WAYE ANGON CHAPTER 34 BY MARYAM JAFAR KADUNA

Ta ce, “Ni fa in na shiga takura ni suke har dukana take:

Yace, “Ina nan ba mai taba min ke, zo muje.” Ya jata.

Don dole ta yarda ta shiga din har lokacin fuskarta ba ta sauya ba. Ya zauna yana cewa, “Don me za ku matsa nata har a hanata shiga gida?”

Momy ta ce, “Wa ya hanata? Ita ta hana kanta.kan

shegen kafiyarta.”

Imran da yake kishingide ya tashi zaune yana kallonta. Suka hada ido biyu da shi, ta dallo masa harara tare da kauda kai, yayin da ya yi murmushi ya ci gaba da kallonta din.Sharifa ta turbune fuska ta jawo waya tasa earphone a kunnanta kar ta saurari me ake cewa, duk don . Mabarukar.

Ganin yanda ya matsa mata da kallo yasa ta dubi

• Daddyn ta ce, “Zan shiga ciki in kwanta Daddy.” Ya ce, “Ba laifi, jeki ki huta.” Ba ta ce komai ba ta

mike tayi wucewarta tana harararsa.

Momy ta bita da kallo har ta shige dakinta, ta juyo da kallonta gun Daddyn tana cewa, “Sai shegen fadin ran tsiya, ban taba ganin yarinya mai kafiya irinta ba.”

Ya ce, “Za ta bari alamar nasara kenan, zamu sha mamakinta.”

” A nan Imran din ya ce “Ku ku ke damuwa

da haka, ku bar ni da ita ni nasan yanda zamu kare.” Momy ta ce, “Allah ya nuna min wannan ranar.” Rafi’atu ta ce, “Kuma Mabaruka saukin kai ne da ita, abu kadan zai sa ta tsani mutum kuma abu kadan zai sa ta so mutum. Idan ina tambayarta me yasa take son Sulaiman? Sai ta ce min ita har yanzu bata ga dalili ba, ita dai kawai tasan tana sonshi. Na ce ko wani abu nashi ba ya – burgeta? Ta ce ita bata ga komai ba, nace to me yasa ba ta son Imran din? Tayi shiru har saida na taba ta na ce me yasa ta tsane shi?

Ta dube ni ta ce, “Ban sani ba Rafia, ni dai kawai nasan ba na sonshi na tsane shi, haka nan ko muryarsa bana son ji

Na ce, “Ko wani abu da yake miki yasa ki ke jin haushinsa?’ Ta yi shiru, sannan ta ce “Ni dai kawai ba na sonsa. To a haka yasa na ce kamar bata san ma meye son ba, meye kiyayyar ba.

Daddy ya yi dariya ya ce, “Zata bambance idan taje gidansa.” Momy ta ce,, “To ta ya ya kenan zata

bambance da kanta har tasan meye son bayan tasawa kanta tsanar?”

• Rafi’a tayi dariya tana kallon Imran, ta ce “Wannan kuma aikin Imran ne.

shima ya yi dariyar yana mikewa

yace, “Sosai kuwa.”

Momy ta ce, “Ina za ka ne?” Ya ce “Wanka nake so nayi.”Lokacin da Rafi’ar ta shiga dakin Mabarukar tana waya ta hau gadon ta zauna tana sauraronta, da Sulaiman ta fahimta suna waya, rabi duk shagwaba take masa.

“Don Allah Sulaiman kazo ka dauke ni daga nan, wallahi _kokarin raba ni da kai suke, bayan kai ne

Angon.”Daga can ya ce, “Kada ki damu Mabaruka, kowa yasan ni ne aka daurawa aure da ke saboda Babanki shi ya daura min aurenki, kowa kuma yasan uba shi ke da aure ba uwa ba, babu in da uwa ke daura aure, don haka nine Angon babu in da za ki je gidana za ki zo.

Ta lumshe ido tana jin damuwa a ranta.

Ta ce, “Allah yasa Sulaiman, ka dage don Allah kar kayi wasa a raba mu.” Ya ce, “Insha’ Allahu ba mai shiga tsakanin masoya ni da ke.

A haka suka gama wayar, tayi lamo idonta a rufe.

Rafi’atu tasa hannu ta dauke wayar ta dubeta ta ce,

“Mabaruka!” Ta bude idonta tana kallonta tare da cewa Na’am!”Ta ce, “Na kagara ayi ta ta kare a yanke hukunci a ba mai mata matarsa.

Da sauri ta tashi zaune idanuwanta suka yi rau-rau a yanayin tsoro take kallonta, ta ce “Ina tsoro Raff’a, zuciyata ta dade da karyewa kullum cikin zullumi nake, wallahi ina tsoron kar kotu ta yanke hukuncin da zai yi sanadiyyar ajalina.”

Ta dubeta da kyau ta ce, “Me kike nufi kenan?” Ta ce, “Idan har kotu ta tabbatar Imran shi ne angona

zan mutu ne da na rayu da shi.”

• Ta ce, “Mabaruka kin san me ake nufi da mutuwa kuwa?”Ta ce, “Na sani Rafi’a, don tafi min ko kadan bana jin walwala kasancewar da shi ake rigimar nan, koda muryarsa na tsana bare in gan shi har naje gidansa a matsayin matarsa.Ta ce,

, “Shi yasa na kagara a yanke hukunci ke

zuciyarki ta huta mu ma mu huta, ki daina daukar zunubbai.”Ta dubeta da kyau ta ce, “Zunubbai kuma, wadanne kenan?” Ta ce, “Kasancewarki tsakanin daya daga cikinsu kina magana ko ma suna taba jikinki alhalin ke matar aure ce matar wani ce ko Imran ko Sulaiman.

Ta ce, “Har kina tunanin in nayi magana da dayansu ina da zunubi alhalin bani da laifi, ban san waye angon ba?”

Ta ce, “Ban ce dama kina da laifi ba, amman ki taka tsan-tsan har zuwa lokacin da za a tantance waye

angon?”

Tayi shiru hawaye na kokarin zubo mata, tsawon dakiku sannan ta dubi Rafiar cikin mutuwar jiki da kasala bakinta ya yi nauyi kamar zata yi kuka ta ce,

“Dole ne daya daga cikinsu, ko Sulaiman ko Imran dole daya za a ba ko Rafi’a?”

Ta ce tana kallonta “Sosai, daya ke da mata daya ya kama iska.” Hawayen suka zubo ta ce,

“Ya zan yi kenan

idan Imran aka ba?”

“Hakuri mana, ki koya wa kanki sonshi ki hakura da Sulaiman, don samawa kanki lafiya da neman Aljanna.” In ji Rafi’atu.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *