DEEMAH CHAPTER 7 BY ZAHRATEEY
No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by ////////////
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.
Tunda na tashi yau nake jin faduwar gaba, ga wani irin bugawar zuciya dake damuna, ga zazza6i duk ni kad’ai, toh meke ishirin faruwa ne haka? Nayiwa kaina tambaya, tabbas akwai wani abu dake faruwa wanda ya danganci rayuwata. “lafiya kuwa, meke damunki?” _Kisma_ ta fad’a tana k’arasowa kam gadon, hannunta ta kai ta ta6a wuyana da goshina duk taji zafi rad’au “baki da lafiya fa, kinji jikinki kuwa, bari in had’a miki ruwa kiyi wanka sai muje asibiti” ta fad’a tare da shiga toilet din. Mintina kad’an tayi sannan ta fito ta taimakamin na daura towel sannan na shiga nayi wanka, ban wani dade ba saboda rashin karfin jiki, dan ma ruwan dumin ya min dadi.
+
Bayan na fito na samu harta fito min da kaya doguwar riga me dogon hannu, daker na iya fesa body spray ko mai na kasa shafawa kawai nasa inner wears sannan na saka doguwar rigar, turare ma _Kisma_ ce ta tayani fesawa. A falo muka samu su _Alaja_ “lafiya meke damunta” duk suka fad’a a tare, bayan ta musu bayanin cewa zazzabi ne kuma asibiti zamuje sai sukamin fatan samun lafiya, sannan mijin _Alaja_ ya bamu kud’i masu dan yawa wai muyi amfani da shi. A waje muka samu direban yana jiran mu, babu wani 6ata lokaci muka kama hanyar asibiti.
Kamar dai ko yaushe asibiti ba’a raba shi da tarin jama’a, kasancewar saurayin _Kisma_ yana da duty din safe sai komai ya mana sauki bamu bi layi ba, dan ya fito da kansa gurin nurses station yasa suka mana abubuwan daya dace sannan ya kar6i folder dina muka wuce tare, dayawan mutane sunji haushi domin tun safe suke gurin amma ko gamawa da nurses station basuyi ba balle ace an kai folder dinsu har su saka ran ganin likita, domin wanda suka samu dama ire iren mu duk sun shige sun bar su, da wanda suka san nurses da wanda suka san doctors da wanda suka san metrons duk dai wanda suke da connection da manya da kananun ma’aikata. (Jama’a muji tsoron Allah mu rinks adalci a duk inda muka tsinci kan mu, ku rinka bin komai yadda yazo ba wai mu rinke juye shi ba, wallahi idan wani ya yafe wani ba zai yafe ba haka kuma bakin wani guba ne sai kaga ka kasa samun cigaba ko nasaran dakake bukata idan da zaka bincika sai kaga is all due to irin wadannan kananun laifukan da ba’a d’auke shi a bakin komai ba, akwai emergency cases wanda ba sai an sanka ba da anga yanayin ka za’a fara ta kanka amma wanda zai iya jira ya daure ya rinka yin abu tsakani da Allah dan kowa nada nashi uzurin a rayuwa a kuma ko ina Allah ya ajiye mu muyi kokarin kwatanta adalci).
Bamu wani jima ba muka fito muyi running wasu test, wanda zamu kar6a a ranar muka jira sauran kuma sai washe gari, abin ma yazo da sauki ba sai mun dawo ba yace zai kar6o ya kawo mana sai yamin bayanin duk abin daya dace, wasu magunguna kawai muka saya muka wuce, a mota nake cewa _Kisma_ bamu kyauta bafa munje mun samu mutane amma saboda mu muna da yanda zamuyi ga shi har mun gama mun fito su kuma ko oho, daure fuska tayi alamun haushi taji kenan, ni kuma ban fasa magana ba sai da na fad’a mata rashin jin dadin abin da muka aikata duk da cewa ina jin jiki amma dayawa kila sun fini amma basu da mafita, karshe ma earpiece ta saka ta kyaleni, murmushi kawai nayi na kwanta a jikin kujeran motar har muka isa gida.
Sai a lokacin ta kulani ta taimakamin muka shiga cikin gida, lokacin sallar azahar yayi da alamu shiyasa muka taras ba kowa a falon sai su _Ummita_ suna wasa amma anata cin zalinta, idan tayi ihun tayi ihun sai tayi shuru idan ta samu dama sai ta gantsara musu cizon da sai hakoranta ya fito daganan sai ta sulale ta gudu idan kuma suka kamata gashinta shi zai yi bayani ranar. As usual hakan ne ya faru, ta samu dama ta aikata abin da take so ta gudo d’aki, ina shan tea ta fado kan gadon tana zare ido alamun rashin gaskiya “ke meye hakan wai” na tambaya ina kallon yanayinta, dama fuska tayi tana shirin kuka, ita dai kuka baya mata wuya asaran hawaye kamar a kanta aka sauke kuma tanayi tana lashe hawayen, ni dai ba haka nake ba sai dai idan wani a cikin dangin babansu ta biyo, “idan kika min kuka sai na zane ki sai kiyi me dalili” da sauri ta hadiye kukan ta kara matsowa kusa dani tana kallon kofa, bance mata komai ba har na gama na sha magani, alwala ma da zan shiga ban d’aki bina tayi sai da _Hindatu_ ta dauketa suka fita.
Ina idar da sall na kwanta dan hutawa, duk da cewa har yanzu jikina da zafi babban damuwata faduwar gaban dake damuna, na san dai hakan na yawan faruwa dani ne idan har wani abu zai samu wani na kusa dani ko kuma ma abin ya riga ya faru, ganin na kasa samun sukuni yasa na samu _Alaja_ ta kira gida taji komai lafiya lau sai dai 6atan mu shine kawai damuwar, daki na koma na kwanta ina yan adduo’i a zuciyata, idan ba gidan mu ba kenan mijina ne wani abu yake faruwa da shi, tunanin hakan ne ya karamin tashin hankali nan danan zazza6i ya sake karuwa jikina ya koma kamar garwashi.
Har dare jikina yaki dadi sai da aka dauramin drip sannan na samu barci, yaran kuwa ashe kuka sukayi tayi dan ganina a kwance babu lafiya, daker _Hindatu_ da _Kisma_ suka rarrashe su suka samu sukayi barci amma sai ajiyar zuciya sukeyi. Ni kam barci ne ya daukeni sosai amma mafarke mafarken da nayi sune basumin dadi ba _Sufyan_ dina tare da wata mace bayan _Jidda_.
_______________________
Jama’a ne da yawa a ciki da wajen masallacin dake cikin karamin kauyen dake a cikin Forest wanda yake hanyar _Jos_ mutane sai fitowa sukeyi suna musabaha da ango tare da taya shi murnan aure, sosai yake cikin farin cikin auren _Bibalo_ domin yarinya ce me hankali da tarbiyya wanda mazan gari kowa yake fatan ta kasance matarsa amma sai Allah yasa shi din shine mijinta, fara’a sosai ke bayyane a saman kyakyawar fuskarsa. A haka har aka soma watsewa ango da abokansa suka nufi gidansu amarya domin su kwashi gaisuwa.
Amarya tayi kyau matuka a cikin atamfa riga da zani ta sha d’auri me kyau haka kwalliya dai-dai misali sosai kowa ke yaba kyaun da tayi ita kuwa babu abin da yake ranta kamar taga d’an binni, so take yazo ya yaba kwalliyar da kansa hakan zai fi sanyaya zuciyarta, tana cikin tunani akayi sanarwan ga ango da abokansa, wani irin dadi taji a ranta kamar tayi tsalle taje ta shige jikinsa ita kam Allah ya gani tana son d’an binne sosai da sosai, kawayenta ne suka gyara mata lullu6i sannan suka riko hannunta suka fito tare, direct gurin ango da abokansa sukaje inda akayi ta daukan hoto, su kuma ango da amarya sai satan kallon juna sukeyi har aka gama aka waste.
Kasancewar gidanta na bayan gidan _Baffa_ shi yasa ba’a kaita da wuri ba sai bayan da akayi sallar magriba, sosai tayi kuka duk da cewa ga gida ga gida, babban abin da yasa ta kukan nasihar da iyayenta da kuma goggoninta suka mata shine ya tsinka mata zuciya ta fahimci cewa auren ma yaki ne na mata wanda sai kayi hakuri ka kauda kai kuma ka kai zuciyarka nesa sannan zaka samu salama tare da natsuwar zuciya domin ba wai dadin cikin auren zaka fuskanta ka
wai ba har da rashin dadi da kuma wasu jarrabawa da zai iya riskar ka, sosai suka mata nasiha me sanyaya zukata mesa zuciya ta rusuna, kuma ta tuna da cewa zaman duniyar kanta ma ibada shine a kan gaba balle kuma zaman aure wanda yake dauke da taken “aure ibada” a haka har aka kaita gidanta tana kuka tare da sanyawa a ranta cewa ibada shine abin da ya kaita kuma zatayi kokari gurin kare martaban da mutuncin gidansu ta hanyar yin biyayya tare da kiyaye ayyukan dana sani. Bayan sallar ishai ango da abokansa suka iso akayi duk wata alada da aka saba sannan suka tafi suka bar amarya da angonta, suna masu musu fatan alkairi acikin rayuwarsu.
wace mace sa’ar mijin kwarai me son farin cikin iyalinsa…
kin dangin mu ba, tabbas ke d’in yar halak ce kuma wacce take abin koyi ga ko wata mace a doron duniya musanman ma wanda suka zauna dake, banyi dana sanin sanya wa d’iyata _Jidda_ ba domin inason tayi koyi da kyawawan halayyarki, tabbas na yarda fin mutum shekaru ba shi bane zai sa kafi mutum sani ko ka fishi hangen nesa ko kuma ka fishi iya zama da mutane, tabbas kina da halayya me kyau da kuma kyakyawar zuciya, ba zan gaji da maimaita hakan ba ina me alfaharin samun sirika irin ki, duk da cewa ana mana kallon masu kyaun zuciya da bamu d’auki duniya a bakin komi ba duk da tarin dukiyar mu amma idan aka had’a da naki halayyar ba komai bane, y’ay’anki sun samu uwa ta gari, kuma nima kanina ya samu mace ta gari kuma dangin mu sun samu sirika ta kwarai, Allah ya cigaba da kara daura zuciyarki akan turba ta gaskiya, muma Allah ya bamu kyakyawar zuciya irin naki” _Hajja_ dake kokarin shigowa ta duba jikin _Jidda_ ta amsa da amin, sannan ta shigo “tun d’azu nakejin tattaunawar ku, Allah ya muku albarka kuma ya bayyana mana _Sufyan_ a duk inda yake” amin duk suka amsa sannan suka shiga tambayarta ya jikin ta, sun dad’e suna d’an ta6a hira kafin _Hajja_ ta koma 6angarenta _Anty Aisha_ kuma sai da sukayi sallar magriba sukaci abinci sannan ta tafi.