ABBAS CHAPTER 10

ABBAS








CHAPTER 10






Teemah kamar bata ji abinda mummyn ke fad’i ba taci gaba da rera kakanta ahankali kanta akan cinyoyinta.

Da mummy taga kamar Teemahn bazata yi magana ba sai ta sakeyin wata maganar da d’an d’agun murya tace ” idan zaki bud’i baki kimin bayani toh inkuma bahaka ba ki tashi kiyi tafiyarki” .

Daga haka mummy bata k’ara yin wata maganar ba illah ido data zubawa ‘yar tata tana kallonta.

Ahankali Teemahn ta d’ago kanta suka had’a idanu da mummy, take tausayinta yah kama mummy musamman yanda taga idanun Teemahn sun k’ara girma da jaaa, alamun rashin nutsuwa kaf sun bayyana agareta, sai taji sam bata kyautawa gudan jinin nata ba, bahaka yakamata tayi mata ba tunda bata ta6a samunta da irin laifin ba yakamata tayi mata uzuri, ita kanta sai ta rasa dalilin da yasa ta d’aukewa Teemahn wuta ma, amma yaxatayi, mutunci da darajar y’arta take son karewa bakomai ba.

Kauda kai tayi gefe daga kallon Teemahn, yayinda Teemahn ma tak’urawa hannayenta idanu tarasa me zata ce da mummyn, tanaso tayi mata bayani amma sam tarasa abinda zata fad’a.

Da ‘kyar ta daure ranta tafara magana ahankali cikin natsuwa.

” Mum……my kiyi hak’uri dan Allah ki yafemin , kar kiyi fushi dani, ni bansan wayeshi ba, last week na fara ganinsa nima, kuma duk ranar da…….dana fita saina ganshi, shine dakansa yafara zuwa k’ofar makarantarmu amma wallahi mummy ki yadda dani banta6a sauraransa ba yau d’inma bada son raina bane bayadda zanyi ne shiyasa natsaya………….daganan mummy dakatar da ita daga magana inda tace ” saurara yah isa”.

Tsawon mintina biyu kafin mummyn ta mik’a hannunta ta kamo na Teemahn yayinda hakan ya matuk’ar haskaka zuciyar Teemah tare da sanyayawa tasan ko ba komai hakan kad’ai da mummy tayi yana nuni mata ne dacewar mummyn nata ta d’an sauk’o daga fushin data keyi da ita……..

Mummy ne taci gaba da fad’in ” kina jina ko?

Da wuri Teemah ta d’aga kanta alamar ” ehhh tanajinta” wa mummyn.

” Waye mahaifiyarki?
Mummyn ta tambayeta tana kallon fuskarta.

” kece”.
Teemah ta bada amsa a sanyaye

” waye ya kamata yasan damuwarki da kuma walwalarki?

” kece mummy” 

” kina ganin zan iya ganin kin hau hanyar da bata dace ba in kuma barki akanta kici gaba dabinta? 

Kai Teemah ta girgiza tare da fad’in ” a ‘a “. 

Toh kin gani ko, ki fahimceni, ba ina nufin k’untata miki ko kuma takuraki  bane sam, bani da burin da ya wuce inga kina farin ciki Teemah sannan duk duniya babu wanda zaiso ganin walwalarki sama dani………amma banda ta wannan hanyar, har yanzu ke yarinya ce, da sauranki, banason tun yanzu ki fara wannan kule-kulen samarin saboda bashi da amfani. 

Story continues below


kuma ma baki san wani abu ba ayanda kike d’innan duk wani wanda yake ganin sonki yake da gaskiya toh iyayenki zai fara nema ba ya dinga bibiyarki yana tsaidaki a ko ina ba, me sonki bazai ta6a yi miki haka ba ki kiyaye kinji. 

Kai Teemah ta sake d’agawa alamar toh 

Sai mummyn tacigaba da fad’in
” daga yau karki k’ara kula kowa ki bari ko secondary school d’inma ki k’arasa ta tukunna kinji kafin nan ki,ga awancen lokacin ko auren kikace kina so babu Me hanaki.” 

‘Kasa Teemahn tayi da kanta dan k’arshen maganar mummyn kunya ya bata sosai. 

Daganan mummyn tasake mata hannu tare da fad’in tashi kije ki kwanta toh. 

Bata mik’e ba kamar yadda mummyn ta umarceta sai ta jefawa mummyn tambaya kanta ak’asan batare da ta kalli mummyn ba tace
” shikenan kin huche mummy” tana murmushi tayi maganar. 

Mummyn ma murmushin tayi sannan tace mata ” zan huce dai idan naga kin kiyaye maganata”! 

” da sauri ta tashi tana murna har hak’oranta na bayyana afili tace ” insha Allahu zan kiyaye mummy” 

“Allah yasa ” kawai mummyn ta’kara fad’i tare da yun’kurin mik’ewa da niyyar shiga bayi. 

Teemahn ma hanyan fita tayi tana jin ranta fari k’al ” Mummy sai da safe ” tace wa mummyn tana tafiya ahankali. 

Mummyn ma na gab da shiga bayin ta amsata da ” Allah ya bamu Alkhairi”. 

Koda mummy tagama uzurinta tafitoh ma zama tasakeyi abakin gado tana tunanin hali irin na zamanin yanzu, daga k’arshe addu’a tayiwa ‘yarta akan Allah ya kareta ya rabata da sharrin masu sharri yarabata da soyayyar wahala da duk wani al’ummar musulmi. 

Dan wannan soyayyar wahalan ita tafi lalata al’ummah yanzu, sai kaga matashi ya 6ata lokacinsa da dukiyarsa akan yarinya zai nuna mata so tamkar ya had’iyeta in akayi rashin sa’a itama yarinyar sai ta fara masa mahaukacin so inda wannan son da ta fara yi masan in ba sa’a ba sai ya zame mata abin dana sani agaba. 

Domin dashi samarin yaudara suke anfani su lalata tarbiyar yara at last kuma su guje su batare da sun aure sun ba. 

Shiyasa ita tun da idanta yaga ‘yarta tsaye da wannan saurayin hankalinta yagagara kwanciyah bawai dan Teemahn bata kai ta tsaya da saurayi, bane a’a kawai dai in so samu ne yazo gida su gana da mahaifinta kafin nan, inda hakan yayi bazata ta6a jin yayi ba dai dai ba ko kuma tayi fargaban ke6ewarsa da y’arta. 

( ALLAH YA RABA AL’UMMAR MUSULMAI MUSAMMAN ‘YA’YA MATA DA MUGAYEN DAKE CIKIN MAZA,SUMA MASUYIN HAKAN ALLAH UBANGIJI YA SHIRYE SU.). 

Mummy bata samu tayi bacci da wuri ba aranar dan sai yanzu ta k’ara tunowa da halinda rayuwa take ciki a yanzu, sai ya zamana tana kwance ne amma baccin gaba d’aya ya k’aurace wa idanunta, duk juyin dazata yi kuwa sai ta jefi ‘yarta da addu’an kariyar ubangiji haka har kusan k’arfe biyu kafin bacci 6arawo ya saceta. 

Yayinda Teemah ke can ad’akinta tana ta kwasan bacci cikin kwanciyar hankali, tun lokacin data ga murmushi a fuskar mummynta tajita wasai shiyasa koda ta dawo d’akinta cikin farin ciki tayi addu’a ta kwanta dan bata tare da wata matsala a yanzun tunda mummy ta huce. 

*****
Tun daga wannan lokacin Teemah ta dinga kiyaye had’uwar su da wancen gayen, bama shiba duk wani wanda ya nemi ya tsaya da ita ko wani abu daban kyakykyawan kallo ma baya samu ballantana kuma lokacinta gaba d’aya. 

Haka saurayi Imran ya gama iyah biye-biyen da zai yi mata dayaga bata da niyyan sauraransa sai ya hak’ura ya daina kulata dama shima bawai son nata yakamashi sosai bane Imran irin samarin nan ne wad’anda a duk inda auka ga yarinya sai sun kulata musamman ma idan ta birgesu , sai Allah ya taimaki Teemah tak’i sauraransa hakan ne kuwa ya ku6utar a ita daga fad’awa tarkonsa. 

Tsabar yanda take kiyaye wa ma saboda kar ta ringa had’uwa da kowa ciki kuwa harda imran yanzu kwata-kwata ta daina zuwa ko’ina, duk  dayake dama itan ba gwanar yawo bace, daga makaranta sai islamiyah, toh su d’inma yanzu bata fiyah zuwa ba, kasancewar ta gama karatun ta yanzu muraja’ah takeyi da kuma gya-gygyara haddanta, boko kuma tunda aka mata registern weac sai ta daina 6ata lokacin ta wajen zuwa, tana d’an zuwa amma ba kullum ba sai ranar da taga dama tukunna take zuwa, kuma ko zata je d’inma amota ake kaita akuma je adawo da ita gida bata ta6a yadda ta matsa ko’ina batare data hango motar gidansu ba tana fitowa kuwa babu 6ata lokaci sai cikin mota. 

Wannan dalilin ne yasa ganinta yayiwa imran wahalar gaske shiyasa dan dolensa badan yaso ba ya hak’ura da ita. 

Mahmud kuwa kusan duk sati sai yazo musu week end inkuwa be samu yazo asati d’aya ba toh satin gaba sai yazo ko kuma alokacin da ya samu dama koda ba week end bane sai yazo, kamar de yadda wannan weekend d’inma ta wuce basu ganshi ba haka nagaba ma. shiru gashi kuma gurin babu network me k’arfi ko sun nemeshi bazasu ta6a samunsa ba. 

Sai da yayi kusan 3weeks kafin yasamu dakyar yazo shi gida sai kawai suka ganshi tsulum kamar anjeho shi. 

Mummy da Teemah na zaune Teemah na gyarawa mummy farce kawai sai suka ji sallamarsa. 

Aikuwa dukkansu bak’aramin farin ciki sukayi da zuwan nashi ba ji sukale kamar sun shekara ne basu ganshiba. 

Koda mummy tayi masa complaint akan rashin jin nasa dasu ba d’in sai ya bata hak’uri tare dayi mata bayanin rashin network d’in da suk ke fama dashi amma yace yakusan barin wajen ma zai dawo gida inyagama abinda yake yyi acan d’in yanzu zai dawo gida inyaso duk sanda aka buk’ace shi sai ya je shi. 

” sosai sukaji dad’in hakan dayace d’in musamman ma mummy saboda dama tafison ya zauna agida ko dan saboda insecurityn da ake d’an fama dashi alokacin amm shi Mahmud d’in yak’i yadda da hakan yace shidai yana son zuwa k’auyen. 

Haka suka cika masa gabansa da kayan ciyeh-ciyeh dan acewar mummyn wai rama yayi sosai kamar bashi ba dan ya bud’e ciki yaci abinci ko zai warware tace idan ma yak’i dawowa wannan karon kam dakamta zata je k’auyen ta dawo dashi gida ta k’araseh da fad’in ” hab irin wannan wahala haka. 

Dariyah sukayi mata shida Teemah mummy kuwa sai ta tashi tana mita ta barsu awurin. 

Teemah dakanta ta rink’a bashi labarin, imran lokacin da suka fita yawo dashi, shikuwa yayi ta kwasan dariyah yana fad’in village girl toh haka akeyineh ke,? 

“Gaye ya dage yaga ‘yan mata sai kuma kika kwafsa bai san dama da ‘yar k’auye ya had’u ba.” 

Turo baki Teemah tayi gaba tace ” nice y’ar k’auyen ko yayah” . 

Shiru yayi yana gumtse dariya batare daya kalle ta ba. 

Kasa hak’uri tayi sai da ta k’ara cewa ” abinda ma naa fishi kyau” 

Dariya ne sosai yakama Mahmud Teemah kuwa sai ta kauda kanta gefe kamar zatayi kuka ta tsani wannan dariyar har ranta sai da yagama dariyar sannan yace 

” sorry lil sis wasa nake miki ai shine babban d’an k’auyen ma “. 

Ko kulashi k’inyi tak’ara yi har suka koma gida sai da mummy tasa baki kafin suka shirya. 


Shak’uwa ce sosai tsakanin Mahmud da Teemah fiyeh da zaton me karatu, sai dai compared to shak’uwar dake tsakaninsu ayanzu toh wancen nabayan ba komai bane. 

Tun da Mahmud ya tattaro yadawo gida shikenan Teemah tasamu d’an uwa, aboki kuma yayah, batada da matsala ta kowani fanni, sosai Mahmud yayi k’ok’ari wajen ganin ya gina zumunchi mai k’arfi a tsakaninsu and he win. 

Yakan 6ata lokacinsa sosai wajen ganin yah koya mata karatu musamman dayaji labarin zata zana weac ashekaran, sosai shima yaji dad’in wannan labarin dan Teemahn kam masha Allah akwaita da saurin girma.

Haka idan suka fita yawo sukan 6ata lokaci sosai suna zaga gari, dan Mahmud ma ba de son yawo ba sai akayi sa’a kuma itama Teemahn gwanar son yawo ce shiyasa bakinsu yake yawan zama d’aya dashi. 

Ko sabon saurayi Teemah tayi ko kuma irin wani ya nemi yin magana da ita d’innan toh tare suke raina musu hankali da Mahmud d’in. 

Wani lokaci idan ya tsare ya 6atarai yana masifah har zakayi rantsuwa akan ehh lallai akan gaskiyarsa yake masifahn nan kuwa duk yanayin hakan ne saboda Teemah tu,da ya lura batason hakan shima sai ya biyeta. 

Axuk lokacin saza’a mata magana toh nuna sukeyi kamar wai ai they are already married, ma’ana matarsa ce, wani idan yaji hakan sai yabshi hak’uri yawuche abinsa, wani ko k’in yadda yakeyi da hakan sai ya k’aryatasu tare da k’ara dagewa akan shifah lallai sonta yakeyi kuma da aure. 

Idan kaga Mahmud na masifah wa saurayi akan Teemah toh baya rasa nasaba da k’in yadda da saurayin yayi akan cewa Teemahn matarsa ce. 

Haka zai dage yayi ta bud’e ido yana masifah Teemah kuwa sometimes dariyah ma yake bata amma bazatayi dariyar ba dan kar agano su. 

Sai idan su, ke6e ko kuma su shiga mota sannan sai tafara dariyah tana kwatanta masa yadda yayi alokacin dayake masifan, shima tayata dariyar yakeyi suyi tayi dayake suda kansu sunsan abin dariyar sukeyi. 

Akwai ranar da wani yabiyo bayansu har k’ofar shiga gida, da Mahmud yaga kamar binsu akeyi sai yayi parking shima atare suka fito da me binsu d’in sai kowa ya tunkari d’an uwansa da mabanbantan manufah.

Mahmud shi damuwarsa yaji dalilin binsun dayakeyi yayin da d’ayan kuma yake burin son magantuwa da yarinyar daya gani d’azu tashiga motar.

Fitowan da Teemah tayi ne ya d’auke hankalin mutumin daga kallon Mahmud ya mayar dashi kan Teemahn,  ya wani k’ura mata idanu kamar zai cinyeta d’anyah. 

Lura da inda mutumin ya kai duba da hankalinsan da Mahmud yayi ne yasashi fahimtar manufan binsun dayatayi har zuwa gida. 

Sun had’u da mutumin amma sam hankalinsa yatafi wani wuri be ma san sun had’un ba may be shi de ya tsaya da tafiyar daya keyi. 

Story continues below


Ahankali Mahmud yajuya ya kalli inda mutumin yasa hankalinsa sai suka yi four eyes da ita. 

Da saurinta ta k’araso inda uake ta rink’e masa hannu da dukka hannayenta biyu yayinda take k’ok’arin 6oye fuskarta da rigar dake jikinsa. 

Dukkansu sai suka tsaya kallonta ganin tana k’ok’arin 6oye fuska ne yasa Mahmud d’ago idanu ya kalli mutumin dai dai shima ya kallo Mahmud d’in suna had’a ido dai Mahmud ya d’age masa gira alamar tambaya. 

Sannan yah furta ” hakalinka ya kwanta ko? 

” Kana ganin yanda ka tsoratar min da ‘yar uwa, meke faruwa ne? 

In ina mutumin yafara yanaso yayi magana amma yanda Mahmud d’i. Yayi masa magana sai yasa shi fargaban abinda yakeso ya furta d’in. 

” Dakatar dashi Mahmud yayi tare da d’agamasa hannu ” go straight to the point mr. man don’t waste my time here”. 

Haka de mutumin ya daure ua furta abinda ke cikin ransa nan kuwa Mahmud yafara masa bori kamar zai ari baki. 

” can’t you see that she is married?, how dare you said you love her? 

Karkata kai yayi tare da rik’e kunkuminsa sanna, yace ” owhh wato kune irin mutanen nan masu lalata tarbiyar al’ummah ko? 

Mutumin najin hakan ya rik’e baki tare da saurin bawa Mahmud hak’uri, yace shi bahaka bane manufarsa, kuma be masan da aurenta da bazai ma fara binsu ba balle har yayi musu magana, hak’uri sosai yayita bawa Mahmud kafin yajuya yakoma cikin motarsa yaja yayi gaba. 

Har yaja moitar tasa Mahmud natsaye ayanda yake yana binsa da idanu sai da ya daina hango motar kafin ya juya kad’an ya kalli gefensa inda Teemah ta k’ank’ameshi yace “ke sakeni” 

Ahankali tad’ago kanta dataga mutumin bayanan kafin ta sakeshi gaba d’aya.

Cemata yayi ”  miye hakan wai kikeyi naga harda su 6uya? 

” wallaho yayah tsoro yabani ni yafiyeh kallo dayawa” 

” Daga kallon kuma fah? 

tace ” shikenan” 

“Hmm,Toh ke nakasa ganewa haka zaki tazama ba saurayi ne? naji fah daddy na cewa aurar dake zaiyi daga kin k’are secondary school ke kuma sai sani kike ina ta kore in- laws d’in nawa.” 

Dariya kad’an tayi tace” kai yayah harda wani in-laws? 

” ehh mana,musammam ma wannan duk yafi birgeni wallahi da alama zai so ki da gaskiyah gashi ba laifi harya d’an fiki ma kyau ya k’arasa da zolaya. 

” haba yayah ahakan nidai wallahi be fini kyau ba….. , 

” toh naji yah isa wasa nake miki ai daman ki, fishi kyau waneshi ya kamo lil d’ina kyau.” 

” amma ai de shid’in yah miki ko” 

Dawuri ta jijjiga kanta tare da 6ata rai tana tura baki. 

” mekenan” 

ya tambayeta 

” nidai banaso….. 

“Sauran fah toh ? 

Yasake tambayarta 

amsa shi tayi da fad’in ” dukkansu”! 

Ido yah zaro waje yace ” babu wanda ya miki? 

kai ta d’aga alamar “ehh” 

” ta6 lalle kam”.
Haka kawai yace tare da jajjiga kansa alamar mamaki sannan yasake kallonta “ki shiga gida barin shigo da motar sai mu k’arasa maganar agida ko? 

” uhm tace tare da juyawa ta tura k’aramar ‘kafar dake jikin gate d’in gidan tashiga ciki. 

Shima sai yaje ga motar ya tayar tare da danna horn take kua axka bud’e gate d’in yatura motar yashiga yanayin parking yafito yasameta a inda take tsayuwan jiransa. 

” muje “

Yace mata atak’aice tare da nufar k’ofar dazata sada su da babban parlourn gidan.

Baifi taku uku yayi ba yaji yo muryarta ta k’ira sunashi a hankali.

Tsayawa yayi tare da waiwayowa ya kallota ” ya akayi” ya jefa mata tambayar agajarce

” fishi kayi danine yayah?

yanajin abinda ta fad’a ya juya yafara tafiyarsa sannan yace ” ba dole nayi fushi ba, lil sis k’arfi da yaji kin maida ni babban mak’aryaci a gidannan.”

Daga yadda yayi magana ta fahimci babu wani fushin dayakeyi da ita kawai dai ………

Garin saurin ta taroshi sai k’afanta d’aya yad’an karkace aciki. High hill d’in dake k’afar tata bata ji ciwo, komai ba amma sai tace wash tare da rage tsawo ta kama k’afar kaman dagaske ciwon taji.

Aikuwa dawuri Mahmud yadawo yana tambayarta ” menene ya faru?

” yar k’auye kawai yanzu dan wannan takalmin ne shine harda fad’uwa?

Abinda yace kenan bayan ya fahimci dalilin wash da kuma durkuson nata .

Hannunta yakama ya mik’ar da it tsaye,sannan yace cire takalman ki rik’e ahannunki tunda mun iso gida, bazanma k’ara siya miki irinsu ba tunda kin kasa iyah koyan tafiya dasu har yanzu.”

Gaba tayi tafara tafiya tabarshi agun sannan tace ” ni ba abinda yasameni dama so nake ka jirani”.  

” kut lalle Yarinyar nan” yace tare da mik’a hannu kamar zai kamota ita kuwa sai ta kwasa da gudu tayi ciki shima sai ya bi ta abaya.

Mummy na zane kawai taga mutun tazo kanta da gudu ta ruk’unk’umeta kafin tana k’ok’ari, yin magana kawai sai ga Mahmud ma yashigo kamar yanda Teemahn ta shigo.

Salati mummy tasake tare da fad’in ” wai meke damunku ne wai?
Haka ne sallamar ?

” kyaleta mummy Allah yarinyar nan tarena ni sosai.”

tana daga jikin mummyn tafara fad’in

” bawani mummy niban raina shiba kawai dan na……..

Kafin taka’arasa mummy ta buge mata baki ” kubb”
yimiin shiru ni”.

Sosai taji zafin hakan aikuwa take idanta yai jah kamar zatayi kuka Mahmud kwa mezeyi inba dariyah ba, haka yatashi yafice ad’akin da sauri yana kwasar dariyah.

Teemah kuwa gefe tayi tayi zugum tarsa meke mata dad’i.

Sai da ta daina jin zafin kafin ta tashi ta wuche d’akinta.

Tana shiga tamik’e agadonta tana shan iska bayan ta rarrage kayan jikinta.

Waya taji na vibrating ad’akin nata gaba d’aya sai tarasa takamamman inda k’arar ke fitowa har k’iran ya yanke bata samu inda wayar take, vibration d’in ne yasake tashi akaro na biyu kuma sai asannan ta tuna wayar Mahmud dake cikin jakar ta wanda tafita dashi d’azun.

Ai da gudu ta tashi taje ga jakar taciro wayar “AUNTY” tagani arubuce akan fuskar wayar, k’iran na gab da yankewa tayi recieving ” hello” tace ahankali.

Dan tunda ta fahimci me k’iran sai taji gabanta ya fad’i shiyasa ma ta amsa asanyayeh.

” shiru taji ta d’ayan 6angaren hakan yasa ta k’ara furta “hello…..d’in akaro biyu tana shirin yin na uku ne taji an amsa mata da

” keh dan ubanki kyaleni ni!”
” ina mai wayar” 

” asanyayeh ta amsa mata da ” kiyi hak’uri Anty bari in kai masa.”

” ‘duut”
Taji wayar ya yanke sai ta dafe k’irji da hannunta d’aya saboda yanda taji bugun zuciyarta na k’aruwa komawa tayi ta kwanta rigingine tana ayyah na hali irin na wannan matar data rasa dalilin tsanar datake yimusu wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan.

Ahankali tatashi dan ta kaiwa Mahmud wayar sa, cikin sa’a kuwa sai suka had’u da Mahmud d’in yazo ansan wayartasa.

Mik’a masa tayi kawai tajuya ciki shikuwa sam be damu ba saboda azatonsa tun fushin d’azu nake bata sauk’o ba.

Haka yajuya yayi tafiyarsa zuwa d’akinsa,yana shiga d’akin kuwa yana shirin ajiye wayar sai yaga Anty ta k’irasa.

D’auka yayi tare da zama akan side drawer yayi receiving called d’in.

” Assalamu Alai….. ….

Kafin yak’arasa sallamar sai yaji tace
” wacce ‘yar iska kabawa wayarka Mahmud?

” kai Anty ‘yar iska kuma?,
” Teemah ce fah,yarinyar Anty….??

” shine ne me?

Shiru yayi be sake yin wata magana ba sai itace tacigaba da fad’in ” yaushe zaka dawo gida?

” ni kam babu rana gaskiya ” yafad’i akufule.

Itama dataji haushi sai ta fara yi masa masifah akan babu ranar dayace.
Wai saboda me ze ce haka, tsabar ya raina ta har tana tambayarsa ranar dawowarsa ko kunya wai baya ji zaice mata barana dan yaje ya tare agurin waccan munafukar, umarni tabashi akan cewa nan da 1week take buk’atan ganinsa a lagos koma ya zeyi ya neni hanya yazo tana buk’atan ganinsa.

Cire wayar yayi daga kunnansa kafin yakashe ta gaba d’aya ma ak’asan mak’oshi yake fad’in “baza’a zo bad’in”.

Mahmud be sanar da kowa yanda sukayi da mahaifiyarsa ba daga mummy har daddy babu wanda yake da labarin domin yadda ya yanke aransan cewa bazashi ba toh sam bai da niytar zuwan ne shiyasa yak’i sanar da kowa dan yasan mummy najin labarin zatayi convincing d’insa akan lalle sai yaje.

Hatta Teemah ma bata sani ba.
Amma yadda Antyn ke yawan tuntu6arsa awaya akan tafiyar kad’ai yasa mummy fahimtar wani abu game da shi.

Dan ayanda ta lura duk sanda zai d’aga wayar indai na mahaifiyarsace tana lura da canjin fuska atattare da shi matuk’ar akusa da ita yake.

Kuma ko minti nawa zai kai da wayar akunnansa bazaka ta6a jin yayi magana ba shiru kawai yakeyi yana sauraronta. Hkana kad’ai dayakeyi babbar alama ce dake nuni da wata matsalar azahiri.

A kwana na biyar ne ta zaunara dashi ta tambayeshi abinda ke faruwa domin walwalarsa gaba d’aya tayi low.

Aranar kama be 6oye mata ba haka ya zayyano mata duk yadda sukayi da Antyn tasa a tunaninsa ko Mummyn zata bashi shawaran da zata taimake sa.

Ai kuwa mummyn fad’a tayi masa sosai itama har kamar zata yi kuka, take fad’in me yasa zai yi haka, ai koma me Antyn ta buk’aci ya mata kamata yayi ya mata batare da musu ba kodan darajar ta na uwa agare shi.

Tace akan me zai 6oye yak’i yin bayani bayan yasan koma miye zai faru ko yafaru toh kanta abin zai koma tunda ahalin yanzun tare yake da ita.

Koma badan hakan ba tace ” mahmud mahaifiyar ka ce fah ai tafi k’arfin hakan, tafi k’arfin tace kayi abu kuma kak’i yinsa matuk’ar bai bar kan hanya ba toh dole ne kayishi koda kuwa ranka bayaso.”

Hak’uri sosai yabawa mummy tare da fad’in shi abinda Antyn keyi ne yafara isansa shi yasa yak’i zuwa amma insha Allahu zai shirya yaje shi d’in kamar yadda ta buk’ata.”

” Murmushi ne ya kwace wa mummyn take kuwa tasanya masa albarka tare da yi masa addu’a da fata mai kyau daga indallahi kana ta sallameshi dan yaje yafara shirin tafiya acewar ta gobe take so yawuche.

Haka Mahmud wannan karon ma ya shirya yatafi bada son ransa ba wani lokaci ji yake kamar yakai k’aranta wurin Abbansa dan yadda take takurawa rayuwarsa amma idan ya tuna cewa aikin banza zaiyi sai kawai yafasa dan ko da yafad’a d’in toh kamar yakai kukansa ne inda bazai samu biyan buk’ata ba koda kuwa kad’an, .ai san dalili ba amma shi wani lokaci ji yake kamar yana jin haushin iyayen nasa musamman Abbansa da sam baya fighting masa komai sai dai ya zuba masa idanu ko ya k’yale sa sai de inshi yana so ya yunk’ura, shi yasa yafi son zama awurin Antynsa Khadija shi aganinsa acan yafi walwala idan yana can sam baya jin cewa yana da matsalar komai.

*****
Lafiya lau ya sauk’a ,koda ya sauk’an kuwa be k’ira kowa yasanar da sauk’an tasa ba aidansu, wani friend d’insa yak’ira yazo ya d’auke shi yakawo shi gida, be ma shiga ba yajuya yakoma saboda akwai uzuri agabansa godiya kawai Mahmud yamasa sannan shima ya shiga gida.

Ahankali yake tafiyar tamkar bazaiyi ba hannunsa babu komai sai agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa, gefen kafad’arsa kuma ‘yar jakar da yake saka  kayansan da zai bukata inzaiyi tafiyane.

Haka ahankali har yak’araso k’ofar parlournsa, key hondern dake tare dashi yaciro ya lalu6i makullin da zai bud’e masa d’akin yasaka ya bud’e yashiga ciki.

Sake tura k’ofan yayi ya rufe abinsa tankar ma ba’a bud’e ba.

D’akin ma ashare tsab bawani datti dayake duk bayan kwana biyu Anty take sawa a share masa koda ma bayanan so bashi da matsala da wannan, kawai sai ya ajiye jakar kayansa tare da rage kayan dake jikinsa.

Bayi ya shiga ya watso ruwa tare da d’auro alwala yazo ya tada sallah ya rama wanda yawuche shi tare da sallatar wanda tagabato adai dai lokacin.

Yana idarwa ya d’auki wayarsa ya k’ira mummy ya sanar da ita isowanshin lafiya harma suka d’anyi hira da Teemah kad’an basu wani d’au lokaci ba yace mata bacci yakeji he need to rest, sallama tayi masa tace idan yatashi yak’ira zata bashi wani labari, ” toh kawai yace mata atakaice dan yasan babu wani larin da zata bashi k’aryace kawai da kuma son yak’iratan datakeyi. daganan ya  kwantaa bayan ya maida wayar a silent da niyyar kishingid’a, kamar wasa kuwa sai bacci ya d’auke shi suka tafi.😜

Antynsa bata san ya iso ba, kuma duk k’iran data ta yi masa aranar ko guda d’aya bai d’auka ba hakan kuwa bak’aramin 
6ata ranta yayi ba amma sai ta kyaleshi da niyyar duk lokacin data sameshi awaya sai taji dalilin hakan inma zigashi ake yi yamata rashin kunya toh duk zataji.

Bashi ya tashi ba sai da aka k’ira sallar maghrib,koda yatashi alokacinma sai yaji gaba d’aya kansa yamasa nauyi,hakan ya sa yad’an 6ata lokaci abayi yana cikin ruwa da kyar yasamu yafitoh.

Sallar maghrib d’in yagabatar tare da zaman jiran lokacin isha’i yacika itama ya gabatar da ita, baya son yaje masallaci su had’u da Abbansa ne shiyasa baije ba amma da farko harya yi niyyan zuwa sai fasa.

K’arfe takwas da rabi daidai tayi masa ne ak’ofar babban parlourn Anty.

Hannu yasa yatura ahankali tare da yin sallama ciki ciki.

Suna can wajen cin abinci dan haka basu ji sallamar tasa ba amma sunji k’arar k’ofan.

Jin k’arar dasukayi yin ne yasa suka maida hankulansu wajen k’ofar shiru sukaji babualamun mutun kuma domin daya shigo tsayuwansa yayi awuri d’aya shiyasa basu kuma jin motsinsa ba.

“Waye ne?
Abbah ya tambaya batare da ya mik’e ba.

Ahankali yah amsa da ” nii neh” kamar dole aka saka shi.

Suna jin muryarsa suka mi’ke atare suka nufo shi tare da ambatar “MAHMUD” alokaci guda.

” Mahmud kani da daren nan?
Abbansa ya tambaya cikin mamaki.

Kai ya d’agawa Abban alamar ehh 

Hannunsa yakamo suka koma gurin cin abincin dukkansu nan take Anty ta had’a nasa nasa plate d’in ta tura masa shima.

Dayake daman yunwa yakeji sai be wani yi yanga ko gardama ba ya bud’e ciki ya kwashi abincinsa sai da suka gama kafin Abbansa ya tambayeshi meyasa yayi tafiyar dare?

” bayanzu na zo ba Abbah”
Yabawa Abban nashi amsa .

Ido Abban ya ware “bayanzu babana tun yaushe kazo?

” Tun da rana”.

Salati Anty tasaka takama baki sanna tace ” yanzu Mahmud tun da rana ka iso amma kak’i zuwa inda muke sai yanzu”.

Abbane ya d’aga mata hannu yana murmushi yace ” pls barshi Maryam may be yagaji ne shiyasa……

” amma me yasa bazai ko sanar akan yana hanya ba…..

Anty ne tasake fad’in hakan.

Abbah kuwa cewa yayi wannan tsakaninku amma dai kibarshi kwa gama dasafe idan Allah yah tashemu lafiya”.

Juyawa yayi ya kalli Mahmud yace ” abana jeka huta sai da safe koh”.

Mahmud da tun d’azu yake zaune kamar mutum mutumi kallon Abban sa yakeyi da mamaki, domin yajima baiga Abbansa na irin hakan acikin gidansa ba, sai yau yaga Abbansa na dakatar da Anty akan abu kuma tayishi, sosai hakan yasashi mamaki matuk’a, shiyasa be ma ji abinda Abban ya fad’a da farko ba sai da Abban yasake maimaitawa kafin ya yi firgigi.
be san cewa addu’ar da mummy keyi akullum bane yafara tasiri akan Abban.

” meke faruwa ne ?
Aban ya tambayeshi.

“Ahh bakomai Abbah “

” toh maza jeka kwanta sai da safe”

Tashi yayi tare da sake yi musu sallama ya wuche abinsa.

Anty kuwa abin ne yafara yimata yawa domin ga matsalar Mahmud daya d’an d’au lokaci aranta tana tunani ta yadda zai yadda da batun auran Munirat, sai rana tsaka kuma matsalar Abbah ta kunno kanta kusan sati kenan tarasa gane kansa, gashi duk tarasa dalilin hakan.

Koda tayiwa Anty chideh magana kuma sai ta rink’a yi mata yanga kamar ma bata son zuwa.

Itakuma vagane gurin zatayi ba yanzu kuma bata son canja wa tagi son wancan wurin d’in dasuka yi mata aikin tun farko dan sosai ta yadda da aikin nasu.

Washe gari daya zo gaida iyayen nasa sai yace wa Antyn yanso me yakoma dawuri domin akwai aikin dake jiransa acan idan wani abu take so ya mata tafad’a dawuri sai yagama mata shi ayau dan yanaso yakaoma”

Antyn kamar bazata fad’a ba dan tsoron abinda zai biyo baya kar kuma tak’i fad’a yace yau yake son komawa tunda babu abinda zai mata, sam bahaka taso ba , taso su ka6e su biyu sannan suyi maganan musamman ma dayanzu yadda yakasance Abbansa na yawan yi mata katsalandan a abu shiyasa take tsoron fad’in abinda ke ranta a gaban idanunsa.

Tunanin hakan yasata ta bud’i baki badan ranta yaso ba  anan ta yada manufarta nasawa datayi yazo d’in.

Haushi Mahmud yaji sosai bayan yaji bayanan Antyn.

Dayake cewa tayi yakamata ya tsaida matar da sai aura kodan gudun lalacewar da duniya take ciki dan hakneta mtsa akan yazo gida domin su tsaida magana wuri d’aya.

Haushinsa d’aya ne dayaji wai duk wannan masifan data tayi masa d’in wai akan batun aure ne toh ni wama zan aura ?
Ya tambayi zuciyarsa.

Azahiri kuma murmushi yamata kana yace ” kwantar da hankalinki Anty, nibama yanzu na shirya yin aure ba gaskiya, shiyasa ma har yanzu banda kowa da muka yi batun aure da ita kinga kuwa ai da sauran lokaci”

Abbah ido kawai ya zubawa wayarsa tamkar baya jinsu amma kuma gaba d’ayan hankalinsu da kunnuwansa na gare su ne.

Anty ne h tasake fad’in cewa ” ai karka damu Akwai wata ‘yar k’awata……….
sai tadakata ta kallo Abban Mahmud d’in….

” mahmud aransa yace dama nasani ai” yayinda afili kuwa kallonta yakeyi kamar wanda tana fad’an maganar zai amince.

Gani tayi Abban Mahmud d’in sam hankalinsa baya tare da su sai tayi hamdala azuciyarta.

Daganan taci gaba da fad’in……

” yarinyar nada hankali Mahmud shiyasa nayi sha’awan kai ka aureta nasan baza’a samu matsala daga gareta ba bansan dai kai ba”

Takarashe maganan da yanayin tausayi.

Shi kanshi sai yaji tausayinta amatsayinta na uwa mahaifiya agareshi, idan har tana ganin bata da matsala da yarinyar toh why not shi data haifa kuma?

Batare da wani 6ata lokaci ba take yace mata gobe yake so ya koma amma insha Allahu kafin ya tafin zaije yaga yarinyar inyaso sai yabar komai ahannunsu.

Farin cikin da Anty taji tamkar ta goya shi haka taji kawai sai fara yi masa godiyah kamar wanda yamata kyautan wani abu.

Sai asannan kuma Abbah yayi magana inda yace ” ga dukkan alamu yarinyar tatafi da hanakalinki gaba d’aya ko?

Murmushi tayi amma bata yi wata magana ba dan karta 6ata plan d’inta tunda tasamu ya amince ai shikenan.

Da yamman ranan Anty ta had’a Mahmud da drivernta dayake ahi yasan gidan sai ta masa bayanin abinda zai kaisu gidan atsanake.

Fita yayi bayan sun isa ya bar Mahmud d’in zaune acikin mota shikuma yaje yayiwa Mai gadin gidan bayani take kuwa yawuce ciki yah isar da sak’on da aka bashi.

Minti goma mai kyau bata cika sai ga Munira tafito cikin shirinta na k’asaitacciya awurin iyayenta.

Riga tasa iya gwiwanta yakuwa yi mata kyau sai dai rigarasosai yakama mata jiki dayake roba ce da dogon wando daga ciki kanta kuma wani d’an k’aramin veil me tayane kanata dashi, tana tafiya tana karairaya dayakr dama tasan da zuwansa mahaifiyarsa tariga ta sanara tun kafin ma ya iso shiyada tayi masa shiri na musamman.

Tun daga nesa Mahmud ke k’are mata kallo yana karantar yanayinta.
Murmushin takaoci yayi lokacin daya fajimci yarinyar ya kuma tuno inda yafara ganinta,sam ba irin matan dayake ao ya aura ba kenan asali ma shi baiga wani abinso tattare da yarinyar ba tun farko dahar Abty take ganin dacewansu dashi.
Tsaki ne ya subce masa lokacin daya tsinkayo muryarta tana fad’in ” Hi “

Bai kulata ba sai ma kauda kai da yayi gefe kome yatuna kuma oho sai ya fito yazo tagabanta ta tsaya tare da folding hannayensa a k’irjinsa.

Gaishe shi Munirah takuma yi tare da yi masa iso zuwa cikin gida.

Bai amsa mata ba sai ma tambaya daya jefah mata nacewa ” wacece ita?

Murmushi tayi tare da fad’in ” ohh sorry” 

Sunana Munirah kuma nice wacce Mahaifiyarka ta za6a maka atsayin mata.

” oh really “
Yafad’a da sigar rainin hankali yana kuma murmushi.

Kallonsa ta tsaya yi domin afili zaka fahimci manufarsa koda baka da wayo balle ita.

” kinsan wani abu?

Idonsa acikin nata yayi maganar sai kawai ta jijjiga kanta dan sosai jikinta yafara yin sanyi.

” ko kad’an bakiyi min ba!

Sake matsowa yayi kusa da fuskarta yakuma fad’in ” kinsan dalili?

Da kai ta bashi amsa alamar ” a’a”.

Sai yace mata ” saboda ko kad’an baki dace dani ba”.

” Ki gayawa zuciyarki cewa Mahmud d’innan banaki bane, dan nasan wannan duk munafurcinki neh,ni kuma insha Allahu bazan ta6a auranki ba, mark my word.”

Yana fad’in haka yajuya ya shiga mota da gudu driver yazo ya shiga shima yatada motar suka fita agidan.

Har suka bar haraban gidan Munirah bata iya motsawa ba, mintina yakai uku ta k’ara bayan fitan motar tasu daga gidan kafin ta dawo hayyacinta, gefe da gefenta ta kallah taga babu kowa da gudu tayi cikin gida tana rusa kukan takaici bata zame ko’ina ba sai gurin mahaifiyarta.

Da k’yar tasamu Muniran tayi mata bayanin abinda ke faruwa ai kuwa take ta d’aga waya ta k’ira Anty tafad’a mata abinda Mahmud d’in yai wa ‘yarta.

Ran Anty ya 6aci sosai aganinta ai tozarci yayi mata, inbahaka ba yasan baya so mai yasa tun farko yace mata yaya yadda da batun auran sai da ta riga da ta sanar da su amincewarsa kuma sai yaje yaci musu mutunci har cikin gidansu?

Safah da marwa take tayi tana Allah-Allah ya dawo ahima yazo yasameta tunda shi bai san mutunci ba.

Mahmud kuwa k’in komawa gida yayi da wuri yace su wuce yawo acikin gari basu suka dawo gidan ba sai kusan 11pm beyi niyyan shiga ciki bama dan yasan had’uwarsu da Anty yau bazaiyi musu dad’i ba.

Bai san cewa Antyn tun d’azu gadinsa takeyi ba yayinda Abbah ma duk yake kula da ita batare data sani ba.

Tana jin tsayuwar mota kuwa ta fito da gaggawa ta tare shi alokacin yana gab da shiga d’akinsa.

Mahmud!

Tafad’a ranta a 6ace.

A hankali ya tsaya tare da juyowa daidai kuwa yaji sauk’an mari tasssss akan kuncinsa.

Ido kawai ya rintse ta re da bud’e wa ya sauk’e su akan Antyn.

” baka da hankali ne Mahmud , ni zaka raina ma wayo , so kake ta tozarta ni ko,wallahi akan wannan maganar bari kaji zamu matuk’ar samu matsala ni da kai matuk’ar kace bazaka bi abinda nakeso ba……….

“Uhm-uhm fah Maryam kar muyi haka dake, karki ce zaki takurawa yarona akan abinda bashida ra’ayi domin ni bazan lamunci hakan ba “.

Bazata suka jiyo muryar Abbah nafad’in hakan sosai k’irjin Anty ya buga dan bata ta6a zaton idansa biyu ba awannan lokacin.

Shi kuwa Mahmud har yanzu kallon Anty yake da mamaki, aransa yake k’ara jinjina hali irin na Antyn tasa yana ganin cewa lalle halinta sai ita, idan dai har zata iya d’aga hannu ta mareshi akan waccen yarinyar tun yanzu toh ashe idan ya aureta ma har zanashi zata ce zatayi idan ya 6ata wa yarinyar rai, toh taya ma za’ayi na auri yarinyar da ake marina akanta, tun yanzu Anty hanyan raina ni ta bud’ewa yarinyar.

Abban sa neh ya taho ahankali izuwa inda Mahmud d’in ke tsaye,yana cikin tunanin yaji ankamo hannunsa, firgigi yayi ya kalli hannun sannan ya kalli Abban nasa.

” je ka kwanta Mahmud ” kaji!

Baiyi magana ba still yaci gaba tsayuwa Abban ne yakama hannunsa ya shigar da shi cikin d’akin sannan yafito yaja masa k’ofar.

Zuwa yayi yabi ta gefen Antyn yace  “wuche muje”

Ahankali ta bishi abaya har d’akin baccin nasu.

Abbah bai k’ara bi takanta ba yayi kwanciyarsa yayinda abin yaso daya farun yaso hana Anty bacci dan tana tsoron maganar Abban bata so yaji ba amma ya shammace ta, bata sani ba ashe ya biyo bayanta, dole nayi maganin abin tunda wuri tunkan abin yazo yafi k’arfina, dole nayiwa tufkan hanci.

Mahmud kuwa wayarsa ya lalub’o ya nemi Abbas a waya……….

Sau kusan uku wayar nayin ringing amma no response, har yayi shirin sake k’iransa karo na hud’u sai kuma yafasa kawai ya ajiye wayar.

Kishingid’a yayi ajikin gado na tsawon mintina shida ransa a hargitse yake jinta wai yau Anty ne ta mareshi akan wata banza, sai daga baya sannan ya tashi ya zauna abakin gadon, hannayensa ya d’ago duk biyun ya cusa su acikin gashin kansa tare da furzar da iska mai zafi daga bakinsa.

Halin Antyn sa na matuk’ar damunsa sosai, can you imaging ace mahaifiyarka amma bata k’aunar taganka cikin farin ciki akullum sai dai sa6anin hakan,abinda Anty bata masa tun yana yaro ba wai sai yanzu daya girma ne zata ce zata yi masa saboda me?

Idan da wani yake bashi labarin hakan zai iya k’aryatawa amma sai gashi akan kansa abin ke faruwa.

Ace Anty tarasa da wacce zata had’a shi maganar aure sai da waccen yarinyar??
Toh shi me zaiyi da ita?

Rashin mai bashi amsa yasa dolensa yah hak’ura da tambayar dayake yiwa kan nasa domin yasan idan ya matsa kansa zai jawo wa ciwo abanza and no body cares!

Tashi yayi ya cire rigar dake jikin sa sannan ya shiga bayi ruwa ya watsa tare da d’auro alwala yazo ya shimfid’a dadduma.

Sallar nafila ya gabatar tare da neman sauk’i daga gurin mahalicci akan dukkan al’amuransa rok’on haske, rahama da kuma kariyar Allah yayiwa iyayensa musamman ma Abbansa duk dama yaga kamar Abban ya d’an canja ba kamar kwanaki ba, amma yasan addu’a bata ta6a yin yawa a bawa kamar yanda bata tafiya abanza saboda Allah shida kansa yace a rok’eshi zai amsa.

yadad’e awurin yana Addu’o’i kafin yatashi ya kwanta ko daddumar ma be samu yah nad’e ta ba saboda bacci.

Alokacin kusan 1:06am bacci ne sosai a idanunsa shiyasa daga kwanciya sai bacci yah d’auke shi cikin natsuwa kuwa yayita shek’a baccinsa batare da yasake bi takan damuwarsa ba.

Washe gari ma da wuri ya farka domin tafiyarsa na nan aransa be fasa ba, dan haka yana dawowa daga masallaci yafara tattara d’an abinda yasan zai buk’ata ako’ina yake, abubuwan basu wuche tarkacen amfaninsa ba irinsu laptop wayoyinsa da sauran k’ananan abubuwa .

Dayake sun had’u da Abbansa da asbah a masallaci kuma yariga ya sanar dashi batun tafiyar tasa so bashi da damuwa akan haka yasan Abbahn bazai hanasa tafiya ko kuma wani abu daban ba indai bawani dalili ba kam.

K’arfe tara ya fito daga d’akinsa kafad’arsa rataye da jakansa hannunsa d’aya kuma wayarsa ce arik’e yayinda d’ayan hannun ke rik’e da key holder d’insa me tarin keys ajiki.

Guda d’aya ya ware yasaka ya rufe k’ofar parlourn nasa sannan yasake zareta.

Daga nan ya canja rik’on key d’in izuwa hannun sa na hagu sai ya maida wayar tasa zuwa hannun damansa.

Story continues below


password d’in dake kan wayar tasa ya cire sai yafara neman layin Abbas dan sosai yake da buk’atar ganin sa amma is hardly su had’u d’in shiyasa yake so ko samunsa awayar ma yayi.

Sai dai ko yanzun daya sake k’iran ma _call waiting_ ya gani sai ya dakatar da nashi k’iran ya d’an bashi time zuwa wani lokaci.

Kusan mintina biyar sun shud’e yana nan tsaye a inda yake still sai dai ad’an tsayuwar dayayin har ya samu chance na k’iran mummy suka gaisa yah tambayi lil sis da Daddy mummy tace masa suna nan lafiya qalau.

Hira kad’an sukayi sukayi sallama da mummyn sai yace mata shima d’in insha Allahu yau zai shigo , suna gamawa sai ya sake gwada layin Abbas d’in batare da yayi zuciyah ko fushi ba.

Amma still _call_ _wating_. 

Wannan karon kam tsaki yaja tare da fara tafiyah ya tunkari sashin iyayensa da wayar tasa ahannu.

Mahmud irin mutanen nan masu son fad’ar abinda ke damunsu ga wani wanda ya kasance makusanci agaresu,  yana son akan komai abashi shawara kafin yayi abin, idan ma damuwace tadameshi yafison yayi sharing ga wani sai dai wani lokaci  idan ya rasa wanda zai tunkara da damuwarsa sai ya rik’e abinsa azuciyarsa duk da hakan na damunsa amma bazai fad’iwa kowa ba yafison sai wanda ya yadda dashi tukun na,kuma wannan dalilin be sa yazama mai yawan fad’e-fad’e ba, mutun d’ayan nan dai ne ke sanin damuwarsa baya kuma sake fad’i wa wani daban.

Yakan yanke hukuncin abinda zaiyi dakansa idan abu zaiyi saiyayi abun kawai ayanda ayanda yake ganin shine dai dai.

Adacan baya kafin had’uwarsa da Abbas _Anty_itace abokiyar shawaransa ita yake sanarwa da duk wata matsalar data kunno masa kai arayuwarsa, amma daga baya shikansa be san dalilin dayasa ya daina fad’a mata ba, ko dan irin shawarwarin data ke bashi ne oho, domin akowani abinda Anty zatayi selfishness take fara sawa agaba kafin wani abu, bai sani ba ko wannan dalilin ne yasashi ya janye jiki daga gareta ba, amma haka kawai yaji baya son sanar mata da wasu al’amuran da suka shafi rayuwarsa.

Daga baya ne sai yafara sanar da wani abokinsa dasukayi makaranta tare shikuma matsalarsa baya 6oye k’yashi da hassada afili yake bayyana su fahimtar hakan da Mahmud yayi sai yasa yadaina fad’iwa kowa kawai yake rik’e abinsa shi kad’ai .

Alokacin Abban sa ba sauraronsa yake ba dan abubuwa shima sun masa yawa sosai kasuwancinsa ya bunk’asa shiyasa kullum baya zama, akullum yana kan tafiye-tafiye banda matsalarsa tacikin gida, gara yan zuma daya d’an daidai ta al’amuran sa waje d’aya sannan yasamu yake d’an natsuwa agida.

Tunda suka had’u da Abbas sai yake jin har aransa yasamu aboki jin Abbas yake tamkar d’an uwansa kuma sai akayi sa’a ma jininsu ya had’u da Abbas d’in shiyasa wannan karon yake so yakai damuwarsa gurin Abbas ko zai samu sgawara me kayu daga garesa duk dama yariga ya yanke decision aransa kuma bazai canja ta ba amma dolene yaji ra’ayin Abbas akan hakan.

Yana gab da shiga shiga parlourn yaji wayarsa na vibration ahannunsa d’ago wayar yayi sai  yaga sunan dake k’iran sa, nima sai na d’an lek’a kad’an dan ganin me k’iran nasa☺ _Oga Abbas_nagani 6aro 6aro akan fuskar wayar. 

Yana ganin Abbas neh sai yah dakata da tafiyar tasa cak ya tsaya sannan yayi picking call d’in yakai wayar kunnansa.

Abbas ne yafara fad’in “yah ne corper kana lafiya?

” qalau”  Mahmud d’in yace agajarce, sannan ya cigaba da fad’in ”  tun jiya fah naketa neman layinka amma baka picking me yasa?

” ainasan sekayi magana tunda naga missed called d’inka jiya,nagaji ne wallahi ina hutawa shiyasa kuma banma jiba cuz’ wayar na silent,inama da niyyan k’iranka fah se kuma k’iranka yashigo”

“Ba wannan bama tunda kasameni yanzun then fad’amin abinda ka k’unshe dan nasan wannan duk damuwar k’iran ba’a banza ba.”!
Abbas ne yafad’i hakan yana murmushi tamkar Mahmud d’in na gabansa.

Mahmud d’inma murmushin yayi sannan yace “kana ina ne yanzun inaso mu had’u fah “

” tasamu kenan,
” a’ a kai bakomai babu wani abinda yasamu” Mahmud ya dakatar dashi da fad’in haka.

Sai Abbas yace
” kuma kaga nad’anyi tafiya yanzu haka ina borno inajin kuma anjima kad’an za mu wuche”.

“Shikenan toh nima yanzu nake shirin komawa sai dai da k’yar mu had’u may be kafin na iso kunwuce kasan nazo lagos 2days back” 

” Haba mana 2days kuma har zaka koma?” 

” ehh kamanta bautar k’asata nakeyi ne?,  Kabari insha Allahu idan na sauk’a zamuyi magana.”
Mahmud ya k’arashe maganar da d’an gaggawa dalilin hango mahifinsa dayayi 
ya fito da shirin zuwa office dan hannunsa rik’e take da briefcase d’insa, bayan Abban kuma Anty ce itama ga dukkan alamu fitan zatayi.

Yana yanke k’iran suka had’u dayake dama ba wani tazarar kirki bace atsakaninsu.

Suna had’uwa sai ya gaishe dasu, Anty yafara gaisarwa dayake sun riga da sun gaisa da Abbah tun a hanyar dawowa daga masallaci sai dai ko gaisuwa ta biyu.

Antyn ma adak’ile ta amsa masa yayinda Abbansa ya cira hannu yah mik’a masa sukayi gaisuwar muslunci yana murmushi yace “harka shirya kenan”

” ehh Abbah inajin daganan ma sai airport” 

” Abbane yace bakace tafiyar sai 11:30 ba?

” ehh zanbi wajen Jabir ne kafin na wuche”.

” alright ba matsala Allah ya tsare ya bada sa’a”

“Ameen- Ameen Abbah”.

Duk maganar nan da sukayi Anty kauda kanta gefe tayi tamkar bata jinsu, Mahmud kuwa yana gamawa da Abbansa ya dawo gareta yace mata zai wuche .

Tunani tafara aranta wai dama dagaske Mahmud  ayau d’in zai koma?
Kar dai duk akan maganar Munira ne ya yanke wannan hukuncin? Toh idan yakoma ayau ai tamkar ya dakatar da batun auren ne, while itakuma dawuri takeso ayi.

Koda ta tambayeshi dalilin tafiyar sai ya ce mata akwai aikin dake jiransa ne acan shiyasa.

Sababi tafara ranta a matuk’ar 6ace take fad’in
” aikin banza aikin wofi, harni zaka nuna wa wani aiki, ince dai service kajeyi acan d’in ba neman aiki ba da har zaka min iyayi anan.

Cewa yayi ” shi d’in dai service d’in nake fad’i bakomai ba Anty”.

Bud’e baki tayi tacigaba da masifanta inda acikin masifar tace ai akwai mutane dayawa da wannan bautar k’asan duk ba yinta suke ba why not shima ya tura musu ko nawane suke buk’ata inyaso yayi zamansa agida basai ya koma ba”

Shikuwa yace a’a  yafi buk’atar yayi bautan dai kodan saboda ya jaddada kasancewarsa cikakken d’an k’asa.

Aikuwa sai tacigaba da fad’in wai Mahmud ya raina ta sam baya bin maganarta dan me zai ringa ja inja da maganarta abinda daa ba haka yake mata ba , kenan ya je yakoyo banzan hali zai zo ya rink’a yi mata sai kace ba ita ta haife shi ba”

Kallonta suke yi daga Abbah har Mahmud suna mamakin masifar tata ta dosa da kuma dalilin yinta.

” wallahi indai kace ni zaka raina akan wata banza zaka……….

Da k’arfi cikin tsawa Abbah yace ” shut up maryam….,stop it,how dare you zaki ringa fad’in hakan infront of me!”…

Yatsansa ya d’aga sama yayi nuni da gefensa kana yace ” waccen d’in fah da kike so ki zaga ‘yar uwata ce!, gudan jinina!!, ita kad’ai nake dashi !!!meyasa baki gane abu ne ke,…….yatsan nasa ya dawo dashi saitin Antyn sannan yace ” kinsan Allah, idan nak’ara jin kin fad’i ba dai dai 
ba akan Kha…..kha….di………..

Sai yayi shiru yaja tsaki. 
Hannun Mahmud ya finciko ya yi gaba dashi har gurin da driver ya ajiye motar da Abban zai fita da ita.

Nan yace Mahmud yashiga motar sai dayaga yashiga sannan Abban shima yaxaga yashiga.

Mota d’aya suka shiga suka tafi suka bar Antyn tsaye agurin tamkar andasa ta.

Mahmud kuwa hamdala yake ta yi azuciyarsa duk dama ba hakan yaso ba, hak’ik’a duk d’ah nagari bazai so ya ringa kallon husuma na tashi acikin gidansu tsakanin mahaifansa kuma yaji dad’in hakan ba.

Amma shi kan sai yaji farin ciki kad’an bawai dan Abbah yayiwa Anty masifah ba ” a’a “
Canjin daya gani azahiri tattare da mahaifin nasa shine yasashi farin ciki.

Lalle Allah maji rok’o ne yakan amsa addu’o’in bayinsa aduk lokacin daya so hak’ik’a yau ranar farin ciki ce ga Mahmud domin yau yaga mahaifinsa na acting as Magidanchi cikakke mai fad’a aji acikin gidansa, sa6anin baya da komai in za’a yi baya ta6a tankawa koda kuwa abin ba dai dai bane sai dai yayi shiru yasa ido yana kallo.

Abbah office d’insa ya wuche da Mahmud sukayi zamansu aciki suna d’an ta6a hira kamar bashi bane yayi masifah d’azun, ayyukan dake gabansa ma dakatar dasu yayi yah bada hankalinsa ga d’ansa suka fahimci juna sosai anan ne Abban ya nemi jin asalin ra’ayin Mahmud akan waccen yarinyar Mahmud kuwa bai 6oye masa komai ba ya sanar da shi akan sam baya so saboda yarinyar yaga kamar bata da tarbiya kuma ma shi ba yanzu zaiyi aure ba sai zuwa gaba.

Kwantar masa da hankali Abbah yayi akan batun auren da baya so d’in kuma yace insha Allahu babu mai yi masa dole matuk’ar yana numfashi, amma batun bayanzu zai yi aure ba yama daina fad’i dan aure lokaci ne idan kuma lokacinka yayi babu makawa sai anyishi koda kuwa ba’a so yana faruwa ne tamkar mutuwa.

Godiya sosai Mahmud yata yiwa Abbahn nasa take kuwa sai yaji duk wani damuwarsa ta kau dama dan haka yake so ya had’u da Abbas saboda idan ya yi magana da mutun akan matsalarsa yakanji kwarin gwiwa sosai sa6anin barinta azuciyarsa.

Magabar dayayi da Abbansa sai yaji yama fasa sanar da Abbas maganar tunda Abbansa yah bashi assurance mai kyau akai so yanzu baya buk’atar sake ji, komai daga wani.

‘Karfe goma daidai Abbah yak’ira drivern office d’insu yace ya kaishi airport d’in saboda hold-up ma yasan kafin su isa lokaci zaiyi yak’ara da fad’in ya k’ira jabir d’in yabashi hak’urin rashin had’uwarsun yace masa Abban ne ya rik’esa a wurinsa.

Mahmud
Yana dariyah yace ” haba Abbah bakomai zanyi masa bayani insha Allahu”

Daganan sukayi sallama Abbah yayita masa addu’a har suka rabu.

Tun lokacin da Abbah ya fara yiwa Anty tsawa akanta taji duniyar ta tsaya mata cak, wani duhu taji ya mamaye ilahirin kanta har cikin k’wak’walwarta gaba d’aya, wasu abubuwan daya fad’a d’inma bata jisu da kyau ba ido kawai ta tsurawa fuskarsa yayinda yake mata masifar inka ganta alokacin zaka zaci hankalinta da nutsuwarta ta mayar akansa don ta fahimci me yake nufi da kyau, amma azahiri ba haka bane. 

Anty ta kusan minti goma agurin tsaye tana tunani abin ne takeji wani banbara k’wai it seems different, kamar almara…………wai yau ita Abbah ke yiwa tsawa akan abinda be taka kara ya karya ba. 

Jijjiga kai tayi da k’arfi take sai tunaninta ya dawo daidai, gani tayi ba kowa agabanta ita kad’ai ce tsaye awurin, koda ta kalli gefe da gefenta ma duk haka tagani bakowa,da sauri ta juya takalli inda motar Abban ke ajiyeh sai taga wayam bakomai, alamar sun ma bar mata gidan gaba d’aya batare data sani ba tsabar yanda ta shiga zurfin tunani. 

Ranta taji ya matuk’ar 6aci,wani ‘kullutun daya kullera azuci ji tayi tamkar ta kurma ihu ko zai waraware, ahankali tafara d’aga k’afafunta tajuya da niyyar shiga cikin gida saboda fitar ma jitayi tafice mata arai. 

Kan kujera taje ta zube sharab tamkar wata majinyaciya, sam takasa yadda cewa wannan ABBAn mahmud ne, ji take kamar an exchanging mata shi ne gaba d’aya, inkuwa wannan mutumin da kuma wannan al’amarin daya farun ya kasance gaskiya to kuwa hakika zama bai ganta ba. 

Bazata ta6a bari aci nasara akanta ba matuk’ar tana numfashi,kuma nan take tayiwa kanta alk’awarin tarwatsa rayuwar duk wani mai shirin yiwa aikinta _zagon k’asa_ (khadija candy). 

Tayi alwashin koda waye ke yi mata hakan sai taga bayanshi sannan wannan auren data fara magana akansan bata ga uban daya isa ya hanasa faruwa ba matuk’ar tana numfashi, ada bata d’auki al’amarin da wani girma sosai bama, saboda kawai tana tunanin zata lalla6e shine ahankali ya amince ya auri Muniran tunda ita ta nuna tana sonshi, amma yanzu ji takeyi aranta kodan abinda Abban Mahmud yayi mata ayau d’in sai ta bawa duk wani mai shirin shiga tsakaninsu kunya, sannan kuma daga baya ta kuma tarwatsa shi kamar yadda yafara had’a mata hargitsi acikin gida. 

(Kunsan shi me yin abu akullum shi tunaninsa kowa ma yanayi ne, gani suke kamar duk abinda yasame su toh yi musu akayi, gaba d’aya mantawa sukeyi da k’addara)
Allah ubangiji kasa mufi k’arfin zuk’atanmu _AMEEN_ . 

Koda Mahmud ya koma damaturun babu wani abinda yakeyi saboda already ya gama abinda zaiyi tun kafin yaje lagos kwanaki. 

Abinda ANTY tace yayi d’in batasan yayi hakan tun kafin ta furta ba,so yanzu bawani zuwa wurin bautan k’asa daya keyi zamansa yake kurum agida, sai dai suje yawo, ko suyi karatu suje ziyara inda suka sani idan ta kama,wani lokaci kuma daddyn Teemah yajashi suyi tafiyah tare. 

Yakan d’an ziyarci wajen dayake service d’in amma sai lokacin daya ga dama, kuma zuwan ma yana zuwa ne bawai dan yayi wani abu ba kawai yana zuwa ne dan ya san meke faruwa awurin kar shirun yayi yawa. 

Story continues below


Wani lokaci acikin ransa sai yaji cewa bai kyautawa Anty ba daya k’i zama awurinta, yasan amatsayinta na mahaifiya dole tana buk’atar sa akusa da ita musamman ma daya kasance shi kad’ai ALLAH YA BATA dole tarink’a jin kewar d’anta. 

Amma sam bazai iyah zama a Lagos ba yanzu, sosai yagaji da fitinar Anty, bata k’aunar azauna lafiya ita sai k’ak’ale-k’ak’ale. 

Wannan dalilin ne yasa yaji zamansa a damaturun yafiye masa can tunda mahaifinsa bai hanasa ba.

*****
Lokacin da aka fara zana waec kusan tare Mahmud da Teemah suke yi dan baya ta6a barinta tayi karatu ita kad’ai ko exam d’inma zataje tare suke tafiya. 

Ana tsakiya da waec d’in ANTY tasake hura masa wuta akan yadawo gida haka nan tunda already yagama service d’insa toh zaman me kuma yakeyi, tace masa ya dawo gida wai afara maganan aurensa da Munirah. 

Tambayar ta yayi cewa “wani maganar aure kuma ?. 

Dan shi shaf yama manta da batun tun sanda yadawo nan, bai sani ba ashe abin har yanzu yana ran Anty. 

Koda ya tambayetan haushi taji bata bashi amsa ba sai kawai ta yanke k’iran daga 6angarenta tacigaba da masifah. 

Acikin kwana biyu tak’ira shi yafi sau a’kirga kuma duk akan maganar ne, daya ga haka sai ya ‘kira Abbansa yayi masa bayani. 

Abban nashi ma cewa yayi ya koma gidan kawai tunda haka mahaifiyarshi keso shi yasan mai zaiyi akan maganar auren. 

Bai ‘ki maganar Abban ba amma yace masa sai an gama weac zaizo, daga lokacin zuwa agama d’in yakama kwana tara kenan ya rage. 

Dahaka sukayi sallama da Abban nasa kowa ya yanke ‘kiran. 

Mahmud wannan karan kokad’an bai bari Mummy ta san da labarin ba, dan yasan tana sani zata sashi agaba sai taga yatafi itama kafin hankalinta ya kwanta,bawai dan ta gaji da zamansa tare dasu ba ” a’a ” kawai wai dan kar ashiga hakkin mahaifiyarsa ne. 

Tun kafin a kammala waec kuwa yafara shirye-shiryen tafiya gida, kwana biyu bayan waec d’in ya shirya yatafi wannan karan kam shirinsa na barin garin ne gaba d’aya, saboda da wuya ya sake dawowa, duk wani abu da yyake nashine na buk’atarsa ya tattare su haka yatafi ya bar kowa da k’ewarsa agidan.

***** 

Dawowar Mahmud Lagos shiyafi komai faranta ran Anty dan tana ganin kasancewar sa tare da ita shine zai sa burinta yayi saurin cika, musamman ma yanzu da take ganin yin auren nasa shine zai sa ya rabu da son rayuwa awurin Khadija, tunda idan da aure akansa ai bazai yi gigin son tafiya wani gari yabar iyalinsa ba. 

Adole take sa shi ya shirya ya ziyarci Muniran batare da yaso ba, kuma wannan shine karo na uku kenan dayake zuwa wajen Muniran, sai dai abinda Anty bata sani ba shine zuwan nasa ba anfanan su yake da komai ba saboda a duk sanda zai baya fad’a mata wata magana daban face sake jaddada mata dayake akan baya kaunarta and he can’t even marry her saboda bata dace dashi ba.Maganar arzi’ki bata ta6a had’asu ba. 

Antyn ce da kanta tasa Mahmud ya sanar da Abbansa cewa ya samu matar aure wai aje ayi masa tambaya, afad’ar Antyn 
wai in itace tayi ma Abbab maganar tasan ba amincewa zaiyi ba kuma zaiga kamar ra’ayinta bana Mahmud d’in ba. Shiyasa take so shi yaje dakansa yayi bayani. 

Nan ma da ‘kyar Mahmud ya yadda ya amince akan zashin d’in har sai da yaga ranta na shirin 6aci kafin nan ya amince da zuwa d’in. 

Da farko kafewa yayi akan shi bazai iya ba, ita tayi magana wa Abban nasa mana ai ba dole sai shi dakansa ba, kuma dagangan ya ya kafe akan hakan saboda yasan tana tsoro yanzu bakamar da bah, bazata iya fad’an ba shiyasa shima ya kafe akan hakan. 

Dayaga rantan ya 6aci kafin ya amince akan zaiyi magana wa Abbahn saboda shi wannan mitan ya tsana bakomai ba, itakuwa Anty babu abinda yafi birgeta akan tayita k’ananun maganganu……aganinsa fah. 

Ranar wata talata da dare around 8:00pm yaje yasamu Abban bayan sallar isha’i, 
Abban ma na ganinsa ya fahimci akwai abinda ke damunsa, domin jikinsa sanyi k’alau ya shiga gurin Abban, zuciyarsa duk ba dad’i don ya tsani yarinyar can bai san me yasa ba, gashi mahaifiyarsa ta nace akan dole sai ita zai aura, infact shi auran ma ba yanzu ya shirya yi ba gaba d’aya.

Zuwa yayi ya zauna akusa da Abban ya gaida shi, shiru ne yabiyo baya bayan Abban ya amsa gaisuwar cike da kulawa.

Mahmud rasa ta inda zai fara yayi bai san yanda zai fara fad’ar maganar ba, dayake asali Mahmud shirgin mata bai dameshi ba, shi sam bashi da matsala dasu, aganinsa mata damuwa ne sosai su, ko lokacin da ya ke higher institution d’insa ma inka ganshi da mata toh friends ne ba komai ba, kwatsam sai gashi yanzu mahaifiyarsa ta 6ullo masa da maganar aure alokacin da shi sam  bai shiryawa hakan ba, amma babu yanda zai yi dolensa ya kar6i maganar kodan darajar da take dashi na mahaifiya agareshi bazai bada ita ba, yayi alk’awarin cewa da iznin Allah sai ya nuna cewa shid’in d’aah ne, kuma na halak cikakke.

Ido Abban ya tsura masa da dukkan kulawa yana kallonsa , sosai ya fahimci d’an nasa na cikin damuwa sai yayi gyaran murya ya fuskanci Mahmud d’in da kyau sannan yace masa ” yah akayi ne Babana”!.

Ahankali ya d’aga kai ya kalli Abban nasa suka ha’da idanu take sai yayi gefe da kansa kamar mace tare da k’ak’alo murmushin k’arfin hali.

Da k’yar ya samu ya tattara bayanan dake bakinsa ya dunk’ula ya furta “Ab…bah wai dama maganan yarinyar da zan aura ne, wai ko za’a je ayi tambaya”.

Murmushi Abban yayi sannan yace “Mahmud ba dama, wai ko za’a je ayi tambaya ko kuma kana so aje ayi maka tambaya?

Murmushin yakuma yi batare da magana ba.

” babana yau d’in kai ke yin abu kamar mace!?

” hmm toh a ina yarinyar take?

Abban ya sake tambayarshi.

Ahankali ya kwatantawa Abban nasa,daga yanda yake maganar sai Abban ya fahimci abin sam baya ran Mahmud d’in musamman daya tuno ranar da Antyn ta maresa akan wata yarinya,sannan ranar da Mahmud d’in ya ‘kirasa alokacin dayake damaturu akan maganan auren da Anty take yawan yi masa harma ta uzzura masa  yadawo gida duk akan maganar ba shakka wannan duk tilastawar Maryam ne, ni kuwa bazan ta6a tilastawa yarona abinda baya so akan wad’anda bama sanin asalinsu yayi ba.

Lokacin da Mahmud yasanar da Anty cewa sun gama magana da Abban kuma ga abinda yace ji tayi kamar ta goyashi saboda farin ciki.

Tayi zaton ai Mahmud d’in zaiyi mata taurin kai ne yak’i zuwa amma kuma sai yaje, hakan kuwa ba k’aramin farin ciki yasata ba.

Abbah binciken yayi kamar yanda ya fad’ad’in yayinda binciken ya d’aukesa kusan sati kafin ya gama gamsuwa da duk wani abinda yake son sani game da wannan family d’in.

Bai sanar da Mahmud ba ya k’yaleshi, yana so ne yaga ko Mahmud d’in zai zo dakansa yasake tambayarsa idan yaga shiru ko yayah ,yasani cewa matuk’ar da yaddansa a auren to shi zaifi kowa rawar jiki dan ganin an kammala komai dawuri inkuwa bahaka ba ma’ana bai sakeyin magana ba toh kenan shima be wani damu da maganar ba kenan rashin damuwarsa da maganar kuma na nuni da cewa baya ra’ayin abin har ransa.

Hakan ya sanya Abbah yayi gum da magabar shima yana jiran yaji daga Mahmud d’in.

Rashin ha’kurin Anty yasanya ta kasa ha’kuri da taji shiru babau wanda yasake bi takan maganar sai ta tuntu6i Abbah da maganar shikuwa yace mata bincike yake yi tukunna har yanzu, ita a ganinta tunda Mahmud yariga yayiwa Abbansa magana ai itama zata iya yi masa maganan irin kamar Mahmud d’in ne itama ya sanar da ita.

Bata wani damu ba saboda ita kanta bata san asalin tarihin ‘kawartan ba shiyasa koda Abban yace zaiyi binciken bata damu ba.

*****
Teemah kuwa tana can sun gama hutun interval d’in dake tsakanin waec da Neco d’in har sun fara Neco yau suke na biyu,tun kafin ayi nisa tafara missing d’in Mahmud domin tasaba karatun dashi sosai yake highlighting d’inta akan wasu abubuwan da bata ganesu, yanzu kuwa babu shi, sai dai tayi ita kad’ai, dayake Daddyn ya sai mata waya a satin daya gabata, arana ta uku tana tsaka da karatun data ji ba sugar sai ta ‘daga wayarta ta ta ‘kira Mahmud tayi ta masa complain akan ita fah bata ganewa tunda yatafi take shan wahalan karatun gashi kuma ya’ki dawowa.

Lalla6anta yayi tayi yana bata ha’kuri a itakuwa tayita masa shagwa6a,ahakan ya tambayeta inda bata gane ba d’in data fad’a masa sai yayi mata bayani ata’kaice yanda zata gane.

Shikenan kusan kullum in tana da exam sai sunyi waya dashi a haka har aka kusan kammala Neco d’in .

2 days to candidate d’inta Daddy suka rabu da Abban Mahmud A lagos basu ma gama abinda sukeyi ba amma daddyn Teemah yace zai dawo gida saboda graduation na Teemah yana so ya halatta.

Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi harma yace badan akwai aiki agabansa ba da shima zai je shi, Daddy ne yace bakomai ai addu’ar ma ta wadatar, sai Abban yace duk da haka ma insha Allahu idan yasamu lokaci ko bayan graduation d’in ne zaije musamman ya ziyarcesu.

Farin ciki ne sosai yacika ziciyar Daddy dan yajima baiji irin hakan daga bakin abokin nasa ba, so yana jin hakan yasan ikone kawai na ubangiji dayake kawo ‘karshen duk wani al’amari inma me kyau ko akasin haka.

Ko da yaje gida kuwa bai sanar da mummy ba saboda yana son koda Abban Mahmud d’in zaizo toh zuwan ya zamewa mummy na bazata, kar kuma ya sanar da ita yanzu cewa Abban zaizo zuwan kuma yak’i yiyuwa duk dama ba’a fatan hakan, amma kuma idan hakan ya faru zai kasance ne kamar shine ma’karyaci a idanunta.


Lokacin da daddy zai dawo gida sai ya siyo wa Teemah tsarabar set ‘din ‘dan kunnan gold mai kyaun gaske afad’arsa wai zatayi anfani da shi ne ranar graduation d’insu as his gift, mummy najin haka tace “a’a sam” badai aranar ba kam sai dai ordinary day haka ta saka dan bazai yiwu taje cikin taro da wannan sar’kar ba, yanda duniya ta lalace d’innan duk dama ba’a fatan wani mummunan abu amma ai _maganin kada ayi_ _toh kada afara_ .

Daddy ma dayaji bayanan mummyn take yaji ya gamsu sosai tuni ya amince da batun mummyn, Teemah kuwa na tsaka da murna ta tsinkayo muryar mummynta na fad’in haka take sai murnar ta tsaya cak, sai ta tura baki gaba tare da sake matsowa kusa da daddyn ta tana ta wani muzurai.

Babu wanda ya kulata sai da yagama da mummyn kafin ya juyo ya fuskanceta yace tayi ha’kuri za’a siya mata wani wanda zata saka ranar inyaso daga baya sai tayi anfani da wannan ‘din……

Kafin ma ya ‘karasa fad’a mummy tace ” ai already ma na siya mata wanda zata saka d’in.”

“Yauwa shikenan ma kin hutar damu ko my angel ” cewar daddy yana murmushi.

Teeamah kuwa ‘kasa tayi da kanta taci gaba da kallon bangles da zoben dake tare da sar’kar  bata ‘kara yin magana ba har mummy tabar gurin, sai da mummyn tatafi kafin ta ‘dan sake har take tambayarsa labarin yayanta Abbas, dayake tafiyan dayayin sai da yaje Abuja tukun na kafin yawuce lagos sai ta tambayeshi wai ya ga Yah Abbas kuwa dayaje Abuja?.

Dariya yayi mata tare da fad’in ” wato yayanki kad’ai kika sani ko? Murmushi tayi harda wani sunkuyar da kai ‘ kasa kamar dagaske.

Daddyn ma sai yayi murmushin sannan yace”  Abbas ai baya Abuja porthacourt yake aiki”

Tana jin haka sai ta ‘dan tura baki gaba kana tace ” aini ba ruwana ma dashi daddy tunda shima ya manta dani”

Ido daddy ya zaro kad’an ” ke da yayan naki”?

” ehh mana daddy,  tunda yatafi fah ya manta dani, kuma inaji ko suna waya da mummy baya tambayata, baya cewa agaishe dani kuma mummy ma bata ta6a cemin in kar6a mu gaisa da shi ba………..shiyasa nima da aka siya min wayata ban saka numbern shi ba, ta yah Mahmud kad’ai na…………

shiru tayi ta ‘daga kai ta kallo ‘kofa sakamakon jiyo muryar mummy datayi tana fa’din

” sai kiyi ta tura bakin nan ai har sai ya ta6o ‘kasa tunda ke bakijin maganan mutun “
Mummy dake ‘ko’karin shigowa ne ta kar6e maganar Teemahn da fad’in haka.

Shiru Teemahn tayi bata ‘kara magana ba,sai kawai ta sunkuyar da kanta ‘kasa taci gaba da kallon abinda ke ri’ke a a hannunta, sai da mummyn ta ta iso ta zauna kafin daddy yace tura bakin me kuma tayi ne hajiya? ” 

” Ka ‘kyale yarinyyar nan ,wallahi ko kad’an bata jin magana, dubi fah ‘karfi da yaji yanda ta maida bakinta kamar tsuntsuwa……..
Dai dai nan ta juya ta kallo Teemah sai idonta ya sau’ka akan hannun Teemahn ganin da tayi tana jujjuya d’an kunnan ahannunta take sai ta sake fad’in ” bani ni karki 6alla shi abanza daga kawowa” tafad’a tare da mi’ka hannunta saitin Teemahn..

Story continues below


Teemahn ma sai ta mi’ka mata sar’kar batare da wani 6ata lokaci ba.

Sai da mummyn ta kar6a kafin ta d’aga kanta caraf sai suka had’a idanu da daddyn, hannu ya ‘daga tare da ware yatsa ‘daya ya nuno mummyn dashi yana jujjuya kai da kuma yatsan nasa duk atare da murmushi akan fuskarsa alamar ” ke bah”
dayake kan Teemah na ‘kasa duk bata lura ba.

Mummyn ma sai ta saki murmushin tana maida sar’kar a gidanta take fad’in ” naji ma ana gulmar yaro na laifin me kuma yayi muku?”

Daddy fa’da’da fara’ar sa yayi sai ya bata amsa da fa’din ” Laifin ai harda ke , ya za’ayi kullum kuna waya da Yayanta tanaji amma baza’a bata waya su gaisa ba,kuma laifin harda naki da kema bakya ce mishi gata nan akusa”.

“au laifin kenan dama?
Mummyn ta tambaya tana ‘dan murmushi idanunta na kan Teemah.

” ‘kwarai kuwa, wannan ‘din ‘karamin laifi ne aganinki? 

” hmm” kawai mummyn tace. 

Sai daddy yace ” ba hmm ba, so muke agyara adaina ware min angel ‘dina agefe, shima Abbas ‘din zan had’u dashi ai”

Take sai yah ‘daga wayarsa da niyyan ‘kiran Abbas ‘din sai kuma cikin rashin sa’a ‘kiran be shiga ba.

” Allah ya taimake shi ai” daddyn yafad’a yana mai ajiye wayar agefensa.

Daganan ya cigaba da lallashin Teemahn da bata ha’kuri akan wai duk ranar daya samu Abbas d’in awaya zai yi masa masifan dan me  baya son tambayanta idan suna waya da mummy.”

Bata dad’eba ta sau’ko daga fushin suka cigaba da hirarsu anan daddy yake tambayan ta yanda aka tsara graduation d’in duk ta fad’a masa,tana gama fad’a tace ta tashi tace zata tafi ‘dakinta,sai yace ta kunna masa NTA kafin tafita.

Tana kunna masa tafice bayan ta mi’ka masa remote ‘din TVn.

Labarai yaci gaba da kallo abinsa,dama daddy gwani ne a kallon labaran duniyah idan yana watching news hankalinsa gaba d’aya suke tafiya awurin. 



*****
Ranar Saturday shine ya kasance ranar da za’ayi graduation d’in Teemah, sosai wannan family d’in suka yi shiri na musamman a wannan ranar just to make their one and only daughter happy, ga wanda bai sani ba idan ya shiga gidan aranar ze yi zaton ko wani d’an hidiman biki akeyi agidan, amma ga wanda yasani sai de yace masha Allah.

*’Karfe 9:00am* 

Teemah ce tafito cikin wata ha’da’d’diyar gown d’inta d’inkin tela kalar ja, d’inkin ba ‘karamin kar6anta yayi ba, ‘dass ya zauna mata kamar ajikinta aka yi ‘dinkin rigar, yayinda kanta yake ‘daure da head golden colour kamar ba da hannu akayi ‘daurin ba, tsabar yanda ya zauna akanta , wata mata data amsa sunan ta ce afagen make-up ita tayi mata ‘daurin, wanda mummy  musamman ta sa aka nemo mata matar dan kawai tayi wa Teemah kwalliyan graduation d’in,
gefen kafad’anta shima golden colour veil ne mai kyan gaske , ba naa ce ga adadin kud’insa ba dan ko nima bansan lokacin da mummy tayi wannan siyayyan ba,ga wani high hill d’inta mai kyau shima duk kalan gyalan nata.

Turare kuwa ba laifi ‘kanshin na tashi dai-dai ajikinta bata saka daya wa ba dayake Teemah ba son anfani da turare mai ‘karfi take ba body spray kawai ta fesa ajikinta tafito.

Kallo ‘daya zaka yiwa Teemah kayi zaton ko amarya ce dan tsabar yanda tafito tamkar wata tauraruwa.

Ahankali take tafiya tana wani basarwa, ita adole irin an girman nan.

Kalle-kalle takeyi acikin harabar gidan tana ‘dan waiwaya wa, sai kuma tacigaba da tafiya yayinda ta tunkaro inda mummy ke zaune ahankali.

Tun daga nesa da mummy ta hango ta fara’arta ya ‘karu aranta take fa’din _tubar kallah masha_ _Allah_ Allah yah ya raya minke ‘yata.

Kafin Teemahn ta iso gurinta ma harta mik’e tsaye tana murmushi Teemah na isowa kuwa ta bud’e mata hannu Teemah kamar jira takeyi tafad’a ciki tana dariya.

Dariya mummyn ma tayi dukkansu sai ya zamana ha’koransu kawai zaka gani afili tsabar yanda suke jin dad’i fuskarsu kawai zaka kallah kasan cewa ehh lallai suna cikin farin ciki.

Mummy aranta take tayiwa Teemahn addu’an kariya daga kowani irin abun k’i.

Koda ta saki Teemahn ma abinda tafara fad’i azahiri shine ” Masha Allah, yarinyata anzama ‘yanmata, Allah ubangiji yasa wannan level d’in yah ‘kare kenan har abada, Allah yasa anyi a sa’a, Allah yasa ba’a yi gaba anbar baya da ‘kura ba”.

” Ameen yah Allah ” Teemahn ta fad’a tana d’an dariya.

Sannan tace mummy ni nagama shiri yanzu zan wuche,kinsan ance mana kar muyi african time, gashi ma yanzu 9:00 d’in kusan da rabi ma “!

Ta ‘karashe tana mai duba agogon cikin wayarta.Dayake ance ‘karfe goma ake bu’katan su awajen gaba d’aya candidates d’in.

” toh kije ki samu Habibu ya sauk’e ki,  sai mun iso muma”

Juya wa tayi tare da fad’in ” toh mummy sai kun iso “

” yauwa kar amanta da addu’an barin gida fah” 

Wannan karan kam da kai ta amsa batare data juyo ba.


10:00am aka fara programme d’in,Teemah na can ita kad’ai daga ita sai ‘kawayenta, akai akai take duba hanya ko zata hango mummy amma shiru harta gaji ta ha’kura ta maida hankalinta ga abinda ke gabanta.

*10:35am* 
Mummy na tsaka da aiki sai ta tashi ta je kitchen ta d’auko abu fitowan da zatayi kamar ance ta kalli harabara gidan sai idanunta suka sau’ka akan Abbas daidai ya bud’e mota ya fito.

Aikuwa mantawa da abinda ta ‘dauko in tayi da ke ri’ke a hannunta,da sauri tafara tafiya ta nufi wajen data hango shi d’in, shima da farko be lura da zuwan nata ba sai da ta kusan isoshi kafin ya ankara da ita, aikuwa sai yafara murmushi kana yace ” mummy har kin ganni ne “.

” ai dole in hango ka wannan irin suprise haka Abbas”!

” wallahi kuwa mummy”.

Tafiya suka farayi ska nufo cikin gidan atare yayinda mummy take tambayarsa ya wajen aikinsa yace ” aiki kam Alhamdulillah sai godiyan Allah kawai”. 

Zuwan nashi ya matu’kar bawa mummy mamaki domin bata ta6a kawo cewa zai halacci taron ba, sai kuwa gashi nan yazo.

Sosai taji dad’in zuwan nashi, basu ko gaisa da kyau bama dashi dan hankalinta na wajen aikin data bari anayi acikin gidan, data d’an tako masa tace mishi yaje 6angaren daddyn su yana ciki be fita ba tukun na, bari ta dubo abu tana nan zuwa yanzu itama, tana gama fad’a sai ta juya ta wuce cikin gidan.

Shikuma sai ya tsaya awajen, sai da yaga takoma kafin nan yajuya ya koma inda suka yi parking motarsu ya je ya ciro wani kwali me d’an girma amma ba sosai ba,wanda suke taren na jikinsa na rawa yake ‘ko’karin ‘dauka masa sai Abbas ya dakatar dashi da hannu yace yayi zamansa ba matsala zai ‘dauka kawai ga dukkan alamu drivern sane mutumin duba da yanda yake ta ambaton ” sir ” adukkan maganar dazata had’a shi da Abbas ‘din. 

Lullu6e kwalin yake da wrapping sheet baka gane kami game da kwalin faa ce size ‘din kwalin.

Sai da ya kai dubansa inda yaga mummy ta nufah ‘dazu sai yaga hankalinta gaba d’aya baya wani guri aikin dake gabanta kawai ne tasa agaba ga da alama a’kage take taga aikin ya kammala ganin hakan dayayi yasa ya taho da sauri ya nufi ‘k’ofan babban parlour, amma cikin rashin sa’a daf dazai shiga parlourn idanun  mummy ya hango shi akaro na biyu, hannunsa ta duba da wuri ganin cewa yana ri’ke da abu ahannun sai dai bata wani gane abun ba sai tayi zaton ko jakar kayansa ne. 

Da yake yasan kan gidan sosai batare da an jagoran ce shi ba sai ya wuce direct ‘dakin Teemah ya ajiye kwalin dake hannunsan kafin ya mi’ke tsaye sai da ya tsaya ya ‘karewa ‘dakin kallo kaf kafin ya fito ya nufi 6angaren daddyn.

Koda yaje 6angaren daddyn kuwa sallama yafarayi sai yaji shiru ba’a amsa masa ba, sai da ya sake yin wata sallamar sau d’aya yaji still ba’a amsa ba sai ya d’an tsaya na ‘dan da’ki’ku, ‘karan TVn daya jiyo ne yasa shi fahimtar dalilin dayasa daddyn be ji amon muryarsa ba, kuma yana da yak’inin cewa koda zai yi sau ba adadi ne daddyn bazai ji ba matuk’ar TV d’in akunne yake.


Sanin cewa daddyn shi d’aya ne acikin ‘dakin yasa ya tura k’ofar tare da sake yin wata sallamar ciki-ciki, ahankali ya maida ‘kofar ya rufe bayan ya shigo d’in, sai ya tsaya kamar an bashi umarni, daddyn ya tsaya yana ‘karewa kallo yanda yasha manyan kaya yawani fito shar dashi tamkar wani sabon matashi.

Ahankali yafara takawa yayinda salon tafiyar tashi ya matu’kar amsan zubi da tsarinsa ga duk wanda yasan menene had’uwa toh ba sai na gaya masa yana kallon Abbas yasan cewa ya ha’du sosai, be tsaya ko’ina ba sai dayaje gaban TV d’in kafin ya tsaya, sai dai kuma be bari daddyn yaga fuskarsa ba,baya ya juya wa daddyn da sauri ya maida fuskarsa take fuskantar inda bangon da TVn  yake bayansa kuma na kallon daddyn.

Daddy da bai san anshigo bama balle yasan waye ya shigo kawai sai yaga mutum tsaye ya tare masa news d’in dayake gani, lumshe idanunsa yayi dayaga hakan tsawon dak’ik’a goma kafin ya bud’e tare da fad’in ” _ABBAS_ ” .

Dariya Abbas d’in ya kwashe dashi sannan ya juyo yafara tahowa zuwa inda daddyn ke zaune.

” ya akayi ka gane ni da wuri haka daddy bayan baka kalli fuskata ba ” ya tambaya yana kallon daddyn bakinsa d’auke da murmushi.

” toh wa nake dashi da zai min haka banda kai” 

Daddyn ma yabashi amsa yana murmushin shima.

Dukka sai suka yi d’an takaitaccen dariya.

sai daddyn ne ya kuma cewa ” ja’iri daga ina haka kamar an jeho ka?”

” wallahi kuwa, escaped nayi daddy yau d’innan za koma ma kafin anemeni, ba shiri nataho kuma akwai ayyuka agabana”.

” haba kuma sai kace dole ai daka bari zuwa wani lokaci in kasamu isasshen time basai ka zo ba.”

” ba na so na…..,,.

Daidai nan mummy tashigo da sallamarta abakinta.

Sai Abbas d’inma ya dakata daga maganar da ya yi niyyan fad’i duk sai sukayi shiru suka jira harta iso ta zauna.

Barka da isowa tayi masa tare da fad’in ” dazu ina sauri bamu wani gaisa da kyau ba “.

Murmushi yayi mata kawai sai ta sake fad’in ” gaskiya ka shammace mu Abbas gashi bansan da zuwanka ba ko muhalli ba’a gyara maka ba” .

” Ai ba komai mummy ina ma kan hanya ne yanzu zan wuce”

” dawuri haka?, ka de bari ka ‘dan huta ka’dan de ko,ai nayi zaton ma graduation d’in kazo halatta dana ganka”!

Abbas cewa yayi wai ” a’a shi yama manta da wancen batun ai tuntuni tun bayan data sanar da shi abin be kuma zuwa kansa ba.”.

Su kuwa duk sai suka yadda akan ehh dagaske yamanta d’inne ba mamaki ko dan saboda irin aikinsan,wani lokaci abubuwa kansha kan mutun sosai.

Abinci aka shishshigo dashi da abin sha aka jejjera sai da aka gama sannan mummy tace toh bismillah ya d’an samu ya ta6a ko kad’anne ma kafin ya wuce d’in.

Dukka atare suka mik’e har daddyn suka nufi wajen da aka jera abincin, mummy na zuzzubawa tace

” kamar kuwa kasan kullun sai anmin mita agidan nan, harda su kaiwa ‘kara na wai bana bata waya kuma kaima baka tambayarta ko ka ‘kira wayan “.

” daddy ne ya kar6e da fad’in toh dah d’in ‘karyane?, ai da gaskiyarta” , daganan sai ya dawo da dubansa wurin Abbas yace ” me yasa baka tambayarta awaya idan ka’kira kuma ko sa’kon agaishe ta ma baka ta6a fad’a ba.”

Dukkansu sai maganar daddyn da yanda yayita kamar titsiye sai ya basu dariya, shima daddyn sai ya taya su dariyar, sai da suka tsagaita kafin yace

” toh haka nayi al’kawarin zanyi ku kuma naga kuna min dariya”.

Abbas baiyi magana ba sai mummy ce tace “ai idan kabiye Teemah kam abinda yafi haka ma zakayi shi”.

Murmushi sukayi daganan suka fara cin abincin da mummy tagama zuzzuba musu, mummyn kuma tafita abinta ta basu waje tatafi domin ta shirya.

Abbas na gamawa yacewa daddyn shi zai wuce dama ya shigo ne brief ya gaishe su, cikin sa’a ma kuma saiya samu daddyn nagida.

Albarka da addu’o’i sosai daddy yata yimasa sannan ya rakoshi har wajen parking inda drivernsa yake, tambayar drivern daddy yayi wai anya kuwa yaci abinci yace” ai be san cewa tare suke ba da an masa iso shima”, sai ya ‘daga hannu ya d’an mari ‘keyar Abbas yace ” ai duk laifin kane dabaka fa’da cewa dawani kuke ba “

Abbas ‘kasa ya d’anyi kad’an tare da shafa gurin kamar irin yaji zafin nan, sai yace ” Afuwan daddy Allah na manta ne shiyasa”.

Murmushi sukeyi gaba d’aya har drivern ganin yanda Abbas yake yi agaban daddy kamar bashi ba amma idan awurin aiki ne ko ha’koransa da wuya kake gani.

Sai drivern ma yace ” yalla6ai aina ci abinci Hajiya ta aiko an kawo min anan”

” Ahh toh shikenan sai ya juya ya kalli Abbas d’in ya sake cewa “Allah ya taimakeka da sai ka jira yaci abinci duk da saurin naka”.

Abbas da daddy kawai yayi sallama ko mummyn be jira sun sake had’uwa ba yayi tafiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *