SARAUTAH TAH CE CHAPTER 9 BY NUCEELUV

Sosai yareema yaseer ya matse ta akan fa!adan kirjin nasa Wanda babu komai a jiki sbd cire Masa kayan da tayi, har yanzu bilqees kokawa take akan ta kwace kanta Amma ta kasa, a kasalance yareema yaseer ya Buda baki dakyar yace,
“pls wait I need your help.”
Ya furta Hakan dakyar Yana Jan numfashi a wahale jikinsa na rawa ya sanya hannayen sa duka a cikin gashin bilqees Yana yamutsa shi. Ba karamin tsorata bilqees tayi ba da karfi tace,
“Annur…Annur Dan Allah ka sake ni”
ta furta Hakan tana kokawar kwace kanta sai kuma ta kasa, jiyowa tayi jama’a dayawa a bakin kofar tasu na salati da tafa hannu.

kukan nata ya sashi sakin ta da sauri idonsa a lumshe bilqees na ganin haka itama ta mike da sauri tana Komawa gefe lauwali ya shigo dakin a fusace Yana kaiwa yareema yaseer naushi a fuska a zafafe hade d huci yace,
“Shege Dan iska ba Wani batan tunani Karya kke Wlh.”
A gigice yareema yaseer ya rike fuskar tasa domin naushin aka Kai masa ba zato bare tsammani mikewa yazo yi sai Kuma ya kasa haka ya cije lips Yana Kara kokarin tashi sai kuma hajijiya ta kwashe shi a wajen ya fadi sumamme.
Kasa fitowa wajen bilqees tayi yadda dandazon kauyen nasu suka taru a kofar dakin Kai kace Wani sabon halitta ake jira ya fito a gani.

A can bangaren su inna Zabba kuwa sune Nan suka dinga bi layi-layi gida-gida Suna tseguntawa jama’ar kauyen yau asirin bilqees ya tonu ita da bakon ta an kama su turmi da tabarya.
Jawoshi lauwali yyi ba tausayi bare Imani yareema yaseer gaba1 baya cikin hayyacin sa domin ya Suma a sandare yake Hakan ya bawa lauwali damar jansa tamkar Wani buhu ko kayan Wanki har bakin kofa yyi ta Maza dakyar da nishi da yarfe gumi ya iya turo yareema yaseer waje.
Wasu yara ne kauraye irin yaran mafarautan Nan zagaye a wajen d mutanen gari suka fara jifan yareema yaseer da duwatsu kamar yadda lauwali ya basu umarni. Bilqees dake cikin dakin ta fito a guje hannun ta rike da Rigar sa tana kare shi hawaye na bin kumatun ta tace,
“ku daina jifan sa, ba Abinda yyi fa? Ba Abinda kuke zargi bane…”
Ihu suka sa mata Suna tafi Saude wacce tafi kowa zakewa tace,
“kur’anin Allah idona idon su turmi da tabarya na gansu Suna aikata masha’a Wlh Anji Kunya sumi-sumi da ita Ashe munafuka ce.”
Bilqees ta duka kasa daidai Inda ake ta jifan yareema yaseer kamar Wanda akaje hawan Arfa Ana jifan shedan ta duka daidai kansa tana tarewa jifan nasu hade d sa Masa rigar hawaye na ci gaba da kwarara akan fuskar ta.
“Kai…Kai…ku dakata meye haka?”
Cewar dattijon garin me unguwa Yallabai haruna. Tare da mlm Idi d sauran wasu manyan gari suka karaso wajen harda mahaifin bilqees daya gama juye kwandon jaraba acan gidansa wajen inna habi data kasa fitowa itama.
Dakatawa mutanen garin sukayi yallabai haruna yace,
“wai meke faruwa ne a wajen Nan? Ko Zaku iya yi Mana cikakken bayanin Abinda ake ciki?”
Saude tayi tsalle ta dire gabansu kafin tace, “Allah ya Kara maka yawan rai yallabai…”
A hankali Yareema yaseer ya yatsina fuska hade d cije lips dinsa sai kuma ya Daina motsi.

Saude dake gefen su taci gaba d fadin,
“Na rantse da zatin Allah yallabai Wannan yarinyar bilqees da Wannan bakon a tare muka gansu turmi da tabarya Suna aikata Zina, idan Karya nake ga lauwali da yayata can zabba’u sune shaida.”
Inna Zabba ta gyada Kai da sauri tana yabawa Saude yadda ta fadi abinda suka shirya gayawa mutane domin likawa bilqees din kashin kaji.
Mai gari ya dubi lauwali da ya cika fam saura kadan ya fashe kishi karara a fuskar sa yace,
“Lauwali Abinda yarinyar Nan ta fada gsky ne?”
Lauwali ya gyada Kai domin burinsa a Kori bakon a garin Dan haka yace,
“tabbas turmi da tabarya na gansu d idona Yana lalata min mata.”
“Qalu innalillahi wa’inna ilaihin raji’un”
tso!in suka furta Hakan yyinda mlm Idi ya kasa cewa komai domin ya Gaza fahimtar gsky ne ko a’a? A zuciye Mlm Musa ya kaiwa bilqees data duka kanta Wani wawan rankwashi me karfin tsiya yace,
” ‘yar jakar uba, ni dama nasan haihuwar ki ba Alkhairi bane a gareni uwarki ta cuceni Wlh ba’a taba abin kunya a Wannan kauyen ba sama d Abinda kikayi Kin tozarta ni.”
Zafin rankwashin yasa bilqees ta saki karar azaba tana fashewa da kuka a firgice yareema yaseer ya bude idonsa daga dogon suman daya tafi take kansa ya Sara da karfi d sauri ya dafe wajen yana fadin,
“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un…” hade da cije lips d karfi.
“Kaima jakar ubanka zakaci.”
Mlm Musa ya furta Hakan yana kokarin Kai masa rankwashi yareema yaseer ya rike hannun nasa da sauri Yana binsa da kallon mmki. A nutse yace,
“who are you?” Mlm Musa yace,
“uwarka da ubanka Nima na rama idan ma zagi na kayi Dan iska kawai.”
Ya furta Hakan yana kwace hannun sa ya kasa domin har yanzu yareema yaseer be daina yi Masa kallon mmki ba Kuma fuskar sa a hade. A takaice yace,
“waye Kai?”
“Au tmby ma kke waye ni? Toh Dan uban uban ka nine Nan mahaifin yarinyar Nan daka lalata min ita. Kuma wa billahillazi bazan taba yadda ba saika biyani diyya.”
Sakin hannun nasa yareema yaseer yyi da sauri yana kallon mitsitsitar yarinyar da akace ya lalata ta duke kanta a tsugunne dab da shi ya matsa gefe da sauri hade d dagowa sosai sai kuma yaga jama’a ne dayawa Ashe a wajen, Hakan ya sake jefashi wata duniyar mmkin Yana ja Baya hade da girgiza yace,
“Wacece ita?”
Kowa na wajen mmkin furucin sa ne ya kama shi, yyinda bilqees ta dago Kai d sauri jin Abinda yace. Yareema yaseer ya sake fadin,
“Sannan suwaye ku?”
Ya furta Hakan yana karewa duk jama’ar wajen kallo fuskar sa a hade Dan izuwa yanzu sun fara bashi haushi ga wata kucakar yarinya a gefen shi wai zai afka mata. Toh wai ma a Ina yake…?
“Yanzu ka dubi tsabar kwayar idanun mu kace waye mu? Sannan ka kalleta kace wacece ita?”
Mlm Musa ya furta Hakan a fusace. Lauwali ya matso wajen d sauri yace,
“Sbd ka gama keta mata haddi shiyasa zakace wacece ita?” “Enough… enough pls”
Yareema yaseer ya furta Hakan yana mikewa tsaye ransa a bace yace,
“I don’t know you All. Su waye ku? Ban sanku ba gaba1, inane Nan? A wanne kauyen nake Nan? Me nakeyi Anan? Taya nazo Nan? Dawa nazo Nan? Meya kawo ni Nan?????”
STORY CONTINUES BELOW
Yareema yaseer ya furta Hakan cike d karaji izzar mulki na motsa Masa.
Mikewa zumbur bilqees tayi tana kallon babanta da sauran jama’ar da kowa ya saki baki Yana kallon abin Al’ajabi tace,
“Na fahimci da alama tunanin sa ne ya dawo. Ba bukatar a tunatar Masa baya, tunda har hankalin sa ya dawo karshen mu’amalar mu dashi tazo zai tafi, zaibar kauyen, dama sbd besan kansa ba shiyasa yake zaune….”
Bilqees ta furta Hakan zata tafi zuciyar ta a cunkushe da haushin yadda Annur ya dinga yagewa be Santa ba, duk irin zaman d sukayi a kalla koda tunanin sa ne ya dawo Bata tsammaci ace ya manta wacece ita ba koda zai manta kowa. Binta da kallo yyi kasa2 sai kuma Mlm Idi ya matso wajen da sauri yana kallon bilqees yace,
“dakata bilqees.”
Kamar bazata tsaya ba sai kuma ta tsaya tana dukar d kanta hade d kokarin shanye kukan daya taho mata. Mlm Idi ya dubi Mai gari yace,
“Yallabai idan baka manta ba jiya d safe nayi maka bayanin bakon bilqees ko?”
Maigari yace, “hakane.” Mlm Idi yace,
“yauwa, kamar yadda bilqees tace ba ko shakka bawan ALLAH Nan tunanin sa ne ya dawo, Kai Kuma bawan ALLAH….”
Ya dubi yareema yaseer da manganun su ya fara daure Masa Kai wai tunanin sa? Toh d Ina tunanin nasa yake? Mlm Idi yace,
“Wannan yarinyar da kace baka ganeta ba itace Nan yarinyar data taimaka maka a halin daka Rasa me taimakon ka, itace Nan ta Hana kanta nutsuwa da zama har Saida taga ka samu matsugunni, da ita ka fara haduwa tun bayan daka fada sabuwar rayuwa, rayuwa irinta mantau wacce mutum yakan manta waye shi idan lalurar Hakan ta sameshi, bata sanka ba, Bata San asalin ka ba, batasan waye Kai ba, Amma haka taji ta gani ta Kuma shanye zata tsaya maka. Toh cikin hukuncin ubangiji sai gashi ba’a Wani ja lkci ba ka dawo hayyacin ka…, Inaga Wannan shine takaitaccen bayanin yadda ka kasance Anan wajen, a bangaren mu bamu damu da cewar lalle saika gane waye mu ba, Amma wacce tayi silar kasancewar ka a garin Nan itace Wannan yarinyar.”
Ya nuna bilqees data juya masu baya.
“Kuma Wallahi tallahi be isa yaci bulus ba sannan yace zai tafi, nifa kur’inin Allah ban yadda baida lpy ba dama can kalau yake so yake ya lalume yarinya ya Kara gaba Toh gashi nan burin Dan iskan ya cika.”
Mlm Musa ya furta Hakan da fada2 rungume hannun sa Yareema yaseer yyi yana kallon yadda yake kumfar baki har Saida ya gama, kafin yace,
“Ba Abinda nayi mata.” Ya furta Hakan a takaice.
“Karya ne, Wlh Karya yake so yake ya barwa lauwali tsiya Toh Wlh koda kudi lauwali yafi karfin bilqees yanzu”
Saude ta furta Hakan da sauri tana kokarin Kara cusa tsanar abin a zuciyar Lauwali. Rai a hade yareema yaseer ya dubi lauwali d alama ko saurayin yarinyar ne rai bace yace,
“Kinada tabbacin Abinda kika fada ne ko kuwa kin fadi ra’ayin kanki ne??”
Ya furta Hakan zuciyar sa na zafi, har yanzu kallon bayanta yake yana mmkin shikuwa meya gani a wajenta da har yyi mata fyade kamar yadda sukace?
“Kai ku dakata.”
Mlm Musa ya furta Hakan yana wara hannu yace,
“Duk wata boye2 ko kwana2 Wannan bashi bane. Badai nine uban ‘yar ba? “
Kowa ya gyada Kai, Mlm Musa yace,
“Tohm Madallah. Ni Mlm Musa uban bilqees na yanke shawarar kawai da ita da Wannan bakon a daura masu aure….yanzu basai anjima ba Kuma Subar Mana kauyen gaba1 Dan bazan juri kallon ta bakin cikin ganinta ya kashe ni tun lkci na beyi ba.”

Haba.. mlm Musa, haba.. idan rai ya baci ai hankali ke Nemo shi.”
Cewar maigari daya Kara matsowa Yana dafa mlm Musa, Mal. Musa yace,
“Wlh na gama mgn, yarinyar Nan duk itace silar jawowa komai, d ace tun da farko data ganshi ta kyale shi a daji idan yaso ma ko kura ce ta cinye shi d duk haka Bata faru ba. Amma Wlh ko yaron Nan yabar garin Nan sai yarinyar Nan tabar garin Nan Dan bazan juri hawan jini ba.”
Mal. Idi yace,
“Hannun ka fa baya rubewa ka yanke Mal. Musa”
Mal. Musa yace,
“aha! Sai Kuma me? Ai saidai beyi maka ciwo sosai ba yaseen.”
Bilqees ta juyo a gigice tun bayan da taji furucin mahaifin ta tace,
“ba!a Wlh Karya suke ba Abinda ya hadani dashi.”
“Kanwar tawa ce zatayi maki Karya? Ko kuwa lauwali daya so rufa maki Asiri shine makaryacin???”
Inna Zabba ta matso wajen da sauri tana huci duk ta matsu taga an koresu gaba1 dama burinta kenan Kuma da alama ya kusa cika.
Dukawa tayi daidai saitin kafar baban nata tana zubar da hawaye me cike da kuna da ban tausayi tace,
“Dan Allah ba!a ka saurare ni, kayiwa Allah Kaji Kaina, Dan Allah kada ka yanke hukunci cikin fushi Wallahi summa tallahi sharri akai Mana.”
Janye kafarsa ba!a yyi Yana huci yace,
“Idan baki matsa kusa dani ba billahillazi saina hambare ki, Kai Mlm Idi fara Addu’a daga Nan Subar Mana gari.”
Fashewa da kuka Bilqees tayi hankalin ta a mugun tashe Bata San Kuma Ina zata sa kanta ba. Mal. Idi yace,
“Amma Mal. Musa hukuncin Nan naka beyi tsauri ba kuwa? Aure yanzu sai kace za’ayi kiyama? Dan Allah ka sawa zuciyar ka ruwan sanyi kada a daura auren nan”
Mal. Musa yace,
“Idan bazaka daure ba Wlh zan sa Wani..”
bude baki Mal. Idi yyi zaiyi mgn yareema yaseer ya Tako dab Inda suke Yana kallon su a nutse yace,
“Daura.”
Yyi mgnr yana kallon Mal. Idi. Duba haraban gun Saude take Inda zata hango lauwali Bata ganshi ba baya wajen ko Ina yaje? Bilqees kuwa kasa motsi tayi lkcn da taji yyi mgn cike d umarni. Dan kallon sa Mal. Idi yyi na wasu ‘yan dakiku sai kuma yyi murmushi,
“Toh Alhamdulillah”
ya furta Hakan yana kallon Mal. Musa daya juyar da keya gefe yace,
“Toh Mal Musa za’a daura.”
Mal. Musa ya juyo yana jifan su d kallon banza yace,
“au dama umarnin sa kke jira ka daura? Ai ko bayaso dole Dan uban mutum ma ya yarda..”
Cije lips da karfi yareema yaseer yyi yana kokarin controlling kansa beyi mgn ba ya matsa gefe kawai Yana rungume hannu. A haka mazan duk suka matso kusa aka shimfida babbar taburma a tsakiyar Fili, Mai gari shine Nan walin amarya sai Mal. Idi Walin ango da shaidu dayawa da suke tsaye a wajen aka fara kokarin daura auren bilqees aure mafi Araha wato auren sadaka. Dan Mal. Musa yace sadaka ya bayar da ita domin Bata Kai darajar a biya sadaki ba. Bilqees ta fitar da hawayen bakin cikin tozarci da mahaifin ta yyi mata a Wannan Rana, tozarci mafi Muni,
Ya aura mata mutumin da ko asalin sa ba’a sani ba, be damu da sanin inane asalin sa ba kawai ya kyautar da ita sai kace Marar galihu. Mal. Idi ya dubi yareema yaseer a nutse yace,
“Saidai bawan ALLAH bamu san asalin sunan ka ba.”
Yareema yaseer da har yanzu hannun sa rungume a kirji ya cije kasan lips dinsa a hankali tamkar bayaso yace,

Yaseer.”
YASEER…. BILQEES ta maimaita Hakan a ranta tana tunanin tunda uwarta ta haifeta Bata taba jin irin Wannan sunan ba, Amma yyi yanayi da sunan larabawa.
“Masha ALLAH yaseer bismillah kowa ya zauna.”
Duk sauran Wanda basu zauna ba suka zauna anan aka fara gaddamar da shirin daurin auren bilqees da yareema Yaseer gaban shaidu auren da babu sadaki sbd sadaka ne.
Yareema yaseer ya zuba masu ido dukkansu Yana mmkin irin Wannan daurin aure d be taba gani ba a rayuwar sa. Shi har yanzu ma a duhu yake ya Rasa taya akai ya fado hannun irin Wannan mutanen shi da yake can Adamawa.
Duk iya tunanin sa ya Gaza gano Abu na karshe da zai iya tunawa da yyi Wanda ya jawo bacewar tunanin sa Harya kasance Anan wajen. Wannan Yana daya daga cikin aikin boka Markus koda ace an samu bacin Rana ba fata suke ba yareema yaseer ya dawo hayyacin sa Toh kada ya tuna asalin Abinda ya sameshi Har nannauyan bcci ya dauke shi Wanda da Hakan suka samu damar dauke shi daga cikin masarautar MANARAS.
Mintuna kalilan aka shafa Addu’a aure ya dauri. Daidai lkcn lauwali yazo da sauri yaji Ana fadin an daura aure.
“Dur*n uwr Nan kayyasa Wanne Dan iskan ne ya baku izinin daurawa bilqees aure da Wannan shegen? Daga zagawa ta na kasayar da kashin daya matseni shikenan Zaku yanke muguwar shawarar bashi bilqees?”
Inna Zabba ce tayi caraf ta cafe zancen tace,
“kaga lauwali tuni Mal. Musa ya bashi ita domin shi kansa ya kyamaci Abinda bilqees ta aikata da Wannan Dan iskan bare Kai da kke shirin aure me zaka samu Kuma yanzu? Me Kuma ya rage? Kasan tun yaushe suke badalar su?”
Lauwali yace,
“Toh amma saiku tsaya kuji ra’ayi na ko? Haka kawai kun Wani aura Masa bilqees na rantse da Allah sai an warware auren Nan ko kuwa na tada bori yanzun Nan.”
Nan fa mutane suka fara ja Baya. Yyinda yareema yaseer ke can gefe tsaye Yana kallon ikon Allah besan meyasa ba amma tunda hankalin sa ya dawo yakejin kwata2 mutumin Nan d ake Kira da lauwali beyi Masa ba. Da Sauri inna Zabba tace,
“Indai mace kkeso Toh ga kanwata Nan Saude Wlh ko kyauta kkeso sai a baka”
ta fadi Hakan da sauri tana janyo sauden gabanta.
“Ke dallah ni matsa can me zanyi da Wannan bulaliyar? Abu sototo haka babu gaba ba Baya tsohuwa da ita.”
Baki sake inna Zabba ta ware yyinda Saude tayi wuri2 tana kunshewa a hijab duk kunyar mutanen wajen ta kama ta yadda Duk kallon ya koma kanta. Mal. Musa tunda yaji Abinda lauwali yace yyi azamar barin wajen da sauri tun bayan da inna zabba’u ta dauke Masa hankali ya samu damar guduwa.
“Tashi bilqees.”
Alaramma Idi ya furta Hakan lkcn daya lura lauwali hankalin sa ya karkata gasu inna Zabba, yace,
“Tashi muje ki same sa.”
Mikewa tayi jiki ba kwari tabi bayan Alaramma Idi. Acan Inda yake tsayen ya tsaya, Alaramma Idi ya dubeshi a tsanake yace,
Gaa amanar yarinyar mu Nan Dan Allah ka kula da Amana.”
Girgiza Kai yareema yaseer yyi batare d yyi mgn ba, can lauwali ya hango su ya taho a guje Yana zare Addar sa a daidai lkcn daya karaso yace,
“Saketa.”
Yareema yaseer ya dauke kai beyi mgn ba. Mal. Idi yace,
“me za’a saki?”
Lauwali yace,
“so nake ya warware igiyar auren Nan da aka daura yanzu ko na fille Masa Kai Wallahi.”

Mal. Idi yace,
“haba lauwali taya za’ai kace ya saki bilqees? Wannan ba hurumin ka bane, Kuma yanzu bilqees ta zama matar Wani Dan haka kada kayi yunkurin yin Wani Abu a kansu.”
“Idan naki akwai shegen daya Isa ya hanani?”
Lauwali ya furta Hakan yana hararar Mal. Alaramma Idi yaja baki ya tsuke beyi mgn ba.
Lauwali ya dawo da hankalin sa kan yareema yaseer sai yaga ya watsa Masa Wani irin mugun kallo, take ‘ya’yan cikinsa suka kada dama can dauriyace Amma sbd bilqees ya maze Yana kokarin sake mazewa yace,
“Kai sakar min matata.”
Ko Kara kallon Lauwali beyi ba ya dubi bilqees da Duk ta zama Wani iri yace,
“Muje.”
Yana fadin haka yyi gaba.. da sauri lauwali yasa hannu da nufin juyo da yareema yaseer yace,
“Dalla malam tsaya kayi Abinda na saka”
jiyowar da yareema yaseer zaiyi kenan ya dauke lauwali da Wani irin gigitaccen Mari. Take lauwali yyi taga-taga kamar Zai fadi sai kuma ya cake hannun sa kan kumatun sa har yanzu Yana iya juyo karar sowar da kunnen sa ya dauka sbd mugun Marin da yareema yaseer yyi Masa.
A firgice Bilqees taja Baya, yareema yaseer ya sake dubanta a tsanake yace,
“Muje.”
“Bilqees kuje.”
Mal. Idi ya sake maimaita mata Hakan yana Al’ajabin yau dai an samu fiye da lauwali domin a take ya juya da sauri yana hada hanya idonsa na rufewa.
Bilqees data firgita da Marin ta juyo da hankalin ta kan Mal. Idi dake yi mata mgn tace,
“banyi sallama da mahaifiyata ba.” Bilqees ta fadi Hakan bakinta na rawa.
“SUBHANALLAH anso ayi kuskure Wlh. Mu koma wajenta gsky kuyi sallama. Kai Mal. Yaseer sai ka jira tayi sallama da mahaifiyar ta.”
“Bilqees… bilqees”
Suka jiyo muryar Shema’u kawarta na kiranta a bayanta inna habi ce ke tahowa idonta jike da hawaye, bilqees na ganin su ta nufesu d sauri tana zuwa suka rungume ta hade d fashewa da kuka. Shema’u tace,
“shigowata garin kenan naji mummunan lbri a kanki Ina aje kayana a gida na garzaya gidan ku anan na tarar da inna habi tana ta buga kofa babu kowa an kulleta ta waje, Ashe ba!a ne ya kulleta sbd kada ta fito tasa Masa baki akan hukuncin dazai yanke.”
Kuka Bilqees ta sake fashewa dashi. Yareema yaseer ya juyo a tsanake yana kallon yadda suke koke-koke. Saiya rungume hannun sa kawai Yana kallon su.
“Bawan ALLAH Dan Allah ka saketa banaso nayi nisa da bilqees.”
Da Sauri Mal. Idi yace,
“kada kice haka habiba, Mal. Musa koda ace be aureta ba toh be shirya karbarta idan ta koma ba, gwara ki bita da Addu’a kawai muyi Masa kyakkyawan zato.”
Inna habi ta gyada Kai badan ranta yaso ba, Amma gefen zuciyar ta tana ganin kamar zaiyi hankali da tunani Hakan yasa ta hakura Dan dole.
Shema’u na kuka, inna habi na kuka, bilqees na kuka haka suka juya sauran ‘yan kauye na kallon su suka kama hanyar fita daga garin.
Tafiya suke batare da sunsan Inda zasu nufa ba, bilqees har yanzu hawaye take tana ganin kamar ba lalle ta sake haduwa da mahaifiyar ta ba, bayan haka ko yayunta mata da suke aure a kauyikan makotan su Bata samu sunyi sallama ba, Wannan Abu ba karamin Kona mata zuciya yyi ba ainun. Suna tafe sai kace kurame yareema yaseer kuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *