ZUMA CHAPTER 2 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 2 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Inajin tamkar na tafi kawai na fada muku wanene Aliyu cikin rayuwa ta amma se naga zaifi muhimmanci idan na baku labarin daki daki. Dukkan mu munyi tunanin Daddy zai hakura kamar yadda ya saba, amma wannan karan shima se ya kyale mu, ya daina shiga harkar mu kai tamkar bai san me muke yi ba, hakan ba karamin tayar min da hankali yayi ba, saboda hakan na nufin ba zanje FUD din ba. Seda mukai kwana uku a haka sannan a rana ta hudu duk suna bacci na fito na nufi parlon shi, dake Saturday ce nasan dama babu inda zaije, ile kuwan yana zaune yana waya, language din da yake using ya tabbatar min da yan uwansa lawyers yake magana, zama nayi a cushion din dake facing dinshi time to time muna hada ido dashi se inyi saurin dauke nawa idon, idan kuma muka hada se na marairaice kamar zanyi kuka, bayan wajen mintina talatin yayi hanging wayar tareda kallona yace+

“Nanah! Ya akai?”

Langwabar da kaina nayi nace

“Daddy good morning”

“Morning sweetheart, akwai wani abin ne?”

Ya fada kamar bai masan me muke ciki, a karo na farko se na fara wasa da hannuna tare da yin shiru ina auna kalaman da zanyi amafani dasu.

“Daddy dan Allah…”

Se kuma nayi shiru shima bai cemin ba se ya zuba min idanu sannan nace

“Ka bari naje FUD?”

Kanshi ya girgiza yace

“A’a!”

Bance komai ba se hawaye ya fara zarya akan kumatuna, hannuna nasa na rufe fuskata dashi ina kuka a hankali at least tunda bazan iya masifa ba ina ganin hakan zai dan sanyaya min zuciyata. Bai hanani ba seda nayi ya isheni sannan yace

“Nayi tunanin a yadda nake muku komai da kuke so nayi tunanin once zaki min alfarma ki karba kudirina nima”

Kaina na gyada mishi ina jin kamar ni din ba yarinyar arziki bace nace

“To Daddy kayi hakuri”

Mikewa yayi yace

“Ai Nanah ke zaa bawa hakuri tunda ke aka batawa”

Nima tashi nayi har lokacin idanuna basu daina zubda hawayen ba, naso har cikin zuciyata nayi attaining goal dina amma tun kafin aje ko ina Daddy ya datse. Haka na fito na shiga kitchen na daura ruwan zafi na dama custard na tsiyaya evaporated milk gwangwani daya sannan nasa spoon na fara sha, can naji taste din bai kai yadda nake so ba na dakko ayaba nayi peeling bayan nayi slicing ciki sannan na saka sugar, se naji taste buds sun bude bakina ya fara appreciating abinda nake bashi. Duk kokari nake na ganin na kawar da wannan zancen school din daga raina amma ina abin ya faskara, se na kai spoon bakina se na mayar na goge hawayen dake gangaro min, anan yaya Mariya ta shigo ta sameni. Zama tayi gefe na tareda dauke cup din daura can gefen mu

“Nanah! Menene yake damunki?”

Se na kasa bude bakina kawai na dinga kuka harda shesheka, bayana ta dawo tana zana min wasu soothing circles tana fadin

“Haba Nanah mana, ki daina kuka!”

Kaina na gyada mata, inata suppressing kukan amma the more nayi hakan se naji kamar zuciya ta zata fito daga kirjina ne. Se ta kyalleni kawai ta fara kokarin hada breakfast dukda kana kallon ta kasan akwai damuwa a tattare da ita. Daya bayan daya sauran suka fara janyo jikin su lazily suna shigowa kitchen din, lokacin na daina kukan na wanke fuskata, kowa tazo se ta dauki cup me dama custard nayi, masu tea wasu oats hakanan dai suka gama muka zauna cikin kitchen din suna hira, nikam nayi shiru ban ma gane abinda suke fada nake ba.1

“Yaya Nanah me yake damunki ne? Kinga kamar wadda ake zuke ki fa?”

Kaina na kawar nace

“Nothing”

Kai Nawwarra ta gyada bawai dan ta yarda ba sede kawai dan kar aja maganar tayi nisa. Lubna tace

“Aa Ya Nanah you look terrible ta yaya zaki ce mana babu komai”

Shigowar yaya Rahama yasa ban bada amsa ba, zama tayi gefena tana fadin

“A miko min cup yau horlicks zan sha”

Hannuna nayi stretching na dakko sannan na mika mata, haka muke kamar yaran goye, indai wannan abin na madara ne to idan kika zo gidan mu zaki samu, kai a cikin mu har da me shan cerelac kuma Daddy baya taba complain, shidai burin shi muji dadi kuma kada mu nemi iyayen mu.

A hankali na hakura dan na buga naga babu riba se kawai na sawa raina salama, se lokacin naji wai ashe buk wani friend dinsa ya masa alkawarin bashi slot shiyasa yace kawai na hakura da FUD din. Bayan sati daya dukka muka koma normal kamar yadda muke da, se gidan mu ya koma tamkar yadda yake, farin ciki ko ina. Muna zaune ranar Friday dukkan su sun dawo daga school dama ni ina gida, so kafin su dawo na gama tuka tuwon da nayi niyyar yi nayi musu kuma miyar da nasan se sun kwana suna mita.

“Ya Nanah se yaushe zamu ci abinci ne?”

Nayi dariya ina kara kallon allon tvn dake gabana nace

“Ni ku nake jira Aysha, kira su Nawwara yau a tray zaa ci a kara zumunci”

Ta kuwa juya ta nufi inda bedrooms din mu suke, kafin wani lokaci dukkan su sun fito, dole na hakura da kallon da nake yi na nufi kitchen bayan na diba ma Baba Asabe da ta fita kasuwa siyo zogale. Cikin katon tray na hada tuwon da miyar sannan na kawo mana, wani zabura Aminatu tayi tare da fadin

“Haba ya Nanah but this is unfair wallahi”

Hararta nayi nace

“Dallah zauna, kowa se yaci wallahi”

Miyar kukar tayi dadi saboda na bata lokaci sosae wajen hada ta shi ne zasu min iya shegen da suka saba. Tunda aka fara ci kowa yayi tsit babu me complain se kawai gani mukai tray din wayam, muka kalli juna muka kwashe da dariya, yaya Rahama tace

“Nanah kinyi mana azaba, amma dai ya danyi dadi”

Nayi dariya nace kuma dai. Amal da ummu sukai wanke wanke sannan kowa ya zauna muka fara shirya yadda zamu je hadejia ranar Saturday gurin Mom, Sunday kuma muje kano wajen Anty Sumayya da Yaya nasiba. Haka kuwan akai Daddy bai ki ba yasa driver dinshi ya kwashe mu very early se hadejia, Mom tayi murnar ganin mu dan mun kwana biyu bamu hadu ba, har lokacin bata haihu ba Allah bai kawo ba. Mun dan zaga dangi kadan har wajen Ummansu Mom seda mukaje. Se dare muka iso Dutse washegari muka isa kano.

Bansani ba ko tafiyar da mukai da kuma canjin abinci ne yasa Nawwara yin rashin lafiya, dandama normally idan kayi tafiya kana exceeding abinda kake ci, tunda komai aka baka dan ka farantawa host dinka rai zaka ci. Hakan ce ta kasance akan Nawwara, washegari early Monday morning dukka sun tashi suna shirin tafiya school, ni kuwa ina nade cikin bargo ina bacci, se can naji gidan shiru wanda ya tabbatar min sun tafi, fitowa nayi na leka dakin Daddy bayan nayi brushing na samu ya gama shiri zai fita. Na gaishe shi ya amsa yana tambayar gajiyar da muka kwaso+

“Daddy kaci abinci ne?”

Kanshi ya girgiza yace

“Aa suna ta sauri ina tunanin suma basu ci ba”

Kaina na gyada dan banga alama ba, se nace

“Idan ba sauri kake ba should I make a cup of tea for you”

Murmushi yayi yace

“Thank you Allah yayi miki albarka daughter me”

Da sauri na juya na shiga kitchen na soya masa kwai biyu na hada da tea da bread na kai masa. Seda ya kammalla sannan ya nufi office se ya rage ni kadai a gidan, na danyi gyaragyaren daya dace na koma bacci. Wajen 12noon na farka na shiga gurin Baba Asabe muka gaisa sannan kuma na koma kitchen dan daura abinci. Na gama grating attaruhu kenan naji sallamar Nawwara da sauri na fito dan ganin ko lafiya tunda nasan time din closing baiyi ba,she looks terrible, idanunta sunyi ja sannan sun nutse ciki, ga wani bags a kasan idanun nata,hannun ta akan cikin ta wanda zai baka insight din cikin ke ciwo, laddle din hannuna na yar a kasan kitchen sannan na nufo ta ina tambayar ta menene? Nawwara shagwaba ai se ta fara kuka tana cemin cikin ta ke ciwo kuma gudawa take. Daki na raka ta inata lallama ta sannan kuma ta kwanta tana ta murkususu, a karamin tunani na se na kawo mata tea, she don’t resist tea haka ta karba ta sha se ya lafa tayi bacci ni kuma na lallaba na koma kitchen, lokaci zuwa lokaci ina dubata, a haka na kammalla abincin na zuba inda ya dace na koma dakin da take, tayi amai tun daga bakin gado har toilet ko ina karni yake dole na kure fanka na hau gyara, wasa wasa se karamar magana ta zama babba ko yunkurin amai tayi se gudawa, na rikice na rasa yadda zanyi, se can na kira driver office din Daddy, shi yake kaimu duk inda ya dace apart from makaranta, bai bata lokaci ba muka tafi se Shekoni. ATM din da Daddy yake bar mana reserve na dauka, nasan da kudi a ciki dan dama in case of hakan ya bar mana. Seda na taimaka mata ta gyara jikin ta sannan muka tafi.

Jabir shi ne saurayi na na farko, laboratory scientist ne a cikin shekoni. Bayan an gama duk wata resuscitation procedure kuma God so kind gudawar ta tsaya aka dauka blood aka ce  na kai lab, dake suna da side lab a cikin emergency unit din se yasa ban je can main lab ba. Ina zuwa na bayar aka rubuta min invoice nayi payment sannan aka bani reciept yace naje after 5pm na dawo na amsa. Banma lura da yaya yake ba kawai nasan naga namiji a gurin that’s all, dan ni a wannan lokacin soyayya ita ce last thing dana ke kawowa a cikin rayuwa ta.

Na dawo na zauna a gurinta a raina ina ayyana by now nasan sun dawo kuma zasuyi mamakin bana gida, wayata na fara lalubawa amma naga kwata kwata babu wayar, cikin sauri na mike amma ko kadan na kasa ganin inda wayar take, shiru nayi wai ko zan tuna inda na barta amma na kasa, dan na kasa tuna ko ma na dakko ta daga gida. Bayan nayi sallar laasar naje station din nurses na gaida su dan wanda na samu da safen sun tafi se wasu da suka karba dutyn. Mata biyu namiji daya suna hira saboda babu pt din ma sosae. Suka amsa daya daga ciki ta zuba min idanu se dayar ce tace min

“Akwai wani abun ne?”

Hannuna na saki nace

“Dama dan Allah zan dan iya amfani da wayar ku na kira babana nace my sister is hospitalized?”

Namijin ne ya miko min wayar shi na karba nayi dialing number Daddy amma har sau uku baiyi picking ba, dan tsaki nayi na mika masa nace

“Thank you amma baiyi picking ba”

Kara miko min yayi yace

“Babu wanda kika rike number dinshi a gidan?”

Kaina na gyada dan na rike ta yaya Rahama, karba nayi nayi dialing number, kamar jira ake akai picking.

“Ya Rahma Nanah ce”

“Nanah ina kika je keda Nawwara se neman ku muke?”

“Muna shekoni anyi admitting Nawwara, ku fadawa Daddy sannan ku zo”

Daga haka mukai sallama na bashi wayar tareda godiya na koma wajen Nawwara na samu bata tashi ba, na jima ina kallon yadda ta rame lokaci guda, ga period ga diarrhea abin yayi yawa. Ban jima ba yazo da wayar wai ana kirana, karba nayu naga yaya Rahma ce nsyi picking nan take gaya min na bar wayata a lab naje na karba. Se lokacin ya dawo min tabbas acan na bari , mikewa nayi na bashi wayarta na koma side lab din sede wanda na tarar daxun ya tashi it’s a new face, fuskarshi a cikeda kasumba wadda tasa shi yayi looking old, amma da zarar kunyi eye contact zaka fahimci he’s young. Sallama nayi ya amsa Ba tareda ya dago ba saboda yana dauka sample jikin wata yarinya wadda ke bashi tough time saboda kukan da takeyi. A haka ya dauka uwar tana ta masa godiya. Juyowa yayi ya dube ni ina tsaye a jikin window, hannunshi ya miko min alamar na bashi investigation form din, se nace dashi

“Nazo dazun kawo sample na bar wayata, dan Allah ko ka ganta?”

Kan shi ya girgiza yace

“Ban gani ba!”

Ya fada kanshi tsaye, se na girgiza kai na ciro receipt na nuna mishi nace

“Kaga wallahi i came amma wanda ya tafi bai fada maka ba?”

Receipt din ya karba yayi min retrieving result din ya miko min, karba nayi na fara zama frustrated nace

“Kaga sister dita ta kira kuma ance mata wayar yana lab dinnan fa”

“Kije ki dakko sister din taki”

Shiru nayi ina tunanin yadda zan masa , gani nayi ya cigaba da abinda yake bai ko kara kallona ba, raina yayi mugun baci na wuce na nufi EU din, ina zuwa na samu su yaya sunxo dukkansu, da uban kaya na kai lab result din sannan na tafi wajensu nan na samu Nawwara ta tashi. Abinci take ci na fadawa yaya Rahma yadda akai tace muje lab din. Muka tafi muna karasawa tayi dialing number dita se gata ta fara ringing, dauka yayi zaiyi swiping nace

“Hey! Bani”

Na fada ina mika masa hannu na, kallo na ya tsaya yi kawai se ya miko min, na karba tareda dalla masa harara nace

“Aikin banza kawai”

Se naga yayi dariya wanda ya kara kular dani amma se muka koma naci abinci, anan Daddy ya same mu. Se dare suka tafi ya zama ni zan kwana a gurin ta. Washegari jikin da dama dan har tana tashi, amma sunce akwai medications din da bata gama ba so ba zancen discharge haka dole muka cigaba da zama. Da yamma ina zaune wannan nurse din ta turo aka kirani, naje na sameta tace min

“Meye sunanki?”

“Nanah Fadima”

Na bata amsa, kai ta gyada tace

“Akwai wata da kuke min kama da ita sosae hatta idan kikai murmushi, in fact tafiyar ku ma iri daya ce.”

Kaina na yada nace

“Ayya”

Se tayi min murmushi tace

“Kina da yan uwa a Bidda?”

Kaina na girgiza nace

“Aa! Ni yar jigawa ce dukkan yan uwan mu a jigawa suke”

Kai ta gyada tace

“Allah me halitta.”

Daga haka na tafi, kilan kuga wauta ta, maganar gaskiya I don’t know anything bidda, ban masan ina ne bidda din ba balle nasan mamata yar bidda ce saboda ni Anty Sumayya tace min mamana yar niger ce so na saka niger din a cikin raina.

A rayuwa na fahimci tabbas komai daki daki yake tafiya, lokutan da zakai dating yarinya kasa da shekaru ashirin, wannan lokacin tana jinta a peak level din yanmatancin ta, tana kuma jin itafa mace ce wadda dole maza zasu bita sannan kuma kafin a samu makullin soyayyar nan gani take you have to go down and leak her foot.

+

An sallame mu mun sha yan dubiya sosae musamman daga hadejia, ni har mamakin su nake shi fa Daddy bai damu dasu ba mu din bamu wani dauke su da daraja ba amma su sunata tamu. Hardly kaga munyi cikakken wata guda ba tareda wani yazo ganinmu daga hadejia ba. Akan orals aka maida ta muka koma gida. Kafin mu tafi na nufi wajen cashier dan settling bed fee da bamu biya ba, ina tsaye na karba invoice dina, na biya sannan kuma na koma karbar receipt ni da Lubna muke wannan zirga zirgar, na gaji sosae Allah Allah nake na koma gida na cire kayan jikina, dan hatta kaina se na wanke shi, bana son asibiti saboda wannan antiseptics din, kwana biyun da mukai se ina cikin bacci se in farka se in kalla sauran pt dake dakin se naga duk sun zama gawa. Da kyar nake komawa bacci bayan na karanta series of addua. W
ayata dake cikin hand bag dita ta fara ringing, kokarin in dakko yasa na maida dukkan hankalina cikin jakar kuma muna tafiya, kawai ji nayi na bige goshi na wani hard abu, bawai taurin da zausa gurin ya fashe ba ko kuma yayi jini ba, cikin sauri na dago kaina na Zuba deep brown orbs dina cikin nashi, dan tsaki na saki a hankali tare da kawar da kaina nayi gefe da niyyar rabe shi na wuce, hannun shi yasa da niyyar kama nawa Lubna tayi saurin shiga tsakanin mu, da mamaki na kalleshi na kuma kalla hannuna tare da kallon nashi hannun, so he mean da hannu na zai kama na ayyana hakan a raina. Fuska ta na kara hadewa babu alamar wasa ko dariya nace

“Me kake shirin yi? Ina fatan ba gigin taba hannuna kakeyi ba ko?”

Na tambaya sounding pissed, hannayen shi ya hade alamun bada hakuri yace

“Kiyi hakuri i was just trying to stop you ne. Bawai dama zan rike ki bane”

Se na samu kaina da fasa yi masa masifa kamar yadda na kudurta, hannun lubna naja mukai exiting daga building din muka nufi can inda EU yake daf da entrance din ya kara tareni so ganin hakan yasa na tsaya dan jin me zai ce.

“Though ban san sunanki ba amma kiyi hakuri da abinda ya hada mu ranar, nasan ban kyauta ba amma it’s  for security”

Tabe baki na nayi nace

“Ok!”

Na juya zan shiga ya kara shan gabana hakan yasa nace

“Yanzun meye kuma?”

Tabbas idan kana son kashe bakin mace kace mata tana da kyau, haka jabir yace min, ni kyakyawa ce and he likes everything about me, se nayi lukus inata suppressing murmushi dake son kubce min,

“Meye sunan ki dan Allah?”

“Nanah”

Na bashi amsa a takaice sannan nayi gaba dan naji yadda komai na zuciyata ke budewa, wa yaga farin shiga. Da dan karfi yadda zanji yace

“Jabir!”

A take na rike wannan sunan amma ban juya ba duk kokarina nasan maintaining class dina. Ina shiga kamar ni ake jira mukai ma nurses sallama dake munyi zaman mutunci, dayar me cewa ina kama da wata data sani ta cemin

“How i wish inada hoton Anty A’isha da na nuna miki kinga kamar da kukeyi!”

Se nayi murmushi kawai, ni ko a wildest dream dina ban kawo mummy take nufi ba, ban ma saka abin a raina ba saboda ina ganin ta yaya ma zaayi wani yasan mamata, kuma uwar tawa dama ba a raina take ba.

Muka koma gida muka cigaba da rayuwa, sede ni wani abu ya canja a cikin tawa rayuwar, ba kamar da ba da zamu zauna muyi ta kallo, hira ciyeciye and stuffs. Yanzun inada saurayi wanda yake kauna ta dan ba zance jabir so na yake ba, idan nace haka ina ganin kamar ban mishi adalci ba. Dukda ni din banma fahimci ko ina sonshi ba ko akasin haka, amma dai nasan ban taba bashi dama ba, shi yayi kidan shi kuma haka shi yayi rawar shi.

A dukkan asubar duniya jabir kefara tashi na daga bacci, bayan ya tabbatar na tashi zai kashe kuma. Tunda na fada masa bana zuwa makaranta to wajen ten zai kira yayi ta min hira amma ni a dole mace ce wai kada class dina ya zube ina ganin duk yadda na saki jiki sosae dashi to zaiga kamar ma ni ce ke sonshi plus banma yarda da committing kai a soyyaya ba, sannan ina tantamar ko da gaske son yana a doron duniya ko a kasin hakan. so bana wani bashi amsa daga eh se aa. Bai taba gajiya ba haka nan kullum yana stalking dina.

A kwana a tashi aka samo admission din kamar yadda friend din Daddy ya masa alkawari an samo min pharmacy, ban taba son wani abu clinicals ba saboda i hate asibiti, those walls, white spread sheet na gado da kuma karafunan su balle azo kan antiseptic, gani dama banda hakuri so wannan aikin requires extra tolerance. Haka dai na yadda na karba saboda banida wani option kuma indai ba ina so ne nayi ta zama a gidan ubana ba. An kammalla shiri komai da komai, ni na fara fita wajen jigawa nayi karatu kuma ni na fara zuwa university haka ni ce na fara zaman hostel, hakan na nufin tabbas ni din ta daban ce.

Katon trolley dake gabana inata zuba kaya, Ummu na zaune a gefe na ta gama kukan tafiyar tawa, nikam inata mata dariya, ganin da gaske ba zatayi shiru ba yasa na dakko mata candy na bata se ta zama kamar nayi bribing dinta ne Aikuwa se tayi shiru ta daina kuka. Kaya nake ta lubgawa kamar yadda Anty Sumayya ta fada min, tace na tabbatar na dauka komai. Wayata dake gefe na ta fara ringing, hannu na kai tareda yatsina fuska ta ganin numbers din Jabir, sede ya kira sau uku sannan na dauka muryata can kasa na masa sallama, shi kuma kamar ko da yaushe very cheerful yace

“Nanah sarauniyar mata, ya kike?”

Cikin yanayi na na kullum nace

“Lafiya kalau”

Haka ya dinga min hira daga uhm se uhm uhm shi ne kadai amsa ta har naji alamar ya gaji amma he never complain. Sallama na masa saboda na gaji. Zama nayi  na cigaba da abinda nake , yaya Mariya da tun tuni hankalinta na akan wayar da nake tace min

“Nanah, idan baki son Jabir dinnan ki hakura mana “

“Me kika gani?”

Na fada ko dagowa banyi ba balle na bawa maganar tata muhimmanci. Zama ta gyara tace

“Yadda kike amsa masa ba daidai bane, haba Nanah yana ta fadi tashi a kanki”

Dariya nayi nace

“Ke ya Mariya se kace me saya min abinci, ni fa wallahi babu wani namiji da zan zauna ina bata lokaci na akan shi, ke nifa ya Mariya gani nake love doesn’t exist at all!”

Se ji nayi anyi audhiyya, juyawa nayi naga Laila majnoon tsaye tana min wani mugun kallo, ku se ku rantse kuce Daddy nace ba yq existing. Zama tayi nasan yau mun taro match wajen yaya Rahama, ita din yar soyayya ce sede soyayyar taki karbar ta se gwara kanta take, duk wani famous love story da kake son sani to kazo gurinta, ita din fa duk wani indian love films to ta kalla, haka take

“Soyayyar zaki ce bata existing? Lallai yarinyar nan! Soyayyar”

Ta fada tana stressing letters din da sukai forming soyayya, ni kuwa uwar magana nace

“To meye zaki nuna ya tabbatar tana existing, ni fa gani nake soyayya wahala ce, ta yaya zakai committing dukkan rayuwar ka akan wasu haba ai da sake!”

Nan ta zauna ta dinga zuba ita a dole se tayi convincing dina soyayya does exist, ni point dinta ma ba fahimtar shi nake ba balle na auna shi cikin kaina, ban sani ba ashe soyayya na jirana, bansan haka soyayya take da karfi ba, bansan love can do and undo ba seda abin yazo kaina, ina ganin kamar soyayya ta hukunta ni da fadin cewar ita din bata existing shi yasa ta gwara kaina ta kuma wahalar dani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *