WATA SHARI’A
CHAPTER 9
Duk kukan da mukeyi baisa mutanen sunji tausayinmu ko daya ba, Cike da rashin imani suka ringa watsi da baki d’aya kayakinmu, Ga gawar Afrah cikin buhu ga kuma Baba da yake kwance baya ko alamar numfashi,
Kukanma nemanshi nayi na rasa, sai mama daketa ambatar sunan baba amma har yanzu ko alamar motsi bayayi.
“Ku tashuwa min daga k’ofar gida bana son ganinku, idan ba haka ba kuma a
wulakantaku cikin unguwar nan” mutumin mai gidan hayar ya fada cike da izgili da gadara.
Mutanen da suka kawo gawar Afrah d’aya daga cikinsu yace
“Kai kuwa bawan Allah ka tausaya masu mana, bakaga hakinda suke ciki ba? Ka barsu suji da d’aya mana, tunda dai kasa an fitar masu da kaya ai sai ka shafa masu lafiya haka, tunda mai gidan nasu ma gash!” nan kwance bama asan halin da yake ciki ba”.
A wulak’ance yace
“Babu ruwana da halinda suke ciki, gidana kawai na sani kuma na basu minti goma
subar harabar nan, idan kuma basu bari ba duk abunda na masu su sukaja”.
Cikin rashin tsoro na tashi tsaye, Ko alamar kuka babu a idona na dubeshi ido cikin ido nace
“Kaga malam ka kama kanka, na kula kai baka da tunani kuma baka san darajar dan adam ba,
Munfl karfin ka wulak’antamu wallahi,
Sannan kuma duk halinda ka tarar damu daga Allah ne, bawai dan Allah baya sonmu bane kaga ya barmu a haka,
Jarabtace kuma babu wanda yafi karfinta, Kaima bakafi karfin Allah ya jarabceka ba”.
Dariya ya kyalkyale da ita tare da fad’in
Yan mata Kenan, dama an bani labarinki tun kafin inzo, wallahi kinji na rantse, idan na tafi na dawo na sameku anan zakiyi mamakin abunda zan maku, ni nafl karfinki fad’a min wannan maganganun marasa dad’i” yana gama fadin haka yajuya ya tafi,
Gardawansa ma suka mara masa baya.
Sai a lokacin na sakejin wani irin kuka maras control yazo min, Wannan mutanen su suka ringa rarrashinmu tare da kwashe mana kaya suna kaiwa gidan daya daga cikinsu,
A gidanshi aka sallaci Afrah, a lokacin har ankai Baba asibiti domin duba Lafiyarsa.
Bayan ankai Afrah ne muka tafi”: asibiti,
Mukayi sa’a kuwa Baba ya farfado,
Farin ciki mukayi sosai Mama ta matsa kan gadon ta rike hannunshi,
Da kyaryake iya bude idonshi sai hawaye ke fita daga idonshi, A hankali ya iya bude bakinshi tare da furta
“Ku yafemin nasan tawa ta kare,
Wanda suka zalunceku ku barsu da Allah shi zai maku sakayya,
Ku rike addu’ah a ranku kamaryanda Baffa da Hassu suka riki addu’ah kuma tayi masu
jagora a cikin ‘Dodon Jatau,‘ dukwanda ya riki addu’ah baya tabewa,
Sannan duk wanda yazo neman aurenki Aishatu karki boye masa abunda aka miki, bana son zalunci ya shigo ciki,
ldan kika fada masa yaji zai iya aurenki shikenan, idan ba zai iyaba kuma sai kici gaba da neman zabin na gari”.
Kuka muke sosai nida Mama har babu mai rarrasar wani,
Da kyar baba yaci gaba da fad’in
“Ku kula da rayuwarku, kuyi kok’arin rike ,,, karku jefa kanku a wani hali saboda abun duniya” tari sosai yaci kamashi,
Jini ne yabi bayan tarin saigashi gulluma gulluma yake Fita abun tausayi,
Salati muka dauka nida mama, hakan yasa shima baba ya dauka yanayi,
Muna direwa shima yana direwa, bai iya furta komai ba sai ajiyarzuciya da yayi wanda shine fitar ranshi.
“lnnalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Kawai muke fadi nida Mama.
“Bai mutuba wallahi da ranshi, likita! Likita kazo ka tabbatar mana da Abubakar bai mutu ba, nasan bazai taba tafiya ya barmu ba” Mama ta kara fashewa da kuka. ‘
Bayan likita ya shigo ya tabbatar mana da Baba ya rasu, hakan yasa muka karfafa kukan namu, Da kyar muka fita daga d’akin saboda gadon da gawar baba take mama ta rike da karfin gaske tana kuka.
Sai washe gari aka kai Baba, kasantuwar yamma tayi lokacin da ya rasu din, ko kafin akai gawar a shiryata ma duhu ya fara.
A gidan mutumin daya jagoranci gawar Afrah da Baba muka zauna, Bayan munyi sati biyu zuwa uku a gidanshi a lokacin har mun fara ,,,, ya samar mana wannan gidan da muke ciki anan unguwar Tudun wada, Anan muke rayuwa nida Mamana, sosai kawu Nasiru (wanda ya taimakemu) yake kula damu tamkar ‘yan uwanshi na jini, Duk lokacinda nama mama maganar mu tafi wurin danginta kona Babana sai tace a’a, saboda lokacinda zasuyi aure duka danginsu basu soba, lyayenta sukace inharta auri babana to babusu babu ita har abada, A gidansu babama haka akace masa, Sun aminta da hakan sukayi aure sannan suka bar Kaita suka dawo cikin Katsina. Wannan shine labarina, ina fatan zaki taimakemu inhar kinada halin yin hakan, ki kwatomin ‘yar uwata inhar tana raye”. Ummimah na gama fadin haka ta fashe da kuka.
Mama ta share hawayenta tace “Tabbas duk abunda Aishatu ta fada miki gaskiya ne, cutarmu akayi amma an nuna anfi karfinmu ta hanyar dukiya, bamuda galihu ko kad’an”.
Cike da tausayi Sultana tace “Ki daina fadin bakuda galihu Mama, Allah yana sonku ai, kuma insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe tunda har Allah ya jefoni a rayuwarku”.
“To waima waye ya fada miki muna cikin wani hali?” Mama ta tambaya saboda abun ya bata mamaki.
“Ni kaina ban sanshiba Mama, ya boye kanshi koma waye, Amma kuma yanzu duk ba lokacin wannan bane, Na daukar maku alkawarin zan taimakeku bakin karfina, sannan kuma mijina babban
Lawyer ne am sure shima zai taimaka min dan ganin mun gurfanar da Salmah a gaban alkali”.
Koda duka duba har dare yayi duk basu sani ba, Da hanzari ta duba wayarta tayi kicibus da 21 missed calls, Tashi tayi ta masu bankwana sannan ta fita ta shiga motarta tana kokarin dialing
number’n Umar mijinta.
Bugu daya kuwa Umarya dauki kiran cike da zakuwa yace “Hello wifey”
“Honey kamin uzuri dan Allah sai yanzu na kula da kiranka”,
“Ehh tunanin da nayi kenan dama, ina fatan dai lafiya”,
“Lafiya kalau wallahi, ka jini shiru wallahi najima a inda naje din ne, kuma akwai magana sosai sai na dawo, barin dauko su Hafsa sannan mu wuto gidan da sauri”,
“Ai su Hafsa tun d’azu suna gida wifey, kuka tayima Hauwa’u wai tunda ba zaki dawo ba ita gida take so, a dole saida naje na d’aukosu”,
“Oh ni Hafsa ba hakuri, bari to indawo yanzu gani a hanya”,
“0k sai kin dawo” Umar ya fada tare da tsinke wayar.
Nannauyar ajiyarzuciya ya sauke kasantuwar jin matarshi tana lafiya, damajinta shiru da
yayi yasa hankalinshi ya matuk’ar tashi.
Ajerin missed calls d’inda ta tarar harda na Hauwa, Hakan yasa ta kiranta, Babu bata lokaci itama ta dauka.
“Maman Hafsa lafiya dai ko?” Ta tambayeta cikin tashin hankali. ‘
“Lafiya kalau Maman Zarah, na saka wayar ajaka ne ashe a silent take ban sani ba, kin sanmu lawyers da yawon bincike, shi,isa kukaji shiru ban dawo ba”,
“To masha Allahu Aunty, Hafsa dai basu yarda sun tsaya ba”,
“Ehh haka Abbansu ya fad’a min yanzu, bansan mesa ba Hafsa batada yarda, waini gani nayi ga Zarah nasan zasuyi wasa tare ashe bata yarda ba”,
“Wallahi kuwa, bakiga kukanda tasha ba kamar wacce zan cirewa kai”.
Dariya Sultana tayi tace “Ai dama dai ku kuka zabarwa kanku rigimammiya, ga Haydar dina dan albarka yaro shiru shiru babu hayaniya sai natsuwa”, Itama Hauwa dariyar tayi “Ai sai shiru shiru din, wannan yaron ai saike, yaro sai barna da rashin ji? Yau saida ya fasa min kaf kwaina dake cikin fridge, tumaturina kuwa saiya fasa ya fara sha sai ya yarya sake fasa wani, duk ya gama wulakanta min kayan fridge, Haydar saike kadai Aunty
Sultana”.
Wata dariyar Sultana tayi saboda Haydar ya bata dariya sosai, itama kanta haka take fama da barnarshi kullum cikin dukanshi take amma kamar tana tunzurashi.
“Aunty Hauwa ai dan albarkar kenan, danma kun samu ya saka miki albarka a kayan fridge? Dana yaron kirkine”,
“Wallahi Aunty Sultana zan kashe wayar nan indai maganar d’ankin nan zakina yimin”,
“Naji dai Aunty, dama na kariso gida yanzu nima, ki gaisarmin da ‘yata Zarah, saida safe”,
“To saida safe, ki shafamin kan Hafsa ‘yar albarka”,
“To Aunty Hauwa zan shafa miki kan Haydar dan albarka”.
Murmushi tayi tare da hanginp up na kiran ta miyar da hankalinta ga kwanar gidansu da
zata shiga.
Parking tayi bayan ta shuga gidan, da hanzari Haladu ya iso gareta, hand bag dinta ya karba bayan ya gaishe‘ta
Ciki ta shiga yana biye da ita har suka isa parlor,
Bayan ta karbi jakar tayi godiya ta kalli inda Hafsa take kwance tayi bacci hawaye duk sun bushe a idonta,
Murmushi tayi tare da furta “Hafsa kayan rigima” ta shiga dakin mijinta.
Dan kishingidawa yayi yana ‘yan rubuce rubuce a wata takarda dake karkashin wani file,
“Assalamu alaika ya Habeebee” ta fada cike da soyayya.
Kanshi ya dago fuska d’auke da murmushi yace “Wa’alaikissalamu ya Habibty“, “Sannu honey, kajini shiru afwan”,
“Babu komai wifey, ina kika shiga ne kika dauki wannan tsawon lokacin?” Ya tambayeta
bayan ya harhada takardun a cikin file, saboda baya hada aikinshi da kuma kula iyalinshi.
“Ka gafarceni Uncle Umar da bayanin da zan maka”,
Saurin tashi zaune yayi saboda yasan akwai matsala, duk lokacin da Sultana zata kirashi da Uncle Umar to tabbas akwai matsala ne.
“Me farune wifey? Allah yasa lafia” ya furta idonshi kyam a kanta.
“Uncle Umar na saba maka, ka hanani kula wanda yake turo mana text messages din nan amma na kasa hakuri dole saida na kula,
Wadda yake fada mana din tana cikin wani hali tabbasa tana cikin matsanancin halin, kuma tanada tsananin bukatar taimakonmu, dan Alkah inaso ka taimaka min mu hada
karfi da karfi domin kwatar mata fansa”.
Kallonta ya sakeyi bayan ya rike mata hannu cike da soyayya “Anything for you wifey”.
“Yauwa honey na, sunanta Aisha Abubakar…” ta labarta masa komai tun daga farko har karshe bata boye masa ba.
Ba karamin tausayawa Ummimah yayi ba shima, “Lallai ke jaruma ce wifey, kin cika ‘yar aljannah, Allah ya bamu ikon taimakonsu”,
“Ameen mijina na kaina,Allah karya kawo ranar rabuwarmu”. Murmushi Umarya mata tare da cewa
“Aikuwa dole zamu rabu wifey, akwai ranar da mutuwa zata rabamu”.
Wata ‘yar kwallah ta digo mata take tace “How I wish mutuwar ta d’aukemu tare honeyna, ko kuma ta fara d’aukata, bana fatan ka mutu ka barni saboda bansan yanda zan iya rayuwa idan babu kai ba”.
Dode mata baki yayi yace
“ki daina wannan maganar wifey, lets close the chapter, kije Hafsa na can kwance a parlor ki kaita dakinsu, Haydar ma yana dakin Safiyya”.
“0k honey” ta fada tare da share hawayen daya fara fito mata.
Bayan ta dauki Hafsa ta kai d’aki ta koma d’akin Safiya ta samu Haydar ya makalkale Safiyya yana bacci, Ita kuma sai dan bubbuga bayanshi take itama baccin yana shirin daukarta.
Kallonsu tayi cike da so, a bayyane ta furta “Allah sarki Safiyya Akwai soyayya tsakaninki da Haydar, ban san ya zakuyiba idan zakiyi aure”. Bude idonta tayi tayi murmushi ba tare data furta komai ba.
“Yau bacci tunda wuri haka Safiyya? Ko dan bana nan ne?”,
“Momy kenan, ai idan bakya gidan nanjinshi nake kamar babu kowa a ciki, mun saba kullum wannan lokacin muna tare parlor muna fira, amma kuma yau bakya nan, gashi Hafsa ma kawar Firar tayi bacci tun dazu”.
“Hmm! Wallahi Safiyya wata ‘yar matsalace ta tsayar dani”,
“Ayyah Momy, Allah ya warware matsalar”,
“Ameen Safiyya, kawoshi” ta mika hannunta ta karbi Haydar da jikinshi yayi kace kace da ruwan tumatur duk ya bushe yayi dabbura dabbura.
Dakinsu ta kaishi ta saka mishi pyjamas dinshi sannan ta dorashi akan baby bed d’inshi blue, Hafsa kuma tana kan nata pink. Bayan ta tofesu da addu’ah ta fita, Kai tsaye alwala ta dauro ta gabatar da sallolin da ake binta na magrib da isha, tayi shafa’i da wutri sannan tayi addu’ah sosai ta koma dakin mijinta.
Ta sameshi yana kwance yanajiranta,
Murmushi ta masa sannan ta isa gareshi tana fad’in
“Na gaji wallahi honey” tayi hamma tana kallonshi
“Wallahi honey ba zakaji tausayinsu ba sai idan ka gansu, kaga gidan da suke, kaga halinda suke ciki, mamanta fa tace tun daga lokacin da abun ya faru yarinyar bata kuma samun walwala ba, kullum cikin kuka take”.
“Allah sarki bayin Allah, insha Allahi komai ya kusa zuwa karshe, zamu taimakesu sosai bakin karfinmu, har School ma zata koma da yardar Allah”.
“Allah ya yarda mai gidana na kaina” ta kama hannunsa ta bashi peck sannan ta mike domin canza kayan jikinta tana mai kara son mijinta, tana kuma karajin dadin yanda yake da taimakon mutane.