KINA RAINA CHAPTER 7
Me kike nufi da zaki aureshi in ya aiwatar da abinda kika ce?” A firgice ta juyo tana kallon mubeena dake jingine jikin kofan office dinta ta hard’e hannunta a kirjinta fuskanta sam babu annuri.2
A hankali ta sauke hannayenta kafin ta fara cire kafarta ta iso table din maimunatu ta kara maimaita tambayanta kafin maimunatu ta bata amsa ta cigaba da fad’in “maimunatu dont tell me kina so khalid ya watsar da wancan maganan auran nasa da ya rage saura kwanaki ke kuma zaki aureshi ne?” Zaro idanuwa maimunatu tayi tare da bude baki amma ta kasa cewa komi ita sam wannan tunanin bai tab’a darsuwa a zuciyanta ba she is not that selfish ganin ta kasa magana yasa mubeena dafata cikin sanyin murya tace “ban taba yi miki wannan kallon ba,ban taba kallonki a matsayin mace me son kanta ba pls kar ki canza daga yanda na sanki,ka sowa dan uwanka abinda ka so wa kanka.”1
Murmushi maimunatu tayi tace “thank God kin shede ni sam ni ban cewa khalid ya fasa auransa ya zo ya aureni ba,mubeena khalid ya dameni sai na saurara shi bayan ya auri habiba ya aureni,ni kuma nace mishi ya sanar da habiba da iyayensa in sun amince nima na amince zan aureshi,na san ba zai taba iyawa ba shi ya sa nace mishi haka dan a zauna lafiya.”1
Shiru Mubeena tayi tana kallonta a hankali tace “Allah yayi zab’i,duk yanda nake sonki da khalid ban so ki zama silan bacin ran wata.” Wani kallo maimunatu tayi mata can kuma ta saki murmushi indeed ciwon ya mace na ya mace ne.1
“Ke yanzu in ya nemi yardansu suka yadda zaki amince ki aure shi?” Dan d’aga kafadu maimunatu tayi tana idonta kan computer da take kokarin kunnawa tace “abu ne mai wuya su amince shi yasa ma nace mishi hakan.” Numfashi mubeena ta sauke tace “what IF suka amince?” ta emphasising akan if din tabe baki maimunatu tayi tace ba tare da ta kalli mubeena ba “sai in aureshi.” Zaro manyan idanunta mubeena tayi tare da rufe bakinta da tafukan hannunta tace “wow! You love him!” Rolling idanunta maimunatu tayi tace “ke dai wallahi.” Da dan yatsa mubeena ta nunata tace “so you love him all this while kike denying har ma da ce min kina da wanda kike so,wallahi maimunatu kinji haushin kanki.”1
Maimunatu bata ce mata komi ba sai da ta connecting tab dinta da system dinta sannan ta juyo tana fuskantar ta dan shagwabe fuska tayi tace “i cant believe ni boss dina ke hana ni aiki.” Ta fada kaman zata yi kuka.1
Kankantar da idanu mubeena tayi can ta saki wani marayan kukan shagwaba kafin ta bubbuga kafanta tare da barin wurin ta shiga office dinta har da banging kofa,murmushi mai fadi maimunatu tayi sannan ta juya ta cigaba da aikinta sam taki bawa tunani muhalli a brain dinta bata so ta tuno abinda ya wakana a yau din har sai ta je gida ta nutsu.1
Ta dan aiwatar da aiki taji kanta na mugun sarawa lokacin ko la’asar ba ayi ba kifa kanta tayi a jikin table dinta tana mayar da numfashi d’ai d’ai a wannan halin mubeena da ta fito tambayanta abu ta sameta,dan is hardly kaga mubeena ta kira maimunatu office dinta sai dai in aiki yayi mata yawa amma duk abinda take so zata zo ta amsa ta koma ita dai haka kawai Allah ya saka mata soyayyar maimunatu.1
“Subhanallahi! Maimuna me ya sameki?” Ta tambayeta tare da daura hannunta bisa jikinta dago da kanta maimunatu tayi tana lumlumshe ido tace “wallahi ki bari fa magrain tashi daya.”
“Innalillahi sannu ina ga ki tafi gida ki samu kisha magani stress ne zuwa gobe inshaaAllah u will be alright.” Gyada kai maimunatu tayi ta fara tattara kayayyakinta tana yiwa mubeena bayanin abubuwan da akwai.1
A daddafe maimunatu ta koma gida ko wanka bata iya yi ba taci abinci ta sha magani sannan ta kwanta bacci ne mai nauyi ya dauketa cike da mafarke mafarke!1
Marwan bai samu sukuni ba saboda aiki da rincabe mishi ga na oficce dinsu ga na company dan shi sam bai cika waiwayan company din ba sai in abu yaci tura.1
Zaune yake a cikin wawakeken office dinshi tuni ya cire jacket din suits dinshi daga shi sai light ash colour shirt hatta necktie din sa ya cire ya balle bottuns uku na saman rigar gaba d’aya ya rasa tunanin da zai yi ganin maimunatu ya rikita masa lissafi ya ganta a lokacin da yake da tsananin buqatarta a rayuwarsa sai dai me? Ganin nata ya zo mishi da kalubalen da bai taba tunani ba. Ya rasa fushin menene take yi dashi haka? Ya rasa menene laifinshi a wajenta.1
Shi ya kamata yayi fushi,shi tayiwa laifi ta tafi ta bar cyprus without a second glance in da ka san bata taba rayuwa a cyprus ba sam babu alamunta wani son ganin ta yaji tsam ya mike can kuma ya koma ya zauna ganin da yayi mata ya tabbata wannan ba maimunatun da bace wannan is a wild cat ba zai so yan uwanshi su san da maganan maimunatu ba har sai ya shawo kan abarsa he is very sur hakan ba zai yi mishi wahala ba,duk tsagerancinta ya san tana mugun shakkansa kuma ko ba komi akwai soyayyarsa a cikin zuciyanta wannan zai taimaka mishi wajen shawo kanta murmushi yayi tuno da kalmar dan iska da ta kirashi eh din yaji shi dan iska ne kuma wallahi sai taga iskanci.2
Kyakyawar wayarsa ya dauka wanda ke zaune bisa table dinsa direct email dinsa ya shiga inda ya fara lalubo hotunanta na da a hankali yake kallo yana ganin bambancinta da ganin da yayi mata yau a hotunan babu komi bayan yar yarinya mai dauke da tarin yarinta a wancan lokacin ba karamin appreciating surarta yake ba amma ganinta shi da ita yau ya sare sai yaga da ba komi ma take dashi ba yanzu ne ta mallaki abubuwan da za a kira kaya.1
“Damn!” Ya furta tare da mayar da kansa jikin tattausan leather seat dinsa ya limshe ido yana shafa kirjinsa da hannu daya shi kadai ya san tunanin da yake kai kawo cikin brain dinsa “he have to win her back,he have to have her!” Abinda yake ta nanatawa kenan sam Taheer is not a threat to him Taheer bai isa su had’a nema dashi ba,ya san Tahir ya san wanene Taheer kar yake kallonsa.1
Maimunatu bata farka ba sai dab da magrib Allah ma ya sa ba sallah take ba,alhamdulillah ciwon kan ya sauka wanka ta fara shiga ta kintshe kanta sannan ta saka irin over size t shirt din nan sannan ta zauna tana duba missed calls dinta kiran Taheer,mubeena da khalid ta gani sai message daga wajen khalid da yake mata ya jiki dan ya bi office suka hadu da mubeena take gaya mishi ,reply tayi mishi da taji sauki ta gode.
Daga nan ta bi bayan kiran mubeena sun dan taba hira kiran Khalid ya shigo wayanta shima basu wani dade ba dan ana shirin shiga sallah time din.
Tana ajiye wayar ta tashi ta nufi kitchen ta samu an riga an gama abinci fruits salad kawai ta deba me sanyi dan sam bakinta babu appetite tana fitowa momy itama ta fito tana sanye da hijab da alama sallah tayi ko zata yi “sannu da gida momy” shine abinda tace tana kokarin wucewa1
“Keh! Ke nayiwa fruits salad da zaki je ki deba baki tambayeni ba?” Dan daga gira daya maimunatu tayi da alama yau rigimar ta momy ta motsa in ba haka ba ai a cikin saura ta deba ba na cikin bowl dinsu ba.1
“Ba dake nake magana ba kin mayar dani sakara? Wato ke rashin kunyanki gaba gaba yake ko saboda kinga tsawonmu ya zo daya muna gogan kafadan juna?”
“Toh fah!” Shine abinda maimunatu ta furta
Momy na shirin kara magana daddy ya shigo yana fadin “yaya ne haka nake jin hayaniya? Wai me kuma ya faru?” Cikin tsananin bacin rai da bata san a ina momyn ta aro ba tace “wai daddy ka duba yarinyan nan sam babu da’a a tattare da ita kaman maimuna da girmanta ta dinga yin abu kaman mara wayo yaya zan hada maka abu taje tana deban son ranta ba tare da ta tambayeni ba,ni boyi boyinta ne? Duk kokarin da nake yi kan baby wani sa’in sai ta nuna rashin tarbiya in ita ba zata taimaka min ba ai sai tayi nata ko?”1
Sam daddy bai ga abin fada ba a nan kuma sosai yaji wani iri da ta kira mishi yarinya da mara tarbiya yace “dear kiyi hakuri,ke kuma maimunatu” ya juyo kan maimuna dake kallon wannan draman baki a bude “sam baki kyauta ba in ba zaki tayata aiki ba sai ki tambayeta kafin ki debar mata abu.” Ciki ciki momy tace “ai ba laifinta bane taga kanmu ya zo daya ne.” Cikin dan hasala daddy yace “haba Rahina ya zaki dinga magana irin haka? Ke ba mahaifiyar maimunatu bace in tayi abu ba dai dai ba ke ba mai tsawatar mata bane? Haba! In aure kike so tayi ke ba mai zaunar da yarki kiji manemanta bane? Nifa bana son shashanci,ke maimunatu wuce kije ki fara tunanin wa zaki fitar a manemanki ai na san dai ba ki rasa masoya ba…….
Daki maimunatu ta wuce ranta na yi mata tukuki gaba daya sai fruits salad din ya fice a ranta kuka ta fashe dashi ganin momy taci nasara akanta daman ta san dalilinta na takalanta fada kenan ai.2
Shiru tayi tana kwance tana kallon roofing dakin tunani ne kala kala a ranta wayarta ce ta fara ringing a hankali ta janyota kasancewar tana kusa da ita Taheer ke kira dan guntun tsaki ta ja a hankali ta picking wayar tare da yin sallama
“Pretty shine kika gudu kika barni ko.” Yayi maganan cike da shagwaba dan murmushi ta saki tace “ba guduwa nayi ba T kaina ke ciwo shine mubeena tace in dawo gida.” Dan jim yayi jin ta ambaci sunan mubeena kaman wanda aka tsikara yace “ya salaam pretty sorryyyy buh ya jikin naki? Hope kan ya bar ciwo?” Limshe ido tayi tana murmushi dan ita tabararsa dariya yake bata tace “da sauki Taheer.” Turo baki yayi kaman yana gabanta yace “uhm uhm ni dai T zaki ce min kaman yanda kika fara.” A hankali ta dan yi dariya tace “T it is then.”
“Yauwa nagode yanzu dai bari kar in kara miki ciwon kan kiyi bacci me dadi and also dream of me ko?” Cikin murmushi tace “ok,nagode nima” kiss ya blowing mata sannan ya kashe wayar dariya tayi tana kallon fuskar wayan yana tuna mata da zamanin zamanta da marwan a cyprus gabanta ne ya fad’i tunowa da tayi Marwan fa ya dawo rayuwarta and da alama ba zai barta ta shaki numfashi mai dadi ba.4
Moment dinsu na dazun ta tuno yanda ya wani cukuikuyeta dan ya raina mata wayo Allah sai yanzu ta kara tabbatar da tantirancinsa limshe idanu tayi tana comparing marwan din da da na yanzu marwan din da is a lil bit slim wannan is muscular kilan yanayin training ne na sojoji hmm she cant believe marwan soja ne toh tun suna tare ne ko bayan sun rabu ne cos apart from sanin da tayi shi doctor ne kuma yana studying medicine ba abinda ta sani game dashi bata ma taba sanin yana da sisters ba ko wani company hmmm.2
Cigaba tayi da comparison dinta marwan da ta sani yana barin a very short beard wannan kuma babu gashi ko d’is a fuskansa he looked more huge kasancewan dama akwai tsawo to yanzu ga muscles sai dai a fuska he look younger idanunsa masu bata tsori sun kara girma sai yanzu take ganin kamansu da mubeena idanun nan nasu kwal kwal nashi ma ya fi nasu girma
Duk yanda ta so kar maganganun mubeena su dawo mata na rayuwar marwan sai da ya dawo mata she feels used,played ita ba komi bace facce wawuya one of his flings da bai samu ya keta ba yanzu da ya ganta shine zai dora daga inda ya tsaya.2
Kuka ta fashe da shi tare da juyawa ta kife kanta a jikin pillow kuka tayi me yawa wanda ya saukar mata da zazzabi me zafi daren ranan ko runtsawa bata yi ba saboda zazzabin da ya rufeta sai rawan dari take haka ta kwana cikin mawuyacin hali sai gabannin asuba bacci ya dauketa bata farka ba sai wajen 10am jikinta a sanyaye ta sakko daga kan gadon tana me tausayin kanta ace an ga har goma tayi bata fito ba babu wanda ya leka yaga halin da take ciki? Yatsunta ta sa ta goge kwallan da ya zubo mata maraici bai yi ba da uwarta na nan ai da ta san halin da take ciki yanzu da mutuwa tayi kilan sai tayi wari za a san ta mutu.1
Da wannan tunanin tayi alawla ta fito a zaune tayi sallah dan jikinta ba kwari wayarta ta dauka dan ta gayawa mubeena ba zata samu daman zuwa ba missed calls dinta ta gani Allah sarki mubeena dama haka rayuwa yake sai ka ga naka bai damu da kai ba amma wani bare ya dauki lalurarka ya sa akanshi.3
Mubeena na zaune tare da Marwan a office dinta wayarta tayi kara murmushi tayi tace “kagani ma ita take kira dama na san haka kawai ba zata ki zuwa ba.” Dan dama yanzu yake mata korafin ina sexretary dinta sun sani sarai ba ya son wasa da aiki,zuwa yayi ko ganin fuskar maimunatu yayi sai ya tarar da table dinta empty ba mamaki shi take gujewa.1
Ajiye wayar tayi fuskarta da alamun damuwa tace “wallahi yayana jikin nata ne har yanzu.” Dan tabe baki yayi dan shi ya sani sarai shi maimunatu ke gujewa ba wani rashin lafiya he just pray ta gama fake ciwonta kafin week din nan ya kare dan zashi military office dinsu na ibadan week me zuwa cikin kulawa yacewa kanwarsa. ” kar ki damu she will be ok.” Safeena ce ta dan knocking kofar kafin ta shigo gaisawa suka yi da mubeena kafin cikin yauki tace “yah ga nan sajidda diyar hajiya baraka ta haura office dinka.” A hankali ya furta “wtf!” Ya mike tsaye ba tare da ya saurari kowa a cikinsu ba ya fice.
A tare suka ja tsaki sai kuma suka sa dariya ganin sunyi tsakin a lokaci daya mubeena ce tace “wallahi na tsani yarinyan nan su suke kara dulmiyal da yayana duk da dai yanzu ba ya biye musu amma ina tsoron shedan kar ya rinjayeshi.”2
A zuciya safina tace ni da zan samu ko da wannan sigan ya kalleni ai da naji dadi a fili kuma tace “hmm kema dai mubeena akwai son kai mace na bata namiji ne ai sai dai ma shi namijin ya rinjayi mace.”
Dafe kai mubeena tayi tace “ke baki gane ba wallahi duk iskancin namiji sai mace ta bashi dama,mace kuma yanzu yanzun nan zata iya seducing namiji ta sigogi da dama kuma ya fada tarkonta shi yasa nake ganin in mata zasu kame kansu zina zata ragu.” Gyada kai safeena tayi cike da gamsuwa tace “toh Allah ya dada shiryar damu ameen.”Ko da ya bud’e office din bai ganta ba,dan juye juye yayi can ya hangota zaune cikin mini palo din office din ta daura kafa daya akan daya. Dogon wandon jeans ne a jikinta sai wata yar karamar riga sai ta dora kimono na wani rantsatsen yadi me santsi kanta yasha fixing da human hair me tsadan gaske ba zaka tab’a cewa ba nata bane sai shi din da ya santa ciki da waje.1
Hannunta rike yake da can juice tana sha lokaci daya kuma tana sakar mishi murmushi,numfashi ya ja ya fesar kafin cikin takunsa na isa ya taking steps zuwa gareta,tsam ta mike tare da ajiye juice din hannunta ta ware mishi hannu dan rungumanta yayi cikin 5 seconds ya zare jikinshi,kokarin kai bakinta da ya sha oily lipstick ga nashi take yi ya kau da fuskarsa gefe.1
Dan pouting bakinta tayi tace “haba! Marwan kaman baka yi kewana ba.” Dan kallonta yayi cikin ido tare da d’aga gira d’aya yace “gaskiyan kike so?” Shiru tayi dan ta san waye marwan yanzun nan sai ya lalata mata zuciya duk da shirun da tayi bai hanashi gaya mata gaskiyan ba
“Sincerely speaking banyi kewanki ba asalima ni na manta da ke,wai ke kam sajida me kike nemane ba kwanaki naji senator hambali ke nemanki ba? When will you settle down? You are already 30 ban san me kike ji a wannan hanky panky din ba its about time ki san me kike ciki.”1
Kankantar da idanunta tayi tana sauraron wannan cin fuskan na marwan har kura zai ce da kare maye?1
“Lallai ma Marwan wato baka san me nake ji a wannan hanky panky din ba? Toh wa ya koya min tare da waye muke jin dadinshi ko zaka ce min ka tuba ne?” Ta tambayeshi tana me zagaye hannunta a wuyansa cikin fushi ya cire hannunta yace “damn you sajida i didnt fucking teach you how to fuck da iyawarki na ganki so kar ki yarda kiyi min sharri.” Ya juya mata baya yana kara gyara necktie dinsa.3
Murmushi tayi ta leko fuskarsa tace “ai dole ka juya min baya ko da ba kai ka disvirgining dina ba but you fucked me more than he do saboda haka ni yanzu a shirye nake ka fito ko wani time ne muyi aure.”1
Wani kafirin dariya marwan ya saki yace “maimaita abinda kika ce muji?” Waro idanu tayi tace “nace ka fito muyi aure” tabe baki yayi tare da mata wani kallon rainin hankali yace “oh really?” Ta gyad’a kai girgiza nashi kan yayi yace “you most be sick.”
Tana shirin kara magana yace “saj pls ki tashi ki tafi ni da ke mun san abin nan da kike fad’a ba me yuwuwa bane ,ko da can ban so ki ba balle yanzu,in baki manta ba bari in tuna miki ke kika ce kina sona ni kuma na gaya miki bana jin sonki me kika ce bayan nan?”
Juya idanu tayi tace “naji naji ni nace muyi friends with benefits but i thought after that zaka soni ne ai.”
Girgiza kai yayi yana murmushi yace “then you are mistaken,ta ya za ayi in soki just because i screwed you ke kadai na taba kwanciya da ita? Ashe da duk sauran ma na so su kenan. Lemme tell you something sajida,in kana son mace you dont have a reason to love her,ko da bata baka sex wannan soyayyar a zuciya take kaman baki banbance so da sha’awa,just spending time with the person you love ya wadatar a zuciyan masoyi ganin murmushin wanda kake so tamkar cin nasara a yaki ne.” Limshe idanu yayi yana picturing fuskan maimunatu with a wide smile shima murmushin ya saki me sauti tsakin sajida ne ya dawo dashi daga duniyar da ya fad’a1
“Kai dai wallahi marwan dan wulakanci ne yaushe ka dawo love guru ban sani ba last i checked you dont want to be in love duk macen da ta fada soyayyarka ita ta sani.”
Murmushi yayi yace “saj ba zaki gane ba.”1
“Mmm toh who is the lucky babe?” Manyan idanunsa ya watsa mata wanda sai da ya saka heart beats dinta skipping har ta mutu idanun marwan will have an effect on her. Fuskarsa dauke da murmushi yace “sajida ki tafi ki barni inyi aiki gwara keh bamali ya tara muku.” Wani harara ta watsa mishi kaman idanun zasu fado can kuma cikin karamin murya tace “marwan ina da health problem.” Ba tare da ya dubeta ba yana me zama a kan kujerarsa yace “kije hospital.”
“Marwan i am serious ka saurareni mana.” Yana shirin bude baki yace mata shima be ia seriouse ai nan ba hospital bane yaga idanunta cine taf da hawaye.1
STORY CONTINUES BELOW

Matsar da system dinsa yayi yace “Saj meye damuwan?”
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsunta sosai marwan yasha mamakin nutsuwarta lokaci guda “Sajida ke nake sauraro aiki ne a gabana masu yawa.” Dago kanta tayi tana kallonsa a hankali ta furta “lump gare ni a nono.” Hawayen da ke cikin idonta ne suka zubo.2
Waro idanu marwan yayi sai kuma ya seta kanshi ya fara kwantar mata da hankali,tambayoyi ya fara yi mata tana amsa mishi sai da ya gamsu da bayananta sannan yayi rubutu a jikin paper ya janyo drawer dinsa ya dauki wani card ya bata yace”wannan card din Dr Zakiyya ne ki kirata zanyi mata magana ki bata wannan paper din zaku karasa da ita.”
Murmushi ta mishi tare da ansa paper din tace “nagode marwan wani sa’in kana da kirki.” Dan tabe baki yayi yace “zaki ji dashi.” Mikewa tayi taje mini palo din ta dauki jakanta da karamin gyalenta ta yane kanta duk yana kallonta.
“Amm saj ji..” Ya furta daidai lokacin da take shirin fita dan juyowa tayi tana mishi tambaya da ido.
“Wallahi a dai dinga sanin an girma,sannan a mika min gaisuwana wajen sanata.” Harara ta balla mishi ta fita ta barshi yana dariya.
3
Wasa wasa maimunatu har da shan drip duk satin nan gaba daya bata je aiki ba kuma ta kashe wayarta babu wanda yake samunta in hankalin marwan yayi dubu toh ya tashi gashi baya son tambayan Mubeena number dinta bai kara shiga tashin hankali ba sai da mubeenan ta rude masa itama tana son sanin halin da maimunatu take ciki tsoronsa daya kar dai ace ta bar aiki kenan lokaci daya ya zabge baka ganin komi sai hanci da idanu.2
Taheer ma ya shiga tashin hankali ba karamin dauriya yayi ba wajen kin zuwa ga mubeena yaji ko ita suna waya.1
Kwananta hudu sannan ta watsake ranan friday ganin short day ne yasa tace bari taje aiki dan ta san tayi laifi shi yasa bata damu ta kunna wayarta ta kirasu ba shigan atamfa tayi ta kashe dauri sannan ta dauko bakin glasses dinta ta saka (kun san mutuniyar da glasses)1


Bata dau mota ba ta kira urba tana zaune cikin bayan cab din ta kunna wayarta messages ne suka dinga shigowa rututu ta san dama za ayi haka messages din daga Tahir,mubeena,Khalid ne sai na cousin dinta daya da tace zata zo abuja biki.
Babu wanda ta replying ma,haka kawai taji ina ma zata ga message din marwan tsaki tayi ta riga ta sani sam bata ran marwan dan in da marwan da ta sani ne wallahi ba kashe waya tayi ba sai yazo har gida ya fito da ita da wannan shegen son nuna ikon nasa tunawa tayi da ko mubeena bata san gidansu ba haka duk magiyar Taheer bata taba yarda ya ziyarceta ba.1
Khalid kam yazo so ba adadi amma bai samu ganinta ba. Mayar da kanta bayan seat din tayi tana tunanin kalar rayuwanta har tayi ciwon nan ta gama masu aiki ke kula da ita sai lokaci lokaci da dday yake lekowa ya dubata.1
Zuciyanta da kwakaalwanta fal tunani ta isa ma’aikatar ajiyar zuciya ta sauke tana addua,ita kanta bata san adduar me take yi ba cos deep down tana son taga marwan ta wani gefen kuma tana scolding kanta tare da kiran kanta mara zuciya.1
Tun daga recption ake tambayanta ko lafiya kwana biyu bata zo ba sai tace musu bata da lafiyane su kuma sai su gaisheta da jiki
Office dinta ta wuce direct ta ajiye jakanta da wayarta a table dinta sannan ta knocking kofar office din mubeena kafin ta murda handle din mubeenan ce kadai zaune kan table dinta ta dukufa sai aiki take yi dago manyan idanunta tayi ta sauke akan maimunatu da sauri ta mike tare da zagayowa ta rungumeta cike da murna can kuma ta saketa tare da tureta cikin masifa tace “haba! Maimunatu ina kika shiga kika kashe wayarki kin sani cikin tashin hankali last time da muka yi magana kince baki da lafiya sai kuma in jiki d’ip what happened?”1
“Ta saba da yin hakan ai,karki wani ji mamaki autah!” Aka ansa su daga bakin kofa ashe ya hango shigowarta. Kau da kanta gefe tayi ba tare da ta bashi amsa ba yayin da bugun zuciyarta ya karu fiye da zaton me karatu.1
Dan pouting bakinta mubeena tayi tace “uhm uhm wallahi bata saba da haka wannan karon ne kawai aka samu matsala and i am sure tana da dalili.”
Murmushi yayi tare da kama kumatunta a zuciyarsa yana fadin dalilin kenan ni.1
A fili kuma yace ba tare da ya kalleta ba”sai ta fadi dalilin”
Sam hankalin mubeena bai kawo mata komi ba ta juya ga maimunatu dake ta rarraba idanu tace “mems me ya faru ne?” Cikin inda inda tace “well,jikin..jik…fever din bai sauka ba sai da aka sa min drip.” Ta karasa maganan cikin saurin baki tare da dago hannunta da aka cire canular jiya da dare kafin mubeena ta rije hannun carab marwan ya rike yana kallo wani mugun kallo maimunatu ta watsa mishi amma bai ma san tana yi ba.1
Cikin dabara ta zare hannunta tana murzawa kara rungumota mubeena tayi tana ce mata sorry shi kam gogan hannunsa ya cusa a aljuhu yana kare musu kallo.1
A hankali ta zare jikinta daga na mubeena tace” bari in dan taba aiki.” Cikin kulawa Mubeenan tace “zaki iya? Ko kawai ki zauna a can muyi hira tunda yau da wuri za a tashi,girgiza kai tayi tace “bari dai in taba.” Daga haka ta fita dan gujewa azabar kallon marwan tana fita ta samu wayarta na ringing da sauri ta picking khalid ne.1
Ajiyar zuciya ya sauke yace “munah kin kusa kasheni,ki sakko ina kasan office dinku na bi gidanku ko yau zan sami ganinki aka ce kinzo office shine na kasa hakuri na biyo.”
Murmushi tayi tace “Toh gani nan zuwa.”1
Tana fita marwan na fitowa sai yayi tunanin ko ta shiga bathroom ne murmushi yayi dan ya san tarkon da ya dana mata in ma gudunshi take,shi yasa yace mubeena ta bata wadu files ta kawo mishi,saman sa ya haura ba tare da ya damu da fitowanta ba.1
Yana shiga office dinsa yaje ya tsaya a gaba glasses din bayan kujeransa yana tunanin yanda zasu kwashe da sauri ya karasa jikin glass din tare da dafawa yana kara matso da idanunsa dan ya tabbatar ita din ce kuwa dai dai lokacin khalid ya matso da fuskar sa kusa da nata.
1
Dan baya ta ja tana murmushi tare da rufe fuskarta da gyalenta tace “kai dai wallahi,kar ka tafi sai kayi latti.” Murmushi yayi yau ko ba komi ta sake dashi zuciyarsa fari kal yace “shikenan bari in tafi tunda korata ake.” Yana shirin bude mota call din mubeena ya shiga hannu ta daga mishi ta koma ciki da sauri ta san nemanta take.1
Kallon file din tayi ta kalli mubeena gaba daya ma ta kasa magana toh me ma zata ce mata? Ganin hakan yasa mubeena tace “ki tafi mana ni sam na rasa me yasa kike tsoron yayana.” Ajiyar zuciya ta sauke ta fice daga office din.
A hankali ta knocking kofar bayan ta gaishe da sakateriyarsa bai bata umarnin budewa ba sai ma karasawa da yayi ya bude mata da kansa tsab ta lura ransa a mugun bace yake ko kafin tayi magana ya mayar da kofan ya rufe tare da hadata da jikin bangon office din kafin ta san me ke shirin faruwa ya hade bakinsu waje daya a zazzafe yake kissing dinta ita kuma tana kiciniyar kwace kanta hannunshi yasa yana shafar cikinta hakan yasa tayi lakwas sai da ya tabbatar ya samu lagonta sannan ya cirr bakinsa a nata ya cigaba da kissing wiyanta tare da mayar da hannunsa kan boob dinta lumshe idanu tayi tana feeling touch dinsa kaman daga sama taji muryarsa “did any of them touch or kiss you like i do? Har shi wancan da ya tafi yanzun? Wani irin hankadeshi tayi tare da zubawa fuskansa kyakyawan mariKyakyawan mari ta watsa mishi tare da binshi da wani mugun kallo shima ranshi a b’ace yake kallonta tofa mishi yawun bakinta tayi tare da goge bakinta da bayan hannunta. Cikin mugun mamaki yake kallonta muryarta a dakushe tace “kana ce kowa dan iska ne irinka? Ko dan kayi amfani da damar da ka samu a shekarun baya ka lalata min rayuwa kana ce na cigaba da harkar da ka dora ni akai ne? Toh albishirin ka Allah ya kubutar dani daga mugun tarbiyar da ka d’ora ni kuma kayi kadan ka mayar dani ruwa marwan sannan one more thing mazan dake rayuwata ba fasik’ai bane irinka.”2
Daga haka tayi kokarin rab’awa ta gefensa ta wuce damkota yayi ya mayar da ita jikin bangon da karfi har sai da files din hannunta suka zube kokari yake su hada ido amma sam taki sai ma kiciniyar kwace jikinta da take yi.
Cikin muryan da ta san yana using in ranshi ya kai kololuwa wajen b’aci yace dan sosai maganganunta suka kona mishi rai duk da ya san rabi a kan gaskiyarta take”listen here maimunatu,ki san da wa kike magana bar ganin nonuwa sun kara cika kirjinki nine dai marwan da kika sani babu abinda ya canza na daga zafin raina sam ba zan dauki raini a wajenki ba,ke ko kunya ma baki ji kina kirawa kanki wai mazan da ke rayuwanki,maza nawa ya kamata su kasance a rayuwar diya mace da ya wuce namiji daya? And believe me ba Tahir ba,ba shi wannan da ya tafi ba,babu dan iskan da ya dace da rayuwarki a cikinsu in ba ni ba,ni ne first love dinki nine wanda jikinki ya fara sani and nine farin cikinki kaman yanda kece tawa,i fucking own you and you know damn well ki gayawa duk wani shege ya tattara tsumman rayuwarsa ya fita a sha’aninki tun ban dau mummunan mataki ba.” Ya fada cikin matsanacin tsawa.4
Sosai maimunatu ta tsorata amma ta dake wani irin yawu me kauri ta hadiye kafin ta kwace jikinta kasancewar ya sassauta rikon da yayi mata cikin kyafkyafta ido tace “wallahi ni ba mallakinka bace,in akwai wanda ya kamata ya fita a rayuwana toh kaine dan duk tare kazo ka sameni dasu and you dont get to choose who is in my life,you dont get to decide for me ka rabu dani da su…” Ta fada muryarta na rawa.1
Dan sassauta murya yayi yace “eh nazo na same su amma i was here before them ni kike so ni kika fara so…”
Cikin sauri ta tari numfashinsa tace “Ba kaine first love dina ba,ba kai na fara so ba,khalid was here before you,shi na fara so kafin kai i am not even sure if what we had was love not lust.”1
Cikin daga murya yace “karya kike ni kika fara so dont even try to play games with me,yes we have chemestry but what we had and still have is love not lust.” Ya karasa maganan cikin sanyin murya.1
Dan tsaki taja tana so ta samu hanya ta wuce amma yayi baka baka sai ma mata katanga da yayi da hannayensa ta hanyan dafa bangon matso da bakinsa yayi dai dai kunnenta tana jin dumin numfashinsa nan da nan tsigar jikinta ya fara tashi cikin wani kafirin murya yace “miemie ina sonki pls ki ya hakuri koma fushin me kike yi ki ajiye shi na tuba.” Ba tare da ta san shirinsa ba sai jin lips dinsa tayi a gefen wuyanta idanunta da kashin kansu suke son lumshewa saboda kasalan da ya sakar mata.2
Wani kuzari ta tattaro ta hankadasa tana binsa da wani irin kallo tace wai kai me yasa babu Allah a ranka ne?” Waro idanu yayi shi fa ya kasa daina mamakin wannan sabuwar miemie din tasa “miemie nine babu Allah a raina?” Ba tare da wani shakku ba tace “yes! Cos in akwai Allah a ranka zaka ji kunyansa wajen dakumata tunda ai ba kudina ka biya da zaka dinga kai hannunka jikina anyhow.”2
Murmushi yayi tare da harde hannunsa a kirjinsa yace “kina so in kai kudina gidanku ne?” Wani uban harara ta watsa mishi tace “ko maza sun kare!”
Maimakon furucinta ya bata mishi rai sai ya saki yar dariya yace “ho ni marwan! Ko meye laifina a wajen wannan yarinyan sai Allah.”
Tabe baki tayi tana jinjina rainin wayon marwan2
“Miemie da gaske meye laifina?” Ya tambayeta in a serious tune.
Idonta ne ya kawo kwallah amma bata ce komi ba sai ma fizgan kofan da tayi ta fita a hanyan hawaye ne kawai ke sintiri a idonta marwan ya mugun raina mata hankali wato ma menene laifinsa a wajenta tunda shi bai ga ya yi mata laifi ba itama ba zata taba ce mishi ga laifinsa ba dan da alama dariya zai yi mata tunda ta bashi matsayin da shi bai bata rabinsa ba.2
A haka ta gama aikinta na ranan ba tare da ta kara sashi a ido ba amma maimakon hankalinta ya kwanta ma sai gaba daya ta rasa nutauwarta she wished a reception yake zaune da tayi ta zirga zirga ko dan ta rinka ganin shi ita da kanta tayi Allah wadai da irin zuciyarta.3
Marwan kam bayan fitan maimunatu shiru yayi yana tunanin me yayiwa maimunatu da zafi haka take nuna mishi wannan kiyayyan shi ya sani ya tafi ya bar maimunatu cikin tsananin sonshi da kewarsa amma yazo ya tarar da akasin haka yanzu in tana fushi da tafiyarsa ne kamata yayi ta tsaya ta ji uzurinsa kafin ta yanke masa hukunci. Toh ko da gaske ta daina sonshin ne? No no no yana da tabbacin har yanzu tana sonshi ko da kuwa ba kaman da ba, “na shiga uku who is this fucking of a khalid?” Ya fada a fili cikin tashin hankali a kasan office dinsa ya zauna tare dafe kansa ya rasa tunanin da zai yi he is ready to fight the world for his miemie……….Ya dad’e a zaune yana tunanin ta inda zai fara shawo kan maimunatu ya kasa karshe tashi yayi ya zari makullan motar sa ya fita bai wuce ko ina ba sai main house.1
A zaune ya sami mami a palo daya daga cikin ma’aikatan gidan tana jera mata fruits a kan darduma a hankali ya cire jacket dinsa ya ajiye kan hannun kujeran kafin yaje ya kwanta a kasa kan darduman tare da kwantar da kansa bisa kafar mami dake mike hannunta ta dora bisa kansa tana shafawa tace “Marwan sai ka karasa kafar kaji dadi ko?”2
Maimakon ya tura baki yayi mata shagwabar da ya saba sai taga ya lumshe ido kawai yayi ganin hakan da tayi ta san babu lafiya,shafa kansa ta cigaba da yi a hankali kuma tana karanta mishi addua.
Fahimatan da yayi na cewan addua take mishi ya saka shi kama “Allahuma ajirni fi musibatin wa akhlifni khairan minha.”2
A hankali yaji nutsuwa na ratsa zuciyarsa har wani bacci me dadi na dan fuzgarsa a hankali tace “maza marwan tashi kaje kayi wankan juma’a” bude idonsa yayi yana kallon fuskarta da ke dauke da kulawa murmushi ya sakar mata tare da cewa. “Thank you maminah” itama murmushin ta sakar masa tace “kul! Kar in kara jin kalmar godiya a bakinka,in uwa bata tsaya kan ya’yanta ba wa kake tunanin zai tsaya kansu.”1
Haka kawai ya sami kanshi da mayar da kanshi ya kwanta kan cinyarta a haka daddy ya fito ya samesu kallo daya zaka yi masa kanhango tsananin kamansa da yaransa musamman manyan idanunsa da yake dauke da su da dark skin dinsa.
Murmushi yayi yace “haba no wonder aka barni ina ta kiciniyar shiri ni kadai ashe dan gaban goshi na kusa.” Tashi yayi zaune yana murmushi yace “daddy ashe kana ciki? Barka da war haka.”1
“Ina ciki,likita,soja kuma dan kasuwa,anya na taba ganin had’amemme irinka ka kuwa marwan?” Tura baki yayi yace “daddy ai a cikin sojoji akwai likitoci ni kuma kasuwanci ba ra’ayina bane.”1
Daga kafad’u daddy yayi yace “oho dai ra’ayinka ko ba ra’ayinka ba babu wanda zai maka wahala,wai auta ma da kananan shekarunta ka bata gurbi me nauyi.”
Tab’e fuska yayi yace “toh daddy ya zanyi? Kannena are hard working.”
“Sosai kuwa dan in ba dan su ba da kamfanin tuni ta rushe.” Cewar daddy1
Sai lokacin mami dake kallon draman nasu tace “ah ah fa dear marwan na kokari shima yana shiga sabgogin company din sosai duk da abubuwan da ke kanshi ga aiki ga kasuwanci ga ginin asibiti haba ai ko dan nawa na kokari sosai.”1
Mikewa tsaye daddy yayi yana kara saba babbab rigarsa yace “ai ke dama baya laifi a wajenki ni na shiga cikin gari sai na dawo.”1
A dawo lafiya suka mishi ya sa kai ya fita mayar da kallonta kan marwan tayi tace “babana kai va zaka tashi kayi shirin masallaci ba? Har ya mike ya koma ya zauna tare da kallon wrist watch dinsa ya mayar da hankalinsa kan mami yace “mami ina da matsala.”
“Subhanallah me ya faru?” Numfashi ya sauke tare da tankwashe kafafunsa yace “mami ina yarinyan da nace miki ina so tun shekarun baya?” Cikin zumudi tace “eh eh na ganeta,ta gama karatun ne,ko me ya faru?”
Limshe idanunsa yayi yace “mami na ganta but taki saurarata.”1
Cike da confusion tace “ban gane ka ganta ba kuma taki sauraranta dama ka ta bata ne ko kuma wani laifi kayi mata?”
Yace tohm mami gashi nan dai fa amm dama dama a cyprus ne,mmm”
Waro idanuwa waje mami tayi tace “ban gane dama dama a cyprus ba,marwan ba dai ka b’ata musu yarinyan mutane bane an turata karatu na san kadan daga aikinka.”1
Kau da kai yayi gefe ransa na kuna ya san abinda ta fada gaskiya ne amma ai ya canza hali “mami ban b’ata ta ba fa ni but i almost did shine shine…” Ya sunkuyar da kai1
STORY CONTINUES BELOW

“Shine yanzu taki sauraranka saboda tana maka kallon dan iska ko kuwa?”
Mami ta karasa mishi maganar
Watsa hannunsa yayi yace “mami i dunno ni gaba daya ban san meye take tunani ba,na kasa gane menene takamenmen laifina ba,yeah tana ce min dan iska but mami ni ban taba yin komi da ita ba and i am very sure,so sure that tana sona.”1
Harararsa tayi tace “toh in tana sonka me ya hanata kulaka?”
“Mami ban sani ba wallahi mami ni kuma ita nake so i want to settle down ni aure nake so.” Ya karasa maganan cikin kunkuni1
“Wow! Marwan yau kaine me kiran son aure? Lallai kam dole in ga wannan yarinyan a ina take?” Tura baki yayi yace “i still dont know her background amma a moh enterprises take serving.”1
“Au ko dai ita ce sakateriyar auta da kullum sai ta bani labarinta?”
Murmushi yayi ya gyada kai
“Mmm kenan yau ita ta taboka?” Shiru yayi haka ya bata ansan tambahanta tace ” Yanzu dai ina ganin ka dan bata lokaci mu gani, ni kuma zan sami daddy da maganan kayi kokari ka san background dinta ko da sunan da aka san mahaifinta dashi ko gidansu ina ganin a fara samun mahaifinta daga baya sai ka shawo kanta ina ga haka zai fi sauki.”1
Murmushi yayi mai fadi yace “thanks mami amma bana son su auta su sani tukun na,bayan sallahn juma’a zan wuce ibadan”1
Tace “ha’a ina ce sai sunday zaka wuce.” Dan rusunar da kai yayi yace “mami in ban tafi yau ba i cant stay away fron her.” Dariya mami tayi tace “da kyau! Ni kam har yarinyan nan ta shige zuciyata yanda tayi maka kamun kazan kukun nan dan kam duk macen da ta aureka in baka tsananin sonta nata ya kare, ni kam me sunan surukar tawa?”1
Murmushi yayi cikin nishadi yace “mami sunanta miemie i mean maimunatu” mashaaAllah
Mutmushi yayi tare da mikewa peck ya manna mata a goshi yace “mami kiyi min addua ki sa min albarka.”1
Tace “marwan kullum cikin yi muku addua nake Allah ya dafa muku a dukkanin lamuranku yayi maka albarka.” A hankali ya amsa ya kama hanya part dinsa na gidan yana murmushi,mami kenan uwa ta gari haihuwarsa kawai mahaifiyarsa tayi ko rikesa bata yi ba Allah ya dauki ranta mami ta reneshi kaman ita tayi nakudansa a kan maimunatu ne kawai ya san cewa matar uba nayi wa diyan mijinta mugunta sosai yayi mamaki lokacin da ya san momy bata san maimunatu he wonder all this years ya take coping da kiyayyar matar ubanta.
1
Ranan mubeena ita ta mayar da maimunatu gida wai akan sai ta san gidansu saboda gaba ita dai maimunatu yake kawai take mata dan abinda yake damunta shi yake damunta.
1
Iya shegen Marwan ya dameta ta kasa daina mamakin takadarancinsa abin haushi babu abinda ya ya ragu akan abinda take ji akanshi ta sani tana denying ne kawai but deep down marwan na kwance shame shame a dandariyar zuciyarta.1
Daren ranan tana zaune a gaban system dinta tana rage wasu ayyuka momy ta banko kofan dakinta har sai da ta firgita harara ta watsawa maimunatu tace “sai kizo inji yaya sufyan .” Ta ja kofar da karfi nimfashi maimunatu ta sauke sannan ta ta shi taje ga closet dinta ta cire short rigan dake jikin ta sa doguwar riga ta material sannan ta saka mayafi ta fita tun daga sama ta ji shi da daddy suna hira a hankali ta sakko ta dan rakube a gefen kujera tana gaishesu wani kallo uncle sufyan yake yi mata yana amsa gaisuwar ita kam duk tsoro ya gama cika kar uncle sufyan ya saka ta a uku.2
“Abdul bamu wuri da maimunah” uncle sufyan ya fadawa daddy maimuna a ranta fadi take lallai ma uncle din nan wato “Abdul bamu wuri a haka take son yin surkunta da daddy da wannan shakuwar tasu tab.1
“Madam da kanta” uncle sufyan ya katse mata tunani sai lokacin ta farga daddy ya fita”tunanin me kike yi bayan gani nan a gabanki.” Dan murmushi tayi tace “uncle kenan!”
“Mmhmm zaki fara uncle kenan din naki na fama ko? Ni duk ba wannan ba Daddynki yace min yace ki fitar da mijin aure” shiru tayi tana sauraronsa lallai ma1
“Maimunah in bayyanawa daddynki kaina?” Zaro idanu tayi tace “ah ah dan Allah uncle ka yi hakuri,pls kar ka gayawa daddy wani magana makamancin haka uncle i cant look at you that way ba zan iya ba.” Fuska a marairaice yace “sabida me munari wallahi ina sonki and i can take care of you fiye da yanda dan saurayi zai kula dake so pls give me a chance.”2
Kuka ta fashe mishi dashi ganin haka ya sa yayi shiru yana sauraron sautin kukanta da yake yi mishi zafi bai san wani irin jarabawa Allah ya dora masa na son yar cikinsa ba he wish zai iya kyaleta kaman yanda ya lura hakan ta fi so.
A hankali yace “Tashi kije zan kiraki” kaman wacce take kan kaya ta mike tsam tare da yi mishi sai da safe “
1
“Mama maganan gaskiya baku kyauta ba haba dan Allah sam ba ayiwa sister adalci ba ace jininta an wofintar da ita ni wallahi all this while ban san cewa maimunatu bata zumunci da mu ba.”1
Wata yar gajeruwar mata ce a zaune tana sauraron diyarta a hankali tace “zauna khadija zauna,ya kike so muyi mahaifinta ai shi ya kamata ya dinga kawota wajenmu amma tunda bai yi haka ba itama da ta girma bata shigo cikinmu ba ya zamuyi? Wallahi Allah ya sani sosai abin nan ke yi min ciwo toh amma me zance?”1
Tsaki wacce aka kira khadija tayi tana girgiza kafa tace toh ni zanje har gidan yaya abdullahin in ga halin da take ciki shi yasa ni fa ba zan bar sadiq a hannun babansa ba fa.”1
Mama tace “haba khadija me yasa kika fiye fitina ne ai kya bari ki gama idda tukun na ko? Daga dirarki kasar nan sai da kowa ya san kin dawo tsabar masifarki ayi mutum in bai yi jaraba ba baya jin dadi? Haba!”
Juyawa khadijan tayi tana kunkuni….
2
_wai kam me yake faruwa ne a wannan page din?_
1