DA MA NI CE CHAPTER 18 BY JAMILA UMAR TANKO

Zainab dai murmushi take tana aikinta Nasrin tana ta babatun ta ita kadai.

Nasrin ta yi fari ta zauna akan wata kujerar roba ta ce, “Antimi in baki labari?”

Zainab ta ce, “Engr. Fu’ad zai zo ko?”

Nasrin ta yi tsaki ta ce, “caf? wannan da

zuwansa da rashin zuwansa ma duk daya. Wai

fushi yake yi da ni , mutum ne mai yawan fushi

da daukar magana. Ke ni ba zan iya ba.

Zainab ta ce, “ke dai na rasa mai Fu’ad

ya yi miki bakya sonsa.” Nasrin ta ce,

“kana son mace amma bazaka lallashe ta ba. Shi fa baya lallashi kuma baya bada hakuri sai dai a bashi, ya cika son kansa. Zainab ta girgiza kai ta ce, “a’a haka ba zai yiwu ba aure ai dan lallashi ne da tausasa

harshe, ba’ace mace ce kadai zata yiwa namiji

ba haka ba’a ce namiji shi kadai zai lallashi

mace ba itama sai ta lallashe shi.”

Nasrin ta bata hannu suka tafa ta ce, “ina

sonki saboda fahimtar nan ta ki Antimi.

Labarin mutanen da suka san abinda suke zan

baki, irin mutanen da suka yi karanci a kasarmu, irin mutanen da ya kamata su mulke mu, wadanda Allah Ya yi musu baiwa ta iya tsara magana a rubuce.

Zainab ta gyara tsayuwa ta ajiye cinyar kazar da take wankewa. Ta ce, “wannan wanene, daga Amerika yake shima? A ina kika sanshi,ko a gidan talabijin dinku?”

Nasrin ta yi murmushi ta ce, “Ban taba ganinsa ba rubutunsa nake gani a facebook kawai. Dr.Jalo sunansa, Dinah ta san shi, munyi ta yi masa magana yaqi amsawa saboda jan aji. Amma yanzu kin ga yana kula ni har ma in tambaye shi abu ya ban amsa.”

Zainab ta harare ta, ta yi tsaki ta juya ta ci gaba da aikinta. Nasrin ta ce “au Dr.Jalon kike yiwa

tsaki?” Zainab ta ce “ke wallahi haushi kike ba ni.

Daman har yanzu baki rabu da bibiyarsa ba. Ni da na karanta wani post dinsa bai birge ni ba, kawai dai ya iya turanci ina ga a turai ya yi makaranta. Nasrin ta mike ta fice daga kicin din cikin fushi, Zainab ta biyo ta tana kwala kira, Nasrin taqi dawowa dan ta yi fushi, Zainab ta sha dariya ita kadai.

Nasarin na shiga daki ta mayar da kofa ta rufe ta ci gaba da karatun rubutun mutuminta. Har yanzu dai bai hau ba. Ta dauko wayarta ta kira lambarsa, a kila-wakala take, zai dauka ko ba zai dauka ba. Sai gashi-kuwa bai dauka ba. Bata ji dadi ba ta ji jikinta ya yi sanyi sai ta fara daina ganin laifin Zainab gaskiya ne mutumin da bai ma san tana yi ba har ta tsaya tana batawa kanta rai.Bugun kofar da ake yi mata ta baci, sai yi ake yi ana sakewa. Ta san Zainab ce sai bata amsa ba amma daga baya ta jiyo muryar Zainab da kuma ta kawarta Dina. Dan haka ta taso ta bude. Ita da Dina su ka yi tsalle suka rungume juna suna murna. Dinah ta ce, “kin huce? Aka ce fushi kike yi. Waya taba min ke?” Nasrin ta zunburo baki ta koma gefen gado ta zauna. Zainab tana ta dariya ta ce “wai dan na kushe wani abokinta a facebook take fushi. Ni da na ji tana yabonsa na zaci ma ta sanshi, ko cewa ya yi yana sonta. Saikawai na ji ta ce bata taba ganinsa ba haushi ya kama ni.” Dinah ta tsaya akanta tana harara ta ce wannan dan wulakancin kika ci gaba da kulawa? Wallahi ke abin haushi ne da ke.

Nasrin ta ce, *ke ma ki biyewa Anti Zainab ki ci gaba da bata min rai. Ni fa ban ce wani wani abu ba fada mata zanyi in ce ya rage girman kai fa, yanzu yana ba ni amsa.”

Zainab ta yi gatsine tayi  zumde da baki ta ce “Ayyah Kanwata yi hakuri, na zaci wulakancin ya yi miki kuma. Yi hakuri my sweetsister.”

Gaba daya suka yi dariya, zainab ta fice.

Dina ta zauna a kusa da Nasrin suka ci gaba da Kallon rubutun Jalo a Facebook, gaba daya suka hada kai suka rungumo Computer suna karantawa a tare suna shewa, suna tafa hannu suna jinjina.

Suna fadin “Allah Ya taimaki likitan likitocin Naija. Dinah ta ce, “gaskiya ya birge ni gashi yaro bai fi shekaru talatin da biyar ba. A wanne gari yake ne?”

Nasrin ta tabe baki ta ce, “inazan sani ni da ba kula ni yake yi ba? Amma mu duba profile dinsa.

Suka dukufa suna ta bincike akansa sai bayanai suka nuna shi likita ne, mazaunin Lagos yana da mace daya da yara biyu maza.

Matar tasa ma ‘yar gidan Minister lafiya ce, sunanta

Rayyana Abbas sun san sunan

Babanta. Nan da man suka koma neman Rayyana Abbas a Facebook, sai kuwa suka bankado ta.

Tubarkallah! Masha Allah!! yar gayu ce matuka sai dai  kyau,baka ce Kirin gajera mai kiba, amma akwai ilimi da kudi. Ita kuma cikekkiyar lauya ce.

Dinah da Nasrin suka yi shiru suna kallon juna suna mamaki. Nasrin ta ce, “shege ai dole ya ja aji ya san yagama zabar mace. Ita kuwa ta yi sa’ar miji mai kwanya, sai ta godewa Allah kuma ta kula da shi dan idan ta yi sakaci mahara zasu

Hmmm