MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 13 Na Samira Harouna

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 13

Na Samira Harouna


👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *49*

Cikin b’acin rai da fitar hayyaci tace “Ke Aisha wacece ke da zaki raina min yan uwa? Akan wane dalili ne zaki shammaci halittarsu? Saboda ina auren ubanki ne?”

Turata tayi da k’arfi har saida kanta ya bugi bango ta d’ora da fad’in “Zaki takani yanda kike so a gidan nan na k’yaleki, amma idan kika ce zaki tab’a iyayena ko yan uwana wallahi kutumar ubanki zan ci a gidan nan saidai uban ki ya sakeni.”

Juyawa tayi har zata nufi wajensu Yaseen sai kuma ta juyo ta kalleta tace “Ba kiyi kama da yar Abdul ba, sam halayenki basu dace dana wacce ta fito a tsatson Abdul da Hafsat ba, kaiconki wallahi, kuma fa duk wannan abun da kike yi kina yi ne saboda na auri Abdul ko?”

Yatsina fuska tayi tace “Mun riga da mun zama d’aya Aisha, zan fad’a miki wani abu kuma wanda na tabbatar cikin biyu za’ayi d’aya tunda ke ma aure zakiyi, ko dai mu haihu tare da ke, ko kuma na rigaki haihuwa dan tsohonki ya jima da tura sak’onshi kuma na karb’e da hannu bibbiyu, mu zuba ni da ke a gidan nan tunda kin kasa fahimtar a yanzu ni ma d’in uwarki ce tunda na gauraya da ubanki .”

Sama da k’asa ta bi ta da harara ta wuce zuwa wajen su Yaseen da sukayi tsuru suna kallonta, saida suka fita a gidan ta juya ta koma ciki ko kallonsu ba tayi ba, Aisha kam ta cika kamar zata fashe ta kawo wuya, Heezam kam girgiza kai yayi yace “Kin ga irinta ai, gobe ma ki k’ara.”

Aswan ma murmushi yayi yace “Gaskiya ta fad’a miki, sam bakiyi kama da yar gidan nan ba.”

Odar da sukaji tasa su fita da sauri amma ban da Aisha da take tafiya kamar wacce k’wai ya fashe ma a ciki, kalaman Mimi sun tsaya mata sosai a zuciya, musamman yanda take kiran sunan mahaifinta ba girmamawa Abdul gatsau, saida suka shiga mota sai kawai ta fashe da kuka kamar wacce aka k’wak’ulewa ido. Har suka isa islamiya tana kuka bata daina ba, a aji ma ba abinda take sai shashek’a, shiyasa ma ana tashi daga islamiyar ko da dreba ya d’aukesu bai tsaya ko ina ba gida ya diresu. 

*Tun* fitarsu dama sunyi waya ita da sheikh suka sha hirarsu ta soyayya, Hafsat ma a can ta wuni sai yamma lik’is ta dawo daf da lokacin tashinsu, tunda sheikh ya dawo da ita kuma bai fita ba yana gida, hakan yasa suna shigowa falon da sallama sun samesu dukansu a falon.

Sheikh na tsaye zai shuge b’angarenshi ya dakata saboda jin shigowarsu, Mimi ta fito daga madafa rik’e da kofi a hannunta ta kawowa Hafsat shayin da tayi na goruba, Hafsat d’in kuma na zaune kan kujera.

Kusan a tare suka amsa sallamar yaran duk suna kallonsu, da sauri Hafsat ta mik’e gabanta na fad’uwa saboda ganin fuskar Aisha, idonta sun k’ank’ance sun kumbura abu ga jar fata, fuskarta ma duk tayi wata kala tsabar kuka sai shatin yatsun daya zauna a kuncinta, dan marin da Mimi ta mata a bazata ne ya zo kuma da mugun k’arfi, da hanzari ta tarbeta tana fad’in “Aisha lafiya? Me ya sameki?”

Sake sinne kai tayi tana ci gaba da shashek’ar kuka, hankali tashe ta kalli su Heezam tace “Kai me ya sameta? Fad’a tayi ne? Ko wani laifin tayi da aka daketa a makaranta?”

Aswan ne ya turo baki ya girgiza kai alamar a’a, sai Heezam daya d’aga kafad’a shi ma alamar uhum! Muryar sheikh ce ta dakesu a bayansu yace “Munzeer yaro na.”

Cikin d’aga sauti Munzeer yace “Na’am Abie.” Ya fad’a yana nufa inda yake tsaye, kusanshi ya tsaya ya shafa kanshi yace “Shi ne bayan bana nan tayi fad’a ko?”

Da sauri Munzeer yace “A’a Abie, aunty Aisha ce ta yi wa aunty Mimi rashin kunya, shi ne ta mareta a fuska kuma ta zageta.”

Tsuru tsuru duk suka zubawa Mimi ido da ita ma ta kafe Munzeer da ido, amma data ga kallon da suke mata sai kawai ta d’auke kan ta tare da aje kofin shayin hannunta akan k’aramin table d’in ta dafe k’ugu alamar tana jiran a yi duk wacce za’ayi.

Hafsat ma d’auke kanta tayi daga Mimi ta kama hannun Aisha da k’arfi suka nufi d’akinta cikin hushi, ganin haka sai sheikh ma ya bi bayanta dan gaskiya baya son b’acin ran Hafsat musamman ma da ita d’in macece da bata cika saurin nuna b’acin ranta ba, Mimi na kallo suka shige d’akin tana tsaye zuciyarta na tafasa tana jin kamar bak’uwa ce ita a gidan nan, kamar bata da wani galihu ko mutumci. 

Had’e hawayenta tayi tare da wani abu daya tsaya mata a wuya ita ma t shige d’akinta, saidai zaune tayi a kujerar falo zama irin na jiranka kawai na ke ka zo a yi ta ta k’are, ka zo ayi duk wacce za’ayi amma ba zan d’auka ba.

*A* d’aki kuma yana shiga Aisha na zaune bakin gado Hafsat na tsaye a kan ta tana d’an tab’a fuskar ta ta, da sauri ta juya ta kalleshi cikin hushi da b’acin rai tace “Akan me zata marar min yarinya? Ni ko kai akwai wanda ya tab’a dukansu ne bare kuma mari a fuska mai daraja, fuskar da ubangijinmu kad’ai muke turmusata a k’asa dan bauta masa, me ta mata da zata mareta haka har hannunta ya kwanta a fuskar yarinya?”

D’auke idonshi yayi a fuskar Hafsat d’in ya kalli Aisha yace “Me kika mata?”

A tsorace ta kalleshi cikin shakakkiyar murya tace “Abie ban mata komai ba, kawai daga zata raki k’annanta da suka zo, daga sun wuce nayi murmushi shi ne kawai ta mareni, har zagina ta dinga yi tana ambatar sunanka da sunan Amie tana fad’in wai ita ma matarka ce kuma zata…”

A tsawace yace “Shiru!”

Shiru tayi tana kallonshi tana sauke ajiyar zuciya, da mamaki Hafsat ta kalleshi tace “Tsawa ma kake mata? To wallahi ba zan d’auki wannan wulak’ancin ba, nayi hak’uri akan abubuwa da dama sannan na shanye b’acin rai bila-adadin, amma ba zan tab’a d’aukar cin zarafin ‘ya’yana ba.”

Kusa da shi ta matsa tana kallon idonshi tace “Ka fad’awa matarka karta sake sauke gigin haukarta akan yarana, inba haka ba wallahi da kaina zan d’auki mataki.”

Tana fad’a ita ma ta shige ban d’akinta dan samo ruwan d’umin da zata gasa mata fuskarta data kumbura.

Kallon Aisha yayi ya girgiza kai yace “Allah ya kyauta.”

Fita yayi a d’akin shi ma ya nufi d’akin Mimi, tana ganin ta mik’e dan cike take da bala’i ita ma, saida ya tsaya gabanta cikin halin ko in kula yace “Me ya had’aki da Aisha? Shin baki san ‘yarki bace ita da zaki zauna d’aukarwa kanki raini a wurinta.”

A gadarance ta yatsina fuska tace “Sanin haka yasa ni gaggauwar d’aukar matakin dakatar da rainin da take son d’ora min saboda na tuna mata ni ma uwarta ce.”

K’ank’ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki yace “Shiyasa kika d’aga hannu kika mareta?”

Rumgume hannaye tayi a k’irji tace “E, saboda ta raina min yan uwa, ni kuma ba kowane raini nake d’auka ba.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace “Na ji to kiyi hak’uri, Aisha ba zata sake miki rashin kunya ba na miki wannan alk’awarin.”

Shiru tayi tana wani kumbura baki ba tace komai ba, matsawa yayi kusanta ya rumgumota jikinshi yace “To saki fuskar mana, ko sai na had’aki da aljanuna?”

Da sauri ta saki hannayenta daga rumgumesu da tayi a k’irjinta tana dariya tace “A’a Abdul karka kirasu.”

Dariya yayi shi ma ya rad’a mata a kunne “Ko ke fa, bana so irin wannan hatsaniyar na d’aga min hankali a gidan nan, kamata yayi ki nuna musu ke ma fa gyatumarsu ce.”

Dariya ta k’yalk’yale da ita ta d’aga k’afafunta sosai ta rad’a masa a kunne cewa “Shiyasa nake so na kama girmana, dan ni d’in ba matar yaro bace.”

Dariya yayi ya bata hannu alamar su bige yana fad’in “Gaskiya ne matar old man.”

Farin cikonsu suka ci gaba da yi kamar babu abinda ya so faruwa yanzun. Saidai a daren bayan fitar sheikh da su Heezam zuwa masallaci, Hafsat da Aisha basu fito cin abinci ba, Mimi kuma bata damu ba hasalima ita ma tana b’angarenta, sai kusan 10:54 na dare suka dawo gidan, da kan ta ta zubawa su Aswan abinci suka ci sannan ta d’iba ta kai wa sheikh falonta shi ma ya ci.

Saida kowa yayi bacci a gidan baka jin komai sai k’arar panka da ac, a lokacin sheikh ya mik’e ya nufi d’akin Aisha, cikin nutsuwa ba tare da tunanin komai ba ya bud’a k’ofar d’akin, ganinta kwance akan gadon tana bacci a nutse ba k’aramar salama ya sama mishi a zuciya ba, dan sosai yake tsoron zamanin nan da mutanen cikinshi, k’arasawa yayi gaban gadonta ya tsaya ya daddab’ata, cikin magagi ta bud’a ido ganinshi yasa ta yin zunbur ta tashi zaune tace Abie?”

Yanda ya tsaya gabanta k’ik’am yasa ta sauka daga kan gadon tana lalubar hijabinta kan gadon, sakawa tayi ta b’oye rigar baccinta tana zaunawa k’asa. 

Zaune yayi bakin gadon ya had’e hannayenshi yana kallonta, saida ya gama mata kallon tas kafin ya d’aga hannunshi ya kwad’a mata mari, a gigice a rikice ta dafe kunci tana sakin k’ara.

Kallonshi tayi tana sako hawaye inda shi kuma ya nunata da yatsa cikin taushin murya yace “Wannan marin dana miki tun ranar da kika ma Mimi rashin kunya da safe ya dace na miki shi, ya kamata ki sani ita ma uwarki tunda ni ke aurenta, darajar aure ya siya mata darajar da zaki kalleta kamar uwa, addininmu ya koya mana yanda zamu mutumta d’an adam ko baka san shi ba bare wanda kake da alak’a dashi.”

Kama kunnenta yayi a cikin hijabin cikin sigar fad’a yace “Aisha har na zauna na nuna ga yanda za’ayi saboda gudun matsala amma ke ki nuna ba haka, da kika ma yan uwanta fitsara me kike so ki nuna musu kenan? Ke *tantiriyar gidana ce*? Haka kawai zaki tarwatsa min farin ciki da zaman lafiyar gida, tunda kike kik tab’a ganin b’acin ran mahaifiyarki a zahiri? Ko kin tab’a ganin ta kalli idona ta fad’a min abinda ke ranta kai tsaye? Sai yau kuma duk a dalilinki.”

Jinjina kai yayi sanda take neman tashi daga zaunen tana rik’e kunnenta tana fad’in “Abie zafi zafi, kayi hak’uri na tuba wallahi.”

Mik’ewa yayi ya sake nunata da yatsa yace “D’aurin aurenki ba fashi Aisha ranar juma’a, ko ki shirya ma hakan ko karki shirya duk d’aya, amma ki sani kin fara sani tunanin ko dai kin san me aure yake nufi shiyasa kike kishi da wata wacce kike ganin ita ma ta rab’i jikin ubanki, to koma a ya ya dai kika d’auka ki sani hakan ne.”

Yana fad’a ya wuce ya barta nan tana wani kukan tare da gyara zamanta a k’asan ta had’a kai da gwiwa.

Daren yau ma sheikh ya so ratsa gonar Mimi amma ta buga kai k’asa tace bata warke ba, dole ya hak’ura ya d’anyi wasa da ita kamar dai jiya sannan yayi wanka ya shiga karatun Qur’ani.

*Da* safe ma haka yara suka shirya suka fito, saidai Aisha kai tsaye ta wuce farfajiya sai su Aswan ne suka tsaya suka karya kumallo, suna gamawa suka fita Mimi na musu a dawo lafiya, saida suka fita ta nufi d’akin Hafsat da sallama a bakinta, zaune ta sameta bakin gado da wayarta a hannu, k’asan mak’oshi ta amsa sallamarta, bata damu ba haka ta k’araso tsakiyar d’akin tace “Aunty Hafsat abincinki na ce ko na kawo miki nan? Na ga baki fito ba yau.”

Yatsina fuska Hafsat tayi tace “A’a ki barshi ma na k’oshi.”

D’an satar kallonta tayi sai kawai ta jinjina kai tana murmushi tace “Shikenan, na barki lafiya.”

Fita tayi a d’akin tana jinjina kai a ranta tana fad’in “Ku kaini bango kuka aiki da cikawa.”

Fita tayi ta kai wa sheikh na shi abinci yana gama ci sukayi sallama ya fita. Haka har rana ta dora girki ta gama bata ga Hafsat ba sai zuwan yaran daga makranta ta dinga jin hayaniyarsu a d’akinta, tana gama aikinta ita dai ta shige d’akinta uta ma da abincin dan tayi niyya bama zata fito ba sai yamma in zata d’ora girki.

*Dare* ma haka suka kasance kasancewar sheikh bai shigo da wuri ba Mimi ta nemi su ci abinci, kowa ya zo amma ban da Aisha da Hafsat, saida ta gama zubawa su Heezam ta kallesu tace “Ina zuwa, bari na kira aunty.”

Jinjina mata kai sukayi alamar to, tana zuwa ta fara k’wznk’wasa k’ofar tana sallama, jin ta amsa yasa ta turawa a hankali ta shiga, da ladabi tace “Aunty Hafsat ina kwana?”

“Lafiya lau.” Ta amsa ba yabo ba fallasa, sharewa Mimi tayi tace “Abinci na ce ko zaki ci?”

Yatsina fuska tayi tace “Um um! A ci lafiya.”

Ita ma yatsina fuskar tayi ta juya dan fita, k’wafa Hafsat d’in tayi ta jin haushin takurawar Mimin, juyowa Mimi tayi cike da shak’iyanci tace “Magana kike?”

A gatsala ita ma tace “Kika ji nayi?”

D’aga gira tayi tace “Ok, Allah ya kyauta.”

Juyawa tayi amma dake Hafsat dama can fin k’arfin zuciyarta ne takeyi sai kawai tace “Ke! Rashin kunya zaki min?”

Juyowa Mimi tayi cike da rashin tsoro tace “Rashin kunya kuma? Kika ga alama zan miki?”

Sai kuma ta gyata tsayuwarta tace “Wai tsaya, ko dai haushina kike ji saboda na daki ‘yata? To ai ke ma na ga kamar uwa kike gareni kina iya rama mata.”

Mik’ewa tayi tsaye ta nunata da yatsa tace “K’arya kike wallahi, Aisha ba ‘yar ki bace, da ‘yarki ce ai da baki mareta a fuska ba, saboda baki san darajar haihuwa ba.”

Bushewa tayi da dariya tace “Haihuwa? To ai ban tab’a yinta bane shiyasa, amma kwana nawa ne ya rage ni ma na haifo nawa.”

Ta fad’a tana shafa mararta, girgiza kai Hafsat tayi tace “Dama da ganin idonki zakiyi fitsara, to ki ji da kyau karki k’ara dukar min yarinya dan bâ jakarki bace, da fari na so baki girma da darajar da zasu dinga kiranki da Amie, amma tunda baki da mutumci na fasa.”

 Gaba d’aya jikin Mimi ne yayi wani irin sanyi har tsakiyar ranta ta ringa jin wani iri, yau gata ta daki yarinyar data mata rashin kunya a kan gaskiyarta amma mahaifiyarta da take jin k’aunarta a zuciyarta tamkar ‘yar uwarta har tana jin ta samu ‘yar uwa ta kalleta ta wulak’antata a kan hakan, anya kuwa idan jininta ce koma ta ce idan ‘yar uwarta ce ko zane mata ‘ya ta yi zata kula? Zata d’aga kai ta kalleta? Duk da zamani ya cenza amma akwai na kirki har yanzu, akwai zumunci har yanzu.

Shin Hafsat bata ganin irin abinda ‘yarta ke yi ta katseta tunda wuri ko hakan na mata dadi? Shin Hafsat so take su fara zaman kishi da juna ko menene? A matsayinta na babba, babbar ma wace ta san ba haka kawai ta d’auko kanta ta kawo gidan mijinta ba a ganinta ya dace ta mata adalci.

Muryarta a sanyaye ta d’ago tana kallon Hafsat cikin ido tace “Allahn da ya baki aunty nima bai manta da ni ba, kuma ina rok’onsa idan ya tashi bani ya bani masu tarbiyar da ko da Abdul na da damar k’ara wani auren nan gaba su kirata da Amie, bare kuma ke, ke ina so yarana su kiraki da Mama, haka kawai na ga kin isa ki zama uwarsu dan a d’an zaman da na yi da mijinki sai nake ji da kuma ganin girma da darajar wani ma wanda ya rab’e shi bare matar daya hayayyafa da ita.”

Suna tsaka da muhawarar nan sheikh ya shigo, rashin sa’a kuma shi ne daidai Mimi ta kuma sakin wani murmushi tana girgiza kanta ta bud’i bakinta zata yiwa Hafsat wata maganar wacce Hafsat d’in kuwa gaba d’aya yanayi na b’acin rai ya saka har wata k’walla da b’acin rai sun nuna a tare da ita, uwa uba a yau idonnta ko kwali babu tsabar ta sakawa kanta damuwa bayan ba haka Hafsat  take ba, hakan ya saka hankalinsa tashe ya kuma nazartarsu kafin muryarsa kamar a d’an kausashe yace “Ryam, rashin kunya kika zo har d’aki kike yi wa matata ko me? Shin rashin kunya kike yi wa Hafsat? Kin kuwa san zan iya take komai na had’iye komai na danne komai amma banda cin zarafin uwar gidana? Kar na ji, kar na gani kar na ji kar na gani ko da wasa kar ki saki ki kuskura na kama ki da y iwa matata fitsara domin zaki yi mamakina Nana.”

Da mamaki take kallonsa,  yanayi na yarinta da d’anyen kai da b’acin rai ne ya sakata kuma kallonsa idanunta a bayyane tace “Wato ni ga matar kutse ko Abdul? Ni matar haye? Allah ya sa nima ce min aka yi jeki ga mijinki ba hauka nake a kanka ba bare daga kai har matarka ku wulak’antani!” 

Ta karashe tana mai danne muryarta dake rawa sakamakon b’acin rai da kukan dake son k’wace mata.

Ransa ne ya b’aci saboda jin ya ya zata ringa maida masa magana ta wani siga wai kenan shi ga sakarai shi da bata so ko? Ransa b’ace ya nufota yace “Me kike nufi da maganarki? Kenan kina so ki nuna ni d’in banza wofi ne a wurinki? Ya zaki nemi raina min matata na miki magana kuma ki nemi yi min fitsara.”

Cikin d’aga murya da kwaratsi Mimi ta ja baya tace “Ya isa! Ya isa haka.”

Kallonshi tayi tana sako hawayen da take rik’ewa tace “Kowa sai ya dinga kirana da fitsararriya ko marar mutumci, to na gaji kunji na fad’a muku, idan zaman gidan nan ba zai yiwu ba ka sallameni na tafiya ta mana, a’ah, wai ana dole ne?”

Da wani irin sauri ya kai hannu zai shak’o wuyanta ya gaura mata mari, sai kuma ya tsaya tare da dunk’ule hannunshi yana kallon fuskarta, girgiza kai yayi ya feso iska dan maganar sakin nan na tab’a mishi zuciya wallahi, kai dole ma ya zauna zama na musamman da ita ya nuna mata babu kyau abinda take fad’a, wani numfashi ya kuma saukewa yana ci gaba da kallonta yace “Ryam ban tab’a dukan mace ba, ba zan fara yau ba, amma ki sani ita mace da kika gani kamar abun tuk’i ce, idan har kika zamar min mummunan abun tuk’i har tuk’inki ya k’wace min zan zama sakarai kuma malalaci, a gaskiya ba zan bari haka ta faru ba.”

Ja baya yayi sosai ta yanda yake hangensu tsaye dukansu kuma yana kallon kowace yace “Na yardaina sonki ne daga lokacin da muka fara zama a matsayin ma’aurata, soyayyata ta farko gareni na farata, k’aunarki na gaba d’aya zuciyata saboda ke d’in nan ke ce b’angare na jikina, zubar hawayenki ba k’aramin d’aga min hankali yake ba, karki so kiji yanda zuciyata ke bugawa musamman dana shigo d’akin nan na fahimci ba kya cikin farin ciki, ina son ki, na fad’a miki haka bila-adadin, ki yarda, ki yarda da ina sonki kinji.”

Kamar shed’an nan da aka tofawa a’uziya haka duk suka zuba mishi ido sukayi tsuru, kowace tana d’aukar kalamai tana d’orasu a muhalli, saidai kuma wani b’angare na zuk’atansu na sa musu wasi-wasin da wa yake a ciki? Musamman Mimi da tafi raja’a ce wa da Hafsat yake, a wajen k’arshen ne kawai zata ce da ita yake dan yana yawan fad’in yana son ta kuma ta yarda. hafsat kam ta yarda tabbas da ita yake, tafi kokonton me yasa bai tsayar da kallonshi kan ta kawai ba.

Mimi kam juya baki tayi tace “Ni da ba’a so sai naje na nemi mai sona ai.”

Tsai yayi yana kallonta, “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.” Ya fad’a a zuciyarshi, wallahi wani irin gudu zuciyarshi tayi sanda ta anbaci ya sallameta, anya kuwa ba mutuwa zaiyi ba ko kuma dai yarinyar nan ce hawan jinin shi ba? Kasa maganar da yayi yasa ta kallonshi tace “Ba ma kada lokaci na ko? Shikenan ka tura min takardata a gidanmu.”

Juyawa tayi zata fita ya rik’o hannunta a mugun firgice, kallon juna sukayi tana kallon yanda yake sauke numfashi. Sautin kukan Hafsat daya ji ya dawo dashi daga shirin fad’in “Ryam kiyi hak’uri, karki tafi dan Allah.” 

Kallon Hafsat yayi cikin fizgo kalamai yace “Me ya had’u Manga? Ban san ki da rikici ba.”

Da sauri ta nuna Mimi tace “Ka tambayi dak’ikk’iyar yarinyar nan mana.”

Kallonta Mimi tayi da mamaki tace “Dak’ikk’iya kuma?”

Kallon sheikh tayi tana jiran ta ga me zaiyi amma sai wani kakkawar da kai yayi kamar mai kokarin b’oye kukanshi, fizge hannunta tayi ta kallesu da kyau tace “A tare na sameku dama, zan tafi na barku yanda na ganku, ni ma Allah zai had’ani da wanda zai iya kare kima da darajata, amma wannan ba gidan zama bane.”

Tana fad’a ta juya da sauri ta fita a d’akin wanda kowane tako ke sauka kan k’irjin sheikh, iya yanda mazaunanta ke juyawa cikin tafiyar b’acin rai yasa jinin jikinshi rage saurin gudu. Juyawa yayi ya kalli Hafsat dake ta sharar hawaye, wani iska ya feso dan gaskiya zuciyarshi na son ya bi *yarinyarshi*, amma kuma ga Sawwama na kukan b’acin rai wanda bai tab’a ganin hakan daga gareta ba, duk da bai san asalin me ya kawota d’akin ba yasan dai zaiyi wuya a ce bata da gaskiya.

Zaunar da Hafsat d’in yayi ya zauna gefenta yana shafa bayanta ya kasa ceewa komai dan hankalinshi da nutsuwarshi na wani wurin gaskiya.

Mimi kam na fita ai kuwa da gaske take dan akwatin da aka mata na lefe ta d’auko guda a ciki ta shiga zuba mata kaya saida ta mata nak da kaya ta d’auki hijab ta saka ta fito, su Heezam na zaune suka ga fitarta babu wanda ya mata magana saidai suna fatan ba matsalar Aisha ce ta jawo wannan babbar matsala ba.

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *50*

Jin yanda zuciyarshi ke ta buga mishi da sauri har sai ya bud’e baki yake sauke numfashi yasa shi d’an janye Hafsat daga jikinshi ya mik’e, zai fita ta rik’o hannunshi ya juyo suka kalli juna, cikin dakusashiyar murya tace “Kayi hak’uri idan na b’ata maka rai.”

Kasak’ai yayi yana kallonta kamar baya hayyacinta sai kuma ya kawar da kan shi yace “Ya zanyi idan ba hak’urin ba, tunda kun sani mun taru mun wa yarinya rashin adalci, mun nuna mata mu jahilai ne marasa tunani…”

Sab’ule hannunshi yayi daga rik’on data mishi ya juya ya bar mata d’akin, da kallo ta bishi tare da jin wata matsananciyar kunya ta rufeta, sai ta samu kan ta da jin nauyin kan ta da kuma mijinta da Mimi, tabbas tasan abinda ta aikata har da rashin fitar da abinda ke ranta da tayi na wani lokaci, shiyasa yanzu ta fake da abinda ya faru ta d’an furzar da abinda ke ranta, gashi sun tafi sun barta da tunani kamar kan ta zai fashe. Alamu sun nuna sheikh yayi hushi da ita, ga kuma mamakin yarinyar da take kallon fuskar mijinta tana kiranshi da Abdul.

Wani lallausan murmushi ta saki ta furta “Har yanzu bana iya kiransa da sunan Abdul Waheed ko da bayan idonsa ne, amma ita kai tsaye a gabanshi take kiran Abdul Abdul.”

Yana fita a rud’e ya nufi d’akin Mimi, ganin bata nan sai kaya dake kan gado a barbaje yasa shi durk’ushewa ya kifa kanshi a gadon yana furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”

Ya maimaita haka sau uku kafin ya mik’e yana lalubar wayarshi tare da fita a d’akin ya nufi waje, d’aya daga cikin jami’anshi na ganinshi ya taso a sukwane, da sauri ya tara masa hannu yace “Makulin mota?”

Da girmamawa yace “Sheikh mu je sai na sauk…”

Bai gama fad’a ba a tsawace yace “Ka bani makulli bana so.”

Da sauri ya mik’a mishi yana ja baya da d’umbin mamaki, tunda suke haka bai tab’a faruwa ba sai yanzu, bak’ar Mercedes ya shiga yana d’ora waya a kunne yana kiran lambarta, data fara k’ara sai ta kashe kiran hakan ya k’ara d’imauta tunaninshi, yana fita dama ya nufa da fatan had’uwa da ita, saidai sam bai ga alamarta ba har saida ya iya kwanar unguwarsu.

K’ofar gidan ya k’urawa ido yana kallo dan yasan dai nan zata zo, amma shiru bai ga alamarta ba saida ya d’auki waya ya sake danna kira, k’it ta datse kiran da sauri ya shiga rubuta mata sak’o kamar haka _”Ryam ki rufa min asiri, karki d’ora min hawan jini da tsufana, dan Allah na rok’eki.”_

*Mimi* kam ta jima da shiga gida dan haka ma bai ganta ba, tunda ta shiga taxi take kuka kamar an mata mutuwa, tana fita ta mik’awa mai taxi jaka guda ta shige gida da jakarta, Abba dake shirin fita kicib’us sukayi a k’ofar shiga, kaucewa yayi a hanye ta wuce yana d’aga kai sosai yana kallonta da fad’in “Ke daga ina? Uwata anya kuwa baki da aljanu? Me ya fito dake yanzu daga gidanki?”

Durk’ushewa tayi ta fashe da wani kukan ba tayi magana ba, sake gusawa yayi a bakin k’ofar yace “Ina zaki da k’atuwar jaka haka?”

Had’a kanta tayi da gwiwa cikin kuka tace “Abba ni gidanmu na dawo, Abba na ba zan iya zama a gidan Abdul ba, wallahi bak’in cikin ‘ya’ya…”

Da k’arfi ya kai mata bugu a baki yana fad’in “Astagfirullah! Uwata sheikh d’in ne Abdul kai tsaye? Ban gane ba zaki iya zama ba ?”

Juyawa yayi ya kalli k’ofar d’akinsu ya k’walla kiran sunan Mama da “Rabi, Rabi’a kina ina? Zo nan zo kiga haukan ‘yarki.”

Da sauri Mama ta fito k’undul k’undul kamar zata fad’uwa tana fad’in “Malam lafiya?”

Nuna mata Mimi yayi data rufe bakinta daya buga yace “Ga ta nan ta fad’a miki kiji.”

Kallon Mimi tayi hankali tashe tana jin wani suka a zuciyarta bakinta na hard’ewa tace “Mimi lafiya? Me ya faru?”

Abba ne yayi tsal yace “Ba wani lafiya, wai fad’i take ba zata iya zaman gidan sheikh ba, ke dan Allah a nan gidan ba hak’uri kike dani ba ?”

Sunkuyar da kai Mama tayi tana jin kamar tace mishi ya fita ya barsu ita da ‘yarta ta ji me ye matsalarta, amma yanda ta ji ya fara fad’in “Ke Maryama bana son shashancin banza da wofi, ni zaki mayar k’aramin mutum da bai san me yake ba, duka yaushe kika tare a gidan na ki da zaki fara min yaji, kenan kinfi k’arfin a b’ata miki rai ke ‘yar gwal? Yanzu haka ma ba da izinin gafarta malam kika taho ba, to ni ba za’ayi haka dani ba, maza tashi ki koma gidanki kamar yanda kika kawo kan ki, ba zan zauna na baki mafaka a gidana ba kwana kad’an ki fara min laulayi kamar yanda uwarki ke fama da na ta laulayin.”

Da sauri Mimi ta d’aga kai ta kalleshi sai kuma ta kalli Mamanta, a ranta tace “Mama ciki ne da ita?”

Sai kuma ta yatsina fuska tace “Allah sawak’e ma na d’auki cikin mutumin nan, tsoho kawai da wata akwalar matarshi da ‘ya’yanshi marasa kunya.”

Had’e fuska ta sakeyi ta kalli Abba ta marairaice tace “Abba dan Allah karka koreni a gidan nan, Abba ka ga fa da shi da matarshi da ‘yarsu suka min taron dangi, ni wallahi Abba…”

Takalminshi ya cire yana fad’in “Ke in ban kakkarta miki…”

Ganin Mama ta juya tana rufe bakinta dan dama ya gama kasheta da kunya tunda yayi maganar cikin nan yasa shi binta da kallo, Mimi da tuni ta mik’e da gudu ta fita waje ta fashewa da kuka, akwatin ya kama da nufin cilla mata ita saidai ta fi k’arfinshi dan a tsayi ma kusan kansu d’aya da akwatin, turata ya dinga yi saida ya fito mata da ita ya nunata da yatsa tana tsaye nesa da shi yace “Wallahi kika bani na d’aga murya a kan ki ba zakiji dad’i ba uwata, har gidan na ki zan sameki na zazzabga miki dukan mutuwa.”

Cikin sand’a ta jawo akwatin na ta tana kallonshi ya koma cikin gidan yana fad’a, had’e hawayenta ta kalli unguwar ta su da kyau, duk da ba dare bane sosai amma babu mutane sai masu wucewa, numfashi ta sauke cikin disassashiyar murya tace “Kayi hak’uri Abba na ka yafe min, amma ba zan iya komawa gidan Abdul yanzu ba, idan na koma kamar ban da zuciya ne da kuma gata, ku a wajenku haka da kukayi shine daidai, amma ni tunda ni ke zaune dashi dole na bi kowaxe hanya dan samawa kai na mutumci a gurinshi, Mama na ta fad’a min na koyi yanda zan kula da kai na, kuma na yi alk’awarin zan k’watarwa kai na ‘yancina ba tare da taimakon kowa ba.”

A hankali ta ja akwatin na ta ta d’auki hanyar zuwa gidansu Iya Delu, haka ta dinga kakkare fuskarta dan bata so yan unguwar su ganeta musamman da take d’auke da akwati shak’e da kaya.

Tana zuwa gidan malam na cin tuwo Iya na gefenshi suna hirarsu a nutse, ko sallama ba tyi ba ta k’arasa cikin shagwab’a tana saki akwatin ta fad’i ta cire hijabi ta zauna tsakiyarsu, mamakinta na neman kashesu da k’yar Iya ta kalleta galala tace “Ke kuma fa daga ina?”

D’ora kan ta tayi a gwiwar Iya ta shiga rera kuka a sanyaye tana fad’in “Kakani na bani da gâta a duniyar nan, kasheni zasuyi da bak’in cikinsu da bautarsu, dan Allah ku zame min gata kunji.”

Cire hannu malam yayi a tuwo ya kalleta ya dafa kafad’arta yace “Ta gaban goshina, waye ya tab’a min ke?”

D’agowa tayi ta kalleshi cikin Luka tace “Malam na gaji da zaman gidan sheikh, dan Allah ku barni na zauna anan na huta, na je can Abba bai ma saurareni ba ya koroni da takalmi.”

D’ora kanta tayi shi ma a kafad’arshi tare da rik’e damtsenshi gam, cikin tausayawa da nutsuwa yace “Me ya faru amaryata?”

Ba tare data d’aga kan ta ba ta shiga labarta masa komai daya faru tun daga farkon abinda Aisha ta fara mata har zuwa yau d’in, saida ta gama abinda bata tab’a tsammani ba daga Iya ta ji tace “Maganar banza, yo an fad’a musu ke d’in a bishiya muka tsinkoki? Ya zasu taru gard’ama gard’ama dasu su nuna miki fin k’arfi.”

Gyara zama tayi ta jawo Mimi ta shiga daddab’ata tana fad’in “Ke rabu dasu kinji, nan zaki zauna na ga wanda ya isa ya maidaki k’arfi da yaji, kaga iskanci.”

Dariya malam yayi yana girgiza kai bai ce komai ba, dan gaskiya yanda yake son Mimi shi ma sai yaji bai ji dad’i ba musamman da ita kan ta uwar yarinyar ta fad’a mata maganganu sannan shi bai tsaya ya bincika ba kuma ya d’ora mata da fad’in matarshi matarshi, yana gama cin abincin shi ya wanke hannayenshi ya d’auki k’aramar rédion shi zai fita ya kalli Mimi yace “Ki shiga da kayan ciki ki kwanta zuwa safe zan san abun yi.”

Mik’ewa tayi da sauri tana fad’in “Ni da safen ma makaranta zan tafi, kawai ka k’yaleshi yana tsohonshi dan ma ya samu na kulashi.” Da kallo suka bita malam na dariya ya fita a gidan.

*Ya jima* nan amma bai ga wulgitawarta ba sai kawai ya sake kiran wayarta, a lokacin tana d’akin Iya tayi kwance a gadon k’arfe tana d’an lilawa kad’an kad’an, d’aga wayar tayi ta d’ora a kunne cike da gatsali tace “Ina ji?”

Shiru yayi idonshi lumshe murya k’asan mak’oshi yace “Ryammm.”

Tsam tayi tare da dakatawa da lilawar da take a gadon, wani tsammm ta ji gaba d’aya jikinta saida ya amsa, d’an basarwa tayi tace “Ina jinka.”

Cikin sanyi da taushin murya yace “Kina ina Ryam? Dan Allah ki dawo.”

Cikin shagwab’ar da bata san tayi magana ba tace “Um um! Ni ba zan koma ba tunda ba so na kake ba, Abdul baka so na kuma baka son zamana a gidanka, sannan ‘yarka da mahaifiyarta basa so na sun tsaneni, kawai ka zauna da iyalinka na yafe musu kai har abada, kaga ai dama ni ma kawai had’ani ne aka yi da kai ba dan ina so ba.”

Da sauri kamar wanda zai fashe da kuka yace “Ba haka bane Ryam, nasan an miki ba daidai ba amma ki yafe mana kinji, Ryam in kin san yanda nake ji wallahi da baki tafi kika barni ba.”

Tashi tayi zaune tace “Ba wani nan, kawai wayo kake so ka min dan ina yarinya, to ni ma da hak’orana ashirin da bakwai.”

Dariya ce ta kubce mishi har tana jin sautinta a kunne kafin yace “Ryam, kenan bakiyi hak’oran hankali ba.”

Turo baki tayi irin bata ji dad’i ba kafin tace “Ni dai saida safe, kaga yanzu ba gidanka na ke ba.”

Zata kashe wayar yayi saurin fad’in “Inna Issa ina kika je?”

Cike da yarinta tace “Ina wani wuri.”

D’if ta kashe wayar ta aje gefe ta kwanta, wayar ya bi da kallo sai kuma ya aje ta ya wa motar ky, ba zai iya tafiya gidansu ba a yanzu dan haka zai bari har da safe, duk da yana jin wata irin kunyar had’uwa da iyayen na ta, dan gaskiya abin nan ya dakeshi sosai, kuma yasan yana da laifi ta wani b’angaren, da wannan tunani ya isa gida kai tsaye b’angarenshi ya wuce. 

Hafsat ma ta jima zaune kafin ta mik’e dan duba yaran ko sun kwanta, saida ta shafawa dukansu addu’a kafin ta nufi d’akin Aisha, zaune ta sameta tsakiyar gadonta tana karatu da Qur’ani, k’arasawa tayi ta tsaya gabanta tana kallonta, ita ma d’aga kai tayi ta kalleta tace “Amie baki kwanta ba?”

Ba sakin fuska a tare da ita tace “Ta ya zan kwanta bayan bansan halin da kike ciki ba.”

Murmushi tayi na jin dad’i tace “Amie lafiya ta lau, kiji ki kwanta ke ma.”

Wani malalacin murmushi tayi tace “Yayi kyau, haka yayi kyau tunda gashi har ina ganin murmushinki saboda yau kina farin ciki mahaifiyarki tayi fad’a a kan ki.”

Wani kallo ta mata baki sake irin tana jiran k’arin bayani, ruugume hannaye tayi tace “Kin fahimta mana, ya kamata kiyi farin ciki a zuciyarki tunda dai Mimi ta tafi gidansu.”

Zabura tayi tana aje Qur’anin tace “Me? Ta tafi Amie?”

Wani dogon tsaki ta ja ta juya zata bar d’akin Aisha ta sauko tana rik’e hannunta tace “Amie da gaske ta tafi? Amie ku yafe mi…”

Tureta tayi ta fizge hannunta tace “Shiru dallah! Hak’urinki na banza da wofi kike ba mutune, kullum ki ce kin tuba kuma ba zai hana anjima ki sake aikata abinda kika aikata ba, Aisha me yake damunki? Me aka miki da zafi haka da kike neman tarwatsa mana zaman lafiyar gida? Tunda kike kin tab’a ganin sab’ani tsakanina da mahaifinku? Kawai saboda an yi min kishiya k’waya d’aya, ba dan mahaifinki ya kasance mutum da bai san matsala da a yanzu Mimi ta hud’u ce ita.”

Nunata yayi tana k’yasta hannunta tace “Ki ji da kyau zan daidaita gidana da kai na, wallahi wallahi wallahi kinji uku ko? Na rantse miki da Allah Aisha kika sake wani abun da bai min ba a gidan nan sai na miki d’an banzan duka sannan na wankeki a haka na kaiki d’akin miji.”

Harara ta watsa mata sannan ta wuce ta barta nan tsaye, wani iri take ji gaba d’aya ta ma rasa inda zata saka kan ta ta huta, haka ta koma kan gadon ta zauna ta buga tagumi tana tunanin abun yi.

                  *Washe gari*

Tunda sassafe malam ko da yayi sallah ya samu Abba a masallacin unguwarsu ya fad’a musu abinda ya faru, rai b’ace duk da kunyar sirikina shi saida ya kalleshi yace “Yanzu malam can ta tafi kenan? Dama bata ji magana ta ba?”

Saka takalminshi yayi yace “Malam muje gidan nan dan Allah ka yarje min na daki hancin yarinyar nan.”

Dakatar da shi malam yayi yace “A kan me? Kaga ni bana fad’a maka bane dama dan ka je ka d’aga min hankalinta ba, na fad’a maka ne dan ka sani kuma ko da mijin na ta ya nemeka ka sanar da shi inda ta ke.”

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace “Shikenan malam, insha’Allahu da kai na ma zan kirashi.”

Jinjina kai malam yayi yace “Hakan ma daidai.” Da wannan suka rabu kowa yayi gida, Abba na zuwa da fad’a ya shica fad’awa Mama tare da d’aukar wayarshi ya fara kiran lambar sheikh, yana ganin kiran amma bai d’aga ba saida ta tsinke sannan ya d’aga, a mutumce kuma a kunyace suka gaisa kafin Abba ya d’an sosa kai yace “Gafarta malam dama shiriritacciyar yarinyar nan ce jiya da dare ta zo mana da wani hauka, to ko da ta zo ma na maidata ashe bata tafi can ba.”

Shiru sheikh yayi kamar bai ji, har ga Allah lamarin yi masa yake kamar a mafarki, da k’yar ya cira bakinsa yace “Ayi hak’uri malam, insha’Allah idan na dawo daga aiki zan zo da kaina gidan muyi magana, ina mai bada hak’uri dan Allah, insha’Allah haka ba zata k’ara faruwa ba. “

Cike da girmamawa Abba yace “Shikenan sheikh ba komai, ban da ma abin yara ina abun hushi a nan? Allah dai ya shirya mana su.”

“Ameen.” Ya fad’a a hankali, sallama sukayi kafin Abba ya kalli Mama dake kad’a miyar d’umame yace “Ban san me uwata take son zama ba, ki ji yanzu babban mutum kamar wannan yanda yake kwantar min da murya yana bani hak’uri.”

K’wafa yayi ya mik’e zai nufi d’aki yana fad’in “Yarinyar nan in batayi sannu dani ba saina b’ata mata rai wallahi.”

Mama dai da kallo ta bishi dan ita ban da ganin ‘yarta babu abinda take son yi, dan wannan kamar a dakeka ne a hanaka kuka, yarinya kamar Mimi a kai wa dattijo kamar sheikh, shin in bai bita a sannu ba ya za’ayi?

                      *Mimi*

Tana zaune ta tank’washe k’afafu tana cin tuwo tare da malam hannunta hannunshi suna ta ma Iya tsiya wai ba zasu ci da ita ba wayarta tayi k’ara, juyawa tayi ta d’auka tana dubawa ta ga Asma’u, wani murmushi ta saki ta danna ok ta d’ora a kunne, cikin nutsuwa tace “Hum! Ashe kina iya tunawa da mutane?”

Dariya Asma’u tayi daga wajenta tace “Dan kar na fara miki k’orafin shi ne kika rigani?”

Tab’e baki tayi tace “Ba wani nan, kin manta da mutane saboda kina shan amarcinki.”

Asma’u dai na dariyarta tace “Kedai tafi can, yanzu har sammakon da na yi na kiraki ban tsira ba kenan?”

Gwalo ido tayi tace “Oho! Kenan kin kirani da safe ne dan na yafe miki?”

Cikin marairaicewa Asma’u tace “Kiyi hak’uri to, amma ke me ya hanaki kirana? Ke ma amarcin kike sha da yayanmu ko?”

Yatsina fuska tayi tana kallon malam tace “Ba wani nan dan Allah, ni da ma na bar muku yayan na ku ku dafa ku cinye tunda baku san mutumci ba.”

Dariya Asma’u tayi tace “Kamar ya? Su waye marasa mutumcin?”

Kai tsaye tace “Ke da yar uwarki mijinki mana.”

Da sauri Asma’u tace “Wani abu ya faru tsakaninku? Me Hafsat d’in ta miki kuma?”

Tab’e baki tayi tace “Rabu dasu can su k’arata tunda ni dai na baro musu gidan.”

Hankali tashe a kid’ime Asma’u tace “Kamar ya Mimi? Ban gane kin baro musu gidan ba? Kina ina yanzu ke?”

Kallon kwanon tuwon tayi tace “Ina gida wajen Iya gani ma ina cin tuwo da angona.”

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Asma’u ta sauke tace “Me ya had’aku Mimi? Me yayi zafi haka?”

Mik’ewa tayi ta cire hannunta a d’umamen burabuskon da Iya tayi ta fito waje ta shiga d’akin Iya t zauna ta shiga labarta mata abinda ya faru, Asma’u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta bar d’akin da Asas yake kafin tace “…

*Hohoho, gaskiya fa an sha muhawara, sannunku sannunku, sunana har ya kare😁.*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *51*

Asma’u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta d’akin da Asas yake kafin tace “Assha kuwa? Mimi ke da kan ki kikayi kuka a gaban kishiya? Ke ce kika rasa sanin hanyar shawo kan matsalarki har kika bari aka fara sakaki yaji ko kwana bakwai bakiyi ba, ya akayi haka ta faru? Ni da nake tunanin ke ce malamata ta wannan fannin, sabida kin tab’a fad’a cewa ko a cikin mata uku aka kaiki zaki iya zama dasu kuma ki k’waci kanki a hannunsu.”

Numfasawa tayi tace “Kinga Mimi duk yanda nake k’aunar yar uwar mijina bai kai k’aunar da nake miki ba dan ke tare muka tashi, ban ce ina so ta zama mowa a gidan nan ba, amma kuma ina so ki zama bora a gidanki ke ma, dan haka kiyi wani abu Mimi, a sanina dake kina da shiga mutane da kutsa kan ki inda yafi k’arfinki, kina karance karance da saurare da kallo sannan ga babbar waya a hannunki, dan Allah ki daure ki samu shawarwarin da zasu taimaka miki zama da mijinki da abokiyar zamanki da ma ‘ya’yanku.”

Mimi da tayi shiru tana saurarenta saida ta ji ta dasa aya ta numfasa sannan tace “Nagode k’awata, kin k’arfafa min gwiwa kuma zanyi aiki da abinda kika fad’a min.”

Da fara’a Asma’u tace “Yawwa Mimi ko ke fa.”

D’orawa tayi da fad’in “Ni fa na kiraki ne dan muyi wata magana.”

Da zumud’i Mimi tace “Wace magana fa?”

Cikin jin kunya Asma’u tace “Dama wani abu nake so ki d’an fad’a min da zanyi na k’arin…”

Shiru tayi hakan yasa Mimi fad’in “Ina jinki?”

Cikin dariya tace “Kedai kawai zan miki magana ta WhastAp.”

Kyab’e baki tayi tace “Kin samu babbar waya kenan?”

A sanyaye tace “Na yi, idan mun had’u zaki gani.”

A take Mimi tace “Yaushe ma zamu had’un?”

Cike da tsokana Asma’u tace “Ga bikin ‘yarki da za’ayi juma’a.”

D’an gajeran tsaki tayi tace “Hummm! ‘Yar masu ita dai.”

Suna sallama Mimi ta fito da sauri ta wanke hannayenta ta koma d’akin, wayarta ta shiga dannawa tana duba abubuwan k’aruwa musamman a WhastAp, duk abinda ta ga an turo a grp ta kan tsaya ta dubashi a tsanake, ita da Asma’u ma hira suka sha inda Asma’un ta fad’a mata tana son abun k’arin ni’ima ne, wanda ta sani ta fad’a mata sannan tayi alk’awarin binciko musu wasu.Tana tsaka da aikin gabanta kiran sheikh ya shigo wayarta, tana ganin kiran kawai ta datse shi tare da ci gaba da aikin gabanta, haka yayi ta kira dan su gaisa amma ta k’i d’agawa, sai sak’o ya tura mata da _”Amincin Allah ya tabbata a gareki, da fatan kin wayi gari cikin k’oshin lafiya?”_

Shiru yayi ta jiran amsa amma bata maida ba dole ya sake tura mata _”Da alama ba zaki yafe min cikin sauk’i ba, Ryam ki yi hak’uri kinji.”_

Nan ma shiru bata maida ba sai kawai ya aje wayar ya buga tagumi yana kallon na’urar gabanshi dake jiran ya loda mata wasu bayanai dake gabanshi a takarda amma ya kasa.

Saida tayi sallah azahar ta d’auki wayarta ta rubuta duk abunda take da buk’ata sannan ta shirya ta fito Iya na tsakar gidan tana gyara wake, tsaye tayi gabanta inda Iya ta shiga kallonta da mamaki tace “Ke kuma ina zaki je kika wani shirya haka?”

Turo baki tayi tace “Iya kasuwa zan je akwai wasu abubuwan buk’ata da zan siyo.”

Cike da raini ta kalleta tace “Ke fita ido nq in rufe? Wato ga marainiyarki ko? Daga tahowarki jiya zaki ce zaki fita a gidan nan? To da izinin wa?”

Bubbuga k’afafu tayi tace “To Iya dan Allah ba gidanmu ne nake ba kuma na fad’a miki.”

Cikin fad’a tace “A’a, dan kin fad’a min a banza tunda ba ni ke aurenki ba, ke Mimi in kikayi wasa wallahi saina hau bishiya na tsinko tsumagiya na ci ubanki a gidan nan, ni zaki mayar tsohuwar banza?”

Galala ta kalleta tace “Ka ji min tsohuwar nan da wata magana, to ki hau bishiyar mana dan Allah, ni na fad’a miki ki daina zagar min uba fa.”

A harzuk’e tace “An zaga d’in, kiyi abinda zakiyi na gani.”

Murmushi tayi ta durk’usa gabanta ta dafa hannunta tace “Iya ta, kinga fa idan na je kasuwar nan zan siyo miki goro da tantak’washi da kifi d’anye, sannan yanzun nan Asma’u ta fad’a min wani abu da ake sha ana zama mowa a wurin miji, shine fa zan je na siyo.”

Hararanta ta dinga yi amma ba tayi magana ba, sun jima suna kallon juna kafin Iya ta sassauta murya tace “Shikenan na yarda ki je, amma Mimi kar kiyi abinda zaki sa a zageni dan Allah.”

Shafa kuncinta Mimi tayi tana mik’ewa tace “Yawwa Kakata, shiyasa nake son ki.”

Girgiza kai tayi tace “Kiyi sauri dan Allah kinji, ni ma zan je wajen malam Hadi na sa ya maki rubutu na bakali a wurin miji.”

Wata lalatacciyar dariya Mimi tayi ta jinjina kai dan tuni ta hango yanda zatayi ta tsokano sheikh kafin ta fice a gidan.

Ta d’aya hanyar ta bi ta kusa da makarantarsu anan ta samu taxi ta wuce, tana ciki Salma ma ta kirata bayan sun gaisa take sanar mata jibi fa zata shiga lalle, da rawar kai da zumud’i Mimi take ta fad’in Allah kai su ranar su sha biki.

Gurin masu siyar da litattafan hausa ta fara zuwa ta siyo na girki da kuma wasu na ki gyara da kan ki da saurarensu, daga nan gurin masu kayan marmari ta nufa ta shiga had’owa kala kala, ta gama siya ta juya zata nufi Inda zata samu dabino da cukui suka had’e da yayar Asma’u Rayya, gaisawa sukayi saidai jikinta har rawa yake tsabar ta kwab’ar da zance tace “Mimi ke ce kasuwa a lokacin nan? Dama malamai na barin matansu fita haka?”

D’an murmushi tayi dake tana kallonta kamar yar uwa sai tace “Ni ma na je gidan Iya ne shine na biyo siyan wannan.”

Murmushi tayi ita ma tace “Lallai fa su Mimi an shiga sahun manyan mata, kin ga yanda kikayi wani fresh dake wallahi kamar na saki a jakata.”

Dariya Mimi tayi ba tace komai ba, kama hannunta tayi tace “Zo muje ki gani, ni ma nan ga ne zan je neman d’anyen madarar rak’umi.”

Mimi dai bin ta kawai tayi suna tafe take fad’in “Kina ji ko k’anwata, wani sirri ne zan baki ni ma wata malamata ta bani shi, amma fa karki fad’a ma kowa kinji?”

Jinjina kai tayi suka ci gaba da tafiya tana fad’a mata abubuwan buk’ata, hakan yasa Mimi kallonta galala dan duk kayan data fad’a ita ma sune a ledarta, hatta da nonon rak’umin a wata alimentation ta sameshi nan bakin kasuwar, amma sai ta bita da to kawai har saida ta rakata ta siyo na ta kayan ita ma.

Duk da haka ta k’aru da zamansu a d’an lokacin sanda take fad’a mata “Kinga kishiya gareki, karki yarda abokiyar zamanki ta dinga fahimtar halin da kuke ciki ke da mijinki, idan ya b’ata miki karki bari ta sani, idan duka ya miki a d’aki ki fito kina dariya, karki bari ta san k’uncinki ko kukanki bare damuwarki, dinga sakin fuskarki kina nuna farin ciki kawai. Haka kuma dan kina yarinya ba mahaukaciya bace ke, ke ma ki ja d’amara sosai ki k’waci wani kaso a zuciyar mijinki.”

Kallonta tayi ta rik’o hannunta sanda suka tsaya bakin titi zasu tafi tace “Mimi ki kula sosai, kishiyarki ta girmeki nesa ba kusa ba tunda ta haifi kamarki a yanda na ji, kinga kenan ta fiki sanin wanene mijinku, kuma kinsan an ce wanda ya rigaka kwana to fa tabbas zai rigaka tashi, zata iya biyo mikita wata sigar da ba lallai ki fahimta ba, zata iya nuna miki ta fiki wayo dan haka ta dinga miki siyasa tana mikina babba da yaro, to fa idan ba nutsuwa kikayi ba a wannan lokacin zata iya rubtawa da ke.”

Galala Mimi ta kalleta tace “Kamar ya kenan Aunty Rayya?”

Murmushi tayi ta dafa kafad’arta tace “Misali ko a wajen kula da mijinku, zata iya nuna miki yafi son abu kaza alhalin ba gaskiya ba ne, ko kuma ta nuna miki baya son abu kaza alhalin yana son wannan abu, ke ko a wurin girki idan kika samu makira zata iya saka ki zuba awon da ba zai ishi fad’in gidanku ba, k’arshe da an tambayi ba’asi zamewa zatayi ta barki a ciki.” 

Shiru Mimi tayi saidai inzata fad’i gaskiya tasan Hafsat tsakani da Allah take fad’a mata wasu abubuwan, tunda wani abu bai tab’a faruwa ba dalilin taimaka mata da tayi, to amma ai ba’a k’in ta mutane tunda shawara ce ta bata.

Daidai lokacin da Rayya ta tsayar da taxi a lokacin Mimi tace “To ya zanyi kenan aunty?”

Kallonta tayi a gaggauce tace “Nutsuwa zakiyi  da kyau kisan me mijinki yafi so me ye baya so, sannan ki kwantar da kanki ki girmama duk wanda kika ga yana girmamawa, hakan ba fad’uwa bane ke siyawa girma da soyayyarsa.”

Murmushi tayi sosai tace “Nagode aunty Rayya.”

Ita ma murmushi tayi tace “Ba komai, kamar Asma’u na d’aukeki.”

Mik’o mata wayarta tayi tace “Aunty saka min lambarki mana.”

Karb’a tayi tana saka mata tana fad’awa taxin inda zai kaita, mik’o mata tayi kafin ta shiga suna sake sallama, ita ma taxin ta samu ta d’auki hanyar komawa gida abin ta zuciyarta fes bata jin wani k’unci.

                    *Sheikh*

Lallai idan har bak’on yanayin da baka saba dashi ba ya riskeka dole ko da a yanayi na gangar jikinka ne zai nuna, yau sheikh Abdul Waheed bai iya jira gari ya waye mishi ba a masallaci ya taho gida, kai tsaye kula bayan gidan ya nufa ya tsaya ya zubawa tsintsayen dake shawagi ido, shi ba salatin Annabi ba, shi ba hailala ko istigfari ba, haka kawai yake tunanin yanda ‘yarcikin ke neman zama silar tarwatsewar gidanshi da kuma jefashi damuwar da bai san ya zaiyi ya fito da kan shi ba, yarinyar daya rena da hannunshi ya tarbiyanceta, yarinyar da har a cikin gidan nan idan mahaifiyarta bata samu dama ba ita ke karantar da matan auren unguwar nan, amma ita ce yau take neman canzawa gaba d’aya har take iya shiga hurumin da sam bâ na ta bane.

Babban abun damuwar shi ne yanda daga jiya zuwa yanzu da gari ke wayewa yake sake jin wata kewa da muguwar k’aunar Mimi na sake baibayeshi ta yanda har yake jin idan yaje gidansu ko k’asa ne zai durk’usa ya ce tayi hak’uri ta dawo gareshi, uwa uba matsananciyar kunyar had’uwa da iyayenta da yake ji, baisan ya zai ce musu ba, ya fad’a musu ‘yar shi ta fi k’arfinshi ne ko kuma dai yace yaro ne na yanzu ka haifa baka haifi halinshi ba?

Wata ajiyar zuciya ya sauke ya na ci gaba da kallon yanda tamtabaru ke tsatsagar k’asa suna d’aukar abincin da ake watsa musu, yana wannan yanayin ne kiran Abban Mimi ya shigo wayarshi, wani mummunan fad’uwar gaba ya ji kamar wanda aka daka da k’atuwar gudumar bak’in k’arfe, har tsigar jikinshi ne ya ji ta tashi saboda rud’anin daya shiga, da k’yar ya d’aga kira ya d’ora a kunne jikinshi har wata makyarkyata yake, a daddafe suka gaisa har ya fad’a mishi zai zo anjima, suna sallama ya sake maida wayar aljihunshi yana tunanin dole ya kira Alhaji Ibrahim tunda uba ne gareshi ya rakashi wajen iyayen Mimi. Rintse idon shi yayi sosai dan har ga Allah wani kuka kuka yake jin yana taho mishi sakamakon abinda yake ji a zuciyarshi, shi da Hafsat ko da wasa basu tab’a musayar yawu ba ta fad’a ya fad’a bare ta kai ta ga yaji, amma yau ga shi wai zai je bikon macen daya tabbata idan bai je ba rayuwarshi ma zata shiga garari.

Wasa wasa sai gashi lokaci ya wuce mishi a wurin nan bai tsinana komai ba. Hafsat ma da taga shiru kuma ta duba d’akinshi baya nan ta tambayi su Heezam sun ce ya jima da dawo gidan sai ta d’auki waya ta kirashi, lalubo wayar yayi ya k’urawa lambarta ido, saida kiran yayi kamar zai tsinke ya d’aga amma kuma sai yayi shiru alamar yana saurare.

Hafsat kuma sai ta d’auka ko har yanzu hushi yake da ita, a sanyaye tace “Ranka shi dad’e, barka da safiya.”

A yanayin da zaka san mutum baya cikin walwala ya amsa da “Barka, antashi lafiya?”

“Lafiya lau.” Ta fad’a a ladabce kafin ta d’ora da “Dama na ga shiru baka dawo ba tun asuba, ko ka wuce wurin aiki ne?”

Wata zabura yayi yana waro idonshi akan tsintsayen, dafe gaban goshinshi yayi yace “Subhanallah! Na manta wallahi, ina zuwa.”

Da sauri ya kashe wayar ya nufo hanyar sashen shi, Hafsat kam da mamaki ta bi wayar da kallo tana fad’in “Mantawa kuma? Aikin da babu abinda ka d’auka da mahimmanci bayanshi sama da mu?”

Tana nan tsaye a falon na ta ta ji k’arar k’ofar b’angarenshi alamar ta k’ofar baya ya shiga, takawa tayi ta shiga falon na shi, a gaggauce ta sameshi yana cire kaya zai shiga ban d’aki, d’an murmushi tayi tace “Yallab’ai garin ya ya ka manta da aikin jama’a haka?”

Kallonta yayi yace “Kuyi hak’uri dan Allah, wallahi na…”

Sai kuma yayi shiru ya sauke numfashi, ban d’akin ya shige da sauri inda ta rakashi da ido, d’an murmushi tayi dan ita dai wani abu ta hango a tare da shi, juyawa tayi da sauri ta je ta had’o masa abun kari a babban faranti ta dawo, tan a shigowa shi ma ya fito alamar bai yarda ya d’auki lokaci ba, cikin sauri yake goge ruwan jikinshi yana fad’in “Manga kiyi hak’uri ba zan tsaya cin abincin nan ba na sake b’ata lokaci, idan na je can na ci idan na shiga hutu.”

Kallonshi tayi jikinta a mace tace “Amma ko ya ya ka ci mana, jiya ma fa baka ci abinci ba.”

Girgiza kai yayi yace “Ba zan k’ara b’ata lokaci ba Manga, aikin nan na jama’a ne ba nawa ba, hakk’in mutane dayawa ne a kai na, bana so Allah ya tambayeni ko da da lattin minti d’aya ne.”

A ladabce tace “To ko na juye maka shi sai ka tafi da shi?”

Da sauri ya kalleta tarrr a fuska dan Mimi ta tuna masa sanda take magiyar ta dinga aika masa abinci, k’arasa d’aure zariyar wandonshi yayi ya girgiza mata kai, bata k’ara magana ba har ya gama saka kayan ya d’auki jakar na’urarshi ya nufota, sumbatar goshinta yayi yace “Sai na dawo.”

A sanyaye ta bishi da kallo dan har ya nufi fita tace “A dawo lafiya.” Saida ya bud’e k’ofa zai fita yace “Allah yasa.”

Yana fita bai ga ko d’aya daga cikin yaran ba alamar duk sun taafi makaranta su ma, da sauri ya shiga motar da jami’in ya bud’e mishi k’ofa suka tayar da jiniya suka d’auki hanya.

              *08:30 na dare*

Tun yamma da malam ya dawo yace mata mijinta zai zo anjima ta shirya dan tare zasu koma ta fara fad’awa Iya “Ni wallahi kai na ma ke ciwo.”

Iya kam da bata san manufarta ba sai ta d’auki jibda ta bata tace ta shafa dan ta santa ba magani take so ba, ana magriba ta sake kallon Iya tace “Iya kai na fa bai daina ba, kuma ma amai nake ji yana taso min.”

Kallonta Iya tayi ta rufe baki sai kuma ta kawar da kai, murmushi ta saki tana girgiza kai tace “To Allah ya sawake ya raba lafiya, bari a yi sallah sai na baki garin hatsin nan kisha aman zai kwanta.”

Zuwa 08:30 ta rikita Iya da tsarabe tsaraben kaza ke mata ciwo kaza ta jin na mata ciwo, Abba ne suka shigo tare da malam dake kallon Iya yana fad’in “Mik’o mana tabarma ga mai gidan na ta nan su zo.”

Mik’ewa Iya tayi tana fad’in “Sannunku da zuwa, bari na d’auko.”

Tabarma ta d’auko ta shinfid’a musu a kusa da d’akin malam d’in tana kallon malam tace “Amaryar ta ka ma fa bata da lafiya.”

A tare suka kalleta da Abba suka ce “Bata da lafiya kuma?”

Kallonsu tayi ita ma tace “E wallahi, tunda yamma daka fita tace kanta na ciwo, yanzu haka dai amai ne tace ya fi damunta da tashin zuciya.”

_🤣 Uwata sha’ani_

A rikice malam ya nufi d’akin yana fad’in “Subahanllah! Amma kuma baki aika a fad’a min ba, ina bakin masallaci ai da ba an kaita asibiti ba.”

Wani galala Abba ya kallesu dan shi yanzu lamarin Mimi ya daina bashi al’ajabi ma, tab’e baki yayi yace “Malam karku wahalar da kanku, iskanci ne wallahi yarinyar nan zata mana.”

Shigewa malam yayi bai ce komai ba sai Abba daya fita dan shigo da su sheikh, jim kad’an suka shigo suna ta gaisawa da Iya a mutumce shi da Alhaji Ibrahim, zaune sukayi inda Iya ke sake fad’a musu “Ai ja’irar ma tana ciki duk ta rikice ba lafiya.”

Da wani sauri ya kalli Iya yana d’an jimk’e hannunshi akan gwiwarshi sai kuma ya kalli k’asa ya huro iska bai ce komai ba dan baya so yayi magana ya kwafsa a fahimci rauninshi akan yarinyar, Alhaji Ibrahim ne yace “Assha kuwa, an tafi asibiti kuwa?”

Fitowar malam yasa Iya bata bashi amsa ba dan yana fad’in “Jikin na ta dai babu zafi, aman ne kawai tace yake damunta da ciwon kai, sai k’afafunta da tace suna tauna mata.”

Wani kallo Abba ya masa sai yaga ai fa yarinyar nan ma ta rainasu wallahi, to me take nufi? Sheikh kuma sake sunkuyar da kai yayi bakinshi na son furta “Ku min izini na shiga na ganta dan Allah.”

Amma kunya da kawaici yasa shi  had’ewa ya shanye, Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh d’in yace “To me zai hana ka kaita asibiti?”

Iya ce tayi saurin cewa “Wacece? Mimin? Tabb’!”

Malam ne yace “Ai bata san zuwa asibiti saboda magani da allura.”

Abba ne ya gyara zamanshi kan tabarmar yace “Allah gafarta malam bari na fito maka da ita ku wuce gida, ba wani ciwo dake damunta iskanci ne.”

Mik’ewa yayi zai shiga d’akin malam yace “A’a fa Adamu, kiyaye ni wallahi akan amaryata.”

Sunkuyar da kai Abba yayi yace “Kuyi hak’uri malam dan Allah ku barni da yarinyar nan.”

A tausashe kuma a sanyaye sheikh yace “Ku barta.”

Shiru sukayi suka zuba masa ido shi kuma yana kallon k’asa, d’orawa yayi da “Ina me baku hak’uri dan Allah da gaba d’aya zuciyata, abinda ya faru sabo ne a gari hakan yasa na rasa hanyar da zan dakatar da abun, amma insha’Allah na tsawatar ta yanda bana tunanin hakan zai sake faruwa nan gaba, kuyi hak’uri dan Allah ita ma ku bata hak’uri, nasan an shiga hakk’inta dayawa amma muna neman afuwarta ni da iyalina.”

Cike da girmamawa da ganin dattakonshi Malam ya zauna yace “Ba komai sheikh, komai ya wuce ai insha’Allah, Allah ya yafe mana baki d’aya ya kuma baku zaman lafiya.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa kafin Iya tace “To ya za’ayi da ita yanzu? Zaku tafi tare ne?”

Sheikh ne yace “Tunda bata jin dad’i kawai ku barta, amma dai ya dace a tafi asibiti.”

Da murmushi Iya tace “Insha’Allahu zamu k’ok’arta mu gani, indai bata yarda ba ka sani ni zaneta zanyi sannan ta bar min gida.”

Murmushi yayi ba tare da sanin bakinshi ya furta ba yace “Kiyi hak’uri Iya karki tab’a ma…”

Sai kuma yayi shiru sanda sukayi ido hud’u da Abba, mik’ewa malam yayi da Abba tare da Alhaji Ibrahim, a sanyaye sheikh ya mik’e sai malam daya kalli Iya yace “Ki mata magana ta fito ko gaisawa suyi.”

Iya ce ta mik’e tace “Ko kuma dai ya wuce ba, ciwo ne fa ya zo ga uwayen mita da raki, ko ruwa bata tashi zaune tasha.”

Dariya sukayi inda Iya ta gyaraw sheikh tace “Wuce ciki.”

Jim yayi a tsaye yana sussunkuyar da kai sai kuma ya shiga takawa babu takalmi a k’afarshi ya nufi d’akin, yana d’aga labulen da sallama Mimi ta sauko daga kan gadon da sauri ta shige k’ark’ashin gadon da babu komai a k’asa sai buhuna.

Baki ya saki yana kallon sarautar Allah matarshi a k’ark’ashin gado, takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsugono irin na maza yana lek’awa k’asa yace “…

_Masha’Allah, hak’ik’a aka ce yaba kyauta tukuici, bamu rok’a ba, bamu shawarci wani ba, haka kawai kuka ga cancanta ta isa ta sa kuyi mana kyautar kud’inku, lallai kun cika mutanen kirki masu daraja a garemu da karamci, kayi a yaba ma kad’ai babban arzik’i ne, sai gashi a wasu grps d’in har da ware mu mu biyu kawai ni da kuma k’awata aminiyata *Sajida* kuka ce zaku mana kyauta saboda k’ok’arin da muke, tabbas zan iya kiran labarin *matar mutum* da gawurtaccen labarina kuma bakandamiyata, dan Allah ya k’ara d’aukaka ni ta dalilinshi, Allah nagode maka ina k’ara godiya a gareka, ba dubarata bace ba kuma wayona bace._

Yan *Nigeria* da kuka kawo wannan shawara ta yi mana kyauta, da kuma yan *Niger* da kuka goya musu baya Allah ubangiji ya saka muku da alkairi, duk da mun dakatar daku mun ce ku bari muyi littafi na kud’i ku siya, amma gaba da gaba kuka nuna mana kunyi niyya kuma ba zaku fasa ba, Allah ya saka muku da alkairinsa, Allah ya biyaku da aljanna ya yafe mana kurakurenmu.

         *Sajida* & *Samira*

         _(Kwate da Kwate)_😁

*Allamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *52*

Takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsuguno irin na maza yana lek’awa k’asa yace “Ryam.”

Yanda ya kira sunan na ta a tausashe yasa ta yin shiru ta sake lafewa, tayi niyya ba fa zata bishi ba saidai in da k’arfi zai d’auketa ya kai gidanshi, a hankali ya sake fad’in “Ryaaaam.”

Yanda yaja a d’in yasa ta saurin fad’in “Na’am.”

Cikin barkwanci yace “Ki fito kinji, ke ba mage ba, ke ba b’era ko kaza ba, ya zaki shige k’asan gado ki taushe min cikina, ko kina so ki ja min b’ari ne?”

Zazzaro ido tayi baki bud’e tana rarraba ido, muryarshi ce ta katse mata tunanin data tafi yi tana fatan Allah yasa dai kar Iya ta d’auka ma ciki ne da ita, kai ita yaushe ma ta d’auki cikin na shi? Haba haba ai abun kunyar sai yayi yawa, ita wallahi ba zata yarda tsohon nan ya mata ciki ba, shikenan sai a kalleta a kalli sheikh Abdul Waheed a ce ya kusanceta har ma ta samu ciki?

Haka kawai ta ji tausayin kan ta ya kamata sai ta fashe da kuka tana murza ido tare da gyara kwanciyarta, cikin sangarta da sakarci tace “Ni kawai ka tafi bana son ganinki kuma ba zan bika d’in ba.”

Sanyayyen numfashi ya sauke yana sakin murmushi ya zura mata hannunshi na dama yace “Na yarda ba zan tafi da ke ba, amma ki fito na ganki kinji, zan miki addu’a ne ki samu sauk’i.”

Shiru tayi tare da tuna ranar da suka wuni gidan shi nan yace zai mata addu’a, salon tashi addu’ar ba irin ta kowa ba ce, da sauri ta girgizz kai alamar a’a dan ba zata yarda ta had’a jiki da shi ba a gidan Iya, ai zata sha tsiya a wurin Iya har ranar da zata daina numfashi, saita d’auka ita ma jarababbarshi ce, mak’ale kafad’a tayi tace “Um um! Ni lafiya ta k’alau.”

D’an k’ankkance ido yayi yace “Kamar ya? Amma kuma aka ce baki da lafiya.”

Shiru tayi tana mutsu mutsu da bakinta, cike da gargad’i yace “Ryaaaam! K’arya ko? Bana hana ba?”

Shiru tayi tana kumburo baki ba tace komai ba, mik’ewa yayi yana fad’in “Shikenan bari na fad’awa Abba k’arya kike, sannan na bashi carbita ya zane min ke da kan shi.”

Wani marayan kuka ta saki a hankali tare da fad’in “To ai ba zan k’ara ba ko, kayi hak’uri.”

Kallon gadon yayi yana jin ina ma ba gidan da yake jin matsananciyar kunya bane, da cak zai d’aga gadon ya fito da ita su kalli juna, amma saiya d’aure fuska yace “Haka kike fad’a kullum amma ba kya dainawa, Innar Issa duk randa kika kaini bango a game da k’aryar nan wallahi zaki gane shayi ruwa ne.”

K’wafa taji yayi ya laluba aljihunshi ya aje mata d’aurin kud’i akan gadon tare da fita a d’akin, da sauri ta fito tana murnar bai tafi da ita ba, kwance ta sake yi akan gadon dan kar Abba ya dawo ya ganta ya wulak’anceta, jin alamun ta zauna abu yasa ta lalubawa ta jawo kud’in, d’auka tayi tana dariya ta jawo k’aramar jakarta ta sokasu a ciki.

D’akin Iya ta shiga tace mata “Ya kike jin jikin yanzu? In kinsan baki jin dad’i ki tashi muje asibiti.”

Mik’ewa tayi zaune tana yatsina fuska tace “Iya aman ma ai ya kwanta, ki bari na gani zuwa safe.”

Jinjina kai tayi tace “To shikenan, ni dama bana son k’aramin ciki a saba mishi da likitar nan, sai ya zama komai kaji sai ka je asibiti.”

A zabure ta kalleta tace “Iya waya fad’a miki ciki ne dani? Haba dan Allah bana son haka fa.”

Turo baki tayi ta juya kan ta, dak’uwa ta mata tace “Ubanki ne ya fad’a min, in bâ ciki ne da ke ba uban waye dake saka ki jin amai.”

Cike da tsiwa tace “To wai ke Iya dole komai sai dai ki zagi ubana ne, me yasa baki tab’a zagin Mama ba? Dan baki haifeshi bane, kuma ni ba abinda nake da.”

Juyawa Iya tayi zata fita tana fad’in “Ina zan tsaya fad’a dake ki ja min jafa’i, ina tab’aki a ce ni ce silar komai, can ki k’arata da jarabarki.”

Kallonta tayi har ta fita saidai ran ta a b’ace dan sosai ta ji haushin maganar wai tana da ciki, cikin sheikh? Tsoho wanda ya girme ma Abbanta? A tsiwace ta murgud’a baki tace “Allah ya rabani.”

                 *Washe gari*

Saida ta gama shirinta tsaf kawai ta zauna bakin gado ta d’auki wayarta ta danna masa kira. Suna tafe a nutse cikin mota zai fara biyawa wajen Hajia ya gaisheta su wuce ya d’aga kiran cike da farin cikin yau ita ta fara kiranshi, cike da karsashi yace _”Assalama alaiki.”_

Cikin yarinta ta amsa da _”Wa’alaika salam, ina kwana?”_

Kyab’e baki yayi yace _”Ban gan shi ba.”_

Kallon wayar tayi sai kuma tace _”Ya aiki, ya gajiya, ya gari, ya hak’uri, ya fama damu?”_

Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace _”Allah nake rok’a ya k’ara min hak’uri da juriyar iya tafiya dake, dan na lura Ryam d’ina tana son gayyato min ciwon da har yanzu ko Hajiarmu bata da.”_

Wata shak’iyiyar dariya tayi ta yan duniya tace _”Ni Maryama a wa? Da zan d’ora maka wannan ciwon?”_

Samun kanshi yayi da kalar dariyar da tayi kafin yace _”Ke mai mulki a zuciyar Abdul mana.”_

Waina idonta tayi tace _”Daina zolayata malam, ni dama na kiraka ne na fad’a maka ina so zan fara tafiya makaranta.”_

Wani dam! Ya ji gabanshi ya buga, makaranta ta me kuma? A nan zaman lafiya zata wani tsokano masa fitina, d’an girgiza kan shi yayi yace _”Wace irin makaranta kuma?”_

Turo baki tayi alamar bata so tambayar ba tace _”Amma fa kana da yara, kuma kasan tun jiya an koma makaranta.”_

A hankali ya fara sauke numfashi yana sauraren na ta bugun numfashin a kunnenshi, a sanyaye sosai kamar mai rad’a yace _”A’a Ryam, karki d’auko min abinda zai fi k’arfina dan Allah, ni ban yi maganar karatunki da iyayenki ba, bana so gaskiya, ki hak’ura kinji.”_

Mik’ewa tayi tsaye tana dafe k’ugu irin fa da gasken nan take tace _”Me? Baka so fa ka ce? Kasan matakin karatu na ne da za’a datse min shi ban shirya ba? Ina so na zana jarabawar bac shekara mai zuwa, dan Allah Abdul ka barni na tafi ka ji.”

Saurarenta yake tas yayi shiru abun shi, yanda ta fara maganar da zafi da farko sai ya bashi mamaki, amma a k’arshen nan da ta kashe murya tayi a sigar rarrashi ta kirashi da sunan da saka mi shi jin k’uruciya sai ya murmusa akan labb’enshi, tunani ya shiga yi ya barta ne ko kuma dai ta hak’ura, sanda aka yi aurensu da Hafsat ma tana tsaka da karatu kamar yanda shi ma yana tsaka da na shi karatun a Madina, yana tafiyarshi k’arasa karatunshi ita ma ta ci gaba da na ta a gidan Hajia, saidai inda matsalar take Hafsat da Mimi ba d’aya bane a halaye da yanayin zubin halitta kai har ma yanda yake jin su a zuciya, yana da yak’ini d’ari bisa d’ari Hafsat bata karya dokoki da sharud’an daya gindaya mata ba, amma Mimi? Wani iska ya feso yace “Ba zai yiwu ba gaskiya.”

Da sauri Mimi tace _”Yanzu duk magiyar da na maka ba zaka barni ba? Haba sheikh na Allah, haba ustaz haba Abban Humaira da Munzeer, haba an tsohon yan matanshi.”_

K’yalk’yalewa yayi da dariya yana fad’in _”Ryam, na ji to na ji.”_

Da zumud’i tace _”Yawwa ka amince?”_

A take yace _”A’a, yanzu ki fara fad’a min me ye burinki idan kin kammala karatun?”_

A sanyaye ta feso iska ta koma ta zauna tace _”Abdul.”_

A tausashe kamar zai k’urma ihu saboda yanda ta kirashi yace _”Na’am.”_

Cikin shagwab’a tace _”Kud’i na zasu k’are, ka kirani da wayarka.”_

K’it ta kashe kiran tana murmushi, shi ma dariya yayi yana maida mata kira da fad’in “Allah shirya min baiwar nan ta ka ta min sauk’in juyawa.”

Tana ganin kiran ta d’aga shi kuma yace _”To ina jinki.”_

A ladabce tace _”Ka ga dai idan na gama karatu ina so na samu babban aikin da zan siyawa Abbana gida, na siya mishi mota na siyawa Mama mota na had’ata da dreba, sannan na d’auki nauyin karatun su Yaseen a makarantar kud’i mai kyau ba kamar ni da nayi ta gwamnati ba, sannan na cika musu d’aki da kayan abinci da masu aiki a kewaye dasu, sannan duk shekara ina kaisu aikin hajd, shikenan.”_

Cikin farin cikin jin burinta ba wani mai tsanani bane yace _”To ke kuma baki da abunda kike son yi ma rayuwarki ne?”_

Sauke ajiyar zuciya tayi tace _”Ni kam ba wani babban abu na ke so ba, dama dai burina bai wuce na samu d’an yaro ba na aura, wanda zai dinga kai ni shan ice cream sannan duk shekara ya kai ni k’asar waje nayi yawon bud’a ido, sai kuma na dinga haihuwa duk bayan shekara  bakwai bakwai.”_

Dariya ya shiga shek’awa kamar yaron daya samu kallon kartoon d’in Tom and Jerry hannunshi rik’e da sweet, sakin baki tayi tana mamakin me ya bashi dariya haka? A marairaice ta sake fad’in _”Abdul in tafi ne? Lokaci na tafiya.”_

D’an tsagaitawa yayi da dariyar yace _”A’a Ryam, zamuyi magana a kan karatunki idan kin dawo gidana.”_

Kyab’e fuska tayi irin zatayi kuka tace _”Yanzu duk yanda na gamaka da Allah baka ji ba, ku fa malamaina magada Annabawa, ko bakuyi niyyar abu ba aka had’aku da Allah kuna yi, ka tuna da cewa Imam Malik har mata ya aura saboda kawai ta had’ashi da Allah, kuma ya zauna da ita da kyautatawa duk da baya sonta a zuciyarshi, amma kai…shikenan sheikh ba komai, ka nuna min ban da mahimmanci a wurinka da zaka iya yi min wannan alfarmar.”_

Sheikh ban da saurarenta da girmama lamarinta babu abinda yake yi, rik’e hab’a yayi a ranshi yace  “Oh Allah! Wai ka haifi mutum a shekaru amma ya ce da tsiya zai maka wayo.”

Cikin sakin murmushi yace _”Ya kike so na yi Ryam? Bana so ki je gaskiyar magana, amma tunda kika had’ani da Allah zan miki wani lamuni.”_

Gyara zama tayi da zumud’i tace _”Yawwa ina ji.”_

Sanyaya murya yayi yace _”Ki girka min abinda zan ci anjima.”_

Yatsina fuska tayi tace _”Girki kuma?”_

A hankali yace _”Um! Ko ba zakiyi  ba dan ki samu lada?”_

Da sauri tace _”Ni d’in me da zan ce ba zan yi ba? Zan yi mana.”_

Murmushi yayi yana hangen falon Hajia dan tun d’azu suka shigo kafin yace _”Da kyau yar albarka, Allah ya faranta miki yanda kika faranta min.”_

Wata dariya tayi tana nunashi da hannu kamar yana gabanta tace _”Abdul wannan addu’ar wallahi ta wayo dan kayi galaba a kai na, ba komai ka ci gaba da yi min yawo, wata rana zan rama ni ma.”_

Dariya yayi yana fitowa a motar yana me jin kamar ya zauna yayi ta hira da ita yace _”Ai kin rama tun jiya, ko kin manta na je bikonki kika min wayon baki da lafiya, haka na dawo ni da k’atuwar rigata.”_

Tintserewa tayi da dariya _”To wai idan na dawo yanzu me zan maka? Ga matarka nan da kake so da kuma ‘yarka da kuka shigar ma fad’a kuka min taron dangin, dan kunga bana da wanda zai shigar min ne ai.”_

Cikin murmushi yace _”Ryam ba na bayar da hak’uri ba? A yafe mana dan girman Allah mana.”_

D sauri tace _”Na yafe, wallahi na yafe tunda ka ce girman Allah.”_

Da jin dad’i yace _”Yawwa ko ke fa, ina sonki Ryam, na sumbaceki a bakinki.”_

Da baki sake tace _”Ta ya ya? Bayan ban ji sumbatar ba.”_

Dariya ya bushe da ita cikin tsokana yace _”Ke wata Mairama, ashe ma kina so na sumbaceki.”_

Rufe fuska tayi da kunya tace _”Ni bana so, kawai tambaya ce na yi.”_

K’it ta datse kiran tana dariyar jin kunya, shi ma soka wayar yayi aljihu yana girgiza kai da murmushi a fuskarshi yana shafa k’eyarshi, jami’an su dai da kallo suka bishi har ya shige falon suna mamakin wannan sabon shehi na su, su dai kam tun daga ranar da aka d’aura aurensu suke ganin bak’in abubuwa a tare da shi, kuma basu ga laifinshi ba tunda yarinya ya aura wacce ko su dake da k’uruciyar da baya da suka auri sa’arta zasuyi fiye da haka ma bare kuma shi.

A nutse yake zaune k’asa gaban Hajia yana d’an jujjuya kofin tangaren d’in data aje masa da zazzafen shayin na’a na’a a ciki, bayan sun gaisa ne Hajia ta numfasa cikin d’an fad’a fad’a da dattijuwar uwa kuma wacce take gaba dashi ta kalleshi a zafafe tace “A ce duk abubuwan nan na faruwa amma ni babu wanda zai iya fad’a min, ba ma wannan ba sheikh akan menene zaka zauna k’aramar yarinya ‘yar cikinka har tayi sanadiyar barin matarka d’akinta? A kan me?”

Kuma sunkuyar da kai yayi bai yi magana ba yana son bata damar fad’an abinda take son fad’a, d’orawa tayi da “Yanzu fa kwana biyu kenan, tunda Hafsat ta fad’a min tun shekaran jiya ta tafi, ni abunda ya ke k’ona min rai shi ne yanda ku ma dana haïfa kuka min biyayya kuka karb’i Mimi da hannu biyu, bare kuma ‘yar da kuka haifa a ce ita ce zata bamu matsala.”

Cikin ladabi da nutsuwa da girmamawa ya kuma sadda kan shi yace “Ayi hak’uri Hajia, insha’Allahu zamu gyara kurenmu.”

Kawar da kai tayi tace “Shikenan Allah yasa, amma ku sani ban ji dad’i ba, kuma nayi niyyar tafiya gidan na ci uwar Aishan a gabanku, in ya so na ga zaku rama mata ne kamar yanda kuka taru akan baiwar Allahr yarinya, wannan ma ai shirme ne sai kusa na ji kamar tusa muku ita ne nayi a dole kuke zaune da ita.”

Girgiza kai yayi ya d’an d’aga kai ya kalleta yace “A’a Hajiarmu, sam ba haka bane, mu kanmu iyayenta kun isa damu bare kuma ita.”

Sake d’auke kai tayi tana sauke numfashi da k’arfi, dan har ga Allah jarumta ce tayi wajen yi mishi fad’an nan, abu ne da bai tab’a faruwa ba a tare dasu, shiyasa ko da Hafsat ta fad’a mata a waya abinda ya faru tare da cewa ta rok’a mata gafararshi yasa ta yanke shawarar dole ta nuna masa ita ma kamar uwa ce a gareshi. Cikin sanyin murya kuma ta d’ora da fad’in “Sannan Hafsat ta ce tana mai baka hak’uri akan abinda tayi, ta fad’a min ita ce da laifi ba Mimi, ita ta fad’a mata magana mai zafi, sannan ta ce na fad’a maka a d’an zaman da sukayi babu wani abu mai sunan raini daya shiga tsakaninsu, Mimi yarinyar kirki ce kawai wannan ma shed’an ne ya shiga tsakaninsu, kayi hak’uri ka ji.”

Shi ma wani sanyayyen numfashi ya sauke yana lumshe ido lokaci d’aya kuma ya bud’e, kallon kofin hannunshi yayi yace “Ba komai Hajia na yafe mata, dama kuma ni babu abinda ta min, abinda na gani ne a ido ya min kama da za’a ci mutumcinta, ni kuma ba zan bari haka ta faru ba indai ba na daina numfashi bane, shiyasa na yi haka.”

Jinjina kai tayi cike da k’aunarshi tace “Mun gode Allah ya biya, kuma ni ma insha’Allah zan je na samu iyayen na ta na sake basu hak’uri, dan kuwa ni ce nan na karb’a maka aurenta, dole wasu abubuwan su rataya a wuyana, kamar yanda idan kuka cuta mata to ni kuka ci amana.”

K’anshi sadde kasa yace “Insha’Allahu ma haka ba zata sake faruwa ba Hajiarmu, amma kuma…”

Da kulawa ta kalleshi tace “Amma me?”

Cikin jin kunya yace “Bata gidansu tana wajen kakaninta, ina ga kamar bata san komawa ne ita ma shiyasa da muka tafi jiya tace bata da lafiya.”

Dariya Hajia tayi tace “Allah sarki Mimi, ina k’aunar yarinyar wallahi, ai ko ni ce ita zanyi abinda ta yi, dole ta tsorata daku ta ga baku da adalci a rayuwarku.”

Rufe ido yayi sai kuma yayi saurin d’aga kan shi yace “Hajia ki je ki bata hak…”

Shiru yayi dan ya tuna zai yi kwafsi fa a gaban suruka kuma uwar ta shi, murmushi Hajia tayi tana girgiza kai tace “Ba damuwa zan je na bata hak’uri, sannan na fad’a mata ba haka kake ba akasi ne aka samu yanzu ma, amma kai ma abinda nake so da kai shi ne ka bita a hankali kana lallab’ata har ta koma, kaga fa haka kawai sai kirana kayi a waya ka ce min ta tare a gidanta, na tabbata bata ji dad’in haka ba, to bana so yanzu ma tayi yaji a tilasta mata dawowa.”

Yar dariya yayi yana jin wata kunya na rufeshi tare da tuna washe garin ranar daya angwnce ya kira yace ai ta tare gidanta, k’eyarshi ya shafa yana mai d’an turo hularshi a gaba yana sissine kai. Murmushi t sake yi tace “Shikenan Allah yayi albarka, Allah ya baku zaman lafiya da hak’urin zama da juna, ka tashi ka tafi lokaci na wucewa.”

Da ladabi yace “Ameen Hajiarmu, nagode Allah k’ara lafiya.”

Mik’ewa yayi suka sake sallama ya fita yana mai godiya ga Allah da yasa yau akwai wanda zai iya zaunawa gabanshi kanshi k’asa ya masa fad’a, lallai wannan ma babbar ni’ima ce a gareshi ace akwai mai fad’a maka ka ji.

Yana daf da shiga mota motar Asas ta danno hancinta cikin gidan, shiga yayi suka saita na su motocin zuwa k’ofar fita, tsayawa sukayi inda Asas ya tszya a daidai da motar sheikh, sauke glas duk sukayi suka kalli juna, dukansu mamakin yanda zumuncinsu ke neman ja baya sukeyi saboda mata, tunda akayi aurensu ta waya dai babu wanda ya nemi wani, Asas bai sake zuwa gidan shi ba har yau, hakan duk saboda abinda ya faru ne?

Murmushi Asas yayi cike da kunya yace “Sheikh barka.”

Lumshe ido yayi alamar amsawa, cike da zolaya yace “Gashi kuma ganinka na zo kai zaka fita, tunda na ga yanzu amarci yasa ka manta da d’an uwanka.”

Harara ya watsa mishi yace “Tunda kasan inda nake ka sameni a can.”

D’aga gilashinshi yayi ya ma dreban umarni da su tafi, dariya Asas yayi yace “Zan zo har gidan na sameka.”

K’arasawa yayi shi ma su kuma suka fice a gidan zuwa wurin aiki.

                  *10:46*

*Alhamdulillah*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *