwatar cikin yardarm Allah, komai tsanani! 2

* * * 

Asiya ta na kwance a dunkule ta gefen jaririyar, wadda ba ta dade da kwantar da ita ba. Hasali ma tun bayan batar Mariya ba ta kaunar abin da zai raba su, sai ko yin sallah da kuma idan za a kai ta wajen da likita zai duba lafiyar ta. 7

A halin yanzu ba ta iya tunanin komai sai kulawa da jinjirar nan. Ta rasa dalilin da ya sa Mariya ta bace mu su alhali ta san yin hakan zai iya kara dagula komai. Tabbas Mariya ta kai kololo wajen son kan ta, ba tare da la’akari da kowa ba.

Yarinyar ta motsa, Asiya ta mike don lekawa cikin karamin gadon katakon da a ka tanadar ma ta. Tausayi da kauna suka rungume zuciyar ta. Ta kai hannun ta ta na shafa kumatun jaririyar, ta na jin cikowar kwalla cikin idanun ta. Haka kawai, ba bu laifin tsaye da na zaune an dora ma ta maraici. Iyayen ta duk sun bar ta tun ma ba ta san ko su waye ba.

“Ki yi hakuri Baby, Allah Ya dora miki jarrabawa.” Ta furta wa Baby A, kamar yadda ta gani cikin fayel din ta.

“Ga shi yau kwanaki bakwai ke nan ki ka shiga da zuwan ki nan duniyar, amma ko huduba ba a mi ki ba balle a rada mi ki suna.” Ta ci gaba da shafa ma ta kai da fuska ba ki daya. Baby A ba suna ba ne. sai ka ce wata abar yin gwaji na dakin likita? 6

Ta saka hannu ta dauke ta daga cikin gadon, Baby A ta kara dunkulewa jikin ta, ta manne idanun ta cikin barcin da ta ke yi. Tun zuwan ta duniya cikin barci ta ke fiye da rabin rana. Ko ba ya isar ta ne? 2

STORY CONTINUES BELOW


“Zo nan mu yi hira, ki gaya min, wane suna ki ke so a saka mi ki?”

Baby ta ci gaba da barcin ta. Ita kuwa ta kai ta dab hancin ta ta na sunsuna kamshin jikin ta mai dadi na sabulun wankar ta da hoda. Ta kara jin zuciyar ta ta matse kamar yadda a ke matse kaya kafin a shanya su bayan an wanke.

“Wane suna ya fi dacewa da ke? A’isha, Maryam, ko Hauwa? Ya kamata a ce ke ma ki na da suna kamar kowa.”

Asiya ta nisa a daidai lokacin da ta ke mayar da kwallar cikin idanun ta. Ya dace a ce ta na da suna, ko don ma idan a ka kai ta gidan marayu a samu abin da za a rika kiran ta da shi.

Ko ma idan ta girma za ta samu abin da za ta amsa magana da shi. ‘Yancin kowane dan Adam ne a ba shi suna, amma ita ba ta yi dacen hakan ba. Lallai idan ta girma ba a san abin da za ta zama ba a rayuwa.

Ta ji an kwankwasa kofar dakin a hankali, ba tare da dogon tunani ba ta yi izini wa mai shi ya shiga. Ta san ba zai wuce Nas Samira ba wacce ke aikin dare. Da ma ta yi mu su alkawarin shiga wajen asuba ta duba su. Ta duba agogon wayar Mariya ta bari, karfe hudu saura kwata na dare.

“Assalamu Alaikum.” Sallamar ta fito, amma ba daga bakin Nas ba.

Yadda silin gashin ta ya mike tsaye ta san Dokta Yusuf ne. Ta juya ta fuskance shi, kamshin turaren say a shige hancin ta. Mamaki da rudani suka kamata a lokacin. Me ya ke yi a dakin su a wannan lokacin?

Tambaya ce marar ma’ana ta yi wa kan ta. Asibitin sa ne, kuma shi babban likita ne. Don haka zai iya shiga wurin da ya ga dama a lokaci da ya ga dama.

Akwai wanda zai kayyade ma sa aikin sa ne? Ko yaushe za a iya neman sa don ceton rai. Sai dai ba neman sa ta yi ba a yanzu, me ya sa ya bayyana? Idanun ta suka zaro, ko dai Baby A ce ke cikin hatsari?

Ta amsa sallamar sannan ta kawar da kan ta zuwa kan yarinyar ta kura ma ta idanu. Ta na cikin fargaba, sannan a duk lokacin da ya ke gaban ta sai ta rika jin takura. Ga shi a lokacin sun a daki daya da shi, babu wa ta tazara tsakanin su wajen karfe hudu saura na dare.

“Mu ga Baby?” Ya mika ma ta hannu.

Ta zuki numfashi cikin huhunta, ta na kokarin kar ta nuna fargabar ta. Ta mika ma sa tare da yin hattara kar hannayen sa su shafi nasa. Bayan ya dudduba ta, ya ce gyada kan sa a hankali, “Na gamsu da samun lafiyar ta sosai. I am impressed.”

Wani irin numfashi ta sake da ba ta san lokacin da ta rike ba. Ya kalle ta sosai, ta lura da kayan jikin san a tun wanda ya saka da safe ne. Hakan ya nu na cewar bai koma gidan sa ba tun safe.

“Na ji dadin ganin ki a nan, tare da ita. Tun jiya ina ta tsoron kar a zo a sanar min cewar ke ma kin bar gari.”

Asiya ta kalli fuskar sa, duk da cewar hasken dakin ba ya iya bari ta kalli kwayar idanun sa. Muryar sa ce cike da taushi da fargaba. Abu ne mai wuya a ce yadda ya ke da girman jiki a samu muryar sa mai taushi haka.

Ta mayar da hankalin ta ga kalaman da ya furta ma ta, ta ce da shi,”Ba zan iya tafiya bar yarinyar nan ba tare da sanin halin da za ta shiga ba.”

Muryar sa da murmushi, ya tambaye ta, “Ba kya tsoron mahaifin ki?”

Tambaya ce mai ma’ana, amma a halin yanzu ba ta ita a ke ba, ta jiriryar da ba ta san komai a ke yi. Ta amsa, “Na fi jin tsoron hukuncin Allah a kan na mahaifina. Na san ba ni na aikata laifin da ya kawo yarinyar nan duniya ba, amma ina tsoron ranar da zan tsaya a gaban Allah na amsa tuhumarSa game da yadda na bar ta wa duniya alhali ina da yadda zan ba da gudumawa mai muhimmanci ga rayuwar ta.” 2

Tun jiya ta ke jin haushin kan ta. Hakika, duk laifin na ta ne. da a ce tun farko ta matsa wa Dada kar a yi auren Mariya da Mudassir, da ba a kawo ga yanzu ba. Sai me ye don a lokacin ba bu wanda ya saurare ta? Ai da dai ta kara matsawa har ta yi nasara.

STORY CONTINUES BELOW


Dokta ya ajiye jaririya cikin gadon ta a hankali. Dan hasken da ke dakin har a lokacin bay a bari ta kalli kwayar idanun sa. Amma ta san suna cikin tsananin kulawa ne da kauna. Hakan ya sosa zuciyar ta. Ta ji ya ce, “Zauna mana.” Ya nu na ma ta kujera talon da ke dakin. “Akwai maganar da na ke son tattaunawa da ke.” 2

Gaban ta ya fadi ras! Kar dai lokaci ya yi ne da zai raba ta da Baby A, ya kai ta gidan marayu? Ta san dai lokaci zai zo na hakan amma ta so a ce ta kara samun lokaci tare da ita. Ga shi ya na tsaye a kan ta bai kara cewa komai ba. Watakila tauna zancen ya ke yi kafin ya furta. Hakan ya kara dagula ma ta kai.

An fara kiraye-kirayen sallah a lokacin. Ya jira lokacin da a ka idar, sannan ya ce da ita, “A ina ne ki ka tsaya da karatun ki?”

Karatun ta kuma? Ba ta yi tsammanin wannan tambayar a lokacin ba. Alakar meye karatun ta ya ke da shi da yanayin da a ke ciki? Ta amsa kai tsaye, “Na sauke karatun Al-Qur’an , a yanzu haka na fara haddar sa.” 2

Mamaki bai bar ta ba, ta na kwada kwanyar ta kan dalilin wannan tambayar ta sa. Mece ce alakar wannan tambayar ta sa da yanayin da su ke ciki? Ta dai san ba zai yi tambayar a banza, sannan bai yi kama da wanda zai yi komai ba tare da dalili ba.

“I see.” Ya furta cikin Karin sabon nazari. Ya zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa. Hakan ya kan sa shi ya yi kyau matuka.

Ya nisa a hankali sannan ya ci gaba da cewa, “Kamar yadda ki ka furta yanzun nan, ba kya da laifi wajen zuwan yarinyar nan duniya, amma na ji dadin ganin yadda ki ka jajurce wajen tsaya mata da kulawa.

Ba ta san ko dadi ya kamata ta ji ba, don kuwa a tunanin ta, akwai sauran zance. Ta matsu ta san sauran, duk da ba ta gwada ma sa hakan ba.

Ta ce da shi, “A shirye na ke wajen ba wa jaririyar nan kulawa gwargwadon iyawa ta.” Ita kan ta so take ta roke shi a lokacin, kan kar ya kai yarinyar gidan marayu, ko ya ce bayar da ita. A kan yayi hakan gwara ya ma ta allura ta mutu. Hakan ya sa numfashi sama-sama ta ke iya yi.

Ya dan sake fuskar sa, a kalla hakan ta dan lura cikin dan hasken dakin, sannan ya ce, “Ya yi kyau. Na ji dadin jin hakan daga gare ki. Hakan ya nuna min cewa kea bar yard ace, kuma abin dogaro. Shi ya sa na ke ga ke ce za ki iya taimaka min wajen samun maslaha ga wannan matsalar.”

“Ta ya ya zan iya taimakawa?” Ta ji dadin taimakon ta da ya nema, Allah Ya sa za ta iya.

“Wannan hanya ita ce hanyar aure.” 6

Kan ta ya kara dagulewa, “Aure kuma?” Idan ya na nufin ita ce za ta yi aure don ta samu damar kulawa da Baby A to za a dan samu matsala. Domin Rabi’u Gwammaja, wanda shi kadai ne ma ta dan yarda da tayin soyayyar sa, bai kai gaisuwar neman aurenta wajen iyayen ta ba. A halin da a ke ciki ma, gwara da hakan. 2

Don ta na ganin yarda da shi zai mata wahala, saboda abotar sa da Mudassir. Ta tabbata ya san halayen Mudassir amma ya ki fada mu su. Ba mamaki halayen na su ma daya ne. A halin yanzu yarda da duk wani da namiji zai mata wahala. 2

Idan kuma ya na nufin shi zai yi auren don ya dauke ta aikin reno da kulawa da baby, ba ta da matsala kan hakan. Sai dai ba ta san yadda iyayen ta za su dauki wannan tsarin ba.

Ba tare da dogon nazari ba, ta ci gaba da cewa, “A gaskiya ba a fara magana kan aure na ba a gida, don haka ta bangare na zai dan yi wuya. Sai ko in kai za ka yi auren in ya so na kula da baby, to.” 6

Ya saki murmushi sosai. Tana iya ganin fuskar ta sa sosai don idanun ta sun saba da yanayin hasken dakin. Ta ce, “Ni da ke abu daya mu ke tunani.” 2

Ta dan ji sanyi. Ashe dai ba gidan marayu ya ke shirin kai ta ba. Ta kara da cewa, “To amma ai gwara tunanin ka da wadda za ka aura ya zama daya. Ko ka tattauna da ita ne?”

Ya fadada murmushin sa, “Shi na ke kokarin yi yanzu.” 4

“Ban gane ba.” 3

Ya zauna a gefen gadon da ke dakin, ya ce, “Jin cewa ba a fara maganar auren ki ba ya kara saukaka min komai. Tambayar da na ke son yi mi ki ita ce; za ki aure ni?” 11

Wani irin bugawa zuciyar ta ta yi, numfashi ya yanke cikin huhunta. Ta yi tsammanin kowacce irin tambaya daga gare shi, amma ko cikin mafarki ba ta yi tunanin wannan ba. Wai me ma? Dibb, kwanyar ta ta dauke. Ta kura ma sa idanu kamar wanda kaho ya tsiro tsakiyar kan sa a lokacin.

Shi ma kallon ta yake yi, ya na ganin yadda fuskar ta ke canjawa tare da tunanin ta. A lokacin ya ke ganin wautar sa da shirmen tunanin sa. A lokacin da ya ke nazari, komai ya yi masa daidai, amma a yanzu bai yi tsammanin daidai din ba ne. Shi kan sa muryar sa ta bayyana fargabar sa da tsoro. Ta ya ya za a yi ita ta amince da bukatar sa?

Ya tabbata ya tsorata ta, shi ya sa ta kasa furta komai. Shi ma kafin ya shigo dakin ne wannan tunani ya fado ma sa. Da ya tattauna da su Hadi da kila sun canja ma sa shawara.

Amma ya ga cewa ya fara maganar da Asiya tukunna, tun da komai zai dogara ne da amsar ta. Ba kuma zai janye ba saboda babu kowa a gaban sa face jinjirar da ke kwance a gefen sa. Hatta shi kan sa layin baya ya koma, ba ya tunanin hatsarin da zai iya shiga.

Idan ta ci gaba da kallon sa haka ba tare da cewa komai ba za ta iya saka shi jin karaya. Saboda haka, sai ya canja salon sa, “Kar ki damu, wannan aure da za mu yin a wucin gadi ne. Za ki taimake ni wajen renon baby A har zuwa lokacin shigar ta makaranta. Ni kuma na yi alkawarin daukar nauyin karatun ki na gaba da sakandare a duk makarantar da ki ke so ki kuma karanta kwas din da ki ke ra’ayi.”

Har a lokacin ba ta ce komai ba. Ba hakan ya dauka ba. Ya yi zaton za ta fahimce shi, ta ba shi hadin kai, tun da ga alama abin da ya ke so shi ta ke so. A kalla, sun san babu wata alakar soyayya a tsakanin su. To me ye matsalar?

A tunanin sa za ta fi kowa farincikin jin maslahar da ya nemo mu su, kuma wannan tayin da ya yi zai yi wuya ta kauce ma sa. Ya sako abin da zai amfane ta a ciki, ba wai zai bautar da ita ba ne a banza. Cude ni in cude ka ne abin.

“Idan mun ci gaba da zama haka babu abin da zamu iya warwarewa. Me ki ka ce?” A kalla ya fada ma ta abin da ke zuciyar sa, ko da ya yi kamar yaro karami ne ya yi tunanin. Kwallon ya na filin ta ne, ya rage na ta. Ya ma fi son ya ji ta ce a’a din ma, idan har hakan ne ra’ayin ta.

“Me ka dauki aure ne Dokta?” Ta tambaye shi, muryar ta ba ta nu na fargabar ta na farko. 1

Ya kawar da kan sa, don ba ya kaunar abin da zai tona masa abin da ya birne cikin zuciyar sa. Ba ya son ta ga irin zogin da zuciyar sa kan yi ba a duk lokacin da a ka tabo masa maganar aure ba. Bai yi zaton bayan halin da ya shiga game da rashin Abida, zai iya fuskantar wata mace da batun aure ba. Sai ga shi ya na maganar da wadda bayan sunan ta, bai san wani abu game da ita ba.

Ta ci gaba da tambayar sa ba tare da jiran ya ba ta amsar tambayar farko ba, “Me ya sa kayi zaton mun dace da mu auri junan mu? Me ya sa ka ke ganin zan amince.”

“Saboda aure ne hanyar da ya fi dacewa gare mu a yanzu. Kin fi kowa cancantar rike Baby A don na san kamar yadda ke ma ki ke son ta samu rayuwa mai inganci, ni ma hakan ne a gaba na. Auren nan ba don kai na zan yi shi ba. Zan yi ne don kar rayuwar jaririyar nan ta shiga matsala. Ina son ki san cewa ba zan matsa miki ba idan har kina ganin hanyar da na fit aba ta dace gare ki ba. Ba zan ji haushi ko na kullace ki ba. Ina son ki san cewa zan samo wadda za ta iya kula da ita cikin aminci da yarda, don haka baa bin da zai dame ki ba ne. ke dai fada min ra’ayin ki kawai.”

Ya kamata ya ji kunyar abin da ya ke yi, na tilasta mata amincewa kudirin sa a kaikaice. Ya san idan ta ji wannan bayani ba za ta so rabuwa da baby ba. A kalla, hakan ya ke fata.

Ya lura ta sunkuyar da kan ta kasa. Yayi kyau, hakan na nufin ta na nazari ke nan. Ya fara taya kan sa murnar samun nasara. Can ya ga ta dago kan ta, idanun ta cike da rauni…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *