Ayshat Ɗansabo lemu ✍NAILAH CHAPTER 3 BY

Ƙarfe 8:30pm suke haɗuwa a dining domin cin abincin dare kafatanin iyalan gidan,wannan sabon sune tun fil azal sai dai wanda keda uzuri ya tafi wani wajen to sai aci babu shi,amma matuƙar kana gidan zaka fito a haɗu aci abinci tare da juna.

Duk an hallara harda Dady da dawowansa kenan bada jimawa ba yai wanka ya gabatar da sallah ya fito,yana sanye cikin jallabiya ash color dayai masa kyau sosai,dattijo me shekaru 65 aduniya ma’abocin fara’a,kirki da sanin yakamata uwa uba mutum ne me tausayi da taimakon talaka,mutum biyu basu hallara ba wato Nailah da bata jima da fitowa daga watsa ruwaba kaman yadda tasabarwa kanta indai weather na zafine sam bata iya bacci idan bata watsa ruwa ajikinta ba komin AC daza’a saita watsa ruwa,sai dodon nasu da shima yake can part ɗinsa bashida niyyan fitowa domin sam baya son yayi tozali da yarinyar sam.

Momy ce ta dubi Amal dake ƙoƙarin sarving ɗin Dady,tana faɗin.”Amal kinga gama ki kira Anwar a phone kice maza ya shigo.”

Dady ya dubi Momy ya saki murmushi batareda yace uffan ba,itama murmushin tayi tana janyo plate ɗin da Nafeesa ta zuba mata tuwan semo da miyan ɗanyar kuɓewa da yaji naman cow da fish,ita kuma Nafeesa jallof ɗin cous cous ta zuba da salad,Amal ce tayi dialing numbern ya AA kaman yadda tai saving ta saka a hands free,tana cigaba da sarving Dady bugu biyu ya ɗaga call ɗin muryansa can ƙasa sosai.

Memakon Amal tayi magana sai Momy ta janye wayan zuwa gabanta tana faɗin.” Anwar ka shigo yanzu an haɗu adining.”

Kafin yayi magana ta katse kiran tana turawa Amal wayanta,babu wanda ya sake magana kowa hankalinsa nakan abincinsa,lokacin ne kuma Nailah ta iso sanye cikin doguwar riga daya sauka mata har kasa na bacci,rigan me taushi ne saidai sam baya nuna jiki ta ɗaura ƙaramin hijab akai wanda ya rufe jikinta daga sama zuwa guiwan hannunta,gaida Dady tayi da yimasa barka da dawowa kafin taja kujera ta zauna,tana janyo plate ta fara zuba macaroni pasta,ƙaramin bowl taja ta zuba fruit salad ƙadan suka haɗa ido da Amal suka murmusa,sallaman ya AA da isowansa dining area ɗin yasa Nailah saurin maida hankalinta kan abincinta,bayan ta saci kallonsa sau ɗaya yana sanye cikin baƙin jallabiya me ƙaramin hannu daya haska farar fatansa Dady ya gaisar yana me tsugunawa har ƙasa,hannu Dady ya miƙa yana shafa kansa kafin ya Hussain ya gaida Anwar ɗin ya amsa ataƙaice,Amal ma ta gaidashi sannan su Nailah suma suka gaidashi ya amsa adaƙile ,kujeran kusada Dady ya zauna bayan yaima Momy sannu da dawowa.

“Nailah tashi zubawa yayanku abinda zaici please.”

Atare Doctor Anwar da Nailah suka dubi Momy,itako ta basar tana cigaba da cin abincinta hankali kwance,Nailah ta miƙe tana kallon side ɗin da ya AA yake tana tambayansa abinda zata zuba masa,yana jinta sarai amma saiya shiga danna waya tamkar me yin wani abu me muhimmanci,har saida ta sake maimaita tambayanta kafin ya zuba mata wani mugun kallo yana faɗin.

“Just pepe soup with salad.”

Kowa yasan shi baya son abu me nauyi da dare saboda shi dama ake yawan yin soup dasu salad da dare,da irin su cous cous haka duk yana so,sai data xuba ta tura gabansa tana shirin zama ta fara cin abincinta ya furta.
“Wait zuba fruit salad cikin bowl kije kisamin cikin frige kafin na tashi wucewa ɗaki yayi sanyi yadda zan buƙata.”

Babu yadda Nailah ta iya haka tabi umurninsa,can ƙasan zuciyanta na ƙuna saboda tasan da gayya yayi hakan don yasha jin ana faɗin bata son cin abinci idan yafara hucewa,kafin takai kitchen ta dawo kuwa tuni abincin data zuba ya wuce dama ba abu me wuyan hucewa ta zubaba,daga Hussain har Amal da Nafeesa duk sun gane da biyu ya AA ɗin yayi hakan,suna kula tun shigowansa yake wani cika da batsewa gawani uban harara da yake bin Nailah dashi a fakaice,duk abinda yake Momy na gani sai tayi tamkar batasan meke wakana a wajenba,koda Nailah ta dawo memakon taci pasta ɗin data xuba kawai saita ja bowl ɗin data xuba fruit salad ɗin tana sha ahankali,Momy ta dubeta tana faɗin.

“Nailah maza ɗauki abincin kije kiyi warming ɗinsa sai kici da zafinsa,taya zaki sha fruit salad kawai bayan ranki nason abinda kikai sarving.”

Ba musu Nailah ta ɗauki plate ɗin ta nufi hanyan kitchen akaro na biyu,idanun AA Mainasara na binta da kallo harta shige ya saki siririn tsaki ta yadda bamai jiyo sautin fitansa,kafin ya faracin abincinsa cikin nutsuwa har zuwa time ɗin da gimbiyan tasa ta doko masa kira,hakan yasashi ɗaukan plate ɗin salad ɗin ya nufi cikin falo yana zama cikin seater yake amsa call ɗin,atare Momy da Dady suka tashi don sun kammala,Dady ya nufi side ɗinsa yayinda Momy itama ta nufi nata side ɗin,Dady ne ya dawo da baya yana sanar da Anwar cewa idan ya gama ansa call ɗin ya sameshi a falonsa yana jiransa.

Anwar saiya yanke wayan yana sanar da Hudah cewa zaiyi calling ɗinta back idan ya koma part ɗinsa ,ya aje plate ɗin salad ɗin da saura kaɗan ya ida cinyewa ya nufi part ɗin Dady.

Da sallama ya shiga ya samu Dady zaune hankalinsa nakan TV,yana kallon News ya amsa sallaman Anwar yana maido da hankalinsa kan Anwar ɗin,daya samu kusada Dady ya zauna daga ƙasa yana faɗin.

“Dady gani.”

Dady ya dafa kansa yana faɗin.”Anwar likita bokan turai gani nayi yau sai wani botsare baki kake fuska kaman hadarin watan augusta,sanar dani damuwanka my son kaji.”

Sai yanzu naga Anwar ya saki mumushi cikeda narke murya yake sanar da Dady yadda sukayi da Momy da Hajiya Dadah,yaƙare maganan yana faɗin.
” Dady ina zan iya haɗa mata biyu na aura bayan kokai ban tashi naganka da mata biyu ba Momy ita kaɗaice,kuma Dady idan ma haɗin akeson yi baga Usman da Hussain nanba duka sun isa aure musamman Hussain dana kula suna shiri da yarinyar.”

Anwar yaƙare maganan yana duban fuskan Dady,tareda sauraron abinda Dadyn zaice,kaman saukan aradu ya jiyo muryan Dady ya soma faɗin.

“Anwar manya yanxu saboda wannan maganan kaketa cika da batsewa,to aini banga abin damuwa ba tunda har Fateema tai maka gata ta baka zaɓin haɗasu duk su biyun ka aura idan har bazaka iya rabuwa da ita ƴar gidan Commissioner ba,don ni cewa nayi ta sanar dakai kajanye zancen yarinyar gaba ɗaya domin bata samu shaidan tana da isasshiyar tarbiya ba,amma tunda kaji kagani Anwar zan shige gaba wajen nema maka auren Hudallah kaman yadda kake so sai dai kasani babu fashi tareda Nailah xa’a ɗaura muku aure ko kana so koba kaso,inyaso idan anɗaura auren ka saketa ka nunawa duniya cewa bamu isada kaiba,sannan ina so kasa aranka munfika sanin cancanta ko akasinta da xaka dinga sanyo Usman ko Hussain cikin lissafinka,mu dakai mukaga ta dace bada suba maza tashi kabani waje,gobe idan Allah ya kaimu xanma iyayenka Aminu da Salisu magana suje atsaida magana saika sanar da yarinyar domin ta sanar da ubanta.”

Dady yaƙare maganansa yana nunawa Anwar hanyan ƙofar fita,fuskansa a haɗe yake tsaf babu alamun wargi hakan yasa Anwar tashi jikinsa har wani rawa yake ya baro falon yana tafiya tamkar zai kifa sabida yadda zuciyansa ke tsananin ɗaukan zafi,fitowansa daga sashin Dady yayi dai-dai da fitowan Nailah daga kitchen inda anan ta zauna taci abincinta bayan tayi warming,gamawanta kenan ta fito domin wucewa room ɗinsu,don yau bataji zata tsaya wani zaman hira afalon,cikin sa’a suka haɗa ido da Anwar wani matsiyancin kallo me cikeda nuna tsana ya jefeta dashi yana nufan hanyan barin sashin nasu baki ɗaya,yana jiyo muryan Amal na masa saida safe amma ko waiwaye ya fice abinsa,Nailah ce tayi saurin nufan hanyan corridor dazai sadata da ɗakinsu,jikinta na rawa tana jin wani iri gameda mugun kallon daya jefeta dashi,xamanta abakin bed yayi dai-dai da zuban hawaye daga idanunta,meyasa ya AA ya tsaneta har haka? wani sashi na zuciyanta ya bata amsa da cewa sabida keɗin bakowa bace face mare asali,taya kike tunanin kowama dolene ya ɗaukeki wata aba me muhimmanci,nan da nan hawayenta suka sake gudu suna rige rigen sauka a kumatunta,a hankali ta motsa bakinta tana faɗin.

“Ya Allah ka bayyanamin asalina,Allah kada kasanya na zamo cikin ƴaƴan da aka haifa bata hanyar aure ba,Allah kasa abinda aka rubuta atakaddan da aka tsinceni dashi ya zama gaskiya cewa niɗin ƴar sunnah ce ba shegiyaba.”
Duk wannan maganan afili Nailah ke yinsa,tana nufan wajen wardrobe ɗin kayanta,daga can ƙasa ta janyo wani jaka da take adana ƙananun takaddun skull ɗinta masu muhimmanci,can tsakiyan wani littafi ta janyo wani takadda,kana kallon takaddan xakasan ajiyayyen takaddane da aka jima ana ajiyansa,sai dai koda ta buɗe rubutun da akayi da blue ɗin biro nanan raɗam ajikin takaddan,wanda akayi rubutu da manyan baƙi ɓaro-ɓaro kamar haka,,,,,,

SUNANKI NAILAH MUHAMMAD,ƳA CE DA AKA SAMEKI TA HANYAR AURE BA SHEGIYA BACE ,KODA KIN GIRMA KINYI WAYO KISANI KINADA UBA KAMAN KOWACE ƳAR SUNNAH.’

Iyakan rubutun dake jikin takardan kenan,wanda lokaci bayan lokaci Nailah kan ɗakko tana bitan waɗannan kalmomi tamkar karatun sallah,a duk time ɗin da take karanta takaddan tana jin tsananin zafi acikin zuciyanta,tareda shiga ruɗu da taraddadin anya kuwa da gaske ƴar da aka haifa da ubanta za’a yadda ita akofar orphanage,tun tanada watanni biyu xuwa uku aduniya,kuma Baba me gadi ya tabbatar da cewa macece ta ajiyeta aƙofar gidan marayun ta guda ta barta tana callara ihu amma bata ko waiwayetaba ta tafi tabarta.idan harda gaske ita ɗin ƴar halak ce to menene dalilin kawota a yar a ƙofar gidan marasa galihu?

Ninke takaddan tayi tamaida shi inda yake tareda maida jakan ma’ajiyansa,ta nufi toilet don ɗaurayo face ɗinta,fitowanta yayi dai-dai da shigowan kira daga phone ɗinta hakan yasa ta nufi saman mirrow inda wayanta samfurin Iphone X keta faman ruri,sunan da tayi saving da My man keta yawo bisa screen ɗin wayan yasata saurin ɗauka,tana nufan bed ɗinta ta kishingiɗa tana manne wayan akuninta,daddaɗan muryan Sultan ne ke ratsa kunnuwanta,hakan ya saukar da nutsuwa a zuciyan Nailah ta narke murya tana gaidashi cikeda ladabi.
Duka da haɗuwansu da sultan bai wuce sati biyu ba amma tana jinsa sosai acikin zuciyanta,har mamakin kanta take na yadda yaci nasaran sace xuciyanta alokaci guda,sai dai tana tsoran bashi zuciyanta gaba ɗaya tareda bashi daman zuwa gida kaman yadda yake muradi,sabida tsoran abinda xai iya biyo baya dazaran Sultan ɗin ya gane itaɗin ba’a san cikakken asalinta ba,abinda idan ta tuna harta kejin bata cancanci baiwa kowani namiji zuciyanta ba sabida gudun samuwan heart break daga lokacin da duk wanda zai raɓeta da sunan so ko neman aurenta xai gane batada asali,sai dai duk iya taka tsantsan ɗinta saida Sultan yai nasaran sace zuciyanta,yanzu bashida burin daya wuce ta amince yazo gida asan dashi ita kuma tana tsoro,shiyasa ko Amal batasan da labarin Sultan ba sai Nafeesa kaɗai.Wacce Nailah ke mamakin yadda sam ita rashin sanin cikakken asalinsu bai cika damun Nafeesa ba tunda rayuwansu ta dawo gidan Dady,sabganta takeyi son ranta tana kuma kula duk wani wanda zaizo da tayin soyayyansa,Nafeesa akwai son kula samary donma Momy da Dady ne suka taka mata burki akan cewa ta nutsu har su kammala skul sannan saita fidda wanda take so acikin masu son nata ta turoshi garesu suyi bincike,hakan yasa sai dai tayi tashan soyayyanta awaya da samari daban daban,itako Nailah sam bata ba kowa fuskan da zai iya taranta ma daxancen soyayya ba,duk nacin samarin samaru haka sukayi suka barta,sai ayanzu ne Sultan yayi nasaran sace zuciyanta,daga haɗuwa a Yusad shopping mall ya liƙe mata.

Sunfi mintuna talatin suna waya yauma ɗin dai magiya yake akan tabarsa yazo a gobe lahadi tunda weekend ne,yaganta agidansu domin monday da zaran ya wuce Abuja wajen aiki sai after 2 weeks zai shigo zaria,amma haka Nailah ta lallaɓashi akan yayi haƙuri zata bashi dama amma ba yanzu ba saboda wasu dalilai,koda sukai sallama saita zame ta kwanta tana me lumshe idanunta,tareda jin tausayin kanta na lulluɓeta har batasan sanda hawaye fita daga idanunta suna bin kyakyawan face ɗintaba har saida taji ɗumin hawayen na gangara a kumatunta suna ɗiga a kirjinta,ahaka Nafeesa ta shigo ta samu Nailah,sam Nailah bata ji shigowan Nafeesan ba har saida ta isa gareta tana tambayanta da lafiya tazo ta kwanta tana zubda hawaye,sannan ne Nailah ta buɗe idanunta tana me tashi xaune,takai hannu ta share hawayen kafin ta dubi Nafeesa cikin ido tana faɗin .

“Lafiya lau fa kawai dai ina tausayin kanmune Nafeesa,ina so naga wacece tayi silan zuwana duniya da dalilinta na wofintar dani,da ace bamuyi dace da samun su Momy har suka ɗauke mu suka riƙemu kaman ƴaƴan da suka haifaba,haka xamu ƙare rayuwanmu a gidan marayu? tabbas a yanzu banida burin daya wuce insan cikakken koni wacece?”

Yadda taƙare maganan cikin karyewan murya yai masifan taɓa zuciyan Nafeesan……✍

NAILAH is for sale for just 300 naira.

Ayshat Ɗansabo ce. ✍

DOMIN KARANTA CI GABA DANNA

https://arewabooks.com/book?id=62a4973c772e179ad6e577b4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *