YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 7 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 7 BY HARUNA USMAN

 

 Www.bankinhausanovels.com.ng

 A JIYA MUN TSAYA

Bayan wata shida sai ga Sarki ya dawo don sake sabon shirin fita, duk ya rame ya fita kamanninsa, saboda tsananin Kawazucin ‘yarsa. Ya shiga gida mutanen gari suna ta murna, ana ta kade-kade da bushe-bushe saboda murnar dawowarsa. Matan gida, barori da bayi suka shiga hada-hadar da suka saba in Sarki yana gari. Lokacin da kowa ya bar shi don ya huta, abin mamaki sai ga ‘yarsa da yaje nema ta zo ta rungume shi. Mai martaba ya ji kamar mafarki ya ke yi. Sai da ya 

 ZAMU TASHI

dauki ruwa ya wanke idanunsa sannan ya tabbatar cewa ba mafarki ba ne. Ya zura mata idanu yana hawaye saboda tsananin murna da Kauna da ya ke yi mata. Yana hawaye ita ma tana yi, a dalilin irin shakuwar da suka yi da kuma tausaya wa irin halin da ta ga ya shiga a dalilin rashinta. Yarinya ta kwashe labari kaf ta shaida masa. Da ya ji labarin, sai ya sake fashewa da kuka saboda takaicin Waziri. Ya yi tunani wai shin ko ya taba saba wa Waziri ne? Amma dai ya kasa tuna ko da rana daya da hakan ta taba faruwa, sai ya cewa ‘yar tasa, “Lallai sha’anin dan Adam yana da ban tsoro.” Yasa aka yi yekuwa cewa yana son kowa ya hallaraa Kofar fada gobe don yana da jawabi. Nan da nan masu shela suka bi kwararo-kwararo suna cewa, “Sarki ya gaishe ku, bayan gaisuwa Sarki ya ce a sanar da ku cewa, yana da jawabi, saboda haka kowa ya hallara a kofar fada da hantsin gobe.” Da daddare Sarki ya fito fada, Waziri ya zo ya yi gaisuwa Sarki ya amsa kamar yadda ya saba. Sarki ya tambaye shi labarin gari, sai ya ce, “Ranka ya dade ai gari lafiya lau sai dai alheri. Babu wata matsala da ta wuce kewar ka da ta gallabe mu. Kai da

Gimbiyarmu” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarki ya ce, “To madalla, na gode. Allah dai Ya bar zumunci.” Waziri ya tambaya, “Allah Ya taimake ka ko an yi naSara wurin nemo yarinyar nan?” Sarki ya ce, “Waziri ai watakila wannan yarinya fa ba ta da rai.” Waziri yana jin haka sai ya barke da kuka wai yana taya Sarki bakin ciki. Da Sarki ya lura da halin da Waziri ke ciki da kuma irin makircinsa sai haushi ya kama shi don ya ga KiriKiri an mayar da shi wawa za a raina masa hankali. Saboda haka sai yace ya gaji zai shiga ciki sai gobe. Ita kuwa ‘yar Sarki ran nan ma sai da ta zo muka yi karatu kamar kullum a wurin malam. Bayan mun gama ta kawo wasu irin riguna na alfarma ta ba ni ta ce gobe in malam zai tafi amsa kiran da Sarki ya yi wa jama’ar gari in sa mu je tare, ni dai na ce mata to, kuma ban tambaya ba. A kullum mamakin ta nake ta yi, ina tunani a zuciyata cewa duk yadda aka yi dai wannan yarinya daga babban gida ta fito, kuma ga ladabi da kyakkyawar dabi’a. Wayewar gari ke da wuya muka karya kumallo, malam ya yi shigar kaya irin na alfarma, ni ma na shige cikin nawa, kai in ka gan ni sai ka dauka wani Www.bankinhausanovels.com.ng dan Sarkin yanka ne. Malam ya yi umurni barorinsa suka kawo dawakai biyu, su ma dawakan da irin tasu kwalliyar ta alfarma. Muka hau ni da malamin, ban fada maka sunansa ba, sunansa malam AbdulKadir, muka tunkari fada, kowace Kusurwa ka duba jama’a kake gani suna fitowa kamar za a je Idi, duk kowa ya amsa kiran Sarki. Isarmu fada sai aka kama dawakanmu aka kewaya da su, sai na ga an nufi kujerun da ke kusa da Sarki an zaunar da mu a kan wasu na mutunci. Fada ta cika makil, ko ina ka waiga babu abin da za ka gani sai kan mutane. Can sai ga Waziri ya iso. Tambura suka fara tashi wanda hakan ke alamta fitowar Sarki, kowa ya mike don girmamawa, da Sarki ya zauna sai kowa ya zauna. Daga nan sai mai martaba ya mike don yin bayani. Ya fara da gai da jama’a, kuma ya yi musu godiya saboda irin Kauna da kuma addu’o’in da suka yi ta yi masa lokacin da ya shiga cikin tashin hankali, ya kara gode musu irin yadda suka zauna lafiya bayan ba ya nan. Daga nan sai ya jefo wata tambaya, yace, “Ya ku mutanena, ina rokon ku ku gaya mini gaskiya don girman mulkin Allah kada ku boye mini komai. Don Allah kuna jin dadin mulkina ko kuwa ina zaluntar Www.bankinhausanovels.com.ng ku? Don Allah idan ina zaluntar ku, to ku fada mini yanzun nan in cire’’wannan rawanin, ku zabi wanda kuke da kyakkyawan zato a kan adalcinsa ni kuma na yi muku alkawarin cewa ni zan fara yi masa mubaya’a.” Kafin a bari Sarki ya kammala sai wuri ya dauka, “A’a muna son ka! Muna son ka! Allah Ya ja zamaninka.” Bayan sowa ta lafa, sai Sarki ya ci gaba da jawabi, “Ya ku jama’ar wannan Kasa mai albarka ku sani cewa na riki Wazirina kamar dana, ina son sa kamar yadda mahaifiya take son danta, na amince masa, kuma na tabbata ban taba saba masa ba, hasali ma babu abin da bai sani ba game da sirrina don tsananin amincewa.” Sai ya juya gefen Waziri ya ce masa, “Waziri ko ba haka ba ne?” Waziri ya ce, “Haka ne Allah Ya ba ka nasara.” Tunaninsa ko Sarki ya yanke shawarar sauka ya dora shi gadon sarautar ne don mayar da hankalinsa wurin neman ‘yarsa. Ana cikin haka sai ga keken doki ya kawo ‘yar Sarki. Da mutane suka gan ta sai sowa, wajen kamar zai tsage don tsananin murna suna cewa, “Sarki ya samo Gimbiya, lallai tafiya ta yi nasara, mun gode wa Allah ‘yar Sarkinmu Fa’izah da ta bata ta dawo.”Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan sowa ta lafa sai ‘yar Sarki ta gaisa da jama’a cikin girmamawa da ladabi, sannan ta zauna kusa da mahaifinta. Waziri kuwa Kirjinsa sai bugawa ya ke ta yi don tsoro da bakin ciki, ga kuma mamaki.Bayan Sarki ya ga mutane sun natsu sai ya ce, “Ya ku jama’ata masu girma akwai abin mamaki, amma kuma dai ba za ku ji daga bakina ba, don an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi. Yarinyar nan za ta ba ku labari da kanta” Yar Sarki ta sa aka kawo mutanen nan guda biyu a daure, ashe ranar da muka iso ta damka su ne a hannun wasu amintattun bayinta don a tsare su har zuwa dawowar Sarki. Ta sa aka kwance su daga daurin da aka yi musu, sannan ta ce musu, “Ina so ku shaida wa Sarki da sauran jama’‘a abin daya faru.” Sai suka nuna Waziri Jatau suka ce, “Shine ya ba mu kudi jaka hamsin-hamsin kowannen mu, mu shida ne, muka je muka sace ‘yar Sarki, ya ce mu je can nesa mu kashe ta. Mu dai ba mutanen wannan kasa ba ne. Bayan mun yi tafiyar kwana da kwanaki da ita ne muka isa wurin wani rafi inda gardama ta sarke a tsakaninmu kan shin a kashe ta ko kuwa a sayar da ita a Kara samun wasu kudaden? Kuma kasancewar muna Www.bankinhausanovels.com.ng  cikin mayen giya ne ya sa fada ya kaure tsakaninmu da wadanda ke son a kashe ta bayan sun zare takobi sun nufe ta za su kashe, shi ne dai muka yi nasara a kan su muka kashe su, sannan muka koma shan giyarmu har barci ya kwashemu. Can sai muka ji ana ta bugun mu har sai da muka yi lilis sannan suka daure mu, suka dora mu a kan doki, wato ‘yar Sarki da wancan saurayin.” Sai suka nuno ni, ai duk sai idon mutane ya juyo kaina. Bayan wadannan barayi sun kammala ba da labarinsu, sai yarinya ta waiwayo ta dube ni ta ce, “Ya kai masoyina tashi ka shaida wa jama’a yadda abin ya faru” Na tashi na ba da labarin abin da na sani tun daga farko har Karshe. Mutane kowa ka duba sai ka ga yana Kwalla saboda takaici, sai Sarki ya tambayi barayin ‘yarsa, “Shin ku ko wane irin dalili ne Waziri Jatau ya ba ku na abin da yasa ya keso a halaka mini ‘ya?” Sai suka ce, “Ya ce mana ne wai so ya ke yi bakin ciki ya taru ya kashe ka, don in ba ita aka sace ba, to babu abin da zai iya jefa maka babban bakin ciki.” Sai Sarki ya cewa jama’a, “To kun ji abin da Waziri ya yi mana.” Nan take wuri ya hargitse, kowa yana fadin albarkacin bakinsa, “A tsire Waziri! A tsire maciyin Www.bankinhausanovels.com.ng amana! A hada su a tsire! A yanka shi! A miko mana shi nan mu yagalgala shi danye!” Kowa dai yana ta fadin albarkacin bakinsa. Can sai Sarki ya yi magana ya ce, “Ya ku jama’ata, ku sani cewa nina dade da Waziri, kuma ni ba zan iya yi masa komai ba sai dai in bar shi da Allah. Amma daga yau na fitar da shi daga wazirci, kuma na ba shi sa’a hudu ya bar mini Kasata.” Jin wannan jawabi sai wata sabuwar hayaniya ta tashi, mutane suna ganin lallai dole sai an halaka Waziri sannan hankalinsu zai kwanta, shi kuma Waziri ya yi shiru kamar wanda ruwa ya Ci, sai ya yi wuf ya jawo wata sharbebiyar wuka daga kuibinsa ya daba a cikin sa, bayan wuka ta shiga sai ya farke cikin, nan take sai ga ‘yan hanjinsa a waje, ya yi ‘yan shureshurensa ya mutu, mutane suka ce, “Ya yanke wa kansa hukunci. Da ma Karshen maciyin amana ke nan.”Sai Sarki ya cewa mutanen da suka sace ‘yarsa lallai yanzun nan su bar masa kasarsa, ya sa askarawa su raka su. Mutanen suka ce suna da magana. Aka amince musu. Sai suka ce suna neman a yafe musu, kuma suna son in Sarki ya yarda suna son zama tare da shi a cikin fadawansa ba don komai ba, sai don irin Www.bankinhausanovels.com.ng  adalcinsa, kuma suka ce su daga yau sun zama Musulmai Sarki ya yarda aka ba su masauki, suka zama masu tsananin biyayya ga Sarki ta yadda ba dama a shirya makarKashiya da su. Ni kuma nan take aka nada ni Waziri. Mutane suka yi ta murna, aka yi kwana da kwanaki ana shagali, kuma Sarki ya amince da ni a cikin gidansa. Aka fitar da iyalan tsohon Waziri daga gidan hukuma aka ba ni. Na ci gaba da zuwa wurin malamina daukar ilmi, kuma soyayya ta yi Karfi tsakanina da Fa’izah ‘yar Sarki har kowa ya sani, kuma na yi sa’a Sarki da mutanen gari kowa ya amince. Sarki ya sa aka yi ta koya mini dabarun yaki daban-daban, na shahara har ya zama da wahala a sami jarumin da zai iya fuskantata gaba-da-gaba. Kai ba alfahari ba, ko ta baya mutum zai bullo mini sai ya shirya. Aka shirya tsaf za a daura mana aure ni da ‘yar Sarki, aka Kawata kowane gefe na gari cikin shirye-shiryen tarbar baki da fuskantar shagulgulan biki da ke tafe. Abin da kawai ya rage yanzu shi ne daura aure, sai wani abu ya zo ya sungume yarinyar nan tana cikin ‘yan mata Kawayenta suna wanka. Aka dai tabbatar wannan aikin aljani ne, saboda haka sai muka yanke shawara ni da Sarki a kan cewa duk inda wannan yarinya ta ke a duniyar nan, matukar dai tana da rai, to ko a hannun aljanu ta ke sai mun samo ta, shi ne muka debi askarawa dubu uku da malamai guda dari muka zuba a cikin jiragen ruwa guda biyu muka shiga duniya har Allah ya hada mu da kai a wannan teku. Wannan shi ne labarina ya kai dan’uwana Idrisu.” Shi ma Idrisu sai ya labarta masa yadda ta kasancea gare shi tun daga rabuwarsu har zuwa yanzu. A Karshe dai duk suka amince cewa Sarkin aljanu Sham’una da ke satar ‘yan mata ne babu ko shakka ya sace wannan yarinya da su Habu da Sarkinsa suka fito nema. Saboda haka sai Waziri da dan’uwansa Idrisu suka dunguma suka je wurin Sarki suka sake jaddada masa labarin Sarkin aljanu da kuma irin mugun halinsa na kama ‘ya’yan mutane, da kuma labarin Idrisu da irin niyyarsa ta zuwa don yakar wannan mugun maridi. Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Sarki ya ce, “Ya kai Idrisu, na yi matukar farin ciki da jin wannan labari, kuma inarokon Allah Ya ba ka nasara a kan wannan aljani, kuma na Kara farin ciki da ya ke Wazirina Habu dan’uwanka ne. Zan tambaye ka, shin wane irin taimako kake so Www.bankinhausanovels.com.ng  daga garemu? Kana so in ba ka jirgi daya da askarawa su raka ka? Ko kuwa kana so mu tafi dukkan mu? Duk abin da kake so ko mene ne ka sanar da mu.” Sai Idrisu ya ce, “Ran Sarki ya dade na gode, duk abin da nake bukata ina tare da shi, ina da dokina da takobi da mashi da darduma, wadannan sun ishe ni. Kuma wannan tafiya tawa ba ta mutane da yawa ba ce, don akwai hadari mai yawa a cikinta. Abin da kawai nake bukata daga wurinku shi ne ku kai ni gabar teku, ku sauke ni sannan ku koma gida kuna ta addu’a tare da saurare.” Sarki ya ce, “Wannan mai sauki ne.” Amma duk da haka sai da ya kawo Karin guzuri ya kuma tursasawa jarumin karba. Da gari ya waye Sarki ya ba da umurni jirage suka mika a cikin teku, daga wannan lokaci aka ci gaba da tafiya ba dare ba rana, sai da suka kwana goma sha tara sannan suka isa gabar teku a cikin tsakiyar dare. Da gari ya waye, sai aka shirya liyafa aka huta na kwanaki uku kowa ya koma cikin hayyacinsa. Daga nan aka yi sallama, Idrisu ya rataya takobinsa, ya rike mashinsa ya yi tsalle ya haye dokinsa, ya daga musu hannu. Ko waiwaye bai sake ba, ya zaburi dokinsa a guje zuwa cikin duniya. Shi kuma Waziri da Sarkinsa sai Www.bankinhausanovels.com.ng suka juya jiragensu suka nufi garinsu cike da tunanin jarumi Idrisu dan Hamidu. In ba,a manta ba, Yahaya, wato dan’uwan su Idrisu da Waziri Habu, Yamma ya nufa bayan fitowarsu daga gida. To shi ma haka ya nutsa da tafiya ba dare ba rana har sai da ya isa wani katon lambu wanda babu abin da babu a ciki na kayan marmari. Rashin sa‘arsa na lokacin shi ne bai tarar da kowa da zai agaza masa game da yunwa da tun tuni ta sa shi gaba ba. Wannan dalili ne ya sa idanunsa ko kadan ba su sami wani tsaiko ba wurin hango wata gwanda Katuwa kuma nunanniya a sama. A gigice yaje ya dauko wata doguwar sanda ya zunguro ta ta fado, ya dauka zai yanka amma sai ya yi tunani cewa, “In na ci wannan gwanda ai na ci wa kaina haram, don kuwa mai ita bai ba ni ba… amma bari in dan dakata, in ya zo in tambaye shi, in kuma bai zo ba, to gaskiya a kan lalura zan yanka in sha.” Ya jingina a jikin wata bishiya don amfana da irin Www.bankinhausanovels.com.ng inuwar da take saukarwa, hannunsa kuma rike da gwanda, ai kuwa sai barci ya kwashe shi. A haka mai lambun ya zo ya tarar da shi. Ya duba itaciyar gwandarsa kuma ya tabbatar da abin da ya ke tsoro, wato ita ce dai yaron nan ya zunguro, alhali dalilin zamanta tun tuni ba a shanye ta ba shi ne Sarkin garin aka ajiyewa. Shi dai mai lambu mamaki ne kawai ya rufe shi irin yadda har za a yi wani mutum ya shigo cikin wannan lambu ya yi sata, sannan kuma don tsananin Karfin hali, ya zauna azo asame shi. Ya tsaya a kan Yahaya wanda ke ta sharar barci. Zuciyarsa ta fara saka masa abin da ya fi kamata ya aikata don hukunta wannan yaro. Shin ko zai cire takobi ne kawai ya dauke masa kai, ko kuwa ya sami sanda ya lakada masa dukan tsiya. Sai kuma wani tunani ya zo masa, to ai shi wannan kyakkyawan saurayi da a ce barawo ne, to lallai da kwando zai dauko daga cikin kwandunan da ke ajiye a gefe ya cika kayan marmarin ya Kara gaba abinsa. To amma kuma bai aikata hakan ba, hasali ma gwandar da ya zunguro, bai sha ba kuma bai tafi ba. Kai lallai akwai wani dalili. Sai ya sa gindin takobi ya zunguri Yahaya, ya tashi firgigi, sai ya ga mutum Kato mai saje da gemu, fuska Www.bankinhausanovels.com.ng  a murtuke tsaye a kansa da takobi tsirara a hannu. Nan take a cikin zuciyarsa ya yi addu’a, “Allah Ka kiyaye ni daga sharrin wannan mutum.” Cikin ladabi ya gai da mutumin, kuma lallai mai lambu ya ji dadin irin wannan gaisuwar girmamawa da ya yi masa. Mai lambu ya ce, “Wane dan Sarki ko Waziri ko kuwa wane dan mai arzikin ne kai? Ko kuwa kai dan wani gawurtaccen malamin ne? Mene ne labarinka? Me yasaka sata kana saurayi kyakkyawa kamar ka? Babban abin da ya sa tun kana barci ban cire maka kai ba shi ne don na ga alamar mutunci a cikin fuskarka, kuma na yi tunanin ban san asalinka ba kada in kashe ka in jawo wa kaina jangwam. To amma kuma in kana ma da wata daraja ko wani asali, yaya za ayi ka yi sata? To yanzu na yanke shawarar ba zan kashe ka ba, zan bari sai Sarki ya zo zan sanar da shi cewa gwandar da ya ke ta tsimi ka zo ka cire.” Ya Kara tambaya cewa, “Mene ne labarinka ya kai barawo?” Sai Yahaya ya ce, “Ya kai mai lambu, babu shakka ni ne na ciro wannan gwanda, dalili kuwa shi ne ni bako ne wanda yunwa ta nemi zautawa. A cikin irin wannan halin ne na ciro gwandar sai kuma hankalina ya dawo jikina na tuna cewa haram ce zanci Www.bankinhausanovels.com.ng kasancewar ban tambayi mai ita ba, shi ya sa na yanke shawarar sai na ga mai wannan lambu sannan in nemi izininsa, in ya yarda in sha. T’sananin gajiyar da ke tattare da ni ne ya sa har barci ya kwashe ni ka zo ka same ni a cikin wannan hali. Kuma zaton kasancewata dan masu mulki ko wadata ko tarin ilmi da ka yi, to a gaskiya ni ba daya ne daga cikin su ba, amma na san mahaifina sunansa Hamidu dan Usman, almajirin ilmi ne, kuma ya ba mu kyakkyawar tarbiyya, muna kuma godiya Allah Ya saka masa da alherinSa. Sannan kuma ka yi hakuri, babu shakka kana da damar kira na duk abin da ka ga dama don kuwa na shigo cikin muhallinka kuma na taba kayanka. Amma gaskiya ni ba barawo ba ne.” Jin zancen wannan yaro, sai tausayi da mamaki suka kama mai lambu saboda irin gaskiyarsa, kuma ya Kara tausaya masa saboda irin tsananin yunwar da ya ba da labarin cewa yana ciki, amma saboda ba ya son cin haram bai sha gwandar ba. Nan da nan mai lambu ya shiga can ciki, ya debo kayan marmari iri-iri masu dadi ya kawo wa Yahaya. Akwai wata gasasshiyar tantabara a burgamensa, ya ciro ya hada masa. Yahaya ya ci nama da kayan marmari ya Koshi ya yi hamdala, ya yi wa mai lambu Www.bankinhausanovels.com.ng  godiya sannan ya tambayi labarin lambu da kuma shi kansa mai lambun. Mai lambu ya ce, “Kafin komai, farko dai sunan wannan gari da ka iso shi ne Burdan-Yamma, wannan lambu kuma na Sarki Salahuddin ne, mai mulkin Kasar. Ni kuma sunana Haladu. Ni ne Sarkin lambu, akwai masu aiki nan kamar mutum dari Karkashina, yau ranar hutunsu ce, kuma a irin wannan ranar ne Sarki kan zo gewaye, shi ya sa ba ka ga kowa ba.” Sarkin lambu ya ci gaba da cewa, “Babu shakka ina da tambayar da zan amsa a kan wannan gwanda da ka tsinko. In Sarki ya ji, in ban yi sa’a ba yana iya yanke mini mummunar hukunci don a gaskiya Sarkin namu yana da zafi. Abin da kake ganin ba a bakin komai ya ke ba, shi wannan Sarki sai ya dauke shi da babban muhimmanci don ya sami damar hukunta mutum.” Da Yahaya ya ji jawabin Haladu Sarkin lambu sai yace, “To tun da yake haka ne, mu gudu mana kafin Sarki ya iso.” . Mai lambu ya ce, “Yaro dai yaro ne “in na gudu to lallai Sarki zai yi zaton akan wannan gwandar daya ne, saboda haka zai ‘sai a kama iyalina yasa a kashe su 

 

 

 

HMM LABARI NATA TAFIYA FA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG&

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *