KANDALA CHAPTER 12

KANDALA 
 
 
 
 
 
 
 
 
CHAPTER 12
 
 
 
 
 

 

 

 
Tana k’wance A jik’in sa yana shan lemon ya kusa k’aiwa rabi sai tare sai Amai!!   
  ” k’ande ke faman kuk’a tana jijjiga shi A lok’acin mukhtar ya shigo yatarar da haruna yana ambaton Allah ga wane abu kamar kumfa abakinsa… +
 
      ” mukhtar ne ya shigo cikin gida sallamar da yayi i’don sa yayi karo da Haruna da jini ki kokarin fita ta bakinsa har hancin sa…
  
    ” Kande ce kifaman kuka ta saka kanta acikin sa tana jijjiga shi yaya yaya innalillahi wa’inna ilahirraji’un…
 
      ” Mukhtar ne ya fara matsowa yana Kin kashe shi kin…
 
   ” ihu ta saka tace wallhi bani bace ba mukhtar kada kayi mun haka….
 
     ” Daukar sa yayi har cikin motarsa hijjabi tasaka tana kuka suka isa Asubuti suna zuwa likitoci sukayi kansa…
 
      ” Kukan da kande takeyi yabawa mukhtar tausayi hakan yasa ya danno su dady awaya yasanar dasu…
 
     ” kande dake tsaye tana kuka dady yashigo wanka mata mari yayi yakara wanka mata…
 
     ” wallahi dady bani bace bani bace ba…
 
       ” mumy ce tace tsanar taki har takai kisaka masa guba a abun sha….
 
     ” durkusawa tayi tace wallahi wallahi bani bace ba ku yarda dani…
 
     ” Aliyu yana shigowa da hawaye a fuskarsa ya tankada ta takara waduwa kuka ta cigaba dayi….
 
     ” Dr ne ya shigo yace ambashi poison wadda yanada hatsare sosai so yanzu mun kira babban likitan bangarin wato Dr suleiman domin shi kadai zai iya da wannan matsalar…
 
    ” Dady ne ya shigo yace yanzu wane hali yake?
 
     ” yana cikin halin mai mutukar hadari so in dr yazo nan da 3hours to…
 
       ” mama farida ce tajijjiga kande tace me isa? Me isa kike kokarin kashe shi?
 
        ” Bani bace ba bani bace ba Wallahi ku yarda dani….
 
     ” firdausi ce tace Daman tsanar dakikeyi masa har takai ki kashe shi?
 
   ” goggo ce ta shigo ta shigo asubutin ta shiga taga halin da haruna yake ciki, kuka tasaka ta fito ta rufe kande da doka babu wanda yace ta bare likitocin gorin ne sukace haba hajiya kada ki kashe ta mana…
 
    ” kubarni gwara Na kasheta batada Amfani batada amfani!
 
     ” Wallahi bani bace ba wallahi bani bace ba……
 
    ” Yimun shiru shaidaniya dan ubanki yau kika fara wannan shidancen shiyasa Nake cewa *ke ta daban ce* turata tafarayi fita daga asubitin babu ni babu ke afusace ta hankada ta tafice waje…
 
    ” yadda taga ta wade yasa ta fashe da kuka…
 
      ” idan kika kara shigowa asubutin nan sai na nakasa ki kije ki canja iyaye….
 
     ” mikewa tayi tana kuka ta tashi tana tafiya Na shiga uku kawai take fada…
 
     ” goggo kuwa tana zuwa ta wada kan mumy tana kuka!
 
      ” Mama farida tace Amma goggo abunda kikaye baki kyauta ba…
 
       ” ke kalli yadda tayi musu da d’a kikalle yadda ta mayar da haruna…
 
    ” Su kansu likitocin sai da sukayi hawaye…
 
     ” kusan karfe 3 Na dare babu wanda ya kwanta dr suleiman ne ya shigo Aka nuna masa haruna ya kusan 1hours yana bincike…
 
    ” Nan ya tarar dasu daga mai kuka sai mai tagumi! Excuse me..
 
     ” Dady ne yace yes?
 
          ” wannan poison din yanada hatsare Nan da 24hours zai iya mutuwa Dan ne banda aikin da zanyi masa Amma akwai dr haris a abuja kuje ku anso makaren poison din…
 
     ” Aliyu ne yace dr in akayi amfani da makaren zai samu lafiya?
 
     ” inshaa Allahu saboda shi poison dinnan hanjin ciki yake fasawa so kahau jirge karkafe 3hours…
 
    ” Aliyu ne ya fita ya nufi Airport..
 
Karfe 5 su Iya habu suka isa asubuti, tana shiga ta wankawa dady mari..kaje ka nemi kande kaje kanemo ta ke kuma banga asararriyar uwa irinki ba hamza kuna gani ta koreta kande bazata kashe haruna ba bazatayi ba…hannu ta goggo taja zuwa dak’in da Aka kwantar da haruna… +
 
    ” Tana shiga tafashi zuwa kuka kirjenta ya buga hankalin ta ya tashi ya haka yasa tayi saurin fitowa zama tayi tana kuka me haruna yayiwa kande tayi masa haka, Allah kabawa ‘dana lafiya wayyo kande kin yaudare ne kin cuceni…
 
     ●●●●●●
 
    Tafiya take tayi tarasa inda zata zauna kukan karuwa yakeyi tazama kamar haukaciya akan titi ….
 
     ” Nafeesa ce ke kokarin driving sai taga kamar fuskar kande har tayi gaba tatafi sai kuma tace Kai waccen Aisha ce parking tayi sannan ta huce zuwa kusa da ita…
 
     ” Tana karasawa ta rungume kande ta fashi da kuka Aisha ya naganki haka…
 
      ” kuka tasaka tace ki kyaleni Natafi zuwa inda babu kowa har na mutu sunki su yarda dani….
 
    ” Nafeesa ce taja hannunta tasakata a mota directly gida suka huce mom din Nafeesa taga kande kamar mahaukaciya tace subhnlhi Aisha???
 
     ” rungumeta kande tayi tace mom wallahi bani bace ba…
 
      ” zaunar da’ita tayi kusa da ita sannan ta kalli Nafeesa ina kika ganta?
 
    ” mom akan titi naganta tanata surotai tana kuka!
 
     ” dad din nafeesa ne yashigo yace barister? Meke faruwa ne?
 
     ” kalli da idonka!
 
         ” Ah Aisha lafiya kike kuka me yafaru?
 
     ” Nafeesa ce tace wallahi dad bakaje maganganub da ta gayan ba hakan yasa jikina yayi sanyi…
 
     ” mom ce tace ki daina kuka Aisha ki gayamana abunda ya faru?
 
      ” bazan taba ganin daidai ba tunda uwata tayi fushi dani ta kuma ce babu ni babu ita!…
 
     ” garin yaya kika bata mata rai Aisha? Cewar dad…
 
     ” Nan tana kuka tana basu labari tana kuka tana basu labari …..
 
       ” innalillahi tabbas wannan tsaka me wuya ce Amma kuma bai kamata mahaifiyar ki tayi miki haka ba…
 
    ” Nafeesa ce tace tabbas zanyi shaida zanyi rantsuwa wacce bazan taba kaffara akanta ba! Aisha bazaki taba saka wa haruna guba ba domin kin kasance kina fadin gaskiya kinayin gaskiya, kamar yadda kuje cikin wane hadisa da aka karbo daga Abdullahi Allah ya qara yarda a gareshi yace: Manzon Allah SAW yace: (( An wajabta muku yin gaskiya, domin yin gaskiya yana shiryawa zuwa ga biyayya, biyayya kuma na shiryarwa izuwa Aljannah, kuma mutum bazai gushe yana yin gaskiya ba kuma tana kirdadon yin gaskiya ba har sai rubutashi a wurin Allah cewa ya zama mai gaskiya..Bukhary & Muslim Nasan gaskiyar ki kikafada Nasan baki zuba masa ba…
 
     ” Mom tace wannan itace kaddara dan haka kada ki damu kicigaba da Addu’a Allah zai daidai ta komai hakuri yazame miki jagaba…
 
     ” ita dai hawaye taketa gogewa!
 
       ” dad ne yace kada kisa kanki cikin wane ciwo ki dauke mu amatsayin iyaye! Nafisa dauketa kutafi ciki tayi wanka tace abinci….
 
   ●●●●●
 
  Karfe 9 Aliyu ya dawo dr suleiman sai sintiri yakeyi yana shigowa yace Ansamu? Ansamu?
 
    ” Aliyu ne yabashi wata takarda sannan yaje ya zauna kusa da iya habu yana bata hakuri…
 
    ” Dr suleiman yace makarin yana gurin Dr musa a lagos so wane yazo ya tafi …..Hamza ne ya mik’i yace bari yaje can din.. +
 
       ” Ka kula ka saurareni domin dr musa yanada sharadi Nafarko shine ba’a zuwa kai tsaye ace yabada magani…
 
    ” hamza yace to yaya zance masa?
 
    ” yauwa zakaje amatsayin bako in kuka gaisa sai kace masa anya za’a samu makaren poison○2°¤?
 
    ” Hamza ne yace to directly airport ya nufa bai tashi ko’ina ba sai lagos acikin jirgi yake godewa Allah da bai aure kande ba…
 
     ” lokacin da ya sauka mota yashiga Aka kaishe kauyen yana zuwa suka gaisa sunata hira dr musa yace zo muje gidana, suna isa Hamza yace anya kuwa za’a samu makaren poison me°2○¤?
 
     ” Dr musa ne ya dakko wasu ganyaye ya mika masa yace kaga wayannan duk likitocin daka basu zasu hadashi da wasu magungunan yanasha mara lafiyar zaita fitar da gubar cikin 3days zai warware…
 
    ” Nawa ne kuma kudin maganin?
 
    ” Dubu 50 zaka bayar..
 
     ” Yana bashi ya tawo akace masa jirge bazai tashi ba sai 3…
 
    □□□□
 
Dr suleiman ne yace remain 2hours yayi sauri fa!
 
     ” Dady yace he have tell me flight bazai tashi ba sai 3…
 
    ” Nan dr suleiman yayi masa hanya yabi flight din yan 12…
 
      ” yana kawo maganin kowa yayi hamdala tare da godiya ga Allah..
 
      ” Mukhtar ne ya shigo yace lallai nayi binciki wannan ba kwalbar maltinar gidan haruna bace ba inaje kawo musu akayi…
 
     ”  babu wanda ya kulashi hakan yasa yasamu guri yayi shiru…
 
     ” Dr ne yafito yana murmushi yace mun fitar da poison din wannan magunguna ne aje asiyo…
 
      ” Hamza ne yace wayakai kara kotu kuma!
 
     ” mumy ce tace nice nan domin Abun nan sai da kotu….
 
      ” Goggo sai dataje babu dadi amma sai cewa tayi Ai gwara dakika kaita…
 
     ” Dady yace kuma duk inda take zataje Ai…
 
   ●●●●
 
Wane wawan tsalle muneeba ta daka tace aikin mu yayi yusra!
 
    ” wanne aiki? ” poison mana yanzu yana Asubutu kinga Nasamu hanyar rabasu da matarsa ita kanta yarinyar nasan dangi an koreta….
 
     ” hahaha ta haruna forever…
 
    ” yeap tashi muje hospital din mu dubashi…
 
   ” okay bag dinsu suka dauka basu tsaya ko’ina ba sai asubuti sallama sukayiwa su iya habu…” Nasan baku gani mu ba daga company aka turomu domin muyi jajin jikin manager… +
 
    ” mama farida ce ta tsayar da ita dacewa ko kece muneeba?
 
    ” murmushi tayi tace aishe kema kinji labari na?
 
   ” shiru ita dai mama farida tayi muneeba sai aibun kande taketa fada…
 
   ” Mukhtar yace ke wacece da zakizo kina Ai bata matarsa…
 
   ” kanaso kaji ne wacece?
 
         ” ka dauke wayanka and search mubeenah borce, sai ta dauke bag nata to Allah yakara sauke mu mun tafi….
 
     ” Suka hada baki suka ce ameen mungode!…
 
      ” Dady ne ke faman sintiri yana fadin yanzu ya kukeso nayi ne kunji kun kai kara kotu ko’ina zancen akeyi both radio and tv….
 
    ” goggo ce tace ranar monday za’afar shara’a kaga yau asabar so duk inda take sai taje kotun nan sai an yanki mata hukunci daidai da abunda tazo zata aikata…
 
    ” Mumy ce tace tabbas hakane dolene ayi mata hukunci…
 
      ●●●●●●
 
   Kande ce ke faman yin kuka ta kusan karar da tissue!
 
    ” Aisha when zak’i daina wannan k’ukan when zaki kwantar da hank’alin ki?
 
       ” kuka takara fashiwa dashi sannan ta kwanta ajikin ta bata ankara ba sai amai aguje tayi toilet, Amai taketayi mom Na kokarin riketa sannu tun yaushe kike aman?
 
    ” Hawayen fuskarta ta wanke sannan ta koma palour ta zauna!
 
     ” Aisha dake fa nake magana!  Am telling you fa zakisa kanki cikin matsala…
 
      ” Tun shekaran jiya nakejin jire da ciwon kai ga kuma haki …..
 
      ” To bari dad yazo sai ya dubaki, kai mun ctv inada shiga court gobe domin ankawo min case din wane yaro….
 
    ” ita dai kande hawaye ne kawai yake dawainiya da fuskarta taga idonta dazatayi taje mai labarai yana fadin:- kotu ta kai sammaci ga yarinyar nan datayi kokarin kashe mijinta har ta zuba masa guba acikin lemo, Dan haka za’a fara kara jibe idan me duka ya kaimu…
 
     ” Mom da hawaye ke kokarin wanke mata fuska, sai jitayi kande ta wade yar akasa! Innalillahi aisha aisha Nan dad yashigo kwantar da ita sukayi agado sannan yafara ‘yan gwaje gwajen sa!…
 
     ” Dad yanaga kanata murmushi ne? ” Dubarta yayi yace Aisha tana da juna biyu wata 2 kenan kuma jininta ya hau ki kula da’ita bari nasiyo wasu magungunan….
 
     ” futarsa babu wuya Ta farka tana kuka yanzu wa zai shigar min kara? Yanzu yaya zanyi da rayuwa ta?
 
    ” Mom ce tace ina tare dake Aisha zan tsaya miki kuma zan taimaki ki yanzu kitashi kice Abinci…..
 
       ” Maganar mom ce tasa ta danji dadi hakan yasa ta danci abincin…
 
      ” Cikin murmushi mom tace kinada ciki Aisha!…
 
     ” ciki? Ciki?? Ciki??? Kuka tasaka Dan Allah kuzubar min dashi wallahi banaso banaso….
 
      ” Zubar da cikin ki zai kara sa al’amura su dabarbare dan haka wannan cikin da kike gani zai taimaki ne A kotu….
 
      ” rungume mom tayi tana fadin bana tunanin zan kubuta…
 
       ” I will try my best dear so stop this crying…..
 
       ●●●●●
 
    Karfe tara na dare mama farida ta dawo daga gida tana kokarin shigo da Abinci taga sai murna sukeyi Haruna ya farfado…
 
     ” Iyah habu ce ke kusa dashi tana yimasa sannu karka damu abunda kande tayi maka mun kaita kotu…
 
     ” cikin manyan idanuwansa yace kotu? Dan tayimin wannan abun zaku kaita kotu?…
 
      ” goggo ce tace indai ne Na haifi kande to sai anyi mata hukunci…..iya habu takara dacewa wallhi ka hana zaman shari’ar nan sai na daga maka nono…. +
 
      ” hawaye ne ya wanke masa fuskarsa, Nan dr yashigo yace su fita su barshi ya huta…
 
     ” mukhtar ne yace kakwantar da hankalin ka abokina komai zaiyi sauki…
 
   ” haruna cikin gajiyayyar murya yace me isa kande takeso ta kasheni?
 
    ” kande ba ita ta zuba maka guba ba….
 
    ” why why why zaka karyata bayan dagane sai ita agidan wallhi inason matata kuma ina kaunar ta….
 
     ” hmmm Allah ya warware sannan ya fita….
 
    Tun daga ranar haruna baya shiga harkar kowa hakan ya kan bata ran su dady! Kuma kullum zancen sa bai huce kun koreta wane hali take yanzu?
 
     ●●●●●●●●
 
   Nafeesa ta kalle kande kin hana kanki bacci daga sallah sai kuka da addua…
 
     ” Addua itace babbar bacci na…
 
    ” Uhm to sai da safe!!!
 
HIGH COURT!!!
 
    Mutane sun taro a babbar kotun nan da aka fe sani da high court , haruna kawai ke zaune tunani halin da matarsa take ciki…
 
    ” Kusan Awa daya sannan su kande suka shigo kana ganinta kasan tana cikin matsala mom ce ta rike hannunta suka karasa suka zauna!…
 
   ” yadda haruna keta kallonta kai kace ya ruga ya rungume matarsa…….
 
     ” Alkali ne yayi gyaran murya A……Yadda haruna k’eta k’allon ta k’ai k’ace ya ruga ya rungume matarsa……. +
 
     ” Alk’ali ne yayi gyaran murya Ayau Litinin 16/3/16 zamu fara shari’a akan yarinyar da tayi yunkuren kashi mijinta! 
   
Ina lauyan mai kara?
 
   ” Ya mai girma mai shari’a Ne ni lauyan mai kara barister Adam…
 
    ” ina lauyan wacce Ake kara?
 
      ” Ya mai girma mai shari’a Ne ce lauyar wacce ake kara brstr hajara…
 
      Kande da fuskar ta ke wanke da hawaye ta sunkuyar da kanta shi kuwa haruna sai kallon ta yakeyi….
 
     ” Muna bukatar wacce ake kara ta fito…
 
      ” Nafeesa ce tace tashi kije kande komai kifadi banda tsoro kinje…
 
     ” cikin kuka tace bazan iya ba nafisa cikin kuka….
 
      ” Zaki iya mana kada ki damu zaki iya…
 
     ” mik’iwa tayi jikinta babu kwari tafi tashi cikin abun tsayawa…
 
    ” muna bukatar wanda yake kara yafito….
 
     ” Haruna ne yaki tashi sai da iya habu tazo tayi masa magana,wallahi haruna indai kakiyin magana ban yafe maka ba! Eyes  dinsa ne sukayi jajir sannan suka tafi cikin abun tsayawa…..
 
    ” Alkali ne yace Aisha Ance kin zubawa mijin ki guba acikin lemo domin yasha ya mutu kinyarda?
 
     ” Sai da ta dauki lokacin sannan ta goge hawayen fuskarta sannan tace bani bace ba wallahi bani bace….
 
     ” To kaji abunda matarka tace kayarda ba’ita bace ba?
 
    ” Shiru yayi sannan ya dago ya kalle ta can kuma ya tuna da zancen iya habu kan idan yayi shiru! A hankali yace aa ban yarda ba!
 
    ” ko lauyan wacce ake kara wanda yake kara yana da abun cewa?
 
    ” brstr adam ne yace ya mai girma mai shari’a inada Tambayoyin da zanyi musu…
 
     ” Alkali yace Anbaka izini…
 
      ” brstr adam ne ya matsa kusa da kande yace Ranar laraba da ta huce misalin karfe 10 na dare dake da wanene agidan?..
 
    ” Ni kadaice sai daga baya haruna ya shigo…
 
      ” aranar kun same sa’in sa har takai ya wanka miki mari, Dama kuma kinajin haushin sa sai kika zuba masa guba a lemo???
 
    ” cikin kuka tace tun safe muka shirya dashi kuma bani na zuba masa guba ba!
 
     ” me isa dayace ke miko masa lemo kika mika masa maltina?
 
    ” Saboda ita yake sha ne bana sha…
 
    ” Saboda kinsan komai dadiwa zai sha maltina shi yasa kika zuba masa aciki?
 
     ” barstr hajara ce tace lauyan wanda ake kara yana huce ka’ida..
 
    ” Alkali ne yace kara ta karbo akiyaye brstr…
 
     ” Anan Na kawo karshen tambayoyin da zanyiwa kande inaso mukhtar yafito…
 
    ” mukhtar cikin zare idanuwa yazo ya tsaya…
 
     ” Da gaske haruna Aminin ka ne?
 
     ” eh domin munzama yan uwa ma…
 
     ” Toh A ranar larabar data huce awani hali katarar da haruna…
 
     ” Natarar dashi akusa da matarsa jini yanata zuba ta ko’ina matarsa kuma tana kuka…
 
     ” mungode brstr adam ne ya kalli kuliya yace har yanzu kande bata da hujjar da zatace ba’ita ta zuba goba ba! Alkali ne yace ko lauyar wacce ake kara tanada abun cewa? +
 
    ” inada abun cewa ya mai girma mai shari’a, barstr hajara ce ta dirfafi gaban kotu ta huce kusa da haruna…
 
    ” haruna dake kallon kande…
 
     ” Malam haruna ko zaka gayawa kotu Alakar ka da wannan?
 
    ” matata ce!
 
         ” To me isa kake zarginta akan zata kasheka dama ba auren soyayya kukayi ba kokuma daman akwai kudurin kisan tun abaya?
 
      ” Auren soyayya mukayi a’a ne bata tana cewa zata kashe ni ba…
 
      ” To Amma me isa kayarda ita tazuba maka guba a lemo??…
 
      ” Ne dai duk wata kyautatawa ina yimata, kuma dalilin da yasa nace ita tazuba min guba shine dagani sai ita agidan kokuma tasan bana shan kowanne lemo…
 
    ” Amma kuma malam haruna aranar kunyi fada da safe akan me kukayi fada?
 
    ” akan bako akayi bata fito da hijjabi ba…..
 
    ” wannan yana nuna tsakanin ku ne kenan?
 
        ” eh…Amma nema bansan me isa takeso ta kashi ne ba!…
 
     ” Anan kana nunawa kotu cewa baka yarda da matarka ba kenan?
 
     ” Na yarda da ita dare bisa dare sai dai kuma bansan dalilin ta Na zuba min guba ba…
 
     ” Amma kuma tace ba ita bace ba!
 
     ” mu kadai ne agidan…
 
   ”  Ya mai girma mai shari’a zanso mahaifiyar kande ta fito…
 
    ” Goggo ce ta fito..
 
” brstr ce ta kalle ta munaso muje menene Alakarki da kande?
 
       ” ‘yata ce ne nahaife ta da cikina!…
 
        ” Daman tuntuni tana sakawa mutane goba kokuma yanzu tafara?
 
      ” Kande yarinya ce maraji tun tana karama tana da fitina wanda hakan yasa wasu suke tsoronta komai girman ka indai kagaya mata maganar da batayi mata dadi ba to sai ta rama!…
 
       “Brstr tace Amma bakwa tunanin wannan kuruciya ce? Kokuma har yanzu tanayi? Kuma kema kin yarda da cewa tasakawa haruna guba?
 
        ” Eh to ashekarun baya gaskiya ta canja halinta..” kuma yanzu batayi….” babu wanda bazaiyi zargenta ba saboda ada basa jitowa da haruna kuma daga ita sai shi agidan…
 
      ” mungode zaki iya komawa ki zauna…
 
     ” brster hajara tace ya mai girma mai shari’a zanso nayiwa mukhtar tambayoyi…
 
      ” Mukhtar kotu tana son ganinka…
 
     ” Barister ce ta matsa daf dashi kace kai ka kai haruna asubuti koma daga gidanka yadawo..
 
    ” barister adam ne yace ya maigirma mai shari’a barstr hajara tana huce gona da iri tana kuma kokarin daurawa haruna lefi….
 
     ” kara ta karbo akeyaye barstr…” kara ta karbo akeyaye barstr…
 
       ” alama tayi da kanta sannan tace kace kai aminin haruna ne kataba jin yana kawo maka matsalar matarsa?
 
    ” A’a baitaba ba..
 
        ” baka tunanin wane abokin gabarsa ne yaje ya ajiye musu lemon?
 
     ” Tabbas ina tunani kuma Nasan Kande bazata aikata ba Amma tambayar Anan tace babu wanda ya shiga cikin gidan sai ita kadai…
 
    ” Da wannan tambayoyin nakeso kotu ta zauna tayi nazari akan cewa ba Aisha ce ta zuba guba a abinci ba….
 
     ” Kotu Kotu..An daga shari’a sai 19/3/16….
 
    ” wane sabon kuka kande takeyi wanda ya tabbatar da tana cikin tsananin bala’i…
 
    ” Mom ce ta rungumeta sannan sukayi waje haruna yanata binsu Amma mom taki bari ya kulasu mota suka shiga sannan suka huce gida….
 
      ” goggo ce tace ne banga wane amfanin daga karaba ga abu koru kuru Amma Antsaya sai wahalar damu akeyi…
 
    ” Dady ne yace Amma ai komai yana bukatar bincike…
 
    ” Mama farida ce tace ina jiye muku ranar da gaskiya zatayi halinta kukuma alokacin bakuda mafita alokacin zaku kasa kallon kande….
 
     ” mumy ce tace wacce gaskiya kuma gaskiya nan ana warwarewa…
 
●●●●●
 
    Yusra ce ke faman dariya acikin hotel din muneeba kin huce yar daba fa hahhaha…
 
   ” ke dai yusrah bar ‘yan isa ne zaice bayaso ai ne san samuma ace ya mutu a dorawa wannan shegiyar matar tashi kisa….
 
     ” Amma duk da haka kinsata a matsala fa domin kin rabata da danginta…
 
    ” Ke dai bari ne nafiso ma tafi haka shiga matsalanafiso ta shiga cikin matsalar da life dinta zata wulakanta kinga daga nan ne kuma sai na aure haruna kinga mu cigaba da wolewa….
 
      ” kawata kanki fa yana ja Amma kuma karki manta sun shiga court karmuje sammaci….
 
     ” lallai kin manta muneeba yusrah mutane nawa nasaka cikin morethan this just watch ma steps…
 
      ” Anyway kituromin 50million dear dad yana bukata…
 
    ” okay ina zuwa bari Naje gurin doctor nadawo…
 
    ” Me zakiyi agurin doctor muny???
 
      ” Hmm thats not your problem…
 
     ” okay komai abunki dai baki da kawar data kaine dan haka cool down….
 
     ●●●●●●
 
     Me isa har yanzu baki daina kuka ba kande? Ina tare dake Kuma i will try my best Naga na fitar dake…
 
     ” banda wasu shedu dazasu Nuna cewa bani na saka guba ba…
 
    ” akwai Allah kuma inaso ki kwantar da hankalin ki kitsaya kiyi tunanin wayanda suka shiga gidan ki ba!…
 
   ” Ne fa i can’t remember anything…
 
     ” dad ne ya shigo yace zaki tuna Aisha tunda kince baki kika zuba ba dole akwai wanda ya zuba….
 
    ” Tohm dad zanyi tunani naga ko zan tuna…
 
    ” Lokacin da kande ta shiga daki anyi sallar isha’i tana ta karatun kur’ani bayan tagama hawaye ya wanke mata fuskarta…
 
    ” Nafisa ce ta ajiyi wayar hannunta tace wai Aisha menene nakuka kuma dukkan tsanani yana tare da sauki mu kasance masu yadda da kaddara kuma kice gaba da hakuri…
 
    ” Nasani yar uwata kuma zan cigaba da juriya..
 
    ” yauwa sister ranar laraba kafin abin yafaru suwanene sukazo gidan ki?
 
     ” Shiru kande tayi Na lokuta sannan tace aranar larabar data gabata Da safe mamie tazo daga jigawa sai kuma daga baya gurin dare su haneef sukazo kuma su ne nabasu lemo da snacks!
 
     ” okay daga su wanene suka shigo kuma??
 
   ” Shiru tayi nadan lokaci sannan tace tabbas na tuna tabbas! Domin suna fita naga maltina akan kujera…
 
     ” Nafisa ce tace tabbas sune wayanda suka kawo miki lemon…
 
    ” Cikin murmushi tace Alhamdulilahi Amma kuma mijina shima ya yarda nice na zuba masa gubar…
 
     ” mom ce tace mijin ki yana sonki yana kuma kaunarki tun dazu sai kirana yakeyi yafi sau 7 akan zaizo ya ganki amma kuma na hanasa….mom kasan me kike fadi? Nazata ya rabo dani nayi tunanin yaudara ta yakeyi kullum sai ya gayan kalaman so, Tafashi da kuka yanzu muneeba ta rabamu… +
 
     ” Mom ce tace muneeba koma??
 
     ” ita mum, yanzu d’ana yake bukatar kulawar mahaifin sa…
 
     ” Karki damu Kande Allah shi yake kula da bayinsa kuma komai zai faru Allah ya rubuta Abunda nakeso dake kada ki dura tsana ki durawa mijin ki domin yana kaunarki…
 
      ” Mom in yana sona me isa baiyi wa iyayena bayani ba!…
 
     ” Iyayen ki sunyi fushi dake sosai fiye da yadda kike tunani Aisha…
 
” kuka tasaka sannan tace Allah ne shaidata…
 
     ” All what i want from you is that kice dukkan tsoro kiyi bayani da confedence..
 
     ” okay mom i will..
 
     ” kuma all i want you to know Mumini Mai haquri ne baya wauta koda kuwa an masa wauta, Mai haquri ne baya zalunci idan aka zalunce shi yana gafara, baya yanke wa (zumunci), idan aka yake yana sadarwa (zumunci) baya rowa idan aka masa rowa sai yayi haquri…..
 
    ” kukane ya wanke mata hawaye sannan tayi tagume…
 
    ●●●●
 
Mumy ce tace hakika kande ta bata mana sunan gidan nan ta jawo mana abun fada kaima dady da kwashe kwashe…
 
    ” A’a kande bata ‘bata sunan gidan nan ba kuka mumy kisane cewa Ba mu da damar chanja abin da ya wuce, kamar yadda ba mu da damar tsara abin da zai faru. So meyasa muke kashe kan mu da bakin ciki akan abin da ba a hanunmu yake ba? 
     ” Dady ne yace Ne wallahi abun nan yafara bani tsoro Na kande…
 
      ” Firdausi ce ta gyara zama tace haba mijina kande fa kanwar ka ce Amma har dakai acewa tasaka guba..
 
     ” Hmmm firdausi bakisan halin kande bani ba, kusan sau 2 tana warware mun aure ke agidan nan babu wanda batayi wa kabiru ne kadai take raga masa….
 
    ” A da kasanta Amma wallahi lokacin damuka zauna tare mu mukeyi mata bakin ciki, bama kulata Amma da zuciya daya take zama damu wallahi kande mutuniyar kirki ce kuma bazata taba saka ma yaya guba ba…
 
     ” has u said it! Amma ai gobe zamu hadu akotu gaskiya zata fito…
 
    ●●●●
 
   Goodevening dr suleiman!
 
    ” hope lafiya kikazo?
 
           ” jakarta ta bude sannan ta saka hannu aciki dubu dari 5 ta ajiye masa akan table…
 
      ” zaro idon sa yayi all this for me???
 
     ” yes!!!
 
         ” murmushi yayi what do you what from me???
 
    ” Dariya tayi tare da buga kafarta All i what shine kubani jinin haruna kuma inaso asaka hiv aciki…
 
    ” shikenan Abunda kike bukata???
 
      ” nop inason kayimin test Na ciki da kuma na zubar dashi…
 
      ” Okay! Muneeba just give me 30mins…
 
   ” murmushi tayi tace good Am waiting..
    
●●●●●
 
    Nafisa kiyi sauri yanzu 8:30 kinga hy 9 zamu shiga court…
 
    ” okay mom kije ki saka Aisha wanka don dazu takeyi ..
 
     ” Directly mom ta nufe dak’in ganin kande tayi abakin gado tana kuka!
 
    ” as usually Aisha when zaki nutsu ne? Karki manta fa da pregnant ajikin ki…
 
     ” goge hawayen tayi tare da murmushi afuskarta mom ina cikin farin ciki da jindadi inshaa Allah yau za’awanki nee…
 
     ” Allah yasa Aisha before kuje bari na Aika mata sammaci…
 
      ” Mom kinada ikon aika mata ne?
 
      ” yes i have! Cuz ina aiki da gomnati kuma ina aiki akan kaina so matsayina no be small one…
 
      ” Mashaa Allah…
 
   ●●●●●
 
  How dare she’s? Look yusrah wai ana nemana acourt…
 
     ” Yusrah ce tagyara zama sannan ta kalle muneeba tace Tha’ts Allah what am Always telling you becareful yanzu gashi brstr hajara ta nemiki which shows that kande ta ambaci sunanki….
 
      ” Hahaha yusrah kenan Am ready for this day! Karki manta nece muneebah! Zan nuna musu k’ai din ‘ya mace! Shedancin ‘ya mace after all ma zan rufe brain din lawyer’s din…hmm ki daiyi a hankali cuz ko barister bakida… +
 
     ” who tell you so? My barister is ready tuntuni…
 
       ” gaskiya muneebah ke bomb ce…
 
     ” Nafi bomb hadare Nakuma fi guba illah! *NE KADAN GARAN BAKIN TULUCE AKARNI AKAR TULU ABARNI RUWA YA ‘BACE*…..
 
    ” wannan haka yake Amma karki manta *KANDE TA DABANCE*…
 
     ” That’s why i prepare for this day so just watch…
 
    ●●●●●
 
Kowa ya hallarta a kotu Dukkanin su goggo suna nan har yan uwa da ba’asanar ba suma suna nan!
 
     ” Kande ke faman hawaye tana gogewa!
 
     ” haruna dake kusa da iya habu shima kwallace ta cika masa idanun sa har ya miki zaije kusa da kande iya habu tace toh mai zuciyar kare in har kaje ban yafe maka ba!…
 
    ” Cikin mamaki ya jiyo yana kallon iya habu wato duk soyayyarta da kande akaina ta daina lallai kaje tsoron kande…
 
     ” Sadiya ce tace Allah sarki yaya haruna shikenan kun rabu da kande tasaka kuka…
 
     ” Shima hawayen ne ya zubo masa sannan ya dafa kafadarta yace bamu rabu ba sadiya Allah yana tare damu kuma Wato tausayawa ko sauqaqawa abu ne mai kyau a addini, anaso mu tausayawa duk wanda yake qasa damu, duk wanda aka haramta masa tausatawa ko sauqaqawa to an haramta masa alheri mai dinbin yawa, kuma Allah yana tausayawa masu tausayawa ne kawai!!…
 
    Alkali ne yace Ayau 19/3/16 zamu cigaba da kara akan Aisha dake kokarin kashe mijinta…
 
    ” ina lauyan mai kara da wacce ake kara?
 
     ” brstr adam ne yace gani nan brstr hajara ma tace gatanan…
 
      ” Lauyan mai kara kona da abun cewa?
 
    ” eh ya mai girma mai shari’a zanso wacce ake kara tafito…
 
     ” Kande tana shiga cikin agurin nan yace kince baki kika zuba guba ba to wakike tunani ya saka bayan ku biyu ne agidan?
 
      ” Tabbas bani nasaka ba kamar yadda nace abaya Amma bansani ba ko daga waje yatawo dashi…
 
     ” kinaso kice mijinki yana shaye shaye?
 
     ” Cikin hawaye tace ko taba mijina bai taba sha ba…
 
     ” to mekike kokarin cewa bayan kinsan ke kika saka?
 
     ” barstr hajara ce tace ya mai girma mai shari’a brstr adam yana kokarin tirsasawa wacce ake kara!..
 
     ” Korafe ya karbo sai akeyayi…
 
     ” Alamun to yace sannan yace da wannan rashin hujjar wacce ake kara nakeso azarce mata da hukuncin abunda taso ta aikata! Nagode…
 
    ” Alkali yace ko kinada abun cewa brstr?
 
     ” Eh ya mai girma mai shari’a…
 
       ” Zamuso muje daga bakin ki rabar laraba su wanene sukazo gidanki kafin faruwar abun?
 
     ” cikin shashekar kuka tace mamie tazo misalin karfe 2 Na rana kuma bata dadi ba tatafi!
 
    ” a wanne gari take?
 
          ” A jigawa take.. ” idan zanso na fahimce zancen ki arabar tazo ta tafi kenan?? ” eh..
 
     ” To bayan ita babu wane wanda ya shigo cikin gidan???
 
      ” misalin karfe 7 nadare su maryam sunzo itada sumayya!..
 
     ” Daga ina suke?
 
” Abuja kuma mintunansu 20 suka bar cikin gidan!..
 
  ” Sun kawo miki wane abun ne?
 
     ” A’a basu kawomin komai ba Amma ne dai Nabasu lemo da meatpie sun tafi dashi…
 
     ” bayan su mekuma yafaru???Bayan tafiyar su basu dadi ba wasu mata sukazo cikin gidan nawa… +
 
     ” Me sukazo suyi kuma su wanene?
 
     ” Sunanta muneebah tazo ne Akan tabani hakurin abunda yafaru abaya kuma tazo muryarta cikin lisinama da nuna ayafe mata!..
 
     ” bayan tafiyarta kikaga lemon..
 
      ” Suna fita Naga lemon sai nayi tunanin haruna ne ya ajiyemin ashe sune…
 
       ” kin tabbatar sune???
 
      ” Tabbas su suka kawo lemon domin su suka shigo gidan last!…
 
    ” barister hajara tace da wannan Nakeson kotu tabani dama Muneebah tafito…
 
       ” An baki dama..
 
   ” muneebah ce tafito cikin taunar cingam tana riki da waya!…
 
     ” barstr tace To muneebah kike da suna? Zaki iya cire gum din muyi magana???
 
      ” Ke dai kinaso nabaki Amsar tambayar ki to you can go a head..
 
      ” A ranar laraba mekikaje yi gidan haruna? Me kuma kikacewa matarsa? Me isa kika zuba guba a cikin lemo?
 
     ” canja fuska tayi abunka da fara har idanunta sunyi ja tace naje ne akan neman sulhu da kande Amma kuma maganar data gayamin shi yakara hargetsane hakan yasa na tsorata da ita!…
 
    ” wacce magana ce??
 
           ” A yayin da nake bata hakuri sai cewa tayi ita bata da lokacina kuma wannan maltinar danake gani guba ce aciki zata saka aciki haruna yasha ya mutu…
 
    ” Kande ce ta zaro idanuwa idanunta cike da hawaye…
 
     ” brstr hajara tace ko zaki iya gabatar mana da shidar ki???
 
    ” yusra da baba maigadi..
 
     ” yusra da baba mai gadi kufito zuwa…
 
    ” yusrah a gabanki akayi haka?
 
    ” tabbas agabana kande tafada dan har nasiha nayi mata akan hakkin mijinta amma ta daka mana tsawa mufita mubar musu gida…
 
    ” to baba maigadi lokacin da muneeba suka fito awane hali kagansu???
 
    ” cikin fushi suka fito har nake tambayar su lafiya sai sukace idan mai gidan yazo muyi nagaya mai matarsa tasa masa guba a abinsha…
 
   ” To me isa baka sanar dashi ba??
 
      ” tafara gayamai ya karyata ne!…
 
    ” Barstr hajara ce ta kalle haruna dace dagaske ya fara gaya maka??
 
    ” tabbas yafara gayan na dakatar dashi…
 
    ” Muneebah zamuso kotu taje alakarki da haruna…
 
     ” shiru tayi Na dan lokaci sannan ta fashi da kuka tace Ne karuwar sa ce…
 
     ” kowa sai da yayi mamaki a kotun..
 
    ” ita kanta brstr sai da taje wane shock..
 
     ” Haruna ne ya Nunata da danyatsa kije tsoron Allah muneebah…
 
    ” kuka takara rusawa sannan tace shekarar mu daya muna tare…
 
    ” Brstr ce tace menene hujjar ki??
 
     ” Wasu takardu ta dakko tace wannan sune hujjata tafarko kuma sau biyu yanasa ina zubar da ciki…
 
     ” Kande in banda ta shiga uku babu abunda take fada…
 
      ” brstr hajara ce ta karba ta duba sannan ta kaiwa Alkali…
 
       ” haruna ne yace karya takeyi min wallahi karya takeyi min…
 
    ” yanzu haka inada cikin wata biyu…
 
    ” brstr ce tace ciki? Ciki?
 
     ” Ga shidata…
 
       ” Nan barstr ta karba ta kaiwa alkali…
 
     ” Mukhtar ne ya fito yace karya takeyi karya takeyi…
 
     ” cikin kuka tace idan an yimin izini inaso nafadi komai da komai…
 
     ” An baki izini..
 
        ” Duk abunda take fada karya takeyi cewar haruna…Alkaline yace muje zuwa yarinya.. +
 
     ” Akwai ranar da naje gidan domin mu gaisa sai na tarar da wancan da kande suna lalata….
 
     Brstr hajara datayi mutuwar tsaye tace wakenan???
 
     ” mukhtar…
 
       ” Kande ce ta saka  ihu nashiga uku wallahi wallahi wallahi ban taba lalata ba…
 
     ” Kotu kotu kotu andaga shari’a sai gobe  an ingiza kande zuwa gidan dan kande wato prison…
 
    ” Dady da su goggo sai kuka sukeyi suna Ambatar innalilahi…
 
      ” kande ke faman tirjeya wallahi wallahi banyi komai ba…
 
      ” brstr hajara ce tace ke kwantar da hankalinki kande gaskiya zata fito fili…
 
     ” haruna ne ya karaso kusa da ita sannan ya durkusa yace ki yarda dani wallahi bantaba neman mata ba…
 
     ” Ka cucene da ci amanata ka yaudari ne Allah ya’isa tsakani na dakai nayi dana sanin haduwa da kai…
 
      ” jami’an tsaro ne sukayi ciki da ita sai gidan yari….
 
    ” Haruna yana juyawa ya wanka wa muneeba mari Allah ya tsine miki….
 
      ” hahaha bakaga bala’i ba ma nagama da waccan tsinanniyar matarka saura kai…
 
      ” Goggo ce tace azzaluma muguwa zaki karshen ki…
 
      ” mukhtar kuwa kasa magana yayi sai kuka ga matarsa tace ta rabu dashi har abada….
 
     ” Nafeesa ke faman mom kiyi wane abun mana!
 
   ” i can’t Nafisa i can’t. ….
 
♡♡I can’t stop thanking you for All ur prayer’s…
  
Bazan iya lissafo ku ba amma kusani…
 
     Ina ganin sak’on nink’u na addu’a da kuma fatan Alheri, Nagode sosai kuma ina Alfahari da ku masoya na a duk inda kuke Allah ya tsare ku ya kuma yi muku Albarka!!!Mukhtar k’uwa kasa magana yayi sai kuka ga matarsa tace ta rabu dashi har abada….
 
     ” Nafeesa ke faman mom kiyi wane abun mana! +
 
   ” i can’t Nafisa i can’t…
 
” mom u have to do something banason kande cikin gidan yari please mom kinsan tanada….
 
    ” Duk su Dady sun kasa kunnen su gurin Nafeesa suna jiran suje me kande take da…
 
     ” Nan da Nan barstr hajara ta katse ta u need to keep ur mouth tayi mata Alama da hannu…
 
    ” kuka Nafeesa ta shiga yi, goggo ce ta girgiza nafeesa kingayan meke damun ‘yata…
 
     ” Nafeesa ce tace ke uwarta ce Addu’ar ki k’adai tak’e buk’ata k’i cigaba da addu’a Allah zai warware mata komai kuma gaskiya zata fito fili…..
 
     ” shima haruna da yake saurarar su yace tabbas ko kande zata aikata komai banda Zina! Wallahi karya akeyi mata…
 
     ” iya habu ce taca yimun shiru dan banza kawai ai duk kai kajawo wannan matsala, kaje kanabin karuwai da Aurenka…
 
      ” Dady ne yace wannan maganar bai kamata atattauna ta anan ba ku taso muje gida duk abunda yafaru ma maji Akwai wane abokina lawyer babba zan kirashi….
 
    ” Gaba daya motocin su suka shiga sannan suka nufi gida, Nafeesa ki driving din mom tace mom muje gidan nasu ko za asamu wata mafita….
 
     ” Eh daman can zanje domin dasamu Alakar haruna da muneebah..
 
     ” Bayan sun isa aka zazzauna a palour dady yace Duk abunda yafaru harda ne aciki domin bantsaya nayi bincike ba Nabarku kuka kai kara kotu gashi abu ya cakule gaba daya….
 
         “Mumy ce tace gadai shinan yanzu gaskiya sai fito wa takeyi…
 
      ” goggo ce ta hayyako wacce irin gaskiya wallahi ‘yata bata taba zina ba…
 
        ” mukhtar dake faman kuka sai kace karamin yaro yace Ne da aka kalawa sharri bantaba ganin kande ba tun ran biki sai ranar dana kawo haruna asubuti….
 
     ” brstr ce tace toh wayar da kuka dinga yi kwanaki fa???
 
     ” Nan mukhtar ya zage yabasu labarin duk abunda yafaru da kuma abunda yasa zuka dinga waya da kande….
 
     ” brstr tace yanzu da asirin ya karye shine ta hada bala’in nan…
 
     ” iya habu data kasa magana sai kuka tace lallai haruna ka cuce kande ka zalunci ta shekara daya tana kunsar takaici?
 
    ” Dady ne yace lallai kande ta dabance duk wannan cakwakiyar da suka dinga yi Amma bata sanar ba?
 
     ” Ta sanar min cewar mama farida ta daice min kada Na saki nasanar muku….
 
    ” Yanzu ki kwantar da hankalin ku dole zanje nafara bincike yanzu kai kuma haruna kana bukatar shida domin kuwa idan kukayi shiru zaa kashe kune har ita kanden domin kuwa kunsan hukuncin zina…
 
    ” shiru kowa yayi yana nazari, brstr tayi sallama ta fita….
 
    ●●●●●
 
   Mukhtar yana shiga gidan sa ya tarar matarsa tana hada kaya, kuka ya saka sannan yace wallahi kiyarda dani sweethart wallahi ban taba zina ba….
 
    ” ka yaudari ne wallahi ka cuce ‘ya’yanka duk abunda kakeso amatsaye na na matarka inayi maka shi babu abunda bana yi maka inayin iya kokarina domin Na faranta maka ta fashe da kuka….Wallahi ban taba yaudarar ki ba Dama kuma hakane Rayuwa tana koya maka so, yau da gobe na koya maka wa kake so, matsalolin rayuwa na koya maka wa ke son ka….. +
 
    ” Taja jakarta yau kuma zakaga wake k’inka ba …
 
    ” wane matsanan cin kuka ya saki sannan yace Daga taimako najawo wa kaina bala’i…
 
    ●●●●●●
 
    Kai kai muneebah kina killing fa???
 
     ”  i have tell you ai duk wanda yaga kwai to da askinsa ya ganshe…
 
     ” Amma wannan bala’i dakika hada musu wallahi sharrin yayi yawa….
 
      ” shi uban wanene zance ina sonsa ya bujeri min? hmm to basuga komai ba sai nakai wannan jinin ma da result dinsu…
 
    “Anya muneebah kinajin tsoron Allah? Anya kinada imani to nedai gaskiya zan gaya miki stop it haka…
 
      ” Look at u imani? Ai bansan shi bama gwara ke kina sallah ita kanta sallar namanta rabon danayi ta…
 
     ” ai shiyasa masifun sukayi miki yawa…
 
     ” kisan me zaki dinga gayamin i have tell u…
 
    ” Any way ne nayi Abuja Akwai Alhajin da Zamu hadu anjima yasiye duka kayan kuma zanje naga ummata…
 
     ” my regard to her da akwai lokaci danima naje but sai wane zuwan…
 
     ” okay..
 
●●●●●
 
Kande ke faman kuka ku dinga yimin a hankali mana…
 
     ” wata bakar mata ce tadaka mata tsawa! Sannan ta Hankadata sukayi cikin wane daki na gidan yarin tana shiga in banda wasu ya gulallun yan duniyar mata tagane…
 
    ” Wata ma haukaciyar dariya suka saka yau ankawo mana wata….
     
    ” Kuka kande tasaka mai cike da tausayi sukuma suna yimata dariya har da cewa kyama daina kukan domin zaki saba zaman gidan nan…
 
      Bayan awanne gashi tanason tayi Alwala babu ruwa wane ruwa ta hango tayi Alwalar ta akasa sannan ta juya baya ta kwanta…
 
    ” canna kukalle yarinyar nan har sallah takeyi….
 
    ” ke kyale banza zata daina hahaha…
 
      ” Ita dai kuka takeyi tare da adduo’i..
 
” ke malama kin ishemu da kuka dawane shashsheka, uban wanene yace kiyi lifin mtseww….
 
    ” kyaleta ladi zata daina ne da kanta…
 
    ” wata bakar matace tashigo da bulala tanata zanga musu tana cewa kufita aikin kwata lokaci yayi tunda ta zabgawa kande daya ta duburburci kuka takeyi kamar ranta zai fita….
 
   ” ke dan ubanki bazaki fitaba..
 
     ” jikinta babu karfi ta shige tana fitowa taga sun dauki abun gyara kwata suna ta gyarawa innalillahi wainna ilahir rajiuna taketa fada wane sabon kuka tasaki sannan ta shige  cikin addua da neman tsari ta dauki abun gyara kwatar ita batasan ta inda zata fara ba!..
 
    ” madam ce ta wanka mata mari au kina tunanin zamu rangwanta miki?
 
    ” Cikin wane sabon kukan tace bansan yadda ake ba…
 
     ” Nan ta karba ta Nuna mata…
 
    ” sai karfi uku sannan suka gama aka hau layin abinci…
 
    ” kande itace ta gurin hamsin ga yunwa datake faman da ita, cikin kuka tace ya Allah ka kulamin da wannan cikin nawa…
 
     ” sai karfi 4 akazo kanta dafa duka ce ludayo daya sai ruwa haka tafara ci sai kuwa Amai…
 
    ” Madam ce tace lallai yarinyar nan gata yayi miki yawa…
 
    ” ita dai kande bata kulata ba tayi Alwala sannan tayi sallah tana zaune ta daga hannu tanata Azkar yan dakin suka shigo…
 
    ” fa’iza ce tace ku nifa yarinyar nan tunda tazo tashiga raina kunga kullum sallah da Addua sai kuka…
 
     ” nima haka faiza bari ta idar mu tambayi ta….
 
     ” Kallonsu tayi tace bayin Allah me isa bakwa gaida mahaliccin ku kokun manta shi mai rahama ne akan bayinsa zaku mutu zaku shiga kabari kuma zakusha azabar kabari gakuma ta lahira dukkan nunku kun huce mizanin wasa da Sallah…..
 
   ” Duk’ansu sukayi shiru!…Kuyi hakuri Amma idan nafadi maganar da batayi muku dadi ba… +
 
      ” fa’iza tace kafin nashigo gidan yari mijina yan cimin Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah a dukkan lamuransa…
 
     ”  duk da dai bamusan abunda yakawo ki gidan yari ba Amma kitaimaka kibamu labarin shigowar ki…
 
       ” Shiru tayi Na dan lokaci sannan tafara basu labari kafintaga fuskarta ta cika da hawaye…
 
      ” lallai kin hadu da makirar mata domin kuwa wannan ta sakake a tsaka mai wuya…
 
     ” fa’iza ce tace dukkan makircen ta batakai uwar mijina ba! Domin uwar mijina ita ta kashe mijina da hannunta kuma tace nice…
 
     ” Kande ce tace subhnlhi garin yaya?
 
     ” tabbas nakasance mai biyayya agareta Amma tunda aka kawone bata sona ballantana ta kaunaci ne, watarana mungama fada da migidana akan zuwa gidan mu sai kuwa ta dauke wukar kitchen dina ta caka masa ashe da karar kwana…
 
     ” ladidi ce tace aine ingaya muku kishiyata data isheni sai kuwa ta sakawa gidan namu wuta dakyar muka sha shine nashigo nan…
 
   ” Wata mata tace toh ke yarinya yakamata kisamu mafita fa mijinki mutumin kirkine domin nasansa kwarai da gaske?
 
     ” Kinsan sa fa kikace?
 
     ” kwarai koba haruna ba saurayin muneeba ai dane akaje gurin boka domin ayi masa Asiri kuma daga baya tazo ta sanar dani cewa yake aminciwa dayayi lalata da’ita….
 
    ” kande ce ta share hawayen fuskar ta tace kina nufin dukkan maganar data fada karya takeyi?
 
     ” Wallahi kazafi tayi masa bai taba kwanciya da ita ba wallahi makirar matace muguwa kuma…
 
    ” faiza ce tace yakike ganin zamu taimaka mata tafita daga gidan yarin nan?
 
     ” Kande ce tace Allah ma zai fitar damu gaba dayan mu…
 
     ” Akwai hanya biyu Na farko ko akamata wacce hakan ba zaiyi huba tunda tana da manya a hannun ta..Na biyu kuma ta hanyar kawarta…
 
   ” kande ce tace wacce kawar tata?
 
      ” yusrah ita kadai tasan sirrin ta ita kuma kadai zata warware matsalar nan…
 
   ” Madam ce ta shigo ta dak’awa kande tsawa kizo zakiyi magana…
 
    ” mikewa tayi cikin zuciyarta tace Nasan mom ce…
 
    ” Yana tsaye yasa shaddarsa ita kuma ta lika ta wane daki har zata koma yace…
 
     ” kada ki duramin lifin daban sani ba kada kuma kiyi tunanin wannan zai kawo rabuwar Auran mu wallahi wallahi bantaba sanin wata ‘ya mace ba idan ba ke ba…
 
    ” jiyowa tayi ta fashe da kuka tace Kadaina rantsuwa domin kuwa Na yarda Amma me isa ka yarda Nina saka maka guba?
 
     ” Aisha komai yana bukatar tunani koda kuma komai Allah ya rubuta ki yafene wallahi ina kaunar ki kuma kullum fatana kizams uwar ‘ya’yana kuma koda komai nawa zai kare zanyi iya kacin kokarina gurin fitar dakai…
 
    ” murmushin karfin hali tayi sannan tace Me isa duk ka rame?
 
   ” Matatah tana cikin matsala ai nema ina ciki kuwa, Abunda nakeso dake shine kisaka Aranki ki kuma kudurci Zaki fito daga gidan nan….
 
    ” To Allah ubangiji yasa kagaida goggo kace ta yafemin nema ta daina fushi dani domin mahaifiya take agurina…
 
      ” sai da yaji wane iri da bata ambaci iya habu ba….
 
      ” Sannan ta koma ciki dankwalin ta ta shimfida sannan ta gyara zama…
 
    ●●●●●●
 
         Lokacin da yusrah ta tafi sauka a airport riga da wando ne ajikin ta orange Mota ta hau ta isa gidan ummanta tana zuwa ta rungumeta…
 
    ” masifa umma tafara yimata karki kara rungume ne sha sha sha wallahi haihuwar ki bata amfana min da komai ba kalle shigarki wai ke Al’adar babanki…
 
    ” jikin yusrah ne yayi sanyi tace umma me nayi to?
 
    ” kullum ina gaya miki da ki dinga tsaftace kanki…
 
    ” to umma ina kazanta atattare dani?
 
     ” kazanto ce kai wallahi kije tsoron Allah kuma ki tuna da haduwarki da Allah, domin wannan dabiun naki bana mumina baniba…
 
     ” Toh umma zan gyara muneebah tana gaisheki…Bana ce kada kikara kulata ba, wannan yar iskar yarinyar zata kaiki ta baro ki… +
 
     ” umma tanafa bawa dady kudi…
 
    ” wallahi yusrah kije tsoron Allah Zama da mutanen kirki yana karar da kai ababe guda shida: Son Allah, da bin Allah,da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da barin girman kai…..
 
    ” shiru yusrah tayi tatuna da sharrin da muneebah taje ta hada, ummata bari naje res resturant inada aiki dasu…
 
    ” sai ki saka hijjabi kada kifita haka…
 
    ” hijjabin ta saka sannan ta sau mota sai resturant tana zaune suna tattaunawa wane saurayi Taga sun zauna shida Abokinsa Ankawo musu lemo…
 
    ” Abbas wai kai mekake jirane har yanzu auren ka shiru??
 
” hmm abokina me za’ayi da macen da bata zama agidan iyayenta wacce batasan darajar kanta ba!…
 
    ” yusrah ce ta mayar da hankalinta kan abunda abbas yake cewa…
 
     ” Hakane Abbas Amma ai akwai Nagare acikin su…
 
     ” ta ina mutum zai gane tagari??? yanzu mata sun bace da son abun duniya burinsu kullum tayaya zasuyi kudi kai wasu ma ga shigen bin mazan tsiya…
 
    ” To Allah yabaka tagare ne sai dai Nagodewa Allah domin matata Alhamdulilahi Bangaren Ilimi kuwa ba’a magana…
 
     ” yusrah ce lokaci daya taje Abbas yafara kwanta mata wane tsaki tayi tace ina ai bazai soni ba…
 
     ” Wai abbas yaushe zakaje gurin sis ne?
 
     ” hmm wallahi tausayi ya hanani zuwa kasan baka’isa ka canja abunda Allah ya rubuta ba…
 
     ” Hakane Amma wannan sharri da akayi mata Allah ya fitar da’ita…
 
    ” Ameen Abokina…
 
        ” Yusrah ce tayi sallama suka Amsa…
 
     ” Abbas ne yace sannu baiwar Allah lafiya?
 
     ” Dan Allah in bazaka damu ba zan iya samun numberka?
 
    ” Muna da wane business ne dake?
 
     ” Zakaje abun wane iri Amma…
 
    ” Abbas bata manah ko ma Allah ne yakawo mana…
 
    ” karba yayi yasa mata..” Nagode dear Allah yasaka da Alheri…
 
    ” Ameen yace suka cigaba da hira kai gobe zan huce gurin su dady in sun kawo kudin nan kasaka a banki…
 
  Okay!!…
 
       ” ummata kiyafemin dukkan zunubin dana taba Aikata miki wallahi natuba nakuma bar garari aduniya zan zauna dake auren dakikeso kiga nayi zanyi….
 
    ” murmushi ne ya cika fuskar umma tace wallahi nayafe miki Allah ya dad’a shirya ke, in kika gyaru zakisan tarbiyar uwa da uba akwai bambanci duk wanda yace kafita kaje kayi kudi ba masoyin ka bani tunda ba hanya tagare da zaka samu kudin ya nuna maki ba…
 
    ” umma har aikin company din nadaina…
 
     ” abunda nafeso dake shine kirabu da muneebah har abada…
 
     ” Na rabu da’ita inshaa Allahu..
 
     ” yanzu duk wanda kikasan kin batawa rai ki bashi hakuri domin hakkin mutane masifa ne…..
 
   ” Kuka ta saka sannan tace Akwai yarinyar da mukayi wa sharri ta bata labari tun daga farko..
 
    ” innalillahi Amma kun cuce kanku kun sakata abala’i wallahi kuje tsoron haduwar ku da Allah…
 
    ” kuka yusrah tasaka umma gobe za’azauna akotu…shiru umman ta tayi nadan lokaci tace kiyawaita istigfari..
+
 
    ●●●●●
 
    Da safe muneebah ke faman buga wayar yusrah Amma shiru see this bitch wayan ma switcg off gashi remain 5mint mu shiga court..ba zai huce wannan bad mom dinta ta hanata ba…
 
     ●●●●●
 
Dukkan illahirin family An hadu hatta su abi da ummi sai da sukazo…
 
    Alkali ne ya shigo kowa ya tashi sannan yace Ayau 17/3/16 zamu karasa shara’ar da tazo mana da sababbin abubuwa ina so masu lefi duka su hudun su fito…
 
    ” Muneeba da Mukhtar ne da haruna suka fito…
  
     ” kande da’aka fito da’ita daga wane guri duk tayi bak’i fuskar ta ta kumbura…
 
   ” barstrs zasu iya gabatar da kansu…
 
    ” brstr hajara ce ta miki tace nece brstr din wayanda ake kara haruna mukhtar da kande…
   
    ” Brstr hashim ya tashi yace nine brstr din wacce take kara!!
 
     ” ko kanada Abun cewa?
 
    ” kwarai ya mai girma mai shari’a kusa da kande ya huce yace kinso kikashe shi kuma kin ci amanar sa…
 
     ” Tayaya zan kashe abokin rayuwata mijina uban yayana wanda Aljannata take hannunsa???
 
     ” To me isa kika saka masa gubar bayan kinsan da haka?
 
     ” bazan daina fadin cewa bani nasaka guba muneeba ce itace! Tun abaya da take bibiyarsa banso nakashe shi ba sai yanzu in nayi kisan ribar me zam samu???
 
    ” To ke wanene shidarki…
 
      ” wanda ya halicce mu kuma yaraya mu mukuma ya saukar da kaddara ga wanda yaso Alokacin da yakeso baya bacci kuma yana jinmu yasan mai gaskiya ya kuma san mai karya, Bana cin haram banga ta dalilin dazanyi karya ba kokuma na rantse akanta….
 
    ” kotu akafara Allahu akbar…
 
     ” Alkali ne yayi gyaran murya…
 
     ” brstr ne yagyara tsayuwarsa sannan yace zaki rantse akan cewa bakiyi zina ba??
 
     ” Allah shaidata ne dan haka bazan rantse ba domin rantsuwar danayi ta isa haka…
 
    ” To haruna tayaya kace Amanar matarka har take kokarin kasheka??
 
    ” Amana daya ce arayuwa kuma gaskiya daya ce Wallahi bantaba zina da wannan fasikar fa akasare ma ita taso tayi dani kuma Allah ya taimaki ne…
 
     ” To zaka’iya rantsewa?
 
     ” Tabbas zan rantse..
 
           ” Mukhtar kai kuma dakace amanar mai gidanka kanemi matarsa….
 
    ” hukuncin zina yanada girma Agurin Allah sosai…
 
     ” to ko zaka rantse baka aikata ba???
 
      ” wallahi bazan rantse ba domin kuwa ban aikata zina ba tun tuni nema nake faman rantsuwa….
 
      ” ya mai girma mai shari’a da wannan hujjar ya kamata ayiwa kande hukunci…
 
     ” Brstr hajara ko kinada abun cewa?
 
    ” Eh.. muneebah kin hada gwarama kin bar mutane da aiki kinsan girman zunubin kazafi da shidar zur da karya?
 
    ” Ta yaya zanyiwa haruna kazafe ya cuceni yaci Amanata ku kalle takardar nan ance inada cutar hiv…
 
     ” Hiv kuma??
 
        ” karbar takarda tayi ta mikawa Alkali…
 
        Shiru kotu tayi Na dan lokaci sannan Alkali yace Kamar yanda mukasani acikin kurani da hadisai Akan duk Duk matar Auren da take yin zina, Idan har aka kama ta, kuma shaidu guda hudu suka ganta a irin yanayin da Shari’a ta tanada, Kuma sun cika dukkan sharuda,ko kuma ita tayi Iqirarin laifinta,To
Hukuncinta shine Abinne ta Zuwa Qirjinta sannan Atara jama’a suyi ta jifanta da duwatsu har sai ta
mutu. (Hakanan shima abokin zinar nata ida har ya ta’ba yin aure, ” yanzu kinyarda k’in aikata?…..
 
    ” Kande tana kuka tace bantana zina ba ban kuma aikata zina acikin gida na ba domin nasan cewa dai duk matar da take yin zina, ko tana da aure ko batta dashi, to Tabbas tana cikin La’anar
Ubangiji, Domin kuwa Annabi (saww) yace: IN BANDA SHIRKA BABU WANI LAIFIN DA YAKAI ZINA GIRMAN LAIFI AWAJEN ALLAH…Alkali ne yace Abaki kikasan haka banda zuci Anyanki miki zaman gidan yari na shekara 2 bayan kin gama za’a jefe ki tare da abokin har kallarki kamar yadda doka mai lamba 38 ta hukunta… +
 
    ” Wayyooo Allah Na shiga uku Innalillahi Na shiga uku…
 
    ” Alkali ya tashi zai buga kotu kotu sai ga yusrah ta shigo…
 
     ” Ku dakata ku dakata inada magana…
 
    ” Alkali ne ya koma ya zauna…
 
     ” yusrah ce ta nuna kande da hannun ta tace wannan matar shidan ma yana Alfahari da ita kafira ce maguwa ce kuma makarya ciya ce…
 
    ” Muneeba ce ke ta faman zare ido tana surutai…
 
   ” Duk abunda ta fada karya takeyi kande tsaftacaceya ce kamar yadda mijinta yake kuma mukhtar bai taba zina ba, ita tasakawa kande guba dan ace itace…
 
     ” karya takeyi alkhali bansanta ba bansanta…
 
     ” Alkali wayannan matan kisa yakamace su ne kawarta ce aminiyarta Nema Allah ne ya shirye ne ta durkusa gaban kande dan Allah ki yafemine…
 
     ” kande dai dake faman kuka tace bakomai naje dadi dakika koma kan hanya madaidaiciya bantaba kawowa zaki taimaki ne ba…
 
     ” Nagode haka taje gurin haruna da mukhtar har su dady ma sai dataje kowa ya yafe mata…
 
    ” Brstr hashem ne yace ina shaidarki…
 
      ” Yusrah ce tace kaine shaidata ta farko domin an siyika da kudi domin kazo kayi alkalancin karya, doctor kashigo photograph kaima shigo…
 
    ” Dr suleiman ne ya kalle muneeba kinsa Na Aikata mafi munin laifi arayuwa ta ya ciro kudinta ya watsa mata wannan shine mafi sharrin abu aduniya wato kudi ya mai girma mai shari’a Dukkan abunda takawo nan karya takeyi hatta gubar da aka zubawa haruna ne na bada ita…
 
     ” photogrph shima yayi bayaninsa yakuma nemi yafiyar kande da haruna …..
 
      ” Muneeba ce tace munafuka annamimiya kin tona min asiri to wallahi sai nazama ajalinki…
 
     ” kawance na daki babu abunda ya haddasan sai asara Allah ya wadaran kawa irinki kuma kisane Ne na zamar miki kadangaren bakin tulu..kuma dukkan nisan jefa kasa zata wado Da rashin imani irinki gwara mutuwa wallahi…
 
    ” muneeba ce ta fara kokarin kiran waya nayi din kuma ke kande akan haruna bakiga komai ba…
 
    ” kafin kace me tuni yan sanda sun cakumeta….
 
    ” An yankewa muneebah hukuncin zaman yari na shekara 15 tare da horo mao tsanane da rashin bilinta…
   
    Kuma kotu ta wanke kande daga zarge da akeyi mata ita da haruna da mukhtar…
 
    ” Wane kuka kande ta saka Nafeesa ce ta tawo ta rungumeta sannan tace Alhamdulilahi tasa hannu ta share hawayen fuskar kande…
 
   ” Nagode kawata kincika kawa tagare mai kaunata bai bani shawara duk lokacin da muka zauna saukin nunamin hanyar tsira…
 
     Mom nagode nagode…
 
     ” Tashi kande karki damu kadan daga hukuncin Allah shiyasa dukkan wane tsanani yana tare da sauki…
 
   ” kande ce ta matsa kusa da goggo tace ki yafeni ya mahaifiyata…
 
    ” kuka tasaka tace bankasance uwa ta gare agareki ba ban sharemiki kukanki ba ki yafemin kada Allah ya tuhomine akanki…
 
    ” Dan Allah goggo ki daina kuka wallahi bakiyimin komai ba rungumeta tayu tace kice gaba da shimin Albarka domin Albarkar ki kadai nake bukata…
 
     ” Allah yayi miki Albarka…
 
     ” iya habu kiyafemin kiyafemin, ” iya habu ce ta rungume kande tace kunyar ki nakeji ‘yata ne zakiyiwa afuwa domin hakkin da adduar marainiya da wanda aka zalunta bashida hijjabi…
 
   ” haba uwata dumbun soyayyar dakika Nunamin ta’isa Nagode miki abu mafi kyawu kika auramin Danki…
 
     ” mumy ce tace Dan girman Allah kiyi hakuri kande kiyafemin Dan Allah Dan Annabi….
 
    ” wallahi ban rike ku araina ba Kuyafemin nema Na yafe muku…
 
    Kowa Addu’a yakeyi mata…mama farida ce tace ga ranar da nace muku zatazo ‘Ya‘ya suna da haqqoqi a kan iyayensu kamar yadda su ma iyaye suke da haqqoqi masu girma a
kan ‘ya’yansu. Yana daga cikin haqqoqin ‘ya’ya a kan  iyayen su wadanda musulunci ya dora masu, Kuma dole ne iyaye su sauke wannan nauyi da ke kansu domin samun tsira ranarqiyama +
 
‘Ya‘ya amana ce Allah ya ba mu zai kuma tambaye mu game da amanar da ya ba mu….
 
  ‘Ya’ya suna buqatar addu’ar mahaifansu, Iyaye su yi haquri idan ‘ya’yansu sun vata masu rai su bar tsine masu, Zagin yara da tsine masu yana jawo wa yara hasara da bala’i a duniya da
Qiyama, Mafi yawancin ‘ya’ya sukan shiga harkar shaye-shaye da sace-sace da zinace-zinace ne ta sanadiyar tsinuwar da iyayensu suke yi masu.,Addu’ar mahaifa Allah yana amsawa….
 
   ” Dukkan nin su kukace Allah ya yafemana…
 
    ” Kande dake faman shari hawaye goggo tace kada ki bimo ki huce zuwa gidan mijinki gobe zamuzo mu….
 
    ” Haruna dake tsaye abakin kofar motarsa yanata kallansu..
 
     ” Har tayi gaba Mom tace zo kande…
 
     ” ki kula da cikinki kinje ki kula…
 
    ” Tohm mom sai kunzo…
 
     ” Tana karasawa bakin mota wane sabon hawaye ya wanke mata fuska…
 
    ” Goge mata hawayen yayi yace ya ma abokiyar kyau hakuri Ke yafewa mijinki akan abunda yaye miki…
 
    ” Rungume sa tayi sannan tace Fushin ka gareni kamar garwa sheni akan leda dukkan abunda yafaru yazama tarihi kuma Na yafe maka…
 
●●●●
    ” Suna isa gida haruna ya dakko ta cak daga mota directly toilet yayi da’ita yayi mata wanka sannan yasaka mata towel ya ajiyeta akan gado tana hawaye shima bai jima ba yafito ya rungumeta ya dariya karfa kukanki yakare…
 
    ” Wannan kuka da godiya ga Allah ne dayasa zankara rayuwa da kai…
 
    ” Wayarsa ce tafara ringing yana dauka yake Ance ka kula da matar ka tanada ciki wata 3 agigice ya jiyo what???
 
   ” murmushi tayi tafara kokarin rufe fuskarta..
 
     ” shafa cikin yafariyi yana kissing dinta ina sonki ina kaunarki you know that i miss you dear ple….
 
    ♡♡♡♡♡

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *