Kula da kaya
New book chapter1
Nayi nayi in dasa sonsa cikim raina amman na kasa a kullum tunanina shine ta ina zan fara son yaya sadiq a zuciyata 
Wlh asma,u in ina kaunar sadiq,ina kaunar mutuwata 
Wlh sautin muryarsa banason Naji,
,amman hakan baxaisa naqibin umarnin iyayena ba 
Zan auri yaya sadiq ne kawai sbd bin umarninsu
Kici gaba da tayani da addu,a duk sanda kikayi sallah 
Ta kamo hannun qanwar tata asma,u tayi qarfin halim goge hawayen dake qoqarin zubowa daga idanunta tace
Khadija ki daina wannan tunanin sadiq mijin aure ne sadiq namiji ne kyakkyawa mai kyan hali 
Don Allah kisa sonsa a zuciyarki tsakani da allah bason iyaye ba
Ta zura mata ido ki daure khadija duk wannan dakewar da kikaga yanayi gaba daya dainawa zaiyi 
MiqewA tsaye tayi tana fadin ni xan wuce gida yanzu dan baxan iya daukar wannan laccar ba 
Miqewa asma,u tayi itama tana cewa mu tafi tare idan kika tafi ni kuma zaman me zanyi
Amman dan jirani na gama chin donut dinnan 
KHadija ta miqe tana fadin bazan tilasta miki bina ba don Allah ki zauna kada ace kin bini don naga ansa mana ido 
Sannan ga wannan dan rainin hankalin shima wai sona yakeyi 
Wanene fa asma,u ta tambaya 
Khalid mana 
Haba ai shima yasan ruba ba sa,an kwando bane ta mike tare da fadin muje kinji 
Suna tafe suna dan tattaunawa game da abubuwan dake faruwa sai sukaji qarar horn
Suna juyawa sukayi tozali da sadiq
Innalillahi khadija ta fada a ranta sannan ta qara sauri 
Cikin hanzari yasha gabansu ya zuge glass
Babyna shigo na kaiki gida 
Tayi masa wani irin kallo gamida fadin ka nemi babynka a can ta juya asma,u ta riqo hannunta 
Haba khadija meyé Haka kuma ? 
Sadiq ya bude motar ya fito yana fadin zaki shiga ko saina kwakkwada miki mari,,
Don kinga ina wasa dake ko ? 
Tayi masa kallon uku kwabo ya kwance belt 
Da taga zai tara mata mutane saita ruqo asma,u tana fadin zomu shiga.  
Asma,u dake tsaye tana kallon ikon Allah ta bita suka shiga bayan motar
Yayi kwafa ya shiga ya zauna 
Har zai tada motar ya juyo
Yace ban yarda in zama driver ba ki dawo gaba komu kwana anan ya fada yana kallon khadija
Shiru tayi kamar bataji abinda yake cewa ba 
Yace asma,u dawo gaba kinji 
Bayan asma,u ta zauna saiya ja motar bai zame ko inaba sai,a mr biggs ya fito yace 
Nasan zaku buqaci abinci don da gani bakuyi lunch ba anyway ina zuwa
Bai buqaci amsarsuba ya wuce 
Khadija dai kallonsa kawai take ni na kasa gane kaina idan wannan kwarzababben mutumin yana magana bana iya bashi amsa ta fada azuciyarta amman a fili saita ja dogon tsaki 
Ana cikin haka sai gashi da ledoji niqi niqi a hannu 
Sorry na bata muku lokaci ko? Asmau tace noproblem
Ya kunna motar sai unguwar sarki yayi horn mai gadi ya bude musu gate 
Yayi parking din motar ya fito gamida zagayawa bangaren da khadija take zai bude mata motar 
Yana fadin na yarda zanzama bawanki domin nasan zan fanshe watarana 
Kawai fita tayi ba tare da tace uffan ba asmau ce niki niki da kayan da sadiq ya sayo musu zubesu tayi a kan kapet din dakinsu tana fadin kai gaskia wlh saina watsa ruwa kafin na moru 
Khadija tace asma,u wannan wanne irin maye ne duk indanake yana biye dani 
Wlh na rasamai yasa duk abinda yakeyi bana iya ce dashi komai 
Asma u tace qila kodankina ganin yayankine ko?
Khadija taja dogon tsaki tace ya gama wahalarsa donni bazan yarda a auramin shiba 
Kuma wlh inma lallai saiya sameni a matsayin matarsa tofa lallai saiya gane kuskuren da yayi na aure na asma,u tace kedaiki dinga fatan Allah ya zaba miki abinda yafi xama alkhairi a tare dake 
Ta shige bayi khadija kuma dakin mahaifiyarta ta nufa tana kiranta 
Sallah ta sameta tanayi saita nemi wuri ta zauna zaman jiranta ta idar 
Bayan ummin ta kammala tayi addu,oi suka shafa tare 
Mahaifiyar tata ta dubeta tana cewa ummi wannan kira haka kamar qaramar yarinya
Ta zumburi baki tana fadin ummi nidai ba qaramar yarinya bace shekaruna. Nawa yanzu?