INAAYA CHAPTER 15
Zaune suke suna cin abinci in silence karan spoons da forks kawai kakeji banda aneesah ta ke rike da wayanta tana chatting tana Murmushi chatting takeyi a whatsapp da inteesar tayi saving numbern ta as “ya intee💕” inteesar tayi commenting akan recent pictures din da aneesah tasa a status “keee aneeee ina kika samo pic din nan” dariya aneesah tayi tace “hmm ya intee i dey their house” pictures ne na inaaya da aliyu da ta dauke su na farkon tasa caption “#mrandmrs❤️#” sai second picture din tasa wani caption “OMG! That look😍😫” inteesar ce ta mata reply “please turomun yauwa little sister” da dariya a bakin aneesah tace to karan shigowan message ta kara ji wannan karon mimi ce tace “na baniiiiiiiii aminatu aneeesah ina kika gano wannan kuma” aneesah couldn’t help but laugh har su duka suka juyo suna kallonta na lafiya tace “ohh sorry”
ta ajiye wayan ta ci gaba da cin abinci koda suka gama 3:00 tayi aliyu yace su shirua su tafi yanzu sama kawai inaaya tayi ta dauko veil da takalmi da handbag dinta ta fito aneesah kuwa gyalen abayan ta ta yafa ta dauka jikanta aliyu ya sauko yasa hula black da takalmi black sannan suka fita dukkansu sukayi wurin mota wani bmw ne white color da factory tint aneesah da fauziyya suka nufa baya suka shiga backseat bayan sun gama loading baskets din abincin a boot din motan inaaya kuwa a hankali ta bude gaba ta shiga ta rufe kofan a hankali suka kama hanyan zuwa gidan baffah.
A gaban gidan baffah sukayi parking mota suka fito aneesah da fauziyya ne suka dauko basket daga boot Aliyu dai bai ce komi ba ya shiga gaba ya fara tafiya inaaya na biye da shi a baya suka shiga cikin parlourn gidan ummi ce da khady a parlour suna shigowa ummi tace “ahh a haa sai nake ganin kaman ya’yan nawa ne” aliyu yayi dan Murmushi suka karaso ciki kasa ya zauna a kan carpet ummi tace “kaii habaa dai aliyy tashi tashi ka zauna ya zaka wani zauna haka kaman kazo gaida sirika” dariya sukayi itadai inaaya ta karaso tana rungume ummi itama ummi rungume yar tata tayi sannan ta sama wuri ta zauna suka gaishe da ummi sai ummi tace “neeshasha na ganki da katon basket ina zaki dashi” duk sukayi dariya aneesah tace “uhmm wlh ummi wai girkin amarya ne aka kawo muku fa” inaaya ta harareta ita kam ko a jikinta khady ma tayi dariya tace “wooo dama spags aka dafa mana banaso kuma gashi inajin yunwa banii basket din nan anee muje mu dandana girkin anty amarya inaaya ta bata fuska tace “ummi kin ga ya khady ko ni fa kawai nayi kewarki me shiyasa na yi miki girki na kawo maki” Murmushi ummi tayi tace “kinga kyalesu diyata basuda abunyi ne muje sama ma dai baffahnku na can” aliyu dai zaune yake yana ganin ikon Allah dama haka take da shagwaba muryan ummi ne ya katse masa tunani tace suje sama baffah yana parlour suka tashi suka nufa can sama parlour dinsa suka tarar dashi suka gaishe sa yayi murnar ganinsu sosai kuma da alamu babu wata matsala tare da dayan su ba yaji dadin hakan a parlour din baffah aliyu ya zauna suna dan fira kadan kadan har yake ce masa ina abokinsa dake neman khadyy ko basu daidaita ne ba yaji shiru har yanzu aliyu yace ai yana ganin sun daidaita kila khady ce bata bashi daman yazo ba dan yanata so yazo kara gaishesa baffah yace “ai sakarci kenan ya zaayi ta hanasa to kace masa duk randa ya shirya yazo” aliyu ya amsa ta to sukaci gaba da fira inaaya kuwa dakin mimi ta shiga ta tarar da ita tana bacci ta tasheta mimi tace “aii na sani sai wata ba mrs inaaya ba kullum burinki ki tada ni ina bacci me dadi” inaaya tayi dariya tace “yess ya san ranki” ta tashi ta wanko fuskan ta ta dawo suka fara fira sai lokacin ta kula da kayan dake jikin inaaya sune a jikinta a picture din da aneesah tayi posting ta fashe da dariya tace “aneesah ashe yau ne dan Allah ki turo mani” aneesah tayi dariya tace “haba ya mimi shhh mana it’s our secret” sukayi dariya inaaya ta kallesu tace “me yake faruwa” mimi tace “me fa kawai wani novel ne zata turamun sunan yau akayi publishing dinsa” inaaya bata kawo komi a ranta ba ta kada kai sai ga khadyy ta shigo tace “mimiiiiiii fito da sauri no more eating spags munada lafiyayyen basmati rice da goulash and grilled fish too” da tsalle mimi ta tashi kan gado tace “goulash you said ina aka samoshi” khadyy tayi dariya tace “abincin anty amarya” dariya mimi tayi ta kalli inaaya da ta hade rai da sauri mimi ta sauka kasa ta zubo abincin nata, karfe 4:15 suka baro gidan baffah suka nufa gidansu aliyu suna isa gate me gadi ya bude suka shiga da motan ciki suka fito suka yi cikin gidan kofan a rufe sukayi knocking aka bude Ammah ce suka gani fadada murmushinta Ammah tayi taja inaaya ta rungume tana “my daughter ai tun dazu nake jira naji zuwanku” inaaya tayi murmushi tace “Ammahna i missed you so much” aliyu kallon ikon Allah ya tsaya yi Ammah ko ta kanshi bata bi ba ya karasa kawai cikin parlour aneesah ce ta gyara murya tace “uhmm poor aneesah kullum sai inaaya aka sani” Ammah tayi dariya tace “ahh harda manya kenan” sukayi dariya kafin suka karasa cikin gidan suka zauna a parlour sai a lokacin aliyu ya gaida Ammah ta amsa masa sai aneesah ta tashi ta nufa hanyan kitchen tana cewa “Ammah ga girkin amarya nan zan ajiye maku kitchen” dariya Ammah tayi tace “kaii aneesah ba dama.. haba inaaya miyasa kika wahalar da kanki” tace “kai Ammah babu wani wahala fa kuma su aneesah sun taya ni…. Ammah ina inteesar” Ammah tace “tana daki sallah taje tayi yanzun nan” inaaya tace “to bara naje dakin ina abbahna” tayi dariya tace “ai nasan sai kin nemesa bayanan yana can gidanku tare da daddynki” tayi Murmushi ta gyada kai ta nufa sama, Aliyu ne yana zaune Ammah ta juyo ta kalleshi ta dan fara jan dan nata da fita. Zainabuuuuu where are you fito gani nazo inaaya ta fada tana karasawa cikin dakin inteesar ita kuwa daidai lokacin ta fito daga bathroom ta murna ta karaso tana hugging inaaya tace “anty ineeee sai yau muke ganinki” inaaya ta bata rai tace “wace wata anty wai” inteesar tayi dariya kawai suka fara fira nan sun jima suna fira inteesar tace “uhmm su inee har kin kara wani haske kinata glowing duk amarcin ne” harara inaaya tayi mata tace “intee banson haka fa miye wani amarci mtsww” dariya inteesar tayi tace “eh ai yanzu zakiyi denying after all nagani da idona kuna shan loveeee wani love look da kukewa juna” inaaya tayi tsaki tace “ke wlh you’re jobless intee wai kin gani da idonki” inteesar tace “oya deny it let me see, ina wayana” wayanta ta jawo ta shiga status ta bude na aneesah tace ga proof nan inaaya kuwa baki bude take kallon picture din ko baa gaya mata ba tasan aikin waye tace ” what the heck wannan yarinyan na wasa da ni let me go and get her” da sauri inteesar ta tashi ta tareta tana “miye hakan inee mi tayi kawai dan ta dauka picture as it is ai ba haramun kukayi ba ko” inteesar ta dinga danne inaaya har tayi hakuri suka ci gaba da fira har sai wurin 6 saura aneesah ta shigo dakin tace “ya inee uncle aliy is calling you yace muxo muje gida” ai kuwa inaaya kaman jira take ta taso ta rike kunnen aneesah tana murdewa tace “zaki kara” aneesah kaman zatayi kuka take tambayan ta me inaaya tace “snapping and posting a picture of us” aneesah tasa dariya sai da tayi me isanta sannan ta shiga bata hakuri duk suka gama sannan suka sauko kasa Ammah ce kawai a parlour sukayi mata sallama ta rugume inaaya sun dade kafin ta saketa suka yi waje inda suka tarar da aliyu a cikin motan suka shiga suka wuce gidansu inaaya da ko 10minutes baayi ba suka isa, aneesah da fauziyya suka dauka sauran basket sukayi cikin gida inaaya dai har da saurinta taga mamii tana shiga suka tarar da mamii pa
rlour da twins a guje sukazo suka rungume inaaya ayman na cewa “ya inee we’ve missed you so much ya aneesah is not being nice at all” hugging dinsu tayi back tana patting bayansu kafin ya sake su ta karasa ta fada kan mamii tana hugging dinta tace “my mamiii i miss you so much” harda dan guntun hawayen ta mamii tayi dan murmushi tace “ke dillah can dagani babba dake kike shagwaba” daidainan aliyu ya karaso cikin parlour twins sukayi kanshi da gudu suna rungumewa suna kiran “uncle aliyyyyy” Murmushi yayi masu yace “hey champs! Kuna lafiya” suka amsa masa da eh ya karaso ya zauna kasa a carpet yana gaishe da mamii tayi Murmushi tace “lafiya lau son shine zaka zauna kasa kaman wanda yazo gidan sirikai kaida gidanku haba tashi mana” Murmushi yayi ma mamii ita kuwa inaaya tsit kake jinta kaman an dasa ta. Ya jima a gidan duk da daddy ya fita da abbah suna zaune da sa’id suna taba fira sai kuma twins da ke ta bashi labari saboda sunayi da shi, sai bayan magrib ya bar gidan yana cewa zaya dawo ya dauke inaaya yana fita direct gidansu fareed ya nufa cikin gidan ya shiga ya tarar da mahaifiyarsu a parlour da kanin fareed, Abdurrahman gaisawa sukayi da aliyu sosai sannan ya gaishe da mahaifiyarsu its amsa masa da fara’a tace “ahh yau ango ne a gidan namu to ya akayi baka kawo mana amaryan mun gani ba kaman kana fushi da mu” Murmushi aliyu yayi yana sosa kai yace “habaa Aa mama ba haka bane tana gidansu Amma InshaaAllah zani kawota” Murmushi tayi tace “to madallah” yana nan zaune suna dan fira da Abdurrahman sun jima kadan sai yace bara yaje gun fareed haka ya fita ya nufa part din fareed inda ya tarar dashi daki kwance kan gado ya lumshe ido baima ji karan kofan ba dan waya yakeyi ji fareed yayi yace “No! My love please stop this kind of talk cux I don’t know what will happen to me without you, Khadija you’re my life my blood my everything I cannot live without you please don’t ever leave me no matter what please” aliyu dake jikin kofa tuni jikinshi yayi sanyi kafafun nasa ma sun kasa daukansa saboda jaan dinsa daya tuna zuciyansa ke bugawa ga zafi da take masa kafafunsa kasa daukansa sukayi ya ji shi kasa, fareed da hankalinsa baya wurin yaji kara da sauri ya juyo sai yaga aliyu a kasa da karfi ya furta “subhanallah Aliyu meya sameka” dayan bangaren jin abunda fareed yace yasa khadyy shiga damuwa tace “meya samu ya aliyu” da sauri fareed yace mata “ina zuwa I’ll call you back bawani abu bane” ya kashe wayan yayi kan aliyu ya taimaka masa ya tashi ya kaisa wurin gado ya zauna sai ya bude dan karamin fridge din dake dakin nasa ya jawo ruwa ya mika masa aliyu ya karba yasha sannan fareed ya fara magan yace “lafiya me yasa meka ka fadi” kada kai aliyu yayi yace “babu komai” fareed yace “no you can lie to everyone but not me is it about lailah” da mamaki aliyu ya juyo yana masa wani kallo sai fareed yace “i knew it! But Aliyu why? Meyasa do you think da tana nan she’ll be happy seeing you like that why can’t you accept fact and move on qadr destiny believe it for god sake yanzu you’re not only ruining your life but the poor girl’s life you’re married to do you think she will be happy living with you like this” Aliyu shiru baice komai ba dan yasan da gaske fareed yake sai can yace “fareed I believe in destiny and I’ve accepted it just that she’s irreplaceable and i have no space for love in my heart and it’s not my fault I don’t choose to feel the way I feel fareed now tell me! You love Khadija right what will you do when she leave you what! Fareed tell me!” Aliyu yayi maganan da karfi nan da nan jikin fareed yayi sanyi zufa ta fara keto masa sunfi 10minutes shiru sai can fareed yace “Aliyu I’m not saying you’re wrong i just want you to be happy yes I know it hurts beyond explanation and it’s not only you her loss is affecting but every is trying hard to surpress it think of it you’re stronger than this think of you poor wife fatima! What do you think she is and will be going through because of this, you can do it just open up to her and let her in you’ll never regret it she’s your wife now your completion and even your younger sister you should take care of she deserves happiness” tsit Aliyu yayi yana tunanin maganan fareed he’s right she’s always sad duk sanda yake ganinta but today with her family she was happy and smiling but then he can’t do anything about it he himself is not happy how can he give someone happiness, yanata tunanin nan har can a hankali yace “fareed even i am not happy with the way things are going but I can’t help it it’s hard I can’t give her happiness when I’m not happy” Murmushi fareed yayi yace “then find happiness in her and give her the happiness Aliyu! I know it’s so hard but trying a bit won’t hurt just put an effort, the girl can’t even have a proper conversation with you without stammering she’s scared of you that’s why she’s not happy around you I’m not telling you to love her or something be her friend, her older brother, her father and her mother I’m certain she’ll be free with you and things might change the way you don’t expect” kada kai aliyu yayi alamun amincewa yace “ohhhk fiine I’ll try thank you so much” Murmushi fareed yayi masa sai yace “uhmm let me call my life she’s worried” dariya aliyu yayi yace “ayita wani my life my love to mu gani a kasa” fareed yace “kar ka damu ai zaka gani data bani izini” Aliyu yayi dariya yace “uhmm sai ka jira din…ni ai bakasan ma mi ya kawo ni ba yau dinnan da goodnews nazo ma” gyara zama fareed yayi yace “ohhhh har na kosa please gaya mani” Aliyu yayi dariya yace “ai dazu naje gun baffah ne yace mun kana ina ko baku daidai ta da mutuniyar ba nace ai kun daidaita kila itace bata baka izinin zuwa ba yace haba wannan ai sakarci ne ya zatayi ta hanaka to duk rannan da ka shirya kazo” fareed daya zaro idanu yace “kaiiiiii gaya mun ba da wasa kakeyi ba” Aliyu yayi dariya sosai yace “ni dama ina wasan nan ne” tashi fareed yayi yaba aliyu manly hug yace “wow you have no idea how happy i am thank you so much you’ve made my day no kai my entire life ma bari nayima babe Albishir” Murmushi aliyu yayi yace “lallai albishir in me bayan ita ta hanaka” yace “hmm bazaka ganeba khady da kunya All this while wai ita bata iya gayama ummi zanazo wurin baffah saboda kunya kar ace kiri kiri take cewa aure takeso shiyasa wai tace na jira sai baffah ya mata maganan” Aliyu yayi dariya yace “wow! Na zama super hero to nayi saving rayuwan lovers” dariya sukayi a tare sun jima suna fira wurin 9 Aliyu yace zaya tafi fareed ya rakosa har parlour zayayi ma Mahaifiyarsu sallama nan ta tsare shi ta mishi nasiha kan ya kula da matarsa nasiha mai shiga jiki har jikinsa yayi sanyi a haka ya fito ya shiga mota ya hau hanya, gidansu ya fara zuwa ya tara da Abbah ya dawo sun dan jima suna magana sannan yayi masu sallama ya nufa gidan daddy ya dade a mota ya rasa yanda zayayi yana tunani ya jima ya fito ya shiga gidan ya tarar da daddy a parlour sun yi kusan 10minutes kafin daddy yace “dare nayi fa yakamata ku tafi aliyu” shi kuwa dan sosa kai yayi daddy yayi Murmushi yace ma twins su je su kira yayartasu, A bangaren inaaya ba dan taso ba haka ta fito kyar da dan kwallanta zasu tafi ta yi hugging ya Sa’id da daddy kafin ta sakesu ta nufa hanyar fita duk su aneesah sukayi masu rakiya ta shiga motan tana daga masu hannu har motar tasu ta bar wurin, tsit kakeji babu mai magana a cikin ita da aliyu can dai after so much contemplation aliyu yayi gyaran murya yace “uhmm hope you enjoyed your day” inaaya kuwa maganar tasa a bazata tazo mata har wani rawa jikin ta yakeyi tama rasa me zata ce saida tayi gathering courage tace “la..la..lafiya qlw” kada mata kai kawai yayi a cikin ranshi yake tunanin maganan fareed gaskiya ne she’s scared of him a haka ya ci gaba da driving yana tunani can kaman wanda ya tuna wani abu ya taka burki ya tsaya ta gefen ido inaaya ke satan kallonsa taga ya jawo wayan sa yayi danne danne sannan ya ajiye ta ya kara volume a hankali ta kalla wayan taga a google map yake yasa location bata ga dai destination din ba tayi shiru batada bakin magana yaci gaba da driving har sai da ya isa a bakin chicken capitol dake a wuse 2 yayi parking ya juyo ya kalleta yace lets go a hankali ta juyo ta ga in shi ya
yi maganan idanunsu ya hadu da juna suka kasa breaking eye contact din suka shiga kallon juna kowa da abunda ke ransa.
Saida suka dauki kusan 2minutes lost in looking at each other sannan aliyu yayi saurin juya kai yace “uhhmm shall we” sai a lokacin inaaya tayi kasa ta kai ta bude motan a hankali ta fito a ranta tana mamakin chanzawan Aliyu a haka side by side suka shiga ciki amma daka gansu ya fita tsayi nesa ba kusa ba but they look so perfect together shawarma yayi placing order har tambayan ta yayi yanda takeso tace chicken and sausage with extra garlic and pepper suka zauna cikin 10minutes aka gama aka kawo masu suka fita suka koma mota ya fara driving nan da nan suka isa gida shi ya dauko ledan ya shiga da ita a kan dinning table ya ajiye ya nufa sama itama inaaya kawai sama ta nufa daki ta cire kayan jikinta ta dauro towel ta shiga toilet tayi warm bath ta dan jima sannan ta fito ta gama shirinta cikin pyjama’s red color tasa wani black hula ta dauki dogon hijab dinta tayi sallah sannan ta zauna gefen gado ta jawo wayanta ta fara danne danne, wanka aliyu yayi shima yasa wani jallabiya fara tas ya fito parlour amma wayam ba kowa yaga ledan da ya ajiye untouched ya girgiza kai yana mamaki hali irin na inaaya a ransa, yayi sama ya nufa dakinta ya manta da wani knocking ya bude dakin tana zaune hankali kwance ya kalleta sannan yace come down now, jiki na rawa tabi bayansa yana fita ta sauka kasa lokacin yana zaune a parlour ta ja ta tsaya ta dauka dan lokaci kafin tace “umm whh..whaat do you want” shiru yayi sai ya samu kansa da cewa coffee kaman tana jira tayi sauri ta nufa kitchen har ta kusa faduwa saboda tsayin hijab din ta cikin kankanin lokaci ta hado masa coffee ta dawo parlourn ta ajiye masa a side table ta juya zata tafi yace “who’s going to eat what you ordered” cak ta tsaya dan a yanzu ma yunwan nata ya tafi ta tsaya bata juyo ba yace “am i not talking to human” da rawar jiki zuciyanta na dum! Dum! Tace “eh..ehh.daa..daa..ma zanci ai” kallonta ya tsaya yi yana mamakin yanda take stammering da wata irin murya a hankali me ratsa jiki yace “please fatima I don’t bite you don’t have to be stammering” ai kaman anyi tripling dukan da zuciyan nata keyi saboda yanda muryan da yayi amfani dashi ya shigeta ta kasa cewa komai saboda halin data shiga, sai ji tayi yace sit a hankali ta zauna a kujeran dake opposite him yaci gaba da magana “i know you barely know me even though I’m your brother but I don’t bite people you don’t have to be scared of me I’m a normal human being just forget about any marriage thing i am your brother and you can freely talk to me,gist or even ask for advice and on top of that we can be friends too since we are housemates now we share the same house so we can be friends and you know older brothers too can be your friends” magana yake da mamaki take kallonsa yanda akayi yake mata magana ma har yace they can be friends cux batayi expecting hakaba but still ta dan samu relieve a ranta but still she was hurt yanda yayi addressing din relationship din nasu as housemates yanzu haka zatayi rayuwanta duka tare da shi as housemate kaman tasa hannu a kai ta zuba ihu haka taji amma babu yanda ta iya haka ta dan kakalo Murmushi tace “yess thank you” dan Murmushi yayi mata yace “ohhk now get us the shawarma I’m hungry” mikewa tayi ta dauko ledan da mamaki a ranta dama haka yake har ta dawo parlourn they ate in silence suka gama tana nan zaune ta kasa tashi duk da tana so ta tafi daki dan she’s feeling awkward amma shi kuwa Aliyu normal ya dan fara janta da magana yana tambayanta a kan school din nata da dreams dinta da short answers tayi ta masa reply har 12:00 tayi sannan yace taje ta kwanta sum sum ta tashi ta nufa dakinta tana shiga ta fada kan gado bayan ta cire hijab din nata still da mamakin canzawan na Aliyu da kuma bakin cikin kalma housemates din daya furta kawai sai sharr hawaye suka zubo mata a ranta tana tunanin wace irin rayuwace wannan ba haka take dreaming married life dinta to be ba a haka har bacci ya dauke ta.
Two weeks later*
Yau Saturday ya kama three weeks into their wedding zuwa yanzu inaaya ta dan sake da aliyu ba laifi saboda shima yana trying yaga ta zama comfortable with him and free saboda kar ya ruguza mata farin ciki, to zaman nasu Alhamdulillah dan ba laifi suna magana sosai yanzu har mamakin abun inaaya takeyi. a satin daya wuce fareed ya je ya gaida baffah sannan baffah yace masa ya turo iyayensa azo ayi maganan auren farin ciki sosai har kasa rufe baki fareed yayi da matukar farin ciki ya kwana a ranan sannan kuma ya sanar da mahaifinsa da yayi farin ciki shima sosai aka saka ranar zuwa nan da sati biyu, A bangaren ya habeeb da mimi kuwa relationship din nasu sai karfi yake karawa duk da akwai obstacles na kowane relationship but they’re moving smoothly. Inaaya ce tsaye a kitchen gaban coffee maker tana kokarin gama hada coffee, sanye take da wani dogon riga na atamfa yayi mata kyau ta dauka cup din data tsiyaya coffee a ciki ta nufa sama zuwa dakin Aliyu knocking tayi sannan ta bude kofan a hankali a shiga Aliyu na kwance a kan gado alamun yanzu ya tashi bacci inaaya tace “good morning coffee is ready” da dan Murmushi a fuskan ta shima dan Murmushi aliyu yayi kadan yace “ohh morning little sister thank you so much for the coffee sis” kada kai tayi sannan ta fita ta koma kitchen ta cigaba da hada breakfast pancakes take making sunyi kyau so fluffy, bayan ta gama hadawa ta kai komi dinning ta gama kenan Aliyu ya sauko da dan slight Murmushi a fuskan sa ya nufa dining sukayi breakfast din nasu in silence yake tambayan ta yaushe zasu koma school tace in two weeks ya ce “ohhk good nima I’m resuming work in two weeks and Abbah yace banda next week na gabanshi on Thursday zamu koma InshaaAllah” inaaya tace “Allah ya kaimu ya bada saa” da dan Murmushi ya amsa mata da “Amin little sister” itama dan Murmushi tayi suka kammala cin abincin nasu in silence ta kwashe komai ta nufa kitchen duk ta wanke ta fito ta tarar aliyu ya koma daki parlour ta zauna tana kallon 90 days fiance on TLC. A daki aliyu ne zaune a bakin gado rike da wayan sa gallery ya shiga wani folder daban ya shiga da saida yasa password ya bude hotunane masu yawan gaske na lailah jaan ya shiga kan daya yana shafa fuskan nata ya fara fadin “jaan today i woke up with you in my mind i miss your presence i love you so much my life is difficult without you no matter how hard i try I can’t be normal even tho for the past few weeks i have been trying to take fareed’s advice but it’s hard sometimes I just want to scold the girl for no reason cux I don’t want her presence I only need you and your presence jaan but..but you left me whyy…” duk muryansa na rawa yake maganan yayi dan pausing sannan yaci gaba “jaan why why did you make me love you so much when you know you were going to leave me whyy whyy” zuwa yanzu idanun nasa sun kada sunyi ja yace “I don’t know what to do cux I can’t keep up with everything i know I’m going to fail abbah and I’m going to hurt Ammah even daddy he’ll be hurt but will try to hide it mamii she will still hug me and call me her son despite the fact that she’ll be broken because of me and baffah he will be super mad at me and fareed will surely stop talking to me because of what my mind is telling me and want to make me do, jaan I’m thinking of divorcing their daughter cux I can’t make the girl happy and she deserves happiness i can never look at her as my wife never! But then I’m still thinking of what will happen if I divorce her I’m sure Abbah can disown me for that cux I’ll be a failure to him and i never wanted that jaan please help me I’m feeling like I’m a garbage I don’t want to inflict pain on my parents but I can’t do what they’re expecting me to I can’t live with her as a wife I can’t love her I can’t” hawaye kadan ya silalo daga idon nasa yasa finger ya goge ya cigaba da kura ma hoton ido kaman me son ya gano wani abu haka ya jima zaune a nan.