BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir


zuku-zuku, daya filas din kuma soyayyen dankali ne da kwai. 

Ta mayar ta rufe don duka babu irin cimar ta. Ta jawo jug din ta bude, kunun farar shinkafa ne mai kyan gani, fari sol dashi yaji madarar NIDO yayl shar, da gani wadda ta dama ta kware da damun. Da zafinsa abin sha’ awa. 

Ta ja wani matsiyacin tsaki tsuuuu! Kamar zata tsinke halshen ta. Ta koma ta kwanta yunwa na cin ta, tana tuna barities na dining din gidan ubanta, tana cewa cikin ranta, kowa yana aure don ya ci gaba, amma ita anyi mata auren da za ta koma baya. 

Ba ta san da tsayuwar mutum a kanta ba, haka nan ba ta ji takun shigowar sa ba, kasancewarsa mutum mai nutsatstsen taku. Wani sassanyan kamshi ne mai ratsa zuciya da bargo, na turaren ‘Dior Addict’ wanda ba yau ta fara jin shi ba, saidai idan Zahraddeen din bai shigo wuri ba, shi 

ya bakunci hancinta. 

Idonta a lumshe yake, sai ta sake lumshe shi sabida dadin kamshin, ba sabida farin cikin zuwan mai kamshin ba, sannan ta bude su a kan angon nata, wanda ke cikin ruwan madarar yadin filted dinkin Mohammed. Idanunshi rufe cikin dark spaces, don haka ba za ka iya karantar halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. Fuskarshi kadaran-kadahan, babu tsana babu tsangwama, amma babu fara’a, don ya gama karantar yarinyar ‘yar rainin arziki ce da rainin wayau. A ranshi fadi yake, “zan daidaita miki sahu”. 

Ya ce a hankali, “Kin tashi lafiya?” 

Ta balla mai harara tana daga kwance, a fusace ta ce, “Da ban tashi ba za ka ganni?” 

Ya yi murmushi ya ce, “Zamu wuce Kaduna ta-sani (gaida surukai da yi musu ban gajiya da abokai da angwaye ke yi a washegarin ranar da aka kai musu amare a al’adar hausa) , 

any problem?” 

Ta hura hanci ta sake galla mai harara da dara-daran idanunta tamkar kwayar idanun sa fado, ta ce, “Na yi maka kama da ‘ya’ yan dake cikin matsala?” Ya juya yana cewa, “Wannan kuma rayuwarki ce”. 

Har ya kai bakin kofa zai fita ta ce, “Ka ga malam, dakata, ka yo min cefane in girka abin da zan ci, ba zan ci wannan jagwalgwalon ba………. ” 

Ya wani irin juyo gabadaya ya dube ta, sannan ya kada kai ya fice ba tare da ya ce da ita komi ba. 

Wannan ya fi komi bakanta mata rai, don so take ya kula ta su haura, ta samu hanyar yarfa mishi rashin mutuncin da za ya sake ta. 

Amma kamar ya san takun nata ya ki kula ta. Ta lura shima miskilin kanshi ne, da bai dauki al’amarin mace a bakin komi ba. 

Tunda suka hawo kan titi shi da Kutama zuciyar shi zugi take, zai 

dauki komi amma ban da a raina mahafiyarshi. 

Girkin Innar tashi ne jagwalgwalo? Ya yi kuta ya ce a fili, “Yarinya zan yi maganin ki, zan koya miki hankalin da baki da shi’. 

Kutama ya ce, “Wace yarinya kake magana kai kadai kamar zararre?’’ 

Ya girgiza kai, “Barni kawai Kutama, ina jin lokacin daina aiki na da ‘Dan Kasa Holdings’ ya zo!”. 

A gaggauce Kutama ya faka mota a gefen titi ya ce, “Me ya yi zafi Zahraddeen? Kowa na ganin ka lucky tunda ka zamo surukin Dan Kasa? Ka gama tsallake SIRADIN RAYUWA, ka gama samun duk wani ALHERI na rayuwa da dan adam ke burin samu. Ka bar TUNA BAYA…(lokacin kuncin talauci), haka kawai zaka jawo mana GIRMA YA FADI…… alhalin kai da arziki ana yi muku kallon ALKAWARI HAR BAYAN RAI, kada ka jawowa kanka ABARI YA HUCE… irinna’ Prof. Junaidu 

Galadanchi, ka zamo mai YAKANAH akan diya mace, ZUCIYAR MUTUM….ita take jawo masa danaSani, me ya yi zafi har da hakan za ta faru?” 

Idanunshi sun kada sunyi jajir ya ce, “Ina so in nunawa diyarsa da ke cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE surukuta ta da shi, bata da alaka da arzikin sa. Na auri “yarsa ne don kaunar da yake mini, amma ba don kwadayin arzikinsa ba. 

Daga yau ba zan kara aiki a karkashin wani ba, sai a karkashin gwamnati. Tunda hakan illa ne ga martaba da mutunci na a idon diyarsa. Idan zan yi yawo ‘naked’ (tsirara) ba zan kara aiki a karkashin Dan-Kasa ba. 

Sannan ba zan taba sakinta ba saboda kaunar da nake yiwa mahaifinta. Idan za ta iya zama dani a matsayina na talaka ta zauna, idan ba za ta iya ba zabi ya rage nata…… 

Amma sai nayi mata saiti wallahitallahi. Yadda nan gaba bazata kuma 

yiwa wani rainin arziki ba, wai don yana ci a karkashin mahaifinta….” Ahmad ya ce, 

“Kada ka yi haka Zahraddeen, Alh. Alhaji Aliko bai cancanci wannan sakayyar daga gareka ba…… ” Lumsassun idanun shi ya_ sauke ahankali akan Kutama…. “Kutama sai in zauna in zama mijin hotiho da lafiyata, da kuruciya ta, da ilimina, da martaba ta da komai? Ko ko sai in zauna in zama mijin Hajiya don kawai a ce ina auren diyarsa? 

Dama a ce yarinyar ta san mutuncin mutane ne kamar ‘yar uwarta da da sauki, to ba ta san wannan ba”’. Kutama ya ce, “Wai me ta yi maka ne?” 

Ya ce, “Ban sani ba, tunda duk bayanin nan da na bata lokaci na nayi maka baka fahimci komai ba”. 

Ya ce, “Na fahimce ka mana, sai dai bana bayan ra’ayinka. 

KUDI! Sune mutuncin da martabar my friend. Ya fada yana bubbuga 

kafadunsa. 

Kada zuciya da shirmen mace yasa ka yi saki-na-dafe, ka san dai yadda yanayin kasar tamu yake a yanzu. Takamar ka shine kana da kwalayen ilimi, to akwai wadanda suka fi ka fal a kasar nan amma suna nan zube ‘unemployed (babu aikin yi). Zahraddeen wulakancin da rainin yana tsiro ne? Ko yana toho a jikin dan Adam? 

Balle nawa yarinyar take? Da ka dora mata nauyin kirjinka ka kalallame ta da kalaman soyayya shi kenan za ka mantar da ita shirmen ta. Kai fa ‘giant’ ne Zahraddeen. Irin mazan da baku da yawa a duniya. Wallahi ba irin ku ne mace ke cewa bata so ba, duk abinda take takama dashi kuwa; kyau, ilmi ko arziki. 

To kai matsalata da kai ‘fadin rai’ da ‘ji da kai’. Ko da yake YEEESSS…..! Kana da abubuwan da za ka yiwa diya mace yanga dasu ko ‘yar shugaban kasa ce ba ‘yar Aliko ba. 

To ka yi amfani da wadannan makaman da Allah ya baka, ka yi yakin neman soyayyarta dasu ku zauna lafiya. 

Amma fa ra’ayina ne wannan nake gaya maka, don gaba nake da kai na fi ka edperience a kan rayuwar yau. Ban ce lallai ka yarda dani ba, amma ka yi tunani”. 

Ya tada injin motar suka hau kwalta suka ci gaba da tafiya. 

Zahraddeen kallon sa kawai yake, yana mamakin matacciyar zuciya irin ta al’umma, sabida kudi sai su sarayar da martabarsu da mutuncin da Allah Yayi musu, Ubangiji (SWA) da kanSa Yace “Na girmama bani — Adam!” sai bai ga amfanin ci gaba da magana da mutum mai karamin tunani da kwadayi irin sa ba. 

Don haka ya ja bakinshi ya yi shiru. Har suka shigo Kaduna bai bari sun kara yin maganar ba. 

Nan suka hadu da sauran abokansu suka je wa Daddy Ta-sani. Daddy ya yi murna sosai har ‘yar kwaryakwaryar walima yasa aka hada musu. Zahraddeen ya tambayi Imam Daddy ya ce ya je Abuja kan shirye-shiryen komawar shi, don gobe zai tafi. 

Suka shiga suka gaida Mami, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu, Ssannan ta kawo atamfofin English masu dauke da hoton Safah da Marwah da angwayen nasu da aka bugo daga Ghana na taya murnar aure ta ce su kai wa matansu, da botikai cike da kayan gara su alkaki, nakiya, dubulan, cin-cin, bakilawa ta basu. Duk da ranta bai son Zahraddeen da auren diyarta, amma ya ya Za ta yi? Alhaji Aliko ya fi karfin gidansa. Zahraddeen ya riga ya zamo bangaren iyalin ta. Basu bar gidan ba sai bayan la’asar, motocin kayan gara suka mara musu baya. 

Inna Binta na alwalar sallar magariba aka soma shigo mata da buhunhuna da 

katon-katon da bokitai tare da jarkokin mai iyakar ganinta. 

Duk fadin tsakar gidansu cika ya yi taf, tun tana salati har ta yo lullubi ta fito tana ce da masu saukewa “Ina zan kai wadannan kayan? Ku barsu haka nan’. 

Basu bari ba sai da suka gama saukewa tsaf sannan suka kada kan motocinsu suka tafi, ko tukuicinta basu tsaya karba ba. 

Zahraddeen na shigowa ta soma fada ta ce, “Lallai yasa a maidawa Alh. Aliko wadannan buhunhunan ita ba ta da yadda za ta yi dasu, sai ka ce siyar musu da ‘yar ya yi?” 

Zahraddeen shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi, don ya san halin Alhajin nasu, yanzu idan ya ce a mayar zai yiwa al’amarin wata fassara ta daban ne. 

A nan ne yake gayawa Inna kyautar gidan da ya yi masa, da ya ce ba zai karba ranshi ne ya baci, kuma bai fasa kyautar da ya yin ba. 

Har karfe sha biyun dare yana tare da mahaifiyarshi suna ta hirarsu irin ta da da mahaifi. Sai da Rabi’a ta shigo za ta kwanta ne Inna ta ce ya tafi haka dare ya yi, ita ma barci take ji. 

Sannan ne ya yi mata sallama ya tafi. Ya yi amfani da makullanshi ya bude kofar glass (slidingdoor) ta falon sassanshi ya shiga falon. 

Babu kowa babu motsin komai sai hucin split wadda ta ni’imta falon sosai kamar babu wani mahaluki a cikin sassan saboda yadda falon ya yi shiru. Ya shiga wara idanu a hankali yana kallon yadda aka tsara falon kamar kana falon Alh. Aliko sabida tsari ba tarkace ba. 

Dakinshi ya nufa kai tsaye ya sunce ya shiga toilet ya sakarwa kanshi shower na ruwa mai sanyi. Ya fito yana tsane kai da karamin tawul yayin da babban ke daure a kugun shi. 

Ya dubi kanshi cikin madubi, ya yarda cewa shi namiji ne mai surar MAZA irin wadanda basu da yawa a cikin 

al’umma. Kamar yadda Kutama ya fada. 

Ga koshin lafiya da kuzari, sannan da dakakkiyar zuciya. Kwakwalwar da kullum a shirye take da daukar duk abinda aka koyar da ita. Idan har yana da wadannan ilhamomin, mai zai hana ya ci gaba da yunkurin neman ilimi da fafutukar rayuwa? He has to applaud the idea that, Indibidual is an actor seeking for goal…… 

(and these goals are endless/limitless) wato basu da karshe. 

In haka ne mai zai sa ya zauna diya mace na yi mishi kallon raini saboda kawai yana ma’aikacin § Babanta? Namijin da ya san ciwon kansa, ba mace ce kawai a gabanshi ba, bai dauketa a matsayin jigon rayuwa ba, sai dai wani bangare na rayuwar namiji, wanda amfanin nata bangaren bai zuwa ma sai ana cikin kwanciyar hankali (when the goals are achiebed). Ba ta san cewa shima ba sonta yake yi ba, ya aure ta ne kawai don ya darajja 

kaunar mahaifinta gareshi? Gaskiya ne da ‘yan magana ke cewa ‘Allah daya gari bam-bam’, kuma ‘kowa da halinsa’, sannan ‘kama da wane bata wane’ halinta ba daya bane da na ‘yar’uwarta ba! Ta kowanne bangare basu yi tarayyah ba, to ya zaiyi? Sai hakuri da kaddara. Domin cikar imani. Har ya yi shirin kwanciya ya yi light off ya tuna cewa duk = rashin mutuncinta hakkinsa ne ya dinga bincikar lafiyar ta. 

Ya ja dogon tsaki ya safko daga lallausar gadonshi ya zura ‘bed shoe’ ya zura farar jallabiyyarsa, ya murda kofa ya fito ya nufi dakin nata. Sallama ya yi tare da murda kofar ya shiga. Dakin duhu didim, sai dai hasken fitilar barci koriya. Ya dauka zai samu ta yi barci a makeken gadon ta, sai ya samu akasin abin da ya yi zato. 

Tana bisa darduma daga can kuryar dakin ta yi nisa cikin sujjadarta, cikin 

yalwataccen hijabin sallah. Ya rufe kofar ya koma ya jingina da kofar a hankali, idanunshi a runtse. 

Sai kuma ya bude ya dubi kulolin dake gefensa wadanda ya san na Inna ne. Na rana ya tadda na safe, na dare ya tadda na rana. 

Ya sunkuya yana bubbudewa yana haskawa da wayarshi, ko cokali daya ba a diba ba, wanda ke nufin, har zuwa yanzun ba ta sa komai a cikinta ba, saboda tana kyankyamin mahaifiyarshi. 

Da kanshi ya kwashe filas-filas din ya kai kicin. Ya samu leda ya juye duk abincin. Ba zai so Inna ta gani ba don ranta za ya sosu. 

Ya yankewa ranshi gobe zai yo mata cefanen, kada ta kashe kanta da yunwa a daura mishi jakar tsaba, kaji su bishi. Dakinshi ya koma ya sauya riga. Ya dauki makullin mota ya fita. 

“Yahuza Soya Spot’ ya nufa ya sayo gasassun kaji biyu da robobin ‘fresh milk’ din ‘Oldenburger’ masu sanyi, 

ya zuba a gaban motar ya dawo gida. Yadda ya barta haka ya dawo ya same ta, wato deep in sujjadah. Ya tambayi kansa me take roka ne haka? Bai yi zaton ‘ya’yan gata irin ta masu ji da kansu da takama da iyayensu suna da bukata ba”. 

A gefen ta ya ajiye ledojin ya juya ya fita. Sai da ya koma daki duk haushin kansa ya kama shi. Me yasa ya sayo mata? Me yasa zai biye mata ta raina abincin gidan su? Wanda kuma hakan raini ne ga mahaifiyar shi karara. Nan zuciyar shi ta tunatar da shi cewa “hakkin ka ne ka ciyar da ita, ba hakkin mahaifiyar ka bane ciyar da matar ka”. 

Da wannan ya kwanta ya lumshe ido, yana kukkullawa yana kwakkwancewa, game da future din rayuwarshi ta gaba, da kuma matakan da zai dauka wajen daidaita sahun Marwah Aliko Dan Kasa, ta san wane ne talaka? Ba abin wulakantawa bane. Kowa da ka gani a duniya ba 

wulakantacce bane duk yadda yake, saidai in shi ya wulakanta kansa. Cikin darajojin da Allah Ya yiwa dan adam, babu zancen kudi a cikinsu. Wulakantaccen dan adam shine wanda ya dogara da wani, ba da Allah ba. Wanda yake ganin in ba wannan dan adam din da ya dogara dashi ba, to bashi da madogara. (Allah Ka bamu wadatar zuci irinta Zahraddeen ameen, Takori) 

Imustapha Zubair Dan Kasa (Imam), ke sharara gudu a kan titin da zai dawo da kai Kaduna daga garin Abuja, yana daidai ‘zuma rock’ cikin motarshi banguish tun farkon shigowarta, a wannan lokacin banguish bata zo Najeriya ba, zai iya kiran kansa mutum na farko, dake yawo a cikin ta a Abuja gabadaya. Yana gab da shiga garin Minna wayar 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *