ABAR SO CHAPTER 3 BY NAFISAT MA’ARUF SHEHU💋(WURARH)💋

ABAR SO CHAPTER 3 BY NAFISAT MA’ARUF SHEHU💋(WURARH)💋

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tsantsan ranin hankali da rashin sanin darajar dan Adam harni zanmawa wannan 100 missed calls amma tarasa miye zatamin Sai flashing 1 tak” yafara yana mai nuna Hasana da bacin rai kwance asamar fuskarshi+

“Wlhy bangani bane shiyasa ban dauka bah kuma lokacin dana kiraka network ne yasa ya katse amma ba dagangan naki dauka bah” Hasana tafada cikin sanyin murya, har lokacin bai sake look din face dinshi bah

” Dallah Malama kirufe mana baki don kinga inasonki ne shiyasa zaki walakanta ni ba damuwa ai naga bake kadai ce mace bah kuma aurenkin ma na fa…”

“What da hell!!!” Ta katse shi

“Nace maka ban gani bane ai  dana gani dana dauka and ka tsaya kana fadamin magana, and kuma inka fasa aurena din so fucking what,ko cemaka nayi na  rasa mashinshine  wlhy ko ranar aurena kace kafasa I can assure that bazan rasa wanda zai aureni aranan bah, ina ma maka magana cikin sanyi Sai botsarewa kake ai……”

“Calm down guys” Nadhira ta Katse ta, shikuwa ido yazuba wa Hasana cos azatonshi zata bashi hakuri ne komai yawuce amma Sai yaga sabanin hakan, shikam Amin banda mamaki babu abinda yakeyi

“Wato har Abdul yasaba dasu haka harda cewan zai fasa aurenta, lallai abin nasu azimun neh” ya raya azuciyar shi, itakam Hasana tuni hawaye yafara sauka a idonta, dagudu tabar wajen tana mai fashewa da kuka duk Sai jikinsu yayi sanyi

“Hey bestie!!!” Nadhira takira ta tareda binta da gudu zuwa cikin gidan, taba kafadar  Abdul  Amin yataba tareda sakar mishi da murmushi shikuwa da yake yamiyar mai, cikin part dinsu Abdul zaishiga  Amin ya dakatar dashi yana mai janshi zuwa nasu part din…

“They need some space” shine abinda Amin yafada bayan sun zauna

“You guys love each other fah!!!, Yaushe kuka hadu” Amin yasake fada,nan kuwa Abdul ya zayyana mishi haduwarsu

” It’s prayer time, in munyi sallah muje ka gaisar da Dadyn Nadhira”

“Ya dawo hayyacin shine?” Yafada cikin mamaki

“Wlhy you need to meet that great man with the big heart” yafada yana murmushi, Shima dai murmushi yayi batareda yasan inda maganar ya dosa bah…..

“Besty!!!kukan kuma na miye??” Nadhira ta tambaye ta

” Miyesa zai karyata ni ?? Wlhy bakarya nake mishi bah” Tafada cikin sanyi murya

“Do you love him??”

” Yanzu kuma  dayace yafasa aurena miye zanyi?” Tafada cikeda damuwa

” Ana so ana kaiwa kasuwa ,wayace miki dagaske yakeyi?”

” Eh mana he looks so serious”dariya Nadhira tasake hade da tashi daga zaunen da take, cire dankawali kanta tayi ta’ajiye shi gefe

” I’m very sure he was pulling your legs and nothing more” tafada tana shigewa bedroom dinsu cos bataji muryan su anty bah

” I pray so” shine abinda Hasana tafada cikeda farin ciki

“Ina Dadyn yake ??” Hasana ta tambaya cikin daga murya ,chan saiga Nadhira tafito

“Shiga kiyi Alwala muyi sallah”

“Am pointing red fah” Hasana tafada

“Ohk” tana idar da sallah tacire zanin da ta daura

“Muje”tafada wa Hasanan dake game awayarta….

“Babynmu!!!” Taji ankirata kuma tasan bazai wuce Salim bah

“Naga surprise din da kikace zaki nuna min”yafada yana murmushi

“Oops!!!”tafada tana shafa gashin kanta ga ta yamutsa fuskanta, dariya yake mata harda gwalo cos ba haka taso bah

“Catch me if you can baby” yafada yana girgiza mata bumbum dinshi tareda  guduwa aiko cikin zafin nama tafara binshi dagudu ,Sai tazo dab dashi zai sulale , Hasana kuwa Sai dariya takeyi harda zama akan daya daga cikin chairs din wajen,nan kuwa ashe su Amin mah suna kallonsu,itakuwa ta dage Sai binshi take yi cos girgiza bum bum din dayayi neh ya tunzirata ga gashin ta Sai tsale yakeyi ta bayanta harta mai gadi kallon baturiya  yakeyi sbd alokacin tacire jacket dinta hango maigadi da yake kallonta Amin yayi ai kuwa wani abu yasoki zuciyar shi…

Tsawan da aka dakamata yasasu tsayawa cak nan da nan kuma hawaye yafara sintiri afuskarta…

“Ke jakar ina ce??” Yatambaye ta cikeda bacin rai daidai lokacin da ya isa wajenta

“Baki da hankali ne?” Yasake jefo mata tambaya, juyawa takeyi don tabbatar da muryan wanda yake zaginta ai kuwa taga babu kowa Sai masoyinta

“Ke!!!” Yakara daka mata tsawa, wani kuka mai tsinka zuciyar mai sauraro tasake cos zagin yashigeta amma ainihin bazallan zagin yasata kuka bah,magana take sonyi amma kuka ya hanata nan da nan jikinshi yayi sanyi.

Kukan da Salim yashiga dashi ne yafito dasu daga cikin gida harda Dady acikin wheel chair dinshi cos suna ta tambayanshi amma bai amsa bah Sai nuna musu waje dayake yi azatonsu wani mumunar abu yafaru shiyasa suka garzayo,abinda suka ganin ne yasasu yin turus, ido Hudu dasukayi da Antynsu neh yasata ruguwa wajenta

“Kya uwah?? Anty ta tambaye ta hade da bin jikinta da kallo

“Tell him abinda banaso” tafada tana nuna shi da yatsa

“Nace miki miye faru?” Anty tafada hade da rike ta cos she’s so scared kwata kwata bata son ganin abinda zai bata musu rai balle azo ga zubar hawayen su 

“Tsawa yamin Antynmu, kifada mai tinda nake arayuwata ba’a taba min tsawa bah , kifada mai natsani tsawa balle wanda yake yinta ,Zan iya mai rashin mutunci ba bu ruwana da inasonshi ajiye soyayyar zanyi agefe na mishi rashin mutunci which bazaiji dadin shi bah kuma Allah yagani that will be the least thing din da zanyi, gwanda yakiyaye cos bana barin bashi kema kinsani” tafada hade da barin wajen

“Babynmu kiyi hakuri bazan kara bah” Salim yafada ganin wajenshi ta nufo, amma still bata daina nufanshi bah while shikuma naja da baya,hawayen da tagani a idonshi yasata tsayawa cak,aiko yana ganin ta tsaya ya ruga ya rungumeta

“I hate  that Salimu nah” tafada hade da goge mishi hawaye

“Am so sorry Babynmu I don’t that it will hurt you”

“Don’t do that again okay?” Gyada kanshi yayi

“Good boy” tafada hade da tashi ta wuce cikin part dinsu, banda na mujiya ba abinda suke dinsu dashi while kowa na mamakin abinda yafaru atsakanin su, Hasana ne kawai tasan abinda yafaru

“Allah sarki” shine abinda  tafada azuciyar ta ,shi kam Amin gabadaya ya damu da cos shi baisan bata fushi bah

“AL-AMIN!!”Dadyn su yakira shi bayan sun gama gaisawa da Hasana harma tashige abinta cos kowa yabar wajen Dady ne yace abarshi cos ya Lura da yanayin Amin din. Karasowa cikin sanyin jiki

“Ya akayi baka san abinda bataso bah??” Cikin sanyin murya yake fadin

“Bata taba fadamin bah” murmusa Dadyn yayi

“Tin yanxu jikinka yayi sanyi??, Amma kasan tanada riko??”

“A’a Dady”

“Yadda ta tafinnan yatabbatar bazata sake maka magana ba Sai after a month” arazane yadago yana kallon Dady

” DanAllah Dady katayani rokonta kozatayi hakuri, in tadaina min magana bansan yazanyi da arayuwa na bah” yafada  cikin rawar murya

“Ai haka halinta yake, ko kasan yar’uwarta?? Dady yatambaya

” Kaga duk son da take mawa yar’uwarta toh koya suka samu sabani toh ta daina mata magana kenan!!, Soboda haka just let her be for now cos duk abinda zaka fadamata bazai yi tasiri akanta bah soboda bata barin bashi”

“Au daman abinda take nufi da bata barin bashi kenan??”

“Kwarai dagaske”

“Hmmm”

“Ka kwantar da hankalin ka soboda kasan ance mai Hali bai fasa halinshi”

“Ok Dady amma tasani wannan hukunci nata yayi tsauri dayawa”dariya kurun Dady yayi…….

“Besty!!”

“Miye”

“Akan kawai yamiki tsawa kikayi wannan kukan ko kuma there’s more to it??”

“Idan natina da babu hanyan dazanbi inbar gidan nan zuciyata kuna yakeyi sosai amma Kuma kinsan abinda yayi is not fair,miye na mishi daxaimin irin wannan tsawa? ”  Ta tambaya cikin sanyin murya

“Nima gaskiya abinda ban gano ba kenan”

“It’s okay”

“Does that means kin hakura??”

“I don’t know cos nasan in yayi gigin min magana I may disgrace him soboda har yanxu inajin karar tsawan dayamin”

“Allah yakawo mana da sauki”

“Ameen”

“Barina mawa Antynmu sallama”tafada hade ficewa….

“Miye zai mata dazaice tazo??”shine abinda Anty ke tambayan Dady cikin sanyin murya ga idonta harya kawo ruwa…

“Toh miye don ya bukaci tazo?? Shima fah amatsayin uba yake  awajenta karki manta” Dady yafada

“Yadda Nadhira bata kaunar shi anya zataje kuwa kasanta da taurin kai” antyn tafada tana share hawayen ta

“Why not aji ta bakinta tukunna”mumy tafada

“Hakane kuma fah” Abba yafada,ganin Hasana yasa Dady aikanta Kiran Nadhira,cikeda sanyin jiki takirawo Nadhira….

Ganin su atsatsaye yasata yin turus

“Karaso baby” jin muryar Antyn yasata karasawa wajen ta dasauri , face dinta ta rike

“Miye sameki Antynmu??” Ta tambaye ta cikeda da damuwa soboda itama bakaramin so takewa antyn nasu bah

“Big Dady neh yace yakamata kizo” wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska  tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen….”Big Dady neh yace yakamata kizo” wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska  tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen+

“Nima kashe ni yakeson yayi kenan??” Wani munafikin hawaye tashare harda Jan hanci sannan tacigaba

” Ba damuwa zanje yanda yabukata amma inhar ban dawo da raina bah ina rokon kowanne daga cikin ku ya yafe min!!!” Tana gama fadin hakan  Sai tayi cikin gida da gudu

“Kutimelesi gaskiya baby drama queen ce taab”shine Hasana ke fadi acikin ranta

“InshaAllah babu abinda zai mata, Hasana ki bita cikin gidan koh” Dadynsu yafada wa Hasanan,dama kuma abinda take jira kenan amma Sai tace

“Daman fah Zan muku sallama ne cos naga dare nayi kuma ana rasa abin hawa anan”tafada hade da kallon Abdul ta gefen ido Sai akayi sa’a Shima din kallon nata yakeyi

“Ga Abdul Sai ya kaiki in kinshirya tafiya”mumy tafada cikeda jin kunya take fadin toh kafin tabar wajen,daganan babu kuma wanda yasake magana  cos kowa da abinda yake sakawa aranshi

“Amma Allah yayi munafika anan”Hasana tafada lokacin da taci karo da Nadhira tana rawa

“Am extremely happy besty, daman yanda za’ayi nafita nake nema gashi da kanshi ya gayyato mutuwar shi”

“Bangane mutuwar shi bah” Hasana tafada afirgice

“Ke kinsan miye ake Kira da kisa kuwa,kinsan hunkuncin wanda yayi kisa amusulunci kuwa toh let me tell you in baki sani bah duk wanda yakashe wani tabbas Shima kashe shi Za’ayi, koh kina son akashe ki kema??”

“Toh shima ai naga har rayuka biyu yakashe arana daya ba’a mishi komai, koh hakan na nufin yaci bulus kenan??”

“Sakkayyar Allah fah wani Babban abu ne in bai gani aduniya ba ai in ya hantaya lahira zai gani,amma pls karki ce zaki kashe narokeki cos bazamu so jini yahau kanki bah please” Hasana tafada cikin sanyin murya

“It’s okay bazan kashe shi bah amma gaskiya bazan kyaleshi bah,zan bashi live to remember”

“Ohk ,nizan tafi”

“Jirani nakwashe kayana saimu tafi tare”haka ta tsaya har tagama kwashe kayyayakin ta  sannan suka fita.

Ganin dasukayi  Nadhira tafito da kayyayaki yasasu sauke ajiyar zuciya cos har Big Dady yasake Kira akan lallai taje ranan.

“Zantafi “Nadhira tafada

“Allah yataimaka and behave your own self there” Dady yafada

“InshaAllah” sannan tarungume Antynsu harda Sumba tabawa Antyn a cheeks dinta

“I will miss you Antynmu” tafada tana mai share guntun hawayen ta all the same time tana share hawayen antynsu,sanda kowa agurin yaji tausayin su dakuma jinjina irin soyayyar dake tsakanin su biyu cos in ba’a fada bah you will think she’s her sister  nan kuwa amatsayin uwa Antyn take awajen Nadhira

“Allah yabiya ki da gidan Aljanna amaryata” Dady yafada acikin aranshi cos yasan dawata daban ne amaryan nashi to ba makawa yarshi tashiga gari amma ji yanda take nuna tsantsan so ga gudan jini Nargis dinshi daya rage

“Take care of yourself Baby” Antyn tafada

“InshaAllah” Salim tagani yakura mata ido, Sai asannan mah ta ganshi ahankali takarasa inda yake ga idonshi yayi raurau ,tsungunawa tayi agaban shi

“Hey why do you look sober??” Ta tambaye shi (yafi jin turanci akan Hausa)”

“I’m gonna miss you our baby”yafada hade da rungumeta

“Calm down I will be back it’s a matter of my troby Salim and I will also miss you dear” tafada tana breaking hug dinsu sannan ta tashi, juyawan ta keda wiya taga Amin yanufi gurin mota da trolley dinta alaman shi zai kaita

” Antynmu!!! I love you so much”tafada da dan karfi cikin sweet slim voice dinta daidai ta isa wajen motan Abdul

“I love you more dear”Antyn ta amsa ga murmushi kwance asamar fuskarta cos itama Nadhiran murmushi takeyi,

(Toh gareku matan da suke kishi da yaran miji,wasu kam ma a idon miji zasuyi behaving normal Wato mai two face kenan wasu kuma they don’t care… Toh bari Kiji daga lokacin dakika fara hantaran yaran kina nuna kishin ki karara akan yaran agaban shi  toh in yana miki 100% So  toh ki tabbatar zai dawo 40% cos bada yaran yakamata kiyi kishi ba da uwansu yakamata kiyi idan kuma bata raye kuma saiki ajiye kishin ki  agefe ki Kula marayu. Ke kuma mai two face kina nuna musu so agaban miji dazarar ya fita Zaki fara musguna musu toh billahi lazi in yazo yagane toh in son dayake miki

100% ki tabbatar ko 15% sonki azuciyarshi baizai sake haurawa kuma kinyi loosing kimarki darajarki da kuma mutuncin ki a idon cos koda kin daina mawa yaran abinda kike musu still zai dauka as pretending kikeyi.  In anzo kuma kice kinason mijinki ko kin manta Suma daga jikin mijinki suka fito neh hala?? In kikaso su tsakanin da Allah zai daukaka kimarki ,mutuncinki da soyayyarki acikin zuciyar mijinki bama shi kadai bah harda yaran nashi cos bazasuyi kukan uwa bah. In bakiso su bah kuma kinason babansu me kikayi kenan ??wannan shi ake Kira da naughty work.Wlhy yaran ma bazasu na kallonki da daraja bah kuma daga karshe suyi sanadiyar mutuwar aurenki da baban su!!! DanAllah mata akiyaye cos  yana daga cikin matsalolin da ake fuskanta ayanzu)

Mamakine yakamashi ganin motan Abdul tanufa bacin kayanta na motan shi

“Jeka fito mi da kayana acikin wancan motan kafin raina yabaci” tafada lokacin data shiga bayan motan

“Ohk ma” Abdul yafada cikeda da tsokana

“Kai miye zakayi??” Amin yatambayi Abdul dake kokarin bude boot din motan shi

“Spare me Aika nazo dauka” yafada yana fitowa da ido waje,haka yagama daukan trolley din sannan ya rufe boot kafin ya bar wajen, haushi kuma kaman ya kashe shi ganin irin abinda tamishi agaban jama’a.

“Ba laifin ki bane”yafada underneath his breath.

“Arrange my meeting with those guys,i will be in your area in no time”shine message din daya shigo wayanshi cikin gaggawa yayi dialing din wata number

“Ya akayi ne??” Shine abinda aka fada  cikin wata katuwar murya daga dayan side din wayan

“Cewa akayi kuzo yanxu”

“Ohk gamu nan zuwa” shine abinda mai katuwar murya yafada.

Cikin motar dasuke babu wanda yayi magana, Nadhira ne ta katse shirun dacewa

“Kafara dire Hasana cos zanmawa ummi sallama”

“Toh matar yaya” Abdul ya amsa mata,suna isa daidai kofar gidan  Nadhira ta sauka daga motan Sai ya rage daga Hasana Sai Abdul amotan,instead of tayi cikin gida sai tabiye wani hanya daban

” Aturo gidanmu sbd susan kafasa auren yarsu” Hasana tafada kaman bata damu bah at the same time tana kokarin bude motan domin fita.

Cak ta tsaya dalilin rike hannunta dayayi

“Haba Hasynah!!!”

“Nibah Hasynka bace” tabashi amsa a hasale

“Ohk Hasyn matar yaya”

“Better”

“Am so sorry,i never mean my words, kin ban haushi ne shiyasa am sorry,taya ma kike tunanin Zan iya rayuwa babu ke acikin?? Ki yafe min kinji” yafada yana girgiza hannunta jin bata juyo bah

“It’s okay” tafada still bata juya bah

“If you know it’s okay pls atleast look at me and smile” daman kuma abinda take jira kenan, ahankali tajuyo sannan ta mishi murmushi

“Wow pretty, one hug for this” yafada batareda tunanin komai bah ta rungumeshi, kankameta yayi Yan mai sauke ajiyar zuciya, breaking hug din tayi sannan tamishi Saida safe

“Baza’ayi haka bah barina rakaki”

“Ok”sannan suka fita

Bangaren Nadhira tana fita daga motan tayi hanyar baya, mika mata abu akayi acikin…..Bangaren Nadhira tana fita daga motan tayi hanyar baya, mika mata abu akayi acikin bakin leda sannan tamusu godiya kafinnan tashige gidansu Hasana.  Tana shigewa toilet yin Alwala Hasana tashigo+

“Kice mai yaje yayi Sallah”

“Toh Tasallah”

“Whatever lover girl” dariya kawai Hasana tayi sannan taje ta fada mai. Tana idar da sallah tamawa ummi sallama akan zata tafi gidan big dady , Addua ummi tamata sannan tafice daidai nan kuma yadawo daga masallaci,rungumeta Hasana tayi

“Take care and don’t do anything foolish over there,and be a good girl cos matar gidan bata da matsala and am very sure heart naki zaiyi melting because of her behaviors”

“InshaAllah Hasynah amma batun heart dina zaiyi melting bai taso bah”

“We shall see to it then”

“Whatever”  sannan tashige cikin mota,shidai bai gane akan me suke magana akai bah

“Darling bae  saina zo hira koh??” Yatambaye ta

“Yauwa sweetest boo saika zo” tabashi amsa

“Ohk bye and take care of yourself”

“I will and you also”

“InshaAllah” yafada sannan tashige mota,sanda tadaina ganin motan tashige cikin gida.

Suna Isa kofar gidan taji wani sanyin dadi naziyartar ta  ahankali ta furta

“Yar’uwarta nakusa cika miki Alkawarin dana dauka miki”

“Ya kikayi shiru kuma matar yaya??” Abdul ya katse ta da tambaya

“Nothing much  wlhy” ta bashi amsa tareda bude kofar motan sannan ta wuce wurin booth,b babu bata lokaci ta fito da trolley dinta sannan tamai Sai anjima kafinnan ta yi wajen gate din tareda kwankwasa wa , alokacin kuma har ya bawa motan Wuta yayi gaba abinshi.

“Ina wuni baba” tagaisar da baba mai gadi

“Lfy yen nan,daman kuna nan?”yatambaye ta cikeda mamaki

“Erh wlhy muna nan”tafada tana kutsawa gaban cikin gate din

“DanAllah baba akwai chemist neh kusa??”

“Eh akwai amma saikin dan fita ta bakin hanya”

“Toh ga kayana nan barina siyo magani nadawo”

“Toh adawo lfy”

“Allah yasa”tafada hade da ficewa, tafiya tadanyi kadan kafin ta iso chemist din babu bata lokaci aka bata abinda take bukata kafinnan ta yi gaba abinta.

“Assalamualaikum”shine abinda wani yafada daidai lokacin daya shigo chemist din

“Wa’alaika Salam” suka amsa mai

“DanAllah ina tambaya neh”

“Allah yasa mun sani”

“DanAllah yarinyar chan data fita miye tasiya neh??”

Sanda suka kalle juna tukunna  kafin daya yace

“Oh kana nufin wancan yar hannun  kake tambaya??”

“Eh ita dai wanda tabarnan yanzu”

“Dinger tasiya” yafada cikin ko in Kula

“Dinger kuma!!!” Sadiq Ya maimaita cikeda mamaki

“Eh mana ko baka gane bane”

“Nagane, nagode sosai” yafada hade da ficewa har lokacin bai daina mamaki bah, ahankali takarasa wajen motan su sannan yashiga

“What’s up dude?? Ina fatan ba ciwo mai tsanani bane yake damunshi??” Amin yatambaya cikeda tsoro , tsaki kawai Sadiq yaja sannan yace

“In fada maka abinda taje siya zaka yarda??”

“Erh mana”

“Dinger taje siya”

“Dinger kuma!!??”yatambaya afirgice

“Kasan miye ake Kira da Dinger kuwa??”yafada har wani zufa ke keto mishi

“Toh da bansaniba ne toh bari na maka dalla dalla, CONDOM tasiya”

“Innalillahi, miye zatayi da Condom kuma??” Yatambayi Sadiq cikeda damuwa

“Waye San mata” Sadiq yabashi amsa

Haka suka bar wajen tareda jimami dakuma tambayoyi aranshi.

“Sannu baba nadawo”

“Yauwa sannu da dawowa” baban yabata amsa sannu takarasa wajen da ta bar trolley dinta sannan tashige cikin gida da sallama sauke abakin ta

“Abin mamaki!!! Waye nake gani kaman enbiyu(haka take kiransu)”

“Nice”

“Ai ba’a fada mana kinji sauki bah(dayake daman basusan tafara magana bah)

“Ai kuwa inaga banyi wata 2 dajin sauki bah”

“Ayyerh Allah yakara sauki”

“Ameen ya Allah”

“Kardai ke Alhaji yace zakizo mana kwana biyu?”

“Eh wlhy “

“Ok sannu da zuwa,bari yaran nan suzo su nu…..”Ok sannu da zuwa,bari yaran nan suzo su nuna miki dakin da zaki zauna”+

“Toh mumy” nan mumy ta Kira Maimuna sabuwar yar aikin ta wanda tayi bayan tafiyan Hasana. Nan tafada mata akan tanuna mata dakin da ta gyara dazu..

“Muje” Maimuna ta fada, batareda Nadhira tayi magana bah tabi bayanta…

Hadadiyar daki aka nuna mata amma baikai dakinta na asalin gidansu bah, kasan mattress tadaga sannan tacire ledar da aka bata ta ajiye likewise Condom dinda tasiya chemist,ta ajiyewa tagyara wajen yayi smooth kaman ba’a sa komai bah ,kai tsaye wajen sif din dakin tanufa ahankali take jera kayanta aciki wanda duk cikin kayayyakin babu atamfa ko daya ,tana gamawa tazare towel dinta sannan tashiga toilet da nufin yin wanka.

Daidai ta fito daga wanka Maimuna tayi sallama sannan tashigo sannan tace” wai inji mumy kizo kuyi dinner kuma Alhaji yadawo”

“Ohk kice sallah zanyi sufara ci ,in na idar Zan fito”

“Toh” tafada tana hararan bayan Nadhira cos tinda taganta taji Nadhira bata mara bah

A Palour tasamesu sannan tafada musu aiken Nadhira din. Daidai kowa yazauna a dinning din Nadhira ta fito, comfy sleeping dress ne ajikinta kasancewan ana sanyi agari ga wani shegiyar kamshin dake tashi ajikinta. Kura mata ido sukayi suna kallon ta,cikin tsarguwa da irin kallon da Nadhira ke jefan shi dashi yasashi tashi yanufe ta

“Babynmu ce tagirma haka, lallai kice sauran kawai muji anzo tambayar aurenki” yafada tareda rungumeta ajikinshi, murmushin karfin Hali ta daura a saman fuskarta, rabe runguman tayi  tareda shagwabe fuska da fadin

“Haba big dady wani irin za’a zo tambayar aurena bayan ga wa’incan  hajiyoyi azaune , su ba’a yi musu aure bah Sai ni??”

“Ai su karatu sukeyi shiyasa” yafada hade da Jan hannunta zuwa dinning table,azuciyarta cewa take

“Wato nine ban karatu soboda banda gata, dan iskan mutum harda goga mun kirji da wayo,wlhy da badan ubanka da ubana daya bane dana auna mai zagi..” zaunar daita akan kujeran dayayi ne yasata dawowa daga tunanin data fada

“Sannunku” tafada batareda ta kalle su Fatiman bah

“Yauwa” suka amsa cikin shan kamshi,cikeda nutsuwa suke cin abinci har suka gama, suna gamawa Maimuna tazo kwashe plates,da gangan ta fadar mata da cup din juice ajikinta

“Wayyo momma!!?”Nadhira tafada da karfi Sai asannan hankalin kowa yadawo kansu dasauri Maimuna take bada hakuri cos bata zaci zata chanchara ihu bah, kallon ta  Nadhira takeyi sai alokacin talura ashe da gangan ne cos inba da gangan bah ai tin kafin tayi magana yakamata ta bada hakuri amma saita share

“Wlhy Sai na rama” tafada azuciyar ta

“Miye kike kallo har Kika zuba mata abu baki sani bah” big dady yafada cikin ihu irin alamun ranshi yabacin nan

“It’s okay big dady,bada sanninta bane” Nadhira tafada hade da tashi daga kujeran

“I need to use the wash room” yafada hade da barin wajen, dukda tabar wajen big dady bai daina surfa ruwan masifa bah,mumy kam hakuri tadinga bashi while su Fatima sunyi kaman ba’a wajen suke ba.

Maimuna nashigewa kitchen tafara tunanin waye yarinyar da har Alhaji zai dinga mata masifa haka ahankali tafurta”zamu hadu da kaine “(nace towww…)

Kai tsaye toilet tanufa tana mamakin halin Maimuna cos she she sees no reason dazata zuba mata abu ajiki itada yaune kawai  zuwanta gidan,dazuma da ta harareta tagani ta mirror,tsaki taja hade da fadin ” zakiyi bayani “…

Sanda tasake wanka sannan tafito a palour tasame su ga tea cup agaban big dady,ahankali takai idonta kan agogo taga exact time din Hasana tafada mata ne acikin zuciyarta tace

“Aikin ki yayi kyau Hasynah..” Big Dady neh yakatse ta da fadin

“Karaso mana Babynmu” cikin sanyin jiki taiso wajen su as usual wannan munafikin murmushin na face dinta

“Ahado miki tea neh??”yatambaye ta cikin kullawa

“Munafiki kawai”tafada azuciyar ta while azahiri tace

“A hadomin kuma bayan nasan hanyan kitchen,karka damu daga gobe nizan na hada mana tea din cos na tabbata Zan fita iyawa”

“Ai Dole kifita iyawa ko kin manta da Mommanku ba indiya ce, kuma sune dagin shayi”mumy tafada, dariya sukasa gabadayan su

“Toh indai hakane Babynmu ce zatana mana tea kullum” big dady yafada

“Kai naji dadin wannan contract din”tafada tareda sakin asalin murmushin daya nuna farincikin ta dahakan

“Natafi bacci,mukwana lafiya” tafada hade da barin wajen..

“Toh nima kasameni adaki cos natanadar maka da kayan dadi” mumy tafada tana shafa gefen fuskanshi kaman na karamin yaro(nace su love kenan…),

Shigarta da 30 minutes Maimuna tafito daga daki ta kitchen tanufa ai yana ganinta yabita, daidai tajuyo ta ganshi kawar da kanta tayi tareda turo baki…

Kishin ruwan daya dameta ne yasata fitowa daga dakinta ahankali gudun karta tashi masu bacci , abinda tagani ne yasata mannewa dagaru ahankali tafurta

“Dan Akuya kawai”, matsawa tayi domin taga kaman magana sukeyi…

Tsaye yake shida Maimuna yawani rungumeta ita kuma Sai zillewa takeyi alaman bataso chan ta numfasa hade da fadin

“Ni kabarni,bayan kagama min masifa dazu zaka wani zo kana manne min ,baga yarinyar chan ba kaje ka sameta tinda naga dazu har runguman ta kayi”

“Haba Rafin dadi nah yazakice min haka, baby fah yar kanina ne, kuma kema kinsan bazan cuceki bah  kuma inason nabaki wani assignment”yafada hade da shafo boobs dinta,itakuwa har wani lumshe ido takeyi alamun nan ne weak point dinta ahankali tace

“Fadi assignment din naji”

“Yauwa Rafin dadi nah daman so nake ki samin Id…

“Yauwa Rafin dadi nah daman so nake ki samin Ido akan wannan yarinyar yazamto kowani motsinta akan idonki zai kasance”+
Wani irin dariya tayi sannan tace”indai wannan ne karka samu damuwa…”ahankali takoma dakinta  batareda ta karasa jin abinda suke fadi bah…
Wata ajiyar zuciya tasauke data shige cikin daki, tunani dayawa neh yake shawagi a brain dinta kafin tasaki wata shegiyar murmushi tana fadin
“Taab lallai kinshirya barin aikinki indai ido zaki samun, ke zanfara kawarwa tukunna…
**********
Amin kam yana komawa gida yashiga matsanancin damuwa, bayani yake bukata gameda condom dinda tasiya…
Tashi yayi yaje palour soboda wani tunanin daya darzu mishi azuciya,yakuwa ci sa’a  kowa na wajen…
Sallama yayi cikin nutsuwa inda suka amsa mai hankali su yana mai komawa kanshi…
Gaban Dady yaje ya tsuguna tareda sune kanshi akasa alamun jin kunya,shiru ne ratsa wajen na mintina…
Dady ne yakatse shirun fadin”Da akwai magana abakinka Aminu”
Gyada kanshi kawai yayi still baiyi magana bah
“Kai banson shashanci inbaka da abin fada kayi gaba,kawani zo kasamu agaba kaman wasu yaranka” ”  mumy tafada ahasale
Cikin nutsuwanshi yace”Ayi hakuri mumy,daman… daman… nace in ba matsala auren…” sai kuma wutanshi ya dauke yana dada sune kai kasa…
Dariya irinta manya dady yayi inda Abba kuma mamakin rashin kunyan Amin yakeyi, antyn ma dariya tayi mumy kuwa kunya taji yakamata…
Dady ne yace”Nagane abinda kakeso, kaje zan neme ka”
Cikin sosa keya yace” Nagode Dady Allah yakara girma”
“Ameen” suka amsa sannan yafita daga palourn
Dady neh yamayarda duban shi zuwaga Abba sannan yayi gyaran murya yace
“Ina fatan kasan inda zancen yaron nan ya dosa??”
“Eh ranka shi dade” Abba yafada cos yana mugun ganin girman dady…
Murmushi dady yayi sannan yace “nalura baka son in cigaba da zama anan gidan fah”
“Na isa??”
“Bagashi kana kirana da ranka shi dade bah bayan ni yakamata nakira ka da ranka shi dade” dady yafada
“Toh nadaina”
“Yanxu yah kke ganin zamuyi??”dady yatambaya
“Ai duk yanda kace haka za’ayi”
“Toh InshaAllah ranar da za’ayi nasu Abdulkadir Sai ahada danasu, Sai afara shirye shirye” Dady yafada…
Wani irin farinciki yakeji acikin ranshi cos tindazu a labe yake ajikin kofa yanajin abinda suke fadi…
***********
*3 days later…*
Yen kwanaki ukun datayi acikin gidan ta kara Lura da abubuwa dayawa acikin gidan,daita ake kowani abinci agidan yanz u inda kuma yanzu Maimuna ce target dinta dan haka yau tayi niyyar fara aiwatar da kudurinta akan Maimuna din.
Maimuna mah bata fasa bibiyarta bah cos itama kowani motsin Nadhira akan idonta yake amma har yanzu bata samo komai gameda ita bah,
Data fadawa Big Dady Sai yace kawai su shareta , yanxu dai zance Maimuna ta share batun sawa Nadhira ido…
Tindazu take kitchen tana taya Maimuna aiyuka inda  Maimuna ta Lura Maimuna ta fiye shan coke,abu kadan Sai adan kurbi coke dinnan,
Fakan idon Maimuna tayi tazuba mata codeine acikin coke dinta ,inda tsantsan mugunta irin na Nadhira babban kwalba tazuba mata aciki, su Maimuna kam banda waka babu abinda takeyi, kuma dayake tabawa coke din baya amma tsantsan rashin Kula irin na Maimuna ko jijigawan datake yi bata ji bah,
“Nikam Maimuna wannan coke din daya rage dinnan zaki iya shan duka alokaci daya”Nadhira tafada tana nuna coke dinda ko rabi bai kawo bah,
Sanda Maimuna tayi wani irin dariya kafin tace” ke bakisan nayi course a iya shan coke bah??”
“Toh taya za’ayi nasani inba gwada min kikayi bah??”
“Tsaya kisha mamaki” Maimuna tafada tana kafa goran abakin ta , tsantsan hadama ko irin kwarewan nan batayi bah,gyatsan da Maimuna tayi bayan ta ajiye gora neh ya katse mata mamakin ta.
“Ya Kika gani??”tafada tana dage mata gira
Dariyan jin dadi Nadhira tayi sannan tace ” wlhy nadauka bazaki iya bah, barina dauko miki nawa kisake sha mugani”
Dadi kaman ya kashe Maimuna cos daman kullum guda biyu take sha arana amma gashi yau garabasa tasamu zatasha guda 3,
Fita Nadhira tayi straight dakinta ta nufa sanda taboye kwalban codeine dinda ta juye mata dafarko abayan gado sannan tasake fitowa dawani again sanda tadan zubar da kadan kafin tasake zubawa aciki(nace kaii Nadhira ke muguwar karshe ceh…) sanda Tajijiga dakyau sannan tayi takoma wajen uwar kwadayi
“Gashi harna bude miki”tafada tareda mika mata,karba tayi sannan tace
“Kin kyauta wlhy” aranta kuwa fadi take ashe Nadhira akwai mutunci(nace Maimuna kenan hhh),
Kafa goran tayi abaki amma ko rabi batayi bah tafara ganin Zion,wani irin zumm zumm take jin kanta na mata,
Ajiye goran tayi tafara ganin Nadhira shida shida, dagudu Nadhira tashige dakinta takwaso kwalaben codeine taje tazube su acikin sif din Maimuna,
Lokacin datakoma kitchen din ta tarar da Maimuna cikin maye,cikin muryan Masha ya tace
“Miye Kika samin a coke??dayake bata gama loosing sense dinta bah
Dariya mara sauti Nadhira tayi sannan tace” duk abinda naga zai zamemin matsala a harkan dana sa agaba toh lah shakka kawar dashi daga hanya nakeyi”
Wani irin sarawan da kanta yayi yasata sakin wani irin dariya amadadin kuka,
Jin dariyar da akeyi yayi yawa yasa mumy dakuma su Fatima saukowa daga sama cikin sauri,hanyan kitchen din da suke jin dariya suka nufa,
Turus sukaja suka tsaya SAKAMAKOn ganin Maimuna akasa,itakuwa Nadhira takurewa tayi jikin garu,tana ganin mumy tayi wajen ta gudu sannan tace
“Mumy bansan miye ke damunta Sai fadin maganganu maras a dadi takeyi akan itada big dady”
“Wlhy son Alhaji nakeyi irin sosai dinnan…”suka tsinkayo muryan ta tana fada,tana tashi tayi tana layi …
Mumy kam notin kanta taji yana neman kwancewa cikin dauriya mumy tace
“Wani Alhajin kikeso??”
Wani irin dariya tayi sannan tace “wani Alhajin kuwa baya…Wani irin dariya tayi sannan tace “wani Alhajin kuwa bayan mijinki?,wlhy Ina mugun son sh….”+
Marin da mummy takife ta dashi neh ya katse ta, cikin bacin rai mumy tace
“Abinda zaki saka min dashi kenan Maimuna??”
Wani dariya tayi dukda marin mumy bakaramin shigan ta yayi bah sai tace”toh an fada miki don ke kadai akayi shi neh?, Kindai San yana da damar yakara auren ire irenki guda  3, toh miye abin daga hankali anan? Kuma bari Kiji har kwana dani yakeyi”
Haba kan kace kabo su  mumy harsun  sun mata taron dangi, mumy sai cewa take wlhy yarinya karya kikeyi, mijina babu abinda zaiyi dake(Niko nace daga baya kenan).
Dukan ta sukeyi kaman ba gobe har sanda sukaga tadaina motsi sannan suka kyaleta,sheka mata ruwa akayi amma ko gizau Maimuna batayi bah
“Kun kasheta!!!,kunyi kisa” shine abinda Nadhira ke fadi afirgice cos tinda suka fara dukanta taja gefe ta tsaya.
“Suma tayi” Fatima tafada in assuring tune,
“Bagashi ankwara mata ruwa bata tashi bah” Nadhira takara fada tana mai tsugunawa akasa.
Kanta tasa atsakiyar cinyarta tasaki kuka mara sauti,she can’t imagine yanzu ace ita tayi sanadin barin Maimuna duniya.
“Yah Salam”shine abinda mumy tafada sannan tace
“Ku kamata mukaita asibiti” mumy tafada cikin sanyin murya cos gabadaya tsoro neh yadarsu acikin ranta.
Cicibarta sukayi suka sata amota Sai asibiti,suna isa asibiti aka karbe ta aka wuce daita direct emergency.
Ansamu numfashinta yadawo amma gabadaya bata cikin hanyacinta, doctor ne yasa aka Kira mai wa’inda suka kawo ta…
“Miye kuke kallon yarku tayi shaye shayen dayasa ta bugu dayawa?” Doctor ya gefawa mumy tambaya
“Yar aiki nace” mumy tabada amsa atakaice
“Yar aiki kuma??”yatambaya cikin mamaki
“Erh”
“Toh aina tasamu cocaine??”
“Cocaine” dukkansu suka fada cikin tsoro amma banda Nadhira
“Erh acikin aman datayi munsamu ashe tahada mixture biyu alokaci daya Wato da cocaine dakuma codeine which is not proper,gashi kuma dayawa tasha shiyasa condition dinta yazamo critical, ahalin yanxu kam Allah yasoku da akwai wani visiting doctor available dole shi zamu gayyato”
Kallon kallo akeyi acikin office din wajen cikeda jimami kafin suka tashi suka fita.
Wayar big dady mumy takira inda ta shaida mai halin da ake ciki.
Banda salati babu abinda big dady keyi, inda ya ce mata su hadu agida.
Komawa gida sukayi suna jiran big dady yadawo, chan saigashi da uwarsu babban riga, hula ma ahannu yariko Sai huci yakeyi kaman wani namijin zaki.
Shigowar shi yasa dukkansu suka tashi tsaye
Cikin bacin rai yake fadin” ina yar iskan yarinyar nan take??”
“Bata farfado bah” mumy tabashi amsa
“Yarinyar nan taci mutunci na dayawa harni zata mawa sharri don batasan hallaci bah??”Alhaji yafada cikin dacin rai kaman da gaske, Nadhira kam babu abinda take yi Sai binsu da ido
“Nima abin yabani mamaki,ai tanuna mana halinta kuma daga yau aikinta yakare agidanan” mumy tafada
“Abinda yasha minkai shine ina tasamo cocaine??”dady yafada
“Allah masani”
“Gaskiya ban yarda bah??”big dady yafada
“Toh aje a bincika dakinta mana I’m sure zamu samu wasu clue” Fatima tafada
“Kin kawo point sisto”daga nan suka dunguma zuwa dakinta, birkita koina sukeyi daga karshe suka samu kwalaben codeine manya manya guda biyu.
Salati suka hau yi sam  basu taba kawowa aransu Maimuna zata iya shaye shaye bah cos ta fiye shuru shuru, ayyerh daman ance duk masu shuru shurun nan basuda dadi.
“Taya akayi tasamu cocaine??” Shine abinda Amin Yafada bayan yagama duba ta
Iska Amin ya furzar sannan yace”Toh gaskiya nikam banyin wannan aikin in har ba’ayi involving din police bah”
“Erh gaskiya nima haka nakeson cewa, bari nakira police din Sai suzo”doctor yafada
Isowar police yayi daidai da isowar su big dady da duka yen gida amma banda yen matan gidan
Statement yen sanda suka karba sannan sukace dole Sai anje an bincike gidan su big dady.
Batareda bata lokaci bah suka dunguma zuwa gidan gabaki dayansu harda Amin.
Ganin gidan da motansu yayi horn yasa Amin sauke boyeyyar ajiyar zuciya.
Zaune suke akan sofa suna kallo while ita Nadhira na kitchen tana girki, muryan su big dadyn dataji yasata fitowa dasauri tana goge hannunta da hand towel.
Runguman shi tayi irin na sannu da dawowa sannan tace”ya naga harkun dawo?”
Sam bata Lura da yen sanda dakuma Amin dinda takafe ta da ido bah,ji yake dama shi ta runguma bah wannan mugun mutumin daya nakasar da sirkinsa bah.
Kuma gaskiya yasha mamakin ta amma daya tina dadynsu yace ya yafe mishi saiya basar da zancen azatonshi itama Nadhira ta yafe mishi neh, dadi sosai yaji wai ABAR SOnshi tana da kyakyawar zuciya(nace Allah yasa)
“Muna tareda police neh sunzo duba gidan”wani irin rass taji gabanta yabada kafin tamiyar da dubanta kansu daya bayan daya take binsu da ido har ta tsaya cakk da idonta akanshi.
Wata uwar harara ta jefe shi dashi tareda hade fuska kaman bata taba dariya bah ganin yana mata murmushi, jikinshi neh yaji yayi sanyi sosai.
Banda kallon shi babu abinda takeyi dukda yanzu tafara mantawa dashi cos dakanshi ya hadata da abokin shi amma kuma abu mai wuya neh ta manta dashi gabadaya a babin rayuwarta.(First love)
Maganar yen sandan neh yakatse su ,inda aka musu gajora zuwa dakin Maimuna din, duk bincike anyi amma ba’a samu komai bah banda kwalaben codeine.
Daki daki suka shiga amma ba’a samu komai bah, saukowa kasa yace aje aduba kitchen.
Duk iya binciken su ba’a ga komai bah, fita suka yi daniyar tafiya, har sun kai bakin kofa wanda yamusu jagora ya tsaya cak tareda  facing dakin Nadhira yayi sannan yace
“Bamu duba wancan dakin bah” wani irin dum dum taji gabanta ya bada, Adduan datake karanta wa azuciyar ta yasa halin da tashiga boyuwa kadan.
“Amana jagora” taji anfada cikin in in na tace toh,gawani zufan dayafara karyowa takowani gaba najikinta.
Amin neh ya Lura da halin da tashiga,
“Akwai matsala neh??” Yatambaye ta
Wani hararan takuma banka mai ahasale tace”ina ruwanka dani”
“Muje” tafada hade da yin gaba, big dady mah alokacin ya daura ayan shakku akanta.
Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mama….
*Nace toww miye suka gani?🙆🙆*
Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mamaki.
Amin neh yakarasa wajen tareda tsungunawa zuciyar shi na zafi sosai har ga Allah baiyi tsammanin haka daga gareta bah kuma zarginsu ya tabbata akanta .
Runtsa idonshi yayi sannan yabude su so yake ya karyata abinda yake gani.
Daya daga cikin police din neh yake karewa Nadhira kallo nan kuwa yayi harba da kafanta cos as usual short gown neh ajikinta.
Dawowa sama da idanunshi nan kuma yakara harbawa da kirjin ta wanda ko bra bata sanya musu bah, wani irin yawu ya hadiye tareda lashe kasar labban shi.
Ganin kallon da suke mata neh yasata tattara duk nutsuwar ta waje daya takuma aza murmushi asamar fuskarta tareda karasawa wajen Amin cos ita kam mah tadauka wani abin daban zasu gani shiyasa tsoro shiganta .
Karban kwallin Condom din tayi hannunshi, tareda lura da yanayin bakincikin dayake ciki kafin tace
“Akan wannan abin kuke kallo na kaman wata sabuwar hallita,nikam mah har kunsa naji kunya”
Ganin yanda take magana naneh yasashi tsura mata ido for some seconds gani yayi duk wannan tsoron dakuma rashin gaskiyan daya bayyana a fuskarta dazu babu su.
Cikin sanyin murya yace”miye kikeyi dashi??”
“Toh miye zatayi dashi ai kowa yasan amfanin wannan abun guda daya neh tal” wannan police din yafada cos bakaramin bata mai rai Amin yayi da wannan tambayan bah.
“Lah😨😨 waye cemuku amfanin shi daya neh??” Ta tambaye su cikeda mamaki.
Shuru dakin yadauka suka sake Baki da hanci suna mai neman dayan amfanin Condom  cause gabadaya ta jefa su aduhu.
“Ke karki raina mana hankali fah” wannan police din yasake fada a kaushashe cos gabadaya tafara bashi haushi ,shidayake son neman hanyan daza su hadu  soboda gaskiya ran shi yabiya(Niko nace kwalelenka)
“Yadai kana min magana saikace yar ka??” Tafada tareda maka mai harara.
Zaro ido yayi ganin abinda tayi mishi amma ba damuwa zaijira insun hadu yafada mata shi baya daukan raini( lallai kam)
“Just say what kikeyi da wannan” yafada cikeda zakuwa
“Packing din gashi na nakeyi dashi” tafada sounding relieved
“What a bullshit” Amin yafada afusace cos gani yake raina musu hankali kawai takeson yi
Itadin mah bai tsira bah sanda ta banka mai nashi hararan, rolling eyes dinta tayi sannan tacire dankawalin kanta.
Nan kuwa doguwar gashin ta ya bayyana wanda aka tufke atsakiya.
Zaro abinda ta tufke gashin tayi tareda mika mishi abin wanda shi bah roba Lin bah。
Karba yayi yana juyawa ahannu shi amma har lokacin bai dago miye bah, shima police din karba(inaga shi yayi leading dinsu) yayi yana dubawa.
Duka dakin sanda suka rike abin suna kallo daga karshe suka miyarda duban su gareta.
“Baku gane miye bah koh??” Batareda ta bari sun yi magana bah ta ciro Condom daya daga cikin kwali.
Fatima kam harda rufe ido wai batason gani, dariya kawai tayi sannan tayi wajen drawer.
Razor blade tadauko sannan ta ijiye Condom din akan dressing mirror.
Yanka daidai wajen band din rike …🙈🙈 tayi Sannan ta dago shi.
Toilet tashiga ta wanke yanda maikon zai bar jikin abin bayan nan  tafito.
Na mujiya suka zuba mata suna kallon ikon Allah.
Mika musu tayi suna kallo Sai sukaga iri daya neh da wanda tacire akanta.
Murmushi tasakar musu tareda fadin” akan nayi amfani da roba Lin ya tsinka min gashi toh gwanda nasa wannan, in takaice muku nafi jin dadin amfani da ”’CONDOM BAND”’ akan kowani  band”
Mamaki neh yacika su jin abinda takeyi da Condom cos basu taba zargin haka abin yakeba sun dai San ana amfani da Condom neh wajen kariya
while Amin ya dinga blaming kanshi akan zarginta dayake yi, sosai zuciyan shi yasamu relief jin ba abinda yake tunani bane
Dariya da ita kadai tasan ma’anar shi tafashe dashi sannan tace” I knew you will all be  shocked, shiyasa ma dafari tsoro tashigeni dana tina da na fito da kwallin kuma dafari I thought bazaku tsaya ku fahimce ni bah”
Ta karashe maganar da murmushi, dukkansu mah murmushi sukayi amma banda wannan police din cos gabadaya shirin shi ya wargaje.
Fita sukayi daga dakin, cewa sukayi zasu duba compound din ba bata lokaci aka musu izinin dubawa.
Har suka gama dube duben basu ga komai bah, haka suka koma akan in Maimuna tafarfado zasuji komai…
Zaune take agaban mirror acikin daki banda murmushi babu abinda yake fitowa daga Samar labbanta.
Daman tin randa taje tasiyi Condom ta lura wasu na binta amma dayake shu’umace saitayi kaman bata gansu bah.
Abin mamaki kuma saitaga abokin Amin neh yashiga nan tasan tareda Amin sukazo kuma sawunta suka biyo.
Washe gari takoma chemist din tareda tambayansu wanda yazo immediately lokacin da tafita ,basu tsaya bata lokaci bah suka zayyana mata abinda ya tambaya dayake bakin su baida rufi.
Nan tamusu godiya tareda ficewa, tana komawa gida tadinga sakawa da warware akan yanda zatayi da Amin cos tasan yanzu yadaura Ayar shakku akanta kuma mai yiyuwa mah yafara zarginta.
Daman tinda taga doctors sunyi confirming substance din Cocaine acikin abin da tasha tasan dole Sai anzo yin bincike shiyasa tinda wuri tasan inda dare yamata.
Amma agarin kwashewa Sai akayi rashin sa’a Condom yafadi,amma batasan takamen men abinda yafadi bah irin bari tagama saita dauka Sai Allah yasa tamanta shi awajen.
Sai alokacin da akace za’a duba dakinta ta tina ashe bata dauki abinda ya fadi bah shiyasa tsoro ya shigata.
Tana ganin Condom neh ranta yayi fari fatt tsantsan murna cos tasan in akan Condom neh zata iya kare kanta…
Numfawa tayi tareda sakin wani murmushi tinawa datayi yanda tayi da cocaine.
Jan drawern jikin dressing mirror din tayi tareda daukan hands glove  sannan ta tashi, dayake dare neh kuma anriga da an rufe kofa kuma tana kyautata zaton kowa yayi bacci.
Ahankali tayi jikin window tayaye labule, sliding glass din tahau cirewa ahankali gudun karyayi kara.
Tana gama cirewa tasauke ajiyar zuciya mai karfi, zura kafafun ta tayi sannan ta dira ahankali.
Wajen bolan gidan tanufa sannan ta sanya gloves din ahannunta, sanda ta daddaga wasu abubuwa kafin tazura hannunta chan kasa.
Torch din wayan ta tukunna daidai tafito da wani bakin leda. Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna…(nace master planner bah…)
Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna…(nace master planner bah…).
Straight kitchen tanufa sannan ta dauko container din gishiri tazazzage gishiri acikin buhun gishirin cikin store kafin ta zuba cocaine din acikin  container din.
Ajiyar zuciya tasauke sannan tasake wannan murmushin muguntan ta kafin ta koma dakinta…
Washe gari ita tafara tashi tashiga kitchen ta dafa musu lafiya yiyar breakfast.
Kafin su fito ma har tagama komai ta feso wankan ta as usual cikin short gown yau kam ko dankwali batasa bah.
Ta zauna da 10mins yen gidan suka fara fitowa, sosai suka sha mamakin ganin abinci asamar dining table.
“Babynmu kece kika bawa kanki wahala haka??”mumy tafada cikin farinciki cos Nadhira bakaramin burge ta tayi bah
“Ai bawani wahala bane” tafada cikin sune kai kaman da gasket
“Madalla Allah ya biya”
“Ameen mumy”
Tashi tayi tareda karasawa wajen dining table din cos su kam har sun zauna sun fara serving Kansu.
Lura datayi Nadhira batacin abinci yasa mumy cewan” ya naga baki cin abinci”
“Inajiran Big dady tinda naga baku jira shi bah” Tafada cikin murmushin daya zame mata jiki
“Kin kyauta Babynmu “suka ji muryan Big dady daga bayansu.
Tashi tayi taje ta taroshi tareda mai Ina kwana amsawa yayi cikin Jin dadi  tareda kawar da duka zargin dayake mata acikin zuciyarshi.
Zaunar dashi tayi tareda serving dinshi nashi abincin, lokacin har su Fatima sun gama cin abinci.
Gaishe shi sukayi sannan ya amsa cos in suna cin abinci ya hana su  magana tashi sukayi suka bar wajen…
“In hado maka coffee neh??”tayi requesting
“Gyada mata kai yayi tareda sakar mata murmushi
Itama murmushin tamiyar mishi tareda wucewa kitchen.
Tea cup tadauko tareda fara zuba cocaine din akasa sannan tasa garin coffee din.
Ruwan zafi tadauko ta sheka akai sannan ta dauka spoon ta gauraya su hasaida aka daina ganin garin cocaine din sannan ta fice.
Ta kaiwa ta dauki cube din sugar sannan tasa aciki..
“Allah yamiki Albarka” dady yafada cikin mouthful
“Ameen” tafada tareda Zama akan kujera tukun tayi serving din kanta mah.
Ganin yakai cup din bakinshi neh yasata cikin boyayyen murmushi…
Dayake baiyi changing taste bah shiyasa Big dady bai fahimce komai bah.
Tass ya shanye coffee din harda gyatsa.
Ya na mikewa itama ta Mike dayake tagama cos bata cin abinci dayawa.
Car key dinshi ya dauka sannan ya mawa mumy magana wacce taje shirin zuwa asibiti.
Chan saigata ta sauko daga sama cikin takunta na matan attajirai…
Da murmushi ta tareta itama tareda taka musu zuwa waje
“Ke bazaki zoh dubiyan bane??”mumy ta tambaye ta cikin kulawa.
Murmushi tasake sannan tace” ni bana zuwa dubiya hannu zalla ma’ana so nake na hada koda kunu neh in case inta tashi tasamu abin sawa abaki”
Sosai suka sha mamaki cos ko kadan wannan tunanin baizo musu bah.
“Madalla Babynmu Allah ya biya ki in kin tashi tahowa driver yakawo ki” dady yafada.
Toh tafada still akwai wannan murmushin afuskarta, bye bye tayi musu sannan ta shige cikin gida.
Straight kitchen takara nufa agagauce ta daura ruwan akan gas tareda kara sa cocaine acikin ruwan..
Sharp sharp tagama hada kunun sannan ta juye acikin flask..
Dakinta tawuce ta Kira wani number,dagawa akayi daga dayan bangaren akace
“Ranki shi dade baki da sauki fah” yafada cikin muryanshi irin na mashaya
Wata karamar tsaki taja sannan tace”ya ake ciki??”
“Gaskiya aikan ki yanzu ya kara kudi soboda da kyar ake samu amma dai Alhmdllh ansama miki   “
“Nawa neh ??”ta tambaya atakaice
“Dubu goma zaki ciko”
“Toh inason mu hadu nan da minti 10 zan taho maka da cikon kudin”
“Toh Hajiya muhadu a inda kika ce zamu hadu??”
Sanda tayi Jim sannan tace “tsari ya chanza”
“Toh yanzu miye tsarin” yatambayeta
“Akwai wani mai shago a anguwan danake ta bakin titi, inkaje saika bashi kace za’a zo akarba nikuma kafin ka karaso zan bashi aika ya ajiye maka, yanajin kace aika kazo karba zai baka kudin amma kayi wrapping dinshi yanda babu wanda zai gane wani Abu neh aciki” tana gama magana ta katse kiran tareda deleting din numbern”
Dariya yayi yana jinjina irin kwakwalwar Hajiyan( bai taba ganinta bah daman) afili yace”komin kwakwalwar ki yau kam saina san wace ce ke”
Tana ajiye wayar tasauke wata ajiyar zuciya kafin tabar cikin dakin da leather a hannunta.
Waje tafita dashi sannan ta gaisar da baba mai gadi.
Yana ganinta yafara wangale baki musamman mah daya hangota da leather.
“Wa’inan yaran fah??”ta tambaye shi
“Ai basu nan amma sun kusa dawowa daga makaranta”
“Ohk in sun dawo amin magana” tafada tareda juyawa”
Yace”toh” yana mai yin adduan Allah yabashi y’a kaman ta.
”’5mins later…”’
Fitowa tayi amma yanzu leathers biyu neh a hannunta.
Yaran suna ganinta suka fara murna cos sosai suke sonta.
Wanda tasan tana da nutsuwa kuma wanda bata fiye magana bah takira acikin su sannan ta jata gefe daya.
Bata leather daya tayi sannan tace “ki kaiwa mai shagon bakin hanyan nan,kina bashi kice za’a zo akarba sannan kijuyo”
Gyada kai yarinyar tayi sannan ta wuce wajen mai shago din.
Kaman yanda tace haka yarinyar tayi, tana dawowa tabawa yarinyar nata alawan cos daman kullum saita raba musu shi sadaka
”’5mins later…”’
Hango wani huge guy nayi wanda kallo daya xaka mai kagane bashida mutunci shagon ya shiga tareda bashi aikan sannan aka bashi kudin.
“Waye neh yakawo kudin??”ya tambaye mai shago
Mai shago kuwa ganin babu rahama afuskarshi yasa shi fada mishi wata ce ta kawo,
“Ya take??”
Nan kuwa ya zayyana mai kallan kayan yarinyar dayake akwai niqab afuskarta(daga islamiya suka taso amma babu uniform ajikinta)
Gyada kai yayi tareda ficewa daga shagon, yaje ya zauna a inuwa yana jiran dawowarta.
Hango shi tayi tacikin mota awajen inuwa,wata murmushi tasake ganin zaton ta yazama gaskiya.
Sanda suka danyi nisa tace mai ya tsaya sannan tace”in bazaka damu bah aika zaka karbo min??”
“Haba miye kuma abin damuwa anan,kifadi komiye ni mai iya miki neh”yafada cikin sanyin murya
Murmushi tasake akaro na biyu sannan tace “shagon bakin titi dinnan zakaje kasiyo min flour mudu 5, sai kaga yafara auna flour din ma’ana in yajuya baya saika dan duba min karamin leathern da aka mai kyakyawan package. Wannan leathern zaka dauko amma fah karka bari yagani. Ga wannan saika ijiye shi awajen da kadauki leathern”
Yace toh tareda karban kudi da wata farar envelope daga hannun ta.
Fita yayi daga cikin motan tareda wucewa shagon ,kaman yanda tace haka yayi ,yana karba ya faki idon mai shago sannan ya tusa leathern acikin flour din kafin yafito.
Yana komawa ya Mika mata leathern flour din karba tayi tareda ajiye wa cos batason ya bata mata hannunta.
“Wajen matan ka zaka fara kaini kafin muwuce asibiti din”tafada mai
“Toh”amsa tareda nufar daita anguwan Mahaukata(karku ce fah Mahaukata neh a anguwan a’a sunan anguwa neh kawai)
Anguwan talakawa neh sosai wanda kowa harkan gabanshi yakeyi ga yen talla sai fitowa sukeyi yasu wajen cin kasuwan su.
Adaidai wani gida mai labulen buhu yayi parking itama fitowa tayi tana jinjina ma masu Zama a anguwan.
Iso yamata zuwa cikin gidan inda ya tayata rike leathers din flour din samun matarshi sukayi inda take cilla dan wake acikin ruwa.
Gaisheta takeyi amma abin mamaki Maimakon matar ta miyarda hankalin ta kan bakuwa sai takara miyarwa kan danwaken ta.
Duban agogon hannunta takeyi inda yanzu taci minti uku azaune cos tintini driver yafita.
Gyaran muryan da tayi neh yasa matar Dan juyowa”gashi ni natafi”tafada tana tashi tsaye
Cikin dan Jin kunyan abinda tayi matan tashi tsaye tareda gaishar da Nadhira.
“Gashi akwai wani leather acikin wannan kidan cire min sai ki karkada min flourn jiki”tafada cikin nutsuwa
Cikin rawan jiki matan tasa hannu ta cire sannan ta karkada harda gogewa da zanin jikinta.
Karba tayi sannan tace”ni natafi sai watarana in Allah yayi zamu sake haduwa tinda na Lura kinfi bawa kasuwan cin ki muhimanci fiye da mutane” tana gama fadin hakan tayi gaba tareda boye leathern acikin side bag dinta.
Sosai matar driver taji kunyan abinda ta aikata cikin sanyin jiki takarasa gurin tukunyan sana’arta…
Suna Isa asibiti tabar side bag nata acikin jaka sannan tafito da flask din kunu.
Shiganta dakin yayi daidai da farfadowan Maimuna kuma alokacin akwai doctors aciki, ciki kuwa harda Amin.
Gaishe su tayi cikin sanyin murya sannan ta karasa wajen gadon Maimuna din.
“Ya jikin ki??” Tafada a hankali,itakuwa Maimuna banda binta da ido babu abinda takeyi.
In akwai liquid abinci abata soboda taji karfin jikin ta”Amin yafada
Mumy neh ta dauki flask din tareda zuba kunun ciki acikin cup.
Nadhira neh dakanta ta sawa Maimuna cup din abaki, ita kuma banda kallon Nadhira din babu abinda takeyi.
So take tayi magana amma saitaji kaman an rike mata makogaron ta.
No tausayi haka Nadhira tabata kunun nan Tass…
”’3hours later…”’
Fita tayi don komawa gida soboda babu kowa, drivern neh dakanshi ya bude mata kofan motan.
Da murmushi tace “ai da baka wahalar da kanka bah”
“Girman ki neh” yafada shima…
Daidai gurin mai shagon takara ganin shi wata murmushi tasake sakewa dayake motan tinted ni shiyasa ba wanda yaganta.
Suna Isa gida tawuce daki, numbern shi tasaka awayan tareda danna mai Kira…
Ganin mai kiranshi yasa shi saurin dauka(private number)…
Dariyan dayaji anyi neh yasashi kallon fuskar wayan cos ko murmushi bayajin tayi in har takira.
Cikin nutsuwa tace…Cikin nutsuwa tace ” I thought you’re a smart guy but unfortunately you’re not,+
You thought zaka iya min wayo koh??”Wani dariya takarayi tace” I trust no one in fact I don’t even trust myself cos tunani nah na iya chanza wa akowani lokaci so….
Katse ta yayi fadin”miye faru neh ranki shi dade??”
Dariya takuma yi tace” all pretence aside, daman shawara zan baka”
Sanda yayi Jim yana dan juyawa ko taganshi neh amma baiga alaman ana kallon shi bah.
“Miye sa kakeson sanin waye ni??” Tambaye shi batareda tajira cewar shi taci gaba” nagane sokake in polisawa suke kama ka kafito dani koh??
Dariyan rainin hankalin yayi yace”kina tunanin in suka kamani bazan binciko ki bane??”
“Toh ka sani ni nan inuwa ce baza’a iya kamani bah ko ka taba jin inda aka kama inuwa neh??”
“Kaman dagaske yafada in amusement, bayan zaki fito daukan aikan ki??”
“Aika?? Nawa yaushe kenan fah??”
“Nadazu mana”
“Kama daina bata lokacin fah soboda nariga dana dauki kayana!!”
A saba’in yamike daga inda yake yace”wannan mah karya neh”
Dariya tayi tace” go and check nabar maka aika awajen mah”
Baijira cewar ta bah ya katse wayar tareda nufar shagon, ko sallama babu yace”ina abinda nakawo dazu??”
Duba inda ya ajiye yayi yakalli farar takarda instead of bakin leather.
Hannu na rawa ya dauki takardan tareda warwarewa wata kyakyawan rubutu neh ya bayyana(irin na 3sweet besties dina💋💋)
“FOOL!!!” Harya cakumo wuyar rigan mai shago kawai sai wayan sa ya dau kara dasauri yasake shi hade da picking din wayan.
“Karka mawa mai shagon komai cos shima baisan lokacin da aka dauka bah”
“Ke waye ceh??”
“Someone who is seeking for revenge on the death of her mom and sister!!!” Tana gama fadin hakan ta Kaste wayan.
“Hello! Hello!! Hello!!!” Ganin batayi magana bane yasashi duba screen din wayan
“Holy shit” yafada tareda nausar gini sannan yasa kai ya fice…
Zama tayi agefen gado ta bude ledar ganin abinda yake ciki yasata fashewa da kuka mai tsuma zuciya, sanda tayi mai isarta sannan ta share hawayen ta tareda shigawa toilet domin yin wanka.
Tana gama wanka tashige kitchen domin dafa musu abincin rana soboda 1 tayi..
Tana cikin hadan abinci mumy tadawo..
“Sannu da dawowa mumy”
“Sannu da aciki Babynmu”
“Ina big dady yake”
“Wai zai shiga ganin likitanshi cos baidan jin dadin jikinshi”
Wani irin faduwa gaban ta yayi amma ta waske tace”shine bakuje ganin likitan tareda shi bah??”
“Ai banma san kin fara abinci bah cos shi nazo dafawa”.
“Ohk, ya jikin Maimuna din??”
“Hmm, jikinta sai sake rikicewa yakeyi gabadaya tafice hanyacin ta” mumy tafada cikeda jimami
“Ayyerh Allah yabata lafiya”
“Ameen” mumy tafada tareda ficewa
Ajiyar zuciya tasauke sannan tayi wannan dariyan muguntan data saba yi tacigaba da aikin ta.
”’Hospital”’
Big dady neh zaune agaban doctorn shi ya nutsu yanajiran yaji sakamakon test dinda aka mishi.
Gyaran murya doctor yayi ya gyara zaman medicated glass dinshi yace
“Sakamakon test dinda aka maka yanuna am sorry to say sir that it’s obvious that ana sa maka some substance I mean like cocaine acikin maybe drink or something else
Afirgice big dady yace “what!!!”
“Yes sir and gaskiya it’s like kaman ana sawa acikin stimulant drug substance kaman  coffee”
“Nadhira” yafurta asarari tareda runtsa idonshi gam, bude idon yayi yana kallon doctorn daya kafe shi da ido.
“Any prescription??”
“Yeah” yafada tareda yin rubutu acikin  paper sannan yamika mishi.
Musabaha sukayi sannan big dady yafita yana tunanin irin matakin da zai dauka akan Nadhira din…
Tana gama dafa abinci tashirya shi acikin basket sannan ta mawa mumy sallama tareda ficewa zuwa asibiti.
Clashing sukayi da big dady inda  tasakar mai murmushi sanda idonsu ya sarke dana juna.
Kwafa yayi acikin zuciyar shi yace “kin kusa bin su kema!!!”
”’9:00pm”’
Big dady neh da mumy zaune akan sofa sai jijiga kafa yakeyi yana cizon labba mumy neh ta tabashi tace
“Lafiya kake kuwa?”
“Lafiya lau”yabata amsa zata sake magana kenan Nadhira tafito daga dakinta daga sanye da Silk Patterned Pyjama, wando Pyjama din dan guntu iya cinya.
Wani yawu big dady ya hadiya yana ayyana abubuwa da dama akanta
“Big dady barina hado mana coffee koh??”ta katse mai tunani tareda shigewa kitchen batareda tajira miye zai ce bah…
Cups biyu a hannunta as usual,mika mai nashi tayi sannan ta zauna gefen shi tana kokarin kai nata baki
Murmushi yayi azuciyarshi yace”shegiya saikema kinsha cocaine dinna”
“Babynmu muyi changing din coffee ma..”Babynmu muyi changing din coffee mana” yafada yana sakin murmushin mugunta.
Daukewa annurin fuskan ta yayi tace” big dady baka shan sugar sosai fah”+
“No yau zan sha “yafada tareda karbe coffee din hannunta yabata nashi.
“Drink”yafada tareda kafe ta da Ido.
Ahankali ta dauki cup din ta nufi bakinta dashi.
Sipping takeyi ahankali sannan shima yakai nashi cup din baki azuciyarshi yace” in kinsan wani baki san wani bah”
Atare suka gama shan coffee din inda ta musu Saida safe ta shige cikin dakin ta.
Tana shiga ta sa key tareda yin wani irin super tafada kan gado.
Juyi tashiga yi asaman gadon cikin Jin dadi abinda yafaru dazu  jira kawai takeyi su ta bacci ta aiwatar da next plan dinta…
Palour kuwa suna zaune kan big dady yafara sarawa cikin sauri mumy ta dauko maganin shi ta balla mai ya sha nan ta taimaka mai ya haura stairs suka shige daki…
”’Washe gari”’
Sosai big dady yadan ji saukin ciwon kanshi kuma daman zaiyi tafiya neh zuwa wani meeting nasu na masu kudi kuma shi kadai zaije…
As usual har Nadhira ta tashi tayi daily chores nata harda girki tayi ta jera su akan dining table…
Big dady sai satan kallon Nadhira yakeyi yana son gano reactions dinta.
Dago kai tayi ta kalle shi sannan tasakar mai da murmushi , ya dauki coffee zai kai baki tace” big dady ko yau ma zamuyi exchanging din cup neh??”
Kura mata ido yayi yace” no kowa yasha nashi”
“Gaskiya bazan yarda bah nikam sai mun yi exchange” tafada tareda komawa ta gefen shi
Ganin yanda ta dage neh yasashi fadin”nikam bazan sha sugar bah ko sokike diabetes dina ya tashi neh”
Bata fuska tayi tace”Oops am sorry”
Azuciyarshi fadi yake”Shegiya an gaya miki zan barki ki Kashe ni da raina neh?? Ai ina dawowa zanyi maganin ki shashasha kawai”
Cikin kwanciya hankali ta fara kurban coffee dinta acikin zuciyar ta kuwa ita kanta bazata iya fadin irin farincikin datake ciki bah…
Ita dakanta ta dauka mai office bag nashi zuwa mota,
Allah yakiyaye hanya  suka mishi sannan suka koma cikin gida…
”’30 minutes later…”’
Zaune suke dukkansu acikin palour suna kallon wani Indian film mai suna  Sanam Teri kasam sosai suka nutsu cos film din sosai yake kayatar dasu kuma suna jin dadin shi dukda su emmatan wajen sai share kwalla sukeyi(🤧nima ko yaushe na kalli film sai nayi kuka😓)
Daidai sun gama kallon wayan mumy yayi kara sanda tayi Jim tukunna kafin ta dauka soboda bakon number datagani
Sallama tayi sannan aka amsa daga dayan bangaren
“danAllah waye neh”tafada asanyaye cos haka kawai taji jikin ta yayi sanyi
“Kina magana da inspector Nasir neh”
Wani irin miyau mai daci ta hadiye tace” lafiya dai koh??”
“Erh akwai wani patients naki a teaching hospital”
Ajiyar zuciya tasauke tace to gani nan zuwa bata jira cewan shi bah ta katse Kiran…
Sosai inspector Nasir yasha mamakin ta amma sai ya basar…
“Miye faru mumy??”
“Ashe yau bamu leka Maimuna bah har an fara neman mu a asibiti so you guys should go and pick up ur khimars”
“OK ” suka fada in chorus sannan fice…
”’Teaching hospital Bauchi”’
Suna isa wayan mumy yadau kara
“Ku taho emergency in kun iso”
“Ohk” tafada sukayi hanyan emergency din
“Yana ga munyi tanan??” Nadhira ta tambaya
“Erh inaga condition dinta yayi worse neh” mumy ta bada amsa
Basu kara magana bah har suka isa
“Kune aka Kira??” Wani yafada
Mumy tace”Erh”
“Ohk ni neh wanda kuka yi magana dashi wato inspector Nasir”
“Ohk nagane ” Tafada tareda gaishe shi shima ya amsa
“Ku biyo ni” binshi sukayi kaman jela har suka iso casualty room…
Gurun gado ya nufa dasu inda suka cika da mamaki ganin Maimuna ba ciwo taji bah amma da sunyi la’akarin kwakwalwar ta yadan samu matsala sai hankalin su yadan kwanta …
Cakk suka ja suka tsaya dalilin hango wanda basu yi tsammanin gani bah akan gado…
Nadhira batayi la’akari da cewan hospital sukeyi bah ta kurma wata iriyan wawaiyan ihu ai basu hankara bah suka jita ak…
*End of book A*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *