MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 14
Yana zuwa unguwar ya ganta a k’ofar gida a zaune tayi wanka tayi kwalliya irinta zamani lokacin ba’a gama sanin su concealer ba, amma tasa eyeshado red janbaki tayi kuma jagira tana ganin mota a k’ofar gidan su ta shek’a da gudu tana gayawa su Inna yazo kafin ta kuma fita kamar wata saban kamu lokacin harya Fito yana rik’e da murfin ya kalleta itama ta kallesa. Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda getzner light blue anyi mata dinki na dark blue ya d’ora hula fuskarsa har wani kyali-kyali takeyi kawai INdo ta saki baki da hanci tana kallansa kallo na kurrullah tamkar tana son ganin wani abu ya mik’a hannunsa yana zagaya shi a saitin fuskarta tayi firgigit tare da yin dariya tace.
“Dacta Habubakar wallahi kanada kyau ai heyau na taba ganin haka.” Murmushi yayi tare da rufe k’ofar ga yara sun fara mai dandazo ya ciro 2k yabasu sannan ya shiga zauran gidan su ta bishi ya tsaya yana kallonta ganin tayi mai wankan dayace tayi harda kwalliya sai yace.”Humaira babu gaisuwa? Bakifa gaida niba.” INdo tace “Au hakane fa ina yini ya gida ya iyaye..?!””Laflya lau baki tambaye ni malam Sadeeq ba why..?!”
Tace tab narasa wanda zan tambaya hewani malam Sadeeq Allah ya tsare ni wallahi.” Kyaleta yayi ganin bilhakk’i bata son Sadeeq tun lokacin daya hanata atamfa, kallonta yayi yace. “Ina baba yake?” Tace “Baya nan.” ‘ Abubakar yace “Toh Inna fa?” INdo tace “tana ciki.”
“Toh jekiki ce zanzo mu gaisa da ita.” Kai dacta Habubakar, kawai kashiga meye na tsayawa ai bazata hanaka ba.” “A‘a Humaira ba’ayin haka a musulinci dole sai kinje kin gaya mata.”Toh hikenan tunda baka yadda dani ba.” Tana magana tana shiga gida, yana jiyo sanda take gayawa Inna sak‘on duk maganar da sukeyi yana jiyo su. “Kai Inna toh meye na saka hijjabi dan nace miki dacta habubakar zai shigo. Lallai saban salo.” Rintsa ido yayi jin yadda INdon keyin magana da mahaiflyarta, lallai yarinyar nan indai yana sonta yadda yake so toh akwai jan aiki a gabansa. Dawowarta kawai ya gani beji motsinta ba, tana dariya tare da wasa da gefen mayafinta tace. “Tace ka higo an hinfid‘a maka tabarma a k’ofar d‘aki.” Tana gaba yana bayanta har suka k’arasa ya zauna, daga bakin k’ofar d‘akin lnna ta tsuguna suka fara gaisawa. Shiru babu wanda ya sake magana sai gasu Nafeesa sun shigo
itada k‘awarta suka gaidashi, Abubakar yace ma Inna. “Inna dan Allah idan babu damuwa ina son ki bani aron su Humaira suyi min rakiya nan cikin gari.” Shiru yaji Inna tayi kafin can kuma yaji tace. “Toh gata nan ai Nafeesah sai tazo kuje tare harda ita.” “Toh Inna na gode.”
Tashi yayi yafita su kuma suka bi bayansa. A baya Nafeesa ta zauna yayin daya kwashe ledojin kayan yasa a k’asa wajan dazata saka k’afa yace ta shiga ta zauna sannan shima ya zagaya drive seat ya zauna tare da tayar da motar suka tafi ‘yan kauyan sai gulmarsu akeyi. Cikin garin Sumaila suka shiga INdo badai surutu ba sai labari takeyi musu sanyin A.c yana ratsata ga k’amshi a cikin motarta kalli Abubakar tace. “Dacta Habubakar wannan motartaka akwai sanyi karmuyi mura a bud’e gilahin.” Dariya yayi sannan ya mik‘a hannu ya rage A.c ya juya yana kallanta itama shi take kallo yace. Humaira ya akayi ne?!” lNdo tayi dariya tana tafa hannuwa tace. “Meye kuwa, wai Ina zaka kaimu ne hefanan Tafiya muke..?”
Paking yayi a bakin titi wajan wani shagon saloon ya kalleta yaga sai kallon window take ya juya bayansa Nafeesa sai bacci take a hankali ya mik’a hannu zai taba kafad’un lNdo sai kuma yayi saurin janyewa tare da bud’e k‘ofar yafita. Zagayawa yayi ya bud’e mata ta fito yace su shiga cikin shagon abar Nafeesah tunda tana bacci suka nufi shagon ya tsaya ta glass inyamurar ta hango su ta fito cikin azama. “Hey!good evening sir how are you.?!” “Fine madam how is your business.” “Fine..fine oooh.”
lNdo tabisu da kallo sai faman tabe baki takeyi ta samu sumintin gurin ta zauna tana kallon titi. Saida Abubakar ya gama gayawa madam Gloria abinda za’ayiwa INdo sannan ya kalleta yace.
“Yauwa toh Humaira tashi ku shiga ciki.” INdo ta kalli madam gloria cikin mamaki ta maida kallonta gurin Abubakar tace.”Mezai kaini wajan arniya dacta Habubakar? Arniya cefa kake cewa naje gurinta, me zata min.. Ganin yadda takeyi ne yasa hankalin Abubakar tashi har mutane sun fara taruwa da k’yar ya satayi shiru yace mata. “Kayanki zata baki amma tunda bakya so zomu tafi gida.”Da sauri ta nufl madam guloriya tana cemai. “Yo toh ai kaine bakayi min bayani ba.”Gloria na gaba tana bin bayanta Abubakar ya girgiza kai sannan ya koma wajan mota yana jiran fitowar Gloria .INdo kuwa suna shiga gurin taga abubuwa birjic ga manyan madubai ta kalli fuskarta sosai sannan ta fara gyara kwallin daya zazzago mata wajan kumatu yarinyar Gloria ta cewa lNdo. “Sister come and seat here.” Sam INdo batasan da ita ake ba Tese Gloria ta kuma yi mata magana still INdo bata juyo ba Tese taja tsaki tare da zuwa ta janyo hannun lNdo tare da zaunar da ita a wajan wankin kan sai masifa take da turanci ita kuma INdo tana Hausa. ‘ Cige d’ankwalin Tese tayi taja wani uban tsaki ganin ko tsefewa batayi ba, gashi Mommy d’inta tace tabita a hankali dan wanda ya kawota yace zata iya guduwa. Kibiya tad’auka ta tsefe mata gashi akwai laushi da tsayi saidai babu cika gashi kuma jah ne. Mayukan wanke gashi ta d’ebo sannan ta janyo kan INdo ta malala mata sai mita takeyi har aka gama Madam guloriya ta kuma shigowa hannunta d’auke da riga da takalmi wanda Abubakar ya bata yace abata tasa ayi mata kwalliya. Lokacin da aka saka kan INdo a dryer taji zafl sai ta saki wani uban ihu wai zafi, Madam Gloria tazo tana d’anyi mata wasa tare da takura mata har aka gama kannan yayi kyau gashi an tura mata shi yayi baki Tese ta nuna mata bathroom a shagwan ta nuna mata tace tayi wanka, INdo tayi da sabulai masu k’amshi gashi ruwan d’umi sannan ta fito sanye da kayan data cire babu wanda ya kulata Tese tayi mata kwalliya sannan aka bata doguwar rigar suka ce ta saka. Duk bayanin da sukeyi mata toh da hannun suke nuna mata tamkar wasu bebaye. Wata irin had’add’iyar abaya ce pink da belt black sai kwalliyan ma black ta jikin rigan, Fitowa tayi daga d’akin bayan tasa saidai jikinta babu bra madam Gloria ta tambaye ta bayan ta nuna mata tajikinta kasan cewar itama INdo akwa breast d’in ta turo baki tana k‘unk‘uni da alamar dai batada ita. Babu kunya madam Gloria tafita wajan Abubakar yana zaune suna hira da Nafeesa tace k’anwarsa batada bra amma suna siyarwa ya bada kud’in. Abubakar kunya ta lullueesa yace toh abata zai had’a a cikin kud’in gyara sannan ta koma aka cire dai-dai size d’inta ta saka suka d’aure mata belt d’in sai ta koma tamkar ba wadda ta shigo d’azu ba. Tese ta sa
mata veil bayan ta jera mata ribbon INdo tayi d’as da ita tamkar ba INdo malam Hamza ba. “Wowww nawawoo see this girl coach, you look so beautiful my daughter.”
Ita kanta INdo data kalleta a cikin madubi saida ta sake taba fuskarta dan a tunaninta ba ita bace, Madam Gloria ta fesa mata turaruka sannan ta kamo hannunta suka fito Tese sai dariya takeyi. Abubakar na ganin sun fito ya mik’e yana kallon lNdo k’irjinsa na mugun bugawa, ita kuma ta kasa kallonsa domin wata irin kunya ce da nauyinsa suka dirar mata a lokaci d’aya. Da kyar Abubakar ya iya kallon madam Gloria yayi mata godiya tare da zaro 15k ya mik’a mata ta k’arba sai k’ara kod’a INdo takeyi shi kuma yajuya tare da bud’e mata k’ofa ta shiga ta zauna ya rufe. Cikin tsananin mamaki Nafeesa ke zuro kai tana lek’en fuskarta kafln tace.iNdo..Koba kebace ne? Nashiga uku, wallahi kece dan ga fashin gohinki nan.”
Banza da Nafeesa INdo tayi domin ita kanta tunda aka haifeta bata tabajin ta a wani irin yanayi na cikar kamala ba irin yanzu. Abubakar ya kalleta yana lek’en fuskarta shima yayi murmushi tare da cewa. ‘ “Humairah kinyi kyau sosai.”
K’irjin INdo ya kuma bugawa kanta ya fara sarawa jitakeyi tamkar an sauyata gabaki d’aya, bakinta kuwa ji takeyi tamkar ansa zare da allura an d‘inkeshi ta kasa cewa ko uffan ta kuma kasa kallonshi. Kunna motar yayi suka fara Tafiya sai magana suke mata shida Nafeesa amma tayi shiru, farin ciki takeyi yau gata cikin rigar da ko a cikin mafarki bata taba zaton zata sanya taba ga takalmi d’an ubansu tayi shigarda duk kauyen Sani babu wanda ya tabayin irinta. Shin mezata cewa dacta habubakar akan wannan abun dayayi mata, shida ba yayanta ba, ba wani nata ba a’a d’an uwane a gurin wani malamin su..Saida ya tsaya a wani shago ya siyo musu abubuwan kwalan da makulashe sannan ya nufi kauyen Sani. Daga shi sai Nafeesa kawai suke magana amma ita batayi rigarjikinta kawai take kallo tanajin ina ma salele zaizo yau ya ganta ta zama sabuwa. ‘ A k’ofar gida ya tsaya Nafeesa ta fito ya bata ledojin INdo ma tazo zata k’arba ya girgiza mata kai sai da Nafeesa ta dawo ya bsta harda ragowar kayanta sannan ya kalleta yace. “Humaira kina son yin karatu..?!”
Shiru tayi tana faman muzurai, a zahirin gaskiya batada wani sha’awar yin karatu domin tun farko dama batasa shi a cikin tsarin rayuwartaba. Gani takeyi ma yanzu wace makarantar zatayi dan tafi k’arfin tsefawa sabida duk mate d’inta sunyi candy dan haka ma ta kuma cire san makaranta a zuciyarta. Kallonta yayi yaga yanayinta ya canza ya ciro wayarsa yana yi mata photo wannan kuwa harda su style, ya d’an matsa kusa da kujerarta tare da cewa. “Matso toh muyi photon tare.”
INdo ta matsa suka kusan had’e fuska yayi musu selfle kusan sau biyar yana d’aukar su gaba d’aya sunyi kyau musamman Abubakar dayasan shika-shikan iya selfe. Agogon tsintsiyar hannunsa ya kalla biyar sauran minti uku yace mata. “Humairah zan tafl sai na dawo please take care.”
Murmushi kawai tayi mai sabida bata san abinda ya fad’a ba bayaga (zan tafi sai na dawo). Ya zaro 5k ya mik’a mata tana kallonsu ta wutsiyar ido tana son k’arba tana jin wani iri ya d‘ora mata a kan cinyarta ta d‘auka zata bud’e k’ofar yayi saurin rufewa tare da cewa. “Humairah baki min godiya bafa zaki tafi haka akeyi daman.” Tayi saurin rufe idanu tare da cewa. “Kayi hakuri inata son yima na manta, ne angode Allah ya k’ara bud‘i.”
Yace “yauwa kokefa harnaji dad’i, duk wanda yayi miki kyauta ki dinga ce mai angode kinji k0?!” Tace “Toh zanyi sai anjima yaushe zaka dawo garin mu?!”
Da sauri ya kuma kallonta jin tana neman ya dawo, cikin wata irin murya yace. “Humairah kina son na kuma dawowa?!“
INdo ta d’aga kai alamar eh yayi murmushin jin dad’i sannan yace. “Toh shikenan wani satin zan dawo amma ki dinga kwalliya gashi can na siyo miki kayan kinji..?”Toh Nagode ka kaida gida.”
“Zasuji amma bakice nagaida malamin kuba.” Tace tana yatsina fuska. “Ai bayida kirki da kaine bakada kirki amma yanzu shine bashida kirki.” “Toh kiyi hakuri ya dena kinga ‘dan biyu nane.” Naji na dena kace ina gaidahi.” Zaiji a gaiheda Inna da baba.” Yafad’a cikin kwaikwayon maganarsu, ta fita daga motar lokacin su Uwani halilu sunzo gulma, shi kuma yaja motarsa yabar unguwar zuciyarsa na kudurta mai son auranta.