UMM ADIYYAH CHAPTER 78 BY AZIZA IDRIS GOMBE
“Eh! Sorry yanzu za mu dawo. Ki kwanta da
hankalinki, Twinkle.”
Ajiyar zuciya ta yi ta koma ta zauna a cikin ku-
jerar, amma ba wani zancen
kwanciyar hankali’ har yanzu cikinta juyi
yake yi. Daman ya iya wasa da mota haka?
Gefenta ta dan kalla a fakaice, ta ga a natse
yake tafiya ko a jikin sa, kamar ma ba
shi bane ya kusa wurgar da su a titi yanzu.
“Noorie, wane wata aka haife ni?”
Juyowa ya yi ya dubeta, goshinsa a tattare
cikin alamar rudani, “October, Me ya
faru?”
“Ba komai, kawai ina dubawa ne ko ka na
cikin hayyacinka.”
Dariya ya yi ya girgiza kai. “Za ki san wannan
cikin kankanin lokaci.”
Ba ta amsa masa ba, suka ci-gaba da tafiya,
tana kallon hanya hade da sake-saken
abubuwan da ya kamata ta yi tana komawa
gida, saboda shirin liyafar da za su yi
nan da kwanaki hudu.