ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU
Bayan watanni hudu nayi nisa cikin service dina, duk yadda nake tunanin idan naje niger zan hadu da ko mutum daya wanda yasan mummy ban samu ba, babu wanda ya kara ce mini ina kama da wadda na sani, bayan na gama camping dina akai deploying dina zuwa jigawa anan general hospital na dutse akai posting dina. Permanent morning aka saka ni Monday to friday, kullum se mun hadu da Amina dake itama permanent morning take a Paediatric, duk wanda aiki ya sararawa zai tafi gurin dan uwan shi. A wannan kwanakin ko nace watanni na fahimci abubuwa da dama gaba daya na hakura da Aliyu na cire shi cikin zuciyata amma duk yadda nake kokarin saka Nasir a gurin abin ya faskara. Ranar wata Wednesday bayan mun tashi na fito na wuce ward din su Amina, ina zuwa na samu ta tashi se kawai na kirata a waya tace min tana male ward wajen Salem. Wucewa nayi male ward din bayan mun gaisa da attendant din sannan da staff din su na kwankwasa changing room din su dan na tabbatar suna ciki ita dashi, shi ya bude min yana murmushi yace+
“Babbar yaya! Ya dai na ganki duk kin gaji”
Hararshi nayi nace
“Kun tula mana aiki dole kace na gaji”
Se yayi dariya ya fito ni kuma na shiga na sameta a kwance kan gado tana mana dariya, zama nayi gefen ta nace
“Yau ba da wuri zaku tafi ba ne?”
Dan tsaki tayi tace
“Shi nake jira kuma wai se sunyi meeting”
Kaina na gyada daidai shigowar Lubna sanye da lab coat, ta fara IT dinta so tana lab cikin asibitin dake tana karantar MLS. Tare muka dinga hira har Salem ya gama da yan ward dinsa sannan muka fito muka tafi gida. Da yamma ina zaune sega kiran Aminatu wai zamuyi magana, nace
“Ke! Me ya hanaki fada min dazun?”
“Bana son muyi maganar muna kallon juna saboda kar kiji kunya ta.”
“Kunya kuma?”
Na fada ina dariya, itama ta danyi dariya sannan tace
“Kinaji uncle Nasir ya kirani…”
Seda gabana ya fadi na fara addua Allah yasa ba cewa zaiyi zai turo maganar bikin ba, saboda nidai har zuciyata ba son shi nake ba what i know ina ganin mutuncin shi da girman shi ne kawai!
“…shi yana ganin kamar bakya son shi kawai kina masa kara ne, yana ganin wai zai hakura kawai, nima kuma na lura da hakan yaya Nanah rayuwar ki ce fa, idan baki son shi kada ki karan ta min, ke zaki zauna dashi aure is too long for you ki zauna da abinda baki so, ba zaki iya kara for long ba”
Naji babu dadi da suka fahimci hakan amma abu ne mai dadi da hakan ta faru, in protesting nace
“Waye ya fada miki?”
Se tayi dariya kawai ta cigaba da maganar ta nima se na hakura kawai na amince cewar zargin su daidai ne. Daga wannan na closing chapter Nasir dukda muna waya sosae kuma yanzun da na san babu komai tsakanin mu se ya zamana nafi sakin jikina dashi.
Bayan yan satittika mu kaga tallar wasu abayas a gurin wata online vendor, Daddy na zaune Nawwara ta nuna mana dukkan mu seda mukai exclaiming saboda kyan abayar , Daddy yace
“Ku tambaya kudin se kowa ya dauka”
Lubna tace
“Yes! That’s lovely Daddy for us”
Yaji dadi mukai masa godiya, there and then mukai placing order kowa da color din shi da size, dama A’isha da Ummu sune kanana amma sun fimu tsayi da cika ido, 3 quarter kudin muka bayar akan zamu cika sauran bayan order yazo. Order ya dauka two weeks kafin yazo, sukai communicating da Nawwara ta fada mata ta aiko kayan dutse through Anty dinta, sannan ta tura mana number Anty din tata sede tace mana bata nan se idan ta dawo.
STORY CONTINUES BELOW
Kullum muka kira se ta bamu excuse one or two, ranar dai ta bamu address tace muje mu karba kawai amma bata gida taje biki amma zata bari a gida. Ranar Thursday ce so dukka munje gurin aiki , tunda nayi parking nasan motar bata da lafiya amma haka ban kira Daddy ba duka muka rabu, kafin naje pharmacy seda na fara wucewa ward din su Amina, ta karaso cikin blue uniform tayi kyau cikin dake jikinta ya fara bayyana, ta rungume ni tana fadin
“Fitowar da nayi gurin ki zanje fa”
Nace
“Sakon na kawo miki”
Na fada ina mika mata ledar hannuna, karba tayi da sauri ta ciro wrapped shawarma cikin wata leda se zobo daya ledar wanda ya kankare, rungume ni tayi for the second time tace
“Allah ya kawo miji na gari, ranar se an rike min zani na”
Nayi dariya na wuce department din mu, da muka tashi na lallaba motar muka je gida, wanka na fara yi sannan na canja kaya zuwa wata creme abaya da adon net red, na saka red turban cap sannan na fito mukai lunch, rufe idanuna nayi ina shakar sassanyar iskar dake kadawa daga fanka, Ummu ta shigo da assignment dinta na physics ta kawo min haka na zauna na koya mata wanda zan iya sauran na mata browsing a net tayi. Nawwara ta shigo parlon tsaf cikin gown na material tace min
“Yaya Nanah kin manta zamu fita”
Mikewa nayi dan da gaske na manta da karbo kayan, mikewa nayi naje daki na dakko karamin veil din abayar sannan nasa jan wedged sandal me kyau a gaban anyi ado da creme ribbon a jiki. Fitowa nayi bayan nasa kwalli sannan nayi damping lip balm akan lebbena masu siranta, idanuna na lumshe na kuma bude ina kallon kaina jikin babban mirror dake jikin bangon dakina, na rame har yanzun ban koma yadda nake ba, ban kuma san se yaushe zan karasa murmurewa ba, amma yar ramar da nayi se naga na kara kyau, wannan idanun nawa masu girma da haske wanda kusan su ke kara min kyau a duk lokacin da wani ya kalleni, kwalla min kiran da Lubna tayi yasa na tsayar da admiring kaina na fita, dukkan su seda suka yaba kyaun da nayi, Amal na cewa
“Wannan fitar kawai jikina na bani zaki dawo mana da in law!”
Na tada mota ina murmushi gaba daya na manta cewar motar bata da lafiya, kuma ko a zuwa bata bamu matsala ba, Nawwara na fada min kwatancen a haka muka isa wani mansion dake nan bayan government house. A kofar nayi parking muka fito na locking sannan nace
“Are we good!”
Ta gyada kai tana fadin
“Gidannan yayi kyau!”
Nace sosae muka knocking, security yace mana mu shiga cikin parlon hajiyar, a parking space motocci ne biyu anyi parking, se flowers masu kyau da aka shhushuka wasu na cikin pot, wasu a pit suke, wasu cikin pot din anyi hanging suna dangling, ba karamin burgeni gidan yayi ba, idanuna na lumshe na bude anan na hango wani daga can gefe mutum ya juya bayan shi zaune akan milk din kujera me purple din flowers, tsayawa mukai jikin giant wooden door din dake kofar parlon tareda bugawa cikin sanyi, for some unknown reason se na kurawa idanun shi, and i found myself having some unnecessary force yana jana zuwa gareshi, wannan knocking da muke yasa ya dan juyo kadan nima daidai lokacin na juya ina kallon shi se idanuna karaf cikin nashi, nidai ba zance ga duniyar da nake ciki ba amma nasan i was mesmerized into a lalaland. Nawwara ta taba ni da sauri nayi snapping daga kallon da nake
mishi tare da jan wani numfashi me karfi, tasowa yayi a hankali ya nufo inda muke tsaye, takun takalmin shi tamkar kara gudun bugun zuciyata yake, amma se na kasa dago idanuna balle na kara kallon shi, har seda ya karaso inda muke yace
“Baku kira su ba? Basa gida”
Nawaara ta zungureni lokacin data gama gaida shi, nima na dago ina hada kalmomi nace
“Ina wuni?”
Yayi min murmushi da ya bawa hakoran shi damar fitowa har na hango gap toothed space din daya saka yayi kyau. Ya amsa min sannan Nawwara ta sanar dashi abinda ya kawo mu, se ya ciro wayar shi daga aljihun gaban rigar shi ta jallabiyya yayi dialing number tareda karawa a kunne, yadda ya maida hankalin shi yasa na kura masa idanu a lokacin na fahimci wanda ke tsaye gaba na ba yaro bane dan a haife zai iya haifata amma Saboda yadda jikin shi yake na asalin fulani yasa ba zaka fahimta ba, fari ne dogo dan se na daga kaina sannan zan masa magana, ba a rame yake ba amma jikin shi ko fatar shi ka kalla kasan….
“Gimbiya…wasu sun zo karbar sako….dakin ki?…ok then se munyi magana anjima!”
Wannan conversation din yasa na dawo daga tunanin da nake, ya danyi excusing kan shi sannan ya shiga ciki within some minutes se gashi ya dawo da katuwar jaka ya mika mana yana fadin
“Shikenan?”
Na gyada kai tareda mayar mishi da murmushin da yayi min sannan muka fita daga gidan baki daya, bayan mun yiwa security da wani dake zaune hannun shi rike da key, muna zuwa na tada mota bayan mun saka kayan cikin back seat amma motar taki tashi, duk kokarina na kasa na jima ina yi amma hakan ya gagara, security ya leko yazo yace
“Ya dai?”
Nace
“Wallahi bansan me ya faru ba amma taki tashi ne.”
Ya danyi tabe tabe shi da driver amma mota taki gashi har an fara kiran maghrib, muna tsaye sega shi ya fito fuskar shi da hannun shi sun nuna alamar alwala yayi, ganin mu yasa ya tsaya yana fadin
“Motar taki tashi ne?”
Kaina na gyada raina a jagule yace
“Habu ko zaka aje su seka gano gidan, daga nan ka karbo number ta yadda zaa kai mata idan an gyara, sannan ka dakko mechanic din”
Habu jiki na rawa yace
“Tohm Alhaji yanzun zaayi!”
Mukai masa godiya ya wuce bayan ya dan min wani brief kallo dana lura ta gefen idanuna.
hi ya kirani Shima, ikon Allah nake ayyanawa nayi more than two months tare dashi Amma har yau bansan sunan shi ba, Bai taba fada ba Nima ban taba tambaya ba. Ina kokarin Kiran nashi sega wata number ta kirani, na dauka na Kara a kunne na