NAILAH CHAPTER 6 BY Ayshat Ɗansabo lemu

Tunda Hudah ta fito idanun AA Mainasara akanta yake harta ƙariso gareshi,cikin takunta me cikeda yanga wanda yake burge Anwar ɗin.Kashe masa idanu tayi tareda yin fari cikin wani rin salo kafin ta furta.”Sorry Baby na barka atsaye muje ko.”

Da alamu salon nata yayi matuƙar tasiri ga wanda akai dominsa,don har wani lumshe idanu yayi yana shaƙo qamshin turaran da Hudah ta shafa,kafin ya buɗe ido ya sauke su akanta yana jin tarin ƙarin soyayyarta azuciyansa,ji yake ayanzu babu abinda yake da burin mallaka nan kusa irin Hudah,yana buƙatan mace akusa dashi sosai,ganin tayi gaba yasa Anwar binta abaya har zuwa sitting room,wanda already an tanadar masa abinci da abin sha,center table ɗin dake tsayan ɗakin cike yake tab da nau’ikan abincin da Mamie tasa a shirya ma Dakta kaman yadda take kiran Anwar dashi,wanda cikin duka abinci da shan babu wanda ba’a zuba magani ba.

Kujeran 1 seater Anwar ya zauna Hudah tazo ta zauna a hannun kujeran,hakan yasa qamshinta da nasa suka gauraye da juna kafin ta rankwafa kaman zata sumbaci wuyansa take faɗin.
“Baby ya hanya,gaskiya kayi kyau sosai Babyna duk na kosa mu zama abu guda kaifa?”

Yadda tayi magana gab dashi da yadda numfashinta ke sauka bisa dokin wuyansa,ya haifar masa da wani irin kasala da mutuwan jiki,wani baƙon yanayi yake sake tsintan kansa aciki,cikin ƙasan zuciyansa rashin kunyan Hudah da rashin ajinta na damunsa,amma ya rasa meyasa baya iya mata complain,ko yaji haushi da zaran ya kalli kwayan idanunta yake ji gaba ɗaya ta gama hautsina zuciyansa da azalzalalliyan ƙaunarta,lumsassun manyan idanunsa ya sauke akanta murya can ƙasa yake faɗin.

“My Queeny na fiki ƙosawa na ƙagara ki xama mallakina,dama yau so nake mu tattauna wani magana,sai dai inaso ki fahimceni Hudah kada ki zargeni akan abinda xakiji duk da nasan bazaki taɓa jin daɗib …..”

” Shishhhhh! Babyna karka damu insha Allah ma zan fahimceka my Man,yanzu dai bari koɗan lemu kasha saimu tattauna maganan Cwtyna.”

Hudah ta katse Anwar ɗin tana isa inda aka jera abincikan,tana me tsiyayo lemun tatacciyar abarba da aka haɗa da coconut aka markaɗeshi,yasha flavour da ruwan magani ya ɗauki sanyi matsakaici kaman yadda ta karanci Anwar ɗin baya taɓa shan abu me irin mugun sanyinan domin yasan illan hakan ga lafiyan ɗan adam,koda ta iso memakon taba Anwar ɗin cup ɗin a hannunsa,saita sake zama a mazaunin data tashi tana kai cup ɗin bakinsa,shi kuma kaman wani sauna haka ya buɗe baki tana bashi harya shanye tas ta dire cup ɗin tana dubansa cikin ido tareda juya idanunta tana sakin masa wani makirin murmushi da ita kaɗai tasan ma’anansa,tashi ta kumayi don zubo masa favourite food ɗinsa data san da wuya yaƙi cinsa wato white rice and stew sai salad,yana matuƙar son shinkafa da miya da salad arayuwansa,sai dai duk sonsa dashi baya cinsa da dare sai dai a launch kawai,wannan karon data kawo a ƙasan carfet ta aje tana masa inkiya daya sakko,bai wani ja ajiba ya sauka yana zama itama zaman tayi tana tsaresa da idanunta,hannu ya miƙa zai ɗauki spoon Hudah tayi saurin riƙe hannunsa tana faɗin.”Haba Babyna yazan barka ka ciyar da kanka abinci miye anfanina?ai tun yanzu yakamata nafara aikina. “

Anwar dai dubanta kawai yake sam bazai iya fassara me yake ji azuciyansa ba,yadai san sam hakan da Hudah keyi baya birgesa amma meyasa baya iya taka mata birki? shine abinda ya kasa sani don shi yana sha’awan mace me class da kunya sai dai yasan awannan fannin ya faɗo don sam Hudah bata iya riƙe class ɗinta akansa,wani irin mahaukacin so take masa da shi kansa yana mamaki, kaman yadda yake mamakin kansa akan irin yadda yake jinta aransa,har yake ganin tamkar idan ya rasata bazai rayu bane,spoon ɗin data kai bakinsane ya katse tunaninsa ya buɗe bakin yana amsan abincin,tabbas shi kansa ya aminta da iya sarrafa girkin me aikinsu don tuni ya kwana da sanin ba Hudah ke sarrafa duk abinda yakeci agidansu ba,me aikinsu Saratu keyi kuma ta tabbatar mai ko aure sukai me aikice xata dinga sama musu abinda xasuci don ita babu abinda tafi tsana aduniya irin tashiga kitchen da sunan girki inya wuce girka indomie ko soya wainar ƙwai .

Yaci abincin sosai tunda abinda yake tsananin so ne,daɗi kaman Hudah tayi rawa don ganin Mamie batayi asaran kuɗinta na magani ba.

A hankali Anwar ya zayyanewa Hudah halin da yake ciki dasu Dady akan saiya haɗata ita da Nailah ya aura,ga mamakinsa sam Hudah bata nuna zafin kishinta kota tashi hankalinta kaman yadda yayi zato ba,saima lanƙwashe murya da tayi tana sanar dashi ta amince da hakan indai zata mallakesa amatsayin miji,ta kuma shaida masa cewa yayi mata alfarman ta xama itace uwargida ta hanyar fara ɗaura aurenta kafin Nailah,kuma Anwar ɗin ya tabbatar mata da cewa angama,koda zai tafi kaman ko yaushe har wajen mota ta rakosa tana zuba masa kalaman soyayya,ji take tamkar ta rungumesa tai kissing ɗinsa,sai dai tana tsoran ya gane ita ɗin wace tun ayanzu,hakan yasa take haɗiye xalamanta akansa,rafar 200 ya miƙa mata wai tasayi Data ta amsa ba tareda ko godia tayi ba,don ita ba’a sabar mata don anyi mata kyauta tayi godia ba,saida motar Anwar ɗin tafice daga gate ɗin gidan sannan Hudah ta shige cikin gidan aguje tana zumuɗin tabbatarwa da Mamie duk abunda suka shirya ya tafi yadda suke so bakuma ai asaran kuɗin da aka narkawa boka Nuhu ba,don kwalliya ta biya kuɗin sabulu tunda Anwar yaci abincin ya kuma sha lemun,ga turaren data shafa daya gama cika hancinsa sabida yadda ta dinga kusanta kanta dashi.


“Sis Razanah kiyi haƙuri ki rage yawan damuwa acikin zuciyanki,ko don lafiyanki,insha Allah matuƙar tana raye zata bayyana,ke dai kawai addu’an da muka sabayi shi zamu cigaba dayi har Allah ya dubemu,ina ji araina tana raye bata salwanta ba.”

Wata haɗaɗɗiyar macece ke wannan maganan idanunta akan Hajia Razanah da kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa,matar kyakykyawar bafulatana ce da suke matuƙar kama da Hajiya Razanan,daga gani ƴan uwan junane don dai kawai ita tafi Hajiya Razanan farine,Hajia Razanah da yaranta ke kira da Ummah ne ta dubi matar tana faɗin.

“Hindatu bazaki gane bane koda yaushe cikin wasu irin mafarkai nake akanta dana kasa gane inda sukasa gaba,hankalina ya gaza kwanciya Hindu ina son ƴata wallahi ina tsananin ƙaunarta,meyasa suka rabani da ita a lokacin dani da Hammad muke tsananin buƙatanta akusa damu don mu raini abarmu kaman yadda mukeda buri,meyasa suka rabani da ita?”

Razana taƙare maganan tana hawaye xuciyanta na tsananin ƙuna,yayinda Hindu ke bata baki da faɗin.”Kiyi haƙury sister jarabawane ke kuma wannan shine taki jarabawan,nasani duk da kin haifi wasu yaran ɓatan yarinyar nan bazai taɓa barin zuciyanki ba,saboda abune da akayi shi na rashin imani da tausayi araba ƴa da uwa alokacin da dukkaninku kuke da buƙatan jin ɗumin junanku saboda son zuciya,amma ina roƙon kisa dangana kaman yadda kikayi abaya Razanah,hakan shi xai kwantar mana da hankali kinga likita kansa yace lallai dole kicire yawan tunani da damuwa domin zuciyanki na barazanan kamuwa da cuta.Don Allah Razanah kisa dangana aranki babu abinda ya gagari rabbil izzati kuma yana ji yana ganin halin damuwan da kike ciki,kuma shixai kawo miki ɗauki kima godewa Allah daya baki wasu yaran bayan anrabaki da ita.”

“Shikenan Hindatu zanyi ƙoƙarin ganin na cire damuwa,amma kuma kudinga tayani da addu’a wallahi yawan mafarkan da nake da itane ke sani cikin damuwa,sam da bana yawan mafarkinta sai yanzu da shekaru suka miƙa.”

Cewan Umman Nawwara idanunta akan Hindu,kalamai masu daɗi na kwantar da hankali Hindu ke cigaba dashi wajen kwantarwa da ƴar uwanta hankali,har saida taga ta kwantar da hankalinta sosai sun shiga hiran zumunci har suna dariya,kafin tayi mata sallama don wucewa gida sabida time ɗin ɗakko yaranta daga skull yayi xata wuce daga nan gidan Razanah ta ɗaukesu sannan su wuce gida,har bakin baƙar camry ɗin da Hindatu ke hawa Hajia Razanah ta rakata,ta shiga sukai sallama da juna kafin taja motar suna ɗagawa juna hannu,har Hindatun ta fice daga gate ɗin gidan me gadi ya maida gate ɗin ya rufe kafin Razanah ta juya don komawa cikin gida,zuciyanta cikeda ƙaunar mijinta da ƴar uwanta ɗaya tilo data mallaka aduniya,su biyu kawai suka rage mata dake share mata hawaye suke damuwa da damuwanta,batada tamkarsu ahalin yanzu sai yaranta uku da suka xame mata sanyin idaniya suke ɗebe mata kewan first born ɗinta da suka rasa shekaru ashirin da biyu kenan,sunyi nema har sun gaji sun barwa Allah,koda ta shiga cikin gidan kai tsaye part ɗin mijinta Alhaji Muhammad da take kirada Hammad ko Abban Nawwara ta wuce,gyaran gadonsa ta shigayi kafin ta kammala ta nufi toilet nanma ta wanke shi tsaf tasa turare me matuƙar daɗi,bedroom ɗinma ta zuba turare cikin burner ta kunna,tuni sassayan qamshi ya fara mamaye ɗakin,tajawo ƙofar ta nufo falon nanma tasake gyara abinda bai mata ba kafin ta kunna turare ta fice,ganin lokaci yaja yara sun kusa dawowa yasata wucewa kitchen don ganin me Rahane ta shirya amatsayin launch,bubbuɗe warmers ɗin tayi ganin komi yayi yadda take buƙata saita fice zuwa ɗakinta,bata fito ba sai data ji hayaniyan su Shaheed alamun sun dawo kenan,bayan yaran sunci abinci sunyi sallan la’asar ne malamin su dake koya musu karatun islamiya yazo,daga Nawwara har su Shaheed suka kwashi littafansu suka fice,ita kuma Ummah saita nufi kitchen don tanadarwa Abbansu abinda zaici idan ya dawo daga office.


Monday tushen aiki yau tun bayan da Nailah tai sallan asuba sam bata koma ba don jitayi batada buƙatan hakan,koda tagama karatunta na qur’ani da azkar saita janyo jakanta da take fita dashi office ta zuba abinda xata buƙata,ƙarfe 6:30am ta shige wanka tana fitowa ta tada Nafeesa itama ta shiga wankan don ita batama tashiba saboda tana fashin sallah,agaggauce ta shirya cikin kayansu na ƴan bautar ƙasa dake amsan jikinta sosai,tareda yi mata kyau ƙaramin farin brazier hijab ta saka daya sauka ya rufe saman kirjinta gaba ɗaya zuwa guiwan hannunta,batada buƙatan fesa wani turare banda roll on ɗin datayi anfani dashi,sabida yadda qamshin mayen turaren da suke turare kaya dashi ya kame dukkanin kayanta,dikansu suna using ɗinsa tun daga chadi ake turowa Momy take siya,kowacce kuma da irin choice ɗinta shiyasa kowacce zakaji da kalan sassayan qamshin da sitturunta keyi,fita tayi tabar Nafeesa dake gaban madubi tana kwalliya sosai a face kaman me shirin zuwa gidan biki,ita ko Nailah daga powder sai man leɓe da kwalli ta saka,illah baƙin gashin giranta data gyara da brush amma tayi kyau don abinka game kyan dama tun farko,kitchen ta nufa don yin saurin samar musu abinda zasu ci,don su Iya da Rabi basa shigowa part ɗin don yin abincin breakfast sai 7:30am zuwa 8 haka, shiyasa duk me fita da wuri shike tashi ya nemi abinda xaici ba ƴan matanba ba mazan ba,kanta tsaye ta sanya kai cikin kitchen ɗin ba tareda tunanin zata iske kowaba,sai dai tuni qamshin mayen turarensa ya bigi hancinta,hakan yasata saurin duban cikin ƙaton kitchen ɗin nasu gabanta na faɗuwa,zaune yake cikin ɗaya daga cikin kujeru shida dake zagaye da ƙaton island ɗin kitchen ɗin yana shan tea, plate ne da yayi tosting bread ya soya egg daga gabansa,cin abincinsa yake hankalinsa kwance,ya gama haɗewa cikin black suits yar cikin long sleeve ɗin white ne sai wandon da falmaran ɗin suka zama black,hakan ya haska farin fatansa ya ɗaura farin lab coat ɗinsu na likitoci dake masifan yi masa kyau,don daga nan direct idan ya isa Abuja hospital zai wuce,Nailah tayi saurin ɗauke idanunta daga kansa,Allah ma yaso bai ɗago don ganin waye yashigo kitchnen ɗinba,sai dai abinda Nailah bata saniba shine tuni Doctor AA Mainasara ya gama haddace qamshin kowacce acikinsu,hakan yasa tunda qamshinta ya ziyarcesa ya sanar dashi wacce ta shigo kitchen ɗin,store ta nufa kanta tsaye ta ɗebo indomie ƙanana guda 2,ta fito zuciyanta sai faman bugu yake,dole saita wuce ta gaban island ɗin dake tsakiyan kitchen ɗin xata isa inda gas yake,hakan yasa dole taja burki don gaida yayan nasu kafin tayi abinda ya shigo da ita kitchen ɗin.

“Ya Anwar gud morning.”

Nailah ta furta cikin sassanyar muryanta,ko kaɗan kuma batayi gigin kallonsa ba bare taga uban hararan daya jeho mata,kaman ana jan idanunsa da lantarki kuma ya samu kansa da ƙare mata kallon cikin shigan kayan NYSC ɗin dake jikinta,tabbas ko shine sarkin kushe bai isa yace kayan basuyi mata kyauba,shi kansa ya amince yarinyar nada baiwan kyau da diri sai dai tsananta da tsananin ƙyamar rashin cikakken asalinta kesa sam baya son ma ganinta.Ɗauke idanunsa yayi akanta alokacin da take yin gaba don jin bashida alaman amsa gaisuwan tata,saima doguwar tsakin da taji yaja yana me sauka daga saman island ɗin ya fice daga kitchen baki ɗaya bayan ya dire cup ɗin dake hannunsa,sam Nailah bata damu da yadda yayinba domin tasawa ranta bazata dinga saka abinda yake mata araiba,don ta kula bazai taɓa dainawa ba ita karan kantane ya tsana,kuma tasani ayanzu ne ma xataga xallan tsana da tsangwama daga garesa,tunda ake shirin ƙaƙaba masa ita amatsayin abokiyan rayuwa,tausayin kanta kawaine ya lulluɓeta haka ta shiga sarrafa indomie ɗin,inda tai wainar indomie ɗin da egg da siden,wanda ta yanka vegetables sosai tayi anfani da mixed spices,tuni kitchen ya haɗe da qamshi don Nailah indai iya girkine to babu tamkarta cikinsu Amal,shiyasa take burge Momy don itama gwanace xan iya cewama abubuwa da yawa awajen Momy ta koya,lokacin da Momyn ke tashen shiga kitchen tayi aiki da kanta ba yanzu da Dady yace ya hakura tabar masu aiki su Iya da Rabi su dingayi ba domin daɗewa abauta ƴanci yanzu lokacine da zata huta.

Cup biyu Nailah ta haɗa musu tea ita da Nafeesa ta jera komi bisa tray ta fice,zuwa ɗakinsu tuni Nafeesa ta gama kintsawa shigowan Nailah ɗauke da tray yasata faɗin.

“Yauwa ƴan matan Momy sannu da aiki.”

Nailah ta harareta tana aje tray ɗin aƙasan center carfet take faɗin ” Oya ni kiyi maza kixo muci koma fita da wuri banso muna yin late wannan fitinannan mutumin na mana mita.”

Nafeesa tayi dariya tana zama suka fara cin abincin,koda suka kammala Nafeesa ta suri tray ɗin ta fice dashi zuwa kitchen yayinda Nailah ta saɓa jakanta tana me ɗaura hulanta saman kanta.Ta fito tana jiran Nafeesa itama ta fito su wuce,basa samun gaisawa da kowa domin duk basa tashi da wuri sai around 9am Momy da Dady suke tashi Amal ko saita kai 10am,don tuni ita tagama service ɗinta tun last year,babu inda take zuwa yanzu sai zaman gida.

Bilya driver shike kaisu ya dawo dasu idan sun tashi office,hakan yasa suna fita suka sameshi har yafito da mota,Nafeesa ta shiga gaba Nailah na baya suka fice daga gidan Babah megadi na musu asauka lafiya …✍

NAILAH is for sale game buƙata xaki tura 300 ta wannan account ɗin. 0504192664 Aisha Ibrahim Ɗansabo GTbank.

Ko kuturo katin airtel na 300 ta wannan line ɗin 07087809778.

Shaidan biyanku tanan 08167768704.

Esha Ɗansabo ce✍

DANNA DOMIN CI GABA

https://arewabooks.com/book?id=62a4973c772e179ad6e577b4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *