Alhaji abubakar dankoli shahararan Dan kasuwa ne Wanda yashahara gida da wajen kasan nan
Allahji abubakar d’an asalin garin Kaduna ne dake zaune a anguwar tudun wada
Ficeccene a duniya duk inda kuke tunani sunan shi yaje
Alhaji abubakar shikadai ne agurin mahaifiyarshi kuma amma agurin mahaifinsa su goma sha hudune
Mahaifiyarshi amina itace amarya agurin mahaifinsa kuma ita kadai Allah yaba d’a namiji wannan dalili yasa kishiyoyinta suke mugun matsa mata
Bama iya kishiyoyi ba harda ‘yan uwan alhaji abubakar duk ba mai sonta kasancewar Allah yawa Dan uwansu arziki
Kofaduwa yayi yamutu suna da kaso mai tsoka acikin dukiyar tunda bashida da namiji
Sai kuma gashi kwatsam ya auro matarshi ta hudu kuma karamar yarinya tahaihu da namiji
Shikuma alhaji shuaib dankoli yayi murnar samun magaji da yayi
Ranar suna yaci sunan Abubakar
Tunda aka haifi abubakar mahaifiyarsa batada ishashan lafiya
Uwargidanta hajiya suwaiba da maibinta suka je gurin wani hatsabibin boka shine yabasu magani sukasa mata a abinci ranar sunan abubakar
Haka tayi ta fama da ciwo
Abubakar na da shekara daya aduniya Allah yayi wa mahaifiyarsa amina rasuwa
Rikonshi yakoma hanun uwargida hajiya suwaiba
Hajiya suwaiba yaranta biyar mata
Babbar yarta rukaiya sai kannata hudu
Rukayya tadau komai na bakin halin mahaifiyarta
Dan haka kawai itama tadauki tsanar duniyar nan ta daura akan abubakar
Gashi duk yadda zasuyi abubakar yabar duniya sunyi amma Allah yace basu isaba
Cikin tsanani da kunci abubakar ya rayu agidan mahaifinsa
‘Yan uwan Alhaji shuaib ma sunfi nuna mishi tsana karara
Bayan shekaru 30 abubakar anzama saurayi kuma mai jini ajika
Mai Neman nakamshi duk da yawan dukiyar mahaifinsa hakan baisa ya nade hannu ba
Yayi karatu sosai inda yakai matsayin babban a karatunsa
Bayanwata biyar da kammala karatun professor abubakar ne
Mahaifinsa ya mishi maganar aure yace ba yanzu ba sai yasamu matar da ta dace dashi
Hajiya suwaiba uwargidan allahji shuaib tasameshi da zancen Yakama ta ya matsawa abubakar akan yayi aure Dan duk abokanshi yanzu suna da matayensu
Alhaji shuaib yace mata tunda yace abashi lokaci abashi mana suwaiba
Ran hajiya suwaiba yabaci tace wallahi alhaji kana bata yaron nan dayawa yanzu auren ne sai yagada ma zaiyi
Tashi yayi yabata guri Dan baicika San surutuba
Hajiya suwaiba taje tasamu kishiyarta maibinta tafada mata yadda sukayi da allahji akan abubakar
Hajiya larai tace aikema dai wasa kika tsaya
Mai zai hana muje musami baffa kisan shima mafa ba kaunar yaron nan abubakar yake
Sai muji shawarar dazai yanke
Hajiya suwaiba ta amince da shawarar hajiya larai
Sukayi gidan baffa sunci sa akuwa suka sameshi agida
Nan yazauna bayan sungaisa sukace fada mishi abinda ketafedasu
Yace aikin banza shi shaaibun ne yake daure masa gindin Dan na lura da hakan
amma badamuwa zanyi maganinsu
Zan hada shida hafsat kunga kenan kawar dashi aduniya bazai mana wuya ba
Cikin jindadi sukace hakan ma yayi baffa Dan wallahi muddin yaron nan yana gidan nan fa bawani morar dukiyar Dan uwanku zakuyi
Dan komai nashi abubakar yakesawa akai yanzu kamai na kadarorin alhaji abubakar ne jagoransu
Baffa yace nima abin yana damuna
Komai yazo karshe ita wannan yarin hafsa zata gama mana dashi
Nan dai su hajiya suwaiba murna yakamasu
Sukayi sallama sukatafi gida
Bayan kwana biyu baffa yasamu kaninshi alhaji shuaib da maganar hada yaransu auren zumunci
Alhaji shuaib yace abashi lokaci yayi magana da abubakar tukun
Baffa yace lalle ma shuaibu Ashe maganar da mutane suke fada akanka dagaske ne nawan wai yaronka yafi karfinka
Alhaji shuaib yace yaya kenan
Wannan kuma wani maganane na mutane Wanda idan mutum yanajin irin wannan jita jitar bazaiyi abinkashi ba
Baffa yace kwarai kuwa shuaibu dole kanunamin ban isa da kai ba balle danka
Duk abunda kefaruwa akunnen abubakar
Yashiga cikin falon yadurkusa harkasa yace wa babanshi abbu na amince
a aura min wace baffan yakeso abbu dalilina bazanso kasaba wa ‘yan uwan kaba Allah yasa haka shine mafi alkari
Alhaji shuaib yace Allah yamaka all albarka abubakar Allah yarabaka da sharrin duniya da na lahira Allah kuma yakareka daga sharrin mutum da aljan
Abubakar yace ameen abbu
Baffa yace kagani ba Dan naka ma yafika hangen nesa idan bamu hadasu zumunci tun yanzu sai bayan ranmu zasuyi
Alhaji shuaib yace tunda ya amince ai shikenan
acikin yaran nawa
Wacece za ahadsun
Baffa ya wage baki yace hafsatu mana
Alhaji shuaib yace Allah yasanya alkari
Sukace amin
Baffa yace saika shirya kaje kufahimci juna ko abubakar
Abubakar yace insha Allah baffa zanyi kokari naga nasamu lokaci naje
Baffa yace yauwa hakan ma yayi kyau
Yace nizanwuce
Abbu yace tun yanzu yaya
Baffa yace tunda nayi abinda yakawoni zama ai banawa bane
Abbu yace hakane kagaida gida yace gida zaiji
Bayan tafiyar baffa abbu yakalli abubakar yace nidai hankali na baikwanta da wannan auren ba abubakar
Abubakar yayi murmushi yace karka damu abbu kasa albarka kawai aciki
Hajiya suwaiba da kishiyarta hajiya larai sunji dadin wannan Abu koba komai idan abubakar yamutu suna da kaso maitsoka cikin dukiyar alhaji shuaib
Hafsa yarinyace ga baffa kuma itace babbar yarshi
Hafsat kyakkyawace ajin farko Dan danginsu sungaji kyau ne Dan shima Abubakar ba bayaba gurin kyau
Hafsat tana da zafi Dan ita bata son raini ko kannata ba kasafai tafiye sake musu fuska ba Dan karsu rainata
Ko a school ba mai taka ta barshi sai dai kuma tana da wani hali Wanda ko agidansu ba asanta nadashi wato tausayi da son ‘yan uwanta
Kwatata bata nunawa dan tasan halin iyayen nata
Lokacin da zancen hadasu aure da Abubakar yazo kunnen ta hafsat tayi murna sosai
amma sai ta bar abinda acinkinta
Ba Wanda ya fahimceta
Bayan auren abubakar da hafsat tun abubakar baya kulata irin kyautatawar da take mishi yasa yafara sakin jikinsa da ita
Soyayya sosai suke inda kasan auren soyayya sukayi
Bayan shekara daya da aurensu
Ranar asabar hafsat tana zaune kusa da abubakar tasa mishi ido kawai tana kallonshi yace yadai madam
Tace wallahi dama sonake kabarni naje gida na wuni yau kaga nafi wata banjeba
Abubakar yace shikenan bukatar tace shikenan
Da kanshi yashirya hafsa ma ta shirya suka shiga mota yajasu sai gidansu su hafsat
Suna zuwa yasauketa yabata kudi masu yawa yace tashiga shi sai yazo daukarta zaishiga
Tace Allah yadawo da kai lafiya
Yace ameen matar kirki tayi murmushi tashiga gidansu
Kannanta na murna ga adda hafsat ga adda hafsat tayi murna ita ma da ganinsu
Taci sa akuwa YAU suna da babbar bakuwa wato rukayya babbar yarinyar hajiya suwaiba
Wato yayar abubakar kenan
Nan akagaisa Rukayya tace anya hafsat kina amfani da maganin da akebaki kizubawa abubakar a abinci
Maman hafsat dinta ce nima dai abin yadameni wallahi ace duk wata sai munkashe makudan kudi akan sa munkarbo maganin
amma sai muji sajinkanya kuwa kina yin yadda akesaki kuwa
Hafsat ta zumburo baki tace inayi mana kawai dai shifa yana da addua sosai ajinkinshi Dan infada muku gaskiya ma baicika bacci ba saboda makiyansa
Rukayya tace a lalle wato mune ma makiyansa ko
Ashe bakida kunya hafsat
Hafsat tace kai nifa barin fito muku a mutum ina son mijina
Kuma koda banasonshi bazan taba kashe mutum ba balle ma Dan uwana kuma mijina
Salati sukasa tare da tafa hanu suna salati cikin tsananin kaduwa da maganar hafsat dasukayi
Hafsat batayi aune aune ba taji saukar bugu kota inta
Bakowa bane yake dukanta illa mahaifinta baffa yace ai wanna yarinya da haihuwarki gwamma barinki
Ashe bakya son cigaban mu kinje soyayya ya rufe miki ido ko
Maman ta tace to wallahi ko kiyi abinda mukace ko na tsine miki
Cikin tsananin tashin hankali hafsat tace mama babu biyayya ga aikata sabo
Barin taba aikata abinda kukeso ba sai dai kuhada dani da shi kukashe gaba daya
Nan ma baffa da maman ta suka rufu mata da duka dakyar rukayya takarbeta
aikuwa tana samun anbarta tadauki Jakarta da gudu tabar gidan takal manta a hanu
Tayi bakin titi ta tari keke nafef
Sai gidanta tana shiga tayi dakinta tayi kuka mai isarta kafin
Ta bakanta hakuri takudiri aniyar koza a kasheta bazata barisuyi galaba akan abubakar ba
Takira abubakar tafada mishi ya wuco gida kawai tadawo
Yana zuwa yasameta ba kaman yadda suka rabu ba
Yace meyasameki madam tace bani da lafiya ne shiyasa ma baffa yace na dawo gida
Yace ashsha maza tashi muje asibiti
Tace a a basainaje asibiti ma jikinda sauki yace shidai baiyarda ba
Bata son mishi gardama sosai
Cikin ikon Allah kuwa kitoci sukayi mata tambayoyi
Tayi ta bada na karya
Daga karshe dai suka mata pregnancy test aikuwa aka sameta da ciki na sati hudu
Itakam ma bata sani ba Dan bata laulayi komai
Cikin farinciki abubakar yayi wa Allah godiya
Bayan sundawo gida ne abubakar yatafi hargidansu yafada wa abbu mahaifinsa cewan hafsat na da ciki
Abbu ma yayi murna sosai daga karshe yayi fatan alkairi
Labarin cikin hafsat yabaza ko ina duk dangi asan da cikin dake jikin hafsat
Hajiya suwaiba da kishiyar ce cikin tashin hankali suke tattaunawa
Hajiya suwaiba tace amma larai kinsan baffa ya mugun raina mana wayo
Hajiya larai tace nima nayi tunanin haka kinga gashi yarinyar zata haihu idan ta haihu musamman akasamu namji fa shikenan kashin mu ya bushe
Shikuwa baffa jika za ahaifar mai kinga koba komai za anfana tanan
Nan dai suma suka hau kulla kullansu
Bayan wata tara hafsat tahaifi danta kyakkyawa namiji fari Sol dashi kaman atsaga jini yafito
Yaro sonkowa kin Wanda yarasa
Ranar suna yaro yaci sunan ABDUL HAKEEM
ana kiransa da HAKEEM
Hakeem yataso cikin soyayyar iyayensa ga wayo ga farinjini
Tako inta Hakeem ya hadu
DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️