K’ADDARA CE CHAPTER 8
Baba mairo tace kikwantar da hankalinki Amina insha Allahu kika zauna wajensu hajiya ba zaki ta6a yin da kin saniba saboda mutuncin su da sanin darajar mutane da tausayin na k’asa da su.+
Murmushi hajiya tayi tace baba Mairo duk mu kad’ai? Yabon kan ai yayi yawa
Baba mairo tace kun ma wuce haka hajiya wlh tsakani na daku saidai addu’a domin banda abunda zan biyaku halarcin da kuke min.
Aunty khairat tayi murmushi tatashi tadawo kusa da Amina da har lokacin kuka take,
Jawota jikinta tayi tana lallashi tace kikwantar da hankalinki insha Allahu zakiji dad’in zama damu ba na tunanin zaki samu matsala daga 6angarenmu kema dafatan zaki zauna damu lafiya ko da naga alamar kama a 6angarenki ba za a samu matsala ba.
Share hawayenta Amina tayi tace nagode maku sosai da har kuka jawoni jikinku batare da kun sanniba kuma kuka yarda da ni Allah yasaka maku da alkhairi insha Allahu nima ba zaku samu matsala daga gareniba zan zauna daku tsakani ga Allah.
Alhaji yace masha Allah, Allah yabamu ikon rik’eki amana kamar sauran yaranmu, kema Allah yabaki ikon Zama damu tsakani ga Allah.
Gaba d’ayansu suka amsa da Ameen ya rabb.
Hira suka d’anyi cikin nishad’i da farin ciki sannan su hajiya sukayi sallama suka tafi yarage daga baba mairo sai Amina da d’iyarta.
Baba mairo tazauna tayi ta ba Amina labarin mutunci da karamcin su Alhaji.
Washe gari kasancewar ran Thursday ne bayan idi driver ya kawo masu breakfast sunyi, fitowa sukayi suka d’an zagaya asibitin ko da k’afar Amina bata ida warkewa ba ammah ta ji dad’in hakan sosai.
Yauma kamar kullum mummy sai wajen azahar tazo takawo masu lunch bayan sun gaggaisa cikin girmamawa daga nan suka hau hira, mummy tana ta lalla6a Amina duk wani motsi da zatayi sai ta tambayi meke damunta, ko da kusan kullum haka take mata abun har mamaki yakeba ma Amina irin yadda mutanen suke kula da ita kamar daman chan sun santa.
Bayan sallar la’asar suna zaune suna kallo a T.V d’in da take a jikin bangon d’akin wasu ‘yan matane biyu kyawawa sunci gayu sukayi sallama suka shigo.
STORY CONTINUES BELOW

Kar6a masu sukayi Amina tabisu da kallo d’aya daga cikinsu tana kama da hajiya.
Baba mairo tace oyoyoo ‘yanmatan hajiya sannunku da zuwa
Murmushi sukayi sukace yauwa baba mairo dafatan mun sameku lfy?
Baba mairo tace lafiya lou.
Mummy tace har kundawo daga school d’in kenan,
Eh wlh mummy tun d’azun ma muka dawo, baki dad’e da baro gidanba muka koma.
Mummy tace ohk, kun dai ci abinci ko? Eh mummy
Kallon Amina sukayi sukace mummy wannan itace patient d’in tamu?
Eh mummy tace sannan takalli Amina tace Amina ga ‘ya’yana nan sunxo dubaki school suke zuwa saisa baki ta6a ganin sunzo ba.
Murmurshi Amina tayi tace tace Allah sarki Sannunku, ina wuninku? Amsa mata sukayi sannan sukayi mata ya jiki tace dasauk’i
Sukace Allah yak’ara sauk’i
‘Dayar takalli Ameerah da take hannun Amina tace masha Allah babynki mai kyau kawo ta mugaisa.
Murmushi Amina tayi tamik’a mata ita, Itama Murmushi tayi tak’ara cewa masha Allah fyn gurl Ameerah ko sunanta?
Eh Amina tace.
Baba mairo tace Amina wad’annan ‘yanmatan hajiya ne wannan tanuna wadda ta amshi Ameerah tace itace fatima, wannan kuma tanuna d’ayar da tunda suka gaisa bata k’ara cewa komai ba sai shan k’amshi take tana danna waya tace itace Salma.
Amina tace Allah sarki sannunku.
Fatima tayi murmushi tace jiki ya yi kyau kenan Amina tunda har kina taka k’afar
Eh gaskiya Alhmdllh gobe ma za a sallamemu inji Baba mairo
Toh Allah yakaimu Allah yakiyaye gaba
Sukace Ameen.
Daga nan suka hau yin hira ita da fatima kamar daman sun san juna sai bayan isha’i sannan suka koma gida tare da su mummy
Amina bataso tafiyarsu ba, fatima ta burgeta sosai saboda sauk’in kanta irin na yaya khairat ko da mummynsu suka biyo cikin ranta tace ba kamar waccan salmar ba da taketa sha ma mutane k’amshi tana d’auke kai (lol su Amina gani d’aya fa kikayi ma salma ammah shine harda mata mummunar fassara ammah dai muje zuwa)
Ranar juma’a tun dasafe sukayi wanka suka shirya Amina tana ta d’okin barin asibitin kamar ba ita bace tace asibitin shine rufin asirintaba…lol
Sai wajen k’arfe goma Alhaji yazo da kansa yakawo masu breakfast, bayan sungama gaisawa yace anyi discharge d’in nata? Baba mairo tace a’a ko da likitan yazo allura yayi mata kawai ammah baice mana komai ba.
Alhaji yace toh shikenan bari inje office d’in doctor d’in, suka amsa da toh.
Amina Allah Allah take Alhaji yadawo sutafi domin ita a yanzu asibitin har ta gundureta kwana shidda da tayi ammah ji take kamar ta shekara d’aya daman rashin wajen zamane yasa taza6i zaman asibitin tunda batasan inda zataje ba lokacin.
Tare da baba mairo suka had’a kayansu suna jiran dawowar Alhaji
Ba afi minti sha biyar ba sai ga Alhaji ya dawo tare da doctor, dubata likitan yak’ari yatabbatar da babu matsala sannan yarubuta masu takardar sallama tare da wasu magungunan.
Idi driver ne yazo yakwasar masu kayansu yakai cikin mota, tunda suka kama hanya Amina murnar da takeyi takoma ciki duk sai jikinta yayi sanyi cikin ranta tace Allah gani gareka ko wace kalar rayuwa kuma zanyi a yanzu, hawaye duk suka cika mata ido cikin dubara tagoge ba tare da su baba mairo sun ganeba.
Tafiya sukayi ta kusan minti goma sannan suka iso wani dank’areren gida, horn driver yayi dasauri maigadi yazo yahangame masu gate ,
Amina sakin baki tayi tana kallon gidan cikin ranta tace wannan ko dae hotel ne aka kawoni uhm ni da ban ta6a zuwa hotel ba ya za ayi insan kalansa koma dai ina ne zan gani,
STORY CONTINUES BELOW

A wajen da aka tanada domin ajiye motoci suka nufa dasauri maigadi yazo yabud’e ma Alhaji k’ofar mota yana ta kwasar gaisuwa.
Fitowa su Amina sukayi tana biye da baba mairo suka nufi cikin gidan Amina bin ko’ina take da kallo baki a sake kamar wata sabuwar bak’auya, cikin ranta tace gaskiya masu kud’i suna hutawa a duniya mukuma muhuta a lahira _(lol ammah idan anyi kyakkyawan aikin sannan za a huta a lahirar domin babbar asarace mutum yazo duniya yakoma ma ubangijinsa ba tare da yayi kyakkyawan aiki ba, da talakka da mai kud’i duk d’ayane a wajen Allah babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi jin tsoron Allah, Allah yasa mudace)_
Baba mairo dariya kawai take ma Amina ganin yadda duk takoma, bata ida rud’ewa ba saida suka nufi main parlour gaskiya ya tsaru maka-makan kujerune a cikinsa Ash nd black colour labulen ‘akin suma ash and black ne sai k’atuwar plasma da aka sa a bango, gefe d’aya kuma dining area ne, up step d’akuna biyu ne sai daga cikin parlour d’in ma akwai d’akuna biyu, Amina cikin ranta tace na shiga ukku kar dai ace ‘yan yankar kaine nayi gamo dasu hawaye suka cika mata ido tace shikenan ni kuma tawa k’addarar kenan da nasan haka zan samu mutanen nan da ba zan amince masuba….
Maganar baba mairo ce takatseta daga tunaninta tace Amina ga wuri kizauna kafin hajiyar tafito bari inje ciki,
Saman lallausan karfe d’in da yake shimfid’e tsakiyan parlour tazauna a tsorace tare da k’ara rungume d’iyarta, daidai lokacin hajiya tafara safkowa daga saman step murmushi d’auke a fuskarta tace oyoyoo ga patient sannunku da hanya,
Waje tasamu tazauna sannan tace Amina kihau saman kujera kizauna mana ai kema yanzu kin zama ‘yar gida kisaki jikinki mana.
Amina duk’ar da kanta tayi k’asa tace nan ma ya yi hajiya cikin girmamawa ta gaishe da hajiyar, cikin fara’a ta amsa mata tare da tambayarta k’arfin jiki.
Amina tace Alhmdllh.
Dai-dai lokacin Alhaji yashigo yace a’ah ashe kuna nan zaune murmushi mummy tayi tace eh muna jiran shigowarka ne, yace toh gani ai shima waje yasamu yaxauna.
Gyaran murya Alhaji yayi yace toh Alhmdllh Amina muna tayaki murnan shigowa cikin family d’inmu dafatan zaki iya zama da mu, insha Allahu zamu zauna dake tsakani ga Allah kema muna fatan hakan daga gareki, dan Allah kar kibari aji wata matsala ta fito daga wajenki kizauna da kowa lafiya insha Allahu zakiji dad’in zama damu kisaki jikinki kimaida nan yazama kamar yadda zakiyi rayuwa a gidanku haka zakiyi a nan, kimance duk wata damuwa da tasameki kar kimance Allah yana jarabtar bawansa ta kowace hanya ya kamata muyarda da k’addara mai kyau da marar kyau, duk abunda kike buk’ata ga hajiya nan kar kiji komai kid’aukemu a matsayin iyayenki.
Amina hawaye takeyi tunda Alhaji yafara magana cikin ranta tace daman haka rayuwar take idan wani ya k’ika sai wani yasoka a rayuwa komai bak’in jinin mutum ba zai ta6a rasa masoyi ba
Share hawayen fuskanta tayi ahankali Amina tace toh insha Allahu daddy zan kiyaye nagode sosai da karamcinku a gareni insha Allahu zan zauna da kowa lafiya ba zakuji wani abu daga gareniba.
Su hajiya sukace masha Allah, Allah yabamu hak’urin zama da juna.
Amina tace Ameen
Alhaji ne yatashi yace idan da wata matsalar kunyi magana da hajiya sannan yafita.
Murmushi hajiya tayi tace taso muje ingwada miki d’akin da zaki zauna domin kihuta kafin agama abinci kici.
Amina tace toh sannan tatashi tabi bayan hajiya
Fita sukayi daga parlourn tafiya suka d’anyi kad’an sannan ta bud’e wani d’aki daga cikin d’akunan da ke wajen mamakine yak’ara kama Amina ganin wani had’ed’d’en d’aki da suka shiga babbane sosai komai na d’akin red nd black colour ne tun daga kan kujeru, gado, dressing mirror, wardrobe kai har labulen d’akin su ma kalar ne sai makekiyar plasma da akasa a bango komai na d’akin fes agyare yake sai toilet daga gefe d’aya, masha Allah Amina tace ahankali, juyowa hajiya tayi takalleta tace nan shine d’akinki ga toilet chan, Amina tace hajiya da dai anchanza min wani wannan ai ya min girma,
Hajiya tace a’a Amina bai miki girmaba kar kiji komai, ga d’akin baba mairo nan kusa da naki kikwantar da hankalinki duk abinda kike buk’ata kimin magana kid’aukeni kamar uwa agareki,
Toh mummy nagode sosai Allah yabiya ku, Allah yasaka maku da gidan Aljannah
Hajiya tace Ameen, kije kikwantar da Ameerah tunda bacci take kema kihuta kafin agama Abinci
Toh mummy
Murmushi Hajiya tayi sannan taficce daga d’akin
Saman makeken gadon takwantar da Ameerah sannan tazo tana k’ara k’arema d’akin kallo komai na cikinsa ya burgeta, sannan taje tashiga wanka toilet d’in ya burgeta sosai da karambani tasamu tayi using da komai na cikinsa,
Gaban dressing mirror taje cike yake da kayan shafa mai da powder kawai tashafa sannan lipstick sai tafeshe jikinta da perfume,
Wajen jakkar kayansu da aka shigo masu da ita tanufa, cikin wardrobe tajuye kayan sai alokacin talura da k’ok’ewar da kayansu sukayi domin tunda tabaro gidansu kala shiddanan su take sanyawa sai wata atamfa da hajiya maimuna tabata, kunya ce taji ta kamata, dakyar talalubo wad’anda suka d’anfi dama tasaka,
Saman gadon takoma tazauna tajawo alqur’ani tana karantawa kafin afito masallacin juma’a tayi sallah.
Bayan tagama sallah zaune take saman darduma Fatima ce tashigo d’akin dasallama, Amina tana murmushi ta amsa mata, Fatima tace oyoyoo sister sannu da zuwa ina murnar shigowarki cikin family d’inmu, mun ji labarinki wajen mummy kikwantar da hankalinki insha Allahu zaki ji dad’in zama damu, Ameerah bacci take?,
Murmushi Amina tayi tace eh, nagode sosai,
Bakomai kitaso muje muyi lunch su mummy suna jiranki, shuru Amina tayi domin ita ba zata iya zuwa chan ba tayi, Fatima ta lura da hakan tace dole fa kisaki jikinki nidai kitaso kar su mummy sujimu shuru, ba dan tasoba tatashi daman bata cire hijab d’intaba da tagama sallah sai tabi bayan fatima,
Da sallama suka shiga parlourn, dining area suka nufa cikin girmamawa Amina tak’ara gaishe da su daddy, suka amsa mata fuska a sake, mummy tace ina kika baro Ameerah, ahankali tace bacci takeyi,
kujera Fatima tajawo mata tace take a sit please, batayi musuba tazauna Fatima ma zama tayi tayi serving d’insu kowa cin abincinsa yake hankali kwance ammah banda Amina da duk tabi ta takura juya cokalin kawai take……….