JIDDATULKHAIR CHAPTER 35 BY KHALISAT HAIDAR

Abuturrab bai ce komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa, Jiddah ta sunkuyar da kanta jin bai amsa ba, Umma tace “Amma you are getting much better now” Ya kalli Umma yace “Alhmdlh” Tace “Toh Allah ya kara afuwa…” Mikewa tayi tace “Allah ya sauwake” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ameen” Kofa ta nufa Jiddah ta bi ta da kallo sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, bata san sanda ta mike ba tana son fita dakin taji muryarsa a tsakiyar kanta, “Dauko min ruwan gora a kitchen” Kallonsa tayi don ta tabbatar da ita yake, ganin shi ma kallon nata yake tace “Toh” sannan ta juya ta fita dakin, Ya kalli su Maimoon da ke kallon tv dake aiki a dakin yace “Toh nagode” Kallonsa suka yi a tare da sauri, Maimoon ta wara ido tana kokarin mikewa tace “Allah ya sauwake Yaya” Yace “Ameen” Safiyya tace “Allah ya kara lafiya” a tare suka fita daga dakin suka kullo masa kofar, bayan few minutes Aunty ta shigo dakin rike da goran ruwa ta ajiye masa kan bedside drawer, ya dinga kallonta, can dai yace “Ke kika dauko da kanki?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Ehh, na sa ta wanke kwanukan da aka 6ata a kitchen din” Bai ce komai ba, ta dau magungunansa ta shiga buda masa yace “Aunty….” Ta dakatar da shi tace “Ehh ka hadiyesu yanxu” Bai kuma ce mata komai ba, ta mika masa tulin drugs din, ya sa hannu ya amsa, ta dau goran ruwan ta bude shi ma ta mika masa ya amsa ya hadiye maganin, kallon bowl din hannunsa tayi ganin ba wani shan pepper soup din yake ba tace “Bani in tafi da shi gun wanke wanke, dama nasan baxa ka sha ba ai” Ya girgixa kai da sauri yace “Aa gashi nan ina sha” Tace “To Allah ya sa” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Ahmad ne ya shigo dakin yana dubansa yace “How are you feeling now?” Abuturrab yace “I’m good” Ahmad ya karasa dakin yace “Allah ya kara lafiya” Ba tare da ya kallesa ba yace “Ameen” Ahmad yace “Bari in je masallaci in dawo” Daga haka ya fita. Bayan fitarsa da few minutes Abuturrab ya cire drip din hannunsa ya mike ya dau bowl din pepper soup da Aunty ta kawo masa ya bude kofa ya fita, sau daya ya saci kallon mutanen dake xaune parlor ya wuce kitchen, muryar Aunty yaji tace “Ina kuma xa ka” Ya ki juyowa balle ya tsaya, ta mike ta bi bayansa Umma ta bi ta da wani irin kallo, yana shiga kitchen din ya rufe kofar, Jiddah dake tsaye tana wanke wanke ta juyo tana kallonsa, sae ga Aunty ta shigo, amshe bowl din tayi tace “To sae ka wani fito? ko a waya baxa ka kirani ba in shigo in dauka” kallonta kawai yake, ta ajiye bowl din a gefen Jiddah tace “Mu je” Bai ce komai ba ya juya ya nufi kofa Jiddah ta bi su da kallo, sae da ya fita sannan Aunty ta fita ita ma ta kulle kofar… Umma na kallon Abuturrab tace “Do u need anything” ya kalli direction din parlon ganin Ummi na parlon ita ma, ya karasa can, Aunty tace “Wai kawai mutum ya fige drip da aka saka masa yayi ta yawo cikin gida, ta ya xa a gane treatment din da ake” Abuturrab na karasowa parlon ya xauna yana kallon Ummi a hankali yace “Ina yini Ummi” Ummi tace “Lafiya qlau” Bai kuma cewa komai ba kamar yanda ita ma tayi shiru, Aunty tace “Don Allah ka taso mu tafi ka maida ruwan nan da ka cire” Umma ta mike tace “Wai ke Hafsah wannan shisshigin da neman wajen xama da kike duk na menene ban gane ba? Ina ruwanki da wani drip da aka sa masa, ko ke kika sa masa?” Aunty ta bude baki ta rike ha6a tace “Shisshigi kuma Hajiya Ramlah? Ban gane Shisshigi ba” Umma tace “Sai ki je ki xauna kiyi naxari ki gane da kyau, duk kin bi kinyi kane kane a kan abinda bai shafeki ba a gidan nan, ke kin isa ki hanasa xuwa ya gaida mahaifiyarsa, wacece ke….” Katseta Aunty tayi tace “Aa kinga ni baxan biye maki ba Ramlah dama kina da wani kuduri can da ban sani ba a kaina dake cikin ranki, banda haka ina ruwanki da issue din gidan nan, ita mahaifiyar tasa ai ta san da cewa ya dawo bashi da lafiya amma ko bin ta kansa ta yi, Aa gaskiya ni ba ruwana baxa ayi tashin hankali da ni ba” Hajja ce ta leko daga dakinta tace “Me ke faruwa ne nake jin hayaniya ga dai mara lafiya kwance shememe a gida?” Aunty ta kalli Hajja tace “Kawai dai daga Aliyu ba shi da lafiya ina tsaye kansa sai Hajiya Ramlah ta xo tana gatsa min magana, da yau ace bani da ‘ya yan nan da nayi kwanan takaici a gidan nan…” Hajja ta fito tayi kasa da murya tace “Atoh ae da gaskiyarta Hafsah, kin bi kinyi bake bake kan d’an mutane kamar ke kika haifosa duniya, duk shekaruna a Masar ban ta6a ganin haka ba wllh, don cewa ma xa suyi kin masa wani mugun abun ne, su basa haka abinda ya shafesu kawai suke, da ran Hauwa fa ba mutuwa tayi ba Hafsah, to ina ruwanki da d’an mutane” Aunty tayi wani murmushi tace “Toh ai shkkn, su ma sai su ja sa jiki kamar yanda nake masa su ga ko baxai yi masu biyayyan da yake min ba, ai ko dabba ma yasan me kyautata masa” Bata jira cewarsu ba ta bar wajen, Hajja tace “Kaji mayya, wani jikin xa mu ja sa bayan mu dai bamu san abinda kika masa ba har yau, yin abubuwansa kawai yake irin na en benue fah, da a masar ne idan hukuma basu garkameki ba shegiya nake, don ai ba a san abinda kika masa ba yake makale da ke” Shi dai Abuturrab kansa na kasa, Umma tace “Xan ga yau ko ita ta haifesa, bari Ahmad ya shigo su tafi can gida ya ci gaba da treatment dinsa idan ta isa ta wanke kafa taje gidana taga tsiya” Abuturrab ya daga kai ya kalli Umma, Hajja tace “Shikenan bakinmu alekum, ni ma sai in tafi da kayana kala hudu duk mu tafi can idan ta isa ta bi mu, wllh sai na nuna mata ni yar banxa ce” su Maimoon dai sai dariya suke kasa kasa, Ita dai Ummi girgixa kafa kawai take, Hajja tace “Abinda duk mun san kan iskanci mu da muka xauna a Masar…” tana fadin haka ta shiga daki ta hau hada kayanta, Ahmad na shigowa kuma Umma ta sanar masa can gidan xa su tafi tare da Abuturrab, sosai Ahmad yayi mamakib musun da Abuturrab bai yi ba, shi da yafi kowa sanin halinsa tafiya ayi masa treatment a can gidan isn’t something easy amma sai gashi yaga bai ce komai ba, Hajja dai tuni ta hada kayanta ta fito da yar jaka tace “Wannan dai sai dai muyi mota biyu idan ana son mu tafi cikin walwala” Ahmad yace “Har ke xa aje Hajja” Hajja ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace “Dadina da Masar wllh Yaro bai isa ya raina babba ba, wani ta6aran ai sai a Najeriya, wai ku ji fa wata tambaya da Ahmad ko wa yake ke min, to ina ruwanka fisabilillahi, gidanka ko gidan Hajiya Ramlah, tun fa da mahaifinku ya rasu ita ke ta fadi tashi na ganin shegun danginsa basu kwace katon gidan nan da ku ke ciki ba, mace me kamar maxa kenan fa Ramlah, duk sai da ta bi ta kwatar ma kanta yanci shi yasa ban ga laifin kibar da ta narka ba wllh, gidajensa biyu da motoci da ya bari duk bata amince an cuceta ba, kun ga inda ta fi Hauwa kenan, tunda ita gashi ma mijin ba mutuwa yayi ba amma er benue ta kwace gida da ‘ya ya tana xaune sandandan, ba a san gawar fari ba amma yau ace Usman rai yayi hali ko tsinke da kyar Hauwa ta tsira da shi a gidan nan, balle dama tsawon rai garesa idan Allah ya amince, toh kuma yaro sai ka wani ce da ni xa aje sai kace xanje gidanka, shi sa tunda ku ka yi aurenku da Ramlah sau biyar naje gidan don kada in ja ma kaina raini” Tana kai wa nan ta kalli Umma tace “Wani motar xa mu shiga Ramlah” Umma ta mike tace “Ku je a na Ahmad, ni sai in ja motar Yaya tunda driver baya nan” Hajja tace “Aa gwara in shiga naki mu tafi a nutse, su kuma yaran su shiga motar Ahmad din” tana kai wa nan ta fita gun mota, Ahmad ya bi bayanta yana murmushi don xuwa ya bude mata motar sannan ya dawo duba Ramlah, Umma ta mike tana kallon Ummi tace “Xa mu tafi can gidan yaya” Ummi tace “Toh Allah ya sawwake” Umma tace “Ramlah fa?” Ummi tace “Tana daki tana bacci” Umma tace “Toh bari dai in dubata” daga haka ta wuce bangaren Ummi, Abuturrab ya mike ba tare da ya yarda ya kalleta ba yayi hanyar bangaren stepmom dinsa, da gefen ido Ummi ta bi sa da kallo. Jiddah ta fito kitchen bayan ta gama wanke tulin kwanukan da Aunty ta ajiye mata, Ummi na kallonta tace “Sannu da aiki” Jiddah tayi murmushi ta karaso parlon tace “Umma fa” Ummi tace “Ta shiga daki yanxu” Jiddah bata ce komai ba ta xauna kasa, Ummi tace “Xauna saman kujera mana” Murmushi kawai tayi ta ki tashi, bayan some minutes Umma ta fito daga bangaren Ummi, tana kallon J
iddah tace “Ki je ku gaisa da Ramlah tana tambayarki” Tace “Toh” sannan ta mike ta wuce part din Ummi, Ramlah na xaune saman kujera tayi murmushi ganin Jiddah tace “Sannu da xuwa” Jiddah ta mayar mata murmushin tace “Ya jikin?” Ramlah tace “Da sauki, ya su Maman Abdallah” Jiddah tace “Suna gida” Ramlah tace “Toh ki gaida min su” Jiddah tace “Xa su ji, to sae anjima” daga haka ta fita parlon. Umma ce ke magana da Ummi kasa kasa tana cewa “Allah bana jin dadin hakan yaya, da wnn shirun da kike kina fita harkansa gwara ae ki ci masa mutunci a fili har ita ta ji, gani take tsoronta fa ake, kuma tana lura da zamantakewarku da shi, shi yasa take samun daman yin duk abinda take yi, Sannan ina gaya maki abinda Aliyu yake Allah ba banxa ba” Ummi tace “Bari kiji, jira yake dama ki gama surutanki ki bar wajen ya tashi ya bi bayanta, kice wai bai san abinda yake ba, wllh tsabagen rainin wayo da walakanci ke damunsa, ba dai Hafsah ba gashi ga ta, sae ynxu abun nasu ke wuce misali, kinsan har kudi ya bata wai ta siya masa fili biyu for two months now, amma sae last week muna wata maganar ta gaya min, ni dai bance komai ba” Umma dai ta saki baki tana kallonta, can tace “Allah mai iko ni Ramlah” Umma tayi wani murmushi tace “Mu je dai xuwa kawai” Abuturrab na dakin Aunty tace “Toh kai baka da bakin budewa kace masu gidan ubanka kake son xama har Allah ya yaye maka ka koma bakin aikin ka?” Ya shafa kansa yace “Aunty ae xuwa gobe i will be very okay in sha Allah, da safe xan dawo gida” Aunty ta ja tsaki tace “Aikin banxa kawai wani ke tashi fadi a kanka banda ni, ita ta wani xo har gida nemana da fada, sai kace idan wani abun ya sameka ta ta6a tsayawa a kanka idan ba kinibibi da ya kawota ynxu ba” Yyi kasa da murya yace “Kiyi hakuri Aunty” tsaki ta kuma ja tace “Dai dai nake da ita wllh wllh, kuma xan nuna mata na fi ta iko da kai tunda auren ubanka nake kuma matsayin uwa nake a gareka” Ya shafa kansa ganin ba shiru xata yi ba, yace “Sai na dawo da safen Aunty” tace “Toh transfer din da kace xaka yi fa, gwara fa ayi ayi a hada abun nan, nan da nan xaka ga har lkcn yayi” Yace “Nawa kika ce?” Tace “Ko akwati ynxu ai yayi kusan dubu dari hudu da wani abu Aliyu” Abuturrab dake ta kallonta yace “Akwatin guda nawa?” Tace “Aa seti biyu xa ayi ai” Yace “Dubu dari hudu da wani abu?” Tace “Atoh don bance maka dubu dari biyar ba, ni na ma san sai na cika wllh, ai ba wai akwatin yaku bayi xa mu siya a xuba masu kaya a ciki ba” A hankali yace “Toh shkkn, idan na isa can gidan xan saka maki kudin ai ina da account dinki” Aunty tace “Toh shkkn, amma gobe dai kamar yanda ka fada ka dawo da safe” Yace “In sha Allah” daga haka yayi mata sai da safe ya fita… Parlor ya tadda su Umma da Ummi har sannan suna magana, Umma ta mike ganin ya fito tace “Yaya bari inje kar Hajja ta shigo yanxu tace ba haka ake a Masar ba” Ummi tayi dariya tace “Lallai kam, toh sai da safe” Umma tace “Allah ya tashe mu lfya” daga haka ta nufi kofa, Abuturrab ya karaso gun Ummi yace “Sai da safe Ummi” Tace “Allah ya kai mu” Kofa ya nufa ya fita parlon. Hajja da Jiddah suka shiga motar Ummi da Umma ke driving suka bar gidan, sun riga su Ahmad isa gida, Jiddah na kawo ma Hajja abinci Abuturrab ya shiga parlon, Ko kallon Hajja Abuturrab bai yi ba ya wuce dakin Ahmad, Hajja ta bi sa da kallo sannan ta ta6e baki tana kallon Umma tace “Idan kin lura komai nasa yanxu irin na Kishiyar uwar yake, wllh abun na damuna amma ni nasan me xanyi…” Umma dai bata ce komai ba, su Maimoon da Safiyya suka shigo parlon sannan Ahmad. Karfe sha daya saura Umma ta shiga dakin Ahmad, Ahmad na xaune yana danna laptop dinsa Abuturrab kuma yayi bacci, Umma tace “Toh drip din fa? Naga baka maida masa ba” Ahmad yace “Yace he is feeling much better, xan jira in ga har xuwa gobe” Umma tace “Toh Allah ya basa lafiya” Ya amsa da Ameen, sannan Umma ta fita dakin. Washegari da safe su Ramlah da Safiyya suka shirya suka tafi makaranta, Ahmad kuma ya tafi can gidansu Abuturrab duba Ramlah, Umma da Hajja na can daki, Jiddah na taya Huraira goge goge kafin malamarta ta karaso don karfe tara bai yi ba, Kamar ance ta daga kai taga Abuturrab ya fito parlon, Dauke kai tayi bayan sun hada ido tana ci gaba da goge gogenta tace “Ina kwana” Ya bi parlon da kallo bai ce komai ba, bata damu da hakan ba tace “Ya jiki?” Yace “Ki kawo min shayi yanxu” Yana fadin haka ya juya ya koma dakin Ahmad, ta bi sa da kallo sannan ta wuce kitchen, ta dauraye hannunta ta dau mug ta xuba ruwan flask a ciki ta yi making masa shayin, ta dauka ta fita kitchen din, ta fi minti daya tsaye kofar dakin Ahmad rike da cup din shayin, tana juyawa taga Ahmad yana tahowa, ya karaso kusa da ita yana murmushi yace “Shayi xaki kai masa…” Ta mika masa tace “Aa ce min yyi in kawo masa” Amsa Ahmad yyi yace “Malamarki ta xo tana balcony” Tace “Toh” sannan ta juya ta bar bakin kofar ta wuce dakinsu ta dau Hijab dinta ta saka ta dau takardunta ta fita, tunda Ahmad ya shigo Abuturrab ke kallonsa da cup din shayin, Ahmad ya ajiye masa shayin yace “Ya jikin?” Abuturrab yace “Shayin waye wannan ka kawo?” Ahmad yace “Jiddah ta bada a kawo maka” Abuturrab yace “Toh ni na riga na sha sai dai ka shanye” Tun da gari ya waye Aunty ke ta kiran Abuturrab, ta kirasa ya fi sau biyar daga karshe kawai ya dau account number dinta ya mata transfer din kudin da tace, ba a dau lkci ba ta turo masa message tace “Yauwa sun shigo, xan fita kasuwan yanxu” Ya dinga kallon message din kafin ya ajiye wayar, wajen karfe goma ya fita ya hado wani shayin da kansa sannan ya dawo ya sha, ya sha magungunan sa ya koma bacci…. Jiddah ta shigo parlor karfe biyu saura rike da takardunta, babu kowa a parlon, ta karasa dakin da Hajja take ta bude a hankali taga bacci take, dakin Umma ta wuce ita ma taga baccin take, sannan ta kai takardunta daki ta ajiye ta fito ta shiga kitchen, plates da taga anyi amfani da ta fara wankewa, ta gama kenan aka bude kofar kitchen din….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *