RAUDHA CHAPTER 4
Iska yafesar ta cikin bakin sa kafin yace “Nasan tana sha ai”.
+
Baki sake Farida take kallon sa, cike da tsantsan mamakin sa tace “kana nufin kana sane tana wannan rayuwan but bakayi komi akai ba?”
Zuwa yanzu damuwa ne sosai yanuna a face ɗin nasa, cikin rashin jin daɗin halin da ƙanwar nasa take ciki yace “Ni kaina bana jindaɗin halin da Baby take ciki amma bansan ya zan yi ba, na rarrashe ta na faɗa mata illan hakan but taƙi ji”.
Ido Farida tazuba masa ta kasa cewa komi, mamaki al’ajabi duk ya cika mata zuciya, bata taɓa tunanin soyayyan da suke mata zai saka su bar ta tana irin wannan rayuwan ba, a matsayin ta na ɗiya mace ma ba na miji ba
“Lallai kam akwai aiki”. Tafaɗa a ranta kafin a fili tace
“Wannan wani irin so kake mata da har zaka kai ta ga halaka?”
Tsare ta da idanu yayi cikin rashin fahimta yace “me kike nufi Wifey?”
“Ina nufin taya zaka bar RAUDHA tana shaye-shaye but ka kasa hana ta? Kana tunanin halin da zata shiga nan gaba? Meyasa soyayyar ta zai rinjaye ka kakasa ɗaukan mataki akanta? Idan baka sani ba wannan ba soyayya bane Husband, idan har baza ka hana ta wannan ɗabi’an ba tabbas nan gaba zaka yi nadama”.
Suhaib yace “ya kike so in yi My Wife? Kar ki manta bazan iya ko ɗaga yatsa bane akan ta, Ni na rasa ta yanda zanyi in hana Baby Shan kayan maye, ko kaɗan bana son ɓacin ranta..”
“Wannan ba hujja bane Sweetheart, tabbas idan har zaka ga tana aikata saɓon Allah kabar ta to wlh baka son ta sannan baka ƙaunar ta, kuma wlh sai Allah ya tambaye ka idan har baka taimaki rayuwan ta ba tunda har da kwamashon ka cikin gurɓacewar tarbiyyar ta”. Taƙarike maganar ta tana ƙoƙarin miƙe wa
Ruƙo hannun ta yayi yana mayar da ita yace “ina zaki je kuma? Don Allah ki zauna ki bani shawara bansan ya zanyi ba, Ni kaina nasan ina da laifi, but ke kanki kinsan halin Baby, hakan zai iya kawo babban matsala a tsakanin mu, sannan bansan ma taya zan iya ɗaukan mataki akanta ba”.
Izuwa yanzu haushi sosai yake bata, duk da tasan girman soyayyan da suke mata shi da Daddy amma hakan ba yana nufin baza su iya mata faɗa ba don kawai kar ranta yaɓa ci..
“Kinyi shiru my Wife? Taya kike ganin zan ɓullo ma al’amarin?”
Ajiyan zuciya tasauke kafin tace “dole ka ajiye soyayyan ta agefe kafaɗa mata gaskiya, idan takama ma har hukunta ta kayi idan har hakan zai saka tadena..”
Dariya Suhaib yasaki hakan yasa Farida tatsayar da maganar ta tana bin sa da idanu
“Wai kina tunanin Baby zan hukunta? Ni ɗin?”
Sai kuma yasake kecewa da dariya
Ita kuwa wannan karon kallon sa take yi cike da tsantsan tausayin sa, tabbas soyayyar RAUDHA ya rigada yayi tasirin da baza su taɓa koda ɗaga yatsa akanta ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwa da farin cikin su ne
Kanta tajinjina kafin tace “to Allah yakyauta tunda baza ka iya ba”.
Sai tajanye hannun ta kawai tamiƙe tafice a ɗakin
Shima be sake dakatar da ita ba yaci gaba da aikin sa, be jima ba yajanye Lapton ɗin yana miƙe wa tsaye, miƙa yayi yana yarfe hannayen sa, sai da yaɗan jujjuya jikin sa yanda zai saki kafin yanufi ƙofa yafice
Akan kujera yatarda ita zaune
“My wife taso muje muyi dinner yunwa nake ji, Ina Baby bata fito bane?”
Yaƙarike maganar yana kallon saman, kafin kuma yamayar da idanun sa kan Faridan da a yanzu take ƙoƙarin tashi, zuwa wajen ta yayi yataimaka mata tatashi
“Bata fito ba”. Taba shi amsa tana yin gaba abin ta
Juyawa yayi yanufi upstairs ɗin don kiran ta
Ita kuma Farida kan dainning tanufa taja kujera tazauna, sannan tabuɗe abincin tana zuba wa a plate iya wanda zata ci
Kamar minti 5 da hawan sa sai ga su sun sauko, tana manne da jikin sa sai mishi shagwaɓa take yi shi kuma yana mata dariya
Idanun Farida na kansu har suka ƙariso, zama suka yi Suhaib ɗin yasoma saving ɗin su shi da ita
Tun da suka soma cin abincin babu wanda yayi magana
RAUDHA tasoma tashi bayan ta ture Plate ɗin
“Aaah Baby har kin gama?” Suhaib yafaɗa idanun sa akanta yana taunan abinci
Gyaɗa masa kai tayi tana langaɓe kai
“Ok Nima na ƙoshi jira Ni muje”.
Tashi yayi yariƙe mata hannu suka nufi cikin parlour’n
Ido kawai Farida tasanya musu ta ma rasa tunanin da zata yi, janye idanun ta tayi taci gaba da cin abincin ta har sanda tagama sannan takoma cikin parlour’n
Hira suke yi don haka itama tadunga saka musu baki.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
A cikin sati biyu da zuwan RAUDHA gidan har Suhaib ya gama mata komi na school ɗin ta, yau ce ranan da zata fara zuwa don haka tatashi da wuri cike da ɗoki, dama ita akwai ta da son karatu sosai
Ta gama shirin ta cikin farar riga me taushi sosai, rigan dogon hannu yake dashi kuma irin me wuyan nan ne dogo, sai tayi stocking ɗin rigan cikin blue pencil Jeans ɗin ta, tasaka Belt baƙi me ƙyalƙyali, Combat tasaka a ƙafafun ta baƙi sannan ta tsaga gashin kanta tasanya Ribom biyu kalan blue, yau har da saka Wrest watch a hannun ta fari, sosai tayi kyau kamar wata baby doll sai tashin ƙamshi take yi, haka taɗau HangBag ɗin ta tafito tana zuba murmushi
Tunda Suhaib yahango ta yake faman zuba murmushi, abinci yake ci but sai ya’ajiye spoon ɗin yana faɗin
“Wow my dear Baby kinyi kyau”.
“Thanks Yayana”. Tafaɗa tana murmusawa har haƙoran ta suna bayyana
Farida dake zaune gefen Suhaib ɗin akan dainning ita dai kallon RAUDHAN take yi cike da mamaki, sai dai bata iya cewa komi ba tana jiran taji me Suhaib ɗin zai ce game da shigan ta
Zuwa tayi taja kujera tana kallon Farida
Hakan yasa Faridan sakin murmushi tana cewa “baby kinyi kyau”.
Cike da jindaɗi RAUDHA tace mata “tnz Aunty”.
Suhaib yace “Baby gan ɗoki baza ki yafa ko mayafi bane a kan ki?”
Ɓata fuska tayi tana kallon sa tace “Ni bazan saka ba”.
Miƙe wa yayi be sake bi ta maganan ba, sai peck da yayi mata a goshin ta sannan yayi ma Farida yay musu sallama yafice
Farida tana so tayi mata magana amma kuma tana jin tsoro, daga ƙarshe dai tayanke shawaran yin mata maganan, ɗago kai tayi tana kallon RAUDHAN dake sipping coffee tace
“Ƙanwata meyasaka zaki yi wannan shigan bayan fita zaki yi?”
Cakk RAUDHA tatsai da shan Coffee ɗin tana kallon Farida, sannan takuma maida idanun ta jikin ta tana kallon abinda Faridan tagani har ta’iya mata magana, bata ga komi ba hakan yasa taɗago kai tana kallon ta, sai dai bata iya cewa komi ba illa zuba mata shanyayyun idanunta da tayi
Murmushin yaƙe Farida tayi tace “naga baki rufe gashin ki bane kamar yanda Yayanki yafaɗa”.
Taɓe baki RAUDHA tayi tana miƙe wa
“Ban buƙata ne”. Tafaɗa tana yin gaba
Kallon ta kawai take yi har tafice, sai tasaki ajiyan zuciya tana faɗin “Allah ya kyauta to”.
Fitan RAUDHA parcking lot tanufa tashiga motan ta da Daddy yasake mata, tunda har dashi duk aka ɗauko mata, jan motan tayi tay bakin Gate tana buga horn
Jiki na rawa Gate man yabuɗe mata tafice da gudun gangancin ta
Bata zarce ko ina ba sai makarantan su, bayan tayi parcking sai da taɗau lokaci kafin tafito cikin motan sannan tarufe, tasoma tafiya cikin tafiyan ta me nutsuwa tamkar baza ta taka ƙasa ba
Dayike school ɗin haɗuwan mutane daban-daban ne kuma ƙabila iri-iri don haka shigan RAUDHA be zama baƙo agare su ba, sai dai hakan be hana idanun mutane sauka kanta ba sabida haɗuwan ta, duk inda tabi ana kallon ta
Ta rigada tasan department ɗin su tunda ranan ƙarshe da Suhaib zai zo ya kammala mata duk registration ɗin ta da ita suka taho, kuma duk ya nuna mata wajaje da dama a school ɗin
English double major zata karanta don haka can department ɗin tanufa.
Holl ɗin da zasu yi karatu ta dosa tashige
+
Babu wasu ɗalibai sosai aciki kasancewar safiya ne kuma sabbin zuwa ne, gashi time be yi ba
Can ƙarshen kujeru tanufa tazauna batare da ta kalli kowa cikin holl ɗin ba, tana nan zaune tana latsa wayan ta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, mutane sukai tashigo wa da ɗai-ɗai har suka yi rabin ajin wanda ga duk kan alamu yawan nasu bazai fi hakan ba
Can kuma Malamin da zai ɗauke su lecture yashigo, suka gaishe shi ya’amsa da fara’a
Da fari Barka da zuwa yasoma yin musu a matsayin su na sabbin ɗalibai, sannan yaɗaura da ɗan guntun nasihan sa kafin yasoma gabatar musu da sunansa da kuma lecturen da zai musu
RAUDHA na zaune har a lokacin kamar yanda take, sai dai yanzu ta ɗauko Tap ɗin ta wanda Suhaib yasiya mata tana yin jotting a ciki, bata kallon malamin amma duk abinda yake faɗa tana ji kuma tana rubuta abinda zata ƙaru aciki.
Bayan ya gama sai yatambaye su idan da me tambaya yayi masa, kun san sabbin ɗalibai akwai su da tsoro sai idan sun saba, don haka kowa yanoƙe yaƙi ɗaga hannu duk da kuwa wasun su suna da tambaya
RAUDHA da sai yanzu taɗago kanta takalli Malamin da mutanen ciki taɗaga hannun ta batare da ta furta komi ba
Malamin da idanun sa yasauka kanta yabata daman tambayan
Don haka kowa yajuyo yazuba mata idanu ana kallon ta, wasu ma sai lokacin suka ganta, wasu kuma basu yi zaton ƴar ajin bane duba da yanda taje can baya nesa dasu ta keɓe kanta
Tambaya tasoma jero masa yana bata amsa
Abun har sai da yaba ɗalibai mamaki, ganin yanda take ta zubo tambayoyi cikin daddaɗan muryan ta me sanyi
Shi kuwa Malamin sai amsa mata yake yi, don har shi ta burge shi, shi a rayuwa yana son ɗalibi me yawan tambaya akan karatu, hakan na saka wa ɗalibi yay saurin fahimta tunda bashi da tsoron tambayan Malami
Ita kuma RAUDHA dama halin ta ne tambaya a aji, ka mun kaga ta ɗaga hannu da sunan ba ma malami amsa to sai dai shi yatashe ta, amma duk tambayan da malami zai yi a aji koda ta sani baza ta tashi ta faɗa ba, but da zaran ya ba da daman tambayar sa to anan ne zatai ta jero mishi tambayoyi kaf abinda take so tasani, kuma baza ta taɓa ko jin kunya ko tayi tunanin shi malamin zai yi tunanin tana son ƙure sa ne ba, ko ya kai ashirin ne tambayoyin ta sai tayi maka, sai dai kai kace ya isa haka nan
Shiyasa sanda tayi secondary school babu malamin da be san ta ba har CE mata suke yi sarkin tambaya.
Questions biyar tatambaye sa kuma duk ya amsa mata
Shirun da tayi yatabbatar ma Malamin ta gama don haka sai yatambaye ta sunan ta
Taba shi amsa da *”RAUDHA ElMUSTAPHA MAKAMASHI”.*
Jinjina kansa yayi kafin yace “That’s good RAUDHA, da fatan dai kin fahimci duk tambayoyin naki ko?”
Tagyaɗa masa kai
Murmushi kaɗai yayi mata yakalli ƴan ajin da suke mamakin ta jin sunan musulmai ke gare ta, yayi musu sallama yafita
Kasancewar Lecture ɗaya suke dashi a yanzu ɗin, sai zuwa goma zasu shiga wani don haka ɗalibai suke ta fita, waɗanda kuma zasu zauna suka gyara zama suka dasa hiran su a tsakanin su
RAUDHA ma tana zaune bata tashi ba tana bitan karatun, sosai RAUDHA take son karatu shiyasa idan har ba komi take yi ba to karatu shine abokin hiran ta, bata wasa da karatu ko kaɗan that’s why take da ƙwaƙwalwa
Har time ɗin lecture yayi Malamin yashigo yasoma gabatar musu da karatun sa, One hour yaɗauka kafin yafice
A lokacin ne RAUDHA tamiƙe tasaka Tap ɗin ta cikin jaka sannan ta rataya tayi hanyan fita, bata lura ba tayar da keey ɗin motan ta
Wata dake zaune su biyu da wani saurayi manne da juna a tsakankanin kujerun bayan, ita talura takalli Saurayin nan tace
“Kaga wancan Babe ɗin ta yarda keey ɗin ta”.
Kallon wajen da tatashi yayi yahangi mukullin yashe a ƙasa, kafin yace “to yanzu ya za’a yi zaki kai mata ne ko kuwa?”
“Bari in Kai mata dai, kasan Babe ɗin ta min kaga sai mu ma ƙulla ƙawance”.
Dariya yayi yace “baki da dama ke dai, daga shigowar ki har zaki soma jaye-jaye”.
Fari tayi da ido tana miƙe wa tsaye tace “ya son ranka? na san ko kai ta burge ka ba dai zaka faɗa bane kawai”.
Still dariyan yasake yi
“To je ki dawo dai sai mu tattauna maganar mu, kar kuma ki shanya Ni fa”.
“Baka da damuwa”. Tayi maganar tana ɗaukan keey ɗin lokacin da taƙarisa wajen
Tana fita hole ɗin tahangi RAUDHA batai wani nisa sosai ba, kasancewar tana tafiyan ne tana latsa wayan ta
Cikin sauri taƙarisa wajen ta tayi mata sallama
RAUDHA bata san da ita ake yi ba duk da kuwa taji sallaman kusa da ita
“Aslm alaikum RAUDHA”. Tasake sallaman tare da kiran sunan ta
Hakan yasa RAUDHAN taɗago kai tana kallon matashiya ƴar gayun dake tsaye a gaban ta, wanda a girme dai baza ta fi ta da shekaru biyu ba
Ganin kallon da RAUDHA ke mata batare da ta amsa mata sallaman ba, sai tayi mata murmushi tasake cewa
“Sannu ko?”
Gyaɗa mata kai tayi tana sake kafe ta da idanu
“Keey ɗin ki kika yar a class shine na ɗauko miki”.
Tayi maganar tana miƙa mata keey ɗin
Kallon keey ɗin tayi kafin tasaka hannu ta’amsa tana maida idanun ta kanta
“Thanks”. Tafaɗa cikin dashashshiyar muryan ta
“Babu damuwa.. Ni sunana Rash ko zamu iya zama friend sabida gaskiya kin burge Ni? Zan so mu kasance ƙawaye”. Rash ɗin tayi maganar tana faɗaɗa murmushin ta
Ɗan jimm RAUDHA tayi tana kallon ta batare da tace komi ba
“Yanzu ina zaki je sai muje in raka ki kafin mu shiga Lecture”.
Waro idanuwa RAUDHA tayi cike da mamakin ta, sai kuma tayi gaba batare da ta furta uffan ba
Duk da Rash taji haushin shirun da tayi mata, amma ita a ganin ta ci gaba ne a ganta tare da RAUDHA, duk da bata san ƴar gidan wanene ba but kallo ɗaya kayi mata zaka san a gidan manyan mutane tafito, barin ma yanzu da mutane suke ta kallon su, tasan idan tayi tarayya da ita zata sake zama Big gril ne
RAUDHA da har ta kai jikin motan ta tana ƙoƙarin buɗe wa, sai tatsinkayi muryan Rash kusa da ita
“Plz sister ko dai ba kya son tarayya Dani ne shiyasa kika ƙi kula Ni?”
Juyowa RAUDHA tayi takalle ta, sai kuma ta ɓata fuska tace “bana son friend.. ba shi.. yakawo ni.. ba”.
Yanda tayi maganar a ɗai-ɗai yasaka Rash tasaki baki tana kallon ta, har tashige motan ta bata motsa a wajen ba, sai da taji an dafa ta sannan tajuya dasauri tana kallon wanda ke kusa da ita
Murmushi yayi mata yace “maganin ki kenan ai, taƙi kula ki ko?”
Huro hancin ta tayi batace komi ba illa maida idanun ta kan motan RAUDHA da tay nisa tayi
“Ke da ganin yarinyan nan kin san ba kalan ki bace, kallo ɗaya wlh nayi mata nasan zatay girman kai ne, muje da Allah kin tsaya anan rana na gasa mu”.
Kallon sa tayi tana hararan sa kafin tace “mtsww dalla kar ka ishe Ni, ina zamu je ne?”
Baki yabuɗe
“Ke fa kika ce yunwa kike ji zamu je capteria amma kuma kike tambayana? Ko dan wannan yarinyan ta ɓata miki rai zaki fanshe a kaina, ke fa baki da mutunci wlh, baki sanin wanda zaki sauke tijaran ki a kanshi sai Ni”.
Murguɗa masa baki tayi tay gaba abinta
Shi kuma yabi bayan ta yana sauya zancen dan dai ta sauko
“Rashh muje mana mu kora wlh yau gaba ɗaya bana jindaɗin yanayin sabida ban jini a sama ba, gashi kuma wancan shegen be zo ba shiyasa yau ko son shiga Lecture bana yi na zo na tare a wajen ki”.
Bata tanka sa ba illa tafiyan ta da taci gaba da yi
Sai shima yayi shiru be sake cewa komi ba.
🌐🌐🌐
Fitan RAUDHA cikin school ɗin sai tasoma zagaye akan titi ta rasa inda zata je, so take yi tasami wajen da zata sayi kayan mayen ta tunda nata duk sun ƙare
Haka tay ta kewaye gari, sai a wani Club tatsaya tashiga tatambaya, bata samu abinda take so ba illa su Wine 🍷 kala-kala da suke dashi, fito wa tayi batare da ta siya ba don ita tafi son na afawa ba kasafai take ƙaunar Giya ba
Motan ta tahau tay gaba, a wani babban kanti ta tsaya tayi siyayya cikin baƙin leda takoma mota, kayan ciye-ciye ne fal a cikin ledan
Tana tuƙi tana cin Cake 🍰 har takoma school, bayan tayi parcking sai tazauna cikin motan taci gaba da ciye-ciyen ta, youghot taɗauka tana korawa da Cake ɗin
Bayan ta gama tazuge glass ɗin ta jefar da goran tamayar tarufe, share bakin ta tayi da tissue sannan takalli Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta, ƙarfe 12:40pm. Don haka tabuɗe motan tafita tarufe tanufi Hole ɗin da zasu ɗau darasi
Tana shiga tazauna a inda tazauna ɗazu
Sai ga Rash itama ta ƙariso wajen tazauna kusa da ita tana mata murmushi
Kallon ta kawai RAUDHA take yi batare da tace komi ba ganin Malam ya shigo, sai taɗauko Tap ɗin ta taɗaura a cinya tasoma sauraron karatun sa
Rash kuma ko a jikin ta sai ma buɗe jakan ta da tayi taciro wani ƙaramin kwalba, ta ɗan duƙar da kai tana kurɓan abinda ke ciki
Hakan yasa RAUDHA taɗago kai tana kallon ta, kwalban tabi da kallo na tsawon lokaci kafin takau da kanta, bata sake kallon ta ba har sai da Malamin yafita sannan tajuyo tace
“Aina zan samu wannan?” Tayi maganar tana nuna kwalban hannun ta
Washe baki Rash tayi tace “kema kice ƴar hannu ce kenan?”
RAUDHA bata fahimci abinda take nufi ba sai tagyaɗa mata kai tasake cewa “ina so ne idan zan samu”.
“Ai kuwa kin zo inda zaki samu duk kalan da kike so, Ina zuwa bari in Kira Maan”.
Wayan ta taɗauka talatsa tanemo wani Numba da akayi serving da Sweety, sai ta danna kira, yana ɗagawa tace
“Maan shigo class ɗin mu yanzu ina jiran ka”.
Wayan takashe tamaida kallon ta kan RAUDHA tace “baki da damuwa domin Zen ke samo mana duk abinda muke buƙata, kema zaki samu”.
Murmushi RAUDHA tayi bata ce komi ba
Dai-dai nan Maan yashigo yazauna saman Deks yana faɗin “ya dai menene?”
Rash tace “ƙawata ce take buƙatan kayan maye ina Zen yake?”
Kallon RAUDHA yayi sannan yamaida idanun sa kan Rash yace “ke dai sai da kika shige mata kamar wata mayya, to yanzu Ni zaki tambaya bayan kinsan be shigo school ba yau?”
Hararan sa Rash tayi tace “wai to ina ruwan ka idan na shige mata, bana son fa saka ido”.
Sai taja tsaki tana kallon RAUDHA da tamayar da hankalin ta kan Tap tana shafawa batare da ta maida hankali kan abinda suke cewa ba
“Ƙawata ki bari gobe wanda zaki samu a wajen sa zai zo, idan ya zo sai in haɗa ki dashi kuyi maganar wanda kike so yakawo miki”.
Ɗago kai RAUDHA tayi takalle ta, sai ta ɗan yi murmushi kafin taɗau jakar ta tabuɗe taciro kuɗi, miƙa ma Rash tayi sannan tayi mata bayanin wanda take so idan ya zo sai ta amsar mata ta’ajiye mata
Rash kuwa sai washe baki take yi ganin kuɗin da RAUDHA ta bayar me yawan gaske
Ita kuma RAUDHAN sai tatashi tafice tabar su nan
“Kutt.. wlh yarinyan nan ba ƙaramar yarinya bace, kai daga gani zan ji daɗin ƙawance da ita”.
Dariya Maan yasaki yace “ke dai kin bani wlh”.
“Eh ɗin naji, kasan yanzu abinda za’a yi? Bari in ɗibi rabo na domin kuɗin nan yayi yawa wlh, wannan kuma kariƙe nasan zaku fi haɗuwa dashi sai kaba shi”.
Amsar kuɗin Maan yayi yatura cikin aljihu yana miƙe wa
“Da Allah tashi muje in sauke ki, yau akwai inda zani wlh, gashi ma ina so in gangara wajen Asha be da lafiya”.
Miƙe wa tayi tana rataya jakanta kafin tace “shine baka faɗa min ba? Ai kawai mu wuce tare don babu inda zan fita yau, wahalan makarantan nan ma ta ishe Ni”.
Dariya yayi yana faɗin “ke dai wlh raguwa ce daga soma zuwa har kin fara ƙorafi, amma idan yawo ne babu inda ƙafanki be takawa”.
“To ya son ranka? Wancan fa neman kuɗi nake yi ka ga kuwa bazan gaji ba, Ni dai muje da Allah na ƙosa in jini a kan gado na”.
Hannu yasaka yatallabe mata ƙeya
“Mayya kawai, to zo ki hau bayana mana”.
Rash da har ta saka ƙafa a waje tajuyo tana buga masa harara tace “wlh Sweety na fi ka iskanci kasan halina yanzu zan ɗare ka, kuma wlh bazan sauka ba duk uban da zai gan mu sai dai yagan mu”.
Taɓe baki kawai yayi yabangaje ta yay gaba
Tabi bayan sa kuwa dasauri tana ɗurma masa duka a baya, ahaka har suka kai wajen Motan Maan ɗin suka shige, lokacin sun sauya hiran su har da tafa wa cike da nishaɗi.
lokacin da RAUDHA ta isa gida Packing tayi tafito rataye da jakar ta a kafaɗa sannan tarufe motan tay cikin gidan
+
Tana shiga cikin parlour’n Farida na fito wa daga kichen riƙe da Plate a hannun ta shaƙare da kayan marmari
“A’ahh ƴan makaranta har an dawo?”. Farida tafaɗa fuskarta yalwace da fara’a
RAUDHA murmushi tayi tana kallon ta sannan tagyaɗa mata kai, sai tace
“Ina Yayana be dawo ba?”
“Eh Yayan ki be dawo ba sai zuwa anjima”.
Bata sake magana ba tayi hanyar upstairs
Ita kuma Farida sai tanufi saman kujera tazauna tana ɗaukan Apple ɗaya tana kai wa baki.
Koda tashiga ɗaki jakan tayar saman gado sannan tazauna gefen gadon tana saka hannu tazare combat ɗin ƙafafun ta, sai tacire agogon hannun ta ta’ajiye sannan tamiƙe tasoma cire kayan jikin ta, anan tazubar tatsallake su nan ƙasa tanufi Toilet bayan ta ɗaura towel a jikin ta, wanka tayi tafito tasanya farar shimi iya cinyan ta, sannan tabarbaza gashin kanta yasauka zuwa kafaɗa kafin taɗau wayan ta tafito Parlour
Har a lokacin Farida na zaune tana shan Fruits ɗin ta tana kallo
Kai tsaye dainning tanufa taja kujera tazauna, sai da tazuba farar shinkafa a cikin Plate sannan takalli Farida taɗauke kai tace
“Aunty Wai baki da masu aiki ne anan?”
Da fara’a Farida tace “eyya ina dasu mana, wani abun zasu yi miki?”
Yamutsa fuska tayi kafin tace “naga yanda nafita nabar ɗakina haka nazo na tarar, na kula ma gaba ɗaya ba’a gyara min ɗaki”.
Farida tace “Ni nace mata kar tashiga ɗakin ki wataƙil baki son me aiki tayi miki gyara idan bakya nan, but zuwa anjima zata shigo sai ta gyara miki, ina sallaman ta ne idan ta gama aikin nata”.
Abinci tazuba cikin bakin ta tana tauna wa idanun ta akan Faridan kasancewar Facing ɗin ta takey, sai da tacinye na bakin ta kafin tace
“Ya za’a yi ki riƙa barin ta tana tafiya ba aiki take yi bane? Idan kuma ana buƙatar ta fa?”
“Eh ai nan kusa take bata da nisa duk da tayi tafiya ne but jiya ta dawo, tana zuwa sau biyu ne a rana, idan tazo da safe tagama aikin ta sai tatafi sai yamma, tunda dama Kuku ne me mana abinci, shine kaɗai yake zama a gidan nan idan yagama abincin sa sai yakoma BQ yazauna sai an buƙace shi, kuma Yayan ki ne ma be son zirga-zirgan ƴan aiki sannan nima ina yin abinda yasauwaƙa da kaina don nima bana so komi ai min”. Farida tayi maganar idanun ta duk akan RAUDHA dake ta zuba abinci a cikin ta
Kaɗa kanta RAUDHA tayi sannan ta’ajiye spoon ɗin hannun ta tana tsiyaya Lemu cikin glass Cup tace “to Ni dai ina buƙatar ƴar aiki kusa dani sabida bana yin abu da kaina, ban saba ba kuma bazan yi ba, and yanzu da kike barin ta tana tafiya gida gashi na cire kayana babu wanda zai matsar min dasu sai Ni kenan?”
Murmushi Farida tayi tace “kai ƙanwata yanzu har kayan naki baza ki iya kai su inda yadace ba dole me aiki zata kawar miki? Ke fa macece yakamata kisan abinda yakamace ki tunda yanzu kin girma a koda yaushe za’a iya kai ki gidan miji, to wa zai miki acan ɗin?”
Waro manyan idanuwan ta da suke farare fat tayi kafin talumshe su tasake buɗe wa tana ci gaba da kora Juice ɗin ta
“Kina tunanin Ni ƴar gata har akwai auren da zan yi nan gaba in koma ina yin aiki da kaina? Ko kin manta wanene ubana?”
Sai kuma tayi murmushi tana ajiye cup ɗin hannun ta taɗau spoon tasoma tsakalan abincin kafin kuma taci gaba da faɗin
“Idan har ina da Daddy da Yayana a doron ƙasa to ba zan taɓa yin bauta ba, ki dena ma wannan shashancin”.
Numfashi Farida taja tana jin babu daɗi ta yanda RAUDHA take gaya mata magana a haka tamkar bata san da wa take yi ba, sai dai tasan bata da ishashshen tarbiyya bare ta san ba dai-dai tayi ba, don haka tamatse ɓacin ranta tare da saka murmushi a face ɗin ta tace
“RAUDHA duk abinda ɗiya mace zata yi a gidan Mijinta to ba bauta bane kamar yanda kike tunani, Bauta ne a wajen Allah sannan neman lahiran ta ne, kuma ta wannan bautan zata samu lada har a gobe ƙiyama ta samu wuce wa ni’imar Allah, wato Aljanna kamar yanda Allah yayi mana bushara, RAUDHA babu yanda za’a yi ace kamar ki har yanzu baki san abinda yadace dake b..”
“Enough Aunty”. RAUDHA tafaɗa da ɗan ƙarfin muryan ta
Miƙe wa tayi tana kallon ta tace “baki da hurumin da zaki shiga rayuwata da har zaki koya min dai-dai da wanda ba dai-dai ba, please and please bana son ganin ɗakina da datti, idan zaki nemo min me aiki tariƙa gyara min ɗaki a duk sanda nake buƙata ki kawo, idan kuma baza ki nemo ba..”
Sai tayi hanyar Steps batare da ta ƙarisa ba, tahaye da gudu ta wuce ɗakin ta
Ajiyan zuciya me ƙarfi Farida tasaki jikin ta duk a sanyaye, tabbas RAUDHA tana buƙatar sabuwar tarbiyya idan ba haka ba tana cikin halaka, tana son yarinyan har cikin ranta shiyasa take son taba da gudunmuwar ta wajen sauyawan ta, amma taya? Bata da ikon da zata iya sauya RAUDHA sabida bata kai matsayin ba, amma kuma idan har Daddy da Suhaib sun so ta sauya to tabbas zata sauya, gatan su a gare ta shine ya gurɓatar da ita sannan kuma su ne a yanzu zasu iya tanƙwara ta wajen sake bata tarbiyya tun kafin tafi ƙarfin su, duk da a yanzu ɗin tafi ƙarfin nasu amma su ne kaɗai zasu iya hukunta ta, idan har bada amincewar su ba to babu wanda ya’isa ya gaya ma RAUDHA gaskiya
Insha Allahu ta ɗau alƙawari daga yau zata soma nuna ma Suhaib kuskuren sa ko zai dawo hankalin sa yakula da ƙanwar sa ta hanyar da yadace, da sannu idan har suna zaune a gidan nan tabbas sai tayi nasaran sauyawan RAUDHA da iznin Allah kuma tare da yardan mahaifin ta da yayan ta, dole abu na farko ta fara nuna musu kuskuren su ta yanda zasu dawo hayyacin su akan wannan mummunan makauniyan soyayyan da suke mata
A karo na babu adadi tasake jan numfashi kafin tayunƙura daƙyar tatashi tanufi kichen ta ajiye Plate ɗin sannan kuma tafito tanufi ɗakin su.
🌐🌐🌐
Tunda RAUDHA tashiga ɗaki wayan ta taɗauka takira Ramcy suka sha hira kafin takira Daddy, but har a lokacin baya shiga, jefar da wayan tayi tana turo baki, ƙunƙunai tasoma yi ita kaɗai tana janyo HangBag ɗin ta taciro Tap ɗin ta tasoma revision ɗin karatun da suka yi yau
Bata sake fita ba sai da tasan cewa lokacin yayan ta ya dawo gida sannan tafita, Can tazauna sukai ta hira har dare kafin tadawo ɗaki
Alwala taɗauro tazo tazauna bakin gado tasoma ƙirgan sallan da ake bin ta na kusan kwana biyar, sai da tagama lissafi kafin tatashi tazurma Hijab tasoma gabatar da sallan
Wajen awa biyu tayi tana gabatar wa kafin tagama, duk da kuwa ƴar faki take yi but sai da yaɗauke ta tsawon wannan lokacin
Miƙe wa tayi tacire Hijab ɗin sannan tasaka kayan barci riga da wando farare masu taushi da zanen Flower kalan Coffee a jikin sa, gado tahaye taja pilow taɗaura kanta tana sakin hamma, dayike barcin ne a idanun ta babu jima wa yaɗauke ta.
Can cikin dare tasoma mutsu-mutsu duk ta haɗa zufa kashirɓan, duk da kuwa akwai a.c ga fan da yake aiki amma haka RAUDHA tajiƙe da zufa yana ta kwaranya daga fuskarta zuwa cikin rigan ta
Mummunan mafarki take yi na baƙaƙen halittu, gashi wani narkeken maciji da yaninka ta a tsawo da girma ya kanannaɗe mata jiki ya cure ta, wannan dalilin ne yasaka take fitar da huci tare da gumi tana son ƙwace wa amma ina ko motsi ta gaza, kuka sosai take yi tana neman taimako babu me jin ta, wani irin baƙin daji ne da babu komi sai ƙoramu da namun daji masu ban tsoro, kukan su kawai ya cika jejin yana wani amsa kuwa a kunnen ta
Macijin buɗe bakin sa yayi tare da saita kanta yanufo da bakin sa zai haɗiye mata kai
Wani irin ihu tasaki wanda lokaci ɗaya tafarka a matuƙar gigita tana ci gaba da ihun a gaske, jikin ta wani irin mazari yake yi gaba ɗaya idanuwan ta sun fito waje tamkar zasu faɗo, izuwa yanzu kamar an ɗibi bokitin ruwa ne an kwara mata sabida yanda tayi tsamo-tsamo cikin zufa
Zumbur tamiƙe saboda yanda idanun ta suka hango mata ƙaton macijin a jikin bango Ya biyo ta baki a buɗe yana wani irin fitar da sauti me ƙara wanda gaba ɗaya ɗakin sai da yagirgiza yasoma juyawa
Ƙofa tanufa a guje tana sakin wani ƙara me firgitar wa, tana riƙe handle ɗin ƙofan sai wani irin juwa yaɗibe ta tazame ƙasa tafaɗi a ƙasa sumammiya.
Kuma duk wannan halin da tashiga da kuma ƙaran da tasaki babu inda be amsa ba a gidan, amma kuma babu wanda yaji ta, har ta su Suhaib da suke cikin gidan basu san meke faruwa ba.
.Bata farka ba sai da hasken rana yabugi fuskar ta sannan ne tafara buɗe idanuwan ta tana lumshe su, juya mata wajen yake yi duk da kuwa bata san takamaiman inda take kwance ba, ta ɗau tsawon mintuna goma kafin tatashi zaune tana riƙe kanta da yayi mata nauyi sosai yake mata ciwo
+
Mamaki sosai tayi ganin ta bakin ƙofa a kwance sabida ko kaɗan bata tuna abinda yafaru jiya ba, komi ya shafe mata kamar babu shi a ƙwaƙwalwan ta
Daƙyar taɗaga kanta tasauke a agogon dake manne a ƙusurwan bangon ɗakin, idanuwanta ta fid do waje ganin ƙarfe 11:10am. yanzu, Kuma ƙarfe goma yau take da lectures tunda kafin takwanta sai da taduba tantable
Tun sassafe da Suhaib zai fita yazo yabuga ƙofan nata don yatashe ta, har yagaji da bugawa yatafi sabida a tunanin sa bata da Lecture ɗin safe ne
Shiru-shiru Farida zata ji ta sauko amma kuma babu RAUDHA babu alamun ta, itama sai tahayo tay bugun duniya but RAUDHA ko kaɗan ba ta jin su, wani irin barci take yi wanda tayi nisa da duniyar mu, dole Farida tasauka tatafi tunda taƙi buɗe ƙofan.
Wani gauran numfashi RAUDHA tasaki kafin tajanye hannun ta a kanta tamiƙe a hankali jikin ta kamar anyi mata duka, ko kaɗan bata jin ƙarfi a jikin ta amma haka nan talallaɓa tashiga Toilet tayi wanka tafito, cikin sauri take yin komin ta duk da kasalan dake jikin ta
Shiryawa tayi cikin dogon wando fari ƙal me guntun skert a saman sa kalan orange, sai tasanya rigan shi me gajeren hannu da igiyoyi a gaban anyi ado dashi, itama rigan orange ne amma kuma akwai ɗige-ɗigen fari a ƙasan rigan da kuma saman rigan, me hula ne don haka ta ɗauka tasaka akanta yayinda ta cure gashin ta a ƙeya, wannan dalilin ne yasaka tuntun gashin be shiga cikin hulan ba yafito waje, Sandal shoes tasaka fari tare da Socks, haka ma Wrest watch ɗin ta da HangBag ɗin ta duk fari ne, sannan sai takanga faskeken eyeglasess na Robber a baby face ɗin ta fari tarr ana ganin idanun ta tamkar ba Glasses tasaka ba
Ƙofa tanufa tabuɗe tafice, ahankali take taka Steps ɗin tana riƙe da ƙarfen benen, tana sauka tayi hanyan ƙofa da ninyan fice wa
Farida dake zaune tana hangen ta takira ta
“RAUDHA ina zaki baki karya ba?”
Ɗan juyo wa tayi takalle ta, sai yanzu ita takula ma da ita tunda tana ɗaya side ɗin ne na cikin parlour’n, wanda babu yanda za’a yi tahangi me sauko wa daga sama sai idan mutum na cikin parlour’n
“Bana jin yunwa”. Tafaɗa ahankali tana yin gaba batare da ta jira amsar ta ba
Kafaɗa Farida taɗage kafin tasoma kwaɗa ma House girl ɗin ta kira
Nan da nan tagurfana a gaban ta
“Yauwa Ester hau sama ki gyara ma RAUDHA ɗakin ta tunda ta fito”.
“Ok Ma’am”. Cewar Ester tare da rusunar da kanta alamun girmamawa sannan tawuce saman.
🌐🌐🌐
A cikin mintuna ƙalilan RAUDHA ta’isa school ɗin sabida gudun da ta sharara, tana yin parcking tafito tarufe motan tanufi department ɗin su
Koda ta’isa ta tarar akwai Malam acikin class ɗin, shiga tayi ta ƙofan baya tazauna taciro Tap ɗin ta tasoma sauraron karatun nasa
12:00pm. Na cika yafice wani yashigo
Duk karatun yau RAUDHA bata wani fahimta sosai, sabida sosai take jin babu daɗi a jikin ta, ƙarfin jikin ta yaƙi dawowa Sai kuma tana jin kamar ana buga mata guduma akai lokaci-lokaci, sannan sai tariƙa jin kamar da mutum kusa da ita ana yawan motsi, idan ta juya sai taga babu kowa tunda dama acan bayan tazauna, that’s why bata maida hankalin ta sosai kan karatun ba
Bayan malamin ya fita sai takifa kanta saman Deks tana fid da numfashi.
Rash ce taƙariso wajen tare da yin sallama tazauna
Hakan yasa RAUDHAN tatashi zaune tana kallon ta batare da ta amsa mata sallaman ba
Murmushi Rash tayi tace “yau kin yi late baki samu Lecture ɗaya ba”.
Gyaɗa mata kai tayi sai dai bata yi magana ba
Izuwa yanzu Rash ta gane halin RAUDHAN ba wai ta cika son magana bane, don kafin tayi magana sau ɗaya ta baka amsa sau ba adadi da kanta
Jakan ta tabuɗe taciro mata wani leda me ruwan zuma babba, tamiƙa mata tana faɗin
“To ga saƙon ki an siyo”.
Hannu RAUDHA tasaka ta’amsa tana jin farin ciki sosai aranta, ba ƙaramin wahaltuwa tayi ba a kwanakin nan da bata ji ta a sama ba, ta rigada ta saba shiyasa ko kaɗan bata jindaɗi in bata sha ba
“Thank you”. Tafaɗa tana murmushin ta me kyau
Itama Rash murmushin tayi tace “to yanzu ki tashi mu je capteria mu ci abinci yunwa nake ji”.
Bata ce mata komi ba tamiƙe suka fito, duk a cikin su babu wanda yay tunanin zuwa sallah tunda babu me damuwa dashi
Capterian suka wuce suka yi odaring abinci, bayan sun gama RAUDHA tabiya suka fito.
“Kai mutumina ga fa yarinyan can da nake baka labari ita da Rash”. Maan yafaɗa yana kallon su Rash ɗin dake doso wajen su
Kyakykyawar saurayin dake zaune saman mota yakai duban sa inda Maan ke kallo, nan yazuba idanun sa kan RAUDHA ko ƙyafta wa baya yi
“Maan wannan yarinyan kuma fa?” Yatambayi Maan batare da ya ɗauke idanun sa kan ta ba
“Nima dai bansani ba yanda kaganta haka na ganta, ai na faɗa maka ƴar Class ɗin su Rash ne kasan ta da jaye-jaye, itace wacce kakawo mata kaya”.
“Haba dai amma fa ta haɗu, kace irin mu ce?” Yayi maganar yana shafa gemun sa still idanun sa akan ta
Dariya Maan yayi yace “kai dai maye ne Zen..”
Shiru yayi be ƙarisa maganar ba ganin har sun kawo setting su, hakan yasa yasauya maganar da kiran Rash
Sai a lokacin Rash tahange su, don haka takalli RAUDHA tace “ƙawata muje wajen su mana, kinga wancan shine wanda yake kawo mana wannan kayan, muje mu gaisa sai mu wuce Class”.
RAUDHA bata ce mata komi ba illa bin ta da tayi suka isa wajen su
Dasauri Zen yasauko daga kan motan yana faɗin “Rash wannan Babe ɗin fa?”
Kallon sa Rash tayi
Yakashe mata idanu
Sai tayi dariya tace “friend ɗina ce Her name is RAUDHA”.
Sai takalli RAUDHAN kafin tace “Ƙawata wannan shine Zen Abokin Maan ne”.
Idanu RAUDHA tasanya masa kamar yanda shima yazuba mata yana murmushi, ƙare masa kallo kawai take yi da shigan da yayi
Yana sanye da farar riga me yankakken hannu, sai wando jeans blue colour duk an yayyanka shi as kwalliya, yasha askin zamani me tugaggen gashi, wuyan sa kuma sarƙoƙi ne wajen biyar da me Cross a ciki, hakan yatabbatar mata shi ɗin Christian ne
Bata ce komi ba illa ɗauke kanta da tayi
“Hi”. Yafaɗa yana miƙa mata hannu alamun su gaisa
Idanun ta tamaida kansa kafin tabi hannun da kallo, sai kuma tace “Hi”. Batare da ta bashi hannun ba
Murmushi yayi yakalli Rash yace “ƙawar ki fa tayi min tana da kyau sosai, zan zo tazama friend ɗina”.
Dariya Rash tayi tace “kaga ga ita nan sai kafaɗa mata”.
Kallon ta yayi yace “ko zamu iya zama friend RAUDHA? I Like you”.
Fuska ta yamutsa kafin takalli Rash sai kuma tajuya tawuce batare da tabashi amsa ba
Hakan yasa Rash tayi saurin ce musu “byee na tafi sai mun haɗu anjima”. Tay gaba itama
Zen be ɗauke kai akanta ba har sanda suka ɓace ma ganin sa, sai yasauke ajiyan zuciya yana kallon Maan dake mishi magana amma be ji ba
“Guy wlh yarinyan tayi sai ta zama nawa, dole ne duk yanda za’a yi nahaɗa alaƙa da ita”.
Maan yay dariya yace “cabb wlh kana da aiki Zen, Nima Tunda naganta taburge Ni but bana tunanin fa ƴar hannu ce that’s why ban ƙwallafa raina ba”.
Kallon sa Zen yayi yace “kai kasan halina duk yarinyan da tayi min dole ne sai ta shiga hannu na, bare kuma wannan Babe ɗin da tahaɗu sosai, wlh dole ne sai ta shiga cikin mu, kai dai kabari zamu san abun yi”.
“Allah ko mutumina?”
Jinjina masa kai Zen yayi alamun tabbaci kafin yace “kazuba idanu kagani”.
Ihu Maan yasaki yana bashi hannu suka kashe
“Yanzu mu je gida, anjima idan mun haɗu da Rash sai mu tattauna”. Zen yay maganan yana nufan ƙofan me zaman banza yabuɗe yashige
Shima Maan motan yashiga yaja suka bar wajen.
Kasancewar Lecture ɗaya yarage musu biyu zuwa uku, suna gama wa RAUDHA tayi gida.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Rash asalin sunan ta Rashida ne, a Kano suke ita da Mahaifiyar ta da ƙannin ta biyu, kasancewar mahaifin su ya daɗe da rasuwa sai yazamana Maman su ke ci dasu tunda basu da me taimaka musu ƴan uwa duk sun guje su
Tun tasowar Rash idanuwan ta suka buɗe da son kuɗi, kasancewar ta yarinya me son ƙarya shiyasa take bin gidajen yaran masu kuɗi tana ƙulla alaƙa dasu, a haka har tasoma haɗuwa da maza ɓata gari tana ba da kanta gare su suna biyan ta
Wannan abun duk da take yi Maman ta bata taɓa hana ta ba, a ganin ta yarinyan ta tayi farin jinin da tun kafin tagama girma samari na mata rubibi, hakan baya damun ta tunda tana kawo mata kuɗi duk abinda tasamu tare suke ci
Abu yayi gaba har takai ta kawo ma Rash ita ke ci da ƴan gidan su, ta zama tantiriyar karuwa wanda duk wani namiji me ji da kansa ya san Rash saboda shaharan ta
Maman ta da tagano ainihin abinda take yi take samun kuɗi hakan be wani ɗaga mata hankali ba, tunda dai tasan wannan shine zamanin, babu me baka sai idan ka ba shi wani abun da zai ƙaru da kai, sai dai ko kaɗan bata yarda ƙannin Rash sun faɗa wannan mummunan rayuwan ba, a ganin ta Rash ita kaɗai ta isa tawanke musu matsalan rayuwan su, ta yarda ta sadaukar da rayuwan Rash don su samu kuɗin da zasu ci gaba da rayuwa gaba ɗayan su, a cewar ta idan sun gama samun abinda suke so sai taja ƴar ta ajiki ta tuba takoma ga Allah sannan tayi mata aure shikenan komi ya wuce hmmm.
Rash babu inda bata bin namiji in dai zai biya ta kuɗi, ana haka suka haɗu da Sulaiman wanda a yanzu suke kiran sa da Maan, a salin haɗuwar su a social media suka haɗu wanda har yakai ga sun haɗu a fili
Maan ɗan Jigawa ne, babu laifi iyayen sa suna da kuɗi sosai, duk abinda yake so suna masa sabida shi kaɗai ne suka haifa
Tun fara abotan su soyayya tashiga tsakanin su, Rash tunda taga hoton Maan takamu da tsananin ƙaunar sa sabida babu ƙarya Maan yana da matuƙar kyau, irin kyakykyawar bafulatanin nan ne tamkar su sukai kansu
Dayake shima ɗan hannu ne shiyasa tunda suka haɗu Rash take bashi kanta suke rayuwan ƙasƙanci, shaƙuwar da suka yi da soyayyan da suke ma juna ko yaushe suna tare tamkar Chwingum
A lokacin da Maan zai tafi karatun sa a Abuja inda anan ne yazaɓan ma kansa don ci gaba da karatun sa, sai Rash itama tace zata bi sa, hakan ya saka sa farin ciki sosai don haka yace tahaɗo kayan ta su tafi
Batare da sanin Mahaifiyar ta ba Rash tahaɗa kayan ta tabi Maan Abuja, ya kama musu hayan gida Plet anan suke zaune, sun ci gaba da zama tamkar mata da miji
Kasancewar Rash tayi karatun ta zuwa matakin primary sai Maan yanema mata school taci gaba, sai dai tana yi tana tsallake sabida tafi son rayuwan jami’a ne, ita babu abinda take ƙauna in banda taganta cikin jami’a tana rayuwan wayewa irin ta ƴan mata masu ji da kansu
Wannan yasa koda tagama Scondary school sai tashiga school ɗin su Maan inda a lokacin yana Degree ɗin sa ne
A yanzu ita take biyan ma kanta kuɗin makaranta sabida Maan be hana ta bin maza ba, shima kuma duk yarinyar da yagani zai bi batare da ta damu ba duk da kuwa cewa har yanzu soyyayyar su tana nan
Zen Abokin Maan ne tun zuwan sa school ɗin, shima Baban sa me kuɗi ne sosai kuma fasto a babban Church ɗin dake garin Abuja
Har shi Zen ɗin yana tarayya da Rash babu ruwan su, iyakan dai yaba ta kuɗi takashe matsalan gaban ta tunda ta ɗau abun yanzu tamkar sana’a ne
A kayan maye babu abinda basu sha gaba ɗayan su, babu Club ɗin da ba sa zuwa duk inda akwai sheɗanan ta to suna nan wajen
Haɗuwar su da Zen shi yaƙara dulmiyar dasu sabida shi yafi su sanin kan duniya, yana da abokai tantirai sosai wanda suke cin karan su babu babbaka tare.Rayuwar RAUDHA ya ƙara taɓarɓare wa because of haɗuwar ta da Rash, yanzu banda shaye-shaye da zuwa club babu abinda take yi
+
Hankalin Suhaib ya tashi musamman yanda yaga RAUDHA tana fitan dare, bata tashi dawowa Sai idan dare ya tsala ko kuma asuba tayi, a wannan lokacin zata dawo musu abuge, ya rasa ya zai yi ya shiga tashin hankali matuƙa
Farida ita ke tausar sa akan yaci gaba da hakuri sannan yakula da ƙanwar sa wajen ceto rayuwan ta, tana nuna masa hanyan da zai bi don nuna ma RAUDHA kuskuren ta, amma duk hanyar da tanuna masa baya jin zai iya bi, abu ɗaya yaɗauka shine yin mata nasiha, yakan zaunar da ita yay ta mata nasiha wani lokacin har da hawayen sa, amma RAUDHA ko kaɗan bata taɓa jin sa ba, a ganin ta rayuwan ta ne kuma hakan tazaɓar ma kanta, babu wanda ya’isa yahana ta yanda take so tatafiyar da rayuwan ta, wani lokacin ma idan yamatsa mata wani irin fushi take yi dashi wanda ada ko kaɗan idan zata yi fushi dashi bata yin hakan, kamar wata mara hankali haka take koma wa, idan tasoma musu hauka sai abun yabasu mamaki matuƙa, har zagin Suhaib ɗin take yi idan fushin ta yayi ƙololuwar tashi, sai takoma tamkar ba ita ba, abun fa yay mugun ɗaga musu hankali ganin yanda RAUDHA tasauya lokaci ɗaya, baza ka taɓa gane bata da hankali ba sai idan ka shiga rayuwan ta, wannan dalilin ne yasaka daga shi har Farida suka shafa ma kansu lafiya tunda RAUDHA bata sauraron su.
Yanzu RAUDHA da Rash tare dasu Zen sun jone matuƙa, duk inda zaka gansu tare suke, RAUDHA ta saki jikin ta sosai dasu, yawon su da ko ina ma tare suke zuwa
Karatun ta yanzu bata cika maida hankali ba tunda bata da lokacin yi, sai dai abu ɗaya tamaida hankali yanzu idan har suna da Lecture bata zuwa ko ina sai ta gama, duk nacin da zasu yi tazo su tafi bata bin su sai ta saurari Lecture ɗin ta, idan kuma suka tafi yawon su time ɗin Lecture na cika duk inda suke sai ta matsa musu sun dawo
Wani lokacin Rash tana biye mata su shiga Lectures tare, wani lokacin kuma taƙi bin ta tazauna wajen su Maan har sai idan ta fito sannan su shiga motan Zen subar makarantar, basa kuma dawowa sai idan time ɗin Lecture yayi, idan kuma aka tashi RAUDHA bin su take yi wani lokacin su tafi gantali
A zaman da tayi dasu RAUDHA ta fahimci halin su gaba ɗaya, yanda Rash take bin mazaje da yanda su Zen suke bin mata hakan baya mata daɗi sosai, tunda suka nuna mata rayuwan tanuna musu ita kuma sam bata so ko kaɗan, ko idan Zen yana riƙe ta tare da rungume ta ta rinƙa faɗa kenan har fushi take yi dasu, sai idan sun lallaɓa ta gaba ɗayan su sannan take dawowa su haɗe tare.
Sai dai abinda bata sani na su Zen ba sun bata lokaci ne yanda zata ƙara sakin jiki dasu ta yanda zasu ƙara nuna mata abunda suke so a wajen ta, idan kuma taƙi suna da hanyoyin da zasu bi don cin ma burin su akan ta, ahankali-ahankali zasu ci gaba da jan ta, musamman ma Zen shine yake shige mata kuma sosai tasaki jiki dashi, shi kaɗai ne take iya bari yana riƙe ta, shima ɗin don taga ba addinin su ɗaya bane, sannan ma ita ko kaɗan hakan ba wai burge ta yake yi ba shiyasa tun farko bata yi kuma bata soyayya tunda ba wai tasan addini bane bare tasan an hana, sha’awar hakan ne bata dashi ko kaɗan, duk idan namiji yaraɓe ta tana jin tamkar zata haukace ne sabida tsananin baƙin ciki da ƙuncin dake ziyartan ta.
🌐🌐🌐
Yau ma kamar ko yaushe daga school suka fito yawon shaƙatawa, suna zaune a haɗaɗɗen wajen huta wa inda akwai ƙoramu a wajen wanda aka ƙawata su sosai, da irin su soomun pool da abubuwan more rayuwa
Daga can gefe Rash ne da Maan zaune akan fararen kujeru tsakiyan an saka musu glassess table, sai abubuwan sha da aka ajiye musu, hira suke yi suna dariya cike da nishaɗi
RAUDHA da Zen kuma suna zaune bakin ruwa, ita RAUDHA ta saka ƙafafun ta ciki tana wasa da ruwan sai jan wandon ta take yi don kar yajiƙe tana murmusawa cike da nishaɗi, sosai irin wajen nan yake mata daɗi tare da faran ta ranta
Ɗago hannun ta tayi takalli agogo kafin tajuya tana kallon Zen dake zaune kusa da ita yana latsa waya tace
“Zen I want to go time ɗin Lectures yayi”.
Ɗago kai yayi yatsira mata idanu, ji yake yi tamkar yarungume ta yay ta tsotson bakin nan nata da yafi komi burge sa a jikin ta, shi dai yarinyan tayi masa ya gaji da jiran ranan da zai mallake ta akan gadon shi
Ganin kallon da yake mata ko ƙyafta idanu baya yi duk da kuwa ba yau yasa ba yin mata irin kallon ƙurilla ba, ita har mamakin sa take yi ko me yake kallo? Murmushi tayi tasaka hannu taɗana masa yatsan ta a saman fuska
Dasauri yayi firgigit yana sosa wajen
Hakan yasaka RAUDHA tasaki dariya tana kallon sa
Tunda yake be taɓa ganin dariyan RAUDHA ba, komin abu bata iya dariya sai murmushi, shiyasa sai yaga ta ƙara masa mugun kyawu musamman da yaga fararen haƙoran ta jere a waje
Sai da tayi dariyan ta son ranta kafin taturɓune fuska ganin dai kallon nasa yaƙi ƙare wa, miƙe wa tayi tana yamutsa fuska
Hakan yasa hankalin Zen yadawo jikin sa shima yamiƙe yana cewa “haba Babe muna tsaka da jindaɗin mu kike son tafiya? Please ki bar Lecture ɗin nan na yau ki zauna mu huta sosai”.
Kallon sa tayi sai tataɓe baki tana yin gaba batare da tayi masa magana ba, mota tashige wajen me zaman banza
Tunda tatashi su ma su Rash suka tashi suka nofo wajen Zen
Maan yace “har time yayi ne?”
Ɗage kafaɗa yayi batare da yayi magana ba
Maan hannu yaɗaura saman kafaɗan sa yace “ka dena damuwa yau komi zai wuce, mu je dai mu mayar da ita school ɗin”.
Dariya Rash tayi tace “babu ruwana Ni dai duk abinda yabiyo baya”.
“Dama wa yace da ruwan ki?”. Zen yafaɗa yana hararan ta kafin yayi gaba yanufi wajen motan
Taɓe baki tayi alamun ko ajikin ta, tashige jikin Maan tana faɗin “mu bar su don Allah su tafi Ni bana son mu bar nan”.
“Ko Babyna?” Maan yayi maganar yana shafa fuskar ta bayan ya ƙara matse ta a jikin sa
Zata yi magana suka ji ƙaran horn
“Mu je Babe kinsan halin Zen, kuma kinsan yau muna da shiri akan RAUDHA so dole mu zauna musan abun yi”.
Gyaɗa kanta tayi batare da tayi magana ba suka nufi wajen motan, baya suka shiga Zen yaja motan suka bar wajen
A cikin motan Rash da Maan suna manne da juna abun su yayinda suke ta romancing junan su ko gajiya basa yi
RAUDHA kuwa titi ta kafa ma idanu tana ta kallon gari
Kallon ta Zen yayi cikin ƙasa da murya yace “My dear Ina alƙawarin da kikai min?”
Kallon sa tayi tana waro manyan idanuwan ta akan sa batare da tace uffan ba
Murmusawa yayi yace “ko kin manta jiya kin ce min yau a gidana zaki kwana?”.
Sai kawai RAUDHA tasaki dariya tana kwantar da kanta jikin kujeran, cikin dishewar muryan ta me sanyi tace “uhmm bazan iya zuwa gidan ka in kwana ba, dama wasa nake maka don ka matsa min nafaɗa haka”.
Marairaice murya yayi yace “haba Babe meyasa Zaki yi min haka bayan kinsan Ni dagaske nake yi?”
Shiru ne yabiyo bayan maganar sa, don haka yasake cewa “shikenan to i know har yanzu baki yarda dani bane, kina ganin kamar zamu cuce ki tunda kinsan halin mu, but kinsan mu friend ne babu abinda zamu iya miki tunda yanzu mun zama ɗaya”.
Sai yayi shiru idanun sa kan titi yana ci gaba da tuƙin sa, kafin kuma yaci gaba da faɗin “any way yau zamu je birthday ɗin Abokina ina gayyatar ki”.
Ɗan kallon sa tayi taɗauke kai tana sake lafe wa akan kujeran tace “bana jin zan je yau bana jindaɗin jikina”.
“No Babe yakamata ki je, nasan ke mayyan rawa ne I have surprise for you”.
Murmushi tayi tana kallon sa kafin kuma tagyaɗa kanta tace “ok zan zo”.
“Yeees ko ke fa Babe”. Yafaɗa cike da murna
Daga nan hira suka ci gaba dayi, inda Zen ɗin ne ke bata labarin birthday ɗin yana ƙara ƙawata mata abun don yashiga ranta sosai.
Suna shiga school ɗin RAUDHA tafito daga motan tawuce class, yayinda su kuma suka fice a school ɗin har da Rash da tace baza ta shiga Lecture ɗin ba.
🌐🌐🌐🌐🌐
Direct gida RAUDHA ta wuce da suka gama Lecture, babu kowa a Parlour lokacin da tashiga sai tawuce ɗakin ta, tana shiga tafaɗa kan gado sai barci don shine a idanun ta ga kuma gajiya da take ji sosai a jikin ta
Sai 06:30pm. Tatashi daga barcin, wanka tayi tasaka ƙaramar riga shimi kalan sararin samaniya sannan tafito Parlour
Suhaib na zaune yana aiki da computer’n sa taƙariso wajen sa tazauna tana ɗaura kanta saman kafaɗan sa
Kallon ta yayi yana shafa fuskar ta da hannu ɗaya yace “Baby kin tashi? Na shigo naga kina barci”.
Gyaɗa masa kai tayi tana lumshe idanun ta
Shima be sake cewa komi ba sai yamaida hankalin sa kan aikin sa yaci gaba dayi
Can kamar shuɗewar mintuna biyar tace “Yaya har yanzu Daddy shiru yaƙi kiran mu”.
“Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu nasan babu wata matsala sai kira mu da yardan Allah, idan kuma hakan be faru ba zan je har can ɗin in dubo sa”.
Kallon sa tayi tana riƙo damtsen hannun sa da duk ka hannayen ta, cikin marairaice fuska tace “yaya nima kaje dani?”
“Baby school ɗin ki fa?”
Turo baki gaba tayi tace “a’a Ni dai kaje dani”.
Shafa kanta yayi alamun rarrashi yace “to shikenan zamu tafi tare duk sanda na tashi tafiya, akwai aiki a Office sosai ga kuma Wifey bata jin daɗin jikin ta that’s why bazan je yanzu ba”.
Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana jin kewar Daddyn nata na ƙara shiga zuciyarta, sosai take buƙatan sa a kusa da ita but yayi mata nisa, tana ji a ranta tamkar wani abun ne yasame sa tunda gashi an shafe tsawon lokaci babu labarin sa bare wayan sa tashiga
Maganar Suhaib ɗin ne yadawo da ita hayyacin ta
“Baby ɗaga Ni zan je sallah gashi can an soma kira, kema kije kiyi kinji?”
Bata ce masa komi ba illa miƙewa da tayi tanufi sama, tana shiga takwanta abunta bata ƙara motsi ba, sai da wayan ta tasoma ringing kafin tatashi ta ɗauka tayi peacking, lumshe idanun ta tayi tana saka hannu saman goshin ta tare da matse gashin kanta ta tattare shi zuwa baya, da alamun dai tana sauraron me maganar ne ta cikin wayan, sai kuma ta yamutsa fuska cike da sanyin murya sosai tace
“Ok I will”.
Daga haka bata sake magana ba har sanda tagama wayan tacire a kunne tana ajiye wa, miƙe wa tayi tashige Toilet tasillo wanka tafito sanye da towel iya cinyan ta, kan stool tazauna tasoma shafe-shafen ta, duk abinda take yi a hankali take yin sa kamar baza ta yi ba, sosai idan kakalle ta zaka ga damuwa aranta, ko kaɗan bata jindaɗin jikin ta, ta rasa kuma meke mata daɗi ga dai tanan ne
Bayan ta gama tashirya cikin guntun wando Light blue, sai tasaka riga da yatsaya mata iya setting wandon me dogon hannu tamkar na sanyi sai dai be da wani nauyi sosai, kalan ruwan ƙasa ne sai siraran zane da aka zana guda uku daga ƙirjinta da Red colour, hill shoes tasaka red sannan ta tufke gashin ta a ƙasan ƙeyan ta da jelan gashin, turare tafesa taɗau HangBag ɗin ta tafito Parlour
Yanzun ma Suhaib ne zaune shi kaɗai saman dainning yana cin abinci
“Baby Ina zaki je kuma baki yi dinner ba?”
Wajen sa taƙarisa takwanto da jikin ta saman bayan sa tare da zagayo da hannayen ta a wuyan sa, batace komi ba illa tusa kanta da tayi a wuyan sa tana shaƙar ƙamshin jikin sa idanunta a rufe
Hannu yasaka Suhaib ɗin yazagayo da ita ta gaban sa yaɗaura ta saman cinyan sa, sai tasake shigewa jikin nasa still idanun ta a rufe
Numfashi ya ɗan ja yana shafa tattausan gashin kanta, sosai yake tausayin ƙanwar tasa tare da wani irin mahaukacin ƙaunar ta a ransa
Tsawon lokaci suna a haka, sai da wayan ta yayi ƙara sannan Suhaib ɗin yaɗago ta don ita taƙi motsawa ko kaɗan
“Sweetheart ana kiran wayan ki”.
Bakin ta takai kan nashi tasakar masa kiss 😘 kafin tamiƙe tana kallon sa da shanyayyun idanuwan ta tace “Yaya sai na dawo”.
Be iya ce mata komi ba illa bin ta da kallo da yake yi har takai bakin ƙofa tafice
Numfashi yasauke cike da tausayin ta, sosai yaga damuwa a fuskarta kuma yasan RAUDHA ko kaɗan ba ta faɗa ma kowa damuwar ta, koda kuwa ya tambaye ta ne kafin tafaɗa masa aiki ne, tana da zurfin ciki ga duk abinda ke damunta, ko kaɗan baya jindaɗin fitan daren nan da take yi duk da kuwa yasan inda take zuwa, sai dai babu yanda zai yi sabida idan yace zai hana ta ba sauraron sa take yi ba, yanzu sai abun ma yajuye yakasa gane mata, tabbas yasan ƙanwar tasa tayi mugun sauya wa fiye da tunanin mutum
“Amma meke damun ta me yasauya ta?” Shine amsar da yakasa samowa har yanzu.
🌐🌐🌐🌐
RAUDHA na fita kanta tsaye tayi bakin Gate
Me gadi na hango ta yatashi yabuɗe mata small Door tafice
Motan Zen na waje suna jiran fitowar ta, shi yafito yabuɗe mata murfin motan tashiga
Tunda suka kama hanya ko magana ta kasa musu har suka dan gana ga kyakykyawar club ɗin, tunda tashiga tasamu wuri tazauna bata sake motsa wa ba, tambayan duniya sun yi mata ko akwai abinda ke damun ta amma taƙi yin musu magana illa idanu kawai da tazuba musu
Lokacin da aka sake cika maƙil a wajen sai tamiƙe tafito waje sabida hayaniyan mutanen sosai yake damun ta, hakan har ya soma haddasa mata ciwon kai me tsanani
Haraban wajen haske ne tamkar rana, ba ka sanin ma dare ne sai idan kayi nesa da wajen
Tunda tafito tajingina da wani ƙarfe taharɗe hannayen ta a ƙirji tare da kwantar da kanta jikin ƙarfen tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana sauraron sarawan da kanta ke mata, gaba ɗaya jikin ta kamar ana ƙara zare mata kuzari ne a duk sokonni, izuwa yanzu har rawa jikin nata yake yi, leɓen bakin ta kawai take cije wa sabida yanayin dake baƙuntan ta, har ga Allah baza ta iya fahimtar halin da take ciki ba izuwa yanzu, kawai tasan zuciyarta ta bata umarni kuma tabi
Buɗe idanuwan ta tayi tasoma takawa a hankali zuwa waje, ahaka har tafice Gate ɗin, tafiya take yi batare da tasan inda tanufa ba, a lokacin wajen ƙarfe 10:00pm. Hasken motoci ne kawai ke gilma wa da fitilu
Bata yi nisa sosai ba tasami wasu motoci guda biyu an faka su, jingina tayi ajikin ɗaya tare da zame wa ƙasa tana riƙe kanta sosai, izuwa yanzu duniyar ce take juya mata hakan yasa takasa tafiya tazauna nan, tana nan zaune tajiyo motsi sai dai ta kasa motsawa bare ta ɗago kanta da ta ɗaura saman gwiwar ta, bata san meke faruwa ba amma taji an haske ta da fitila me tsananin haske sai kuma tajiyo surutun mutane inda ɗaya ke cewa
“Baaba mun yi kamu fa, ka ga wata cikas anan kuwa…”
Daga nan bata sake fahimtar maganar da suke yi ba illa ji da tayi an ɗago ta an sanya mata wani ƙyalle an rufe mata hanci da baki, daga nan ne talumshe idanuwan ta numfashin ta yaɗauke gaba ɗaya.
Saka ta suka yi a cikin mota suka ja da gudu suka bar wajen.