SIRADIN RAYUWA CHAPTER 21 KARSHE
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Miqewa yayi daga dosana dawawunshi da yayi saman hannun kujerar daya zauna akai tun dazun yana duba agogonshi,yaga alamar surutun nata bamai qarewa bane,kimanin minti arba’in da zuwanshi kenan amma babu wani abu me muhimmanci data gaya masa,sai soki burutsu da kwashe kwashen zance
“Allah ya bamu alkhairi” ya fada yana durfafar qofa,tanason ta sake tsaidashi ta bata mishi lokaci amma kuma ya mata kwarjini da yawa yadda ya hade fuska,hakanan tana kallonshi har ya fice
“Ja’iri,wannan baqin ran naka yau za’ayi maganinsa,gwara a soma tarwatsaka,muga qaryar fadin rai da izza,dan banza shi da uwarsa”.
Haka kawai ya dinga ji gabanshi na wani irin faduwa,irin faduwar gaban da bai taba jin irinta ba,ya lumshe idanunsa kana ya bude a hankali kuma a fili ya furta
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil,wala udwana illa alazzalimin” saiya danji faduwar gaban ya ragu,yaci gaba da tafiya a hankali yana dosar sassan nashi,yana kallon yadda sawu ya soma daukewa a gidan,kamar ba shine yayi cikar kwari dazu ba,da alama kowa ya nufi makwancinsa.
Sosai ya galabaitar da ita ya kuma qarar mata da sauran kuxarinta,hijabin jikinta ya tsarge,cikin tashin hankali tasa hannunta ta cukuikuye hijabin sosai ta hanashi sauka daga jikinta,cikin qarfin hali tasa qafafunta ta harbi cikinsa,yayi baya yana dafe da cikin saboda yadda ya qulle masa,hakan ya bata damar yunqurawa ta durfafi falo,shima ya miqe ya rufa mata baya.
Qafa ya sanya mata ya tadeta a tsakiyar falon,ta tafi luuu tayi qasa,wanda kafin takai qasa ta sanya hannunta,hakan yasa ta fadi akan hannun,wani irin zafi ya ratsa qwaqwalwarta,wanda batasan sanda ta saki wani gigitaccen ihu ba.
Kamar a mafarki yaji sautin murya kamar ta bilkisun tana fitowa daga sassansa,cak ya tsaya yana son tantance abinda yaji,sai kuma ya qara sauri zuwa ciki saboda wani bugu da zuciyarsa ta fara yi harya wuce na dazu.
A gaggauce yake ratsa falukan har zuwa sanda ya isa falon da bilkisun suke,daidai sanda yake tura qofar daidai lokacin daya sanya hannu ya fincike hijabin jikinta da taketa faman riqe dashi yana fadin
“Baki isa ki tseremin ba,har sai na cika burina a kanki,bazan zuba idanu yayita yin nasara a kaina ba tsahon…….” Maganar da bai samu damar qarasata ba kenan yaji saukar wani irin naushi a bakinsa,tsananin zafi yasa ya kasa tantance daga inda dukan yake,sai wasu taurari da suka soma kewaye kwanyarsa zuwa cikin idanunsa,kafin ya koma hayyacinsa yaji wata kyakkyawar shaqa data kusa wucewa da duka sauran numfashinsa da yayi saura,sai a sannan idanunsa suka sauka kan azeez,wanda launin fuskarsa zuwa idanunsa gaba daya suka sauya tamkar an watsa musu ruwan barkono
“Me…mmee……” Yaketa qoqarin yin magana,saidai azeez din ya riqe dukkan wata kafar numfashinsa,har sai da numfashin ya kusa katsewa sannan yayi jifa dashi waje guda
“Me kakeyi cikin dakin iyalina?,me kake shirin aikatawa kamal?” Ya fada a zafafe yana durfafarsa,cikin qarfin hali kamal din ya miqe yana son nuna nashi qarfin halin
“Me kake haka?,karka kuskura ku sake dukana malam na gaya maka” ya fada yana nunashi da yatsanshi,zallar haushinsa da yakeji shekara da shekaru a yanzu suna taso masa,tsana da qiyayyar yariman.
Bai kuma ankara ba ya wankeshi da wasu zafafan marin kuncin hagu da dama,sannan ya sake kaiwa fuskarsa naushi,wanda hakan ya baiwa haqoransa na gaba guda biyu da tun naushin farko suka soma girgidi damar xubowa qasa.
Duka tako ina yake kaiwa kamal din,wanda tun yana yunqurin yaga ya rama harya fuskanci zarrarsu ba daya bace ya soma qoqarin qwatar kansa ta hanyar bude qofofi yana neman hanyar da zai kubuta,yayin da azeez ke biye dashi bai fasa ka masa duka ba duk inda ya samu a jikinsa cikin tsananin fushi kishi da fitar hayyaci.
A haka har suka fito zuwa babbar farfajiya,daidaikun masu giftawa wadanda basu kai ga zuwa makwancinsu ba suka soma labewa cikin mamaki,suna kallon yadda azeex din ke jibgar kamal cikin hasken fitilun gidan.
Hannu daya yasa ya damqi wuyan rigar kamal din ya tayar dashi tsaye,kana ya soma janshi zuwa sassan da mahaifiyarsa hajja fauziyya ke sauka.
“Kiramin masu horon gidan qasa su sameni a wancan sashen yanzu yanzu” ya fadawa wani bawa da sukayi arangama dashi a hanya ba tare daya dubi sassan da bawan yake ba,wanda cikin hanxari da zallar biyayya ya wuce don isar da saqon yariman nasu.
Daidai lokacin da hajja fauziyyan ke zaune a katafaren falon dake sashen,sam hankalinta ba’a kwance yake ba tunda fulani adama ta gaya mata abinda kamal din ya tafi aiwatarwa,sam shirin da tsarin baiyi mata ba,har sukaso sudan haura da fulani adaman,saboda tana ganin don ba danta bane shi yasa ta aikashi aikata wannan alfashar,abinda kawai yadan kwantar mata da hankali idan ta tuna cewa idan suka cimma muradinsu to wannan zai bude musu wata qofa da zasu iya cimma muradinsu,amma matuqar komai ya daidaita xata cire adama me daga tafiyar,daga ita sai yaronta xasu amfana.
Bugun qofar da wani irin qarfi,da kuma faduwar wani abu kamar kayan wanki a gabanta shiya dawo da ita daga tunanin data lula,azeez ta gani tsaye a gabanta yana fidda huci da wata irin kama da bata taba ganinsa da ita ba,ta duba gabanta da kyau,sai taga kamal yashe cikin jini dake fita daga hanci da bakinsa.
A razane ta dora hannu aka ta kurma ihu,koda ba’a gaya mata ba tasan cewa lamari ya lalace kenan,idanunta a warwaje a matuqar tsorace tace
“Na shiga uku ni fauziyya,me zan gani haka?,abdul’azeez dan uwan naka zaka kashe?,jama’a kuzo ku tayani gani,yariman kaisa zaiyi kisa” ta soma kwaroroto wanda ya janyo hankulan jama’a,na nesa dama wadanda ke tsaitsaye saman hanya suna jimantawa gami da tattauna abinda suka gani din yanzu.
Tuni qofar sassan ya soma cika da ‘yan ganin qwaf
“Na kawo miki shine ya gaya miki meyaje aikatawa kafin a wuce dashi” azeez ya fada cikin fushi yana fidda idanunsa
“Meya maka haka abdul’azeez?,ashe shaye shayen naka da ake fada dai da gaskene?,to wallahi bazan yarda ba,abinda kayi masa saika karbi sakamakonka” ta fada tana matsar qwallar qarya.
Dai dai lokacin da masu gadin gidan qasa suka qaraso(masu kula da sashen manyan laifuka na prison din masarauta)
“Ku kamashi kuje ku kullemin shi” ya basu umarni yana mai juyawa don barin falon,yana jin yadda hajja fauziyya ke maganganu tana kurin ba wanda ya isa ya fita dashi,saidai sahun giwa ya take na raqumi,haka suka qwamusheshi suka ingizashi inda yariman ya buqata.
Zabura tayi daga inda take takure tana kuka sanda ya tura qofar ya shigo,tana ganin shine saita maida kanta taci gaba da kukanta,ya isa inda take ya dagata gaba daya ya sanyata a qirjinsa ya rungumeta tsam yana sakin wata nannauyar ajiyar zuciya,yana jin wani irin ciwo da qunci idan ya tuna yadda yaxo ya tadda kamal na shirin cin zarafin bilkisun,banda doka da shari’a tabbas sanda ya riqe wuyan kamal bazai sakeshi ba har sai numfashinsa ya wuce,yana jin wani irin zafi tun daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,kamar ana masa feshin wuta,huci kawai yake fiddawa yana sauraren sautin kukanta da yakejin kamar ana yanka mishi zuciya ne.
Tsahon lokaci suna a haka,sannan ya janyeta zuwa ciki,bandaki ya wuce da ita,ya zaunar da ita a toilet sit ya hada ruwan mai dumi sosai sannan ya iso inda take,idanunshi cikin nata yana nata qwarin gwiwa ya soma cire mata rigar baccin jikinta,sai daya rabata da komai sannan ya sanyata cikin ruwan zafin,ya tabbatar jikinta ya gasu yadda ya kamata sannan ya sake mata wanka banda wanda tayi daxu sannan ya maidota cikin dakin.
Wasu kayan ya sauya mata marasa nauyi masu taushi sannan ya suka koma saman gadon ya sake sanyta cikin jikinsa,kanta na saman qirjinsa,har yanzun kuka take,hakanan shima ya gaza furta mata komai bare ya hanata,don wata gobara ce take tashi daga zuciyarsa,yana wassafa hukuncin daya dace da kamal ne kawai,tsattsauran hukuncin da baiga abinda zaisa ya sassauta mishi ba,tunda yayi gigin shiga gonar data masa nisa,ta masa zarra,kwatankwacin nisan da tazarar dake tsakanin sama da qasa.
Sai can tsakiyar dare ya jita shuru bayan kukan ya dauke gaba daya,ya daga fuskarta daya tasa saboda kuka,yayi kissing kyakkyawan lebanta zuwa goshi,sannan ya gyara mata kwanciya a jikinsa yana jin wani qaunarta da kishinta na sake ratsashi,ya sake matseta gam cikin jikinsa kamar wani zai qwace masa ita.
Kwanan zaune yayi,saida aka kira sallar asuba sannan yayi yunqurin zuwa bada farali,zuwa lokacin ita dinma ta farka,sai data fara shiga tayi alwalar sannan shima yayi,shiya jagorancesu sukayi jam’in sallar tare suka idar,tsahon wasu mintuna bayan idarwar tasu sannan ya waiwayo yana fuskantarta,hannuwansa ya miqa mata,batayi jinkiri ba ta isa jikinsa,habarshi saman kanta ya soma lallashinta cikin taushi har zuwa sanda ta sauke ajiyar zuciya tana jin nutsuwa na shigarta,don jiya har barawon baccinya saceta bakinta na dauke da addu’a zuwa wayewar garin yau.
Wayarshi dake daura dasu ta dauki ruri,daga inda yake zaune ya miqa hannunsa ya jawota,sam yama mance da ita tun jiya,daya duba sai yaga me martaba ke kiransa.
Cikin girmamawa ya daga ya soma gaidashi,ba tare daya amsa ba yace
“Duk abinda kake ka barshi kaida iyalinka kazo ka sameni yanzun nan a babban falo” bai jira amsarsa ba ya katse kiran,saiya aje wayar kawai,ya miqe zuwa ma’ajiyar kaya dake dakin ya budeta,ya fiddo yalwatacciyar jallabiyya da wadataccen hijabi ya miqawa bilkisu
“Ki saka,zamuje wajen me martaba” alamun tsoro ya gani qarara saman fuskarta,saiya durqusa gabanta,ya kama hannayenta ya saka cikin nashi ya matse,idanunsa cikin nata
“Baki da buqatar ki tsorata ko ki raxana,zaki gaban managarcin mutum ne mai adalci,indai kuma ina tare dake babu wata halitta data isa taci zarafinki kota tozartaki matuqar ina numfashi a doron qasa” wannan ya bata qwarin gwiwa,saita miqe ta soma shiryawa,shima ya sauya kayan jikinsa sannan suka fito.
Yayi mamakin ganin mutanen dake hallare a wajen kamar ba safiya ba,kamal da mahaifiyarsa wanda yake zaune jikinta,da alamu sai daya ziyarci asibiti,cikin daren ne ko kuwa bayan sallar asuba ne bai san mishi ba,fulani adama,amminsa da babbar diyar me martaba yarinyar fulani saratu.
Cikin girmamawa ta gaida kowa sannan ta samu waje ta zauna,bayan shudewar wasu mintuna me martaba ya fara magana
“Me dan uwanka kamal ya aikata maka har haka cikin dare kahau dukansa kamar wanda Allah ya aiko,ka masa jina jina irin haka?”.
Wani abu me tauri da daci ya hadiye,baison ma ya maida maganar,amma dole ya fadeta,bai boye komai ba ya zayyanewa mai martaba,yana kaiwa aya fulani adama dake zaune gefe,wanda tun jiya da lamari ya baci take cikin taraddadi da tunanin yadda zata fidda kanta,tayi gudawa tafi sau a qirga,saboda ta tabbatar indai wannan abu ya fito da sunanta to Allah ne kadai masanin hukuncin da zai biyo baya,salati ta saka mai qarfi da salallami
“Kai kuwa kamal meya kaika aikata wannan tabargazar,matar dan uwanka?” Da mamaki hajja fauziyya ta dubeta,tabbas banda yau din tana tsoron tonuwar asirin fulani adama nata tonuwar asirinne da ba shakka saita bankadata.
“Kai kamal…anyi haka?” Me martaba ya tambayeshi,cikin hali na ciwo ya gyada kai
“Eh anyi haka,amma ita ta kirani,ita ta nemeni” kalmar data kusa ruguza zuciyar azeez da bilkisu,wadda batasan sa’adda data daga kanta ba,cikin zare idanuwa take kallon kamal din,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare
“Qarya yake!” Fulani aisha ta samu kanta da furtawa cikin fushi,duk yadda taso ta hana kanta magana amma wannan karon ta kasa.
Basu ankara ba har azeez ya isa inda kamal ke jingine jikin babarsa,yasa qafarshi ya take qafar kamal din,ta bada wata qara da yake bada tabbacin babu makawa ya karye,idan bai karye ba to ya samu mummunar gocewar qashi
“Gaya musu gaskiya!” Ya fada cikin qaraji
“Abdul’azeez!!!, agabana?” Me martaba ya fada cikin tsawatarwa,dole ya koma ya zauna ya fidda hucin bacin rai yana jin kamar yasa bindiga ya fasa kan kamal.
Shuru ne ya biyo baya na tsahon lokaci kana ya gyada kai
“Zanyi bincike….zanyi bincike kuma duk wanda na samu shike da laifi bazan daga masa qafa ba dai dai minti daya ba” maimartaba ya fada cikin kaushin murya,saiya waiga ya dubi Aafiya
“Ya ake ciki da likitan saratu” kanta a qas cike da alhini tace
“Sakamakon ganin abinda ya razanata da tayi,yace ta samu mummunan stroke wanda yake da wuyar magani,bugu da qarima wai jini yahaura qwaqwalwarta,akwai yiwuwar lokaci zuwa lokaci a dinga samun wasu dabi’u mabanbanta tare da ita”
“Ya salam” me martaba ya fada yana lumshe idanunsa,ya budesu a hankali yana musu umarnin tashi su tafi.
A yanayin da taga yariman ya shiga wunin ranar sai ta soma tausayinsa fiye kanta,zallar bacin rai qarara,bata tana tunanin haka yake da zafi da kuma fushi ba sai yau,kusan wunin ranar haka suka wuni suka kwana.
Ta fannin su hajja fauziyya kuwa sun cika da farinciki,saboda suna ganin sun samu hanya sassauqa da zata kawo musu qarshen komai,hakanan babu wani abu ko wata hujja da zata kubutar da bilkisu kota wanketa.
A kwana na biyun ana ya gobe kwanakin da me martaba ya diba na zai sake nemansu su cika,wajen goma na dare taga ya tashi zumbur daga inda ya maida wajen kwanansa wato dogiwar kujerar falon dake daura da dakin gadon,ya zura slippers dinsa ya fice,saita bishi da kallo cikin mamaki,don tun daxun take lallamarshi ya tashi yasha koda fresh milk ne,saboda babu abinda yaci wunin ranar,duk da fulani itama tayi iya yinta yaci wani abu.
Ba’a jima ba sai gashi ya shigo da wata laptop riqe a hannunsa,ya zauna bayan yaja qaramin table gabanshi ya dora akai,ya daga hannu ya mata nuni akan tazo,jiki a sanyaye ta iso,sai yaja hannunta ya zaunar da ita gefanshi,gami da dora kanta saman kafadarshi,dukkansu fuskokinsu na kallon laptop din.
Bata gane ne yakeyi ba,illa taga kaman ya rubuta wani kwanan wata ya shigar,sai vedio ya fara motsawa,tsayin mintuna kadan ta fahimci cctv camera record ne,sai kuma ta gane date din ranar da akayi wedding anniversary dinsu,tun daga rana yana wucewa har zuwa sanda duhu ya fara shigowa.
Sannu a hankali saiga gilmawar mutum cikin sanda,yayi zooming hoton saiga kamal quru quru cike da alamu na rashin gaskiya,saiya tafi next camera da zata kaishi daga falo na qarshe zuwa qofar bedroom din,take ta soma nuna masa gilmawar komai ciki harda kai kawon kamal,labewarsa,shigowarsu shiryawarsu da fitarsu dawowarsu da sanda azeez din ya sake fita,fitar data bashi damar afkawa zuwa cikin dakin.
Tsayin mintunan da suka kwashe suna gwagwarmaya a ciki saiga fitowarsu falon again yana yunqurin rabata da hijabin jikinta da qafa daya sanya mata ta zube a qas,fincike hijabin da shigowar azeez din,anan ya tsaida record din,ya sanya tafukan hannayenda duka saman fuskarsa yana shafa fuskar,a hankali ya furta
“Alhmdlh,na godewa Allah daya tunasar dani akwai camera a sassan nan,na godewa Allah zahiri da badini” ita kanta ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,wata nutsuwa na ratsa zuciyarta,ita kanta wannan shine abu na biyu daya taba gigita rayuwarta lokaci guda,tana tunanin ta inda gaskiya zata bayyana,kana ta kubuta,amma da yake Allah mabuwayin sarki ne,sai gashi ya kawo musu warwarar komai.
Ranar dukkansu baccinsu ragagge ne,kowanne na tsumayin ketowar alfijir saboda bayyanar da gaskiya.
A yau din zaman ya sauya salo,saboda samun qaruwar amintattun memartaba cikin xaman,gudun kada yaje ya zartar da hukunci kan kuskure,hakan ya sanya dole ya sakosu cikin lamarin.
Dukkansu tsakanin su ukun shi bilkisu ko amminsa ba wanda yace musu ta tafas sanda suka zage suna maida yadda akayi cike da son rai,da kuma son yiwa qarya kwaskwarima su fidda kansu,dukka saida duka gama zancansu damar magana ta dawo bangarensu sannan ya miqe da laptop din,yayiwa me martaba bayani a taqaice sannan ya kunna ta soma aikinta.
Gaba daya falon ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga computer din cike da mamakin abinda suke gani din,dai dai gurin da kamal din ya fincike mata hijabi me martaba ya rintse idanunsa gami da bada umarnin a dakatar da recording din.
“Oh ni adama naga ikon Allah,yanxu kamalu matar aure matar dan uwanka zaka yiwa fyade,wannan wanne irin lalacewa ne?” Ta fada tana zabgo salati gamida nuna tsantsar alhininta,duk a shirinta na fidda kanta daga wannan tarkon
“Meye banbancina dake?,ni xuwa nayi kawai na aikata,amma kome da saninku da shawararki akayi ko?” Ya fada cikin fushi dajin haushin yadda ta soma luguiguita maganar tun me martaba ko yan fadarshi basuce komai ba,inda yake kallon hakan a matsayin tunzuri kawai dason sanya me martaba ya yanke hukunci me tsauri akansa.
Maganar kamal din ta sanya kallo ya koma sama,sai kowa ya zubawa fulani adama ido,wadda ta zare idanu ta dafe qirjinta da hannu biyu kana tace
“Sharri?,sharri zaka yimin kamal?,fauxiyya kina jin danki?,yanzu irin sakayyar da zakumin kenan?” Yatsina baki tayi tana jin komai ta fanjama fanjam,ba zata bari sunan danta shi kadai ya lalace ba
“Eh to ai gaskiya ya fada,ba sharri yayi miki ba da kiketa wani haqiqancewa” sarai ta fuskanci kai sukeson hade mata su turota rana,don haka taga gwara kawai ayi mutuwar kasko
“Kice dai da saninmu duka,ku daina magana kuna ingizamin laifi na kada mana fauxiyya” shewa hajja fauziyya tayi,ta soma ratttabo.irin shawarwarin da fulani adaman tasha bayarwa akan yariman da uwarshi,ganin tana kwance mata zani a kasuwa yasanya itama ta soma lissafo nasu shirye shiryen,sai kowa yayi tsit kawai aka zuba musu idanu suna tonawa juna asiri kamar zasu doki juna.
Tsawa me martaba ya daka musu ganin abun yana neman wuce gona da iri
“La’ilaha ilalallah,muhammadurrasulullah” me martaba ya maimaitawa,hatta fulani aisha da wasu shirye shiryen tasan dasu amma ba qaramin mamaki tayi dajin wasu abubuwan ba,da hannu me martaba ya sallami fulani aisha da iyalinta,suka baro su adama zaune a gabanshi.
Shuru ne ya ratsa tsakani a lokacin da suke komawa zuwa sassansu,kowa da abinda ke mamayar zuciyarsa,imani ya sake ratsa zuciyar fulanin,tabbas ta sani cewa addu’a ce ta tare mata dukkan wannan masifa da bala’in da sukaso sanyata ita da iyalinta a rayuwa,ba shakka addu’a babu abinda ta bari,amma meta musu a rayuwa haka?,kawai donta hada miji dasu?,kawai don ta fisu siyasar iya zama dashi?,shin ita meye laifinta?,me yasa basuyi tunanin makomarsu a wata rana mai zuwa irin wannan ba?,lallai sau tari bawa shike xabawa kansa qarshensa sakamakon irin ayyukan daya gabatar da hannuwansa.
Ajiyar zuciya azeez ya sauke sanda sukaxo hanyar da zata kai kowannw sashensa,ya bude baki zaiyi magana fulani ta daga masa hannu
“Duk wata magana ta qare abdul’azeez,Allah ya fitar daku,ya fitar dani ya kuma fidda kowa,kuje kawai ku huta,ku samu hutun da baku sameshi ba” murmushi yadan fidda,koda yaushe yana sake jinjinawa mahaifiyarsa,koda yaushe tana hidimawa farincikinsu,tsayayyar uwace daya tamkar da dubu
“Inaso ki bani izini zuwa yammacin yau mu wuce saudiyya….already na siya mana ticket,kuma yau dama a qa’ida tafiyar zata kasance,so banyi tunanin komai zai warware a qanqanin lokaci haka ba,sai nayi tsammanin zamuyi missing tafiyar yau shi yasa nabar maganar”
“Na muku izini abdul’azeez,Allah yaci gaba da tsaremin ku a duk inda kuke,bari nasa afnan ta shirya ma su amatullahi kayansu” daga haka ta janyo bilkisu jikinta
“Kiyi haquri daughter,an bata muku ranakunku masu dadi ko?,amma ina da tabbacin yarona zai maida miki mafiyansu” wata iriyar kunya ta kama bilkisun,saita sunne kanta a kafadar fulanin,yayin da azeez shima ke fidda wani qawataccen murmushi yana jifan bilkisun da wani narkakken kallo,anan fulani tayi gaba ta barsu,saiya matsa kusa da ita ya sanya hannunshi cikin nata a tausashe suka fara takawa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace
“Kinji abinda ammi tace,kinaso na maida miki madadin kwanakinki wadanda suka fisu taushi da dadi?” Shuru tayi ta kasa amsa masa har suka kusa isa sashensu,saiya saki ajiyar zuciya sannan yace
“Nayi alqawarin nuna miki zallar so da zai saki ki nutsu da soyayyar da abdul’azeez ke miki ta gaskiya ce,tarayyarmu zata fara ne daga sanda kika bani amanna da kanki” bata gama fahimtar zancanshi ba amma saita share,gudun kada ya sanyata a kunyar da zata kasa sukuni.
Basu wani zauna ba da kanshi ya shiga hada musu duk abinda suke da buqata don tafiya,abinda ya bata mamaki yadda taga sassan nashi akwai komai da zata iya buqata a ciki,kamar dama can ta taba zama a ciki.
Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga
Adaren yayiwa me martaba sallama suka wuce filin jirgi bisa rakiyar uswa sumaira aafiya da afnan,wadanda suma a gobe suke saka ran wucewa gidajensu tunda komai yayi settling.
Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga suka gaidashi cikin girmamawa da karramawa,wanda hakan yayima bilkisun mahaifinta harma da ‘yan uwanta dadi,saboda girman da sukaga sun bashin sam.basu zaci haka ba.
Ta tadda ‘yan uwanta maza biyu cikin su ukun da Allah ya baiwa malam bilya sun waiwayo gida,babu wani cikakken lokaci na doguwar magana,amma tace su jirayi dawowarta,dama tana da qudurin nemansu koda su basu waiwayo gidan ba,ranta duka babu dadi,don dukansu babu wani gagarumin ci gaba ga rayuwarsu,kawai dai anata nemawa kai na rufin asiri ne,amma dai jiya iyau haka suke.
Suna hanya bilkisu na kusa da afnan,afnan din cikin murya qasa qasa tace
“Layinki fa da akayo swapping,wannan baturen likitan ya addabeni fa da kira,zan sunna masa rashin mutunci wallahi,baisan yanzun kinfi gaban wasa ba?” Ta fada cikin hade gira,murmushi bilkisun ta saki
“Karki masa rashin mutunci don Allah,ni da nakeso kiji dashi” ido afnan ta zuba mata cikin rashin fahimta
“Kamar yaya naji dashi?,gashi nace zan masa rashin m kince a’ah” dariya tadan kamata,saita dan daki cinyarta
“Haba qawata,ki fahimta mana,kiji dashi kawai nace fa” dan janye cinyarta tayi
“Rufan asiri ki daina kirana da qawarki,karki jamin balbalin bala’in mijinki yace na raina mishi mata,barni dai a qanwarki”
“To naji” ta fada tana dariya,sai maganar bilkisun tadan jefata a tunani,kimanin minti ashirin kuma saita saki murmushi tana gyara zamanta.
Saida jirginsu ya tashi sannan su afnan suka baro airphort din,suna saman hanya kowa na yaban bilkisun da yadda ta shiga ransu farat daya,tare da fadar bambance banbance masu yawa tsakaninta da safwa
“Dama tun da can bilkisu bilyamin ta dabance wallahi” cewar afnan,ta fara bata labarin rayuwarsu ta makaranta,da yadda a baya ta tsangwama mata,suka dinga dariya suna mamakin abun
“Yanzu gata sama dake,ta zama yayarki” inji sumaira,murmushi afnan ta saki
“Wallahi kuwa,dama bakasan matsayi da baiwar da Allah ya yiwa mutum ba,shi yasa akace kabar wulaqanta ko yima mutum kallon banza,saboda rayuwa wataran bakasan ya zata kaya ba,saika tsinci kanka a qarqashinsa watan watarana,duk da dani ni dama tun da can qasan raina ina sonta,miskilancinta ke bani haushi a wautata” haka sukaci gaba da tattaunawa har suka kawo gida.
¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶
Babban abinda ya kaisu qasa mai tsarki dama ibada ce,ibadar kuwa sukayi tayi tuquru baji babu gani,babu wanda keda lokacin wani a tsakaninsu,hatta da yaran sun sanyasu sun himmatu wajen addu’o’i,dukkan wanda bilkisu ta sani ba wanda bata saka a ciki ba baya ga kanta ‘yan uwanta yaranta dama surukanta da iyayenta,kwanakin qarshe qarshe suna gab da komowa gida saita tsinci zuciyarta ta karkata ga yiwa aurenta addu’a kan Allah yasa ya zama silar farincikinta dana mahaifanta duniyarta da lahirarta,sai ta sanya afnan,cikin zuciyarta tana jin fata da qaunar haduwa da qulluwar soyayya tsakaninta da dr adam,tabbas da tafi kowa farinciki.
Duk da ibada sukaje amma a wata gudan sun sake fresh da kyau saboda kwanciyar hankali,bilkisun ta yita daukar hankalin azeez din amma yana dakewa yana son cika alwashin daya ci.
Daga saudiyya kai tsaye ya dauketa suka wuce dangin mahaifiyarta,abinda bata san ya shirya masa ba sai ranar da zasu tafi,hakan ba qaramin faranta ranta yayi ba sosai,don dama anty zuhriyya nata saka ran zasu,to amma saboda yawa da suka dada dole akwai buqatar qara samun kudi da zasuyi tafiyar dashi.
Sunyi farinciki qwarai na ganinta da mijinta dama yaranta,dama already suna da labarin maida aurenta,sunso zuwa a sannan,amma ciwon da mahaifiyar mahaifin nata tayi a sannan yasa basu samu zuwa ba,saboda ta galabaita kamar bazatayi rai ba.
Sun shiga dangi sosai kamar wancan karon,su zaga gidan ‘yan uwa qwarai,sai daidaiku da sukayi nisa sosai,kuma duk inda ta sanya qafa tofa tare da azeez ne,hakan ya sanya kafin su taho dangin maman nata da yawa suka sanshi,sati daya suka musu suka musu sallama suka barsu cike da kewarsu,suma sukayi alqawarin zuwa musu nigeria duk sanda wani abu ya sake tasowa.
Ga wani mamakin nata daga can sai gasu a mali dangin fulani aisha,acan taga tarbar girma kamar yadda ta samu daga dangin mahaifiyarta,taga yadda mulki ke aiki,ta tabbatar da cewa sarauta da mulki ba qarya bane,lallai duk wata dagawa ko nuna isa da fulani ko ahalinta zasuyi basuyi qarya,bakuma suyi a banza ba,gada sukayi,ba takawa da hayewa ba,anan ta sake ganin zallar gata da azeez keda shi,kowa nan nan yake dashi da iyalinsa,wani lokaci idan ana lelensu kallo kawai take binsa dashi,saita ringa ji cikin zuciyarta anya batayi xari ba?,anya baifi qarfinta ba?,anya bai girmi ajinta ba?,daga baya da kansa ya karanceta,ranar tana masa wannan kallon ya kama hancinta mai tsaho da tudu yadan ja
“Karki shanyemin kyauna mana gaba kuma kice na miki tsufa kona miki muni,wannan kallon ki adanashi haka,yana son karya min qwarin gwiwata da hanani cika alqawarin dana dauka,ki cire duk wani shakku ko tantama dake ranki,abinda azeez ya sani kawai shine,yana miki zazzafar qauna har muddin numfashinsa,ba gama garin qauna da kika sani ba wadda kika saba jinya ba a bakin kowa” saiya girgixa kai yana sakar mata wani murmushi na musamman sannan ya dora
“zai kuma ci gaba da qaunarki har ranar da za’a tasheshi a qiyama,shi naki ne har abada,kamar yadda kike tashi har abada” ya sunkuya yayi kissing goshinta kana ya soma takawa zai fice,don dama ya gama shirinsa ne zaije su gana da kakanshi ya tsaya amsar breakfast daga hannunta,kamar yadda yanzu ya zame masa al’ada,baicin komai daga hannun kowa.indai har bilkisun bada kanta ta bashi ba,yakance yafi shiga cikinsa ya xauna yaddda ya kamata.
Kwanaki goma sukayi cikin dangi me dadi,a kwana goman nan itama taga dangi dangi sun ganta,sun kuma nuna mata qauna da kulawa kamar su riqesu suyita zama dasu karsu tafi,musamman su amatu da suketa daukan hankalinsu,don wani zubin saisu wuni bata gansu ba.
A kwana na sha daya ya tashi da wayar abdurashid
“To baban soyayya,abun nema ya samu,sai kayi haquri hakanan tunda an cimma buri,kaje ka duba babban kamfaninka,kawai matsala,nayi qoqarin gyara komai amma ya gagareni,dole saika shiga da kanka”
“Naji,kar a sake kirana a irin wannan lokacin” ya fada cikin dakiya yana katse wayar,saiyabar abdulrashid da waya galala,daga bisani kuma ha saki dariya,yarima ne,yasan xai aikata fiye da hakan.
Kusan kamfanin shine zuciyar duka kamfanoninsa,samun matsalarsa zai iya jawo durqushewar harkokin kasuwancinsa dama shuhurar sunansa,don haka ya maida hankali wajen samawa su bilkisu visa din shiga qasar.
Randa ya gaya mata sai tace
“Daka barmu mun koma gida,kai sai ka wuce,ka tarad damu a can” wata harara mai kashe jiki ya aikata mata dariya nason qwace masa,yaso ya dago dalilinta na fadar hakan,tanason kasancewa tare da mijinta amma har yanzu nunawa take baya gabanta,batasan idanuwanta da yanayinta na bayyana mishi komai ba,shi kuma ya zuba mata idanu ne kawai yanason yaga gudun ruwanta,to tana ganin kamar ba amfani kenan kasancewarsu tare shi yasa tace ya barsu su tafi shima ya wuce
“Naqi wayon,ai bari kiji…..wannan wata tatsuniya ce asanda nake abdul’azeez dina da bashi ga tsuntsu bashi ga tarko,yanzu kuwa cikakken magidanci nake me iyali,kisa a ranki duk inda na jefa qafata to akwai taki a wajen” idanu ta fidda
“Aikina fa….ka manta da aikina a brazil?” Yana tattare kayayyakin da sukaci abinci ya bata amsa,don idan dai yana nan kusan shike hidimar yaransa,harma ya hada da nata,abun yana matuqar daure mata kai,yakan zama wani na daban idan yana cikin iyalansa,kai bakace basaraken yariman nan bane,kuma fitaccen dan kasuwa na duniya
“A sanda kike qarqashin umminmu kenan ko?” Sai daya gama hade kayan yakai yara da sukayi bacci daki ya dawo sannan ya kuma dubanta
“Kina tunanin kamata matata zatayi aiki?,aikinma qarqashin wani kodadden bature daya taba sonta?,lallai ko da daga ranar sunana mahaukaci” rasa amsar bashi tayi,kawai saita bishi da kallo,ya dawo da baya ya hure mata idanun da iskar bakinsa.
¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
Isarsu qasar yasa ya sake zama busy sosai,baida cikakken lokacin kansa ma,yana can yana gyara abubuwa da maidasu kan saitin tsahon lokacin daya kwashe baya cikin kamfanin baya kuma ziyartarsa.
Hatta da yara sunyi bala’in missing dinsa,sun riga da sun saba dashi,kusan kome shike musu,amma yanzu saidai maminsu tayi musu,wuni suke suna tambayarta shi,saidai ta kira musu shi a waya ta hadasu.
Lamarin bilkisun nata bashi dariya da kuma qayatar dashi,ita kanta batasan tana nuna mishi fushi da daukewa lamuranshi kai ba,emotio n ne naso da qauna tun daga zuciyarta amma batasan yana tasowa yana tambara kanshi ba,gamida bayyana muraran cikin ayyukanta ba,ita duk a nata zaton tana jan ajinta ne da nuna ko a jikinta.
Ranar da al’amura suka soma daidaita yayi qoqarin dawowa da wuri saboda yaran,ya cimmata a kitchen tana qarasa hada abincin dare,da yake tunda suka sauka tace tafi ganewa ta dinga musu girki,don haka ya musu siyayyar komai na iya adadin kwanakin da yake saka ran zasuyi cikin qasar.
Tunda ta amsa sallamarsa saita ci gaba da hidimarta,ya saki murmushi yana aje briefcase din daya shigo da ita,ya taka a hankali zuwa bayanta,ya kama qugunta da hannayensa suka biyun ya mannata da jikinsa.
Kusan tare suka saki ajiyar zuciya,saidai ita bata shiryawa hakan ba,hakan yasa ta sake hade rai
“Yarafa,kada su shigo” saiya dan rabata da jikinsa,ya sanya kanshi a bayanta ya kwantar sosai
“Bugun zuciyarki ya saba da yadda asali,hakan shike qaryata duk wani lafuzzan bakinki da kike furtawa,kina qaryata kanki da kanki ne kawai,koda baki fada ba na sani kema kinji dadin dawowata,right?” Zame jikinta tayi
“Kayine dama saboda yaranka,nasan kuma zasu fini jin dadin hakan,sannu da zuwa” ta fada a gajarce,saiya saketa yana sakin dariyar daya kasa danneta,shi kansa zuwa yanzun yakai bango,ya gaji yana buqatar akai qarshe,hakan ya sanya ya tsara nan da kwanaki hudu zaiyi qoqarin kammala komai su wuce qasarsu su samu isashen hutun da zai bude mata sabbin shafukan darussan madarar soyayya masu wahalar mantawa a duniyar ma’aurata
“Shikenan,bari na tafi inda ake maraba dani” ya fadi yana daukan jakarsa,kamar tace masa ya dawo yaci gaba da tsaiwa da ita amma saita kasa,tana daga kitcen din tana jiyo dararsu da yarab,saita saki murmushi data tuna wata interview da akayi dashi dazu data kalla a tv,kamar bashi ba yanzun,acan zallar kwarjini tsare gida da aji kawai take kallo daga hamshaqin matashin dan kasuwar,amma a yanzu ya koma magidanci mai samawa iyalinsa farinciki da walwala,kamar ba shine na cikin tv din ba,totally dabi’unsa suna burgeta dari bisa dari,wanda ita kanta batasan sa’adda daya shiga rayuwarta har haka ba.
Tunda suka sauka a nigeria ita kanta tasan ranar ta musamman ce,wani sabon salon kulawa take samu daga gareshi,tsokana yake mata da gayya,kome zai mata zai mata shine in a romantic way,ta yadda zan taba har can cikin zuciyarta.
Kai tsaye masarautar kaisa suka fara sauka,suka kuma yada zango a sassan fulani aisha,wanda ta shirya musu walima,duk da gidan a dan cike yake sakamakon hidimar bukukuwan sallah da akeyi,akwai baqi a gidan da masu zuwa xiyara su fita.
Har bayan magariba tana tare da fulani,wadda a yanzun take daukar bilkisu kamar afnan babu wani banbanci,harma tafi gatanta bilkisun akanta,hakan ya qara sanyawa bilkisu ta saki jiki sosai,kuma take mata kallon uwa.
A wunin ranar ta shiga sassan fulani saratu don ta duba jikinta,har yanzu dai tana nan jiya iyau,ba wani abu daya sauya,komai sai an mata,hatta bayan gida da fitsari a wajen take sai an gyara.
Abun ya baiwa bilkisu tausayi sosai,me rai ba’a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,gadai dukiya sarauta da asali duka tana da,amma basu isa su bata lafiya ba,kuma basu hana qaddararta fada mata ba,sai taji tsoron Allah ya sake kamata.
Baki afnan ta tabe sanda bilkisu ke mata zancan
“Dukkansu abinda suka shuka shi suke girba,itama ashe akwai nata boyayyen abun data aikata sai daga baya nauyin haqqi yasa take fallasa kanta itama,kamar yadda su mama adama sukayi,kinsan idan zunubi da haqqi ya yiwa mutum yawa Allah kuma yaso kamashi da kansa yake tonawa kansa a siri,yanzun haka ita mama adama bamusan ina tayi ba,tuni me martaba ya qara mata wuta da takaddar saki,wanda mu a masarautar nan indai kina matsayin matar sarki kuma akaga ya sakeki lallai kin aikata wani babban zunubi,koda ba’a san meye ba to zai zame miki abun kunya ne sakin daya miki,ba kuma lallai kowa ya aureki ba,baresu da dukka baqin dake cikin gidan nan a gabansu suka fita suna maida magana ita da anti fauxiyya suna ci gaba da tonawa kansu asiri,ita anty fauxiyya an nesantata da masarauta na shekara goma,kamal nacan yana jinya tun daga randa abun ya faru daga qarshe aka gano yana da cutar HIV ne,yanzu meye amfanin irin wannan rayuwar?,shi yasa koda yaushe akeson ka shuka alheri,don ba zaka taba shuka ƙaya ba sannan kace inibi kakeson cira,sam” sosai labarin ya sake kada bilkisu,ya kuma sake zame mata darasi,kusan duk wanda tasan ya aikata zalunci ko wani sharri sai taga qarshensa sakamakonsa baiyin kyau
“Allah kasa mufi qarfin zuciyarmu,kada ka bamu ikon zaluntar kowa dai dai da qwayar zarra” ta samu kanta da furtawa a sarari,afnan ta amsa da amin
“Amin”
Ba’a wani jima da idar da sallar magriba ba yashigo sassan fulanin,tunda suka dawo yau din yana tare da me martaba a fada,da yammaci kuma suka rabu abdulrashid ya janyeshi,sai yanzu ya samu ya yakice,don ya shiryawa ranar yau din sosai.
Daf da ita ya zauna har cinyoyinsu na gogar juna,ko kunyar afnan baiji ba
“Ina ammi” tana dan kauda kai tace
“Tana wajen me martaba” saiya maida dubanshi ga bilkisu cikin wani kallo me kashe jiki
“Tashi kawai mu wuce…..na gaji princess,ina buqatar na huta hakanan” kafada ta maqale kamar qaramar yarinya
“Bamuyi sallama fa da ita ba,sannan su amatu suna tare da ita,kaga dole saimun jira sun shigo”
“Nooo….ba wannan lokacin” ya fada yana miqewa yana zura mata wayarta a handbag dinta dake aje gefanta,da sauran kayan da yasan nata ne.
Dole badon taso ba ta miqe ta gyara yafen mayafinta tana duban afnan
“Muje ki bani ajiyata” batace komai ba ta miqe,saita waiwaya ta dubi azeez dake tsaye yana qare mata kallo
“Zan karbo saqo”
“Minti daya…..karki wuce haka” ya fada yana nuna mata da yatsa.
“Ungo,gwara ma ku tafi,anaso ana kaiwa kasuwa” afnan ta fada tana miqa mata leda mai kauri wadda fulani ta bata daxu,bata buda ba saboda haka batasan meye a ciki ba,fusga tayi tana jifan afnan din da hararar wasa
“Dama waye yace miki ba’aso din bare akai kasuwa,yafi qarfin a kaishi kasuwa,ko a gidama sai mai rabo” baki afnan ta rufe dariya na kamata cikin jin dadi
“Allah y bada haquri,ashe haka yayan nawa yake da bala’in tsada?” Tana murmushi dayafi kama da ‘yar dariya dariya ta soma takawa zata fice sannan ta bata amsa
“Qwarai kuwa,idan baki sani ba gwara ma yau ki sani” dadi ya cika afnan din sosai na yadda ko yaushe soyayyar yayan nata da qawarta ke sake bayyana muraran a idanun kowa.
Su biyu ne rak cikin motar,bai yarda kowa ya bisu ba,domin yana buqatar kadaicewa sosai,tare da nuna mata ainihin abinda ke ranshi,duk da zuwa yanzu shi kanshi yayi amanna cewa bata tantamar komai a kanshi.
Hannunshi cikin nata sanda yake tuqin,yana dan murzawa a hankali,wanda hakan ya kuma kashe mata jiki,sai tayi laqwas cikin sit din motar,sanyin ac yana ratsata,ga wani feeling na daban kan mijin nata.
Juyawa yayi kadan ya dubeta akayi sa’a suka hada idanu,saiya saki murmushi yana maida kanshi ga titi,cikin tattausan muryarsa can qasa kamar wanda ya fara bacci yace
“Ina fata zaki marabceni zuwa sabuwar duniya,zaki jarabtu da soyayyata kamar yadda na dauki tsahon shekaru ina cikin jarabawar taki soyayyar” murmushi tayi tana sunne kanta,saiya dan tsuke fuska
“Princess….wannan kunyar…Allah ya gani zata cuceni,bana sonta wallahi indai a yanayin da muke daga ni sai kene,a rayuwar aurena gaba daya da matata ban rubutata cikin lissafi ba,pls ki barni naci duniyata da tsinke” dariya maganar tashi ta bata,saita rufe bakinta da dayan tafin hannun nata,tana ci gaba da sauraren maganganunsa,wanda babu komai ciki face zallar mayen giyar qaunarta,inda ita kuma suke qara ruguxa duk wani qwarin gwiwa nata,suna sake cusa mata soyayyarsa mai tsananin qarfi.
Da ido ta dinga bin gidan sanda duka isa,village ya kaita,tun daga harabar gidan yanayinsa ya dinga saukar mata da wata nutsuwa ta musamman,komai anyi qoqarin yinsa ne bisa tsarin qauye da gargajiya,har wani qamshin qasa ke tashi na musamman,duk da dama damina ta soma sauka yadda ya kamata,hakan ya baiwa duk wani tsiro dake gidan damar fidda ainihin kalarsa,duk da dama ko da can kafin daminar haka zaka samu tsirran gidan,sakamakon samun ciakkiyar kulawa da sukeyi daga masu kula da gidan.
Rungumota yayi zuwa jikinsa,a hankali ya rada mata
“Inason irin wannan nature din,shi yasa nakeson gidan nan,idan ina cikin nishadi indai ina qasar kaisa,nakan zabeshi a matsayin wajen dazan huta” kaita gyada a hankali,itama zabinsu yaxo daya,don lokaci guda gidan ya mata sosai.
Tunda suka shigi ciki shike jan ragamarta,shike mata komai nata idanu,wanka suka fara yi suka hada da alwala sannan ya jasu jam’i suka gabatar da sallah,doguwar addu’a yayi musu,wadda ta sake ninka mamakinta akanshi,yanayin yadda yake addu’ar kawai ya isa ya shaida maka ya samu ilimin addini dai dai gwagwardo,suka kammala suka shafa,sannan ya waiwayo inda take zaune saman abun sallarta,fuskarsa dauke da fara’a ya matsa gabanta kadan
“Duk da wancan lokacin bamu samu damar yin salla da addu’a ba,har yanxu muna da dama aiko princess?” Murmushi kawai tayi tana tuna darenta a wancan rana,wani irin bahagon dare da bata taba jin koda labarin dare irin nata ba,saiya sanya hannunsa ga goshinta,ya karanto addu’ar da annabi yayi umarni akan kowanne ango ya yiwa amaryarsa.
Yunwa takeji sosai don bataci wani abun kirki ba,don haka ta langabe waje daya,kamar ya sani ya dubeta
“Muje mu samu wani abu muci ko?,dare na dada yi” ba musu ta miqe tabishi a baya.
Madaidaicin daining ne me kyau da akayi da wani irin katako na zamani amma an mishi suffar gargajiya,yadda taga an jera akushi saman teburin sai abun ya sake burgeta harta saki murmushi,shi yaja mata kujera daya ta zauna kana yana daga tsaye ya soma sarving dinta da nau’in abinci mara nauyi
“Yunwa fa” ta fada a shagwabe tana shafa plate tummy dinta,ya gane abu me nauyi takeso,saiya girgiza mata kai
“No my dear…..saiya hanamu rawar gaban hantsi….right?” Ya qarasa maganar yana kanne mata idanu,saita dauke kai cikin kunya,don tuni ta baro jirginsa.
Basu dauki dogon lokaci ba suka kammala,da kanshi ya kaita wani bedroom wanda ta cika fa mamakin tsarinsa shima
“Welcome to my world dear” ya fada yana janta cikin jikinsa,hannayensa saman cikinta
“Anan nake fatan bude sabuwar rayuwa wadda zata jagorancemu zuwa gina wata sabuwar rayuwa cikin sabuwar duniya….”saiya dan zameta daga jikinsa da sauri yana cewa
“Ina zuwa…get ready kafin na dawo” ya fada yana murmushi gami da nunata,bata iya amsa masa ba saboda yadda qafafunta ke rawa harya fita,saita samu gefan gado ta zauna tana qoqarin saisaita kanta.
“Kin manta ke din ba bilkisu bace shekara takwas baya?,yanxun ke dr bilkess ce,maman ‘yan biyu,kuma mata ta aure” zuciyarta ta tunasar da ita,hakan ya zaburar da ita ta miqe ta soma shirya kanta cikin yanayin datake da tabbacin zai faranta ran azeez din.
Cikin tattausan rigar bacci wadda ta tsaya mata iya gwiwa ta shirya kanta,ta gyara kanta da kyau cikin mayuka da turarukan qamshi data gani saman madubin,kowanne lungu da saqo.na jikinta ta bashi haqqinsa,sai data kusa kammalawa ta tuna da ledar da ammi ta bata,sai kawai ta janyo ta budeta.
Wadansu irin turarukane designers masu aji tun daga kwalbar ma bare akai ga kudinsu,tun tana kalla a tsaye sai data janyo kujera ta zauna cike da mamaki,ita kadai amma tana jin kunyar kanta da kanta tare da mamakin nau’in turarukan,turare ne na hammata,qasan gwiwar qafa,na gwiwar hannu daban,na bayan kunne daban,na qasan cibiya daban,na matse matsi da cinyoyi,ga wani na gashi shima,harda na mutstsukawa a tafin hannu zuwa yatsu da kuma na jiki gaba daya,sai wata yar qaramar takarda da rubutu da bai wuce layi daya ba.
_kiyi amfani dasu daughter yadda suke,Allah ya albarkaceku_
A nutse ta bude kowanne ta kuma yi amfani dashi a muhallinsa,kana ta baibaye jikinta dana jikin.
Ita kanta sai data lumshe idanu tana shaqar yadda jikinta ya game da wani irin qamshi mai ratsa zuciya da qwaqwalwa jiki da bargo gaba daya,ta sauke ajiyar zuciya tana maida turarukan cikin kwalinsu.
Daidai sanda ta gama ya turo qofar da sallama a bakinsa,sai tayi tsil a inda take tsaye,saboda bataso ya ganta a hakan ba,don ko gashinya bata samu hadewa ba,bayan ta gama feshi shi haka ta sakeshi ta barshi ya bazu saman kafadunta
“Wow….wow” ya fada idanunsa kamar xai fado qasa yana dubanta,saiya kasa qarasowa a hankali ya soma sassarfa,wanda yana zuwa sama yayi da ita gaba daya,sai kuma ya soma shanshanata lungu da saqo a zafafe kamar wani tababbe,cikin wani irin low tune yace
“Ina kika samu turaren da nafiso a rayuwata princess?….na sake yarda na kuma sake tabbatarwa keta musamman ce….kece mahadin rayuwata” tun daga nan ta fuskanci ya soma sakin layi,ba’a rufa minti biyar ba jikinsu ya yiwa qafafunsu nauyi,tsaiwar ta gagaresu,yana riqe da ita ya isa makunnun fitila ya kashe,ya qarasa gefan gadon still ya kunna wata iriyar fitila mai suffar duma wadda take da sauqaqqen haske,kana iya ganin mutum sosai amma ba tarwai ba,ya qarasa saman gadon da ita a hankali ya direta kana ya biyo bayanta.
Wasu irin xafafan saqonni masu narka tsokar zuciya yake aikata mata,wanda duk inda kakai ga dauriya baka isa ka tsallake musu ba,abinda ya bata tsoro shine yadda tun daga nan bakinsa ya kasa shuru,duk inda hannunsa ko bakinsa yakai saiya yaba mishi kafin ya wuce gaba,ga tsoro ga kunyar yadda yake gaya mata wasu irin lafuzza masu nauyi kanshi tsaye,baiko jin nauyi ko tuna komai,ga wata iriyar soyayya dake son narka mata zuciya,daga qarshe jikinta na rawa ta dora yatsanta saman lips dinsa dake rawa kamar wanda kejin sanyi a hankali tace
“Shshshshsh” saiya dago fuskarta gaba daya ta yadda zai kalleta da kyau,ya nutsa duka yatsunshi cikin lallausan gashinta yana dubanta da birkitattun idanunsa data kasa jurewa kallonsu koda na seconda daya kuwa,kansa ya girgiza,cikin rawar murya yace
“I can’t,bazan iya yin shuru ba princess….idan nayi shuru abun zaimin yawa,saina haukace,qwaqwalwata ita kadai ba zata iya dauka ba,keta musamman ce,wallahi keta dabance tun daga nan,na gaya miki tun daxun,na soke wata aba mai haruffa biyar a sanda muke tare wato kunya,saboda nan din duniyarmu ce mu biyu,daga ni saike….ki taimakeni don Allah ki kaini duniya ta gaba…” Shuru tayi tana saurarensa jikinta na tsuma,wasu irin hawaye masu dumi na farinciki suna silmiyo mata,bata taba kawowa ko a mafarki rayuwar zata juye musu haka ba ita dashi,bata taba kawowa lokaci zai sauya komai ba a tsakaninsu,harsu sake zama qarqashin inuwa daya ba,a sanyaye idanunta a lumshe ta gyada masa kai,saiya soma jera mata godiya yana sanya harshensa saman fuskarta yana dauke hawayen dake kai,daga bisani kuma taji ya sake kunna daya daga cikin qayayen dakin,hasken ya qaru duk da baikai na farko ba,saita bude idanunta da sauri,ta sake maidasu da sauri ta rufesu saboda kunyar ganinsa da taji ta kamata tana girgiza masa kai alamun ya kashe qwan,saiya girgiza kanshi
“Am sorry my princess,wancan karon a wancan ranakun baki ganni ba,ki bari a yau a yanzu ki ganni,ki ganni a yadda nake,ki ganni a abdul’azeez dina,ta yadda zamu sake sanin juna dakyau,ta yadda zaki sake yarda nidin a wajenki ba kowa bane,ta yarda zai sake yarda cewa idan ina hannun bilkisuna ni ba yarima bane,ba dan kasuwa bane,ba kowa bane face bawa wanda sai yadda taso zata juyashi” kai ta girgiza,har yanzu jikinta rawa yake a tsorace take
“Kayi haquri ka kashe,duka na yarda duk abinda kakeso na yarda dashi din” dole ya rage din kamar yadda ta buqata,kana ta sakar masa ragamarta ya kaita duniyar data manta da kalarta,ta kuma.manta da yadda ake shigarta,sai gashi a wannan daren ya tuna mata da komai,ya tuna mata da wani abu da tayi tsammanin ya faru bazai kuma maimaituwa cikin rayuwarta ba kenan har abada,sai gashi ayau komai.ya dawo sabo fil tsakaninsu.
Shi kansa yasan ba qaramar juriya da jarumta ta nuna ba,saboda shi kansa baisan yawan bashin daya tarawa kansa ba saida akazo wajen,saboda tashin hankalin tunanin rasata daya shiga ya bunne dukkan wani feeling nashi,nutsuwa da kwanciyar hankalin daya samu yanzu suka dawo da komai sabo,hakanan itama ta nata fannin ta tsorata da lamarin,sai taga ashe a wancan karon imani da tausayi kawai ya nuna mata sabanin yanzu data ji a ajikinta bakin gwargwado.
Washegari duk wani bashin tarairaya da kulawa da a wancan lokacin ya bar mama sodangi dashi sai daya bashi kaf,tamkar darensu na farko haka ya lalace wajen kula da ita,ita kuma ta baje kolin shagwabarta son ranta harda mara dalili ma,kwana daya rak ya ida daga mata qafa,next day ya kasa haquri yace shifa saiya koma,babu yadda ta iya haka ta bashi dama,a washegari tayi tunanin zasu je su koma gida amma sai taga shi zama ma kamar lokacin ya fara,data masa qorafi sai kawai ya kalleta,ya miqa mata hannu a hankali ya mata masaki zuwa jikinsa saman cinyarsa sannan ya bata amsa
“Nifa bazan rayu cikin jama’a ba dake,saboda zan iya barin abun magana,sonki yamin yawan da bazai barni na iya katabus ba,koda xamuje musun ma keda fita daga gidan nan saikin goge,kin zama ‘yar hannu qwarriya irina,so nake mafa idan mun tashi fita mu fita da tsarabar wasu twince din wa ammi,naga alamun tana buqatar jikoki birjik,tunda du wadan can sun tsaya gayun banza da wofi,basa haihuwa sai bayan wasu shekaru” kunya ta sanyata kwantar da kanta saman kafadarsa tana murmushi
“Amma su amatu fa?” Kanta ya dungure da dan yatsanshi
“Kajimin yarinya,an gaya miki su suna ta tamu ne?,affy ta gayamin ko tambayarmu basa yi sun xama ‘yan gida,kina tunanin ma ammi zata bamu su?,gwara ma ki dage ki samo mana namu eheeennn….” Saiya tura hannunshi cikin rigarta,tasa hannu da sauri ta dafeshi tana turo baki
“Haba mana princess,dan kadan fa,yaufa sau daya na ɗana” saiya shiririce mata,yadda ta bada kai da kanta ba tare data shirya ba.
A ranar ya turama safwa sakinta,tare da rufe dukkan wani babi nata,dama nutsuwa yake son ya sake samu,yana sane da rashin albarka da suka sake yiwa amminsa bayan tafiyarsu cikin azumi data aika ma safwan da kayan buda baki da sunan azeez din,abinda yasa yaji har zuciyarsa koda itace autar mata ya barta kenan.
Cikin kwanakin gaba daya basu da aiki banda suci susha su kwanta,sai hirarrki da bitar rayuwar kowa,kowa yana baiwa dan uwansa labarinsa tun daga quruciya xuwa girma.
Labarin rayuwar bilkisun ya karya masa zuciya,ya qasa sanyashi jin cewa zafi ko sanyi,wuya ko dadi babu abinda xai rabashi da ita,ya sake jin cewa ita din tashi ce,haduwarsu wata rubutacciyar qaddara ce daga Allah.
A zaman nasu kowa ya dinga qoqarin fahimtar dan uwansa,bawai bare baki sukayi akayita xuba soyayya tsurarta ba,tunda suna sane da cewa zomu zauna zo mu saba,kuma rayuwar yau zaqi ce gobe madaci,hakanan indai xa’a zauna tare dole wataran za’a samu sabani fada ko rashin jituwa,hakan ya sanya kowanne ta wani fanni yake qoqarin fahimtar ra’ayi zabi da halayyar dan uwansa domin wanzar da zaman lafiya a rayuwar aurensu.
Duk hankalinta yana gida,tanaso ta samu ‘yan uwanta maza kamar yadda tayi alqawari bayan ta dawo,hakanan tanason zuwa taga anty zuhriyya,duk kullum Allah sai sunyi waya,amma tana son taje ta ganta,don ba qaramin kewarta tayi ba.
Da qyar randa suka cika kwana goma cikin gidan ta lallabashi ya amince xata,amma qafarta qafarshi,tace ta aminta.
Cikin daya daga cikin sabbin motocinsa dabai taba hawa ba samfurin wannan shekarar suka fita,daga ita saishi sai driver ba tare da rakiyar kowa ba.
A mota yayi xamanshi,yace idan baba yana nan ta mishi magana ya leqo su gaisa,idan kuma bai nan shikenan ta gaida mutanan gida,ta samu malam.bilyan ya dan samu ya fita miqe qafa,umma katti ta aika kan ya shigo ko ruwa yasha amma yace aa,dole suka barshi.
A zaman da tayi dasu ta yanke bude manyan shaguna kowanne dai dai qari akan na mahaifinsu,saidai wannan dinma zai xama kamar qarqashin na malam bilyamin dinne ta wata fuskar kuma kamar nasu,zasu dinga raba ribar da aka samu gida uku,su baiwa malam bilya daya daya su su riqe bibbiyu,uwar kudin kuma a sake juyata.
Hakan ya faranta musu matuqa da gaske,basu taba zaton a rayuwa bilkisun zata musu rana irin haka ba,kudaden data fadi zata zuba cikin kowanne shago kawai ya gaya musu ba qarami shaguna xata bude ba,sun nemi alfarmar ta tayasu da addu’a,Allah yayi riqo da hannayensu.
Daga nan gidan anty zuhriyya ya kaita,ta dinga dariya hannunta riqe da bakinta
“Anya bilkisu wannan komawar itama ba wani rabon ne yayi kira ba?,kinga yadda kikayi mulmul kuwa?,wannan soyayya da yarima ke baki karta sangartaki da yawa” maganar ta sata kunya sosai,tadanfi jimawa wajen anty zuhriyya suna tattaunawa da kuma sauran shawarwari data qara bata,sannan sukayi sallama tare da uwar tsarabar da yarima yasa aka shigo da ita kamar yadda aka kai gidansu,wanda duka batasan dasu ba.
Basu fita a gidan sunje masarauta ba sai da suka kwashe wata guda a gidan,duk da shi yaje ya amsa kiran me martaba,wanda ya dinga fada kamar zai cinyeshi danye kan sakin da yayiwa safwan
“Allah ya huci zuciyarka,banda wani sauran zabi tunda ta nuna ra’ayin bata da sauran sha’awar zama dani,ban isa na mata dole ba,sannan babu wani goyon baya daga wajen magabantanta,suma bamu da ikon tilastasu su bamu diyarsu” wannan furuci nasa yasa fafan baiyi wani dogon zango ba
“Aure rai gareshi,saikaci gaba da addu’a idan da rabo.nan gaba za’a koma dole”
“Rabbi kasa bai cikinnqaddarata har abada” ya fada can wasan zuciyarza ba tare daya bari.me.martaba yaji ba,ita kuwa fulani banu a inda tace banda
“Allah ya kyauta,yasa hakanne mafi alkhairi” dariya yaso qwace masa,bai taba tunanin akwai lokaci da zaizo hakan ta faru ammin ta dauki abun da sauqi har haka ba.
Randa xasu gidan murna kamar bilkisu tayi me,shi kuma ya dinga hade rai,harsai data tambayeshi cikin salon tsokana tsokana
“Da kaje za’a isheka da gaishe gaishe tun daga bakin qofa,ko ina ma’aikata birjik,kuma kome kayima iyalinka saiya wani zama abun kallo,kamar kaidin ba mutum bane kamar kowa” dariya ma ita ya bata
“To ai laifinka,kune idan kuka shiga mutane saiku ishesu da hada gira,ku cikasu da kwarjini,kaga kuwa duk abinda xakuyin zai xama sabo a wajensu” damqa yakai.mata
“Zaki to kuwa jawo a fasa zuwa,tunda kinama goyon bayansu ne” a shagwabe ta kama kunnuwanta da hannayenta biyu
“Tuba nake yallabai,ayimin afuwa,inason naje naga mamata ammi”.
Sanda suka isa sassan fulani saita kasa sakewa kamar baya,nauyinta da ada takeji yanxun ya sake daduwa,datace mata
“Baqin haura katanga,babu sallama saidai a lalubeku sama ko qasa a rasa” kamar xata tsaga qasa ta shige haka taji,afnan ta soma taya ammin bilkisu ta jefeta da harara,qasa qasa tace
“Kici gaba,dab nake da tona asirin soyayyarku da baturen likita adamu wajen yayanki” saita kama hannunta da sauri ta riqe tana fadin
“Tuba nake antyna,kimin rai,karki ballomin ruwa,ki bari komai ya gama dai daita don Allah”.
Yadda afnan ta fada kusan hakanne,su amatu yaran ko a jikinsu,sunata shagallensu a gidan,suna zuba shagwabarsu son ransu,’yan gata tako wanne fanni,baga ammin ba baga me martaba ba baga sauran jama’ar gidan ba,wanda rashin fulani adama a gidan da lalurar fulani saratu yasa da yawa da basu gane alkhairinta ba wadanda abaya basa jam’iyyarta yanzu ta zama tasu,sun gane ashe a baya bautar banza kawai suke a inda ba’asan qima da darajarsu ba.
Ranar sunsha hira sosai da mama sodangi irin wadda suka jima basuyi irinta ba,batasan tayi kewarta ba sai a sannan,zataso a bata mama sodangi su zauna tare,saboda matar tayi tako ina,amma.batasan ya yanayin tsarin nasu yake ba,batason ta cika azarbabi da yawa.
¶¶¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶
Tare dasu akayi bukin babbar sallah na bana,fulani ita ta sake zama cikakkiyar me masaukin baqi,ta karbi kowa babu banbamci,kama daga yaran adama dana saratun gaba daya,abinda ya sanyayar da gwiwar yaran,suka soma sauya tunani a kanta,tare da sare kaso mafi yawa na qullaci da qiyayyarta da aka dasa musu cikin zukatansu,musamman yaran fulani saratu wanda sun jima da fara saduda,ganin yadda bata bari mahaifiyarsu ta wulaqanta ba daga wajen jama’ar gidan ko mijinta ba,tana bakin qoqarinta wajen ganin ta samu kulawa yadda ya kamata.
Hawan sallar na bana ya bada qaye sosai,tawagar yarima da abdul sunfi kowacce tawaga daukar hankali jan magana da jawo cecekuce,a ranar ko cikin gidan duk inda ka gifta hirarsu ake,saboda kome iri daya suka sanya,sai suka tashi kamar hassan da usaini,banbancin kawai shekaru ne.
Hutun sati guda kawai da bukin sallar ya tashi komawa bakin kasuwancinsa,sanda yake shaidama ammin hade ranta tayi tsaf
“Wai kana nufin na debi yaran nan na baka kuyita yawo dasu,baku nan baku can?,tab….a’ah wallahi bada ni ba,kudai kuje saikun dawo,duk sanda kuka waiwayomu ku kuka jiyo,amma bada jikokina ba”.
Koda ya shaidama maimartaba shima bayan ammi ya goya,don shi kansa yaran sun shige jikinsa da zuciyarsa sosai,duk da yana qoqarin boyewa saboda sauran jikoki da kuma idanun al’umma,amma dole wani abun bazai boyu ba,don abudul har kujera guda aka masa kusa data me martaba cikin fada a madadin mahaifinsa,sau tari dashi ake zaman fadar,don dole ya haqura suka soma shirin tafiyar shida bilkisunsa.
Kafin tafiyarta sai data tabbatar an gama kome na kasuwancin yayyenta,malam bilya wannan karan kasa jurewa yayi sai daya saka kuka,yadda ya riqesu a baya da abinda yayi ya dinga masa ciwo,da qyar ta kwantar masa da hankali.
Tun cikin jirgi ta soma jin wani zazzabi na cikin qashi,yarima nata zolayarta dako qwallonshi ya shiga raga ne?,sai tsoro ya kamata saboda tuna azabar da tasha laulayinsu amatu,amma kuma kwana biyu da isarsu data huta taji ta warware sai hankalinta ya kwanta,ta dinga ma yarima daya qwallafa rai gwalo tana cewa
“Dama ni nasan babu wani abu” kaman yayi kuka don har ranshi yaso ace ta kamu ne
“Bari murna yarinya,don ni jikina ya bani,kuma na riga da nasan nayi winning” tana sheqa masa dariya tace
“Shikenan zamu gani ai” qaramin ya tsansa ya miqo mata
“Mu daura….duk wanda yayi winning a tsakaninmu zai sadaukar da wani abu ma dan uwansa”
“Na yadda” ta fada tana miqa masa yatsarta tana dariyar mugunta.
Saidai kuma tun ba’ayi nisa ba ta fuskanci yariman nata ya riga da yaci gari,sai taja bakinta ta tsuke tana tsoron tsiyar da zai mata.
Saida laulayi ya soma tabata ya debe ta suka nufi asibiti sannan komai ya bayyana,murna kamar ya maidata cikinsa haka ya dinga zumudinsa tana kallonshi,ji yake kamar ya lasheta,godiya ya dinga zuba mata kamar ita ta baiwa kanta,kula sosai ta samu daga wajen likitoci da nurses din,wanda hakan ya sauqaqa mata wahalar laulayin ba kamar nasu amatu ba.
Baice mata komai ba saida suka dawo gida,bayan sun samu nutsuwa ya miqa mata hannu
“Alqawarina….me za’a sadaukarmin?” Saita langabe kai a shagwabe
“Pls mana (Ameer),ban da lafiya fa?” Dariya ta qwace masa,yadan mintsini cinyarta,saita sake masa kukan shagwaba gaba daya tana fadawa jikinsa,ya sanya hannayensa kuwa ya tattareta gaba daya cikin jikinsa yana sake shagwabata
“Abu daya fa,abu daya fa baby zaki bani” ta sake tura baki gaba
“To meye?” Sai daya dagata sosai ya zaunar da ita saman cinyarsa,idanunsa cikin nata,ya sanya tafin hannunsa tsakiyar nata
“Rayuwarki nakeso ki sadaukarmin,ki mallakamin rayuwarki,kome runtsi kome wuya ki zama a tare dani” qayataccen murmushi ta saki wanda ya bayyana jerarrun fararen haqoranta
“Wannan ai tsohon alqawari ne tsakanina dakai ameer” kai ya gyada
“Yes na sani,amma wannan na musamman ne” saita kama hannunta ta dora saman qirjinta
“Allah ya zama shaida haka zuciyata cewa na mallaka maka komai nawa,idan nace komai ina nufin komai din” qanqameta yayi sosai cikin jikinsa,yana jin kamar yafi kowanne namiji sa’ar mace a duniya,kamar yafi kowa sa’ar samun soyayya.
Wannan cikin kusan tare sukayi rainonsa,ya kasa shuru sai daya shaidawa amminsa,wanda tsananin murna ya hanata sukuni,ba yadda bata so ya dawo da ita gida ta zauna da ita ba amma ya toge,hakan yasa dole ta shirya mama sodangi ta bisu.
Hakan ya farantawa bilkisu rai sosai,saita kuma sakewa abinta,tana jin kamar wata uwace a tare da ita,zamansu da mama sodangin kamar wancan karon,cikin girmama juna nishadi da walwala.
*_BAYAN SHEKARU BIYU_*