DEEMAH CHAPTER 6 BY ZAHRATEEY
A hankali komai yake zama kamar ba’ayi ba, kullun k’ara girma suke yi kuma kamanninsu da mahaifin su na k’ara fitowa, tun bayan da suka cika wata biyar nace wa _Alaja_ ni makaranta nake so in koma, ba tare da dogon jayayya ba ta amince in da na shiga _UDUS_, _Usman dan fodio university sokoto_ nake karanta _Islamic law_, sosai na dage da karatu babu wasa duk da cewa ina fama da yara, sauki na d’aya mutanen gidan suna kula dasu sosai shiyasa bana damuwa. Ina level 2 _Kisma_ ma ta samu admission tana karanta _Islamic Studies_ sai ya zama yaran suna gurin su _Alaja_ ganin kamar kar wahala tayi musu yawa yasa na cewa _Alaja_ ta samo musu me raino, da farko taki yarda amma daga baya ta amince.
+
Kukan _Ummita_ ne ya tasheni a barci, ni kam wataran kamar in fasa ihu, sai mutum ya fara barci me dadi komai zai lalace, har gwara yan mazan kukan su baya wuce idan sunajin yunwa amma _Ummita_ kukan nata har da najin dadi kawai dai taji tana kuka ana rarrashinta, tsaki na d’an ja sannan na d’auke ta, sauran yan uwanta duk barci sukeyi, kallon agogo nayi karfe takwas na safe, _Kisma_ na kalla dake ta barci harda gyara kwanciya, sannan na kai idona kan yaran, a lokacin suma duk sun bud’e ido, idanun su ne kawai irin nawa, amma bayan haka babu wani abu nawa da suka d’auko, cizon data yimin ne yasa na fahimci ta koshi, kamar in zuba mata mari haka naji dan na lura idan ta koshi kawai sai ta cizeni, ajiye ta nayi na d’auki sauran yaran, sai da na tabbatar duk sun koshi sannan na ajiye su.
Yanzu haka shekaransu daya da wata biyar da haihuwa, duk wani kiriniya sun kware a kai, tun suna wata uku da yan kwanaki suka fara zama tare da yan kiriniya ga shi yanzu har sun fara takawa, ga kokarin cin zalin _Ummita_ dan haka kawai sai su had’u su kifar da ita ko suyita ja mata gashi tana ihu suna dariya, ita kuma babu abin data iya sai kuka da cizo idan ta samu dama. Duk wani abu da tsawon su zai kai duk mun dauke saboda rigimar su, kayan wasa ne kawai jibgi muka cika musu guri da su.
Ganin suna wasa yasa na shige wanka, ina fitowa na shirya zuwa doguwar riga yar kanti sannan na d’aura d’ankwalin na fita. Kitchen na shiga na fara taya _Uwani_ wasu ayyuka, sai da muka gama sannan na koma sama lokaci _Kisma_ ta tashi, d’akin _Inna Suwaiba_ na shiga na gaisheta muka d’an ta6a hira sannan na shiga na _Alaja_ a zaune na same su suna hira a kan carpet, har k’asa na tsuguna na gaishe su sannan nace musu an gama abinci yana dinning, albarka suka saka min kafin na fita.
D’akin na koma na samu _Hindatu_ har ta musu wanka tana chanja musu kaya, bayan sun gama suka sauko suna ta wasa a cikin falon, _Kisma_ kuma ta k’araso dinning muka ci abinci, bayan mun gama na koma d’aki na kwanta.
Karfe sha d’aya da rabi na farka, ina bud’e ido na nagan su sunyi wanka da Vaseline, daga fuskar su har jikinsu, _Kisma_ ce ta fito a ban d’aki ganin abin da sukayi yasa tayi sauri ta k’arasa gurinsu ta kwace roban duk da cewa saura kad’an nema a ciki, ni kam rasa abin cewa nayi kawai na tashi na fice na barsu, ita data ajiye musu sai ta san nayi dasu.
Kitchen na shiga na samu _Uwani_ har ta fara had’a abincin rana, sannu nayi mata sannan muka cigaba da aikin tare, sai wajen azahar muka gama, d’aki na koma na sake wanka sannan nayi sallah, ina idarwa suka shigo tare da _Kisma_ har ta musu wanka ta chanja musu kaya, hararanta nayi kawai na d’auke kai, zama suka yi kusa dani suna surutun su da ba kowanne nake fahimta ba, bance musu komai ba na had’e rai, _Kisma_ ce ta zauna a kusa damu tana cewa “ayya basu suka yi laifin bafa, mantawa nayi na ajiye a gurin bayan na gama shiryawa, toh in shiga toilet in mayar da towel shine fa na fito na samu har sun gama wanka da shi” kallon su tayi tace suce “sorry momy” kallona sukayi sunyi tsuru tsuru da ido wannan ya kalli wannan sai da ta maimaita musu sannan suka fad’a a tare, dariya ma suka bani yadda naga sunyi tsuru tsuru da ido, “shikenan amma kar ku sake kunji ko” a tare suka kad’a kai kamar kadangare.
Kasancewar yau lectures din karfe uku ne yasa nayi sauri na gama komai, na shirya cikin atamfa riga da zani, sai hijabi har kasa da safan kafa saboda lallen da nayi, _Saminu_ direba ne ya kaini muna zuwa nace mishi ya dawo karfe biyar ko kuma idan na gama kawai zan kira shi, _Nasiba_ da _Suliyat_ na samu suna jirana, bayan mun gaisa muna wuce lecture hall. _LIL 2303 Introduction to Islamic law ll_ shine abin da muke da shi, sosai muka natsu muna jotting point masu mahinmanci har matar ta gama sannan tace idan da me tambaya yayi, mutane uku ne kawai sukayi tambayi ciki harda _Nasiba_ bayan ta kara mana bayani tayi mana sallama ta tafi.
Cafeteria muka nufa dan suci abinci, bayan sun gama muka fara duba wasu takardun, muna zaune yayi mana sallama kamar ko yaushe, bayan mun amsa ya zauna a kujeran dake kallon nawa, “meyasa kike son walakantani ne _Deemah_? Idan kina tantama a kaina sai ki fara gwadani tukunna” wani irin kallo na watsa mishi sannan na tashi na fara tattare kayana ban sake minti biyu a gurin ba nayi gama bayan na musu sallama, ina zuwa kuwa sai ga motar gida, da sauri na shiga bayan mun gaisa da _Saminu_ sannan muka d’auki hanyar gida.
Nikam na rasa wani irin mara zuciya ko kuma wani irin maye ne _Faruk_ sam-sam bashida zuciya ko kad’an, tunda yake min magana ban ta6a kula shi ba, kuma dadi na d’aya kawayena biyu basu ta6a tursasani ba, shiyasa ma nake sake sakewa dasu, tsaki naja kad’an sai kuma nayi murmushi dana tuna cewa da ada ne da yanzu ya kusa margayawa, tun bayan tarayyata da baban triple babu wani wanda yazo gurina daya rasa rayuwarsa, sosai abin yake bani mamaki sai dai nayi godiya ga Allah domin dama hakan shine burina mutane su daina mutuwa a kaina.
Ina zuwa gida na samu dayan mayen wato d’an kanin mijin _Ajala_ tun bayan haihuwarsu triple daya zo shikenan ya sani a gaba da zancen soyayya, ni sam babu wanda yake raina bayan mijina kuma uban y’ay’ana _Sufyan_ tabbas na kamu da son mijina tun bayan faruwar lamarin kuma ba zan iya had’a shi da kowa ba, ina adduar Allah ya bayyana min shi mu rayu tare da yaranmu cikin aminci da kaunar juna, ba zan iya kula wani namiji ba alhali ni bansan matsayin da nake ba, _Sufyan_ be furtamin saki duk da cewa yace zai sake ni amma bana ma fatan ace ya sake ni din.
D’aki na shiga nayi wanka sannan na nufi d’akin _Inna Suwaiba_ anan kuma na same su baki d’ayansu, yanda naga ran _Alaja_ a 6ace yasa hankali na ya tashi, tambayarsu nayi ko meke faruwa, kallona _Alaja_ tayi tace “zamanki haka yana damuna, gashi kinki kula kowa har _Kisma_ ta samu saurayi amma ke shuru, a ganinki haka zamu zuba ido a kanki, d’azu yaron gurin _Atta_ ya zo kuma _Alaji_ yace yakamata ki ba shi dama ku fahimci juna, wani irin bugawa kirjina yayi, inba wa dama? Wai wannan yaron dake falo, lailai ma kuwa, ai gwarzon mijina ya riga ya tafi da zuciya ta wanda babu wani fili da zan iya amincewa da wani “ba zan iya aure akan aure ba, _Sufyan_ bai sake ni ba, yarana ta hanya me kyau aka samar dasu, da aure a kaina _Alaja_” na fad’a ina barin gurin cikin kunan zuciya, wani irin kuka
ne yake cin zuciyata da sauri na wuce d’aki na fad’a kan gado.
tabarma a gaban wani bukka ” _Isa_ gobe nefa daurin auren mu, a gaskiya ina cikin farin ciki sosai” kallonta wanda ta kira da _Isa_ ya yi fuskarsa d’auke da murmushi “tabbas ni ma ina cikin farin ciki sosai _Bibalo_, banyi tunanin cewa _Baffa_ zai bani ke ba, nayi tunani ko nace zanyi aure babu me bani y’arsa sai ga shi _Baffa_ ya bani ke, tabbas babu abin da zan iya biyansa da shi illa in rikeki bisa amana” murmushi _Bibalo_ tayi “duk da cewa mu yan kauye ne kuma kauyen ma karami irin wannan kuma a cikin daji ba’a bainan nasi ba, muna da sani dai-dai gwargwado, domin _Ilu_ d’an gidan me gari yayi karatu sosai ta fannin boko da addini shiyasa bamu sha wahala ba, bayan daya dawo daga birni sai ba bud’e mana k’aramin makaranta inda yake koyarda mu daga cikin abin da ya koyo” ta fad’a cike da alfaharin _Ilu_ shine malaminta.
mata ne kuma suna da kishi amma na fahimci cewa suna da kyakyawar zuciya domin duk yadda suka kai ga nuna basa son junansu musanman ma _Mama Qudi_ da suka k’i tun farkon auren ta da _Baba K_ idan da ace abu mara dadi zai sameta to suna tare da ita, ko wacce ma idan abu mara dadi ya sameta suna tare da junansu suna jajantawa, ga misali nan _Inna Suwaiba_ ita da ba ita ta haifeni ba ta tsayamin kuma ta amince a bakin aurenta, da ace bata da kyaun zuciya babu abin da zai sa ta zauna dani, kishi halittace wanda yake tare da ko wace mace kuma yake tare da ko wani namiji, sai dai muna fatan Allah yasa namu ya zamo me kyau ta yadda ba zamu iya cutar da wani ba, ba’a raba mutum da kishin abin da yake so, sai dai kuma mutum na iya daurewa ya kai zuciyarsa nesa ta yadda zai samu natsuwa kuma ya samawa wasu suma natsuwar, zama da kishiya sai an kai zuciya nesa, domin wata duk yadda zata tunzuraki sai tayi wata kuma fatanta duk a zauna lafiya amma wata ita dai ta zauna lafiya amma kowa ya rasa kwanciyar hankali, ni bazance ma anyimin ba dai-dai ba dan ban san banda kishi ba tunda komai ma na a dai-dai ya tafi ba, ita matarsa ce ma zan ce anyi mata ba dai-dai ba sai dai ta ga kishiya daga sama, bana kuma fatan in zama me son kaina da yawa ina fatan Allah daya had’a ya daidaita tsakaninmu tare da hade kanmu dana y’ay’an mu idan lokacin haduwar tamu yayi…