MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 5

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 5

Tace da asirin Yakolo zai ci malam da tuni babu sauran Burbushinsa a duniya, domin tana wata iein matacciyar rayuwa ne da babu imani da Allah a cikinta. Da mai ganewa ce da ta gane don ba na mantawa akwai shekarun da aka yi data dinga daga kadarorinta tana saidawa tana bin ‘yan tsubbu. Da malam ya gane hakan, sai ya ware wasu kudi kullum yake bamu, idan yaje ya bata sai yace ga wannan nasan ba za a rasa zagayawa ba, amma don Allah a daina saida kayan jere ai sai . dakin ya yi mini fadi. ‘
Ni da Yaya Kaltum ba ki ga abin arzikin da muka tara ba. don da su ma na sayi gidajen da ake mini haya da su, ita kuwa da Basma ko tsinke ba su ajiye ba suka dinga bin malamai har zuwa sanda ya gaji ya daina bai wa kowa.
Ki sani Allah Ya tsare shi da yawan addu’o’insa, naasan babu wani abu da zai faru da shi, sai dai kedin tunda nasan su ba sa daukar komai da sauki, don haka sai ki dage da addu’a kamar yadda kika saba. Zan kuma tadda malam din akan maganar Muntari, amma bazan nuna masa wannan Ba, da kansa zakiga ya gano, kada kuma ki gayawa kowa, ki kwantar da hankalinki kinji k0”.
Ta daga kai alamar, “Toh”. Sannan ta tashi ta koma dakinta taji dan sanyi a ranta da kalaman
mahaifiyar tata. Ita kam Hajja Iyami daga nan dakin hajja
Kaltum ta wuce ta roqi alfarma tayi mata jagora gurin Malam din ta_ taya ta rokon arziki, ba ta yi musu ba suka wuce tare.
Yana zaune yana kallon tasoshin Larabawa hannunsa da carbi yana lazimi, suka shiga da sallama ya ajiye carbin yana amsawa, fuskarsa a sake yake fadin
“Tunda naga uwargida da amarya sun hadu kai nasan cutata aka zo tabbas” .
Suka zauna Hajja Kaltum tace“Haba malam babu wani ”batun cuta sai gaskiya, muna fatan zaka fahimci =abin da ke tafe damu”.
Ya. gyara zama ya kalle su da cikakkiyar nutsuwa, yace ina jinku”.
Hajja Iyami ta gyara murya, sannan tace, “Malam akan maganar Muntari ne, kasan Hajja Yakolo ta jima tana mitar ana mata rashin adalci a gidan ,nan, yanzu kuma Allah kadai yasan yadda zata dauki wannan maganar. Shine nake ganin mezai hana ka hakura ka baiwa Muntarin wata daga cikin‘ yan dakima a huta?”
Hajja Kaltum ta amshe jiya zan wuce Yakolo kamar zata bangajeni tana ta surutai kalakala, wai tasan n’ice na. zuga ka, ban dai kulata ba.
don haka ka duba maganar Iyami ayi mata abin da akeso a sami lafiya”.
Ya qankance ido cike da fushi yace “Saboda ita ce wa? Wani abu da. baku sani ba, yadda kuke tsoro da shakkar Yakolo ko kusa ni bana yi, shin wai me kuka dauki yakolo ne, eyeh? To ku tsaya ku ji, wallahi idan har’ Yakolo ba zata bi abin da nake so ba ita ma bara! isa na bi abin da take so ba, domin ni ke aurenta ba. ita ce ke aurena ba.
Ya kuma dace a yau nayi muku bayanin dalilin zuwan Hajiya Mariya gidan nan tazo ne akan matsalar Muntari da iyalinshi, ba zuwa kuke ba ita ma ba zuwa take ba, shi ya sanya” ba ku san halin da suke ciki ba. Ni kaina sai a waya muke magana da ita, sai dai idan na shiga Kano na kan dan biya mu , gaggaisa a tsaitsaye, sanda ta zo ta sanar dani duk halin da ake ciki, don haka nayi niyyar aura masa mace mai nagarta, wacce nake fatan ta zama fitila a rayuwarsa. Ta ya ya zan aura masa ‘ya’yan Yakolo da ba su da maraba da irin tarbiyyar matar tashi? Ku sani Yakolo babu irin abin da ba tayi akan maganar nan ba, dazu har abu ta sanya ‘ya’yanta suka binne min asiri a qofar dakina wai ita a tunaninta sai ta tursasani. Ta kasa gane ta kashe
rayuwarta data ‘ya’yanta, na zuba mata idanu,
don nasan dole wata rana duniya zata zame mata makaranta. K0 inn raye ko qasa ta rufe idanuna zata gane abinsa nake nusar da ita.
, Kuma wallahi na shirya daukar-mummunan mataki a kanta wannan karon muddin ta daure“ ma yaran nan gindi suka~bani kunya. Ku kyale ta kawai, kuma daina sanyata a lissafinku idan Allah Ya had‘aka zama da mutum ne babu yadda zakayi ‘dashi sai addu‘a”.
Dole haka suka haqura da buqatarsu domin yafisu hujja, sai dai suna gudun bala’in Yakolo, don ma tana shakkar malam da ‘ya’yan Hajja Kaltum dinda iskancin da zata dinga yi a gidan sai ‘ Allah ~ ~. Sanda suka zo fita sai suka ci karo da Hajj Yakolo a bakin qofa a tsaye tana ta cika tana batsewa, da alama ta taji duk abin da suke fadi, don sanda suka nufo sashin nasa Basma ta gansu ta falla‘ da gudu ta gaya. mata shibe tazo ta labe tana jin komai.
Ba su kallce taba suka wuce domin dai halinta sai dai’su bai wa wani labari.
Ta yi tsaki. tarceda cewa. “Ai munafurci dodo ne mai shi yake ci, kuma a gidan nan bana neman‘ gindin zama gurin kowa da duwawuna nake Zaune‘ ehe! Kuma mu zuba da mutum dan halak ka fasa Ba su kulata ba suka wuce abinsu, don sun san ‘ san hali‘ babu fashi, wannan ya sake qularda ita, tasanya hannu a baka cike da takaici tana cizon yatsa, duk dumbin kudin data kashe sun tashi a banza, amma tabbas fa ba zata haqura ba sai taga inda ya turema buzu nadi

YA DACE MUJI ‘ SU WAYE  WADANNAN IYALAN

Malam zakariya  tsohon’ malami’ ne  mai matuqar tarihin malunta a garin Barno, a cikin matansa ne ya auro Hajiya Fatima daga Kanon dabo wacce‘ itace ta haifi Malam Abdullahi mahaifiin Abbagana, shima. kansa. Malam Abdullahi ya taso da irin gadon gidansu na malumtar saidai ya dan hada da karatun zamani hakan yasa koda ya sami dansa tilo Abbagana wanda yaci sunan mahaifinsa, yabashi ilimin-zamani da dana addini saidai na addinin yafi yawa don har qasar Misra abbagana-ya-tafi neman ilimi kasancewa tun yana dan shekara goma ‘shabiyar ya sauke qur,’ani. dom! haka sauran littafan addini sai suka zame masa masu sauqi.
Ya jima‘ a qasar Misra yana karatu har ya fara koyarwa a can yana kuma aiki da wani
kamfanin hada takalma.
A can Misra suka hadu da Malam Abbas Wanda ya kasance mahaifi Muntari, da farko abota ce ta hada su, sai daga baya suka gano suna da ‘ alaqa ta wajen kakanninsu, domin kakar Abbagana da kakan Malam Abbas abokan wasa ne abotar tasu ta yi girma har ya zamana k0 ina suna tare, sai suka fara turo kaya Nigeria ana saida musu suna sarar  wasu‘kayan suna kaiwa can, ga kuma koyarwa da suke yi, wannan ya sanya basu yi sha’awar dawowa ba, sai da Kyar aka yakito su, shi daman Abbagana yana da baiko da Kaltum, don haka yana dawowa aka sha shagalin _.biki, su Abbas su ne manyan abokan ango.
Allah Ya albarkaci Kaltun da haihuwa a shekara guda daya da auran nasu, inda aka samu
~Abdullahi, .wato Bulama, a lokacin harkar
kasuwancinsu da maluntarsu ta yi nisa, don kowa sai da ya bude makarantar kansa ta haddar qur,’ani ‘. a garinsu, banda koyarwa da suke a makarantun gwamnati.
Shi ma Abbas ya yi aure da matarsa Binta a nan garinsu kano suka tare, amma suna yawan ziyartar juna, shi kam Abbagana mai son ‘ya’ya k0 don shi kadai iyayensa keda shi har suka koma ga
Allah, don haka kullum yake fadin sai ya yi mata
hudu. Haihuwar Kaltum shida duk ‘yan maza ya fara neman auren Yakolo wacce ta yi masa lambu lambu.
Farkon auran nasu bai gano halinta ba saboda yadda ta dinga kulla masa makirci da uwarr ‘ya’yansa har ma da ‘ya’yan, Kaltum ta shiga matsala a wannan lokacin, ta dinga addu’a tana gayawa Allah har Allah ya tonawa Yakolo asiri, tun daga wannan lokacin ya ganota komai zata yi a banza, tsawon shekaru biyu tana gidan ko Batan wata ba ta taba yi. ba, wannan ya daga mata hankali ta fara bin bokaye da malaman tsubbu akan sai ta haihun dole. Cikin shekararta ta goma ta samu ciki, amma ita a ganinta asirinta ne ya bata, domin ance mata wai kishiyarta. ce ta toshe mata bakin mahaifa. Sanda cikin ya isa haihuwa ta haifi mace, ba ta so hakan ba, ta so ace ita ma namiji ta haifa saboda sanya rai da gado, shi’ kuwa maigidan ya yi murna don anyi masa haihuwa har takwas duk maza, don haka ya dinga dokin. macen, wannan ya dan wankewa Yakolo rai.
_ Sanda ta kuma samun wani cikin ta dinga bin bokaye akan ta hafi namiji, nan ma Allah Ya nuna mata Shi ke bayarwa, ta kuma haifar mace har sau biyu, dole ta haqura da bin bokayen. Sai dai kwatsam sai ga maganar auran Basma da
Abbagana, da shi kansa Abbas Wanda ya yi aure na biyu ya auri Mariya, kusan tare suka yi auran da na Yakolo amma ita haihuwa tayi tuni danta Muntari ya yi wayo, shi kam daga kanta bai qara ba.,
Farkon zuwan Basma gidan ta shiga da izza da gatsali da gadara don diyar mai kudi ce don haka suka fara gwabzawa da Yakolo, ba sa shan inuwa daya, don haka Basma ta so Shigewa Hajja Kaltum amma da ta kula da yanayin rawar kan yarinyar taqi sakar mata fuska, sai dai daga sanda ‘ ta yi shekara a gidan ba ta yi ko batan wata ba, hankalinta ita ma ya fara tashi, ta dinga shige-shige amma a banza har ta kwashi shekaru biyar a gidan.
Da farko Abbagana ya dauki son duniya da kulawa ya dora akan diyoyin ‘Yakolo mata, komai zai shigo musu, duk fitar da zai yi sai ya siyo musu gwala-gwalai, ga kayan kwalliya kala-kala, amma ganin tana tabara yaran da .nuna musu kishin yayyensu maza qarara take sanyawa su yi musu rashin kunya, hakan ya sanya ya fara daure musu fuska, don yana da zafi bai son “ya yansa su lalace, wannan ya sanya Yakolo ta fara mita wai an tsani ‘ya ’yanta don duk mata ne.
Gwala-gwalan da yakesai musu ma duk sai Ya daina, don ya kula kasuwarsu takeci tana bin _ malamai da kudin
A sannan ne suka fara hada kai da Yakolo tana gayawa Basma sai ta mike tsaye, don ita kanta sai da ta yi shckaru goma a gidan anayi mata gori, k0 da ta samu ciki ya lalace, kuma tasan Hajja Kaltum ce don haka idan ba ta tashi tsaye ba zata zama ‘yar kallo a gidan, don haka ta fara rakata gurin malamai. ,
Saidai abanza amma suka gaza hakuri,har maigidan ya kula da halin da suka shiga, ya fara yi musu nasiha, amma sai suke ganin kawai Hajja Kaltum ce ta mallake shi, ga yadda yaje yiwa ‘ya’yanta hidima, manyan suna waje karatu daga wadanda suke qasar Sudan, sai masu Misra, sai masu Jami’atul‘ Madina, karatu suke yi sosai, don kusan shakaru uku a jere daga gidansa ake fidda gwanin shekara, wann‘an ma ya tsayawa Yakolo da Basma a ransu saboda kyauta ya dinga yi musu ta bajinta.
Wata musabaqar karatun qur,’ani da aka yi yana cikin alkalan musabakar, Allah Ya hada shi da Iyami, wacce ta zo ta daya ga jaharsu ta Maiduguri, bai yi wasa ba ya nufi gurin iyayenta da ncman aurcnta. Babu mutumin da zaiqi yarda ya hada zuri’a da Abbagana domin Allah Ya ba shi ilimi, ga dukiya ga kuma hali na gari. Ita kanta Iyamin duk da a haife ya haife ta ba ta wani jaba ta ji tana sonshi aka sha biki
Ina wuta Yakolo da Basma su jefa Iyami, musamman da aka kawota suka ganta ‘yar yarinyarda  ta fisu komai. Sai dai ba basu isa su cutar da ita ba. don tuni ya gina qaton gidanshi kowacce da sashinta da na ‘ya’yanta babu ruwan wata da wata, saBanin tsohon gidan nasu da dakunan nasu suke a jere, don haka sai ka so zaka ga wani ma. Hakanne ya yi musu katanga da Iyami, amma duk da haka suna yin duk wani abu da zasu quntata mata, sai dai basa gabanta.
Kuma cikin ikon Allah watan da aka kawota ta sami ciki da yake tana da laulayi kowa sai da ya sani.
A wannan. karon Basma tafi kowa shiga damuwa ganin an kawo wata a bayanta zata haihu ita ba ta ajiye ko kwai ba, sun yi duk yadda zasuyi amma sai da Allah Ya kawo Falmata wacce ta fad‘o a hannun Hajja Kaltum, domin tana fara ciwon ta sanya masu hidimta mata suka sanarwa da Haija Kaitum domin ta taimaka mata domin kuwa  ita ce mace ta gari a gidan.
Falmata ta taso yarinya mai kyau da haquri, ga shiga zuci ga ladabi da biyayya, don haka yayyenta maza ke bala’in sonta, duk inda suka je sai sun dawo mata da tsaraba niqi-niki. sabanin ‘ya’yan Yakolo da kowa ya tsana saboda rashin kunya da fadin rai. Tun suna qanana suke kyarar
(domin ci gaba da karanta littafanmu masu dan karan dadi dannan wannan koren ruburun👇)
https://web.facebook.com/groups/398700057206552/672674679809087/      
masu aikin gidan nasu.
Tun daga kan Falmata ba _ a cika shekara biyu ba sai Iyami ta haihu, kuma duk maza take haifa, abin yake yiwa Yakolo da Basma ciwo ke nan, don haihuwar Yakolo bakwai, amma duk mata, sai ta ke ganin ya ya wata zatazo a banza ace tana ta haifar maza!!!!!!  Allah dai Shi ke badawa, ita kam Basma ta nemi duk wani asiri a banza daga Karshe ta koma ganin likitoci suka tabbatar mata da lafiyarta qalau, illa dai haihuwace da ba a yiwa Allah dole, sai lokacin da Ya ga dama zai bada.
Kasancewar ‘yan uwan Falmata duk maza ne ya sanya ha tajin dadin wasa dasu, sai ta tafi dakin Yakolo gurin ‘yan uwan nata, amma da kuka zata koma sashinsu, Zahra,u ce kusan sa’arta, ko taje bangaren nasu itace mai dan janta a jiki suyi wasa  amman daga qarshe saida mahaifiyar tata ta hanata, ita kuwa falmata azabace ta sanyata daina shiga sashin yakolon don banda Allah yayi da kwananta a gaba da tuni sun kasheta
don har shinkafar bera sun taba zuba mata cikin abinci aka kaita asibiti ranga ranga  aka sakota da kyar wannan ya sanya mahaifiyarta ta dinga kulleta a daki ,
Shi kuwa Malam Abbagana cewa ya yi, duk wacce ta aikata wannab aikin bai yafe mata ba,
Allah Ya isa tsakan’insa da ita.
K0 a jikinsu domin ba su san darajar kansu ba. balle har su san munin Allah Ya isan da aka yi musu ba, ‘tun tana da shekaru bakwai ta fara ciyo gasar karatun izifi biyu a islamiyyarsu, wannan ya sanya Babanta sonta matuka, domin yana bakin. cikin daukacin ‘ya’yan Yakolo su baga bokon ba, balle a islamiyyar, sai shegen girman kan tsiya da masifa, nan suka fiauki.
Yagana ce kawarta a cikin layinsu, tun daga islamiyya har zuwa wasan yara na unguwa tare suk‘e yi, sai dai idan ta shigo gidan suka ci karo da Yakura k0 Zubaida k0 Salima sai sun daketa, wannan ya sanya ta daina shiga gidan, sai dai ita Falmata taje gidansu.
‘ Abin da yake bai wa Hajja-Yakolo da Hajja Basma haushi bai wuce ganin Hajja Iyami da tazo a bayansu tana ta haihuwa ba, suka dinga yin duk yadda zasu iya amma a banza sai don saida ta yi goma sha ‘biyu, Falmata’ ta farko, sai qannenta maza tara, sannan aka haifi mata biyu, wannan abu yana yi musu ciwo, don dai babu yadda za su yi ne da yin Allah, da zasu gane da sun daina asiri tunda baiyi tasirin komai ba.
Hidimar biki kam an farata da gaske, cikin amaren nan guda biyar Zahra ce kadai mai murna, domin itace aka bata wanda take so, duk da mahaifiyarta taso hanawa amma babu yadda zata yi dole ta hakura ta kyale ta.
Falmata kam ba zaka gane bacin ranta ba, domin tana ta walwalarta, sai dai duk wanda ya santa ya san ta rame matuqa, sai qashin wuya, daman ita aba ba auki ba.
Saura kwana biyar daurin aure Malam Abbagana ya kirawo wayar Muntari ya ce, lallai yazo ranar juma’a yana son ganinsa. Yana kuma son ya yi sallar juma’ a a Maiduguri, don haka ya hayo jirgi cike da damuwa muntari yake tambayar lafiya?
Ya cc masa kalau, ya dai tabbatar yazo din. Sun rabu akan zai zo ranar juma’a aka ci gaba da hidima.
Tabbas da ace auren sobe da ‘ya’yan nan sunfi kowa murna, domin mahaifinsu ya yi musu kaya na gani na fada daga Dubai ya yi odar komi. hatta kayan sanyawa sai da ya yiwa kowacce saitin jakunkuna biyu-biyu, don shi sadaki kawai zai amsa. duk wata bidi’a yace idan matarka taje gidanka ka yi mata.
Yakura kam mijinta-mai arziqi ne Alhaji Isa
mai sumunti, sai dai matansa biyu ‘yan bala’i ne kamar wuta, tunda aka fara maganar auran suke rigima, ga shi da zagada-zagadan‘ ya’ ya, shi kam murna yake yi, domin yasan “ya yan Malam Abbagana babu na banza, duk kyawawa ne auren . kyau zai yi
Anje anyi jere a manyan dakunanta guda “uku“. sai dai ‘yan jeran kansu sun san an kawata gidan dai-dai ita.
Zubaida kam nata babban malami ne don haka gidansa gida nena tarbiyya da tsantsani, dole ta ajiye duk wannan gayun da iya yin nata na Turawa, domin gidansa ba a fita da rana sai dare, sannan ba,a karamar shiga, don ko da aka je jere ma yace musu duk wani abu da ya kama na hoto ne su koma da shi ba a sanya hoto a gidansa, matansa uku ne ita ce ta hudu.
Ita kam Salima ita ce mai dan gwara-gwara, domin ita Hassan dalibin babanta ne saurayi ne fil, kasuwanci ne ya kai shi Maiduguri yake zuwa gurin lecture din malam har suka zama daga cikin ‘yan kwamitin masallacin gidan.
. Don haka shi gidan haya ya kama mai daki hudu, da wata amarya a ciki da take da dakuna biYU, shi ma ya amshi biyun, don haka kayama da Yawa sai da aka koma da su gida.
Zahra din dai da ‘ake raina mijinta tafi kowa morewa, domin ya kammala ginin gidansa tsaf, gwanin sha,awa aka jere mata komai ba ta da wata matsala ita kam auran soyayya zata yi.
Falmata kam an ajiye kayanta, domin ita sai mijin nata ya zo sannan za,aji inda zai ajiyeta, don haka jeranta ya rage. ‘
Duk labarin da yake zuwa kunnen Yakolo daga bakin Hajja Basma ba labari ne mai kyau ba, ita da‘ ya ’yanta sun tashi hankalinsu matuka banda taji yace muddin ta zuga diyarta ko daya ce ta bashi kunya akan wannan aurcn to itama a bakin aurenta, da cewa zata yi duk su gudu, sai dai ya ya suka iya? Haka dole suka hakura.
Su kam danginsu . sun cika gida suna ta sha_’aninsu cike da farin ciki, ‘ domin daman zamansu Yakura kamar akan ransu suke saboda yaran ba su da’kunya ko cikin dangin ba su da farin jini ba su da wani kataBus. .
Anti Shafa’atu matar_ Yaya Bulama ce ta tsare Falmata mai gudun gyaran jiki domin mai gyara guda mahaifinsu ya dauka. Zahra ce kadai ke zama a yi mata gyaran hankali kwance, sai da Anti Shafar ta tsare Falmata sannan ta yarda. Ai kuwa gyaran kwanaki uku kacal aka yi mata sai gashi ta fito tana ta kyalli da sheqi sai kamshi ke tashi a
jikinta da ta gilma ka.
Da yake an sha sanarwar daurin auren masalaccin juma’ ar ya cika dankam! Da mutane, ana tsaka da huduba Mukhtar ya iso cikin shiga ta alfarma kamar yasan abin da za a yi, ya sami guri ya zauna yana sauraren huduba har aka kammala, kafin a tayar da sallah ya turawa malam saqon ya iso, don haka ana idar da sallah kafin a daura aure ya sanya aka nemo masa shi suka keBe can waje, tunda shi daman babu shi cikin daurin auren, sai anzo kan Falmata inda zai amshi wakilcin Mukhtar.
A can gefe suka kebe, Mukhtar ya durkusa yana gaida Malam cikin biyayya, Malam Abbagana ya amsa da farin ciki, sannan ya dora da cewa.
“Kasan dalilin da ya -sanya na ce ina nemanka kuwa?”
Cikin girgiza kai yace “Ai nasan nayi laifi Malam, na jima ban zo mun gaisa ba, don za a yi shekaru biyu ko uku ma. Ina fatan za a yi mini afuwa?” .
Malam ya yi murmushi yace “Ai wannan mai sauki ne, tunda ina zuwa Kanon ina kuma tambayarka ace kana nan qalau. Wani muhimmin abu ne ya taso, wanda har ya kawo mahaifiyarka garin nan, tana zubar da hawaye a kanka, kasan Zubar hawayen mahaifi matsala ne babba a

Hmm wai me kuke tunanin zai faru ne?  Ya mukhtar zaiji idan har yaji wannan Albishir din  na bazata ?  shin zaima amince da wannan auren ko kuwa?
Mai zai faru idan har matarsa taji wannan danyen labarin?
Wai anya falmata zama ta soshi kuwa?

Mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *