MAKAUNIYAR SOYAYYAH COMPLETE

 MAKAUNIYAR SOYAYYAH COMPLETE

Yau a garin Kaduna an tashi da matsanancin zafi kasancewar zafi ya fara shigo wa wanda yake hana mutum sakat, dawo wa ta daga makaranta kenan na cire uniform d’ina na fada toilet d'in dake jingine a d'aki na, ko side d'in Ummu ban shiga ba saboda zafin da ke son sa min wani ciwon, ko minti 5 ban d'auka ba na watsa ruwan sanyi kana na fito na zira 'yar t-shirt da wani simple skirt na nufi d'akin Ummu wanda na same ta zaune a 3 sitter rike da hisnul muslim a hannun ta tana nazari.


Sallamar da nayi ne yasa ta katse karatun da take yi ta d'ago ta na kallo na tare da murmushi a fuskar ta, jikin ta naje na kwanta kasancewa ta mai son jiki duk da yaya Aminu ba ya so amma Ummu cewa take yi a k’yaleni ni ce auta kuma  d’iya mace a gaban ta.

"Ummu sannu da gida"

"Yawwa Fatima an dawo? ya lesson d’in"

Cikin shagwa ‘ba na ce "gaskiya Ummu na gaji da wannan lesson d'in waec da neco d’in nan, mutum ya dawo a gajiye gashi ba a tashi da wuri ga zafi yazo, a class mutum yaji kamar ya cire kayan jikin shi saboda zafi yanzu fa daga dawo wa ta sai da na watsa ruwa amma ji nake kamar ana kara min wani zafin, gaskiya ki yi ma yaya Aminu magana saboda shine d’an sa ido shi da wannan abokin nashi yaya Faruk, zan daina zuwa lesson d’in nan, yanzu ban da na school da nake attending kuma an kara sa ni a wani extra school ran weekend sai kace wata mango park"

Dariya Ummu tasa tace "kai auta ina laifin wanda ya damu da ilimin ka ai in ba a gode mai ba bai ci kuma a kushe shi ba, kiyi hakuri ki k'arasa lesson din tunda kun kusa zana waec da neco d’in sai ki huta gaba d’aya tun da kinyi jamb kafin admission ya fito a fara zuwa jami’a

Cikin jin dad'i na rungume Ummu ina murna ina cewa "wa ya ganni a jami’a?

dariya Ummu tayi tace "auta kenan"

sallamar yaya Khaleel ce ya katse mana hirar da muke yi

Amsawa muka yi kana ya saki murmushi yace "auta me ake tattaunawa ne don na ga hirar ta muku dadi"

Hararar wasa na mai tare da murgud’a baki nace "ba sai kaji ba kuma ni kadaina ce min auta saboda na girma kuma in k'awaye na suka ji dariya zasu min"

Dariya yayi yace "to shikenan sister na daina tun da kin girma"

Kallon Ummu yayi yace "yaya Faruk ya dawo yace in gaishe ki kafiin ya zo"

Yalwata murmushin ta tayi tace "ikon Allah yaushe ya dawo"

Amsa mata yayi da cewa "jiya ya sauka kin san ya kwana biyu bai zo Kaduna ba ya ‘boye a Abuja, kin san aikin sojoji sai a hankali ba sa samun hutu, nima na biya gidan ne in gaida momi mu ka hadu"

Ummu juyowa tayi tana kallo na wadda tun san da naji an ambaci yaya Faruk nayi shiru kamar ba na d’akin tace "kin ji yayan ku ya dawo ki tashi ki je ki shirya mai abinci saboda nasan anan zai ci na dare"
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *