Bakura yayi murmushi ya cewa yaron “yaya sunanka?”
Yaron va ce “sunana Yahuza.”
Sai Bakura ya ciro Naira dari biyar ya migawa Yahuza.
•Ya ce “je ka ka sayi kunu kasha sadaka, sauran ka bawa almajirai yan uwanka.”
Yahuza ya karba cike da murna ya na godiya.
Ya ce “ai gidanmu ne ni ba sai na saya ba sai dai in
b’oye in yi dinkin sallah.” Bakura ya zabura yace
“gidanku daya da Sajida kenan?”
Yahuza ya ce “yayata ce uwa daya, uba daya.”
Sai Bakura yayi turus, ya dubi Yahuza ya ga shi
kamarsa daban, Sajida kamar ta daban.
Ya fada a ransa “to lallai kama ce kawai amma ba
had’in Sajida da Zuhuriyya.”
Bakura ya yi shiru can ya sake tunano fuskar Sajida ya
Tuna ta Zuhuriyya ya tabbatar sak kamarsu daya, sai ya girgiza kai.
Ya ce a ransa “ruwa baya tsami banza dole da wani
boyayyen al’ amari a nan.”
Yahuza ya- katse Bakura daga tunanin da yake yi, yace ga Babanmu nan ma ya fito.”
Bakura ya dago da sauri ya dubi kofar gidansu Sajida
sai ga wani tsoho a tsaye dauke da tafkekiyar dorina a hannunsa ta dukan almajirai. Daga ganin fuskarsa ba wasa, tsoho ne wanda baya son wargi.
•
Yahuza ya dubi Bakura ya ce “karka fada masa ka
bani kudi dukana zai yi, zai ce nina roge ka, ya hana mu karbar kudi a hannun baqi. Bakura ya yi murmushi ya ce “ba zan fada masa ba yahuza.”
Baban Yahuza ya kwalla masa kira, ya amsa ya tafi da
sauri wajen mahaifinsa.
Mahaifin Yahuza ya dube shi cikin bacin rai da rashin sakin fuska, ya gyara dorinarsa tsaf tafka kawai yake so ya fara yi.
Ya ce “ka-san shine da za ka je ka naniqe masa, ko kiranka ya yi?
Ba na hana ka zuwa wajen baqi kana yi musu surutun banza ba?”
Bakura ya qaraso da sauri ya ce “Baba ka da ka dake shi ba laifinsa ba ne, ni na kira shi na tambaye shi.”
Baba ya dan saki fuskarsa ya cewa Yahuza “wuce gida.”
Yahuza ya arta gida da gudu, dan har ya saddakar yau sai ya sha duka.
Baba tsoho har yanzu fuskarsa babu walwala ya dubi
Bakura ya ce “yaro ina ka ke tambaya ne?”
Bakura ya ce “mahaifan Sajida na ke nema”
Wannan tambayar ta bawa Baba tsoho mamaki, ya
dago da sauri ya dubi Bakura. Ya ce “kamar yaya mahaifan Sajida kake son gani, me ya faru?”
Ganin yadda tsohon nan ya razana, ya dimauta shine
yasa Bakura ya kasa tambayar kwakwab din nan tasa.
Ya sosa geya ya ce “ance min kai ne Babanta ko?”
Baba ya ce “kwarai kuwa.”
Bakura ya sake cewa “Babanta wanda ya haife ta ko?”
Baba ya tsuke fuska ya ce “‘kamar yaya?”
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce “Baba abunda ya sa nake wannan tambayar ina da dalilina ka yi hakuri a hankali zaka ji komai. Shin mahaifiyar yarinyar nan Sajida ta na raye?”
Baba ya ce “ta na raye in dai ba wannan fitowar ta
yanzu-yanzu ba rai yayi halinsa, dan yanzu na bar ta tana juya kunun kanwa. Me kake so ka ji ne yaro? Idan wani bayani ka ke da shi ka fada mana in ji, me ke tafe da kai?”Bakura ya nisa sannan ya ce “Baba ba komai ba ne, sai dan ina son ma sanar maka cewa ku na tufka ne wani yana warwarewa. Ku na yiwa ‘yarku tarbiyya wani ya na warware muku, magana na ke akan ‘yarka Sajida da Abdul majid
. Sai tsoho ya dauki dogon salati ya ce “au, har yanzu
Abdul majid bai rabu da yarinyar nan ba? Duk irin yakin da mu ka yi da shi a baya. Lallai yau sai na lahira ya fita jin dadi.”
Ya juya a fusace zai shiga gida.
Bakura ya tsayar da shi ya ce “na fada maka badan
hankalinka ya tashi ba, haka kuma ba dan ka daki Sajida ba, sai don ka sake saka ido ku raba su. Duka ko zagi ba shine a’ala ba, ku yi mata nasiha kuma a karbe wayar hannunta don idan an hana ta fita ai ga waya. Ina da zafin rai kamar ka amma ban cika duka ba ko kuma ince ban taba dukan ‘ya’yana ba, ina da tsoratarwa, ina yawan yi musu nasiha da wa’azi cewar su ji tsoron Allah su san duk inda suka shiga suka labe Allah na gaminsu, idan ni bana ganinsu.
kuma na gode.” Baba ya dubi Bakura ya ce “yaro na ji abinda ka ce, Ya juya ya shiga gida da sauri, Bakura ya shiga motarsa ya tafi gida.
Ya na isa gida Auwalu mai gadinsa ne ya taso a guje ya wangale tafkeken get din shiga farfajivar gidan. Sayin ni’ima da gamshin fulawoyi ne za su daki hancinka. Yayin da korayen fulawoyi da jajaye da ruwan dorawa da fararen furanni ne zasu dinga haskake kwayar idonka. A tsakiyar farfajiyar gidan wani round about aká yi shi da tiles amma an dankara fulawoyi a isakiyarsa don haka akwai wani ruwa da yake bululowa ta ciki ya na tashi sama yana ban ruwa. Ga filin ajiyar motoci nan fiye da mota goma za su iya tsayawa a lokaci guda, gefe kuwa ne a jejjere na wasan yara kai ka ce a ‘Wander land Abuja’ kake (wajen wasan yara).
– – Tsuntsaye ne masu kyawun gaske suke kai kawo a .. farfajiyar gidan, kamar dawisu, talo-talo, jimina, aku, da ‘yan qananun tsuntsaye masu launuka daban-daban, gefe kuwa gaton fili ne aka kewaye da birirruka da maguna da burguza-burguzan Karnuka irin na turawa masu gashi buzu- buzu gidan kowananansu akwai bangarensu akwai masur kula da su. Masu kula da filawowi dabam masu wanki da guga daban, direbobi daban-daban. A cikin gida kuwa mata masu aiki kala-kala, akwai makekiyar boy’s quarter a bayan gidan akwai dakunan masu aiki buriik.
Ya na shigowa farfajiyar gidan dan girmamawa sai dukka ma’aikatan kowa ya durgusa ya na kwasar gaisuwa. Dakyar Bakura ya ke daga hannu yana amsawa saboda d’imuwar da ya ke ciki. kai tsaye ya zarce da motar runfunan da aka yi su don ajiye motoci ya tsaya ba tare daya kashe motar ba ya dora kai akan sitiyari ya yi shiru ya na tunani mai zurfi. Bayan Ganin iran halin da Abdulmajid yake kokarin saka Sajida, sai tunanin yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Lallai kuwa kamar ta baci, domin idan ya rufe ido ya hango fuskar Zuhuriyya ada, sai ya hango fuskar Sájida, da maganar da yanayin jikinsu sai ya ga sak iri daya ce babu abinda ya raba su. Ina cikin wani hali. Yaya zan yi na gano bakin zären ne?
Karshen magana dai na je na ga iyayen Sajida kuma babu hadinsu da gauyen Cinkilawa. Kuma na san dangin Zuhuriyya gaba dayansu babu had’insu da unguwar Kawo amma Allah cikin
Ikonsa ya halicesu kamarsu daya sak.” Bakura ne ya fada a bayyane.
Fiye da mintuna talatin Bakura na-zaune a mota ya
kifa kai ya na tunani. Ma’aikata su na ta kai kawo su na tambayar kansu da kansu shin yau maigida lafiya, ya zauna a mota ya kasa fitowa? Tsananin girmamawa da shayinsa ya hana kowannansu karasowa su tambaye shi. Da kansa ya duba agogo, ya ga magaruba ta yi, sai ya kashe mota ya fito.
Idanuwansa sun kada sun yi jawur da alamar tashin
hankali a tattare da shi. Kallo daya ya yiwa ma’aikatan da su ka yi .layi a bayan motarsa sai su duk suka watse domin sun tattaru a waje daya sun yi jugum, hankalinsu ya tashi saboda ganin sabon al’amarin da ba su taba gani ba.
Ya kwallawa Magaji direban yara kira, Magaji ya amsa cikin ladabi ya zo ya duga ya gaishe shi. Bakura ya ce da shi ya mige tsaye kuma ya d’ago da kansa ya dubi kwayar idonsa zai yi masa wata tambaya. Kuma ya tabbatar amsar da zai bashi gaskiya ce kada ya sake yayi masa karya.
Jin haka sai hankalin Magaji yayi mummunan tashi, kan ka ce kwabo ya fara gumi, muryarsa ta hau karkarwa ya tambaya maigida me ya faru?”
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya qurawa Magaji ido,
Magaji ma ya qurawa Bakura ido zuwa wani dan lokaci. Bakura ya ce “daga makarantar boko da ta islamiyya ina da ina Zahra take cewa ka kaita?”
Hmmm