KE NAKESO CHAPTER 6 KARSHE

KE NAKESO




CHAPTER 6 KARSHE




Abdul-Aali baya samun matsalar zuwa Weekend, wani lokaci sai bayan sati biyu yake zuwa. Yara suna hutu, ya karbi nasa hutun gaba daya suka antayo. Muhammad kuwa tamkar jira yake yi, yana ganin ‘Yan-uwan sai murna. +

Suna isa Mimie ta-ce. “Mami, zan je gun Anty Hauwa mu yi wasa da Muhammad”.

Hamama ta zare mata idanu ta-ce. “Wasa? Bayan dazu ku ka shigo? Ku zauna ku huta, ba na son kaudi.”

Mimie ta bata fuska, tana buga kafa. “Mami, ki yi hakuri kin ji? Ba za mu dade ba a falon Anty Hauwa ne fa”.

“Nace miki babu inda za ku je, ku zauna. Ga Cartoon nan na kunna maku, ko kuma ki yi wasan da Ramla, amma daga yau idan na kara ganin ki a falon Anty Hauwa, sai nayi miki bulala.” 3

Abin ka da yaro, sai Mimie ta sa kuka da bori, a haka har barci ya dauketa. Da yamma ya shigo ya sameta a kwance. “Yaya, yau kuma Mimie da barcin yamma, sai ta tashi ta yi ta rikici ko?”

Hamama ta kalle shi, ba ta ce komai ba, idan ya tashi tamkar shi kadai ne mai ‘ya’yan.

“Ki daina bari tana irin wannan barcin.” Ya fada yana gyara mata kwanciya. Sannan ya-ce. “Ba abinda zan samu ne a kicin dinki?”

“Kwadayin ya motsa kenan, me ka ke so?” ta fada murya kasa-kasa.

“Koma meye dai, amma marar nauyi.”

Nan ta koma kicin ta samo masa wani abin, sannan suka zauna suna hira, yana ci. Ba abin da ya fi mata haka dadi, suna zaman zaman su, ya kama ya bata masu rayuwa da wani aure na fama. 1

****

Mai-jidda dai ba abin da yake damunta irin yau kwana uku kenan, ba ta ganin yaran a Side dinta, sai sun tashi cin abinci, duk da haka dai ba ta yi magana ba.

A kwana na hudun ne. Abdul-Aali ya-ce. “Mimie, je ki falon Anty Hauwa ki kira Muhammad ku zo mu tafi yawo.”

Har ta tashi za ta tafi ta dawo ta-ce. “Dadi, Mamina fa ta-ce na daina shiga falon Anty Hauwa ko kuma ta min bulala.”

STORY CONTINUES BELOW


Abdul ya sunkuyo daidai tsawon yarinyar ya-ce. “Mamin ki ta-ce ki daina shiga? Kin yi tsokana ne ko barna?”

“A’a wasa ne fa za mu yi da Yaya Muhammad, shi ne ta-ce kar na je. Har na yi kuka, amma ta ki ta barni na je.”

Ya dago kansa cikin al’ajabi ya-ce. “Kar ki damu ko? Ku rinka zuwa ku na wasan ku Anty Hauwa ma Maminku ce, kin ji?”

Ta daga kai tana murna, da sauri ta bude kofar Side din Mai-jidda. Abdul Ali bai nemi magana da Hamamatu ba, har suka tafi unguwarsu suka dawo. Sai washegari a gabansa, ya ga tana zarewa Mimie ido, don ta ambaci shiga Side din Mai-jidda.

“Mimie kama hannun Ramla, ku je ku yi wasan ku.” Suna fita ya-ce. “Hamama, abin da ki ke koyawa yaran nan ya dace kenan a ganin ki?”

Cikin rashin kulawa ta-ce. “Me kenan?”

“Ina sane da cewa kin hana yaran nan zuwa sashen Jidda. Akan wane dalili za ki hanasu mu’amala?”

“Oh, akan wannan ne, shi ne za ka wani tada jijiyoyi? Ni haka kawai ba na so.”

“Kin yi adalci kenan, idan kin yi haka? Yin hakan da ki ka yi, zai sa su dauketa a matsayin uwa ko kuwa wani abin ki ke nema ki cusa a cikin zukatan yara kanana da ba su san komai ba, na sha fada miki, duk wani abu da za ki yi, kar ki kuskura ki jawo yara a ciki.

Don ranki ba zai yi dadi ba. Jidda matata ce, kuma ya zama lallai su yi mu’amala da yarana, idan kuma ki na da matsala, sai ki fada min tun yanzu na sani.”

Shiru ta yi, tana diri ita kadai, akan me ya sa zai nuna mata iko kan ‘ya’yan da ita ta haifa. Haka kawai ayi ta yin munafunci kamar ana son yaranta, alhali ba haka bane. 1

“Na ji abinda ka ce, tunda kuwa ka na da iko da yaranka, haka ni ma na ke da iko da su, kai idanunka sun rufe kan Hauwa, ba ka ganin komai. To ni gaskiya ba za a munafunceni, sannan a kaleleyeni da zance ba, tunda ai mai hali, baya fasawa.”

“Ki fada min wani abu? Kin taba gani ta cutar da su, ko kuwa radin kanki ne kawai, ki tarwatsa min zaman lafiyan gida?”

“Mai hali yana fasa halinsa ne?”

Mamaki ya kama Abdul-Aali ya-ce. “Shi kenan, ki bi a hankali, don kuwa akan wannan maganar, ba za mu shirya da ke ba.” Ya mike ya bar falon.

“Tabdi! Ai Wallahi ba za ta yiwu ba, haka kawai a cuci mutum.” Haka suka shafe kwana uku, kwata-kwata, ya fita sabgarta, saboda ya gwada mata kuskurenta. Ranar na ukun ne ta tafi gidansu, saboda haka nan akan gaskiyarta, ba zai daure mata fuska ba, ya fita sha’aninta. 1

“Hajiya kin ji yadda muka yi da shi, abu kadan yake jira, idan dai ya shafi Hauwa, sai ki ga ya tattara, duk wani laifi ya dora min.”

“Yanzu fita sha’anin ki ya yi, don kawai ba ki son huldarta da yaranki?”

Tana share hawaye ta-ce. “Eh Hajiya, kuma Wallahi kiriniya Danta ya ke koya masu, da ba su iya wasu wasannin ba, amma yanzu rashin ji ba iyaka. Akan me zan yi shiru?”

“Kar ki damu, ni zan yi magana da Alhaji, ya same shi yayi masa magana, amma ai ba zai yi fushi ba, bayan bai san hujjarki ba.”

Ita ba wanda take so irin Hajiyarta, saboda ba ta kasa da gwiwa wajen tsayawa ta ga ta samowa mutum ‘yanci, shi ya sa ma ta taho, ta san za ta sa Abdul-Aali ya zo tayi masa magana. 1

Sai dai maimakon haka. Alhaji na jin maganar ransa ya baci, ya-ce a kira masa Hamama.

Tana zaune a babban falon Alhajin, ya dubeta daga karatun da yake yi, na wani littafi, “Gani Alhaji, ance ka na son ganina.” 1

Shiru ya yi, sai da ya kare mata kallo, sannan ya-ce. “Hamama, da dai ban san ki da wannan tsirface-tsirfacen ba, ko me ya sa ki ke so ki canza dabi’unki? Yaya za ki sa kafa ki taho gida, kan abin da bai taka kara ya karya ba?

STORY CONTINUES BELOW


A kanki aka fara yin kishiya? Don me ya sa ki ke daga hankalin mijinki, ki fada min, tunda ki ke zaune da ita, kin taba ganin wani mummunan abu da ta yi miki, ko yiwa ‘ya’yanki, da har za ki ce don sun shiga sashenta, za ki tada hankalinki har da yin yaji.” Ya yi shiru, sannan ya-ce. “Ke na ke saurare, ki fada min.”

“Alhaji babu.”

“To, akan babu za ki fitini kanki, ki hana kanki zaman lafiya? Don ke ki na jin dadin rayuwa, ba ki san me matsalar rayuwa ba ko? Komai kin samu ana yi miki shi, mijinki yana biye miki, shi ne za ki samu Hajiya da wani zance na rashin hankali. Kin dauka zaman gidan za ki ji dadin sa ne yanzu? Idan kuma shi ki ka fi so, shi kenan, sai ki tsaya kishin hauka ya kashe miki auren ki zo ki samu a gaba, ki yi ta kallo.” 2

“Alhaji ka yi hakuri, ba zan sake ba”.

“Ki kwantar da hankalinki Hamama, ina son fa ki san cewa wannan auren da mijinki ya yi, kaddara ce, kuma koda duka duniya za su taru, su hana shi, ba zai hanu ba, saboda Allah ya riga ya sa a cikin kaddararsa, sai ya auri wata macen bayan ke. Don haka ki zauna da su tsakani da Allah.

Kar ki zauna da mugunta a cikin ranki ko wata manufa ta sharri, zai yiwu ba ta da sharri a zuciyarta game da ke, kin ga kuwa idan ki kayi mata sharri, alhakinta zai iya kamaki, sannan ga zunubin zargi da ki ka mata.

Sannan idan ki ka faye yawan fitina, to za ki gunduri mijinki, maimakon ki yi aikin ibada, sai ya zama kwasan zunubi ki ke yi. Don haka ki kiyaye, ki zauna tsakaninki da Allah.

Duk abinda mijinki ya ke so, to ke ma ki taya shi son abin, idan kuwa ya ki abin, to maza ki guje shi, sai ki ga kun zauna lafiya matukar bai sabawa Allah ba. Sannan daga yau kar ki kara zuwa gidan nan da sunan yaji. Ina fatan kin ji?”

Tana kuka ta yi masa godiya, sannan ta-ce za ta koma gidanta. Tunda ta fito ta fadawa Hajiya abinda Alhajinsu ya ce, sai Hajiya ta saduda ta-ce. “To shi kenan. Allah ya baku zaman lafiya.”

Tana komawa gida, sai ta ji wani iri, yaran da take ta fadan kar kishiyarta ta raba su, can ta same su suna karatu da ita da kuma Dan cikinta, tana jansu a jiki, tamkar ita ta haifa, sannan Ramlah na zaune kan cinyarta, tana taya su jagwalgwale, sai ta ji jikinta ya mutu. Ta dan sassauto kan maganar yaran.

*******

Ranar Alhamis ne ya ce, masu zai je Dutse gaisuwa, bayan tafiyarsa ne Mai-jidda ta kwanta a falo, saboda kanta dake sara mata, ga shi tana dauke da azumi a bakinta, shigowar sa ta ji, ya sa ta mike. “Lafiya ka dawo?”

“Mantuwa na yi.” Nan ya shiga bude drawer ya dauki abin da ya dawo dashi. Ya zo fita ne ya ankara da yanayinta. “Lafiya na gan ki haka?”

“Wallahi gajiya-ce, kawai kaina ke min ciwo.”

“To ki sha magani mana, sai ki kwanta ki huta?”

Yamutsa fuska ta yi sannan ta-ce. “Ina azumi ai, ba yadda za ayi na sha magani”.

Abdul-Aali ya dube ta kamar wacce ta-ce wani abin tsoro. “Az… Azumi ki ke yi?”

Kai ta daga masa. “Zan iya sanin wanda ya ba ki izinin ki yi azumi, ba tare da sanina ba?”

Mai-jidda tayi masa duban mamaki, yau ta ga ikon Allah, ina ruwan sa da azuminta? Ta ga dai yanzu ta yi karfi, bare ya-ce kar baby ya wahala, don yanzu ya shiga wata hudu da ‘yan kai, laulayin ma ta rage yinsa, sai dan abinda ba a rasa ba. “Na ga ba girki na bane, shi ya sa ban fada maka ba.”

“Saboda ba girkin ki bane, shi ya sa ba ki fada ba? Don ba girkin ki bane, hakan yana nufin ke ba mata ta bace yau ko me?”

“A’a ba haka bane, ka yi hakuri.” Ta fada cikinta na wani kara saboda kallon da taga yake mata.

STORY CONTINUES BELOW


Kai kawai ya gyada ya yi tafiyarsa.

Da yamma ta kammala aikin abinci, kasancewar Mamin Mimie ta mika mata girki, daman ita tarkacen kayan buda baki, ba wai sun dameta bane, don haka abin da ta yi na gida , shi za ta yi buda bakinta da shi, sai kayan marmari da ta yanka.

Tana zaune da su Ramla a daki suna ta wasan su, yayin da ita kam a kwance take akan gado tana azkar, don azumin ya riga ya shige ta. Wanka ta yi ko za ta dan ji karfin jikinta.

Ta zo ta mike, nan ne su Mimie suka shigo, wai ta goya masu ‘yar bebinsu. Ramla kuma wai ayi wa nata kitso, irin wanda tayi mata ranan. Abdul-Aali ya yi sallama, ya shigo, ta dube shi, tayi masa sannu da zuwa, cikin fara’a.

“Yauwwa”. Ya amsa yana ganin yadda ta dawo. “Hmm! Yau azumi yana kwada wata kenan.” Kafin ta amsa, ya dubi Mimie da ta kawo masa ‘yar bebinta na dora ya-ce. “Je ku kai wa Mamin ku ta gyara maku goyon.”

Nan da nan yaran suka fita, suna fita Abdul-Aali ya sa key a kofar dakin Mai-jidda. Ita dai kallon sa kawai take yi. “Lafiya?”

Hannunta ya rike ya-ce. “Zo ki ga wani abu”. Nan ya ja ta gaban madubi ya-ce. “Kin gama aikin ki ne?”

“Eh na gama.” Ganin yadda yake kallonta, ta gano ko meye a ransa, musamman yadda ta ga ya fara shisshige mata. “Meye ne Abdul-Aali? Ta fada tana kokarin janye jikinta.

“hmm… Babu, me ki ka gani?”

“Ka bari mana”. Ta fada tana zulmiyewa.

“Uhm-uhm! Ina tsammanin dai yanzu ke ce da girki?”

Nan gabanta ya yanke ya fadi. “Saboda haka ba laifi bane, ko kuwa?”

“Ina azumi fa?” Ta fada tana rarraba idanu, ya juyo da ita yana kallonta. “Nan gaba za ki sake azumin nafila ba izini?”

Da sauri ta kada masa kanta ya-ce. “Good! Saboda (I’am about to teach you a lesson).”

Nan kuwa ya shiga sarrafata, tana rokon sa da ya kyaleta, amma ina, ya riga ya yi nisa, sai da ya karya mata azuminta rugu-rugu! 22

Haka ta zauna a bakin gado, ta sha kukanta, sai da ya yi wanka ya fito ne ya-ce. “Gobe ko a kasar Sin na ke, ba girkin wata ba, za ki fada min kan ki dau azumin nafila. 3

Sai ka ce wata abin nan, wai ‘ba girkina bane'”. Haka kawai ya karya mata azuminta don mugunta, kuma sai da ya jira ta gama galabaita, sannan ya hanata karasa azuminta. 2

“Yanzu kukan meye ki ke yi bayan kuma…” 2

Ta watsa masa wani kallo tukun ta-ce. “Bayan ka hanani ladan azumina?” 3

“Ai ke ce da riba biyu, kin ga kin samu ladan niyya, kin kuma samu ladan shimfida. Don haka ki daina fushi. Ko ba komai, na san ranki fes! Ba wanda ya kai ki jin dadi.” 8

Yana dariya ya dauki kankana a cikin Plate din Fruits da ta ajiye a dakin, don buda bakinta, ya kai baki. Ranar kwana ta yi tana fushi da Abdul-Aali, amma shi ya san yadda yake sauko da fushinta, cikin lokaci kalilan.

Ganin ta bata rai da safe shi kuwa ya-ce “Hamamatu miko min ruwa a fridge”

Yana sane sarai da cewa Mai-jidda ce ta sa abinci, hakan ya bata mata rai, amma ta danne. Ita kuwa Hamamatu tana jin haka, ta mike ta yi yadda ya-ce, ko da ta ga hirarsa da Hamama ya fi karkata.

Sai ta daina sa baki a maganar. Sai da suka gama karyawa ta same shi a daki ta-ce. “Don Allah ina son zuwa gidan Yaya Maryam anjima”.

“Ga shi zan yi amfani da motar, ki shirya sai na ajiyeki.”

A tsume ta bar dakin, ta gama shirinta ta fito, ta same shi, za ta shiga mota ne, ta ji karar (Text) a wayarta. Sai da ta sa Muhammad da Mimie a mota tukun, don Hamama ta-ce ta bar Ramla, za su zauna a gida, sannan ta shiga ta bude sakon.

Abdul-Aali ya tada motar, daidai da faduwar gaban Mai-jidda. “I miss you, Hauwa” Ta ga sakon da aka turo mata, nan ta shiga karanto “Inna-Lillahi’wa-Inna-Ilaihir- Raji’un!

Abdul-Aali ya-ce. “Lafiya?” Fuskarsa cike da mamakin ganin yanayin ta.

Wasu lokutan ta kan ji kamar ta fadawa Abdul-Aali maganar Dan Kano da matsa mata da yake yi yanzu, don abin nasa ya soma wuce tunaninta.

“Babu, mu je kawai”.

“Ba dai wani abu ke miki ciwo ba?”

Kai ta girgiza masa, sannan ta rubuta reply wa Dan Kano. “Ko ma wanene kai, don Allah, ka barni saboda ka fi-ni sanin rashin dacewar hakan a matsayinka na mai mata. Shin za ka so idan wani yayi ta matsawa matarka haka?”

Nan take ta tura sakon. Abdul-Aali yana lura da yanayin Mai-jidda, har suka isa gidan Yaya Maryam. Nan ya bar su akan idan ya gama abubuwan da yake yi, zai zo ya dauke su. Gaba daya ba ta ji dadin wunin ba, tsabar fargaban al’amarin Dan Kano. Dole ta san abin yi.

*****
Kafin hutunsa ya kare ne. Bikin Yaya Abbakar ya taso, don haka ta tafi Dutse, saboda bikin, ran daurin auren ne. Ya taho da Hamama da yara. Nan da nan kuwa Mai-jidda tayi masu kyakkyawar tarba. Hamama dai ba a son ranta ba, Abdul-Aali ya tattarasu suka taho.

Haka ta tsaya tana karewa gidan su Mai-jidda kallo, daman haka tsiyar take, shi ne ake wani ji da ita? Tana tsegumi a ranta ne kawai, ta ga Muhammad yana bawa Ramla ruwa a cup, da sauri ta wabce ta-ce. “Yaya za ka ba ta ruwan famfo?”

Mai-jidda ta kula da hakan, don haka ta aika aka sayo carton din faro a shago. Ta bude ta-ce. “Yaro kam, duk inda ya shiga zai iya shan komai, kar ki sabar masu da ruwan roba kawai.

Saboda hakan ne zai sa randa suka sha wanda ba shi ba, ya sa su ciwo. Ko kuma ki rinka yi masu yawo da ruwansu.” 2

Jikin Hamama ya yi sanyi, Mai-jidda ta san duk don ta gwada mata matsayinta ne, ta yi hakan, ba ta san duk wannan bai dameta ba.

Ko da suka tashi tafiya, kayan biki tirim! Mai-jidda ta warewa Hamama, ta sa mata a mota, don ita sai ran Litinin za ta koma Kano. Suna tafiya, ta koma dakinta ta samu Anty Fauziyya, wacce take kinshingide saboda gajiya. “Anty Fauziyya ke kam magana nake so mu yi, tun zuwa na maganar take cina.”

“Lafiya? Me ya faru?”

“Kin tuna Dan Kano da na ba ki labari?”

Anty Fauziyya ta yi shiru cikin nazari kafin ta tuno “Oh, mai sonki da ki ke ban labari?”

Mai-jidda ta sauke numfashi ta ce. “Eh, yanzu ya addabi rayuwata. (Text) ba su karewa, ranan kam cikin dare ma ya kirani saura kiris! Abdul-Aali ya ga wayar. Tsorona daya, kar ya ga irin sakwanninsa ya zargeni, shi ya sa na ke son fada masa komai ko me ki ka ce?” 3

Anty Fauziyya ta yi shiru cikin tunani sannan ta-ce. “Gaskiya tunda ya fara haka, gwamma kin fada masa ko don gudun zargi. Ko ba komai za ki wanke kanki.”

Ajiyar zuciya ta yi, ko me yake damunta da har da take son mutumin nan? “Shi kenan Insha-Allahu, ina komawa zan fada masa. Ba ki ga tashin hankalin da yake sani ba, yadda ki ka san wani aljani.”

“Allah ya sawwaka. Ba komai Insha-Allahu, shi zai san matakin da zai dauka, idan abu ya kasa, sai ki canza lambar waya.”

Hankalin Mai-jidda ya dan kwanta, bayan sun yi magana da Anty Fauziyya. Sai da suka taya Umma kimtse-kimtse, sannan kowaccensu ta koma dakinta.

Tana ta tunanin abin da zai biyo baya, idan Abdul-Aali ya ji labarin Dan Kano, ko dai ta yi shiru ne kawai ta canza lambarta? Kayya! Idan ya samu a wani wuri fa?

Tana tsakiyar tunani ne, ya shigo dakinta, ya samu Muhammad ya yi barci a kan cinyarta, ita kuma ta yi nisa a tunani, ba ta ji shigowarsa ba ma. Ji ta yi kawai ya daga Muhammad, ya kwantar da kyau, sannan ya-ce. “Jidda…”

Da sauri ta firgita. “Na’am”.

“Lafiya kuwa me yake damunki ne kwanan nan?”

Wannan ne lokacin da ya kamata ki fada, ta yi tunani a ranta. “Daman akwai maganar da na ke so, na fada maka ne.”

“Shi ne duk ki ka jeme, ki ka shiga damuwa?”

“To ai ban san yadda zan yi na fara fada ba, kayi min alkawarin ranka ba zai baci ba, idan na fada maka.”

Kallonta yake yi sannan ya-ce. “Ina jinki menene?”

Riko hannunsa ta yi suka koma falonta, nan ta soma ba shi labarin Dan Kano, tun daga bin ta da yake yi a mota, kafin aurenta, har wayar da yake mata har dawowarsa rayuwarta, da kuma rabuwarsu da abin da ya soma yi yanzu. Ga mamakinta, ji ta yi ya kwashe da dariya. 2

STORY CONTINUES BELOW


“Dadin Mimie dariya na ba ka?”

Ya tsagaita ya dubeta. “Jidda, ba dole ki ba ni dariya ba?” Ta yi fici-fici da idanu tana kallonsa, ta rasa meye abin dariya a labarinta kaf! “Haba Jidda da dai na zaci you are smart Yaya za ayi ki dauka Dan Kano da gaske yana existing? Meye marabar Kano da Dutse da har ayyuka za su hana shi zuwa wurinki, idan har da gaske sonki yake yi?”

Ita ma kanta ta ga wautarta, “To kana ga na yi hauka ne, na ke ganin sakwanninsa a wayata? Idan baya existing, yaya ake yi na ke ganin sakwanninsa, na ke kuma jin muryarsa?”

“Wannan kuma wani ne kawai, hala yake miki wasa da hankali.”

Mai-jidda ta ji ranta ya baci. “Ba wani wasa da hankali, ni na san me na ke ji idan muna magana. Kai dai kawai haushi ka ke ji, saboda kana ga shi na ke so, ba kai ba.” Ta fada a shagwabe.

A lokacin ne ran Abdul-Aali yayi matukar baci hankalinsa ya tashi, me yake kallo, yana zaune da matarsa tana son wani? Kunar furuncinta ya zaburar dashi amma ya tuna ya mata alkawrin zai saurareta ba tare da ya bata rai ba. Don haka ya sauke numfashi sannu a hankali.

“Ko ba gaskiya na fada ba?”

“Ke dai kina da allergy da ni, kuma ko za ki yi yaya, duniyarki da tawa a hade take, ba ta rabewa.”

“Allergy?”

“Allergy da soyayyata, ba kya iya bari ta shige ki bare ta nuna a jikin ki, ko a zahiri ko badini.”

Ta kasa gane abu guda da Abdul-Aali yake fada. “Yaya aka yi? Ki fada min wani abu guda da zai yi Proving shi mutum ne kamar kowa, meye sunan sa?”

Nan ta fara inda-inda, tunda ko sunan sa bata sani ba, ita wace irin wawiya ce da ko sunansa ta kasa sawa ya fada mata, duk tsawon lokacin nan.

“Ban sani ba, amma dai wannan ba shi zai sa kace ba da mutum nake magana ba.”

“Kina jin me kike fada kuwa?”

Tsumewa tayi hade da harde hannu a kirjinta, da kankance idanu tana dubansa “Naga ma abun nan kaman bai dameka ba, nima maganina da na fada maka.”

“See you, ki dubeni dai cikin idanuna don baki da kunya kina fada min wai wani kike so idan yana existing da gaske ina Kano ina Dutse da bai taba zuwa ya ganki ba?”

Wayarta ta mika masa wurin sakonninta ya karanta da idanunsa, hankalinsa ya tashi sosai. Ranshi ya baci matuka sai dai ya rasa yanda zaiyi da wannan fushin, abu daya ya sani shine cewa matarsa tana sonshi komin yanda taso ta kaucewa hakan kuwa. Kuma shima yana sonta, kuma ya yarda da ita fiye da zaton shi. 1

Domin kuwa da wata ce ko kuma da bai yarda da ita ba a yanda yake jinsa a yanzu bai san me zai aikata ba. Sanin cewa Jidda tasa ce yasa hankalinshi a kwance ya nisa, lokaci yayi da zai cire damuwar Dan Kano a gidansa.

“Jidda, ko ta wani hali na fito miki NI KIKE SO, haka ni ma KE NAKE SO, saboda duk son da ki ke yiwa Dan Kano.

Kin danne shi saboda hakkin igiyar aure a kanki, kin nuna soyayyar mijinki, da yake zahiri ya doke na wanda ki ke yiwa waninsa a badini, so you truely do love me.”

Da sauri ta ja da baya cikin tsananin razana da mamaki,”Kana nufin kaine Dan Kano?” 2

Bai san me zai tarar ba amma ya runtse idanu ya bude sannan yace “Ko me kika ce Hauwa?”

Bugun zuciyarta ce ya karu, yau ta ga ta kanta ba wanda ya san Dan kano Hauwa yake kiranta sai ita. 2

Inna-Lillahi’wa-Inna-Iilaihir-Raji’un! Abdul-Aali ne Dan Kano, yau ta shiga uku, tana son mijinta badini, tana tunanin sa wani ne daban, ba tare da sanin cewa shi take zama da shi ba. 1

STORY CONTINUES BELOW


“Amma ka cuceni, duk wannan lokacin kai ne Dan Kano, shi ne ka ke wasa da hankali na?”

Murmushi yayi mata sannan ya-ce. “Idan ba za ki so Abdul-Aali a zahiri ba, ai za ki so shi a badini. ” Ya fada hade da lakace mata hanci. 4

Kasa ta yi da kanta sannan ta-ce. “Yaya ka ke son na yi? Kai ka kirkire shi, ka ci gaba da ja na ka yaudareni har na fada cikin son shi, kai ka kirkiri damuwar da kanka, meye laifina? Don na fada wannan tarkon?”

Wani abu yaji ya damke shi a kirji cikin jin ciwon kalamanta. Tabbas mutumin can ya masa barna ko ma wanene, shi ya hana Jiddansa sake zuciyarta ta amince da shi tun a karo na farko. 3

Tun ganinsa na farko da yayi mata a Dutse da ya raka yaya Rayyaan wurinta, duniyarsa ta dauke wuta domin kuwa farat daya yaji ta shige masa zuciya, ya mance mai ya kawo su, ya mance wa ya rako, ya mance matsayinsa a wannan yanayin shi dai fararen idanun Jidda kawai yake gani, da kyawawan hakoranta masu dauke numfashi idan tayi murmushi.

A take a nan yasan ya kamu da son Jidda, abun da bai taba faruwa dashi ba, kullum yana boyewa ‘yan uwansa akan ya samu wacce yake so. Sai gashi ya samu wacce yake so da gaske amma yayansa da yafi so yana sonta kuma itama shi take so.

Wannan yasa ya yankewa kanshi barin duk wata mu’amala ko wani hulda da ya san zai hadasu, amma a rashin saninsa duk lokacin da ya nisantar da kansa daga Jiddansa iya tsananin tsumuwan da sonta keyi a zuciyarsa.

“Ina so a karo na farko ki fada min da kanki, kina son Abdul-Ali?” nan take ya samu kanshi da yi mata wannan tambayar domin he really needed to know, dole ya san wannan.

“Kina son Abdul-Aali a matsayinsa na Abdul-Aali? Kina sona as a person, ko a matsayin Dan kano, ko a matsayina na mugun mijinki mai sace ki, ko wanda bayi da sassauci, ko mai zuwa miki a mafarkinki, ko…” Sauke numfashi yayi yana dubanta.

Shiru tayi tana kallon wani intense kallon da idanunsa suke zubo wa nata kwayan idanun, ji tayi kaman numfashinsa ya canza sauti, tamkar abunda yake matukar son ji kenan kafin ya samu daidaituwar numfashinsa.

Lumshe idanu ta yi sannan ta-ce. “Kwarai kuwa, ina sonka. Ko kana tantaman hakan ne?”

Hancinta ya ja.

Sannan ya hada goshinsa da nata cikin ajiyar zuciya. Hawaye yaji sun cika masa idanu, amma bai bude idanunsa ba bare ta gansu. Ya san ko ba komai Yau soyayyarsa ta kafu cikin jini da zuciyar Jiddansa.

A hankali muryarta ta dawo dashi duniyar da suke a lokacin

“Wato shi yasa kake kirana da hidden number don kar naga lambar ka ko? To me yasa daga baya bana samun daya layinka?”

Shiru yayi cikin nazari sannan yace “Na bar UK a lokacin so bana amfani da wancan lambar.” Fatansa daya Allah Yasa gajeren lissafin da yayi a kanshi yayi daidai, karantar kyakkyawar fuskarta ya koma yi. 3

Yana matukar son Jidda, kuma duk wani farin cikin rayuwa zai iya damka mata shi idan yana cikin ikonsa wannan yasa a wannan lokacin yaji ya tsani kansa da mata karya da yayi amma ya zamo lallai, wayarta kawai zai canza mata koda asalain ‘Dan Kano’ zai sake kuskuren tuntubarta, amma ya zamo lallai ya san ko wanene wannan mutumin. 6

Ta yi shiru tana tuno abubuwan da ta taba fadawa Dan Kano, nan ta rufe fuska ta-ce. “Wallahi sai na rama, ka cuceni da yawa, shi ne har da wani kirana ranar muka yi hira, bayan ka san Mamin Mimie tana nan a falon Mama.”

Ya tuno lokacin da yazo shiga dakin maman yajita a kan waya har Hamamatu na mata tsiya, radadin da ya samu kanshi a wancan lokacin ba a magana, hakan ya sa ya hana kanshi fita daga dakin a lokacin ji yakeyi da za a daura musu aure a lokacin tsabar baya son ya bawa wani ma daman sake kalla masa ita bare yaji zazzakar muryarta dake ziyartar mafarkansa.

Murmushi yayi yace “Ba ki san yadda ki ke driving dina wild ba ko? Ina ga har yanzu da sauran ki a daukar darasin soyayyar da na ke miki, shi ya sa.”

Kara ta saka tana zillewa “Na dauka na fahimta, ba sai ka gwada ba, na tuba.” Ta fada yayin da ya janyota jikinsa.

“Tsaya tukun, ina da tambaya guda.” Ta tsagaita dariyar da take yi. “Shin da gaske ka ke yi, za ka iya raba ni da Muhammad da ban aure ka ba?” 2

Fuskarsa ya yalwanta da murmushi ya-ce. “Jidda, koda zan rasa ki har abada ba zan taba ganin ki cikin-bakin ciki ba, don haka ba zan iya raba ki da Muhammad ba, na dai fada ne saboda kin san (You can’t blame a man for trying).”

Mai-jidda ta sauke ajiyar zuciya, wato dama duk barazana yake mata. Hmm sai a gaishe shi.

Wani dogon ajiyar zuci Abdul-Ali ya sauke, cikin godewa Allah da garin bashi labari Jidda ta furta sunan da Dan kano yake kiranta dashi. That was close! 11

********

Bayan wata uku suka nufi asibiti saboda Mai-jidda haihuwa ta taso gadan-gadan. Abdul-Aali banda sintiri, ba abinda yake yi, ya kasa zaune bare tsaye.

Sai ya ji ashe abinda ya ji a haihuwar Muhammad, sunna ne, saboda ya kasa zama ma ya ga halin da Jiddansa take ciki. Can kuwa Yaya Maryam ta zo ta shaida masa Mai-jidda ta samu baby girl.

Bai yi wata-wata ba, ana miko baby. Ya sa hannu ya karbeta, yayi mata addu’o’i, ba karamin dadi ya ji ba, da ya ga kamannin Jidda da baby din.

Dokin wannan haihuwar yake yi, tamkar lokacin aka fara masa haihuwa, ba abinda ya rage su da shi, komai a wadace. Hamamatu dai mamaki take yi. 1

Ganin irin bare-baren da Abdul-Aali ke ta yi, sai ka ce baida wasu ‘ya’yan. Su Mimie dai kaura suka yi side din Mai-jidda, saboda kallon baby.

Ran suna yarinya, ta ci suna Zainab, wato mai sunan Mama. Mabruka musamman ta zo suna, farin-ciki dai ba a cewa komai. Anty Fauziyya dai ba ta samu zuwa ba, kasancewar ita ma ta yi nauyi. 3

Hankulansu kwance Mai-jidda ta ki komawa PH, da haka, sai dai su su zo, hakan yayi wa Hamamatu daidai, saboda duk kyautatawar da take yi wa Abdul-Aalin idan yana gaban Mai-jidda, sai ya rinka wani bare-bare, na ban haushi, ita kuma ba ta jure ganin haka, amma suna nesa da juna, hakan ya fi mata sauki. 6

******
A wannan shekarar ne Abdul-Aali ya samu karin girma a wurin aiki, kwarai sun yi farin cikin wannan canji da aka samu. +

Mai-jidda tana ta shirye-shiryen tafiya umrah da Mai-gidan, kasancewar wancan shekarar tana da tsohon ciki da Hamamatu ya je, don haka ya-ce wannan karon da ita zai je. Komai da komai ya fito, don haka ranar tafiya kawai suke jira, don har Abdul-Aali ya taho da su Hamama Kano.

Ana saura kwana biyu tafiyarsu ne, har ta je Dutse ta yi sallama Abdul-Aali, ya-ce mata. “Jidda.”

Yadda ya fadi sunanta, ta san magana yake son su yi, don haka ta tattara hankalinta ta ba shi. “Daman ina son na fada miki fa tafiyar mu tare za mu yi da Hamama kasancewar Alhajinsu baida lafiya, an kwantar da shi, kuma a asibitin Jedda, za ta dubo shi, sannan mu yi Umrar. Already na gama sama mata visar ta da ticket.”

“Oh, Allah ya kara masa lafiya.” Ranta ya baci, don haka ba ta boye ba ta-ce. “Amma sai yanzu za ka fada min hakan, Dadin mimie?”

“Saboda ga yadda yanayin tafiyar ta kasance ne ai”.

“Amma ai ka samu damar yi mata Visa, ba komai, ku je kawai. Allah ya bawa Alhajin lafiya.”

“Yaya za ki ce haka? Tun farko ba da ke aka shirya tafiyar ba? Ba na son abu da rashin hankali, ko don Hamama za ta je, shi kenan sai ke ba za ki tafi ba? Ko ba jikin mahaifinta za ta je dubawa ba?”

“A’a Allah ya ba ka hakuri, ni ba nufi na ba kenan, kawai ku je tare, wata shekarar, sai ni na je, idan Allah ya bar mana rai da lafiya.”

Zai yi magana, ba ta saurare shi ba, ta wuce bandaki. Ai daman Hamama ta san da rashin lafiyar, me ya sa ba ta tafi ba, sai lokacin tafiyarsu, sannan za ta wani ce za ta je dubo Alhaji.

Sai su tafi har gaba da Jedda ma, idan ana zuwa. Haka ta fara shirin kwanciyarta, bayan ta duba Muhammad da Ummita a dakin da take amfani da shi. Ba ta gama hucewa ba, ya bugo wayarta, ya shaida mata. “Ke na ke jira fa.”

Duk da ranta a bace yake, ta dauki turare ta kara fesawa, sannan ta nufi sashinsa. Kallon ta yake yi, yadda ta hada rai, shigowarta don haka ya sake nasa fuskar. “Sarauniyar rigima, har yanzu maganar ce ba ta wuce ba?”

“A’a na nawa kuma? Ai ni kam ya wuce, sai dai wata kuma.” Dadin sa da Jidda komin fadan da za su yi, ba ta taba kauracewa kiransa, sannan muddin ta fito. 3

Ta fadi ra’ayinta game da abu, to ya wuce kenan a wurinta, ga ta da dan karen kishi. Don haka ya faye kiyayewa da lallaba ta, don kar ta faye tunzura.

Cikin rarrashi ya lallaba ta, ta amince za su tafi tare, yaran duk gidan Mama suka tafi, da Ummita kawai ta tafi. Ta so ace tafiyar su biyu suka yi ta, ta gwadawa Abdul-Aali irin kulawarta, amma kuma hakan ma bai baci ba.

Abdul-Aali yana ganin ikon Allah, don ba daman ya rike jakar wata, dole haka ya bar su da kayansu, ko kallo yayi wa daya, sai daya ta daure fuska, sai suka koma ba shi dariya. Baya dai yi a gabansu, asali nunawa ma ya yi bai san suna yi ba. 18

STORY CONTINUES BELOW


*************

Madina suka fara zuwa. Mai-jidda kuwa ranta fes! Musamman idan tana cikin masallaci, ba ta jin komai sai nutsuwa, ibada ta sa a gaba sosai, ganin haka ya sa Hamama ta rage yawon saye-saye.

Ita ma ta na dan daure zuwa masallacin. Duk lokacin cin abinci. Abdul-Aali ya kan zo ya same su su tafi tare, hakan ya sa suka dan saki jiki da juna kadan. Kwanansu uku a Madina, sannan suka wuce Makkah, suna sauke Umra, suka dunguma Jidda saboda dubo jikin Alhaji.

Gaskiya yana jin jiki. Mai-jidda ta tausayawa Hamama da ta ga ta sa kuka da ta ga mahaifinta, wannan ya sa ta fita daga dakin don ta ba su wuri.

Can sai ga shi sun fito da Abdul-Aali yana rarrashinta. Sun gaisa da Hajiyarta, ita kam nan ta-ce za ta zauna, sai ta ga jikin Alhajin, sannan ta same su a Makka.

Tunda suka koma, muddin suka yi dawafi, sai sun sa mahaifinta a addu’a. Kwananta uku a Jidda ta dawo, ta ce jikin dai da sauki. Sun yi aikin su cikin kwanciyar hankali.

Kwanan su goma sha biyu, suka dawo gida. Mai-jidda dai ta kara godewa Allah, da fushi bai hanata tafiya ba, don ta samu sa’ida, a ibadar da ta yiwo.

Dawowarsu da kwana biyu aka sanar da su Allah ya yiwa Alhaji rasuwa. Wannan ba karamin girgiza su ya yi ba duka. Anyi jana’izar sa, acan, sannan Hajiyarta da yayinta maza suka dawo gida. 2

Duk wani kulawa da support Mai-jidda ta gwadawa Hamama a wannan lokacin, haka take kula da yaran kaf! Idan tana gidan su.

Su Baba da Umma duk sun taho gaisuwar. Tabbas Hamama ta ji mutuwar mahaifinta, kasancewar ta shaku da shi sosai. Wannan ya sa Abdul-Aali ya tsaya mata sosai, saboda ta farfado daga wannan rashin da ta yi.

Ko da aka watse, daga taron gaisuwar, gaba daya jikinta ya mutu, ba ta tsammanin za ta sake koda dariya ba, saboda wannan rashin, amma cikin ikon Allah sai radadin abin yake raguwa a zuciyarta da shudewar ko wane lokaci.

Rasuwar Alhaji ya sa kwarai ta wa’aztu da al’amarin duniya, wannan ya sa kwata-kwata ta rage duk wani kyashin da take nunawa Mai-jidda, baran ma da ya kasance ita ke da mijin, yawancin lokuta sai hakan bai dameta ba.

Ta sabarwa kanta duk da duk wani lokacin da Abdul Aali zai je Kano, sai take jin zafi a ranta, ta daina daga masa hankali, ba kamar da ba.

************

Tana ta shirye-shiryen isowar Mai-gidan tun safe ba ta ga ta zama ba, ta gyare gidan tsab! Ko ina sai kamshi yake yi, yaranta duk a tsabta ce, ko wanne tayi masu kwalliyansu gwanin ban sha’awa.

Girke-girke kuwa ta yi su masu kayatarwa. Dan daidai yadda ba zai barnatu ba. Ka na ganinta, ka san hankalinta a kwance yake, ba ta da damuwa, sai ko wanda ba za a rasa ba, saboda yanayin rayuwa. Misalin karfe hudu mai gidan ya shigo.

Mai-jiddah tana jin shigowarsa, ta mike ta bude kofar falon, daidai lokacin da zai shigo ciki, ba ta jira komai ba, tai masa kyakkyawar tarba. Ajiyar zuciya ya yi ya-ce. “Kai My Jidda, wataran za ki tsayar min da zuciya fa, wannan irin kyau haka? iye, menene sirrin ne?”

Murmushi ta yi hade da sadda kai sannan ta-ce. “Hmm! Dadin Mimie, ba ka rabo da zolaya, wai ma tukun, ina ka baro min yarana?”

Komawa ya yi da baya, ya kallo fuskarta. “Oh ke kam ta yaran ki ma ki ke ko?”

“Afuwan, to sannu da isowa. Shigo tukun na dai ka huta da kyau, amma dole ka fiddo min yara an taba haka ne?”

Murmushi ya yi. Jidda ko ta riko hannunsa zuwa daki yayin da ‘yar jakarsa ta matafiya take daya hannun nata.

Kamshin da ya ji a dakinsa ne, ya haddasa masa son ya kwanta ya huta a cikin wannan ni’iman, amma kuma wasu ni’imomin suna jiran sa, domin kuwa cewa ya yi “Ban ga yarana ba Jidda, ina ki ka boye min su?”

STORY CONTINUES BELOW


“Kai ma ka san da sun ji shigowarka, ba sai ka gayyace su ba. Amma ina zuwa, ni ma na ji shirun ya yi yawa, idan ka ji haka, tabbas suna wani abin ne.”

Ta mike za ta nemo su Muhammad, amma sai ta ji ya jawo hannunta, ya maidoda ita jikinsa, fuskarta na dab nasa, ya sa hannu ya shafo fuskarta. “Ok, yara za su iya jira kafin nan, saurara ki ji yadda ki ka dimautani.”

Ai ko tabbas bugun zuciyarsa da karfi yake fita. Mai-jidda ko ta sunne kanta cikin kirjinsa, cikin jin kunya. Yana kokarin lalumo bakinta ne, suka ji motsin taba kofa, da sauri ta mike daga jikinsa ta-ce. “Young soldiers”.

Dariya ya yi ya-ce “Oya, tafi daga nan, ni ma bari na karasa shiryawa na zo.”

Cikin yanga da yaukin da ta san yana tabo zuciyar Mai-gidan ta fice, tana sane sarai idanunsa na kanta. A bakin kofa ta tadda M.R (Karamin Danta mai sunan marigayi). Ya dage sai dagelgel yake yi, yana so ya bude kofa. Dariya ta yi ta daga shi, sannan ta-ce. “Zo mu je mu ga me su Yaya suke yi. Uhm! 5

Ai kuwa tana shiga dakinta, ta sa salati. “Muhammad lafiyanka, me na ke gani haka?”

Dariya ya yi ya-ce. “Mama, Ummita ce ta-ce nai mata irin kwalliyarki, ita ma tana son ta yi kyau kamar ke.”

Mai-jidda ta juya ta dubi fuskar Ummita, yadda akai mata dumu-dumu da shi, da kalolin jambaki da su eye shadow. 2

“Huh! Muhammad, ina ka taba ganin namiji ya yi wa mace kwalliya?” Tissue ta zara ta fara rage mata maikon fuskar. “Ummita na, ke ma ki na da kyau yadda ki ke kin ji?

Ke Beatiuful Princess ce, kuma Princesses, suna da kyau din su, ba sai sun yi kwalliya ba, sai idan sun kara girma sosai-sosai, sannan sai su yi kin ji ko?”

“Mama sai na yi girma, na yi dogon tsawo irin naki, sai ni ma na yiwa Dadin Mimie na kwalliya?” 6

Mai-jidda kam kunya duk ya bi ya kamata, ko a ina yarinyar nan take jin wannan. Sai Allah “Eh sai kin girma, sai ki yiwa Prince dinki kwalliya. Mu je (Toilet), na wanke miki wannan yanzu.” Da aka wanko ta, sai da aka canza kaya, sannan ta-ce. “Mu tafi falo Dadi ya dawo.” Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya shigo har dakin ya samesu.

Da gudu suka je suka kankame shi, suna murna.

Ya daga su duka. “Wai-wai, wani yana cin tuwo da yawa. Ai Dadi ba zai iya daga ka ba Muhammad, ka zama soldier.”

Ummita ce ta shiga yi masa dariya. M.R kuma sai tafa masu yake yi, shi ma a dole ya gane ana dariya da wasa. “Me Mama ta tsaya baku, ku ka makale a daki?”

Ummita ta-ce “Dadi, ka san na yi kwalliya ta goge min, wai sai na girma na yiwa Prince dina, kamar yadda take yi maka kai ma?”

Abdul-Aali ya kallo Mai-jidda, suka hada idanu ta daga kafada ta fiddo idanu hade da daga gira. “What are you telling these kids? (Me ki ke fadawa yaran nan ne?)”

Ya tambaya cikin harshen turanci, saboda kar su ji, ai ko Muhammad ya yi caraf! Ya-ce. “She tells us nothing.” Ai gaba daya suka sa dariya.

Abdul-Aali ya rike baki cikin Mamaki. “Yi hakuri na manta ashe muna da bature a gidan, Dokta Muhammad Rayyaan ko?” 4

“Yawwa Dadi ashe ka gane.” Nan yaron ya mika masa hannu, suka tafa. Daga bisani suka koma falo aka zauna cin abinci. Sai da suka gama ne, ya fitowa kowa da tsarabarsa.

Mai-jidda ta-ce. “Nuna bambanci, ni ina tsaraba ta, wato yaranka ka sani ko?” Ta fada tana masa kallon tuhuma.

“Me ki ke sauri? Tsaraba kam naki ya fi na kowa yawa, ki jira kawai ki gani.” Murmushi ta yi. Da dare suka je gidan Abba suka gaishe su. Sai da yaran suka soma hamma, sannan suka koma gida kan a isa kam M.R da Ummita sun lula.

Su ta fara kwantarwa, sannan ta shiga wanka kafin ta fito ta samu Muhammad din ma ya sa kayan barcinsa, ya bi sahunsu. Murmushi ta yi ta gyara masu kwanciyarsu ko wanne a gadon sa.

Dan siriri na yara, yayin da M.R ke cikin mai zurfi (crib). Duk ta tofe su da addu’o’i, sannan ta koma dakinta ta shirya. Tana shirin fita ne, ta ga ya shigo ya tura kofar. “Kawai kuma sai ki makale haka ake yi ne?”

“Sorry, hidindimun da yawa, da fatan dai ba wani abin ka ke bukata ba?”

Wani kallo yayi mata ya-ce. “Wace irin tambaya ce wannan?”

“A’a to wai na ga ka shigo ne kuma…”

“Ba dama na shigo dakin matata, sai da dalili? To barci na zo yi, ko ba za a ba ni wuri ba?”

Dariya ta yi game da rufe bakinta da siraran yatsunta. “Yi hakuri, ai da dakin da mai dakin duk mallakinka ne, sai yadda ka yi da su.” Hannunsa ya sa ya zagaye ta game da rikota jikinsa yana shakar kamshinta. “Hmm! Na yi kewarki sosai.”

Da sauri ta juyo ta-ce “Dadin Mimie, ina tsaraba ta, kar ka zaci na manta”.

Ai ko ta samu kyakkyawar tsaraba. Sumbbatarta yayi da kyau sai da taji tamkar tana narkewa. “Ga tsarabar ki, ko ki na son kari, don ina da shi buhu buhu.”

“Ah, wannan coge ne.”

“Wannan din bai miki bane ko me? Ji ta dai tana wani abin nan…”

Hannu ta sa ta dan ture kafadansa “Ni ba na so”. Ta fada a shagwabe.

“Na fada miki, ki daina min karya, ni na san komai, idan za ki ware, ki ware ehem.”

Girgiza kai ta yi sannan, ta-ce. “Shi kenan tunda ka ce haka, na bada gari.”

Dariya ya yi ya ja ta jikinsa. “Ehem ko ke fa.”

***********

16/09/2015

Yana zaune cikin motarsa, kanshi ya dago daga jikin sitiyerinsa inda ya gama karanta sakonnin cikin wayarsa, kallon windon motarsa ya sake yi inda ya ga shigarsu cikin Mall din.

Daga ganin fuskar Hauwa tana cikin dimbin farin ciki gata zagaye da iyalanta. A zuwa yanzu ya kara tabbatar da cewa mijinta na matukar kaunarta. Kuma shima yanda ta ci gaba da rayuwarta dole ya ci gaba da tasa rayuwar, ya mance da ita.

Shekaru Tara… shekaru tara tun randa ya fara daura idanunsa a kanta. Barin Hauwa ba karamin abu bane a gareshi.

Amma ya zamo lallai ya kokarta yayi, domin kuwa yanzu rayuwar Hauwa ba tasa bace, wannan yasa ya bi sakonnin Hauwa wanda ya tura da wadanda ta turo masa yayi deleting daya bayan daya.

“Sai anjima Hauwa, a kullum na san ke mutumce ta daban mai tsananin shiga rai amma ya zamo dole na mance ki ko rayuwata zata zama daidai. Ko zan fuskanci matsalolin rayuwata na magance su. Kin shigo rayuwata a lokacin da nake taka wani mataki mai muhimmanci wanda yayi min sanadinki. Amma farin cikinki shine nawa…”

Karar shigowar waya ce tasa ya fita daga tunanin da yakeyi hade da kara wayar a kunnensa, daga wurin aiki ne.

“Engr. Sufyaan ana bukatar ganinka fa, it’s urgent. Maganar aquisition ne, ban san me ya faru ba amma kaman an samesu kafin mu. They’re backing down.” 3

“Ina kan hanya, just stall them. Ba mai kin tayin Sufyaan Barkindo Sajoh…” Ya sauke numfashi daidai lokacin da ya hango Siddiqa da yaran sun fito daga ciki inda suka shiga sayayya.

“…Ko ke Siddiqa.” ya fada a bayyane lokacin da yake rufe shafin Hauwa daga babin rayuwarsa. 4

LABARIN ENGR. SUFYAAN BARKINDO SAJOH DA MARYAMA-SIDDIQA USMAN na tafe in prints in sha Allah. 11

MAIMAITA TARIHI…

Dan Kano = Another Engr. but not Abdul-Aali, Sufyaan Barkindo Sajoh 21

So how was the reveal? 7

What’s your opinion about the book as a whole? 34

Brace yourself KNS is at #5 in romance today 😱

Alhamdulillah,

Allah knows you have a niche deep down in z bottom of my heart 2

Thanks for all the love.😘

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *