NIDA YAYA HABEEB COMPLETE

 NIDA YAYA HABEEB COMPLETE

Yarinya ce 'yar kamani _16-17yrs_ tana tafiya a hankali hannuta rik'e da _food flask_ tana sanye da atamfar _novou_ blue da touch's d'in yellow da hijab _yellow colour_ kaitsaye ta doshi wani shagon d'inki mai suna ```Ni da yaya Habeeb Teilorings center``` 
tana shiga shagon yanayi annuri fuskarta ya d'auke chak, kamar anyi ruwan sama an d'auke tayi tsaye tana k'arewa samari hudu da ke ciki shagon kallo yayin da idanu ta suka ciko da kwalla cikin zafin rai tanufi wurin saurayin da ke _facing_ d'in k'ofar shigowa shagon tadire masa _food flask_ cikin sark'ewa murya tace yaya salman ga abinci na kawo maka Wanda aka kira da suna salman sai lokacin yad'ago tsanani kamanu shi da yarinyar suka baiyana, fuskarsa a murtuk'e alamu babu wasa a tare da shi yace don gidanku kin saba kawo min abinci ne"?
Da sauri d'aya daga cikin samarin Wanda ke zauna daf da wata kyakyawa budurwa tana nuna masa _styles_ d'in d'iki a wayarta tun lokacin da yarinyar tashigo shagon ya sada kai k'asa alamu rashin gaskiya ya tari numfashi sa ta hanyar cewa haba salman miye haka"?
Tsoki yaya salman ya ja cike da jin haushi, yace wallahi Habeeb ina tausaya maka yarinya k'arama tana juya ka kamar waina a tanda sai an waye gari ta Kore maka _customers_ tass sannan za ka yi hankali in ka aure ta naga da uban da za ka ciyar da ita, ke kuma me kike jira ne"?
maza ki koma gida kuma duk ranar da na k'ara gani k'afar ki a shagonan sai na balla ki wannan wace irin fitina ce sai kace akanku aka fara soyayya ina lissafi a sati nan ak'alan Haleesa ta Kore mana _customers_ sun fi 10 za ki fita ko sai na taso na falla miki mari"?
Da gudu ta fice  daga shagon tana kuka ta nufi gida.

A fusace yaya Habeeb yace banaso abunda kake yi min salman, ka fi kowa sani duk fad'i duniya ba abinda na tsana irin bacin rai _baby love_ amma shine don tsabar wulaqanci had'e da musgunawa zuciyata kayi mata Koran kare.
Salman ya galla masa harara cike da jin haushi yace wallahi Sa'a kayi da banyi mata dukan tsiya in yaso gaba d'aya zuciyar taka ta tarwatsi har yaya salman yadasa aya yaya Habeeb yana watsa masa mugun kallo mai cike da jin haushi, daga bisani yaja dogon tsoki yanufi k'ofar fita daga shagon da sauri kyakyawar burduwa tace Habeeb ya za'ayi katafi batare da mun gama magana ba"?
Harara ya galla mata yace ke har kina tsanmani ina da kwanciyar hankali da za ki yi magana da ni"?
Ga salman nan ki yi masa bayani d'ikinki in nadawo ya sanarda ni yana k'arasa magana yasa kai yafita, yaya salman ya ja tsoki had'e da cewa shege namamajo yayin da raguwa samari da ke shagon suka kyalkyale da dariya shak'iyanci.
Gudu takeyi tana kuka mutane da ke wuce sai kallota sukeyi, wanda suka santa kuwa sai tambayar ta sukeyi Haleesa lafiya kike kuka"?
Amma ko kallon basu eshe ta ba muradinta taga ta kai gida, tana shiga zaure gidansu taci karo da katuwar akuya Ammi ta korota saura kiris ta bangaje ta daka tsalle a gefe d'aya akuyar na ficewa ita kuma ta danna kai  Ammi na tsaye da bulala rik'e da hannuta da alama da bulala tayi amfani ta kori akuyar, tana shiga tsakiyar gida ta cire takalmi ta had'e da hijab ta jefar ae kuwa sai bisa tukunya ruwa hijab d'in yafad'a tasaki kuka mai matuk'ar sautin gaske ta shige d'akin Ammi ta fad'a bisa gadonta na _silver_ tayi rub da ciki tana shasshekar kuka kamar raita zai fita.

A tsorance Ammi tashigo d'akin ta daka mata tsawa ta hanyar cewa ke lafiya kika shigo mini gida kina wannan taratsi na fitar hankali"?
Batare da ta juya ta kalli Ammi ba cikin dasashiyar murya tace Ammi yaya Habeeb nagani tare da wata a shago suna fira, Ammi bakiji irin zafin da nakeji a zuciyata duk lokacin da naga yaya Habeeb yara6i wata 'ya mace jin nakeyi kamar zan yi hauka kum.....kee! Ammi ta daka mata mahaukaciya tsawa da tayi sanadiya
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *