RAUDHA CHAPTER 8
don Allah yasa Daddy me saurin yarda da ƙaddara bane, da babu abinda zai sa be zube musu anan ba, sai dai kuma sosai ya dage wajen danne kaso sittin cikin ɗari na daga damuwar sa, amma hakan be sa fuskar sa ta hana bayyanuwar tsantsan damuwa da tashin hankalin da yake ciki ba, idanuwan sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur, muryan sa na rawa ya ce da su, “yanzu tana asibitin ne?”+
Rayyan ya ba shi amsa da “Eh”.
“Ok ku mu je ku kai Ni”. Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari
Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin.
Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su
Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi har yanzu sabida alluran barcin da aka yi mata. Ahankali Daddy ya saka hannun sa ya ɗauke hawayen da ya silalo masa a kuncin sa, sannan ya juyo yana kallon su yace, “ina ne Office ɗin doctorn dake duba ta?”
“Daddy bari in Kai ka”. Rayyan yayi saurin faɗar haka
Gyaɗa kai kawai yayi yabi bayan sa
Shi kuma Suhaib ya koma kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun ta ɗaya wanda akayi mata ƙarin ruwa aka cire.
Wajen mintuna ashirin da fitan su Daddy kafin suka dawo, dayake magriba tayi, sai suka wuce gaba ɗaya masallaci, har bayan sallan isha’i suna nan a asibitin, har sannan kuma RAUDHA bata farka ba, dole suka taho gida suka bar ta cikin kulawar likitoci, tunda dama asibitin ba kasafai suke barin mutane suna kwana da mara lafiya ba. Daddy ya so ya kwana amma sai su Rayyan suka taushe shi akan ya koma gida, tunda shima yana buƙatar hutu a wannan lokacin
Sai da suka mayar dashi gidan sa, kafin suka wuce su ma, da zummar gobe Suhaib zai kawo mishi Haneep da Farida, sai su gaisa tunda yau basu samu sun haɗu ba.
A taƙaice ranan Daddy be iya runtsa wa ba, kwana yayi a zaune yana nema wa ƴar sa samun lafiya daga wurin mahaliccin mu.
Washe gari tare suka taho da Farida gidan Daddy ɗin, anan suka gaisa, Daddy ya amshi Haneep yana ta faman mishi wasa, sosai soyayyar yaron ya shiga ransa, kuma ya tausaya mishi da rashin lafiyan da yake yi, yayi masa addu’a sosai kafin ya miƙa ma Farida shi, sannan suka fito suka nufi asibitin, daga can Rayyan ya wuce wurin aikin sa.
Wajen awanni biyu da zuwan su, sannan ne RAUDHA ta farka, amma kuma gaba ɗaya ta rikita su da koke-koken ta, kuka take yi sosai tana surutu kamar zautacciya, ba ma ta gane wanda ke kanta
Sosai tashin hankali ya sake bayyana a wajen Daddy da Suhaib, sun rasa ya zasu yi, har kuka sai da Suhaib yayi, shi kuma Daddy sai faman sharan ƙwalla yake yi, musamman da ya riƙo ta yana faɗin, “shi ne Daddyn ta, tayi shiru”. Yana rarrashin ta
Sai tahau zagin sa, daga ƙarshe ta soma ɓaɓɓaka masa dariya tana tokarin sa da ƙafa, wai sai ya sake ta ta hau saman silling
Da gudu Suhaib ya fice yana sharan hawaye
Itama Farida dake riƙe da Haneep ta zauna a gefe tana kallon RAUDHA dake jikin Daddy, bata san sanda hawaye yayi ta kwarara a saman fuskar ta ba, sabida tsantsan tausayi
Hauka tuburan RAUDHA take yi, an rasa yanda za’a yi da ita, tunda tuni Suhaib ya kira likitoci sun duƙufa akanta
Ƙiri-ƙiri Daddy ya ƙi fita a ɗakin koda suka buƙaci su ba su wuri
Yanda suka ga hankalin Daddy yayi ƙololuwar tashi, dole suka tausaya mishi suka bar shi a cikin ɗakin, haka suke iya yin su wajen taimaka wa RAUDHA, sai da suka yi mata alluran barci sannan suka samu lafiya, amma ta karaɗe ɗakin da waje da ihun ta
Daddy kasa jure wa yayi ya faɗi ƙasa a sume, ai nan hankalin su Suhaib ya sake tashi da jin abinda ke faruwa
A wani ɗakin aka kai Daddy aka soma ba shi taimakon gaggawa, sosai jinin sa ya hau, ga shi yana buƙatar hutu, dole suka yi masa alluran barci don ya samu ya huta ko jinin sa zai sauka
Abun tausayi idan ku ka ga Suhaib, ya hana kansa sukuni duk ya tsangwami kan sa, shima ba don jarumta da ƙarfin hali ba; da tuni ya zube, sai Farida da ke ƙarfafa masa gwiwa tana masa nasiha akan ɗaukan ƙaddara. tabbas haka Allah ya so ƙaddaran RAUDHA ce, dole wannan ciwon sai ya same ta, sai dai su yi wa Allah godiya tare da roƙon Allah ya taƙaita abun haka.
Wajen awanni uku Daddy yayi a kwance, sannan ya farka. duk yanda likitoci suka so ya zauna ya sake huta wa a ɗaura masa drip amma yaƙi, nan ya soma buga waya ya hau yi mata cuku-cukun yanda za’a yi a fita da ita Abroad, sai dai basu samu ba, tunda ko wani ƙasa ance a dakata da zuwa, shi kansa Nigeria an rufe, dole Daddy ya bar ta anan asibitin, sai dai ya samu an yi masa hanyar likitoci ƙwararru waɗanda za su iya kula da RAUDHA
Abun ka da ma su kuɗi, a washe gari sai ga likitocin sun iso, nan aka duƙufa wajen duba RAUDHA, sosai take samun kulawa wajen likitoci, sai dai kamar ma ƙara haukan take yi, domin ciwon ci gaba yake ba baya ba, ta kai yanzu ɗaure ta ake yi a jikin ƙarfen gadon, sabida idan ta tashi daga alluran barcin da ake mata, ta rinƙa hauka kenan tana fashe-fashen kayan ɗaki, ko kuma tayi yinƙurin guduwa dole sai an kamo ta, har kayan jikin ta take yagawa, sai dai a sauya mata wani.
Bazan iya misalta muku halin da bayin Allan nan suke ciki ba, har wani rama suka yi sabida tashin hankali, babu abinda su Daddy da Suhaib suke yi sai dana-sani, dana-sanin barin RAUDHA cikin shaye-shaye, ga shi yanzu ta haukace suna ji suna gani, kuma kuɗin su be iya ba ta lafiya ba, babu yanda za su yi yanzu sai bin ta da addu’ar samun lafiya, wuni kuwa cikin yin ta suke yi, duk idan suka zo asibitin nan sai sun zubar da hawaye
Gefe ɗaya ma Rayyan duk ya shiga matsanancin damuwa sosai, duk a sabida ciwon RAUDHA, sosai yake matuƙar ƙaunar ta, ko barci ba ya iya yi sabida tunanin ta, da shi ake yin duk wani zirga-zirga na neman maganin ta, ya kasa hankalin sa gida biyu, a hankali shima a tsaye yake rame wa duk a sabida damuwar da ya ɗaura wa kansa.
Yanzu haka dole aka mayar da RAUDHA asibitin mahaukata tunda abun yafi ƙarfin asibitin, an ware mata ɗaki daban a matsayin ta na ƴar gata, sai dai su Daddy su je can su riƙa duba ta, su kansu likitocin ma su kula da ita daban ne aka ajiye mata.
Wasa-wasa sai ga RAUDHA ta shafe watanni huɗu a asibitin mahaukata, tana fama da mugun ciwon da ba ya baya sai dai gaba, kullum-kullum gaba ciwon nata yake yi ba baya ba, duk wani magani an yi mata amma har yanzu ba’a dace ba, ba’a taɓa samun ranan da aka wayi gari an samu nasarar ci gaba wajen samun lafiyan ta ba, sai dai gaba abun yake yi, da sarƙa ake ɗaure ta, abun mamaki kuma sai da safe a zo aganta a kwance. likitan da ke duba ta sosai yake mamaki idan ya zo ya ganta a kwance tana zaune tayi ta ɓaɓɓaka masa dariya.
Yau ma kamar kullum a kwance ya ganta, sai dai kuma abun mamaki a saman cilling ya hange ta tana ta kwasan dariyan dake fita tamkar na mutane goma, ga shi ɗakin yayi duhu sosai sai uban sanyi tamkar ƙanƙara
Da sauri likitan ya kunna wutan ɗakin yana me mamakin “ta ya ɗakin zai yi duhu bayan yanzu yamma ne ba dare ba?”
Can ya hange ta a sama tana yawo tana wannan dariyan me ban tsoro. Da sauri ya bar ɗakin don kiran sauran ƴan uwan sa
A time ɗin ne Daddy da Suhaib suka zo duba ta
Nan likitan yayi kiciɓis da su, sai ya miƙa musu hannu suka gaisa sannan ya kai su office ɗin sa ya ajiye su, sai ya fita ya bar su suka koma tare da wasu Doctors ɗakin da RAUDHA take ciki
Har a time ɗin tana saman tana shawagi tana wannan mahaukacin dariyan da yake karkasuwa da yawa, suna shigowa ta kallo su da idanuwan ta masu tsananin haske tamkar an ƙara musu haske, har wani walwali suke yi kamar an kunna tocila
Sosai likitocin suka tsorata da wannan al’ajabin, har za su koma sai ɗayan ya dakatar da su
Kamar ƙiftawar ido sai ganin ta suka yi ta koma ƙasa a yashe, gashin kanta ya rufe mata fuska duk ya barbaje
Shi babban likitan shi ya ƙarisa gaban ta ya yaye mata gashin kanta, sai dai da alamun ba ta numfashi, duk inda yakamata ya taɓa don jin tana numfashi amma alamu sun nuna ta sume ne, dama ta saba haka, sai tayi wajen kwana biyar tana barci, ko kuma ta dena numfashi gaba ɗaya, hakan na basu mamaki, amma basu alaƙanta hakan da komi ba, tunda gashi result ɗin su na nuna musu ƙwaƙwalwan ta ta samu matsala sakamakon ƙwayoyin da take sha, kuma koda yaushe suna mata gwaje-gwaje amma abu ɗaya suke gani, duk maganin da zasu ba ta still dai babu ci gaba.
Sake ɗaure ta suka yi da sarƙan, kafin suka soma aiki akanta, bayan sun gama suka fito daga ɗakin, likitan ya nufi Office ɗin sa da su Daddy ke ciki, yana shiga ya sake ba su haƙuri da zaman jiran sa da suka yi, sai da suka sake gaisawa sannan ya soma musu bayani, kamar dai ko yaushe babu wani ci gaba da ake samu
Gaba ɗaya ransu duk a matuƙar damuwa suke sauraron likitan, kullum abu ɗaya yake faɗa musu, duk kuma hanyan da zai kawo yace a gwada, idan an gwada ɗin abu ɗaya ne babu sauƙi, gashi kuma babu yanda za’a yi a fitar da ita wani ƙasan, nan kuma asibitin yana ɗaya daga cikin asibitin da yafi ko wanne ƙwararrun likitoci na masu hauka, da ba don haka ba da tuni sun sauya mata wani wajen, su yanzu har sun fawwala wa Allah komi, sabida kullum babu ci gaba
Ajiyan zuciya likitan ya sauke yana kallon su, sai da ya ɗan ja fasali kafin yace, “sai dai Ni akwai shawaran da nake so in baku idan babu damuwa”.
“Menene likita? Ka faɗa ko wani shawara ne idan har hakan zai kawo samun lafiyan ɗiya ta, muna maraba dashi”. Cewar Daddy da tsantsan damuwa a maganar sa
“Eh to Ni dai a haƙiƙanin hange na da nayi, ciwon ɗiyar ka ba na asibiti bane gaskiya, duba da yanda kuke ta wahala da ita, mu ma kuma muna yi wajen treating ɗin ta, amma kuma har yanzu babu ci gaba, sai kuma abinda ke ɗaure min kai a tattare da ita, musamman idan na je inda take, hakan yasa nayi tunanin tabbas ciwon ta akwai yiwuwar shafan aljanu a tattare da ita, ba wai zan ƙaryata cewa ƙwaƙwalwan ta be taɓu bane a sabili da shaye-shayen da take yi, tabbas hakane, sai dai kuma idan har akwai aljanu a jikinta, to, tabbas babu ta yanda za’a yi maganin da muke mata ya warkar da ita, duba da yanda aljanu suna irin hakan a jikin Mutum, zasu lafe su hana tasirin duk wani magani a jikin ta, haka za’a yi ta wahala da ita a kasa gane meke damun ta, ya kamata a gwada na Islamic tunda an kasa dacewa anan ɗin”.
Daga Suhaib har Daddy zuba ma doctor idanu suka yi suna sauraren sa, har sanda ya dire bayanin sa babu wanda yayi yunƙurin magana, gaba ɗayan su sun tafi ga tunanin abinda ya sa tun farko ba su yi wannan tunanin ba.Sun daɗe a wajen likitan yana musu bayani, har yayi musu hanyar wani babban Malami dake garin Zaria, kuma sun amince zasu gwada ɗin ko Allah zai sa a dace.+
Sai da suka duba RAUDHA kafin suka bar asibitin.
A cikin kwana biyu har an gama shirye-shiryen yanda zasu tafi da RAUDHA zuwa Zaria, tunda an rigada an sanar wa malamin kuma ya ce a kawo ta, gaba ɗayan su zasu yi tafiyan har Farida, tunda dama gida ne zasu koma shiyasa zasu tafi gaba ɗaya
Rayyan ya so ya bi su, sai dai yanayin aikin sa bazai bar sa ba, dole ya haƙura ba don ya so ba.
A jirgi suka isa Zaria, gidan Daddy suka sauka inda anan ne Malamin zai zo ya riƙa duba ta, bisa alfarman da Daddy ya nema a wajen sa, (Chemist) cibiya ce babba suke da shi a Zarian, wanda aikin su ne cire ma mutane aljanu
A ranan da suka zo, a ranan ne Malamin da zai duba ta shima ya iso gidan, a time ɗin RAUDHA na barci ne sabida alluran barcin da aka yi mata daga can asibiti, saboda samun sauƙin tahowa da ita
A tare da Daddy da Suhaib suka raka sa ɗakin da aka ajiye RAUDHA, sai da ya nemi abubuwan da yake buƙata wajen su, sannan ya zauna ya saka mata magani a cikin kasko, ta yanda idan har tana da aljanu dole zasu bayyana kansu idan turaren ya shiga hancin ta
Ilai kuwa, ana saka wa sai ta farka a firgice, gaba ɗaya zubo musu idanu tayi tana kallon su tamkar zata cinye su, sabida yanda ta waro idon nata waje, sai yamutsa fuska take yi tana cije baki
Malamin ta kafa ma idanu, wanda shima ita yake kallo, nan da nan idanun ta suka soma sauya kala zuwa ja, sai ta kawar da kai ta koma ta kwanta batare da ta sake ko motsi ba
Su dai su Daddy suna zaune akan sofa suna kallon ta, ko wannen su ya buga tagumi
Ajiyan zuciya Malamin yayi kafin ya kalli su Daddy yace, “tabbas yarinyan ka tana da aljanu a jikin ta, da alamu dai manya ne, saboda duk wanda na saka mishi maganin nan, dole ne su tashi a lokaci ɗaya su bayyana kansu, amma kuma ita ba haka ba, sai dai ta yanda ta farka ɗin nan, da kuma yanda idanuwan ta suka sauya kala, to, tabbas tana tare da su. Insha Allahu zamu fara aikin mu nan ba da jima wa ba idan abokan aikina sun zo, zamu fara mata ruƙiya ne su fara bayyana kansu, sannan mu san abun yi”.
Suhaib da Daddy jinjina kai suka yi alamun gamsuwa.
Suna nan zaune Sai ga wasu Maza su kusan biyar sun shigo ɗakin
Malamin kallon su yayi yace, “su zauna su soma karatun”.
Gaba ɗaya zama suka yi suka zagaye RAUDHA da har yanzu tana kwance idanu a rufe taƙi motsawa
Karatu suka soma yi da ƙarfin muryan su. sun daɗe suna karatun amma RAUDHA bata yi wani motsi ba, su kuma basu fasa karatun ba, sai da suka ɗau kusan mintuna talatin suna karatu kafin ta soma wani irin gurnani har yanzu idanun ta a rufe, hakan yasa suka sake dage wa suna sake ɗaga murya, nan da nan ta soma ihu tamkar wani ƙaton gardi, kukan yana fita ne kashi-kashi wanda baza ka gane na mutane nawa bane, kukan kawai take yi bata motsa ba, kuma idanuwan ta a rufe
Sai malamin ya tashi ya matso kusa da kanta, ya soma yin wasu addu’o’i yana tofa mata akai, yayinda sauran mutanen suka ci gaba da karatun Alqur’ani da iyakan ƙarfin su, idan suka zo wasu ayoyi na jinnu sai suna maimaita wa kafin su wuce
Addu’o’in da Malamin ke tofa mata, shi yasa ta buɗe idanunta da suka sake matuƙar girma tamkar ba nata ba, sun sauya kala zuwa kore, jajja-jajja, sai kawai ta soma ɓaɓɓaka dariya nan da nan ta tashi tayi sama tana shawagi, take ta tsaga wani uban ihu da ya razana su gaba ɗaya, ba su kaɗai ba gaba ɗaya gidan sai da ya amsa sabida ƙarar ihun nata. Babu shiri Daddy da Suhaib suka miƙe tsaye suna zazzare idanu sabida tsoron da ya shige su, ai nan suka soma addu’a jikin su na rawa, ga shi babu daman fita sabida Malamin sai da ya saka aka kulle ɗakin
Malamin kallon abokan aikin sa yayi, yayi musu nuni su ci gaba da karatun, yayinda shima ya ci gaba da karanto addu’o’i waɗanda zasu saka su bayyana kan su
Kuka ta soma yi sosai a wannan lokacin, sai dai babu hawaye amma gaba ɗaya idanun nata sun sauya kala, ko ɗigon fari ba’a gani, sai shawagi take yi a saman tana wani irin tururi tamkar ana dafa ta, hayaƙi sai fito wa yake yi a jikin ta
Karatun su ke yi, ita kuma tana ƙara yawan ihun nata, gaba ɗaya ta cika ɗakin da kuka ko karatun nasu ba’a ji.
Malamin sosai ya gane aljanun masu taurin kai ne akanta, sabida duk yanda suka yi karatun, sun ƙi yin magana sai kukan da suke yi, daga ƙarshe ma sai taci gaba da ɓaɓɓaka dariya, idan ta gaji kuma sai ta koma kuka, sun shafe wajen awa biyu ana abu ɗaya, sai daga baya da suka ji ayoyi na ƙona su, sun ji azaba na ratsa su sosai wanda baza su iya jure wa ba, sai ta faɗo ƙasa da ƙarfi ta kurma uban ihu, cikin ƙaton murya na gardi take cewa, “ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu”. Abinda take ta ambata kenan, har muryan ma ta koma tana faɗa ahankali sabida tsaban wahala
Gashi sun ƙi dena karatun
Sai ta koma kuka da hawayen ta tana roƙon su sosai
Nan malamin ya ba su daman dakata wa, sannan ya soma tambayan su “su wanene akan ta?”
Amma sai taƙi yin magana ta kafa wa Malamin idanu, idanun ta na zubar da hawaye
“Baza ku yi magana bane?” Cewar Malamin yana kallon ta shi ma
Sai ta ɓarke da dariya me fita muryoyi da yawa, nan ta miƙe da gudu tayi bakin ƙofa ta soma jijjiga ƙofan, kankace me ta kusa cire ƙofan, domin har ya ɓanɓaro tana shirin cire shi, nan suka yi kanta suna riƙe ta, tana bizgewa tana ihu, duk ta gama bibbige su
Su Daddy babu inda jikin su ba ya rawa, yau sun ga tashin hankali.
Daƙyar suka riƙe ta suka dawo da ita cikin ɗakin, haka suka soma kici-kicin kwantar da ita don su danne ta, amma sun kasa, sai ta fara zagin su tana musu gargaɗin “idan basu sake ta ba, sai ta halaka su”
Malamin ganin dai tana son fin ƙarfin su, sai ya ɗauki waya yayi kiran wasu daga cikin malaman su, sannan ya kalli Daddy yace, “idan da hali ku ƙaro mana mutane, sabida tana ƙoƙarin guduwa ne, kuma tabbas idan har ta fice a ɗakin nan da akwai matsala”.
Jikin Daddy na rawa, ya umarci Suhaib ya kira masu aikin gidan maza su shigo
Dasauri ya fita ya kira su, sai ga su kusan su shida sun shigo
Nan Malam ya saka su duk suka taru wajen kwantar da RAUDHA, amma sun gagara, gaba ɗayan su sun kai su goma sha biyu kenan, amma sun gagara kwantar da RAUDHA ƙasa, ihu kawai take yi tana fizge-fizge, duk wanda ta samu ta mazge shi
Karatu suka ci gaba da yi suna danne ta tana kuka da ihu. Ba su yi nasaran kwantar da ita ba sai da wasu daga cikin malaman suka shigo, kusan su huɗu ne, Malamai ne su ma masu cire aljanu, tare suka dage daƙyar suka danne ta a ƙasa, suka hau karatu babu ji babu gani, sosai suka wahalar da ita, kukan ma wani irin kuka take yi tamkar na mage, gaba ɗaya tayi yaushi sai fitar da huci take yi, amma tsabar taurin kai taƙi magana.
Wani magani malamin ya samu ya fesa mata, take ta sandare tamkar ranta ya fita, sai kuma ta fashe da sabon kuka tana buɗe idanuwan ta daƙyar, ta hau roƙon sa wai “za su fita”.
“Ƙarya kuke yi mugaye azzalumai, uban me tayi muku da kuka shiga jikin ta, ku ka wahalar da ita har haka, tsawon lokaci kun haukatar da ita, shin ku wasu irin mugaye ne, na ce uban me tayi muku ne?” Yaƙarike maganar cikin tsawa
Cikin kuka tana nishi tace, “wlh babu abinda tayi mana, kawai muna son ta ne, tayi mana ne shine yasa muka shige ta”.
“Tayi muku? Dama akwai wani abun da ya haɗa jinsin mutum dana aljanu ne?”
Tari ta soma yi babu ƙaƙƙauta wa, gaba ɗaya idanuwan ta sun gama juye wa, sun ƙara tsananin ja har babu kyan gani
“Shin zaku sanar damu ne meyasaka kuka shige ta? Ko kuwa sai mun ci gaba da gana muku azaba?”.
Shiru tayi taci gaba da tarin ta, yi take yi babu ƙaƙƙauta wa
Malamin kaɗa kansa yayi, kafin ya kalli sauran ya ce, “ku ci gaba”.
Nan da nan suka ci gaba da karatun Alqur’ani, shima yana ci gaba da addu’o’i
Atake anan taci gaba da kuka tana shirin bige su ta gudu, haka suka danne ta sosai suka hana ta tashi, kuka take yi sosai tana ihu, har da su majinu, ta jigata iya jigata sai ta hau zagin su tana faɗin, “wlh idan basu sake ta ba, sai ta kashe su”. Amma ko sauraron ta basu yi ba. Sun shafe tsawon lokuta suna karatun, kafin ta soma ba su haƙuri akan zata yi magana, amma malamin ya hana su dakata wa, sai da ta sha baƙar wahala ta sake yin yaushi sosai, ta yanda duk wani taurin kanta sai da suka yi maganin shi, kafin malamin ya saurare ta ya ce, “to ina ji zaku faɗa dalilin da yasa kuka shiga jikin ta ne ko kuwa sai na ƙona ku gaba ɗaya na kashe ku? Shin ku nawa ne ma ajikin nata?”
Cike da tarin wahala cikin wani irin babban murya tace, “muna da yawa a jikin ta, kuma Ni ne mijin ta, Ni na fara shiga jikin ta, sannan sai na jawo ƴan uwana su ma suka shiga jikin ta”.
Jinjina kansa Malamin yayi kafin ya ce, “har ma ka zama mijin ta kenan, sannan saboda tsaban mugunta sai ka jawo ƴan uwanka suka shiga jikinta don ku cutar da ita ko?”
Girgiza kai ta soma yi tana hawaye, sai tayi shiru taƙi magana
“Ina jin ka zaku yi magana ne ko sai na ƙona ku?”
“Zamu yi Malam, zamu yi”. Tafaɗa cikin mawuyacin hali tana juya idanuwa
“Kar ku sume mana anan, ina sauraron ka yi magana”.
Shiru tayi tana rufe idanuwan ta tamkar ba ta numfashi
Malam ya sake watsa mata wani farin magani
Sai ta buɗe idanunta, sun koma fari a yanzu ɗin tamkar nata, cikin siririyan muryan ta da ya gama dishewa tace, “Daddy”. Idanun ta akansa
Ai da sauri Daddy ya nufo wajen shima yana kiran sunan ta
Malamin ya dakatar da shi yana faɗin, “ba ita ba ce, suna son Raina mana hankali ne, ku muci gaba da karatun”.
Karatun suka ci gaba da yi, sai ta soma kuka, sai da taji azaba kafin ta ce, “kuyi haƙuri don Allah, wlh baza mu ƙara muku taurin kai ba, duk zan faɗa maka abinda ya sa muka shiga jikin ta”.
“To ina sauraron ku”.
“Tun farko abinda ya fara jan hankali na akanta sabida ba ta ibada, sannan tana shigan banza, tana barin kanta a buɗe, shine yasa na kamu da sonta, kuma na shiga jikin ta, sai na jawo ƴan uwana muka shiga, sannan sai suka ɗaura mana aure dani da ita”.
“Shin kai Musulmi ne ko kafiri?” Malamin ya sake tambayar sa
“Ni ba kafiri bane, amma ba mu Sallah, kuma tunda muka shiga jikin ta mu ke hana ta yin Sallah, tunda dama ba ta yi sai ta ga dama, wannan dalilin ne muka sake mayar da ita me wasa da Sallah, daga ƙarshe muka rinjaye ta muka hana ta Sallah”.
“To tun yaushe kuke jikin ta?”
“Mun daɗe sosai, tun tana ƙarama”.
Malam ya ce, “kenan duk ku kuke saka ta shaye-shaye har kuka samu damar haukata ta ko?”
“Wlh ba mu bane, amma dai mun san mun ba ta gudunmuwa, ko tana son bari sai mu hana ta, mu riƙa saka ta tana son sha koda yaushe”.
“To yanzu meyasaka ka aure ta bayan kasan babu aure a tsakanin mu da ku?”
“Ai na ce maka ina son ta ne, tayi min ne”.
Malam ya ce, “to yanzu zaku fita ne ko kuwa kun samu wurin zama ne baku da ninya?”
Shiru tayi tana ci gaba da hawaye
“Ina magana kuna ji na, muna son ku fita a jikin ta, ku bar ta ta huta tunda kun rigada kun azabtar da ita”.
“Malam wlh ina ƙaunar ta, ita matata ce”.
“To shine yanzu na ce ka sake ta ku fita a jikin ta, tun kafin in azabtar da ku”.
Shiru tayi taƙi yin magana.
Daƙyar Malamin ya samu Sa’a suka amsa za su fita, shima sai da ya gama gana musu azaba sosai sannan ne suka ce za su fita, ta hanci suka fice, sai faman atishawa take yi, daga baya kuma ta hau barci babu ji babu gani+
Malamin sallaman mutanen yayi, sannan ya soma magana da su Daddy daga shi sai su, anan ya soma ba su shawara akan yanda za su kula da tarbiyyan ta, sabida ya kula kaso saba’in cikin ɗari duk laifin su ne, inda ba ta shigan banza da duk hakan bata faru ba, ita ta soma janyo hankalin su gare ta, kuma ga shi daga ƙarshe ita tasha wahala. Sosai yayi musu nasiha tare da shawarwari, sannan kuma ya ce za su riƙa zuwa ana amsar mata magani don ba zama za’a yi, ko wani lokaci za su iya dawowa idan har ba’a ci gaba da nema mata magani ba, don ya kula taurin kai ne da su, ya san ba su yi nisa ba, tun daga nan ya fara ba su magunguna da za tayi sirace da shi, sannan ya ce musu “idan sun ga ta tashi hankalin ta be da wo ba, dole za su mayar da ita asibiti saboda aci gaba dana asibiti, tunda dama ƙwayoyin da tasha sun birkita mata ƙwaƙwalwa, dalilin aljanun ne har yanzu ana magani babu ci gaba
Sosai suka yi wa Malamin godiya, har waje Daddy ya raka sa tare da ɗumbin alkhairai da ba ya faɗuwa.
Suhaib na ɗakin da RAUDHA take kwance ya tasa ta gaba yana ta kallo, har Daddy ya dawo shima ya zauna kusa da shi, tsawon lokaci suna ahaka idanuwan su akanta, kafin Daddy yaja numfashi yace, “tabbas mun aikata babban kuskure tun farko, ga shi son zuciya ya saka mun yi wasa da tarbiyyan ta, soyayya ya rufe mana idanu daga Ni har kai mun kasa wa Baby tarbiyya irin ta addinin musulunci, duka laifin mu ne, kuma insha Allahu daga yau za mu gyara, Allah mun gode maka da ka taƙaita abun haka”.
“Gaskiya ne Daddy, laifin mu ne gaba ɗaya, sabida son da muke ma Sweetheart yasa ba ma hana ta, shiyasa ta tashi bata san bari ba, duk abinda take so shi take yi, ga shi abinda ya faru daga ƙarshe, Allah ka yafe mana”. Suhaib yafaɗa yana share hawayen sa
Daddy hannu ya saka yana buga bayan sa tare da ba shi baki. Sun jima a ɗakin ba su tashi ba, har sai da aka kira sallah tukunna suka fito suka tafi masallaci, bayan sun saka su Saude su zauna a ɗakin da RAUDHA take ɗin.
Bayan sun dawo ne ta farka, sai dai yanda take yi ne suka gane da akwai matsala har yanzu, dole suka ɗauke ta suka yi da ita asibiti, anan aka sake duba wa aka gane har yanzu tana da matsala a ƙwaƙwalwan ta, amma kuma ba wani sosai bane, don ba sai an dangana dana asibitin mahaukata ba
Duk wani abinda Yakamata an yi mata, daga ƙarshe aka ba ta gado har zuwa sanda za ta warke.
Haka rayuwa taci gaba da gudana, inda RAUDHA tana kwance a asibiti tana amsar magani, kuma ana kan mata na Islamic, da sannu-sannu suka soma ganin sauyi a gare ta, tunda har tana iya gane su tana banbance su, sai dai magana ne ba ta yi sai dariya, to an dai ci gaba da yin mata magani har zuwa sanda ta shafe tsawon watanni biyu a Hospital ɗin, kafin ta samu lafiya.
Su Daddy sun yi murna matuƙa sai godiyar Allah suke yi
A zaman ta a Hospital ɗin, zuwan Captain Rayyan sau uku yana duba ta, shima don babu time ne aiki na hana sa zuwa sosai, amma da Suhaib ya kira sa ya sanar masa samuwar lafiyan ta har za’a sallame su, ya ji daɗi sosai, sai dai babu damar zuwa ya duba ta, haka yayi mata fatar alheri suka rabu.
Koda suka koma gida an dai ci gaba da yin mata magunguna don ba’a zauna haka nan ba, tun ba ta saba wa har ta saba, ita da kanta take yin kayan ta, irin su sirace, shafa magani a jiki, shan zuma, shan wannan da wannan duk ta saba
Sosai RAUDHA ta sauya gaba ɗaya tamkar ba ita ba, duk da dama ba ta da hayaniya sosai, amma yanzu ta sake zama so silent, wuni tana maƙale jikin Daddy ko jikin Suhaib, haka za su zauna su yi ta mata hira ita kuma tana murmushi, har su gama hiran na su, daƙyar take iya yin magana sau ɗaya ko sau biyu
Kayan sakawan ta, gaba ɗaya Daddy ya saka an kwashe, an sauya mata da sababbi, dogayen riguna duk aka siyo mata, sai kuma irin Pakistan ɗin nan riga da wando, tunda dama bata iya shigan Hausawa ba shiyasa ma be haɗo mata da atamfofi ba, amma ƴan kanti da Arabian gown duk su aka siyo mata.
Itama Ramcy sosai take zuwa duba ta, tunda ta ji labarin dawowar ta, har waya suna yi yanzu
Farida ce me kula da ita sosai, sai da ta sake samun lafiya sosai da sosai sannan Suhaib ya tarkata suka koma Abuja
Dayake ana hutun Corona babu school sai zaman gida, haka rayuwan taci gaba da gudana har sanda aka shafe kusan shekara ɗaya da samuwar cutar, sannan aka soma buɗe makarantu anan Zaria da sauran garuruwa, wasu ma garin sun daɗe da buɗe wa, don haka itama RAUDHA ta sanar da Daddy tana son koma wa school, sai dai tace ba ta son zaman Abuja tafi son Nan kusa da Daddy, tunda shima yana gida ba ya zuwa ko ina
Da ya nemi ra’ayin ta akan school ɗin da zata shiga
Sai ta ce masa tana son abroad ne
Da sauri Daddy ya kalle ta ya ce, “haba Baby taya zan bar ki ki je wani ƙasa karatu bayan kin san halin da ake ciki yanzu? Ga kuma halin da kika shiga a baya, ki zaɓi dai inda kike so anan don ba na son kiyi nesa dani”.
Shagwaɓe fuska tayi ta hau buga ƙafa a ƙasa tana hawaye
Janyo ta yayi jikin sa ya hau rarrashin ta, sai da ya ga taƙi haƙura, don daga ƙarshe saka mishi kuka tayi, sosai yake ƙaunar ta, domin soyayyar ta bazai iya bari yana gani tana neman abu ya hana ta ba, sai yace mata, “yi shiru to, faɗa min wani ƙasa kike so ki je umm Baby na?”
Cikin shagwaɓa tace, “Daddy Saudia zaka kai Ni, can nake so sabida in koyi addini sosai, tunda ka ga ban iya komi ba, ka ga idan na je can zan shiga school ɗina, sannan zanna riƙa islamiyya sosai a can”.
Washe baki Daddy yayi yana sake rungume ta ya ce, “iyeeeee ashe Baby na ta girma haka? Ashe kina da wayau? Good dear gaskiya naji daɗin zancen ki”.
Dariya ta ƙyalƙyale dashi cike da farin ciki itama
Nan Daddy yayi ta nuna farin cikin shi, kafin yayi mata alƙawarin zai nema mata insha Allahu idan har an dace, tunda a time ɗin ba kasafai ake bari fita Abroad ba, su ma can ɗin ba sa bari a shigo musu ƙasa.
Koda Daddy ya sanar da Suhaib shima yayi murna sosai, sai dai kuma ba su so tayi nisa da su har haka ba, amma kuma sun san can ɗin zai fi nan, tunda zata je ta nemi ilmin addini ne, kuma can shine garin musulunci, ta yiwu idan ta dawo ma ta zama wata Malama Sheikhiya, hakan da suke tuna wa shi ke saka su jindaɗi sosai.
Babu jima wa Daddy ya soma mata cuku-cukun fitar da ita zuwa Saudia, sai dai ba’a saki hanya ba har yanzu, dole Madina zata tafi tunda can anfi barin mutane zuwa, Saudia kuwa ko ƴan zuwa hajji an hana su zuwa.
Da labarin tafiyan ta ya iske Rayyan, ya shiga wani hali sosai, har faɗa sai da yayi wa Suhaib wai “akan me za su tura ta wani ƙasa bayan sun san halin da take ciki? Kuma yanzu sai su ƙara barin ta tayi nesa da su?”
Sosai Suhaib yayi mamakin faɗar Rayyan ɗin, har dai ya ce, “wai Dude ko dai akwai abinda kake ɓoye min ne a game da Baby?”
“Kamar ya fa?” Cewar Rayyan ɗin
“Ina nufin faɗan yayi yawa, ko matar ka ce sai haka ai”.
“Ok kana nufin Ni ban isa inyi mata faɗa a matsayin yayan ta ba ko?”
“A’a ba haka nake nufi ba, ina..”
Cike da ɓacin rai Rayyan ya tari numfashin sa da faɗin, “haka kake nufi mana, Ni ban isa da ita ba, kana son ka nuna min banbanci tsakani na da ku, tunda har ku kun yarda Ni kuma asuwa da zan hana ta”.
“Haba Dude wlh baka fahimce ni bane, meye na zafi haka abinda be kai ya kawo ba?”.
Ƙitt ya kashe wayan
Sosai Suhaib ya sake mamaki da halin da Rayyan ya nuna masa, ya san shi ba mutum bane me yawan ɗaukan zafi akan abu, idan kuwa ka ga fushin sa, to, tabbas ba abu bane ƙanƙani, har yana mamaki da kasancewar sa ya zaɓi soja, domin kuwa ko kusa aikin be kamace sa ba, yana da sauƙin hali sosai, idan har ba ka ƙure sa ba ne, to shine zaka ga ainihin waye shi, a nan ne zai nuna maka haukan sa tuburan.
Sake kiran sa yayi, daƙyar ya amsa call ɗin, sosai Suhaib ya ba shi haƙuri
Shi kuma a lokacin shima ya sauko kaɗan, don ba kaɗan yayi fushi ba, har yanzu baƙin cikin tafiyan RAUDHA wani ƙasa ne ke nuƙurƙusan shi
Anan suka shirya har suna taɓa hira kafin su kashe wayan, aran Suhaib dariya kawai yayi ya ce, “uhmmm idan tayi tsami ma ji”.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Komi na tafiyar RAUDHA ya gama kammaluwa
A washe garin ranan da zata tafi haka Ramcy ta zo ta wuni mata har zuwa dare, sannan ta tafi.
Washe gari Daddy da Suhaib da ya zo don yin sallama da ita, su suka kai ta har airport, sai da tayi ta kuka kafin ta yarda ta shiga jirgin
Ahaka suna ɗaga mata hannu har jirgin ya tashi, sai da dukan su suka share ƙwalla kafin suka juya suka shiga motan su, suka bar wajen ko wannen su cike da kewar RAUDHA.
AFTER FOUR YEAR’S.*+
Gaba ɗaya haraban airport ɗin ya cika maƙil da jama’a, ciki kuwa har da ƴan jaridu waɗanda suka zo domin samun rahoto, sabida zuwan Jikan Sarkin American da zai bayyana a ƙasar ta mu
Sai dai kuma jami’an tsaro sun hana kowa shiga cikin haraban airport ɗin, har ta da ma su zuwa ɗaukan ƴan uwan su, sai dai suka faka motocin su daga can nesa
Suhaib na ɗaya daga cikin mutanen wajen, yana tsaye jikin motan sa yana jiran saukar jirgin, sosai idan ka kalli fuskar sa zaka ga bayyanuwar tsantsan farin cikin da yake ciki a wannan ranan, saboda dawowar ƙanwar ta sa.
Koda jirgin ta gama sauka sai mutane suka fara fito wa, can na hango wata kyakykyawar cikakkiyar kamilalliyar budurwa tana sauko wa, a ƙalla shekarun ta bazai wuce 24years ba, tsananin kyauwun ta da hasken ta sai da duk wanda ke haraban wajen idan har idanuwan sa sun sauka a kanta sai ya kasa ɗauke ido a wajen ta, a zuciyar sa yana sarkake Allah da yayi wannan kyakykyawar halittan
Tana sanye da doguwar rigan abaya baƙa ce, daga saman gaban rigan har ƙasa an saka kalan ruwan ƙasa, sai aka bi wajen da kwalliyan stones masu tsananin ƙyalƙyali me ban sha’awa, ta yane kanta da ɗankwalin abayan, sai ta toshe idanunta da wani faskeken baƙin Glasses da ya sake ƙawata farar fuskar ta, sak idan ka ganta tamkar wata balarabiyya sabida shigan ta da yanayin ta, baza ka taɓa cewa ita ɗin ta haɗa jini da bahaushe ba, Bahaushen ma Bazazzage.
A hankali take taka matattaƙalan benen, wanda hakan yayi matuƙar ƙosar da matashin saurayin dake bayan ta, shi ɗin yana sanye da riga da wando baƙaƙe ne ma su tsananin kyau da tsada, ya saka rigan sanyi ja me hula, wanda hakan yasa ya rufe kansa da hulan, tare da saka faskeken Glasses a fuskar sa, wanda ya ba shi damar ɓoye fuskar sa gaba ɗaya. Sosai ya ƙosa da ya bar wajen tun kafin asirin sa ya tonu, shi ɗin mutum ne da ba ya son mutane bare kallo, shiyasa ya zaɓi ɓoye kansa batare da an yi talla da shi ba.
Ta Geben ta ya raɓa ya wuce, hakan yasa ya ɗan bige ta har wayan hannun ta ya so kubce wa, sai dai tayi saurin tare wa tana ɗago kai tabi bayan sa da kallo, wanda shi tuni har ya ƙarisa sauka kan benen ma
Dogon tsaki taja, ahankali ta furta, “Useless”.
Tsakin nata kaɗai yaji, don haka ya juyo don ganin wacce har ta samu damar iya masa tsaki. Akan kyakykyawar fuskar ta ya sauke, sai kawai ya ware idanun sa sosai yana kallon ta
Ita kuwa a time ɗin ma ta mayar da hankalin ta kan wayan ta tana latsa wa, har tazo ta wuce sa batare da ta sake bi ta kansa ba, ba ma tasan Allah yayi ruwan tsakin sa ba
Be dena kallon ta ba, har sanda ta ɓace wa ganin sa, sai kawai ya saki numfashi da sauri da sauri, kasancewar tun tozali da ita da yayi ya ɗauke numfashin nasa, be taɓa ganin yarinyan da ta tafi da imanin sa kamar wannan ba, duk kuwa da cewa ya ga ƴan mata bila adadin waɗanda suka fi ta kyau da komi, amma shi dai wannan ɗin ta daban ce a wajen sa. Yana tsaye ya kasa motsawa a wajen har sai da good 5 minutes ta shuɗe, sannan a hankali ya taka ya bar wajen yana sake rufe fuskar sa da hulan kansa, inda ya ga tabi nan yabi amma kuma ko me kama da ita be gani ba, hakan yasa ya nufi wajen ƴan Taxi ya hau ɗaya suka bar wajen.
🌐🌐🌐
*RAUDHA* na fita wajen airport ɗin, ta hangi Yayan ta mafi soyuwa a birnin zuciyar ta, da sauri ta ƙarisa wajen sa sai ji yayi an rungume sa
Wani irin farin ciki ya sake kama sa ganin ƙanwar ta sa rungume da shi, ai nan da nan shima ya rungume ta yana me sake nuna farin cikin ganin ta
Ita kuwa sai faɗin “I Miss You so Much Yaya”. Take yi, bakin ta ya ƙi rufuwa sabida tsaban murna
Ɗago kanta tayi tana kallon sa, cike da washe haƙora tace, “Yaya ina Daddy be zo ba?”
“Baby Daddy yana gida, Ni kaɗai na zo ɗaukan ki”. Suhaib yayi maganar yana shafa kanta shima bakin sa har kunne
Har zata yi magana sai wasu maza biyu masu uniform a jikin su, suka ƙariso mata da Trollys ɗin ta da tasaka su ɗauko mata
Ganin su da akwatin sai Suhaib ya je ya buɗe musu Boot suka saka mishi, sannan ya biya su suka bar wajen, shi kuma ya buɗe mata gaban motan ta shiga, ya zaga ya shiga suka bar wajen.
A cikin mota surutu RAUDHA ta dinga yin masa yana biye mata, tamkar ba ita ba domin ta sauya sosai fiye da da, duk da a yanzu ɗin ba ta yawan surutu ga kowa idan ba da su ɗin ba, har yanzu halin ta na nan na rashin sabo da mutane
Shekaru huɗu kenan ta shafe a ƙasar Madina, abubuwa da dama sun sauya a tattare da ita, duk wani halin ta mara sa kyau ta dena gaba ɗaya, tunda ta je karatu kawai ta saka a gaba, bata da aiki sai karatu sai research akan addinin ta, kafin ta shiga makarantar islamiyya sai da ta shafe kusan shekara da zuwan ta, a time ɗin ta gama sanin wasu abubuwa sosai a addinin ta, sannan daga baya ta shiga islamiyya, makarantun da ta shiga guda biyu ne duk islamiyya, idan ta je boko ta dawo sai ta wuce can wani Islamic school, sai dare take koma wa gida, da weekend ma school ɗin da take zuwa daban ne, babu nisa da inda take zaune
Lokaci ƙanƙani RAUDHA ta gama sanin komi sabida ta saka abun a ranta, dama ga ta da ƙwaƙwalwa, a lokaci ƙanƙani tayi suna sosai a ko wani school da take yi, musamman ma boko.
Su Daddy suna kawo mata ziyara akai-akai, kuma sun ji daɗin yanda take mayar da hankali fiye da tunanin su
Kankace me harshen ta ya gama juye wa irin na larabawa, larabci a bakin ta kamar ruwa, sosai take son harshen shiyasa duk abinda zata yi, tafi son tayi magana da harshen larabci akan ko wani yare, sabida school ɗin da take yi ana karatu ne da English and Arabic
Sometime tana tambayan su Daddy idan suka zo mata ziyara, akan su taho mata da Ramcy, sosai take kewar ta, yawan tambayan ta da take yi ne, Daddy har ya yanke shawarar tambayan mahaifin ta, idan har zai bar ta taci gaba da school, shi kuma zai biya mata makaranta ta koma can wajen RAUDHA ɗin, amma kuma sai Baban Ramcy yace be yarda ba, shi ba ya son ɗiyar sa tayi nesa da shi, hakan ya sa Daddy ya yanke shawaran biyan mata taci gaba anan A.B.U Zaria, kuma akayi Sa’a Baban ta ya amince. Sau uku tana zuwa kai wa RAUDHA ziyara, wani lokacin idan Suhaib zai je sai ta bi shi, wani lokacin kuma Daddy ke tafiya da ita. Itama dai taci gaba da school ɗin ta anan kamar yanda Daddy ya alƙawurta zata yi, yanzu haka kusan watanni bakwai da gamawar ta, har an saka mata rana yanzu saura wata ɗaya bikin ta.
🌐🌐🌐
Suhaib na yin parcking motan, RAUDHA ta buɗe ta fito, cike da zumuɗi ta nufi hanyar cikin gidan
Suhaib na mata dariya yana faɗin “baza ta jira sa ba ta tafi?” Amma ina ba ma taji sa ba, burin ta kawai ta isa ciki ta haɗu da Daddyn ta
A hanya duk ta gama gaisa wa da wasu daga cikin ma”aikatan gidan. Suna mata murnan kammala karatu, ta amsa su cike da farin ciki. Su kansu sun yi mamakin sanja war RAUDHA. Bata bi ta kansu ba ta shige da gudun ta da ya zame mata jiki
Ai kuwa Daddy na zaune a parlour’n ƙasa, yana ganin ta ya miƙe yana mata waƙa yana dariya
Da gudu ta ƙarisa gare sa ta rungume sa tana faɗin, “Daddy na Ni kaɗai! Daddy na da yafi na kowa”.
Still dariya yake yi yana cewa, “na’am my dear daughter, Ina miki murnan kammala school ɗin ki lafiya, Allah ya miki albarka”.
“Ameen Daddy”. Ta amsa shi tana sakar mishi peck a kumatu kamar yanda larabawa suke yi, bakin ta a washe
Time ɗin ne Suhaib ya shigo, bayan sa ma’aikata suna jaye da akwatunan ta, ajiye wa suka yi suka bar wajen, yayinda su kuma suka zauna akan sofa suna ƙara gaisa wa tare da tambayan ta school da inda ta baro
Nan ta washe baki tana ta zuba musu surutu tamkar an kunna rediyo, gaba ɗaya ta haɗa su ta matse idan ta rungume wannan sai ta rungume wancan, tana faɗa musu missing ɗin da tayi nasu, tana tsakiyan su ne tana zaune
Su kuma bakin su ya ƙi rufuwa saboda murna, sai biye mata suke yi, sai da aka kira sallan magriba sannan ta tashi ta nufi ɗakin ta, su kuma suka wuce masallaci.
Tana shiga wanka ta soma yi, komi tana yin sa ne cike da kewa, sai rera waƙan “i miss You home” take yi. Sallah ta soma gabatar wa wanda ake bin ta, sannan ta ɗaura da magriba, ta saka riga da wando ma su santsi da kwalliya ta fito
A Parlour ta tarar da su zaune suna jiran ta, tana fito wa Daddy ya ce, “su hau kan dainning su ci abinci”
Zama suka yi suka ci abincin, sannan suka koma Parlour tana ta ba su labaran da ya ƙi ya ƙare, sai kuma daga baya ta soma raba musu tsaraban da tayi musu, har da nasu Farida da yaran ta biyu, Haneep da Abdullahi da ta haifa kusan shekara biyu da rabi, suna kiran sa da Abdul kasancewar sunan mahaifin Farida ne, yanzu yaran sun ta so kansu ɗaya ne tamkar ƴan biyu, har Abdul ya fi Haneep wayau yanzu sabida halin laluran da yake fama da shi, Suhaib be taho da su bane sabida akwai school na yaran, zuwa gobe weekend za su zo, ranan Lahadi kuma su koma gaba ɗaya har Suhaib ɗin.
Anan suka shantake har kusan ƙarfe 11:30pm. Kafin suka je suka kwanta.
Washe gari da wuri sai ga Ramcy ta bugo musu sammako, kasancewar har yanzu RAUDHA akwai ta da son huta wa, shiyasa idan ta kwanta tana kai wa 11:00am bata tashi a barci ba, idan har ba Lectures take da shi ba to tana wuni ne a kwance da safe, sai da rana zuwa da dare wannan kuma time ɗin karatu ne, ya rigada ya zame mata jiki har yanzu bata fasa ba.
Ramcy bayan ta gaisa da su Daddy sai ta wuce ɗakin RAUDHAN, anan ta ganta shame-shame tana barci, zama tayi ta soma tashin ta
Koda RAUDHA ta tashi, ganin Ramcy a gaban ta, ai da sauri ta rungume ta suna murnan ganin juna, ko wacce cikin su cike da kewar ƴar uwan ta, har da ƙwalla suka share
RAUDHA tace, “ana haƙƙan ishtaƙtu laki ya jamilaty”.
Dariya Ramcy tayi tace, “Besty kin manta ne, nan fa ba Madina bane”.
“Ya Salam naseetu wlh, ana asif”.
Murmushi Ramcy tayi tace, “again?”
Dafe goshi RAUDHA tayi, sai kuma ta kwaɓe fuska tace, “sorry Besty na rigada na saba, sai kin yi haƙuri dani”.
Ramcy zata yi magana, sai wayan RAUDHA ta soma ringing na waƙar larabci me daɗi
Hannu ta saka ta ɗauki wayan tana murmushi tun kafin ta kai ga duba wa, domin ta san mutum ɗaya ne ta saka mishi wannan ring ɗin. Peacking tayi ta kara a kunne, sai ta narke fuska tace, “nayi fushi Ni dai”.
Murmushi kaɗai Ramcy take saki idanun ta akan RAUDHA ɗin, sosai take tsananin burge ta da yanda ta sauya gaba ɗaya, sauraron ta take yi duk da ba ta jin abinda wancan yake faɗa, har ta gama bata ɗauke ido akan ta ba
Hakan yasa RAUDHA da ta cire wayan daga kunnen ta ta ɗage mata gira tace, “lafiya! Kallon fa?”
Still Murmushi Ramcy ta saki tace, “kina tsananin burge Ni ne, ta yanda kika iya tafiyar da soyayyar ki da Ƙalbin ki (dayake haka take ce mishi, kuma har su Daddy babu wanda be san hakan take kiran sa da shi ba, sai dai babu wanda ya san shi har yanzu), ko a mafarki idan wani yace min zaki riƙe soyayya irin haka, zan ƙaryata shi, domin kuwa na fi kowa sanin wacece ke akan yanda kika riƙe so”.
Murmusawa RAUDHA tayi tace, “ai ada ne ba yanzu ba, yanzu ke ma ba ga shi ba har an kusa a shafa fatiha? Bigaddin nazri anil waƙti, (komi da lokacin sa)”
“To yaushe ne zaki nuna mana shi, har yanzu kina min rowan shi na rasa meyasa?”
Lumshe ido tayi tana buɗe wa akan Ramcy, kafin tace, “ƙariban jiddan”. Sai kuma tayi murmushi tace, “sorry Besty, a mean very soon”.
“Ok Allah ya Kai mu”.
“Kin san naji daɗin yanda za’a yi bikin nan naki dani? Tabbas da ina school ne dole sai na ajiye na dawo”.
Ramcy tace, “wa ya isa yayi min aure babu Besty kusa? Ai wlh da bazan taɓa aure ba in dai har sai nayi aure ne kafin ki dawo, dole na saka aka ɗaga”.
“Hal haƙƙan? A mean really?” Tayi saurin sauya zancen tana ɗaura hannun ta a goshi
Ramcy na dariya tace, “yeap I’m sure, but Nima dai dole zan koya larabcin nan ko dan mu riƙa yi, tunda muna baki wahala”.
Dariya itama RAUDHA tayi tace, “ai na dawo da sannu zan rage kar ki damu”.
Daga nan hira suka ci gaba da yi, har time ɗin da Farida ta zo, sai lokacin RAUDHA ta miƙe ta shiga wanka tayi tafito, ta shirya cikin farar jallabiya me hula, ta saki hulan a bayan ta, sai ta ɗaura wani hulan daban
Parlour’n ƙasa suka sauka, inda acan suka haɗu gaba ɗaya ana ta hira, sosai RAUDHA ta maƙalƙale su Haneep tana ta musu wasa, musamman Abdul da ya fi surutu. Sosai take tausayin Haneep sabida rashin lafiyan sa, ko magana be cika yi ba, idan ya zauna ya dinga zilalar da miyau kenan, gaba ɗaya gaban rigan sa sai ya jiƙe, a rana sai a sauya masa kaya babu adadi sabida ɓata wa da yake yi, ga shi ko maganar sa ba ya wani fita sosai, hannun sa ɗaya kuma ashanye duk da yana iya sarrafa shi, wai Nan ma don an ta magani ne.
Anan Ramcy ta wuni sai dare ta tafi gida, sai gobe zata dawo tunda za’a shirya wa RAUDHA partyn murnan kammala karatun ta.
Daga airport kai tsaye Zaria me Taxi ɗin ya wuce da shi, can cikin tudun jugun; gonan ganye. A bakin tanƙamemen wani baƙin gate aka sauke sa, ya fito ya saka hannu cikin aljihun sa ya fiddo kuɗi, kuɗin irin na American ne, sai ya kalli me Taxi ɗin sannan ya kalli kuɗin, guda biyu ya zara ya miƙa masa batare da ya ce komi ba+
Me Taxi ya tsaya sakaka da baki yana kallon sa, sai kuma ya ce, “bawan Allah ban san ya zan yi da wannan kuɗin ba, kana gani wannan ai ba na Nigeria bane”.
Sai a time ɗin ya sauke hulan kansa, fuskar sa ta bayyana duk da ba duka bane, kasancewar akwai Glasses. Murmushi yayi cikin harshen sa da be gama iya hausan ba ya ce, “I know, but ka amsa idan ka sauya dana Nigeria 10k ne”.
Zaro ido drever’n yayi, sai kuma ya washe baki cike da murna ya saka hannu ya amsa, nan ya soma mishi godiya
Sai dai shi murmushi kaɗai yayi ya juya ya nufi bakin Gate ɗin, hannu ya saka ya tura small door ɗin dake buɗe
Me gadi dake zaune saman benci kusa da Gate ɗin, ya kara rediyo a kunnen sa idanuwan sa a rufe. jin ƙaran buɗe Gate, firgigit yayi ya miƙe yana nufo sa, be gane sa ba sai da ya iso gaban sa, sai ya washe baki ya ce, “ranka ya daɗe kai ne?”
Murmushi yayi masa, ya gyaɗa masa kai
“To ai an tafi ɗauko ka, baka gansu bane?” Me gadi ya sake faɗa cike da fara’a
Still Nan ma gyaɗa masa kai yayi, yayi hanyar gidan zai bar wajen
Biyo sa me gadi yayi yana mishi barka da zuwa, har bakin ƙofan shiga parlour’n ya rako sa, sannan ya juya
Shi kuma ya buɗe ya shiga, babu kowa a cikin parlour’n sai t.v dake aiki, ƙamshin daɗi ya cika ko ina, tsaya wa yayi a tsakiyar parlour’n yana bin ko ina da kallo, har hotunan dake cikin parlour’n na mutanen gidan, tare da iyayen sa da kakannin sa, murmushi kaɗai yake zuba wa yana ci gaba da taka wa zuwa cikin parlour’n.
A time ɗin ne wata matashiyar budurwa da a ƙalla baza ta fi 21years ba, ta fito daga kichen tana yarfe hannayen ta, ganin sa sai ta kwatsa ihu tana kiran sunan sa
“Yaya Zulain”.
Juyo wa yayi yana kallon ta, sai ya sakar mata murmushi yana buɗe hannayen sa alamun ta zo
Da gudu ta ƙariso cikin tsananin murna ta rungume shi
Ihun ta shine ya fito da mutanen gidan, Abba da Momy da kuma Sharif. ganin Zulain rungume da Sharifa, gaba ɗaya sai suka yo wajen sa suna me nuna murnan su da ganin sa
Nan shi kuma ya sake ta, ya bi su bayan ɗaya yana rungume su cike da fara’a
Abba na murmushi yace, “amma kuma yanzu Drever’n da na aika tare da bodyguard ɗina, suka kira Ni akan ba su ganka ba har yanzu, ashe kai ga ka har ka iso gida, ta ya ka gane hanya da ka taho kai kaɗai?”
Dariya Zulain yayi yace, “Abba kenan, ba fa yau na saba zuwa ba, kasan ba na son mutanen wajen su gane Ni, that’s why na ɓoye fuska ta na fito na hau Taxi ya kawo Ni”.
Momy tace, “ai kuwa kayi kyan kai wlh, Ni ban san ma wanda yake kiran su ba, nan muka zauna a gaban t.v muna jiran mu ga an haska ka, amma muka ji shiru, ashe kai kayi musu wayau ne ka gudo”.
Dariya suka yi gaba ɗaya, kana suka zauna suna sake gaisa wa, Abba na tambayar Iyayen Zulain ɗin da mutanen can ƴan uwa
“Abba kowa lafiya, suna gaishe ku sosai da sosai”.
“Masha Allah muna amsa wa”.
“Sharifa tashi mana ki kawo masa Drinks, kin zauna kin wani maƙale masa”. Cewar Momy tana kallon Sharifa da ta shige masa
Buga ƙafa ta hau yi kana tace, “Um um Momy! Ba ga Yaya ba ya ɗauko masa, Ni ba na son jirga wa kusa da shi”.
Sharif hannu ya saka ya buge mata baki yace, “a aike ki ki aike Ni, ina wasa dake ne?”
Zumɓura baki tayi tana shirin kuka
Zulain ya saka hannu yana shafa mata kai yace, “oh sorry my dear sister, Kar ki biye masa kiyi kuka bar sa ko?”
Tsamm Momy ta tashi tana cewa, “Ni bari in tashi in ɗauko maka”.
“Tun farko ma da hakan kika yi, da baki ɓata bakin ki ba, kin san halin Sharifa tunda ta ga Zulain ba kuma sauran aiki”. Abba ya faɗa yana murmushi
Sharif yace, “Ai Abba ƙyale ta Ni ne maganin ta wlh, in sake ganin an saka ki ki ɗauko wani abun ki ƙi”.
“Kai da baka ɗauko ba, ina ce ai duk halin ku ɗaya?” Momy tace hakan sanda ta dawo ta ajiye babban Plet a saman Centre table, janyo wa tayi ta matso da shi gaban Zulain ɗin, sannan ta koma ta zauna
Sharif dai be ce komi ba, sai saka hannu da yayi yana zuba wa Zulain Coke a cikin glass Cup
Abba ya ce, “mun yi magana da Yaya yace min zaka ɗan jima ko?”
“Yes Abba, Coz anan zan yi hutu na gaba ɗaya ma”.
“To Masha Allah, ka ga ai ka za ga dangi sosai wannan karon, da waɗanda ma suke min ƙorafin ba su sanka ba duk zaku je su sanka, ga Sharif nan tunda shima ya dawo hutun sa gaba ɗaya sai ku riƙa zuwa tare”.
“Abba nima har da Ni”. Cewar Sharifa cike da zumuɗi
Hararan ta Sharif yayi yana cewa, “wa ya saka bakin ki?”
Momy tace, “ka ji ka dai, to idan bata raka ku ba, ai ina ce duk sammakai da kai da shi ɗin, tunda kaima babu inda ka sani a dangin, dole ita zata nuna muku ko ina ku shiga”.
Gwalo Sharifa tayi masa
Shi kuma yayi ƙwafa yana ɗaukan wayan sa ya ce, “wlh Momy duk ke kike saka wa yarinyan nan tana raina Ni, amma babu komi zan yi maganin ta”.
Daga Abba har Zulain murmushi kawai suke musu
Hira suka ɗan taɓa, kafin Abba ya ce su tashi su tafi masallaci ana kiran sallah.
Ba su dawo ba, sai da aka yi sallan isha’i, inda suka zauna a dainning suka ci abinci, sannan suka dawo Parlour suka dasa hira, sai wajen goma suka watse, Zulain da Sharif suka wuce ɗakin Sharif ɗin, sai da Zulain yayi wanka ya sauya kaya sannan ya hayo kan gadon, sai dai tunda ya rufe idanuwan sa ya kasa barci, illa fuskar RAUDHA da ya bayyana masa, gaba ɗaya ya rasa sukunin sa sai faman tunanin ta yake yi, yana fata Allah ya sake haɗa shi da ita, sosai yarinyan ta hana sa sukuni har ya rasa me ke damun sa, daƙyar ya iya samu barci ya ɗauke sa, sabida ba ƙaramin gajiya ne a jikin sa ba.
Abba Ƙani ne wajen mahaifin Zulain, haifaffun nan Zaria ne, inda Mahaifin Zulain karatu ya kai sa can American, anan suka haɗu da ƴar Sarkin American ya aure ta, kuma suka ci gaba da zama a can, ɗan su ɗaya suka mallaka a duniya wato Zulain, idan ya samu hutu suna kawo sa nan wajen Abba yayi mishi hutu, har zuwa yanzu da ya girma yana aikin sa a can, sai dai yanzu ɗin be cika zuwa sosai ba sai idan ya samu hutun shekara.
Abba babban mutum ne a nan Zaria, kuma ɗan siyasa ne wanda ya ci jiya yana cin yau, kuma yana fata gobe ma a dama dashi a ƙasar, yanzu haka shi aka tsayar a takarar mataimakin Gwamnan Kaduna, yaran sa uku, Hauwa’u me sunan Maman Abba, suna kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yaran ta biyu, sai Sharif da yanzu yake aiki a Abuja, shima yanzu haka an saka mishi rana, sai kuma Sharifa da yanzu ne take aji na biyu a A.B.U Zaria
Tun farko ita Allah ya ɗaura mata ƙaunar Zulain sosai, shiyasa take shige masa sosai har suka saba matuƙa, idan ta samu hutun school can American take zuwa tayi hutun ta, hakan ya sa suka sake shaƙuwa fiye da tunanin mutum, har wasu suna musu kallon akwai soyayya a tsakanin su, ba su san cewa shi Zulain yana mata kallon ƙanwa ce kaɗai, shi a rayuwa babu ruwan sa da mata idan har ba ƴan uwan sa ba, sai dai ya taɓa yin soyayya da daɗe wa, har ya so ya auri yarinyan, sai dai Allah be yi ba ta mutu, yarinyan dangin sa ce a can American, kuma Christian ce, tunda dama itama har yanzu mahaifiyar sa bata musulunta ba, to su a wajen su babu komi idan har ya auri ko wace irin yare ce.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*SATURDAY*
Yau ce ranan da za’a yi wa RAUDHA partyn kammala karatun ta. Gaba ɗaya gidan an yi masa decorations, sosai ko ina yayi kyau gunun sha’awa, a bayan gidan a cikin Garden ɗin wajen za’a yi, sosai wajen ya matuƙar haɗuwa, ga shi an kashe kuɗi, komi green and red aka sanya a wajen.
Zuwa ƙarfe 04:00pm. Har mutane sun soma zuwa gidan, duk da ba wasu gayya ne a kayi ba, domin dai RAUDHA bata da ƙawaye illa Ramcy kaɗai, sai ita Ramcy ɗin da ta gayyaci ƴan gidan su, sai kuma Daddy da Suhaib su ma da suka gayyaci mutanen su na nan Zaria kaɗai, ciki kuwa har da Abba za su zo da su Sharif, tunda dama Abba abokin Daddy ne, tare suka yi Siyasa kafin Daddy ya fita, jam’iyyar su ɗaya, ta dalilin hakan ne Sharif da Suhaib suka san juna har suka zama abokai, to abokan takan nasu tayi ƙarfi ne sanda Sharif ya koma Abuja da zama yana aiki, shiyasa suka ci gaba da zumunci sosai.