YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun bayan kammala sallar asubah Kuzeem bata koma bacci ba, ta duk’ufa aiki a system d’inta wanda ya d’auketa tsawon wani lokaci, daga baya ta buge da online shopping inda tayi siyayya me yawan gaske, don dama ita tana daga cikin mutanen da suka yarda da online shopping saboda yafi musu sauk’i, musamman ma ita da batada wani lokacin kanta, saida ta kammala komai kana taje tayi wanka ta shirya cikin wata blue gown, mai masifar kyau da tsada, tare da feshe jikinta da tsadadden turarenta mai shegen dad’i da k’amshi wanda ke narkar da zuciyar duk wani wanda ya shak’i k’amshinsa.

Wurin Binta dake baje kan gado tana sharar bacci ta isa ta tayar da ita tare da bata umurnin ta tashi tayo alwala ta gabatar da sallah, daga haka ta fice daga d’akin, kai tsaye gaban k’atuwar Tv plasma dake palorn ta nufa ta kunna, kana ta d’au remote ta dawo kan kujera ta zauna, sanja cannel tayi tare da d’an lafewa a jikin kujerar tana kallon news d’in daki-daki. Tsawon 7 minutes sai ga Binta ta iso palorn hannunta rik’e da wayar Kuzeem da aka kira, gyara zamanta tayi sannan ta karb’i wayar tare da d’aga kiran, a hankali ta furta,

ā€œMorning Sirā€.

Daga haka tayi shiru, bansan mai aka ce mata ba naga ta d’an wulk’ita kyawawan idanuwanta harta kai dubonta zuwa ga agogon bangon dake d’akin, sai kuma ta d’auke idanuwanta ta lumshesu kana tace;

ā€œMeyasa za’ayi haka?, shin ba’a yarda dani ba ne ko me?ā€.

D’an shiru tayi don ba k’aramin b’aci ranta yayi ba, idan ta cigaba da magana za’a iya samun matsala duk da ko yanzu ba wai zata k’i fad’in abunda ke ranta ba ne, saida ya kammala maganar da yake, kana ta bud’e idanuwanta tare da sakin wani guntun murmushi tace;

ā€œSir, idan zanyi abu ina yinshi ne da dukkan zuciyata kuma kun dad’e da sanin hakan, so banga dalilin da zaisa a rik’a bibiyar lamurran da suka shafeni ba, saboda ni naji na gani na kuma amince da wannnan aiki, duk da kuwa na san akwai tarin k’alubale a cikinsa, maganar gaskiya Sir banji dad’i ba ko kad’an, kuma nayi mamaki matuk’aā€.

A yanda ta k’arashe maganar zaka tabbatar da ranta yana a b’ace, ta sanadin hakan ne ma yasa bata jira jin abinda zai sake fad’a mata ba ta katse kiran tare da wulla wayar gefenta, ita mutum ce mai saurin d’aukar zafi musamman ga abunda taga alamar akwai cin zarafi a cikinsa, dama tun jiyan da ta fahimci akwai wata a k’asa dauriya kawai takeyi, saboda bata son aikin ya fice mata a rai don ta riga tasa kanta, kuma ta d’aukarma kanta alk’awalin duk tsanani duk wuya bazata ja baya ba.  Tana jin wani kiran ya sake shigowa wayarta amma tayi banza ta cigaba da kallon news d’in da take.

8:00am Rabson da Bash suka iso Estate d’in, don jiran fitowar Kuzeem saidai har 9:30am tayi basuga alamar zata fito ba, hakan yasa suka kama hanyar zuwa asibitin su Saimah a cewarsu ko ta tafi tun d’azun.  Suna barin wurin Saimah ta iso, horn tayi aka bud’e mata get d’in kana ta kunna kan motarta cikin Estate d’in, bayan tayi perking ne ta fito daga motar tare da bud’e back seat ta ciro wani had’ad’d’en basket na alfarma, kana ta nufi hanyar shiga gidan.

Mik’ewa Kuzeem tayi jin anyi Knocking door, gently ta isa wurin k’ofar ta bud’e, nan idanuwanta suka sauka kan Saimah, kusan a tare suka sakar ma juna murmushi kana ta d’an matsa gefe don ta bata damar shigowa cikin palorn, bayan Saimar ta shigo ne Kuzeem ta maida k’ofar ta rufe kana suka isa cikin palorn, Saimah na fad’in,

ā€œNa kiraki baki d’aga baā€.

Saida Kuzeem tayima kanta masauki akan kujerar da ta shi, sannan tace;

ā€œIna wani abune a lokacin, saisaā€.

ā€œOkay ai na manta agogo sarkin aiki kikeā€.

Inji Saimah tana harararta, Kuzeem dai bata ce mata komai ba ta maida hankalinta kan wayarta da sak’o ya shigo.

ā€œGa fa abinci nanā€.

Saimah ta sake fad’amata, a hankali Kuzeem ta kai idanuwanta kan basket d’in kana ta d’auke tace;

ā€œSaidai Binta, ni sai zuwa anjimaā€.

Wata hararar Saimah ta sake b’alla mata tare da tab’e baki kana ta janyo basket d’in ta ciro plate da spoon ta zubama Binta abincin.  Kuzeem kuwa mik’ewa tayi ta nufi k’ofa, yayinda Saimah da Binta suka bita da ido har ta bud’e k’ofar palorn ta fice.

Murmushi wata arniya dake tsaye wurin balcony tayima Kuzeem, tare da fad’in,

ā€œGood morning Ma’am!ā€.

Fuska ba yabo ba fallasa Kuzeem tace;

ā€œMorning, how are you?ā€.

ā€œI’m fine Ma’amā€.

Ta amsama Kuzeem har lokacin fuskarta na d’auke da murmushi, sannan ta nuna mata wata mota dake ajiye a gaban gidan tana fad’in,

ā€œGa kayanki sun iso Ma’amā€.

Sai a lokacin Kuzeem ta kai dubonta wurin motar da wani saurayi keta faman jido wasu manyan bags yana ajiyewa a wurin.

ā€œOkay thanksā€.

Kuzeem ta fad’a cike da kulawa.  Wani murmushin arniyar ta sake yi, na jin dad’in tarin siyayyar da Kuzeem tayi a wurinsu, wacce ta kashe mak’uddan kud’ad’e.

ā€œAlways welcome Ma’amā€.

Arniyar ta sake fad’awa Kuzeem, daga haka ta nufi wurin motar, yayinda Kuzeem ta rufa mata baya, cike da girmamawa saurayin ya gaida Kuzeem ta amsa mishi, sannan ta bashi umurnin shigar da kayan cikin gida, bayan ya gama ne, Kuzeem ta sake musu godiya inda suma suka yi mata godiyar kamar ba gobe, sannan suka tada motarsu suka bar wurin.

Kuzeem na shigowa cikin palor Saimah ta wulgo mata wani k’aramin pillown kujera tare da b’alla mata uwar harara tace;

ā€œWallahi matar nan bakida kirki ko kad’an, yanzu fisabilillahi muna zaune zaki wani turo muna k’aton gardi a cikin d’aki yana muna shige da fice?, haka kawai mun barbaje muna shak’atawa ya wani zo ya kallemu tas a banza da wofi, nidai wallahi kin cuceniā€.

Murmushi Kuzeem tayi, saboda Saimah na d’aya daga cikin mutanen da ke sanyata farin cikin dole, duk irin yanayin b’acin ran da take ciki.

ā€œKuzeem!ā€.

Saimah ta kira sunanta da k’arfin gaske, tana kallon Mom Eshmal da Mom Arif dake tsaye bakin k’ofar palorn ko wace hannunta d’auke da muciya, yayinda Mom Eshmal tasha wata uwar d’amara tana girgije-girgijen rashin mutunci da tijara. 

ā€œSu waye ku?, me kuke shirin aikatawa?ā€.

Saimah ta tambayesu tana mik’ewa tsaye, saidai bata yarda ta matsa daga inda take ba don kad’an take jira tayi wuf cikin d’aki. Kuzeem kuwa kyawawan idanuwanta ta wulga akan extension wire dake jikin d’aya daga cikin socket d’in palorn.

ā€œUwarki da ubanki zamuyiā€.

Inji Mom Arif tana wani tsikare d’an kwalin wata arniyar shadda dake jikinta, kana suka fara takowa zuwa cikin palorn, har lokacin Kuzeem na tsaye a wurin ta basu baya, kuma ko alamar motsawa batada.  Wata shewa Mom Eshmal tayi tace;

ā€œHeeee! lallai yarinya, to maza ki juyo kiga maza bisa kanki, ahayye nanaye yau zan nakkasa banza, billahil azim yau saina sanja maki kamanni kin zama abun kwatance, daga lokacin nasan bazaki sake gigin shisshigi akan lamarin kowa baā€.

Kamar k’yaftawar ido Kuzeem ta fisgo jibgegiyar extension wire d’in, sannan tayi saurin juyowa ta fuskancesu dakyau, don so take yau d’in nan ba sai gobe ba, ta koya musu hankalin da nan gaba sai sunji shakkun  yima wani mahaluk’i kallon banza, ballantana har suyi yunk’urin illata shi. Mom Eshmal na k’ok’arin magana ba zato ba tsammani taji saukar waya a jikinta, ai ba b’ata lokaci ta saki muciyar hannunta tare da kai hannunta saitin da Kuzeem ta lafta mata wayar, ganin abinda ke faruwa yasa Mom Arif tayo cikin Kuzeem saidai tun kafin ta k’araso Kuzeem tayi wuf ta koma ta bayanta sannan ta dagargaje ta lafta mata wayar itama a tsakiyar bayanta, wani shegen ihu ta saki abunka da jan buzu jiki baison wahala😂. Kuzeem kuwa kallon Saimah tayi cikin  wata dakakkiyar murya tace;

ā€œRufemin k’ofar can Saimah!ā€.✍️

*Tashin hankali mai remote*😂💔

       Cikin sauri Saimah ta isa wurin k’ofar ta rufe, tare da waro idanuwanta waje tana kallon Kuzeem da ta nufi wurin su Mom Eshmal. Ba k’aramin tashi hankalin Mom Eshmal yayi ba, ganin dagaske fa Kuzeem keyi jibgarsu zatayi, sai kawai marin da ta sakarmata jiya ya dawo mata a rai, wanda fad’in azabar shi baya misiltuwa. Mom Arif da bakinta bai gama mutuwa ba tace;

ā€œKuttmar uban chan! ke mu zaki daka?, lallai yarinyar nan ashe kuwa kaf danginku zasu k’are rayuwarsu a prison, wallahi kin taro fad’an da yafi k’arfinki gaba da baya, yau sai munga wanda ya d’aure miki k’ugu…ā€.

Kuzeem bata yarda ta bata damar k’arashe maganar ba, ta kai mata wayar a jiki, wani irin duk’ewa Mom Arif tayi a k’asa, tana sakin wata k’arar azaba, don ba k’aramin shigarta dukan yayi ba. Ganin haka yasa Mom Eshmal rugawa zuwa hanyar fita, Kuzeem ta fisgota da k’arfin tsiya ta dawo da ita baya, tare da sakar mata extension wire d’in a jiki, bata jira sun gama tantancewa ba ta aniya jibgarsu kamar donshi aka turota duniya, saboda a lokacin zuciyarta ta riga ta kawo har wuya, abubuwa biyu ne suka tarar mata a lokaci d’aya, wanda ko wannensu ya haddasa mata matsanancin b’acin rai.

Wani irin ihun neman ceto su Mom Eshmal suke, suna ba Kuzeem hak’uri, amma ko jinsu batayi don idanuwanta sun riga sun rufe, jibgarsu kawai take, ga babu damar wani ya jiyo ihunsu daga waje, saboda tsarin ginin Estate d’in daban yake da sauran gidaje, kuma ko banza akwai tazara tsakanin gidajen.  Ganin abun ba na kai sake ba ne, ya sanya Saimah saurin isowa wurin Kuzeem ta rik’eta tana fad’in,

ā€œNa shiga uku!, Kuzeem ya isa haka manah!, karki manta fa ba a hukumarku kike ba, kuma wad’annan mata ne ba maza ba balle kiyita jibgarsu haka, don Allah ki barsu karki jimusu rauniā€.

ā€œSaimah Idris Garba! wallahi kiyi gaugawar sakina ko in had’a dakeā€.

Ai tun kafin Kuzeem ta rufe baki Saimah ta daka uban tsalle tayi baya, jin yanda Kuzeem ta kira cikakken sunanta kai tsaye, cikin wata kalar murya mai cike da zallar b’acin rai. Ta san bak’ar zuciyar Kuzeem da kuma shak’iyancinta, ba k’aramin aikinta ba ne ta had’a da itan ta jibga, daga baya ta dawo tana bata hak’uri.

Binta kam sai murmushin jin dad’i take ganin yanda Kuzeem ke jibgar su Mom Eshmal, sai kuka suke kamar wasu k’ananun yara, sai ta rink’a tuno kalolin azabar da tasha wurin Mom Eshmal, shiyasa ko kad’an bata tausaya mata ba, amma ta d’an tausayawa Mom Arif saboda tana d’an kyautata mata wani zubin. Plate d’in abincinta ta janyo ta fara ci hankali kwance. 

Kuzeem bata daina dukansu ba saida taga sun galabaita har muryarsu bata fita sosai, wayar ta jefar a k’asa, kana ta hard’e fararen hannuwanta a k’irji tana jifarsu da wani d’an iskan kallo tace;

ā€œBa ku k’ananun ā€˜yan tasha ba?, masu degreen iskanci da tijara?, to yau ga mai masters da phd a gabanku, dama kunsan ance gaba da gabanta kou?ā€.

(Feeyaya dake lab’e a bakin k’ofa ta lek’o tace *Aljani ya taka wuta*🌚😂💔💃)

ā€œWallahi tallahi!, duk cika baki ne muke, don girman Allah kiyi hak’uri ki yafe muna, billahil azim daga yau har lokacin da zaki bar gidan nan ko kallonki bamu sake yi, balle har muyi miki wani abunā€.

Inji Mom Eshmal tana zubda k’wallah masu d’auke da azaba. Wani shu’umin murmushi Kuzeem ta saki, kana tace;

ā€œWad’annan kalaman nadamar, ba a yanzu nake buk’atar jinsu baā€.

A tare sukayi saurin girgiza mata kai alamar gamsuwa. Sauke hannunwanta tayi tare da pointing Mom Eshmal da yatsanta tace;

ā€œDaga wane k’auyen kika fito?ā€.

Murya na rawa Mom Eshmal tace;

ā€œRISAM…ā€.

D’an waro idanuwa Kuzeem tayi tace;

ā€œWow! amma ko kad’an bakiyi kama da mutanen Jahar RISAM ba, saboda kowa yasan sunada halin dattako, ilimi, sanin darajar d’an adam, da tausayi, sai kuma gashi ke ko d’aya bakida a cikin duka halayen, da alama dai CI RANI kuka zo a jahar kou? huh!ā€.

Ba k’aramin sukar zuciyar Mom Eshmal kalaman Kuzeem sukayi ba, amma hakanan ta daure tayi shiru tare da sadda kanta k’asa tana sauke wahalallar ajiyar zuciya. Kuzeem kuwa dubonta ta mayar kan Mom Arif tana kallonta shek’ek’e tace;

ā€œKefa jan k’osai daga ina?ā€.

ā€œAsaliiā€.

Mom Arif ta fad’a muryarta na rawa, don har wani zazzab’i takejin yana neman rufeta, tsabagen azabar da tasha, don tafi Mom Eshmal jin jiki saboda fatarsu ba d’aya ba, fuskarta har wani ja tayi kamar k’osai. Rik’e k’ugu Kuzeem tayi tare da d’age mata gira d’aya tace;

ā€œAu! ai ni na d’auka daga gidan shugaban k’asar SARBIK kika fito, a yanda naji kina ik’irarin dangina zasu k’are rayuwarsu a prison, ashe-ashe!ā€.

Ta k’arashe maganar tare da k’yalk’yalewa da wata dariyar shak’iyanci, yayinda suka bita da kallo kawai, don kalaman Saimah na d’azun sun gama tabbatar musu da Kuzeem jami’ar tsaro ce, wacce suka alak’antata da soja. Saida ta gama dariyar ne ta maida dubonta kan Mom Eshmal tace;

ā€œWato ke azzaluma an baki amanar ā€˜yar marainiyar Allah, amma kin cinye saboda mugun hali da rashin ilimin islama, don mai ilimi bazaiyi abunda kikayi ba. Yawwa bari in tambaye ki, yanzu alal misali, ke na cire misalin ma, a zahiri nake nufi.  Yau ki fad’i ki mutu ko mijinki ya mutu, ya zamto kinbar ā€˜yarki shin zaki so ayi mata irin zaluncin da kikayima wannan yarinyar?ā€.

Ta k’arashe maganar tana nuna Binta dake cin abicinta hankali kwance, tamkar babu abinda ke gudana a wurin. Saurin girgiza kai Mom Eshmal tayi tace;

ā€œA’ah wallahi bazan so abinda zai tab’amin Eshmal baā€.

ā€œSaboda ita ce d’iyar da aka haifa kou?, ita kuma Binta daga sama ta fad’oā€.

Shiru Mom Eshmal tayi tare da sadda k’anta k’asa tana jin wani rad’ad’i a zuciyarta.

ā€œTou ki kwantar da hankalinki, a yau d’in nan zan mik’ata a wurin Mamanta wacce ta san zafintaā€.

Cikin wani irin matsanancin tashin hankali maras misiltuwa Mom Eshmal ta d’ago tana kallon Kuzeem kana tayi saurin yin kneeling tare da fad’in,

ā€œDon girman Allah ki rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa miki naki, wallahi in kika maidata gidansu mijina yaji abinda nayi mata saki na zaiyi, banida kowa a duniyar nan sai shi, kuma wallahi ina bala’in son mijina, nasan a matsayinki na ā€˜yar uwata mace bazaki so aure na ya mutu ba, wallahi nayi nadama bazan sake aikata haka wa kowa ba, zan zamo managarciya mai kyautatawa kowa da wanda na sani da wanda ban sani ba, kuma na miki alk’awalin zan rik’e Binta tsakani da Allah, zan k’aunaceta tamkar yanda nake k’aunar ā€˜yata Eshmal, bazan sake cutar da rayuwarta baā€.

Yanda Mom Eshmal ke zubda k’wallah tana maganar zai baka tabbacin tayi nadama ba kad’an ba, saboda hankalinta a mugun tashe yake, a halin yanzu ta daina jin rad’ad’in dukan da Kuzeem tayi mata sai wannan maganar da ta fad’a mata. 

ā€œYanda kika cutar da ita ba laifin tsaye balle na zaune, dole ne kema saikin d’and’ani irin rad’ad’in da taji, kuma ko ba komai ina so wannan ya zamo izina ga sauran mutane masu mugun hali irin naki. Sannan wannan nadamar da kike ik’irarin kinyita ba don Allah kikayi ba, azaba ce da kuma k’aunar mijinki yasa kikayi ta, so yanzu kinada damar rok’onta gafara akan abinda kika aikata mata, kafin tayi miki nisan kiwoā€.

Kuzeem ta k’arashe maganar tana jifarta da wani mugun kallo. Saurin rik’e k’afafun Kuzeem Mom Eshmal tayi tare da fashewa da wani matsanancin kuka tana fad’in,

ā€œKi taimakeni Kuzeem! karki min haka, na rok’ek’i kiyimin alfarma ko sau d’aya ne, wallahi har ga Allah nayi nadama maras misiltuwa, dama sharrin shaid’an ne, yanzu kuma na gane kuskure naā€.

Tana gama fad’in haka ta mik’e da sauri ta isa gaban Binta tace;

ā€œBinta ki yafe min kinji kou?, wallahi bazan sake cutar da ke ba, ki yarda daniā€.

Kasa cewa komai Binta tayi don zuwa yanzu ta fara jin tausayin Mom Eshmal. Cike da tausayi Saimah ta iso wurinta tare da dafa kafad’arta tace;

ā€œKi kwantar da hankalinki, insha Allah zatayi miki wannan alfarmar, amma ki tabbatar kin gyara kuskurenkiā€.

ā€œBafa zan sanja k’udurina ba, dole ne saita girbi abinda ta shuka, a lokacin ne zatayi nadamar gaskiyaā€.

Kuzeem ta fad’a tare da nufar hanyar bedroom, a yanda tayi maganar dukkansu sunsan cewa babu alamar wasa a ciki, daga Mom Eshmal har Saimah duk saida jikinsu yayi sanyi.

ā€œDon Allah ki nema min alfarma a wurinta, ta taimaka ta rufamin asiriā€.

Inji Mom Eshmal cikin sanyin murya da mutuwar lakkar jiki, girgiza kai Saimah tayi tace;

ā€œKarki damuā€.

ā€œNagodeā€.

Mom Eshmal ta sake fad’ama Saimah tare da mik’ewa, itama Mom Arif mik’ewa tayi fuskar nan tata ba alamar rahma, wani kallo ta watsawa Mom Eshmal kana ta nufi hanyar fita ta bud’e k’ofa ta fice daga d’akin, yayinda Mom Eshmal ta rufa mata baya.

ā€œMom Arif!, dan Allah ki tsayaā€.

Dakatawa Mom Arif tayi daga tafiyar da take, tana jifar Mom Eshmal da wani kallo, cike da dauriya tace;

ā€œDon Allah kiyi hak’uri Mom Arif, wallahi bansan reshe zai juye da mujiya baā€.

Cike da tsiwa Mom Arif tace;

ā€œKinga malama, don Allah ki rufemin bakinki, wallahi Mom Eshmal Allah ya isa tsakanina dake, nayi dana sanin saninki a rayuwata, haka kawai ina zamana kin ja anmin dukan da tunda Nenne ta haifeni ba’a tab’a min irinshi baā€.

ā€œNa yarda kice duk abinda zaki ce, amma ina so kiyi hak’uri Mom Arifā€.

Wani kallo Mom Arif ta watsa mata kana taja dogon tsaki tayi gaba abinta.

Saimah kuwa wurin Kuzeem ta nufa, tsaye ta tarar da ita gaban mirrow hannuwanta rungume a k’irjinta, stool taja tare da zaunawa tana kallonta tace;

ā€œKuzeem na san wannan ba halinki ba ne, son ganin mutum ya wulak’anta ya tozarta, wallahi baiwar Allah nan ta bani tausayi, don girman Allah ki rufa mata asiri kinji?ā€.

Banza Kuzeem tayi da ita tamkar bata ji abinda take fad’a ba, hakan yasa Saimah ta marairaice ta cigaba da fad’in,

ā€œDan Allah zakiyi Kuzeem, ba don halinta baā€.

ā€œNajiā€.

Kuzeem ta fad’a can k’asan mak’oshi, murmushi Saimah tayi tace;

ā€œYauwa ā€˜yar lelen Abbaā€.

Hakan yasa Kuzeem tayi wani murmushi ba tare da ta shirya ba, wanda yayi sanadiyar lotsawar dimples d’inta, kana ta juyo ta kalli Saimah tace;

ā€œAmma fa idan yarinyar tak’i amincewa da cigaba da zama a wurinta, wallahi bazan mata dole baā€.

ā€œNa yarda, ina zuwaā€.

Inji Saimah tana murmushi, sannan ta mik’e ta fice daga d’akin ta koma wurin Binta, hannuwanta ta rik’e tace;

ā€œBinta kin yarda da Kuzeem?ā€.

Cikin sauri ta gyada kanta alamar eh, Saimah na cigaba da murmushi tace;

ā€œTou tace in rarrasheki ki koma wurin Auntynki, bazata sake cutar dake ba, kuma Kuzeem tace bata so kik’i amincewa, nima dai bazanso ki k’i amincewa ba, kinga dai Auntynki harda kuka tayi kuma tayi nadama, ko baki yarda da tayi nadamar ba?ā€.

Binta na k’ok’arin magana idanuwanta suka sauka kan Kuzeem dake tsaye a bayan Saimah. D’an tab’e baki Kuzeem tayi tare da barin wurin ta nufi wurin manyan bags d’in da ke ajiye palorn ta fara bud’ewa, domin duba siyayyar da tayi.

ā€œNa yardaā€.

Binta ta fad’a tana murmushi. Rungumeta Saimah tayi tace;

ā€œTou kin amince zaki koma wurinta?ā€.

ā€œEhā€.

ā€œYawwa k’anwata ina ji dakeā€.

K’yalk’yalewa sukayi da dariya, sannan Saimah ta mik’e ta nufi wurin Kuzeem suka cigaba da duba kayan a tare, kayan sawa ne tsadaddu kuma had’add’un gaske, saidai Abaya da dogayen riguna sunfi yawa, saboda Kuzeem tafi son yin shigarsu, sai kananan kaya, da su mayukkan shafa, turarukka, takalmi, jikkuna, da dai sauransu. Kayane masu yawan gaske wad’anda a k’alla har ta bar RADDAL bata gama sanyasu ba. Sai bayan sun gama duba kayan ne, Saimah tayi serving d’insu abincin suka fara ci a tare.

                    ******

ā€œWai Abokina lafiyar ka lau kuwa?, tun jiya na rasa gane kanka, ga baki d’aya ka sauya kamar wani abu na damunkaā€.

Hisham ya fad’a yana kallon Miswar dake zaune bayan boot d’in wata mota dake cikin garejin nasu. Wata nannauyar ajiyar zuciya Miswar ya sauke tare da furzar da wata iska daga bakin shi, kana yace;

ā€œHisham bazaka fahimce ni baā€.

ā€œKamar ya bazan fahimce ka ba?, nidai ka fad’amin miye damuwar?, ka san dai tun lokacin k’urciya bama b’oyewa junan mu komai, so banga dalilin da zaisa kazo ka sanja muna tsarinmu a yanzu baā€.

Ya k’arashe maganar shima yana hawa boot d’in. D’aga kai Miswar yayi yana kallon sama tare da sakin wani murmushi, hakan yasa Hisham ya bisa da kallo baki sake.

ā€œWannan yarinyar!ā€.

Miswar ya fad’a a hankali, yana lumshe idanuwansa. Cike da mamaki Hisham yace;

ā€œYarinya?, wace yarinyar kenan?ā€.

ā€œMiye na tambaya Hisham?, bayan kasan wacce nake nufiā€.

ā€œAu wai kana magana ne akan yarinyar jiya?, hege ashe kaima ka ganta?, shine ka wani rufe idanuwaā€.

Inji Hisham yana b’alle murfin robar ruwan swan da ke hannunsa.

ā€œIna k’aunarta!ā€.

Ai Hisham da ya kai gorar ruwa a bakinshi baisan sanda ya ciro gorar ba tare da furzar da ruwan da ya zuk’a yana zaro idanuwa waje yace;

ā€œKamar banji da kyau ba Abokinaā€.

K’yalk’yalewa da dariya Miswar yayi wacce tayi sanadiyar bayyanar fararen hak’oransa masu d’auke da wata siririyar wushirya a tsakiyarsu, wacce tayi bala’in masa kyau. Lallausan sajen shi ya shafa yana tsagaita dariyar da yake yace;

ā€œTou duk lokacin da ka shirya ji dakyau sai kazo in sake maimaita makaā€.

Shima Hisham dariyar yayi yace;

ā€œWallahi ka bani wata amaryar dariya, yanzu kai don Allah bakaji nauyin fad’in wannan kalmar ba?, ka kuwa yima yarinyar nan kallon tsaf?.  Hmmm!  Abokina tun wuri ina me baka shawarar kayi gaugawar yakice soyayyar wannan yarinyar a cikin zuciyarka, don kuwa tafi k’arfinka nesa ba kusa ba, kai da ganinta kasan ita d’in matar manya ceā€.

Sauka Misawar yayi daga kan motar, sannan ya rungume hannuwansa a faffad’an k’irjinsa yace;

ā€œGa dukkan alama baka san miye asalin so ba Hisham, kawai dai kana yin shi ne kara zube. Tou ina so kasan shi so na gaskiya babu ruwanshi da kyau, nasaba, mulki, kud’i ko chanchanta, muddin tana sona bazata tab’a kallon rashin dacewar mu ba. Wallahi tinda nake a rayuwata ban tab’a jin ina son abu ba kamar yanda nake mugun mahaukacin son wannan yarinyar ba, ina jin wani babban al’amari a tattare da ita wanda na kasa gano miye ma’anarsa. Hisham koda zata k’ini to ni bazan tab’a daina so da k’aunarta ba har k’arshen rayuwata, domin kuwa soyayyarta a cikin jinina take yawoā€.

Kai Hisham ya girgiza cike da mugun mamakin abokin nashi, yasan waye Miswar tun kafin su kawo haka, babu ruwanshi da harakar mata balle har yayi soyayya da su, akwai kyawawan mata dake sonshi har d’iyan masu fad’a a ji amma bai tab’a kulasu ba balle har yayi soyayya da su, sai gashi yau shi da kanshi yake furta kalmar so ga wacce batama san da wanzuwar shi a cikin duniyar ba.

ā€œLallai abokina kayi nisa baka jin kira, to Allah ya tabbatar da alkhairiā€.

Inji Hisham yana rik’e hab’a. 

ā€œAmeen Abokina, kaidai kawai ka zuba ido kayi kallo zaka sha mamakiā€.

                        *****

*_F.C.T FUNADE_*

ā€œMaganar gaskiya Sir Kuzeem tayi fushi mai tsanani, ya kamata a bata hak’uriā€.

Cewar wani mutum yana kallon B.G Atiku Tanko, wani murmushi yayi yace;

ā€œNa rasa gane meyasa Kuzeem take da saurin d’aukar zafi tamkar nine na haifeta, yanzu miye mafita?ā€.

Dariya L.G Aliyu Iko dake gefensa yayi yace;

ā€œZan kira Kuzeem d’in anjimaā€.

Wani uban burki Major Khalil dake k’ok’arin shiga Office d’in na B.G Atiku Tanko yaja, tare da janye hannunshi daga jikin handle d’in k’ofar, a hankali ya furta,

ā€œKamar naji an ambaci sunan Kuzeem?ā€.

Jin alamar za’a bud’o k’ofar office d’in ya sanyashi saurin barin wurin yana maimaita sunan Kuzeem a ransa. 

                  ********

ā€œWannan wanne irin shirmen banza ne?, taya zaku bari ta shammace ku?, na san halin Fatima kamar yinwar cikina da, ga dukkan alama kunyi sakacin da har ta gano kuna bibiyarta saisa ta sanja takuā€.

Inji Abba da ke tsaye a tsakiyar palornshi, wayarshi kare a kunne alamar waya ce yake, d’an shiru yayi yana sauraron su Rabson kana yace;

ā€œZan baku dama ta k’arshe, da zaran kunyi sake da ita shikenan kwangilar ta wuce kuā€.

Yana gama fad’in haka ya ciro wayar daga kunnenshi tare da katse kiran.

ā€œAlhaji me kake shirin yi ne?ā€.

Ammah ta tambaya, don tun d’azun take tsaye a palorn tana sauraren wayar da yake ba tare da ya sani ba. Saurin juyowa yayi ya kalleta, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace;

ā€œHafsa wannan bai shafe ki baā€.

ā€œBan gane bai shafeni ba Alhajiā€.

ā€œKamar yanda kika ji na fad’a miki ba!ā€.

Abba na gama fad’in haka ya nufi hanyar bedroom d’insa ya bar ta nan tsaye, girgiza kai Ammah tayi tare da furta,

ā€œAi idan kasan wata baka san wata baā€.

Daga haka ta juya ta fice daga d’akin tana danna wayarta, har ta lalubo number Kuzeem.✍️

#Anup💋⁸⁶ ⁹⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *