LOVE CYCLE CHAPTER 2 BY nnafie
Koda ta dawo ta shigo parlorn har lokacin daddy ne kadae zaune.. Amsa mata sallamar yy ta zuba masa idanun ta dake nuna alamar tayi kuka snn murya na rawa tace “dad nayi submitting” yana mata wani kallo dake sa taji kuka yace “kin taimaki kanki”… Kamar kau jira take ta fashe masa da kuka… Ko daya bata son taga tayi abinda ze bata ma dadyn ta rai bataso taga yana fushi da ita sbd gaba daya seta jita wani so lonely sbd shi dady mutum ne wanda yake spending duka tym dinsa inhar yana gida a kansu…….
Murmushi daddy yy shi kanshi baya iya jure fushi da ita.. Mika mata hannun sa yy alamar tazo… Aikam kamar jira take ta ruga ta fada jikin sa tana Kara karfin kukanta.. Bubbuga bayan ta ya shiga yi.. “Is ohk daughtee”… Cikin kuka tace “I’m sorry dadd pls ka dena fushi dani I feel so bad very bad daddyy”… Yana murmushi yace “to promise me bazaki karaba bazaki kara misbehaving ba” da sauri tace “Na dena dad”.kara rumgume ta yy “common stop crying girly kamar ba jaruma ba”… Murmushi tayi tana kara shigewa jikinsa snn ta shiga sauke ajiyar zuciya… Sosai yake jin diyar tasa a cikin ransa yana sonta fiye da tunanin me tunani.. Ita da kanin ta kade yake kallo wadan da suke jinin sa sune kade ze kalla yaji farin ciki dukda kuwa yan uwan nasa suna raye amma sun masa nisa basa bukatar sa tare dasu.. Sosai abinda sukayi yake ci masa rai.. Sosai yake fushi dasu kuma shima yy zuciya dasu ya watsar dasu kamar yanda suka masa.. amma deep down inside him.. He missed them…he missed them very bad.but he is hurt… Shiyasa shima ya watsar dasu shiyasa shima ya manta dasu shiyasa shima yazo yacigaba da rayuwa with his own family da basu da yawa yasan suma zasuyi yawa snn ya manta dasu shima….. “Dady” Fannah ta kira sunan sa ganin yanda yy shiru.. Murmushi ya sakar mata yana jan kumatun ta kafin yace “muje muyi breakfast”… Gyada kai tayi suka nufi dining shi yay serving dinta snn ya fara bata tana karba cike da nishadi… Mummy ce ta sauko tana kallosu tare da kama kugu tace “waya baku ryt din taba min Abinci”… Duk zaro idanu sukayi suna kallonta kafin su kalli juna .. Dady ya nuna Fannah yace “itace tace muci”.. Kwalalo idanu fannah tayi tace “ni kuma dad” ya gyada mata kai snn ya kalli mummy… Kafin mummy tayi magana fannah tace “mumm bani bace shine fa”… Zama mumm tayi tana karkada kafa.. Ku gama yau baku da lunch autana kawai zanba …. Daddy yace “sorry love” dauke kai tayi tana kallon fannah fannah ta dukar dai tana murmushi…. Aikam haka akayi da lunch tayi kane kane ta ja dan autan ta gefe tana bashi abinci tama ki kallon su dady da fannah da suke ta rarraba idanu.. Fannah tace “mummy” “shhh don’t mummy me here”… Hisam ya juyo yana mata gwalo.. Ta balla masa harara… mummy tace “Au haka akayi Kinja maku autan nawa kike harara” da sauri dady yace “madam bnd horo da yunwa we can’t take it anymore” ya fada yana langwabar… Hararan su tayi tace “oya kuzo badan halin ku ba” da sauri suka tashi suna murmushi… Suna gama ci Suka tashi suka koma parlor sukaci gaba da kallo ba tare da sun kalli mummy ba… Mummy tace “oh haka akayi zaku sani… Suma suka zauna suna kallon… Da da daddare daddy ya kalli mummy yace “madam how about the dinner”.. Mummy ta dauke kai tace “yau ba dinner dana kade zeci abinci”… Mikewa daddy yy yace “mamana zokiji wani Abu”.. Daga haka sukayi hanyar fita… ganin haka yasa da sauri mummy taje ta dauko mayafinta suka fito lokacin har su dady sun shiga mota.. Mummy ta bude baya ita da hisam suka shiga tana hararan dady tace “kafar mu kafar ku.”.. Duk dariya sukayi snn dady yaja motar suka fita.. Yawo sukayi sosai sunyi ciyeye iri iri.. Se 11 suka dawo daga nan kowa ya neme makwancinsa haka suke rayuwar su cike da farin ciki su hudu se kuma abokanai basu da wani family da zasu ce nasu ne……..
karfe takwas Na safe fannah ta gama shiri sanye cikin wata doguwar riga ashe mai stones.. Rigar ta mugun yi mata kyau seta kara ma fatar ta kyau ta yafa veil din rigar gashin gaban kanta sun kwanta luf luf tayi wani kyau duk da ba kwalliya a fuskar ta 9 ne lectures dinta dan haka tea kadai tasha ta dauki car keys dinta da jakar ta ta fito… Cikin 15minutes ta kawo apartment din su maryam koda taje.. Seta iske maryam se lokacin ma zata shiga wanka… Dafe kai Fannah tayi tace “ai nasani bama ki shirya ba kk ce mun kin shirya” da sauri maryam ta shige toilet tana dariya … Fannah tabi toilets din da harara… Snn ta fara fito mata da kayan sakawa dan tasan wnn ma wani bata lokaci ne inde wajen maryam ne…bata wani dade ba ta fito daga wankan tayi shafa snn ta saka kayan da Fannah ta fito mata dasu . Snn ta dauko hand bag dinta da wayar ta dake ringing.. Tana kallon Fannah tace “kinga yaya khalil din nan tun dazu shiya hanani shiryawa..murmushi kawai fannah tayi suka shiga mota tajasu.. Maryam na cigaba da wayar ta… Ita de maryam da ya khalil din nan birgeta suke .. Gasu family guda kuma suna soyayya suna kuma so su kara creating wani family din se abin ke birgeta su kuwa su hudu inama taga dan uwan da har zasuyi soyayya tare.. She wish ace dan Nigeria zata aura amma ita kap masu sonta yan nan ne se other countries bata da saurayi dan Nigeria ko daya shiyasa bata da tym din duk wasu samarinta bama ta kulasu hakan yasa wasu ke mata kallon me girman kai…. Har seda suka isa snn maryam tayi sallama da khalil… Sun shiga inda ake lectures din bada jimawa ba lecturer din ya shigo dan haka duk suka natsu… Bayan ya fita ma suka dan samu break snn wani ma ya kara shigowa.. Suna fitowa Fannah ta shafa cikin ta tana kallon maryam kamar zatayi kuka tace “yunwa”… maryam tace “ohk muje”… Maryam ce ta masu order suka fara ci.. Maryam tace “zomuje field din nan naji kamar ball ake”.. Zatayi magana maryam tace “don’t se no madam” kafin ma ta karasa magana maryam ta mike babu yanda ta iya haka ta dauki drink dinta ta bita … Kafin ta karasa shiga wajen har maryam ta shige da dan saurinta.. Dan maryam bade son ball ba… Murmushi kawai tayi.. Tazo zata shiga knn taji an buga mata wani abu.. Drink din hannun ta ya zube jikin ashe din rigar ta… Ta rike hannun ta dage mata zugi tace “ouchh” tana bin hand ball din da ta fadi a kasa da kallo… Bata gama tunanin daga Ina ball din take ba taga wani ya duka ze dauki ball din.. Yana sanye da kayan sport.. Da suka mugun amsar jikinsa snn suka dace da fatar jikinsa wacce take ita ba baka ba, ba fara ba, ba kuma wanka tarwada ba. Dan tafi ta wankan tarwada haske.. Irin golden brown skin nan ne me shining wacce ta hadu da hutu snn kallo daya zaka mata kasan tana samun kulawa ta musamman… Jikin sa a mummurde dan daga gani yana sport da gym.. Dagowa yy bayan ya dauki ball din ya juya ze tafi…. Ware idanun Fannah tayi ganin guy din jiya ne daya bigeta… Da sauri Fannah tasha gabansa cike da fushi tace “hey you”… Tsayawa yy tare da Zuba mata manyan idanun sa da suke farare tass snn ya dage gira daya alamar what.? … hakan ya kara kular da ita ganin yanda ya mata cikin kuluwa tace “what’s ur fucking business with me why are trying to ruin me?”…… hannun sa daya tusa cikin sumar kansa tare da dan cizar lips dinsa wadan da suke pink sosai.. Kafin a hankali ya bude baki in a very low voice yace “did I knw you?”….. Ji tayi kamar ta kifa masa Mari ganin bnxar tambayar daya mata…. ganin yana niyar tafiya ya barta tsaye yasa ta kara shan gabansa kamar zatayi kuka dan har muryar ta ya fara rawa cike da masifa tace “which kind of stupid question are you asking who knw’s you too who even care about you just stay away from me stop pretending that you don’t knw what you did the other day and look at what you did to me today” ta fada tana nuna kayanta da suka baci da drink tace “you hit me with ball and you can’t even look and say srry which…. ” “shhhhhhh” ya katse ta ta hanyar daura soft fingar dinsa a kan tattausa lips dinta…. Ya dan ya mutsa fuska murya kamar amma sa dole yace “don’t shout I feel headache”….. Daga haka yy gaba ya barta tsaye cike da mmki da haushi…. Tabi bayan sa da kallo a hankali tace “who is he.. Where is he from”…. Ta tambayi kanta… Shide Na farko ba English bane ba Indian bane ba kuma African bane snn ba American bane.. But he looks like irin kyawawan black Americans din nan ko kuma yan sudan kokuma Nigerians din nan da kudi da hutu ya masu yawa… Taba ta akayi shiyasa ta juya da sauri.. Maryam ta gani tace “ya baki shigo ba wai zomu shiga pls” fannah ta fizge hannun ta tace “dallah malama rabu dani ai duk ke kika jamun abinda akamu… Se a lokacin ta lura da kayan Fannah da suka baci.. Rufe bakin ta tayi tana hana dariyar ta fitowa.. “Ya haka Fannah what happened to ur cloth” fara tafiya fannah tayi tana fadin “nayi gaba idan baki biyoni sekin taho”… Binta maryam tayi tana tura baki can kasa kuma dariya ce ke cinta.. Fannah kau tunanin yanda zata rama Abinda wnn bawa ya mata take.. Suna shiga mota maryam tace “wai meya faru” … Bnx Fannah tayi da ita.. Ta kunna motan hakan yasa itama maryam tayi shiru…… Reverse Fannah tayi… Taji maryam tace “wow what’s a handsome guy gsky guy din nan hadu”.. Kallon maryam da ta wani dunkule hannu tana ware ido fannah tayi… Kafin ta kalli inda take kallo…. Da mugun mmki take kallon guy din nan na dazu ne.. Batasan lokacin da ta figi motar tayi gadan gadan wajesa ba ba…. A rude Maryan tace “ke are you ohk” tana zuwa gab dashi kamar zata bigesa ta danna masa wata irin hon… Hakan yasa ya juyo yana kallon motar… Fannah ta zuje glass din tana masa wani bnxan kallon dan mugun haushin sa take ji rasa mema zata masa tayi kawai seta dauko tissue din dake gaban motar ta ta jefa masa tace “stupid” tare da jan wani dogon tsaki snn taja motar ta da mugun gudu tabar wajen… Dafe kai maryam tayi kamar zatayi kuka tace “kee me kike tunanin kin aikata what’s wrong with you ki jefi mutum ki masa tsaki kinsa kuwa wnn babban wulakanci ne” dan murmushi Fannah tayi dan ko ba komai taji sanyi a ranta… Maryam tace “amma kinsan abinda kikayi ba kyautawa bane ba ko”… Kamar Fannah zata maketa tace “ni abinda ya mun kyautawa ne ai ko” ta fada tana nuna jikin ta… Maryam tace “wai dama shine”… tabe baki Fannah tayi tace “wnn ma ba shine na farko the other day bugeni yy ya tafi ya barni da kwashe takardu yau kuma he hit me with ball and just pass kamar be ganni ba dana masa magana se cemun yy zan saka masa ciwon kai who is he.. who the hell he is da zan zauna yana mun abinda ya ga dama na kyalesa wlh kadan ya gani… Mtswww” dariya sosai maryam tayi tace “well i like this game bana so ya kare dan ina son kara ganin guy din nan da ya hadu over”… Tsaki Fannah tayi tana jin haushin maryam din….
A apartment din maryam tayi wanka ta saka kayan ta snn ta fito dama already maryam ta dafa masu abu me sauki kafin ta fito…zama sukai suna ci.. Maryam ma tsakura kawai take dan rabi waya suke da khalil… Can Fannah ta dago tace “ke madam kici abinci wayar ta isa haka” dan ita Fannah bata cika son waya ba bata ma da wani tym din samarin bare tayi wata waya dasu… Maryam tace “yace ya kusa zuwa ya gudu Nigeria dake ciranin a kasar wasu ta isa haka yakamata a dawo gida”… Dariya sosai Fannah tayi tace “kice masa yazo ya tafi dani”… Maryam ta fada masa snn ta dago tace “yace ai na kusa komawa se ki bini…. ” dariya kawai Fannah tayi batace komai ba. Se taji inama ace ta bita…. Bayan sun gama cin abincin maryam tace “ke wlh so nake naje gida I tried alot dan mun gama wadan nan practicals din da zamuyi zan je nayi ko sati ne kokuma idan mun samu intervals”… Fannah na gyara veil dinta tace “Allah ya kaimu” daga haka ta dauki bag da keys dinta tayi gaba maryam ta rakota ta shiga mota ta tafi gida…. Tana shiga parlor hisam dake zaune yana kallon cartoon ya rugo da gudu ya rungume ta.. Itama rungume sa tayi cike da son yaron tace “Autan har ka dawo” gyada mata kai yy.. Ta jasa suka wuce bedroom din mummy… Gaisar da ita tayi.. Mummy tace “ur food” dan ya mutsa fuska tayi tace “mom I’ve already eaten a wajen maryam may be later ynx bacci nake ji I need some rest”….
Bedroom dinta ta wuce ta canza kayan jikin ta tare da fadawa saman bed dinta mai taushi. Tana lumshe idanu.. Gaba daya se taji duk ba dadi da maryam tace mata zata tafi tasan she will be so lonely dan da ita kadai ta saba se vaneesa da suke good tym sauran sede gaisawa sama sama.. Setaji kamar ta bita itama taje taga family dinsu taje tace masu itace Khadeeja diyar Muhammad Radda suyi yanda zasuyi da ita… Ita de a yanda dadyn ta yace mata da ta matsa tana son sanin danginsu yace sude baban su sunan sa Alhaji Aliyu Radda su yan katsina ne but suna zaune a Abuja sede sallah da duk wani taro na family suna yinsa A katsina suna da family house a Katsina da Abuja.. Alhaji Aliyu Radda ba ba boyeyyen mutum bane sananne ne sosai dayawa an san family din Radda a Nigeria.. Matan Alhaji Aliyu biyu Amina da khadija snn yaran sa takwas biyar maza uku mata… Amina nada biyar (Ibrahim, maimuma, Ahmad, Aminu, da kuma sa’adatu) khadeeja kuma nada (Rabiu, Muhammad se autar su Raheena)… Ibrahim ne baba se maimuna se Ahmad se Aminu shida Rabiu kusan sa’anni ne se Muhammad se sa’adatu da auta Raheena…. Duka matan Alhaji Aliyu basu da matsala mutane ne masu sanyi snn suna hakuri da juna shiyasa suke zaman lafiya ba’a jin kansu Alhaji Radda kau yana da zafi sosai snn yanada tsatstsauran ra’ayi ya matukar son yaransa sosai snn tsaye yake a kansu be yarda kayi ba daidai ba se ka karbi hukunci wnn dalilin ne yasa suke kiyayewa… Kuma kusan duka yaran shi suka dauko zafi Ibrahim, maimuna, Ahmad, Rabiu, Aminu da Raheena duk zafin sa suka dauko Muhammad ne kawai se sa’adatu sune suka biyo iyayen su mata amma duk in sukayi fushi ba kyau…duka yaran sa a kashen waje suke karatu mata ne suke yi a Nigeria Alhaji Radda tsaye yake wajen karatun yaransa both boko and islamiya..duk wanda ya dawo se yanemi mata cikin yan uwa can katsina ya aura .. Hakan kau Akayi.. Baffa dan sunan da suke kiran Alhaji Radda knn.. Yana mugun ji da Muhammad dan shine autan maza da kuma kasancewar sa me hakuri yawanci duka yaran sa kasashen larabawa suka tafi karatu sbd yana ganin kasashen turawan nan lalacewa yara suke shiyasa be yarda ya kai dansa can ba.. But daga kan Ahmad ganin shi yaje America ya samu da kyar ya yarda yaje can ganin har yagama karatunsa be lalace ba yasa ya yarda ya kai Muhammad england da ya samu.. sosai Muhammad ya mayar da hankali a karatunsa be dawo gida ba se bikin yayunsa Aminu da Rabiu lokacin Family din sun dan fara samun yara sbd yaran Ibrahim da maimuna da sa’adatu duk mata matar Ahmad de bata haihu ba.. Da yake kowa yana da katon gidan sa a wajen se yy kamar wata estate dan Baffa baya so yaran sa suyi nisa dashi duk da idan kayi aure zaka iya tafiya kasar da kaga dama ka zauna Amma be yarda ka zauna can ba… A lokacin ne akayo wa Muhammad caa akan daya dawo zasu sha biki dan ga matar sa nan sakeenah datake bala in sosai tana jiransa murmushi kawai yy dan shi kodaya baya son sakeenah halinta be masa bayajin ze iya auren ta sede yasan da wuya yan uwa su yarda yaki auren Sakeenah sede su bazasu gane me ya gani tattre da ita ba kodaya tarbiyyarta bata masa ba hasali ma yana da wacce yake so da suka hadu anan Uk din sede ita din ba muslma bace…….