*YAR TALLA*
CHAPTER7
Laure ta dauke shi da wani mahaukacin mari wanda ya sa shi dafe kunci, ta nuna shi da dan yatsa cikin bala,i
“Gidan uban wa aka samu wannan kayan sata kuke min a gidan nan k0 kuma me?” Rabi‘u ya girgiza kai cike da kunar zuciya ya girgiza kai alamar a’a, ta hayayyako masa. “To gidan uban wa ta samu wadannan kayan?” Rabi‘u ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a. zuciya kafin ya fada mata. yanda a kai ya samu kudin tun kafin ya karasa rufe baki ta sake dauke shi da wani gigitaccen mari cikin zafin zuciya take fadar. “Ni za ka dauka ‘yar iska ni zaka nunawa iyakata, Karya kake Rabi’u baka isa ba wallahi tallahi kaci karya ka kwana da yunwa baka isa kaja daniba,yandanaga bayan uwar data haifeku kuma bazaku gagareniba, don haka ka taka a sannu wallahi idan kai wasa sai na rufe babinka a duniyar nan k0 sunanka babu wanda zai sake ambata a garin nan.
ta janyo Saude ta shiga cire mata kayan tana fadin. “Ban yi niyar ta sanya sababbin kaya ba, kuma kai baka isa ka sata sanya suba.”
Ta cire kayan gaba daya ta hankadar da ita gefe ta wuce daki tana. faman huci.
Rabi‘u ya runtse idanuwansa yana jin zuciyarsa kamar za ta fashe saboda baqin ciki da takaici
kukan Saude ya dame shi a zuciya ya tallabo ta a jikinsa ya wuce daki da ita, ya dauki kayanta masu datti ya saka mata ya jata a jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Ki yi hakuri ki daina kukan nan haka kinji ’ insha Allahu zan siyo miki wasu ki yi shiru kinji
‘ ban san yawan kuka
Da qyar ya samu ya lallashe ta ta yi shiru, har wani barci mai nauyi ya dauke ta sai ajiyar zuciya take saki akai akai, tausayinta ya dirar wa Rabi’u. Tabbas bacin ita da ta rage masa yana ga da ya gudu ya bar garin, to idan ya gudu bai san halin da gudar qanwar tasa zata shiga ba, a dole ya zauna, dole zai yi hakuri ya ci gaba da fuskantar rayuwar dake tunkarar su.
‘ Ya runtse idanuwansa wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo masa a idanuwa suna sauka saman kan Saude wacce baccinta ya yi nisa sosai. yasa hannu yana goge hawayen da suka Bata masa fuska.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya babu abin da ya cansa sai ma abin da ya qaru, kullum da wahalar dake kunno kai. A tallar Saude kuwa sai ma abin da yayi gaba.
Wata rana da safe Saude ta dawo daga markade
Ta zauna bakin murhu’ tana hadawa Laure wuta, Malam Bala ya fito riqe da hannun ‘Yar Baba tana
sanye da sababbin kayan makarantar boko, koran wando da farar riga da koran kallabi da farar abaya, ta sha takalminta sandal da farar safa, ta goya jakar: goyan ta.
Saude ta tsaya da hura wutar tana kallon su cike da sha’awa yanda ‘Yar Baba ta yi kyau cikin sababbin kayan, har bata san lokacin da ta mike ta soma bin su ba don karma su Bacewa ganin ta.
Tinqis-tinqis ta ringa bin su har suka iso makarantar ba ta tsaya aka ba ta labari ba har cikin ofishin Head Master ta bisu ta yi tsaye tana kallon su.
Malam Bala suka gaisa da Head Master sannan ya gabatar masa da ita matsayin sabuwar daliba, shugaban makaranta: ya riqo hannun ‘Yar Baba yana fadin
“Ai tuni wannan ta wuce shiga aji daya dan ta kai shekara goma zuwa sha daya, sai dai a kai ta aji uku idan ma ta maida hankali sosai maimakon ta shiga aji’shida sai ta wuce fom one kawai.”
Malam Bala ya shiga yi masa godiya, Head Master ya dubi Saude da ke tsaye tana zaro ido ya ce “Ke kuma fa lafiya, k0 tare ku ke” ‘
Malam Bala ya yi saurin juyawa yana kallon inda Saude take tsaye
Yasa sallallami ya mike yana fadin, “Yanzu biyo mu ki ka yi ‘yar jakar uba.” Ya fizgo ta yana rankwashi yana zagi.
Head Master ya yi saurin miqewa ya rikeshi yana fadin, ‘Don Allah ka yi haKuri Malam ka kyaleta yarinta ce kawai.” _
Malam yace“Haba, haba yanzu wace yarinta ce wurin wannan iskanci ne dai kawai.”
Head Master ya ce “A’a kar ka ce haka kila abin ne ya bata sha’awa ne hala ita ba ta makarantar neko?
Malam Bala yace, a,a“Ba a sa taba ita talla take.”
Head Master ya ce, “Kai abin nan yana ci mana tuwo a kwarya wai yanzu yarinya kamar wannan a kashe ta a kashe rayuwarta da talla, kullum muna fadakar da iyayen yara a kan su kula da hakkin. ‘ya’yansu a kansu don kiwo ne a gare su Allah ya ba su amma ba saji.
Wallahi mafi yawanci ‘yanmata wurin talla ne suke lalacewa, don a wurin talla ne yarinya za ta saurari maganganun da basu kamata ba. A wurin talla ne yarinya za taji batsar da tunda take a duniya bata taba jin taba. A wurin talla ne yarinya ke sanin abin dake faruwa tsakanin namiji da mace, ba tare da shekarunta sun kai ta sani ba.
Malam idan na soma karanto maka illolin talla sai mu kwana anan ba mu idar ba, sai kun je inda matatar maza suke ka iske mace ta kawo talla kaji
ikon Allah, daga nan sai ka fara ganin namiji ya ci abu ya ce ba zai biya ba yarinya na ta bin sa yaqi ya bayar, kaga ta riko rigar shi sai ya bata ya kwace, ka ga yana gudu tana bin shi daga haka sai kaga kokawa ta tashi, wata rana sai ka same su suna wasan banza da zabgegen saurayi da gandareriyar budurwa mts!” Mts! Yaja tsaki cike da takaici yana fadin.
“Abin dai sai gyaran Allah.”
Jikin Malam ya yi sanyi ya yiwa Head Master sallama ya tisa Saude a gaba suka tafi yana jin wani abu na yi masa yawo a zuciya.
Yana yin sallama a gidan Laure ta yo kan su tana ‘ fadin, “Ina ka samo wannan watsatstsiyar yarinyar? Tun dazu nake nemanta na karade gaba dayan gidan nan bata nan tun dazu na gama waina hatta sandare ina nemanta.”
Ta fizgo Saude dake gabanta tana faman kuka, “Ina ki kaje ‘yar iskar nan? Yawace-yawacen bin ‘ mazan ne naki ya fara k0 Allah ya baki sa,a, wadanda ma suka fiki basu ci riba ba ballantana ke ‘yar ‘ tatsutsuwa, daga ki hura mini wuta ki sa qafa ki fice har in gama wainar ta sandare sannan ki dawo
Malam yace, ‘Gaskiya Laure ki qarasa ido kan yarinyar nan don yanzu Malamin makarantarsu ‘Yar Baba ya rinka gaya mini irin abubuwan da yaran nan ke yi idan sun tafi wurin talla ki rinqa ja mata kunne
Wallahi kar taje ta dauko mana abun kunyar da ba zamu iya saukewa ba.”
Laure: ta ja tsaki tana fadin, “Yo ‘yarinya Ma ta sake ta kwaso abun kunyar ai sAi ta san inda ta nufa, don wallahi korarta za muyi daga gidan sai dai ta nemi wasu iyayen.”
Malam yace, “Gaya mata dai.” Yasa kai ya shige dakinsa.
Laure ta haure ta da qafa, “Tashi ki dauki tallar ki tafi muguwa kuma wlh Batan sisi kikai min sai na ci ubanki cikin gidan nan kin dai san halina ba ni da kyau ba ni da dadi wallahi.” ‘
Saude tana kuka ta duka ta dauki wainar ta fito tana sharar hawaye. A waje su kai karo da Rabi‘u yana ta bunzuma sauri yana ganinta ya nufo ta.
“Saude ina ki ka je ana ta neman ki ba inda ban jeba cikin unguwar nan har kin tada mini hankali.”
Saude tasa bayan hannunta tana goge hawayenta tace, “Ai Baba na bi zaikai ‘Yar Baba makarantar boko shi ne da muka dawo Inna Laure ta doke ni.”
Rabi’u yace, “Toke in ban da abin ki me ya kaiki bin su Baban na dai san ba cewa ya yi ki raka shiba ko?
Taqara share hawaenta tana fadin “Eh, ai nina bisu Yaya ina san makarantar in tafi can yanzu?
Rabi’u yace, “Haba Saude ya za ai ki tafi
kowa sanya shi ake baki ga ita ma Baba ya sanya taba?” ‘ Ta ce, “To, kai ma ka sanya ni yanzu.”
Ya dan yi shiru yana nazarin wasu al’amura, Saude ta riqo hannunshi tana girgiza shi, “Don Allah nima ka kai ni ka ji Yaya?”
Ya tsura mata ido yana kallonta zuciyar shi cike da al’amura masu yawa yasa hannu ya dafa kanta cike da tausayawa ya ce, “Ki yi haquri Saude insha Allahu za ki yi karatun boko, duk rintsi sai na ga kin yi ilimi dole zan cika burin mahaifiyarmu Saude kullum maganarta a kan karatunki ne insha Allahu zan cika mata wannan burin, dole zan nemi kudi k0 dan saboda kek0 dan saboda rayuwarki insha Allahu ba zan bari rayuwarki ta lalaceba, kije tallar
Ki dawo kin ji?”
Kai ta daga masa ya sake ta ta wuce sannan shima ya kama hanya ya yi gaba .
Al’ amarin ya damu Rabi’u matuqa a zuciya yana san Kanwar shi ta yi karatu k0 dan wata rana ta taimaki kanta da kanta, koda baya raye tunda Allah kadai ya san gawar fari. To wacce sana’a ma zai yi yanzu a duniya? Tunanin da ya fado masa kenan, in dai ba ya rinqa’ sana’ar Baban Bola ba, sai dai ita wannan sana’ar dole sai kana da jari a hannu ka rinka tara naka kana siyan na wasu kana
hadawa. Ya ja numfashi sosai yana nazari, can abokinsa Halliru Maigini ya fado masa.
Tabbas shi ya kamata ya nema don yanzu ya tabbatar yana da qarfin da zai iya sana‘ar gini, ya mike daga kwancen da yake ya fito ya yi gaba, yana jin Inna Laure na Kwala masa kira bai kula ta ba, don yanzu yanda yake jin zuciyarsa idan taci gaba da takurawa rayuwarsa gab yake da daukan mataki (Namiji kenan).
Cikin sa’a kuwa yana zuwa wurin abokinsa ya raka shi har “wajen mai gidansa ya amince ya karbe shi ya sanya shi cikin yaransa masu nazari da koyan aiki yace zai rinqa ba shi dari biyar duk safiya, amma ban da ranar da ba a fita aiki ba. Dadi da murna suka kama shi a ganinsa yanzu ya samu sana’ar da zai taimakawa rayuwar Kanwar tasa da ita, don haka har ya qagara gobe ta yi don ya fara . zuwa aikin shima ya ga yana rike naira dari biyar tashi ta kanshi. Mahaifiyarsa ta fado masa a rai, wayyo ina ma tana raye tabbas da ya zamo daya daga cikin ‘ya’ya masu kyautatawa iyayensu.
Kukan Saude ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula ya zabura da sauri ya yo waje, ya iske Inna Laure zaune ta dora qafafuwanta kan ta tana ta mintsini ta ko’ina ita kuma sai ihu take, tana roqonta.
Rabi’u ya jingina da bangon dakinsu yana kallon muguntar da take mata ‘yar Baba ta ruga ta dauko bakin wuta ta mikawa uwar tana fadin, “Karbi ki dake ta Laure.”
Rabi’u ya dauke idanuwansa ba zai iya kallon wannan muguntar ba. Sai da Laure ta tabbatar ta yi mata burdun-burdun da tabbuna sannan ta sake ta ta haure ta tana fadin
‘Tsinanniya ‘yar iska gobe ma idan halin ki ne ki sake Batar min da kudi.”
Saude ta kwaso da gudu ta fada jikin Rabi’u tana ihun kuka ya ja hannunta suka nufi dakinsu, ya zaunar da ita gaban shi yana lallashinta, yasa hannu yana goge mata hawayen, muryarshi a sanyaye yake magana
“Kiyi haquri Saude kidaina kuka kinji insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe nan ba da jimawaba
komai zaizama tarihi,yanzu haka nasamu aiki gobe ma zan fara zuwa, share hawayenki nan ba da jimawa ba wadannan hawayen zasu daina zuba kinji?”
Ta daga masa yana gage mata hawayen ya ce, “To ki yi murmushi mana kobakiji dadin albishir din da nayi miki bane?’
Dariya ta shiga kalkalawa tanayi kamar wata tababbiya shi kanshi har ta bashi dariya ya dungure mata kai yana daria itama tace ala dole saita rama
Hmm mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin yaddah laure da rabiu zasu kaya
Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*