SILAR AJALI CHAPTER A

 SILAR AJALI CHAPTER A

Kwance ta ke kan gadon karfen ta, zuciyarta na bugu fiye da bugun sa, cikinta na murɗa mata tamkar mai shirin gudawa, duk da haka kwakkwaran juyi ma kasa yin shi ta yi, tsoro ne fal a cikin ranta Kasancewar ba ta san abinda daren yau zai zo mata da shi ba .

Da ya ke wata ya kai ashirin da shida, duhun daren ya wuce misali, gari yayi baki kirin ko ganin tafin hannunta bata yi. Sassanyar iskar bazara da ke kaɗawa,da kuma kugin iska da ke tashi daga rassa da bishiyoyin kankarar bai hana zufa keto mata ta koina daga jikin ta ba, sai ma tsoron da ya ke daɗa shiga cikin ran ta don har ganin kamar gilmawar inuwar mutum take hakan ya sa ta kara gimtse idanunta gam, don bata ma son tsautsayi ya sa ta buɗe su. Duk da dai ba ta san takamamman lokaci a yanzu ba, ta san dai akalla karfe ɗaya na dare zai yi.

“Ba shakka ya kusa zuwa, yanzun kuwa zai zo”

Ta faɗa a ranta don kuwa kusan sati daya kenan a jere ya kan zo mata Idan ta na bacci sai dai kawai ta ji hannaye na bin kafar ta ko ma jikin ta, da fari ta yi zaton ko tunanin ta ne ko kuma aikin aljanu ne, sai da ta kama hannu ta rike kamin ta tabbatar da mutum ne ba aljani ba.

Ko da ta fadawa Yagana, wato babbar ɗiyar kanwar mahaifiyar ta wacce ta ke hannun ta, ita kuma ta ba ta shawarar ɗaukar mataki.

Jin kamar an tura kyauran ɗakin, gaban ta ya faɗi , ta yi karfin halin daɗa jawo goran da ta ajiye kusa da ita hannu na rawa, sannan ta yi lamo kamar mai bacci. Kusan minti goma ne ya shuɗe ba tare da ta ji wani abu ba, har ta fara tunanin tsoronta ne kawai, ilai kuwa sai hannu ta ji yana shafar kafar ta, daskarewa tayi a nan wajen don kasa numfashi tayi tsabar firgita, ji ta ke rayuwarta ta zo karshe don duk tattalinta wani na shirin wargaza mata rayuwa duk da karancin shekarunta.

Ta na jin hannun na shafa ta, har aka zo ga cinyarta, ganin hannun na yin gaba-gaba fiye da kullum ya sa ta yi saurin ɗaga sandar ta rantama dai-dai saitin da take tunanin mai hannun na wajan.

Ta ko ci sa’a dan kuwa ihu ta ji an saki, hannun na rawa ta ɗauki fitilar toci ɗin da ta b’oye karkashin matashin kai ta kunna don ta tabbatar da muryar da kunnuwanta suka jiyo mata. Kunnawar da tayi yasa hasken ya garwaya ɓangaren da ta haska cikin ɗakin.

Nan take idanun ta suka sauka a kansa in da ya ke kwance ya na burgima, jini ya wanke fuskar sa sanadiyar fasa masa kai da ta yi. Ganin hasken ya sa shi tashi zai fice a guje…..kan ya kai ga bakin kofa, ya ji muryar ta da ke kakkarwa, cike da mamaki ta ke furta

“Baba…..Baba…Baaaaba”

Dakatawa yayi, sai da yai jim na wasu dakiku kana ya juyo ya na mai watsa ma ta wani irin mugun kallo, nan ta kara tsorata ganin irin raunin da ta ji masa, sannan ya fice da sauri.2

Cike da tsoro, ta kasa ko motsa yatsanta balle ta nemi tashi daga inda ta ke dan kuwa sam ba ta yi zato ba, ba ta taɓa tunani ko kawo abin cikin zucuyar ta ba

“Baba! Baba!!!!! Baba fa…….”8

Abin da ta ke ta maimaitawa cikin zuciyar ta kenan amma kwakwalwarta ta kasa ɗauka, don kuwa idan har Baba zai iya aikata mata wannan mugun aiki haka, toh wa za ta yarda a duniyar nan?

***

Washagari da asubar fari ta ji hayaniyar Baba da Inna, wacce ke cikin ɗanyen jego, hayaniya ce ke tashi daga tsakar gida wanda ya sa Sauran mutanen gidan firfitowa don jin ba’asi da samun rahoton kai wa gaba, abinka da gida ba su kadai ba, gida na haya mai ɗauke da ɓangare ɓangare har goma.

Hakan bai sa Baba ya sassauta ko ma ya dai na kururuwar da kumfar bakin da ya ke ba, Jin ana buga qyauren ɗakin da ta ke, ya sa ta tashi da sauri ta na mai raba idanu.

STORY CONTINUES BELOW

“Za ki fito kokuwa sai na shigo na fito da ke yar nema gantalalliya”

Faɗin Baba kenan ya na mai kumfar baki da haki kamar in ta qara wasu mintoci zai ɓalle kofar ne ko ma fushi ya kai shi ga rusa ginin gaba xaya. Jin haka ya sa ta fitowa da sauri zani a hannu ko ɗankwali bata tsaya ɗaurawa ba.2

Baba ta gani tsaye bakin kofa, Inna rike da jinjirinta ɗan sati biyu tsaye ta na zubda hawaye, ga kuma sauran yaran Inna biyar,suma ɗin kuka su ke, duk da dai kananun ba wani fahimtar abin da ke faruwa su ka yi ba, ganin hawayen Inna ya sa su kuka. Sai kuma sauran jama’ar gidan da su ka fito jin kwakwaf.

Ba kunya ba tsoran Allah Baba ya dube ta yana mai mazurai tare da faɗin

“Faɗa mu su da bakin ki, abin da ya faru jiya”

Da sauri ta ɗaga ido ta kalleshi, duk da dai yarinya ce qarama ta san a iya tunanin ta wannan ba magana ba ce da za’a yi ta gaban jama’a ba, dan haka sai ta yi saurin yin qasa da idanun ta,ta ba tare da tayi magana ba. Shi kuwa Baba dama abin da ya ke so kenan, dan ya san a zahiri ba za ta iya buɗe baki a cikin jama’a haka ta tona masa asiri ba, dama da gangan ya tambaye ta dan ya samu ya ɗaure ta da hakan.

Tun da hakan sa ya cimma ruwa, buɗar bakin sa sai cewa yayi

“shegiyar kaya, dama ai ba kya iya magana ba! Toh ke Amina (Inna) ga ta nan, dama na faɗa mi ki in dai wannan hatsabibiyar yarinyar ce sai ta sa ki kuka da idanun ki, gashi tun ba’a je ko ina ba ta nuna halin ta, yanzu sai ki tasa ta a gaba ta miki bayanin gun wa take zuwa duk tsakar dare na duniya, sati guda kenan ina ganin ta, jiya da daddare ko da na bi ta a baya, saɗaf saɗaf na ga ta buɗe kofa ta fice. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayanta, don ni a gani na yarinyar nan amana ce gun mu, ko ma menene ya same ta mu mu za mu ji a jiki, ashe yarinyar nan fako na ta ke, ta haɗa baki da kwarton da ta ke gani, ban ankara ba sai saukar gora na ji bisa kai na, ku duba ku gani ya fasa min kai……..”

Ya qarasa yana mai fashewa da kuka.3

Gaba ɗaya wajen ya kaure da hayaniya, kowa na faɗan albarkarcin bakin sa, wasu na faɗin za ta aikata, wasu kuwa faɗi suke abin da mamaki, dan kuwa yarinya dai natsattsiya ce, kuma dai mutum babba kamar Baba ba zai yiyu ya yi karya ba.

Ita kuwa don mamaki kasa magana ta yi, baki na rawa ta ke duban Baba da ke ta faman kukan munafunci. Inna ce wacce ta kasa gane komai, ta ce da ita ta shiga ɗakin ta, yanzu za ta biyo ta. Ta juya za ta shiga kenan Baba ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar tare hanyar da za ta kai ta ga ɗakin ya na faɗin

“Lillahi warasulihi yarinyar nan sai ta bar min gida a yau! ke ba ma ita ba, har sauran shegun yan uwan na ta!”2

Jin haka Inna na fidda kwalla ta ce

“Shegu fa ka ce Malam! yanzu yaran yar uwar tawa ce kake kira da shegu, wani asiri naka ne bata rufe ba?”

Ya shiga kif-kifta idanu ya ce

“Su kuwa, na ce wanene uban su? ko kin taɓa ganin sa bayan ga labarin kanzan kurege da ta aiko mi ki na ta yi aure a Saudiyya, ta auri ɗan Sudan, sai kuma bayan shekaru biyar ta turo miki yara har uku, wai saboda tsada da wahalar rayuwa ki rike mata su, ina ki ke da tabbacin da gaske auren ta yi? idan auren ne uban su ko dangin sa su riqe mata su mana! wallahi sai sun bar min gida! su je can idan ma hali irin na uwar ta ta za ta yi ba dai a gida na ba!” ya na faɗin haka ya rufo kofar ɗakin Inna.

Kuka Inna ta sa, dan kuwa ya kwance mata zani a kasuwa, haka ma yarinyar da tabbas ko Baba bai ce su bar masa gida ba ta san zaman gidan dai ya kare musu, ba ma gidan ba garin kano gaba ɗaya, dan kuwa dai ta san kafin gari ya waye tuni sunan su da aka san su da shi zai ɓata a koma kiran su da shegu. Da wannan ɗacin a ran ta juya a guje ta shige ɗakin ta, ta shiga haɗe yan kayan ta cikin Ghana must go, ta na yi ne ta na kuka har ta gama haɗa kayan, ta zauna a saman jakan kenan sai ga yan uwanta maza biyu sun shigo, babban wanda kallo ɗaya zaka masa ka san ya girme mata, shi ke dauke da jakan kayan su, karamin da ko gama watsakewa bai yi ba fuskar sa duk yawun bacci ko ina ya ce da ita

STORY CONTINUES BELOW

“Didi wai Baba ya ce mu bar masa gida, ina zamu Didi? Ko wajen su Mama za mu?yaushe za mu ga Mama Didi?”

Ya fashe da wani sabon kuka mai. Karya zukata. Hannun sa ta ja ta na mai faɗin

“Kar ka damu autan, Allah shi ne gatan mu”

Babban kuwa bai iya furta komai ba, jakan hannun ta ya karɓa su ka fito tsakar gida in da Baba ke tsimayen su, haka ma sauran yan gulma. Ga shi dai an tada sallar asuba amma gulma ya hana su zuwa masallaci.

Gaban Inna ta je ta durkusa, ta na mai neman gafara. Ganin haka shima karamin yayi hakan yayin da babban ya kara rike hannun jakan tare da sunkuyar da kanshi don baya so kowannen su ya ga rauninsa. Inna na kuka ta rungume ta,kana ta ce da Baba

“Malam ka yi wa Allah ka yi hakuri ka bar yaran nan”

Baba ya gyara tsayuwa sannan ya ce

“Kin san Allah,wallahi sai sun tafi,yanzun nan ma kuwa!”

Nan fa mokota su ka yi yunkurin sa baki, amma Malam yayi kyememe ya hana. Inna ta kwance gefan zanin ta,ta fiddo da kuɗin cinikin ta na daddawa ta mik’a masa , kana ta ce

“Gashi kuyi kuɗin mota zuwa Katsina sai ku je MARKE, ku je wajen salame kun san ko da ace kowa zai guje ku salame ba za ta taɓa guje muku ba don ita ta haifi uwar ku, akwai wasu dangin mu a nan unguwar Gwammaja, amma ban san tak’amamman in da su ke ba, da can zan ce ku je ku neme su, Allah ya fishe ku alkahairi”

Hannu biyu ya sa ta karɓa, nan fa kowa ya shiga ba su abin da ba’a rasa ba, mai Ashirin, hamsin har naira ɗari. Inna ta k’ara rokon Baba da ya bari gari ya k’ara wayewa sa tafi,tun da yanzun asubahi ne. Maimakon ya amsa mata, sai ma tasa su gaba da yayi, Inna da yaran ta na kuka, haka ma yarinya da yan uwanta ta,har su ka fice daga gidan.

Sai da ya tabbatar ya raka su har bakin titi kafin ya juya ya bar su cikin halin ko in kula. Babban ne ya dubi yarinya ya kira sunan ta da

“Salma”2

Ta na me goge hawaye,ta amsa da

“Na’am, Ya Salman, wallahi Baba sharri ya ke min, shi ne fa duk dare sai ya shigo min ɗaki…..”

“Yi shiru da maganar nan Salma, za mu yi ta amma ba yanzu ba, tun da kin tsira da mutuncin ki shikenan ai,kan sa ya yiwa. Yanzu ɗaura kayan ki bisa kan ki, bari na goya Suhayl, dan mu yi sauri, kin ga mik’ak’k’iyar tafiya ce a gaban mu, Allah ya taimake mu, mu sami mota tashin farko a tasha” Da wannan Salma ta aza kayan ta bisa kan ta, Suhayl a bayan Salman, ga kuma sauran kayan na su a hannun shi, su ka sa hanyar tasha a gaba. Tun gari na da sauran duhu har gari ya waye tangararan.

Ba k’aramin tafiya su ka yi ba kafin su k’arasa tasha. Duk da safiya ce tashar ba laifi akwai mutane da dan dama, ga motoci jere direbobi sai ihun neman passenger su ke, ga kuma yan kabu-kabu da dako, wanda da sun ga mutum ɗauke da kaya sai su yi kan sa da sauri su na mai riga-rigen karɓan kayan domin yin dako. Haka kuma yan tallan abubuwa Iri-iri kamar su koko, gyad’a da dai sauran su, da kuma mai tuyan kosai.

Ganin su Salman ɗauke da kaya yan dako su ka yi kan su da sauri. Salman ya dakatar da su ta hanyar ɗaga musu hannu ya na mai faɗin

“ku bar mana kayan za mu iya d’auka”

Jin haka su ka bar su da kayan su suna masu faɗin

“Dan bakin ciki sai ku rike tsiyar ku ai!”

Wani ne ya k’araso gare su ganin sun yi cirko-cirko tsakiyar tasha, ya na duban Salman ya ce yaro ina kuka nufa ne? Buɗarbakin Salman sai cewa yayi “MARKE aka ce mu je, cikin garin Katsina” kai mutum ya gyad’a ya ce motar Katsina za ku hau kenan, golf za ku hau ko bus?golf dai dubu ɗaya ne ko wani mutum ɗaya , bus kuma ɗari biyar.

Ba tare da wani dogon tunani ba Salman ya bashi amsa da

“Bus din zai fi”

Dan kuwa ya san nauyin aljihun su ba lalle kuɗin da ke hannun su ya kai su ga hawa bus din ba. Mutumin ne ya kai su har bakin bus ɗin, in da ya umarci Salman da ya kawo kuɗin motar na su. Ko da ya haɗa ɗan kuɗin da ke hannun su sai ya ga dubu ɗaya ce cis. Ya nemi a musu ragi mutumin nan yak’i, dan kuwa haka su ke karbar kudin kowa. A k’arshe dai sai kuɗin maneji ya biya mu su ɗari uku-uku, sannan su ka sami matsuguni cikin motar.

STORY CONTINUES BELOW

Ɗarin da ta rage a dole ya siya mu su k’osai da pure water, dan kuwa yunwa su ke ji, bare Suhayl da tuni ya fara mu su kukan yunwa dan kuwa ba ya jure yunwa.2

Sai da motar ta yi awa ɗaya har da ɗoriya kafin su gama lodi a ɗau hanya. Zaman na su Salma sam ba daɗi sun takura kwarai, jere su ke kan maneji, kafafun su a takure ga wani turiri da ke tashi ta tankin motar, ga shi mai motar ya kwashi mutane da kaya da ya fi karfin motar. Ga haniya da kukan yara da ke tashi ciki, amma hakan bai hana Suhayl gyangyad’awa, shi kuwa Salman gaba ɗaya tunanin sa ya ta’allaka ne kan yanda za su yi su je MARKE neman dangin mahaifiyar su, idan suna da rai kenan, ko da yake baba salame na nan a raye.

Tafiyar awa biyu sai da su ka yi ta awa uku, saboda lodi da rashin gwabi na motar, ga kuma hanyar ba kyau. Isar su Katsina a babban tashar garin aka sauke su. Tashar cike ta ke fam da jama’a, matafiya da wanda su ka iso, yan talla da yan dako, jami’ai ma su kula da tashar, almajirai da kuma yan zaman banza. Hayaniya da cikowa na jamar tashar ba karamin firgita Suhayl ya yi ba, tuni ya kudunnune rigar Salman idanun sa na shirin kawo ruwa. Su kan su Salman da Salma hankalin su ba kwance ya ke ba, musammam ganin yanda yan dako ke ta kawo mu su harin daukar kayan su, Salman na hanawa, haka kuma masu abin hawa na ta mu su tayin hawa babur din su, wanda ke kira “Adaidaita Sahu” amma su ma din sun ki yi.

Sai da ya ga jama’ar sun dan sarara, tukun ya tsada wani dan saurayi ya na mai tambayar hanyar da za su bi ya kai su ga unguwar Marke.

Saurayin ya na mai duban sa ya ce

“da gani dai ku baki ne, MARKE ai gari ne chan a karamar hukumar Dan Musa, ko daga nan zuwa chan ai awa biyu ne, ba motar Katsina ya kamata ku shigo ba ai don kuwa da ta hanyar Gwarzo zaku bi sai Dayi junction daga nan sai ku biyo ta Gora zuwa kankara daga Kankara sai Yan tumaki, sai Danmusa, yanzu kun san inda zaku shiga motar?” ya tambaya yana mai kallonsa

Salman ya girgiza kai sannan ya ce “Ah ah,a kasa za mu je ai,hanya kawai mu ke so a nuna mana”

Dariya saurayin yayi, har da kyakyacewa kafin ya ce “Gaskiya ne mutumin kauye, ka tabbata bako a garin nan shi ya sa ba ka san girma da fad’i irin na jihar Katsina ba, kai idan ka ce za ka silafa har MARKE da k’afa kai kaɗai ma ba tare da yan uwan nan na ka da kayan nan ba, ace ka fita tun safe ba ka isa ka kai marke ba sai ka wuni ka kwana a hanya, bare kuma da su, ai sai kun yi kwanaki! Kai ni ina da abin yi, in da za ka rage ciki ka biya a kai ku toh, ni ka ga tafiya ta!”

Su na ji suna gani saurayi ya wuce su ya na mu su dariyar kyeta. Salman ya yi jigum ya zubawa sarautar Allah ido. Ga wata rana da ake zubawa wanda ta haddasa mu su azababban k’ishin ruwa. Ga shi kuma ko karyawar kirki ba su yi ba, shi kan shi Salman bakar yunwa ce ta sa cikin shi a gaba, bare Suhayl da Salma. Ilai kuwa nan take Suhaly ya sa mu su kukan yunwa. Salma ce mai iya rarrashin sa, shi kuwa Salman wajen ɗaya daga cikin masu yunifon ɗin yuniyo ya isa, ya nemi da ya taimaka ya kai su marke, amma fa fisabilillahi, dan kuwa kwandala ba sa magani. Cike da takaici ɗan yuniyi ya fatattake shi, ya na mai zargin sa da mutuwar zuciya, matashin yaro kamar shi ya ce a kai shi har marke a kyauta!

Da dai Salman ya ga babu sarki sai Allah, inuwa ya ja su Salma da Suhaly din da har lokacin be daina kukan yunwa ba, ya ce su zauna su jira shi, kada Salma ta yarda ta kula kowa, ta kula da Suhaly, bara ya je ko dako ne ya yi, sai ya samo mu su na abinci da ma na mota gaba ɗaya. Da haka ya bar su zaune, ya kutsa cikin tasha. Ya ci sa’ar samin dako har sau biyu, ana ba shi naira hamsin,domin kuwa tashar cike take da yan dako ko ta ina. Da ya sake gwada sa’ar sa be samu ba, sai kawai ya k’arasa wajan mai abinci ya siya mu su shinkafa da wake, wajen mai abuncin ya tsinci gorar ruwa mai tambarin faro,ya d’auka ya d’auraye. Ciki ya taro mu su ruwan sha.

Ganin abincin ba karamin murna Salma da Suhayl su ka yi ba, kan kace mai tuni sun far ma abinci. Ganin ba zai ishe su ba Salman ya bar musu su ci su biyu, ya sake kutsawa cikin tasha, ya na mai fatar barin tashar kafin la’asar, azahar har ta kawo kai, gashi zaman Salma cikin tashar ke ɗaga masa hankali, dan kuwa mutane ne iri iri ciki, ba ka san waye mugu, waye na gari ba.3

Lokaci lokaci ya ke samin dako,ya na yi ya na duba su Salma, a haka har azahar ta yi, ya sa su ka yi sallah. Kan la’asar ta k’arasa kuwa Allah ya taimaki Salman ya had’a kud’in sa har d’ari biyar da hamsin. Ya na mai share zufar da ya haɗa ya ke tsadancewa da ɗan yuniyo din Ɗazu don a ɗauke su a maneji, wanda shi kuma ya dage a lalle sai dai Salman ya biya shi d’ari uku, a hakan ma wai sauki ya masa. Da kyar da magiya, Salman ya masa bayanin halin da su ke ciki, sannan ya yarda za’a kai su din a d’ari biyu. Su ka jera kayan su a baya, Salma ta fara shiga, Sahayl ya bita sai Salman a kusa da kwansasta. Nan direba ya tayar da mota kasancewa motar ta cika, Salman na mai sauke ajiyar zuciya.

Sai karfe tara na dare suka samu isa gidan Goggo Salame kamar yanda mutane suke kiranta. Tafiya ce mai tsawo daga Katsina zuwa marke, ga rashin sanin takamaiman wajen zuwa hakan ya haddasa ma Salman damuwa ga yunwa yana ji hakan ya sa siraran hawaye gangarowa daga idanunsa. Da tambaya da ɓatan hanya suka iso gidan Goggo Salame wacce da farko kin sauraransu tayi sai da suka faɗa mata daga inda suke.

Faɗi take

“oh ni Salame, yanzu duk tsawon lokacin nan kuna wajen Amina bata taɓa nuna min ba. Ita uwar taku kuma abinda ta zaɓa ma kanta kenan. Allah ya shirya”

Ta sa musu tuwo da miyan kuka bayan ta tabbatar da sun watsa ruwa don kauda dauɗan da su kayi. Ci suke kamar wanda suka Share Shekaru babu abinci, nan take tausayinsu ya dira a zuciyar ta karo na farko tun bayan isowarsu gidanta. Bayan sun gama ci ta mika musu tabarma sannan tayi masu jagora zuwa ɗaya ɗakin da ke kallon tsakar gida. Suna godiya gaba ɗaya suka shige ba tare da ɗaukan lokaci ba barci ɓarawo yayi awon gaba dasu.

***

Washegari, tun bayan asuba Salma bata koma ba, gari na yin haske ta fito ta Share tsakar gidan tas, sai a lokacin ta kare ma gidan kallo. Tsakar gida ne sai ɗaura biyu da ke kallon tsakar gidan, chan daga yamma kuma akwai ɗaki amma da gani rabon da ɗakin ya amshi bakoncin mutane an manta.

“Haba, Salama, kya bari ki huta mana , ai kin san kina cike da gajiyan jiya kin fito kina ta aiki” Goggo ta faɗi tana kallon Salma.

Fara ce siririya, shekarunta basu wuce goma sha biyu ba, amma tsawon kafarta ya zarce na sa’o’inta. Gashin ta ya leko ta Kasar kallabinta, murmushin da Salma tayi don ba Goggo ansa ya sa kumatunta lotsawa nan take hawaye ya fara sintiri a idon Goggo tunawa da mijinta da tayi saboda wajen sa Rahanatu ta yi gado gashi ya bayyana a jikin jininta. An take bakin ciki ya cika mata zuciya tunawa da tayi da SILAR AJALIN mai gidanta masoyinta.

Juyawa tayi fuuuuu zuwa cikin daki kamar guguwa, sakin tsintsiya Salma tayi ta bita da na mujiya, in har ba idon ta ya gwada mata karya ba hawaye ta gani a idon tsohuwar. Toh ko me yasa? Taɓe baki tayi ta ɗauki tsintsiyar ta cigaba da shara. Sai da ta Share gidan tsaf sannan ta yi wanka ta chanza kaya, haka ma sauran yan uwanta.

Bayan sun gama cin abinci Goggo ta sa suka shirya ta kai su gidan yayanta hakimin Marke Alh Yunusa Ladan, ko da suka shiga, falonsa ta wuce bayan ta gaisa da matan sa, da sallama suka shiga falonsa, bayan sun gaisa ne take ce da shi,

“sai ka ganni da yara ko? Yaran yarinyar nan ne, jiya Amina ta turo su da yake chan wajenta ta kai su a Kano, wai mijinta ya gaji da rikonsu” ta faɗi cikin Yanayin ɓacin rai ko a ce bata son magantawa

“Dama kin san da zaman su ne, ina ce tun Shekaru goma sha takwas da ta bar garin nan bata sake dawowa ba, ko ta dawo ne bani da labari, kuma ina ta samo yaran da zata turo miki ki amsa” ya faɗi rai a ɓace. Bai tsaya jin ta bakin ta ba ya cigaba da cewa,

“ko akanta aka fara fyaɗe, duk wanda aka mawa shiru suke yi su rufa ma kansu da iyayensu asiri, amma ta kunso ciki sannan a ce fyaɗe, amsa min salame dama kin san da zaman su ne ko kuwa kin san da auren da tayi ta haife su” ya faɗi yana kara huhhura hanci da zare idanu.

Numfashi ma a tsorace su Salma ke fitarwa Salman ne mai karfin hali da jarunta, kukan da suka saki ya kara ankarar dashi zaman su a wajen.

“ku fita ku ban waje yayan gaba da Fatiha” ya faɗi a tsawace yana mai nuna musu hanyar kofa. Cirko Cirko suka taradda matan gidan a tsakar gida kasancewar sun ji duk abin da ya ke faɗi a ɗakin.

“Yaya ban san da zaman su ba sai zuwan da Amina ta yi bara wancan, kasan cewa gwamnati ta biya musu aikin haji, a can suka haɗu da RAHANATU ɗin wai tayi aure, da zuria. Kasancewar tsadar rayuwa a can ba irin na mu na nan bane bayan dawowarsu da yan kwanaki ta turo yaran. Yanzu shekaran su biyu kenan da dawowa. Kayi hakuri yaya, bani son ranka ya ɓaci sannan ni kaina ban ɗauki zancen Rahanen da mahimmanci ba wallahi. Kayi hakuri” ta faɗi tana kankantar da kai alamun neman gafara.

“in ba zata zo ba inaga za’a tura mata Yaranta. Bana son shiririta, a yi rainonta ayi na Yaranta, Sam ba zai faru ba” ya karasa alamun nuna ya sauko daga Fushin.

“kun ga kuyi hakuri ku yi shiru, in Goggo ta kore mu bamu da wajen zuwa, kun san dai sai an shiga jirgi za’a je inda innarmu ta ke, kuma ko a chan ɗin babu wani tsaro, amma ai tace mana zata zo ai ko” Salman kenan yake rarrashin Salma da Suhayl da suke ta kuka tun tsawan da ɗan uwan Goggo yayi musu, nan suka ɗaga masa kai alamun gamsuwa, shi kuma ya cigaba da cewa,

“Kunga in ta dawo baza mu yarda ta koma ba sai da mu, kuyi hakuri banda kuka banda riko, ba zaku gane gatan da Goggo tayi mana ba sai a gaba. Kunga dole muyi hakuri da ita “

Tashi su ka yi zuwa gareshi ya rungomo su. Haj Aziza uwargidan yayan Goggo nan take ta ji tausayin su da kaunar su ya mamaye ta, ba tare da ɓata lokaci ba ta ja su zuwa ɗakin ta. Sannan ta karɓa musu zoɓo da atine amarya ke siyarwa ta ba su suka sha.

“kar ku damu kunji nan gidan kakanku ne, dangin mqhaifiyarku kenan bata da kamar mu haka ku ma, Insha Allahu ba zaku yi dana sanin dawowa nan ba kunji. Duk abin da kuke so ku zo waje na kunji. Ba kuma zaku rasa ba Matukar bai fi karfi na ba.”

Nan take zuciyar su ta fara haske, murmushi ya bayyana a fuskokinsu hakan ya sa ta cikin farin cikin da bata san dalilin sa ba.

Ko da Goggo ta shigo ɗakin bayan sun gama tattaunawa da Yayan ta hakimi, zama tayi suka sake sabon gaisuwa da hajiya.

“Yaran nan dai amana ne a gare ki da mu duka, in kika yarda aka raba ki dasu kamar yanda aka raba ki da uwar su ke kika so, don na lura har yanzu Sam baki san ‘yancin da musulunci ya baki a matsayin mutum ba. Shi da ya aikata mugun aikin ba wanda ya tsangwama ma rayuwarsa sai su da ya nakasa” faɗin Hajja Aziza bayan sun gama gaisawa.

“kai matar yaya, kullum ke dai maganar ki yancin mata, ai musulunci bai yarda mu dinga fito na fito da maza ba, namu ko da yaushe hakuri ne, shi da ya yi fyaden ai ado ne macece dai bai kamata ta fita ba balle har a ganta ayi mata fyade, kin manta har haddi aka yanke ma malam, Allah ya masa rahma” ta faɗi tana murmushin da kallo ɗaya zaka masa ka san cewa iyakarta fatar bakinta..

“Musulunci ya ba maza da mata yancin neman ilimi, haka zalika fita aiki. Matsalar mu mata ba ma zurfafa ilimi sai ayi amfani da al’ada a dankwafar da mu da sunan addini. Laifin RAHANATU fita neman ilimi ko a ina aka karanta mata kar su nemi ilimi, mata sun rike mukamai a zamanin annabi ke mace sai da ta zama shugaban kasuwa, Umar ibn Al-Khattab da kansa ya zaɓi Samrah bint Nuhaik ta shugabanci kasuwa, Khadija yar kasuwa ce amma annabi bai hanata ba, Nusayba bnt kaab Alansariyya jaruma ce da ta fita jihadi da takobi. Ai da sai annabi yace mata basa fita aiki ko karatu, Kawla bint Azwar taje yakin Yarmuk tare da Khalid bn Walid, Aishat ummul muminin makaranta gareta a gida, Zainab bnt Ali itama tayi jihadi da ɗan uwanta Hussain. Kinga kaɗan daga cikin fita da mata suka yi a lokacin annabi. Al’adanmu ce hana mata fita, ko mai mace tayi don samun cigaban al’umma sai a hana ta saboda ana mata kallon mai rauni. Ɗaukakan kowace al’umma yana ga samun mata masu ilimi da nagarta.

Shi yanzu ya mata fyade, tsoron tsangwama yasa tayi shiru, ina ce satin da aka fahimci tana da ciki aka kama shi a ɗakin Amaryar kawunsa yana shirin mata fyade, ihun da tayi don tsabagen son rai ya ja mata saki daga Kawun nashi. Ke ba zaki ja taki jiki ba kin tsaya biye ta alhaji. Kar inji kin yi abin da ya ce, in ita ta dawo don kanta fabi Ni’ima amma in bata dawo ba fatan Allah ya albarkace aurenta da zuri’ar su. “

” Aameen ya rabbi, hajiya na gode, zan dinga zuwa kina bani tarihin mata sahabbai, don na lura ba boko ya wayar miki da kai ba, ilimin tarihin annabi da sahabbai ne ya buɗe miki idanu har ake ganin kin waye da yawa ashe tsabagen sanin yancin da musulunci ya tanadar miki a matsayin ki na mace mutum kamar kowa” Goggo ta faɗi tana dariya.

“kai Salame kenan, Toh akwai gatan da ya wuce wanda musulunci ya bamu, kawai al’ada muke ba fifiko shi yasa muke wahala.

Yanzu misali na RAHANATU, a dole akai zina da ita Kinga a musulunci ba ta da zunubi amma a al’ada tayi gagarumin abin kunya, hakan ya sa aka kore ta, maimakon a hukunta shi wanda ya fi karfinta yayi zina da ita. Yanzu dai ga gudunmuwa ta nan a sa su a islamiyya anjima. Allah ya raya mana su” ta karasa tana mai mika mata naira dubu uku. Nan ta karɓa tana godiya sannan suka yi sallama suka kama hanyar gida.Ko da suka isa gida, Goggo ta fara haraman ɗaura abincin rana, yayin da Salmah ke manne da ita

“oh ni Salame, se kace wata kaska ina ɗaga kafa kina saukewa, ki je cikin yan uwanki ki zauna” ta faɗi sa’ilin da ta bita zuwa madafa.

“zan tayaki ne fa Goggo, na iya Girki ina ma innarmu a kano” ta faɗa cikin murmushi yayin da Goggo ta saki baki tana kallon ta galala.

“Ita Aminar ce ke saka ki Girki? ” ta tambaya tana mai kallon idon ta don ta ga iya gaskiyar ta.

” a’a muna taya ta ne dai, a haka har muka koya, ranar da na fara yin tuwo ko Goggo, rabin sa gari ne, ranar baba sai da ya make ni wai na faye rawar kai” da fari tana maganar tana dariya ne sai da ta ambaci sunan baba ta gimtse fuska tunawa da tayi da abin da ya baro su.

“Oh ni salame, ko dai Almatsutsai gare ki ne, ana raha sai ki gimtse fuska, ko dai Kanon zaki koma mu huta” Ta ce tana lakuto mata haɓarta. Dariya kawai Salma tayi ta watsake.

A haka suka kammala abincin su na rana, suka ci bayan sauke farali ɗaukan su tayi zuwa makarantar islamiyya da ke bayan Layin su.

Bayan gwajin da aka yi musu nan aka sa Salman a aji huɗu, Salma aji uku suhayl kuma rabin aji. Goggo bata tafi ba har sai da ta amshi takardar shiga sashin hadda tare da alkawarin zasu fara zuwa ranar Alhamis kasancewar sashin na karatu ne ranakun Alhamis zuwa Lahadi.+

Sun shiga azuzuwan su ana darasi na biyu. Salma ta iske malamin fiqhu na karantarwa. Nan ta iske kujerar farko a gefen mata da mutane uku ta zauna cikon na ukunsu, ta natsu tana sauraran karatun.

“Assalamu Alaikunna, kaif” ta ce dasu bayan malamin ya fita.

Sai da suka kalli juna sannan suka amsa da “Waalaikumus salam wa Rahmatullah wa barakatuh”.

“ismie Salmah Aarif ” ta faɗi tana mika musu hannu.

” Rufy kiyi shiru in ansa, kar ta raina mana wayau, don ma jiddo bata zo ba da ita zata yare mana ita” cewan ɗaya daga cikin su,

Dariya ya kucce ma Salmah, ita dama tsoronta irin islamiyyarsu ta Saudiyya ce da ba’a wani yare sai larabci duk da kasancewar suna yankin da mafi akasari bakaken fata ne.

“Wacece Jiddan Halan, don Wallahi kun bani dariya, ni fa na sha ba’a wani yare sai zallar larabci ne fa” ta karasa tana dariya. Nan duk sai suka haɗu suna tuntsira dariya kamar wasu sabbin kamu.

“wai tsaya, Salma wai dama kin iya hausa ne kike yare mu, har da wani Alaikunna ” faɗin mai kiran Rufy nan suka kara sakin wani dariya.

” Ai Barta Ummita da fari na aza fa bata iya ba, sai da na ga ta kara karya harshe na ga ai ko da Larabawa take kama” inji Rufy. Suna tsaka da dariya wani malamin ya shigo, suka yi tsit kamar ba su ba har sai da aka kaɗa tashi.

Nan ne Ummita ta haye samar tebur ta ce2

“ga bakuwa an kawo muku a aji, mu dai gare mu ba bakuwa bace don yar wata Goggonmu ce, balarabiya ce kuma, ba ma son shisshigi da neman es, ehe”

“kuma Sunanta Salma Baralabiya, saura su wa’e su turo wasika Wallahi abinda muka yi lokacin jiddo kaɗan ne akan wanda za muyi ma Salmah” Rufaida ta amshe, nan suka tafa suna tuntsire da sabuwar dariya.

Mamakinsu ya cika Salma, duk da tana da tsokana tun tasowarta amma zaman gidan inna ya sa duk ta daina saboda rashin sakewa Matukar baba na gida.

A bakin kofar makaranta ta haɗu da Salman da Suhayl nan ta gabatar masa da Kawayenta suka yi gaba yan mazan na biye da su a baya.

A hanya take tambayarsu gidan su sai suka faɗa mata Mahaifin Rufaida yayan Ummita ne, ita kuma jiddo yar kanwar mahaifiyar Rufaida ce. Ummita ta kara da cewa “ke kuma daga yau yar Goggo na ce. Duk da kuwa Goggo salame kawar kishiyar Mamana ce. Kinga ke ma ya ta ce” nan Rufy ta kai mata duka ta ce

“sai aukin son girma amma duk mun girme ki”2

Nan fa Ummita ta kumbura tana shirin yin rigima sai da Salman ya shiga tsakani sannan ta yi gaba ta Barsu a baya. Su kuma suna ta mata dariya har suka kai kwanar da ta raba su, duk suka yi hanyar gidajensu.

“Assalamu Alaikum Goggo na” ta faɗi tun daga bakin kofa, Ras! Ta ji gabanta ya faɗi don bata san irin tarbon da zata samu daga Goggo ba.

“Waalaikumus salam yaran albarka, ina suhayl ya karatun zo ka faɗa min mai gidana” ta ce tana gwasale Salma. Bayan sun gaishe ta ne take tambayarsu karatun su, sannan suka yi alwala don gabatar da sallan magrib.

Bayan sallan isha’i ne suka taru don cin abinci. Suna tsaka da ci ne aka yo sallama, ashe Kanin Goggo ne da yayanta hakimi. Nan aka sake sabon gaisuwa, su Salma na shirin tashi suka zaunar da su

“abin da ya sa muka yo takakkiya ba komai bane sai zancen yaran nan, mun tattauna da Yaya ga shi nan ni ban goyi bayan a cigaba da rike su ba, yara dai yaran zina ne, ba zamu gurɓata alayenmu ba, shine muka yanke mika su gidan marayu, in har tana son Yaranta da gaske ta dawo gida tayi aure” Kanin ta ya faɗi yana jijjige-jijjige kamar zai mari Goggo.

Kukan da Salma ta saki ya kara karya zuciyar Goggo duk da zancen Kanin nata ya ɗan sa mata tsanar su.

“Amma Jamilu ka bani kunya, har zaka kalli kwayar ido na ka danganta jikoki da zina, Naji yan zinar ne me kai su gidan marayu zai haifar? Ni dai zan rike su tsakani na da Allah, yaran nan guda nawa ne da za’a fara jifan su da muggan kalamai. Toh gaskiya da sake”

“Mun baki nan da kwana uku ko ki mika su ga gidan marayu ko kuma in sa a tayar da ke a garin nan” faɗin Hakimi rai a ɓace, ba tare da ya jira amsarta ba ya Mike ya fice daga gidan, nan Kaninsa ya bi bayan sa shimaHankalin Goggo ya kai kololuwa wajen tashi,  juyi take kan gado idanunta babu ko alamun barci.  Ta saka wannan ta kwance,  duk hankalin ta bai kawo mata mafita ba. A iya sanin ta ba za ta yarda a kai jininta gidan marayu ba amma kuma in aka kore ta ina zata nufa da yara ita ba wata sana’a take kwakkwara ba.  Haka dai ta kasance har sai da kiran assalatu ya fargar da ita lokacin da ta Share kwance.

   Tashin Salma da ke kwance a gefen ta ya dawo mata da dukkan bakin cikin da take tunanin babu a lokacin.  Kallon ta tayi,  ta gama addu’ar tashi da ga barci ta Mike nan take wata irin tsanarta ta dake ta,  “yanzu ita ma ɗin  ba tsira tayi ba da ga jan abin kunya,  mata ko tsiya”  ta faɗi a ranta.

“kawai ki ba da ita a gidan marayu ki huta da abin bakin cikin da zata iya Kwaso miki” wani sashi na zuciyar ta ke shawartan ta,  kafin ta kai ga amincewa Ɗayan sashin tace da ita

“Me zaki ce da Allah yayin da ya tambaye ki dangane da amanar kiwon da ya baki.  Ki haɗe su ki rike duk rikicin da za’a yi” batai wata wata ba ta amince da shawarar.  Da wannan karfin gwiwa ta tashi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallan asuba.2

                      ***

Ko da hakimi ya isa gida ya taradda hajiya Aziza a turakansa.  Sanye take da rigar barci doguwa,  kanta babu ɗankwali kitsonta ya kwanta gunin sha’awa,  nan take ya fara jin abu tun daga tafin kafarsa har kwanya.  Zuciyarsa na kara narke mata,  “Daɗi na da ke kenan sanin ciwon kai”  ya faɗi a ransa bai tsaya ɓata lokaci ba ya dumfare ta ya rungumo.4

“Kinyi kyau hajiya ta,  always looking sweet my dearest ” ya faɗi a saitin kunnen ta,  nan take abubuwa suka dawo masu a rai,  rayuwar su na jin Daɗi sanda yake aiki karkashin mahaifinta.

” tunanin me kake yi bayan ga azizarka a tare da kai? ” ta  faɗi tana dariya kasa kasa.

” Tunawa nayi da kuruciyar mu,  hakika da duk haka mata suke da sai in ce ba za’a samu yawan mace macen aure ba ko zaman ukuba a aure,  Allah ya sada ki da aljanna yanda kika zama sanadin wayar dani cewa mata ma mutane ne da suke da hakki a aure kamar maza”  ya faɗi yana shafo  kitso ta.

“ai da sauran ka yallaɓai,  ba zamu gaji da magana ba don muna fatan samun nasara da canji yayin magana,  wasu na tsoron saki sai suka ki magana hakan ya sa suke zaune cikin ukuba”2

“Maama  me yayi saura bayan ina iya kokari wajen ganin na kyautata muku.  Ko halinku na yan boko zaki nuna min. ” ya karasa yana murmushi don ya san abin da ya tono.

” Ai tsiyar yan Afirka kenan,  ba  dama ace kar a muzguna ma mace sai kuce boko,  alhali musulunci ya koyar da mu haka.  Zancen yaran RAHANATU ne,  shin da ace Batul ce ta wajen mu wannan al’amari ya same ta haka zaka aiwatar?  Dazu na ji zancen ku da wancan jahilin,  wanda ya ki karatun arabi balle a sa ran zai yi boko.  Wallahi kuna kai yaran nan gidan marayu zan haɗa ku da hukuma.  Sannan ka san cewa na bar gidan nan kenan”5

“tsaya Azizah,  kin sha wani abin ne da daddaren nan da zaki haɗa Batul da Rahane,  bazan taɓa haɗa jini da shegu ba don ni tsarkakakke ne haka duka mata na” ya faɗi yana kumfar  baki.  Sanin da tayi zai ji haushi sai ta saki ranta ta yi dariya sannan tace

“Meye bambanci tsakanin su biyun? Duk su biyu yaranka ne ko Kaki ko kaso,  sannan ai ita dole aka mata,  amma ina ce nan ka sa Sanah komawa gidan Nasiru Nasiru,  duk da cewa da ake ɗan luwaɗi ne?  Da wanda aka ma fyaɗe da wanda ke aikata luwaɗi Wanne ya fi?  Sannan ita dai aure tayi ta haife su,  ga yarka chan ka Barta a auren da wuta zai kaita saboda tsinuwar Allah da yake kansu. Duk mijin da yayi luwaɗi ai zai yi da matarsa”  nan hakimi ya cika yana batsewa.

“ke dai baki da magana sai ta saki,  yanzu duk kokarin amso taimako da nake yi daga wajen malamai baki gani ba,  mai gani har hanji yace ayi hakuri zai daina” ya faɗi a iya kan gaskiyarsa kenan.

“tab,  ga shirka ga luɗu Allah ya shirye ku.  Duk auren da zai kai mace ko yan uwanta gidan boka Wallahi  ba aure bane.  Ni dai na gama magana kuka kuskura kuka kori yaran nan Wallahi hukuma zasu shigo ciki.  Haba Allah ya ɗaura muku hakki ku nemi watsarwa,  na barka lafiya” ta tashi ta barshi zaune.  Ta san ba zai juri fushinta ba shi yasa ba ta kyashin nuna fushinta a kansa.5

                               ***

Tun da ta tafi yake tunanin abin da ya faru da yar sa Sanah.

SATI BIYU  DA SUKA GABATA

Ya shigo gida ya iske yarsa da ke aure a ɗan Musa ta dawo gida.  Da fari yayi tunanin ziyara ta kawo masu sai da Hajiya Aziza ta masa bayanin kara Sanah ta kawo.

“Kowa fa hakuri yake a gidan miji shin ba zaku faɗa mata hakan ba,  ni ba abin da zan ce illa kar ta soma kashe aurenta.  Uwar ta ma hakuri take da ni” ya fadi a fusace,  nan take ta mayar masa da cewa2

“neman ta fa yake ta baya, sannan kace kar ta dawo,  cewa a kayi in an aurar da mace Shike nan bata da hakki akan ubanta ?  Ko mai kake nufi “?

” Akan ta aka fara auren ɗan luwaɗi ko cewa akai su sauran basu da mata,  kar ki kashe mata aure ko don ba ke kika haife ta ba” ya bata amsa5

“don ba ni na haife taba sai in bari tayi ta kwasar tsinuwar Allah da sunan aure,  aure fa ibada ce,  kuma ibada sai da biyayya ga Allah ba saɓon sa ba. Haba” tana gama faɗi ta barshi a zaune.

Haka tana kuka da magiya ya tasa keyarta har zuwa dakin ta.  Ta kira shi sau biyu tana rokon sa shi kuma yai mirsisi ,  chan ne abokin sa ya shawarce shi da su nema mata taimako daga malamai.

Da tunanin nan barci mai nauyi yai gaba da shi har sai da aka kira assalatu sannan ya tashi yai harama.

Jazakumullahu khairan…

Bayan sun karya da waina ta tasa su zuwa makarantar gwamnati da ke cikin marke. Bayan sun cike takardu ta biya kuɗi sannan ta juya da suhayl inda shi ma ta sa shi a firamarin garin.

Bayan shigar aji ne ta iske kawayenta su Rufaida da Ummita a ajin da Jiddo da bata gani jiya ba karamar murna tayi ba ganinsu su ɗin ma haka. Basu kai ga fara surutu ba malamin turanci ya shigo,+

” Good morning class ” ya faɗi bayan ya rubuta sunan darasi da kwanan wata.

” who born you sir” Kawai ya fito bakin jiddo tana murmushi.

“fita ki zube a gaban aji, Ace mutum bai da tarbiyya, haka kike ma ubanki a gida” Ya ce yana ciccijewa

Nan sai ummita ta fara dariya, salma ta tare mata suka kai ta kyalkyatawa. Ran malamin yai mummunar ɓaci duk ya rasa mai zai musu ya huce haushi. Bulala ya ɗaga zai fara dukansu nan take salma ta fara kuka tana faɗin

“Ni sabuwar, don Allah malam kayi hakuri”

Ajiye bulalar yayi ya tsaya yana kare mata kallo, dariya ta bashi yanda take kyarma a gefenta kuma jiddo ce sharɓe sharɓe da hawaye,4

“ku biyo ni” Ya ce musu a tsawace, nan suka fita har da tuntuɓe sauran yan ajin na musu dariya.

***

Isarsu ɗakin malamai ya sa su tuka mashin. Har sun fara ya tuna salma ta ce da shi ita sabuwar zuwa ce ya sa ya tara su gabanshi sannan yace,

“me kike son zama a rayuwa?” Ya mika akalar tambayar zuwa ga rufaida, saboda tun bayan dariyar da su kayi ta koma wata salaha, a tunanin sa salahar ce.

“Inna ta tace in zamo mace mara gardama ga miji, ko mai namiji yayi daidai ne”2

“ke fa ” Ya ce yana kallon Ummita

” ina son zama malamar asibiti in dinga taimakon marasa lafiya mata, amma aure za’a min daga mun zana jsce” Ta faɗi a marairaice.

“ke fa? Mara kunya baki kamar reza” Ya faɗa yana hararar jiddo.

“Ni, biki na watan maulidi ne, da yardan Allah saura wata bakwai kenan, innarmu tace a sabuwar shekara zan cika goma sha huɗu “

” wa ya tambaye ki dogon zance? ” Ya ce yana tsala mata dorina a jiki.

” Ke kuma fa sabuwar zuwa”

“Ni ban sani ba, buri na ɗaya in koma wajen innata a Saudiyya, jiya naji ana cewa za’a kai mu gidan marayu” ko me ta tuna kuma sai tayi shiru,  nan kuma duk sukayi shiru chan dai malamin yayi kokarin magana.Shiru duk su ka yi na wasu yan lokuta kamin bisani malam ya ce,

“Salmah ina iyayen ki?”

“mamanmu na Kasar Saudiyya, tare da Mahaifin mu.  Na san dai ya taɓa tafiya aka ce ya je Sudan wajen yan uwansa.  Mun dawo Nijeriya ina da shekara shida yanzu Kaga ina sha biyu,  tun lokacin ban sake ganin su ba. ” Ta karasa tana shassheka.

” gidan wa kike zaune anan,? “

” Wajen Goggo Salame, itama yau kwanar mu uku da dawowa wajenta.  Da muna Kano ne wajen inna Amina” Jin hakan ya sa hankalinsa tashi.  “tabbas idanunsu iri ɗaya ne,  kai akwai kamanni ya akayi ban gane ba tun ɗazu”  zuciyar sa ta faɗa masa.

“Ya sunan mahaifiyarki? “

” RAHANATU “

” what!  Ya faɗi da karfi har sai da suka ɗan firgita.2

Nan kuma sai ya ɗan waye ya kakalo murmushi wanda iyakarta fatar bakinsa.  Sannan yace

“tare muka fara karatu,  sai dai a gabanta nake,  ki yi kokarin koyi dahalayenta don kuwa ita ɗin ta gari ce,  ki kwantar da hankalinki babu inda za’a kaiki,  tun da kika ga goggo ta kawo ki makarantar nan toh ina mai tabbatar miki da ba zata bari a kaiki ko ina ba.

Abu na gaba da zan faɗa muku shine ku sani aure ba shi ne karshen duniya ba,  kai shi ne Mafarin mafarki,  sa ma rai jin Daɗi ne kawai a aure shi ke sa mata shagaltar da rayuwar su wajen faranta ma ɗa namiji. Garin haka har su faɗa ma halaka walau bin bokaye ko wani abin.

Kunga karatu,  yana da matukar mahimmanci a aure,  in kina da ilimi kina aiki zaki taimaka ma al’umma, kai ko bakya aiki zaki taimaka wajen koyar da yaranki,  hakan ba karamin daraja zaki samu ba a idon mijinki,  se kiga bai iya wulakanta ki ba. Saboda haka ku sa ma ranku  karatu baya hana aure, haka aure baya hana karatu. Duk su biyun manzo SAW ya umurce mu da muyi.

Idan Allah bai nufe ku da karatun,  kun san dai kowa da kaddararsa,  toh ku tabbata kun dogara da kanku,  ku kama sana’a ko da ace riban da zaku samu kaɗan ne,  sau da yawa bani bani ke kawo matsala a gidan aure. Amman in kun yi karatu ko kun rike sana’a ba zaku samu wani matsala sosai ba.

Abu na karshe shine akan laifin da kukayi,  in har mutum na neman albarka a karatunsa toh dole ya kasance mai girmama malamansa. Ba ku ji hausawa na faɗin malami yafi uba ba,  ko harafi A mutum ya koyar da kai ya cancanci darajawa da girmamawa.  Hakan zai sa mutum ya kasance mai nasara. Ku je Allah ya muku albarka”

Jiki a sanyaye suka kama hanyar ajinsu, basu taɓa zaton zai kyale su haka ba tare da ya zane su ba.  Suna kauce ma ganinsa ummita ta fara dariya,  nan suka tsaya kallonta.

“kun lura da yanda malam ya bi salma da ido kuwa,  anya ba saurayin mama Rahanatu bane don tun da ta ambata ya shiga wani yanayi” Ta kara sa dariya aiko salma ta kai mata duka ta goce,  nan fa suka fara ma juna dariya.

“Jiddo ke Wallahi son aurenki da yawa yike,  ni wallahi da za’a barni ai sai na kammala zanyi aure Wallahi ” faɗin Rufaida

” ke dilla aure daɗi ne dashi Wallahi,  bari Ado ya kawo min wayata, zaki ga bidiyon da ya ce zai saka min.  In ya zo zance wani lokaci yana nuna min Wallahi nan sai in fara jin lema lema kamar nai fitsari,  yace min kaɗan kenan daga cikin daɗin. ” Ta faɗi tana juya idanu.4

” ku mu shige kangon can ki bamu labari,  ance soyayya daɗi gare shi. Ni don kawai ina son zama likita ne kuma ance wanda ya fara baya iya karatu. ” faɗin ummita.  Salma kuwa kallonsu ta tsaya yi don ita tun da take bata taɓa kawo soyayya nan wuri ba,  Kano da ta baro duk saointa karatu suke yi sai an gama candy ake aure. Haka dai ta bi su zuwa kangon suka zauna sannan Jiddo ta ɗaura.

” Kunga ya ce in mukai aure,  akwai abinda zai dinga saka min sai na suma don daɗi,  wai kamar Susan kunne.  Sannan akwai inda yake tattaɓa min nake jin Daɗi,  amma fa amana fa,  kar ku faɗa ma kowa Kunga dai ku yan uwa na ne,  ke kuma salma aminiyar mu ce.” Ta karasa tana mai mikewa saboda hango discipline masta ya damfara wajen.  A guje suka wuce aji aka cigaba da darussa har aka tashi.4

                                ***

Bayan sun koma gida abinci suka ci suka huta,  bayan la’asar suka kama hanyar islamiyya,  suna gab da barin gidan suka haɗu da hakimi, zai shiga wajen goggo.  Salma da ta san ajiyar su a kanta da yan uwanta ta tsorata ainun.  Amma dai bata ce komi ba,  bayan sun gaida su ne Ya shige cikin gidan

“Zan fi so ace ka aika kira na ne da ka taso zuwa gareni. Ai karami ke bin babba  koda yaushe” Goggo ta faɗi tana mai Shimfiɗa masa tabarma.

“Mahimmancin maganar ya sa bana kyashin biyo ki. Akan zancen yaran nan ne, na amince ki rike su,  duk wani taimako in bai fi karfi na ba zan baki” Ya faɗa yana murmushi a tunaninsa ya yi a bin kirki.

“Yaya amma da mai sa ka ce a kai su gidan marayu?  Ni fa har na shirya kayana don na gwammace in bar garin da a sa ni a faifai, amma ganin zaka ba da naka gudunmuwan yanzu na faɗa maka,  amma niyyata ko sallama bazan muku ba” tace a hankali amma daga jin kalaman ta an san wacce ta ke cike da fushi ne.

“kiyi hakuri,  Shaiɗan ne ya so shiga tsakanin mu, amma Insha Allah ya sa yanzu duk abinda zasu nema na fanin Uba zan yi musu.  Fata dai Allah shi raya mana”. A haka suka zauna hiran zumunci har sai da aka kira sallan magriba bayan su salma sun dawo sannan ya tafi.

BAYAN SATI UKU

A cikin sati uku salma ta saba da garin marke,  kullum safe zuwa azahar suna zuwa makarantar boko,  da la’asar su je islamiyya.  Ranakun Alhamis da Jumma’a kuma makarantar hadda haka Asabar da Lahadi da safe.

Bata yarda da kowa ba sai kawayenta uku duk da jininsu yafi haɗuwa da Ummita kasancewar halayensu kusan daya ne.

“Salma kalli tafiyan malam Aliyu,  ashe chogane kafa yake yi “Ummita ta faɗi tana dariya haɗe da kwatantawa.

” Bari kiga na malam yahaya,  shi haka yake tafiya kamar zai kwatanta,  se kiji yana  “heys heys you oba  ziye”  Ko turancin ma bai iya sosai ba” Ta karasa tana dariya haɗe da kwatantawa itama. 

Shirun da ta ji sunyi ne yasa ta waigawa aiko karaf idanunta suka haɗu da na malamin english.  Bata jira komi ba ta ari na kare tayi cikin ɗalibai masu siyan kayan tara.2

“Ni kuma ya nake tafiya?  Tashi ki kwatanta ko na zane ki” Ya faɗi ya na kallon Ummita,

“Ai ban iya ba tukuna,  bara in kira salma tayi” kafin ya ankara itama ta sheka,  nan ta iske ta a maɓoyar su,  suka cigaba da dariya.

“Ashe baku ji nasihar da nai muku ba rannan,  duk da na ga ku biyu kamar ba ruwanku,  amma Allah kaɗai ya san abinda za ku shuka inda ace ban zo ba,  ku tashi ku bani waje su kuma ku ce su guji haɗuwar mu. ” ajiyar zuciya suka saki ganin ya juya ya tafi.

Tashi su ka yi zuwa inda suke sa ran zasu gan su Ummita,  anan suka gansu  suna cin gyaɗa hankalinsu a kwance

” wato ku don tsabagen iskanci ku jawo mana masifa amma ku gudu ku barmu ciki,  toh wallahi da sake,  don ni kam na tuba” fadin jiddo rai a ɓace

“nyayayaya! Sannu muslimat,  muminat qanitat,  ki ɗauke mu ki jefa mu wuta kawai, ba kiran tuba kawai zakiyi ba,  mstww salma mu tafi don Allah” cewar Ummita tana mai jan hannun Salmah.

“ai ni fa na ɗauka laɓɓanta ne suka koma hakanan naga yar uwar ta ta zama kurman karfi da yaji, ai da na san abin da zai ce kenan tawan da ban gudu ba,  Kinga yanda yake tafiya” tashi tayi tana kwatantawa har zuwa ajinsu yayinda Ummita ke dariya har da tsugunawa.  Rufy da Jiddo kuma sun cika sun yi fam.

Suna gab da shiga aji ta ga Nura saurayin Nafisar ajinsu. Tun suna primary Aka san soyayyar da ke tsakanin masoyan biyu har satin da ya  gabata da labarin sa ranan Nafisa ya karaɗe garin.  Nan kuwa Ummita ta kwala masa kira gami da ɗaga masa hannu ya zo.  Ai ko ba musu ya karaso Wajen.

“Ashe abinda ya faru kenan,  ni bakin ciki na  cewan da suke wai baka isa aure ba” Ta faɗi cikin Yanayin tausayi.  Shiru yayi yana kallonta ganin ya rasa mai zai ce sai ta ɗaura da,

“Shi yasa karatu ke da mahimmanci,  kai ka tsaya soyayya,  har sunanta ka rubuta a hannu da wuta fa,  Allah nura ba’a kyauta maka ba,  ka ganka kyakkyawa da kai,  in kayi karatu mai zurfi ba karamin gaye za’a yi ba kuma ba wanda zai ce baka isa aure ba lokacin. Allah sa hakan ne Alkhairi ” Ta fa ɗi tana dariya,  hannun Ummita ta ja suka wuce.

” kai Nura kai banza ne,  kalli yar ficilar yarinyar nan ke faɗa maka magana ita a dole manyance ko, Ubanta zamu ci Wallahi” faɗin Jamilu abokin Nura.

“ka ga dai ta fi karfin ka  ne shi yasa a

Kake wani kushe ta,  se kace ba ita ta hana zuciyar ka sakat ba.  Ku muje aji kawai. “faɗin Nura, da haka suka wuce aji.

                               ***

Tabuk Saudi Arabia

Zaune take gaban fannin kimiyya a jami’ar Tabuk. Karatu take yi amma hankalinta baya tare da ita.  Tana shirin zage jakanta don ta ɗauko wani abin ko ta a jiye kawai taji an fisge mata littafin da ta ke karantawa.

“ina kika kai min yara?  Shekaru uku kenan nake zaryan ki faɗa min inda suke kinki,  kin san dai nafi ki iko a kansu ko” Ya faɗi yana mai daga murya.

“suna Nigeria,  don haka don Allah ka fita batu na,  abinda ya haɗa mu ya raba mu shekaru da suka wuce.” Ta bashi amsa

“inda aka gagara rike ki ne kike tunanin zasu rike nawa,  ko ce miki akayi na Gaza kula da ku,  ganin sama ta ce wannan don ku mata ba ku san tattali. “

” oho ma ka,  ni daina gama magana,  ka je chan ka Kara.  Ya’ya kuwa sun maka nisa har abada” Ta faɗi tana shirin barin wajen

“Rayhan kar ki damu Ehn! zasu neme ni a duk lokacin da bukatar uba ya taso musu” yana kaiwa nan ya aje mata littafin ta ya juya ya tafi.

Wanda ya ji larabcin da suke yi da zubin ta zai rantse balarabiya ce ba RAHANATU bace ta marke yar gidan malam Tanko da goggo Salame.

Tabuk city
Shiru tayi bayan tafiyar sa,  sam hankalinta ya kai kololuwa wajen tashi.  Wayarta ta ciro ta latsa wasu lambobi sannan ta kara a kunnenta.

“Hajiya Rahanatu ina yini” aka faɗa a ɗayan bangaren bayan an ɗauki kiran.

“innar yara kina lafiya? Ya kuke ku duka?” Ta tambaya zuciyar ta na kuna.

“muna lafiya lau,  su Salma dai yau satin su uku da komawa MARKE.  An sami wani azzalumi da ke neman ɓata ta,  shine na tura su wajen goggo.  Na tabbatar da ma yanzu sun zama Yan gari” Ta karasa tana dariya.  Itama Rahanatu dariya tayi wanda za’a Iya cewa yafi kuka ciwo. +

“Allah dai ya kare mu da zuri’ar mu daga sharrin azzalumai, ita goggon kuna saya kuwa? ” Ta tambaya cikin kulawa.

” Goggonki har yanzu kauyis ce,  cewa tayi tunda ba baba bata da wanda zata kira,  ko la’akari da ganin mu a nesa bata yi” Ta karasa da dariya kuma.

“Allah jikan baba,  yasa yana dausayin Aljanna,  zan turo miki kuɗi don Allah ki je ki duba goggo.  Nagode Allah bar zumunci ” tana kaiwa nan ta kashe wayar a lokacin kuma ta fashe da kuka 
” Ya ci ace na koma gida haka nan,  ina kawar gidanmu” Ta faɗi a gida.  Nan take zancen mahaifinta ya dawo mata;

“karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zai hana mu kwana da yunwa, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu”

Kuka sosai tayi kamin ta share hawayen ta tayi hanyar zuwa gidan ta. Nan ma a kujerar falo  ta zauna tana tunanin rayuwar ta,  tun da ta baro gidansu da ciki wata uku wanda Hadi duk ya ja mata wannan.

MAY 1990

“Rahanatu meyasa zaki min haka, na kwallafa rai na akanki me yasa zaki min haka” faɗin Mal Tanko ranshi  na masa suya,

STORY CONTINUES BELOW

“Baba Wallahi Hadi Shaiɗan ne,  ka tambayi Goggo Tasalla ita ta taimaka min kuma tace inyi shiru kar kowa yaji” Ta ce tana mai shessheka.

Shiru yayi, idanunsa bai bar fitar da hawaye ba,  tun bayan sakamakon da aka basu a asibitin kauyensu (primary health center)  na tana da ciki wata uku yake kukan zuci da hawaye.

Tim!  Ta ganshi a kasa gab da zasu shiga cikin gidan su.  Nan fa mutanen da ke zaune a dakalin kofar gidansa suka taso.  Kukan da ta saki ne ta fito da matan da ke cikin gidan fitowa.
“Na shiga uku Malam,  shike nan kin kashe min miji,  inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ” faɗin goggo salame tana mai rushe wa da kuka.

Ɗaukan sa akayi zuwa asibitin da ya baro,  asibitin da ya jiyo bakin labarin da baya fatan sake jin sa. Take likitan da ke wajen ya duba shi ya bashi gado.

Sai yamma can sannan ya farfaɗo sunanta a bakinsa, haka yai ta kiranta ganin kiran yai yawa yasa ba don rai ya so ba suka kirawo ta, bayan ta iso ne ya mika hannu ya kamo ta ya rike gam.

“Na yafe miki rahanatu, Allah ya albarkaci rayuwar ki ya Haskaka rayuwar ki yasa ki zama abin alfahari ga al’ummar marke da musulmi baki ɗaya. Kada wannan jarabawan ya zama dalilin kin karatu,  yanzu ne zaki dage da karatun.  Allah ya baki sa’a, salame ko bayan ba ni kada ki yarda a hana yara na karatu,  ku yi hakuri ku sani a addu’ar ku bayan kasa ya rufe idanu na.  Na yafe muku nima ku yafe min don Al… ” take harshen sa ya karkace suka dena gane abin da yake faɗi har sai da ya karanto kalmar shahada sai kuma yai dif.  Chan dai ya saki ajiyar numfashi rai yai halinsa.

” me aka faɗa muku da kuka zo asibitin ” faɗin goggo salame a ruɗe.

” cewa sukai wai wata uku” Ta faɗi cikin karfin zuciya.  Don mutuwar da ta gani muraran da raguwar bakin cikin da e tattare da ita ya kekyashe mata zuciya, dukan da taji da tsinuwa yasa ta dawo daga duniyar tunani.

“baiwar Allah kiyi hakuri har ku je gida mana,  yanzu dai a samo motar da zata ɗauki gawar. Allah ya masa Rahma ” cewan likitan da ke asibiti,  duk da mutuwar ta dake shi har ya fara tunanin yana da alhakin mutuwar sa, hakan bai hana masa tsawata mata ba bayan ya karanto addu’ar da manzo SAW ya koyar idan za’a rufe idanun mamatanmu.

” wani gida zata,  ai daga nan sai dai ta nemo garin zama ba marke ba,  babu wacce zata yo cikin shege ta zauna a garin nan” faɗin limamin MARKE da ke tsaye.

Wani karin takaici likitan ya ji,  don ganin ko gawar basu tsaya sun sauke masa hakkinsa ba amma suna ta karamar yarinya.

“In ita kun kore ta shi da ya mata cikin fa,  ballantana na duba ta fyaɗe akai mata saboda karfin da aka sa har yanzu wajen bai koma daidai ba.  Shi Hadi da yayi fyaɗen wani hukunci za’a masa,  ciki kuwa har da kisan kai don saboda abin da ya shuka ne zuciyar malam Tanko ya buga,  shi mai za’a masa nace” Ya faɗi  a fusace yana mai ɗaga murya.

“Toh shi ba namiji ba ne? Ita ke da abin kunya,  sannan lokacin da aka killace mata a cikin gida shi malam Tanko tura tashi makaranta yayi. Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU. sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani ɗan adam bi ta hanyar…. nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi’arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko. Da yawa daga cikin su suna ganin haukar iyayenta da suke iya  barinta tana ɓata sauran adadin shekarunta a hanyar neman karatu. Da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai ya haɗa ta da Hadi, yanzu dai ta tafi can wani wajen ta haife boko.” limamin ya faɗi yana mai kumfar baki, a tunanin sa ya birge kenan.

“Assha!  Ina mai muku albishir da Hadi da kuke gani sai ya hana Yaranku mata fita ko kwar gida duk don ya kawata adonsa,  su kuma ya ranku suyi ta abin kunya sai inga karyan tsiyarku,  na baku minti biyar ku kawar min da gawar nan ko in haɗa ku da jami’an tsaro,  kauyawan banza kawai” likita ya fadi rai duk a ɓace,  zuciyarsa cike da tausayin mamacin da yarsa.

Haka aka ɗauki gawar malam Tanko suka ɗauki hanyar cikin gari.  Rahanatu bata sami wajen zama ba sannan kyarar ta masu tafiya a kasa suka tayi. Tun da ta kai Kasar bishiyar ɗinya da yake dole za’a bi zuwa makabarta, ta zauna ta fara kuka, bata san iya daɗewar da tayi ba har sai da taji alamun sawun mutane. Nan ta ɗaga kai ta hango zanin goggonta Shimfiɗe a saman makara.  “Rabbig fir lahu warhamhu”  tai ta nanatawa kamar yanda malamin su na Islamic Studies ya karantar da su a matsayin addu’ar da ake in an ga gawa.

Bishiyar ta fara shirin hawa cikin ikon Allah sai gata ta haye, tana hangensu su akayi komi har aka saka shi cikin gidansa na gaskiya.  Take suka juyo, ranta ya ɓaci ganin ba su tsaya sunyi masa addu’a ba kamar yanda manzo SAW yace. Saukowa tayi a hankali nan wasu sabbin hawaye suka fara zubowa daga idanunta. Shike nan Babanta mai sonta ya tafi sai sun haɗu a lahira kuma.
Taimama ta kwatanta yi ta tada sallah don nema ma mahaifinta gafara.Zata tada sallah kenan taji motsi a bayan ta,  a firgice ta juya don bata san ko waye ba,  ido biyu tayi da wanda ko gawar sa bata kaunar gani nan take ta gimtse fuska, duk wani tsoro ya kau ta tsare shi da kallo

“ke banza ce Wallahi,  zuwa nayi in taimaka miki da wajen zuwa,  kar kiyi gigin komawa gida don hukuncin kisa za’a yanke miki in ji liman. Wai kin kashe tsohonki”

Ko ɗar bata ji ba don limamin da ta gani yau ko feɗe ta aka ce ze yi ba za tayi mamaki ba. Kallon mai maganar take bata ce komai ba,  can ta juya ta sallaci rakaa biyu.  Har ta idar yana zaune a gefe duk da haka ba ta ce dashi komi ba.

“Ga wannan,  ki rike a hannun ki ya ishe ki yin komi,  ni ma jiya da su baffa suka je Katsina ganin sarki ne ya basu ni kuma na ɗauko yanzu da  suka nufo wajen jana’iza.” Ya karasa yana mai mika mata rafar naira ashirin.1

Kallon shi take ba tare da ta mika hannu ta karɓa ba,  ita tun da take kuɗi mafi daraja da ta rike shine naira biyar, amma Ace wai ita ce ake ba naira ashirin ba guda ɗaya ba,  bandir abinda take tunanin ko mahaifinta bai taɓa rikewa ba.  Bata ankara ba ta ji mutum a jikinta  la lulubenta yake ta ko ina.

“kiyi hakuri sau ɗaya kawai zan miki, ɗanɗanonki ne akwai garɗi da tsayawa a zuciya. Zan kaiki har kasuwar gabashi in sa ki a mota” Ya faɗi cikin raɗa.  Karfinta ta sa ta tura shi amma ina ko motsi bai ba.  Haka tana ji tana gani sake bin hanyar da ba nashi ba.  Bata iya komai ba sai hawaye da kunar zuciya.  Da ya samu natsuwa haka ya sa ta a kariyan kekensa da bata san ya zo da ita ba ya ɗau hanyar kasuwan gabashi. Cikin ikon Allah motar Fijo J5 ta cika saura fasinja ɗaya ta shiga  ba tare da tasan inda motar zata nufa ba.1

“in namiji ne ki sa masa Hadi masoyi in mace ce kisa mata raha masoyiya.  So ya sa aka same su hahahhahaha” Ya karasa yana dariya bayan ya mata raɗa ne a kunne.2

Haka sukai ta tafiya, banda kuka babu abinda ta ke yi,  wata mata kusan Saar goggonta ce zaune kusa da ita. Ganin kukan yai mata yawa ne ta ce

“baiwar Allah kiyi hakuri, komi na duniyar ma ai ɗan hakuri ne,  wajen wa zaki je a birnin Kano” Ta faɗi tana kallonta,  ilai kuwa ta hango firgici sosai a idanunta.

“gudowa kika yi ” Ta faɗi cikin raɗa ganin firgicin da ke idanun RAHANATU.

Girgiza kai tayi,  hakan yasa matar tayi shiru gudun kada ta jawo hankalin mutanen cikin motar.  Haka sukai ta tafiya za’a ba za’a ba har suka isa garin Kano karfe goma na dare. Matar bata ɓata lokaci ba ta shawo kan RAHANATU zuwa gidanta.  Sai washe gari bayan sun ci sun koshi sun huta sannan ta bukaci jin  abin da ya fito da ita daga gida. Bata ɓoye mata komi ba ta faɗa mata komi dangane da ita,  ko da ta gama dukkansu hawaye suke yi.

“RAHANATU zan saki a hanyar da zakiyi kuɗi amma fa sai in zaki yarda a cire cikin jikinki. In an cire sai ki koma makaranta daga nan har Allah ya kawo mai son ki.  Kar kiji tsoro, ki saki jiki guminki zaki nema, ga ki da kyau da kira mai ɗaukan hankali.  Kinga zaki yi kasuwa ba ko kaɗan ba”.Kyan alkawari cikawa. Da kyar na iya haɗa wannan,  na dawo meeting a gajiye, karshe karshe ma ina typing ina gyanyaɗi.  So filis manage dis.

Cikin sati biyu sunyi nasaran cire cikin da ke jikin Rahanatu,  Laraba mai dalili kowa ya san ta a matsayin kilaki mai zaman kanta sannan magajiya ga kananan karuwai. Tana da hanya ga manyan alhazai da yan boko masu kuɗi.  Ta kan haɗa taro asirrance inda take ɗaga sabuwar karuwar da ta samu,  taron kn wakana duk daren goma sha uku ko huɗu ga wata lokacin wata yayi haske. Wanda ya zuba kuɗi  mai yawa shi yake tafiya da karuwan.  Tun da ta samu farar yarinya mai diri ta ji sanyi a ranta don kuwa babu kwastamomi a lokacin.7

Musamman ta biya mai gyaran jiki tayi ma,  aka mata kunshi da kitso nan take kyawunta ya fito, tayi kyau abinda. Sai da ta tabbatar da ta sha ababen da zai motsa mata sha’awarta duk don kar ta gardama ranar taron+

“ki kwantar da hankalinki in muka taki sa’a sai ki kwashi bandir bandir na wazobiya don na san zakiyi tsada, da kuɗin zan saka ki a makaranta har ki kai ga cin ma burin mahaifinki, Kinga dai kamar wasiyya ya bar miki,  in baki cika ba wutar Allah zata ci ki” da irin kalaman nan ta samo kan Rahanatu sannan tasirin magungunar da ta sha yasa bata ko gardama ba.4

                               ***

IMRAN SALMAN

Saurayi ne matashi ɗan shekara talatin da biyu, Asalin sa ɗan Kasar Sudan ne,  Imran na da son karatu ba ko kaɗan ba amma kasancewar sa daga zuriar  da ba’a karatun boko yasa bai samu damar cigaba da karatun ba tun bayan kammala sakandire har sai Kasar Saudiyya ta kai agajin taimakon karatu ga mutanen Kasar Sudan sannan ya samu wannan dama.

Bayan an sama masa gurbin karatu a jami’ar da ke yankin yambus sanaiyya wato yambu industrial city.  Tun bai saba ba har ya saba. Sannu a hankali har suka kammala matakin digiri suka ɗaura har sai da suka kai ga matakin digir digirgir Sanan suka waiwaye gida. Nan ma kwana biyu yayi ya iso birnin Kano don abokinsa Haroon ya faɗa masa saukin samun aiki a garin na Kano.

“Imran ka shirya yau zan kaika wani wajen da se kanka ya ɗaure,  ko hukumar shari’ar birnin nan basu taɓa sanin wajen ba” faɗin Haroon cikin harshen larabci.

Dariya kawai Imran ya sa don shi a rayuwar sa ba abin da ya fi so kamar shakatawa, tunaninsa kuwa wani wajen zai kai shi, don ya kai shi wajajen shakatawa a lardin Kano da dama kamar su ruwan tiga da ɓagwai. A haka ya shirirantar da maganar suka cigaba da hira da shirin zuwa intabiyu da zasu yi a kwana uku.

                       ***

Karfe tara na dare Haroon ya tada Imran da ya fara barci suka kama hanya.  Hasken wata ya sa basu bukaci fitila ba suka gangara zuwa wani gida chan a unguwar Nalambata kusa da fage. 

   

    Naira ɗaya suka biya suka shiga gidan inda mutane sun taru iya taruwa. Don akalla zasu kai 50 a zazzaune kan tabarmin kaba.

Can se ga yarinya karama cikin riga da wando da suka ɗame ta suka fitar da surarta, kanta ya sha kitso hannunta yayi jajir da lalle yayin da na kafafunta yayi baki kirin saboda takin da aka sa mata.  Saman kujera aka mikar da ita kafin Laraba ta tsaya a tsakiyar mazaunin mazan ta ce “ga haja.  Cinikin kwana bakwai kawai za’a bada” 

“me ake yi anan” Imran ya tambaye Haroon kasancewa baya jin hausa. Nan Haroon yayi masa bayanin abinda ya fahimta da irin taron Laraba. Nan ya kalli Rahanatu babu abin da yake hangowa sai tsantsan rashin wayonta da kankantar ta,  takaici fal a zuciyar sa ya dai zauna yana kallon ikon Allah.

Ciniki ya fara tun daga naira ɗari har aka kai dubu ɗaya da ɗari biyar.  Nan ta tsaya chak ba motsi ba komi, ana shirin sauke ta ne Imran ya taka ya fita ya isa har ga Rahanatu ya cire rigar jikinsa ya lulluɓe ta da shi Sanan ya ce cikin gurɓataciyar hausan sa da ya tsinta a bakin su Haroon da yara bayan zuwan sa kano;

“Zan aure ta,  zan baki naira ɗari biyar da mota beetle (kande ba ɗuwais)”

“Bamu yarda ba,  cinikin kwana bakwai tace, zaka ci ka rage mana,  amma don bakin ciki kabila da kai kazo ka ce zaka tafi da haja,  kila ma arne ne baku ganshi fari ba” faɗin wani hakimi cike da kumfar baki.

“Haroon zo ka faɗa musu ko su yarda ko in rubuta kara akan sun sace min mata” Ya faɗi da larabci, nan take Haroon ya fassara musu yana mai cike da mamakin abokinsa.

“Kinga Laraba basu ita, kin ga larabci suke irin yaran nan ne da ake ɗaukan su aikin bincike,  in zance ya koma gun mai martaba Wallahi zamu raina kanmu,  kun san baya son baɗala ” faɗin wani zaune da Babban riga.

Nan waje ya hargitse masu tsoro suka bar wajen tun kafin a zo ayi gaba da su,  wasu kuma na zaune suna jiran su ga an ture ma buzu naɗi.  A Haka Haroon ya fakaice ido ya fice da Rahanatu bayan ya yara ma Imran inda zai jira shi.

Basu ankara da rashin ta ba har se da suka fice, nan fa wasu suka kara tsorata suna cewa “ai wannan Kyawun nata yafi karfin a ce mutumce. Da gani ka ga aljana gashi ta ɓace,  shi ma dai in aka bibbi dangi ne mu gudu”  Haba ai ɗaya Baya jiran ɗan uwansa suke barin wajen.Ganin sun watse ne ya fahimci abin da ke faruwa a wajen, nan ya saki dariyar da shi kan shi ya manta rabon da yayi irin sa. Ganin yana kafirin dariya yasa tsirarrun da suka rage ɓacewa da gudunsu.  Shima bai ɓata lokaci ba ya tafi zuwa inda su ka yi da Haroon zasu jira shi.+

Tafawa su ka yi da ya isa nan ya fara ba Haroon labarin abin da aka yi bayan ficewarsu. Sakin baki galala RAHANATU tayi tana kallonsu suna larabci. Nan kuma sai tsoro ya shige ta “kar dai ya zo aljanu ne” wani sashi na zuciyar ta ya sanar mata da hakan. Kawai sai ji lema tayi a matse-matsinta, shar sai ga hawaye,  nan kuma sai ta kasa ɗaga kafafunta ta daskare a wajen. Tsayawa sukayi suna kallonta ganin ta tsaya cak.

“Baiwar Allah lafiya me ya faru? ” Haroon ya tambaye ta.

Saukar fitsarin da ta ke makewa ne ya sa Haroon fahimtar a tsorace take,  se ya cire kanbas ɗin da ke kafarsa ya nuna mata da yatsa.

” kingani ba kofato garemu ba,  mutane ne kamar ki.  Gidanmu zan kaiki wajen babata, ina da kanni kamar ki sai kiyi kawaye kinji” Ya karasa yana mai lallashin ta.  Nan ya juya ga Imran ya yare masa abin da ya wakana da larabci.  Dariya yayi shima, yana kallonta yana dariya har suka isa gida.

Ɗakin babarsa ya kaita nan ya iske mahaifinsa na cin kwaɗon zogala, nan ya takaita masu abin da ya faru da kuma yanda Imran ya ce aurenta zai yi.

“kana ganin ma barshi ya auri karuwa?  Ina laifi ma y zaɓo ta gari a aura masa. Ni dai anya kar mu yi sanadin abin da gaba zamu zo muna dana sani” Ta faɗa tana jifan Haroon da harara.

“Kinga Binta tsaya, shin kinfi shi sanin karuwa zai aura,  ni a gani na jihadi zai yi sai dai kafin nan ke faɗa mana gaskiya me ya haɗa ki da gidan da aka tsinto ki” Ya karasa yana mai kallonta.

Jikinta na makyarkyata ta labarta masa labarin ta sama sama tun daga fyaɗen da Hadi yayi mata, zuwa mutuwar mahaifinta da haɗuwarta da Laraba. Nan take jikin mahaifiyar Haroon yai sanyi, 

“kin ji dai abin da yayanki yace, abokinsa ya ce aurenki zai yi.  In kin amince amma sai na je can garin naku in tabbatar da maganar da kika faɗa.  Na san cewa duk abin da mace tayi zunubi ne amma sak ɗinsa ga namiji ado ne.  Zuwa jibi zani garin in Allah ya yarda, ko kuma zan ma malam Audu mai gadi  magana in za shi ganin gida sai in bi shi, don wancan satin ya dawo, kuma yana cewa ba zai daɗe ba zai koma, sai mu koma insha Allah”

Da haka aka kira kanwar Haroon laminde ta yi ma RAHANATU jagora zuwa ɗakin kwanarsu.  Sannan ya aika a kira Imran.  Nan ma nasiha yai masa sannan ya faɗa masa abin da ya yanke. Yai godiya sannan duk akai haramar kwanciya.

                           ***

Sai bayan kwana biyu sannan Mahaifin Haroon ya samu damar haɗuwa da  malam Audu mai gadi.  Bayan sun gaisa ya ce da shi

“Nayi tsintuwar wata budurwa yar garinku,  wai an koro ta ne daga can shine nake so in zaka koma zamu je tare don karin bincike ” Ya faɗi  fuskarsa a sake wanda hakan ɗabi’ar sa ce,  da wuya mutum ya faɗi lokacin da ya ganshi cikin ɓacin rai.

“kar dai ace yar gidan malam Tanko ce,  Shegiyar yarinya duk da laifin uban ne,  wai a dole sai tayi boko,  ko anan zan iya kidaya matan da ake bari zuwa boko.  Toh garin yawon boko Hadi yayi mata fyaɗe,  shine ta kunsa ciki. Da ta haife abin kunya aka kora ta,  wallahi kar ka bari ta haife maka bala’i a gida don me za’a yi da wacce ta bari har namiji yayi sha’awa, ta sa shi yi mata fyaɗe.  Ni ba zani marke ba sai nan da wata biyu” Ya faɗi  yana kumfar baki, zuciyar sa kirin fiye da bakin gawayi.2

Mahaifin Haroon bai iya ce masa komi ba sai shafa masa baya da yayi yana murmushi ya wuce ta gefen sa ya wuce gida.  Nan ya sa aka kira RAHANATU,  ta shigo a sanyaye duk da ta dan fara saba wa da mutanen gidan amma duk da haka a tsorace take don gani take suma zasu kyamace ta kamar sauran mutanen garinsu.

“Na haɗu da malam Audu megadi. Ya faɗi daidai abin da kika faɗi.  Zan gaggauta aurar da ke ga Imran don ko ba komi mun shaidi halinsa. Tun kafin a ɓata miki suna a garin nan don na lura malam Audu a fusace yake da ke,  ki sa a ranki baki da kowa sai Allah sai kuma mijinki. Ki masa biyayya, ki kuma rike sana’a, sadakinki ya ishe ki jari, sana’ar ki shine mutucinki.  Bani bani shi ke fara kawo matsala a auratayya.  Ubangiji Allah ya sa albarka a aurenku,  ya baku ikon hakuri da juna” Ya karasa yana jin radadi da tausayinta a ransa.

Bayan tafiyar ta ya kira Imran shi ma.  Sai da ya gama tsokanarsa sannan yace da shi

“kasan a musulunci namiji na amsar ma kan shi aure ko,  mu a al’adanmu wanda bai ci karo da addini ba namiji na tura wakili ne.  Mace kuwa dole sai da waliyyi  wanda dole sai ya kasance musulmi,  balagagge mai hankali.  Dole ya kasance mahaifinta in yana raye ko wakilin Mahaifin (wanda uban ya yarda ya wakilce shi)  ko danginsa a lokutan da bai da rai.  An yarda da limami ko alkali ya zama waliyyi a lokutan da mahaifi da danginsa suke kafirai ko kuma lokutan da ba’a san dangin yarinya ba, da dai sauran lokutan lalura.  Toh Kaga ba’a san dangin mahaifinta ba,  asali ma su suka kora ta,  ni yanzu tana karkashin kulawa na don haka musulunci ya bani damar in aurar da ita matukar tana sonka.

Ko bayan auren ina mai maka nasiha da ka ji tsoron Allah ka rike ta amana. Wajibi a gare ka ne cinta, shanta, tufafinta da karatunta. Allah baka ikon rike amana ya baku zama lfy. ” godiya Imran yake zubawa don har ya cire rai ganin ba’a ce masa komi ba tun ranar farko sai ma ɓoye ta da babar Haroon keyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *