ZUMA CHAPTER 4 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 4 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Fitowar mu kenan daga lectures misalin sha daya, gaba daya nayi zuru zuru saboda yunwar da nake ji, ko dan tea din da nake sha ma yau ban sha ba saboda sauri na kusan makara. Hibba dake gefena tace+

“Nifa Allah ya isa ce kawai zata raba mu da mutuminnan, yasa muzo sannan yaki zuwa kuma ya hana fita”

Tsaki nayi dan gwara ita tana jin karfin magana nikam I’m drained ji nake kamar hajijiya zata kada ni. Tare muka je wani eatery nan cikin school, banma jira menu ba na nufi counter din nayi placing mana order. Babu jimawa aka kawo mana seda nasha lipton din sannan na fara cin fried yam da sauce. Saboda dadi har rufe idona nake, seda muka gama tas mukai settling bill sannan muka fita. Dake se hudu mukeda wani lecture din yasa muka tafi hostel. Muna zuwa Hibba ta cire kayan jikin ta ta dauki zani ta daura tareda yin daidai a gadon. Zuwa nayi bayan na rage kayan jikina nace

“Kiga yadda kika kwanta kamar wata giwa dallah can!”

Dariya tayi ta matsa kadan tace

“Ke matsala ta dake kin faye takurawa mutum wallahi.”

Marairaice fuska nayi nace

“Hibba mana, shift a little”

Tsaki tayi ta tashi ta zauna tace

“Ki koma gadon Afiniki mana”

Bance mata komai ba tunda tasan bazan hau ba, zama nayi na janyo bottled water daga karkashin gado na fara sha, bansan ya akai ba ta tuna topic din da nake ta kokarin ganin nayi avoiding tace

“Ya ake ciki keda Hashir kuwa”

Bata rai nayi nace

“Do i know”

“Seriously, dan Allah. Wai meke damunki ne Nanah, shima zaki ce min bai miki ba”

Gira ta na dage mata irin yes dinnan, pillow ta kwada min banyi dodging ba seda yayi landing tsakiyar bayana, ihu na danyi nace

“Tsakani da Allah nace bana son shi, Hibba dole ne se na soshi? Ke kin cika masifa wallahi, a dinga magana daya kenan kamar karatu”

“Your head no correct wallahi! Ya Allah kasa wani yazo ya dandana miki ZUMA cikin bakinki, yasa ki gane me ake ji ki daina under looking dinmu”

Nidai bance mata ba se dariya da nayi kamar yadda na saba ta gama mitar ta ta hakura.  Bayan sati biyu ranar Saturday na kira Daddy na fada mishi kayan tea dina sun kare

“Ni kuma bana gari naje bayelsa, amma da zaki iya fita da se na turo miki kudin kije ki siyo?”

“Daddy zan iya, kawai napep zan hau fa!”

Dariya yayi jin excitement din dake cikin murya ta yace

“Kar fa ki bata”

“Kai Daddy shekarata daya fa da wasu months din a kano, wannan semester ma I’m coming home myself”

Se ya fara tsokanata wai na girma, yanzun am no more Baby Nanah inata dariya da haka ya turo min kudin mukai sallama. Tashi nayi nai wanka na shirya cikin lace onion color da flowers na ja ajiki. Skirt da riga ne da yayi fitting dina sosae. Powder na shafa na damping lip balm akan lebena bayan nayi combing girata ya kwanta. Na kalla madubi yafi a irga saboda nasan nayi kyau. Red veil na yafa nasa flat shoes masu red ribbon a saman su. Na dauka shoulder bag baka da katon red ribbon a jiki irin takalmina. Afiniki tace

“Fine Nanah, kinyi kyau I love your complexion wallahi”

“Thank you”

Na fada mata na wuce. Tun a hanya nake lissafin irin uban shopping din da zanyi se kuma na fara tunanin wanne store zanje ma, Hibba na kira na tambaya tace min naje Sufi a tarauni, dake nasan tarauni nace

STORY CONTINUES BELOW

“Ke Hibba yayi nisa gaskiya!”

“Baki jin shawara matsalarki kenan, Allah can din yafi”

Haka ta lallabani na tafi, me napep na samu har can ya kaini, na sallame shi na shiga,  dama nayi list cikin wayata, so ban bata lokaci ba na gama cifcif abina. Na biya akai min packaging na fito da kaya nikiniki dukda sun saka cleaner dinsu ya tayani. Ina tsaye a bakin titi inata tsayar da napep amma kowa se yace min bazai je Buk ba. Duk raina ya gama baci naji tsayuwar mutum a gefe na, da sauri na matsa tareda daga idanuna na kalleshi. I didn’t see anything banda naga namiji da shekarun sa zasu tasar ma shekara arbain idan kuma bai kai ba to baifi a rage shekara biyu ko uku ba. Though bashida girman jiki kuma ba karami bane. Yana cikin farar shadda tas da kuma babbar riga, kanshi sanye da hula da akai mata ado da zare kusan uku amma prominent zaren shi ne blue.

“Baki jin rana?”

Ya tamabaya yana kallon sama, ban saba ba da naga namiji a kusa dani haka se naji duk am not comfortable. Kara matsawa nayi nace

“Napep nake jira!”

Baice komai ba ya fara tsayar dasu and God so kind daya ya tsaya tareda tambayar shi inda zanje, kallona yayi kafin ya tambaya nace

“Old site BUK!”

Anan ya tsaya me napep ya fadi kudin sannan ya saka min kayana banma lura da lokacin da ya biya kudin ba, seda na shiga ya dan leko da kanshi karo na farko yayi min murmushi yace

“Allah ya kiyaye hanya”

“Amin!”

Na ambata me napep ya tayar zai tafi yace masa

“Tsaya mana!”

Ya dubeni yace

“Can i at least know your name please”

Ya fada yana hada hannayenshi wuri daya, kamar wanda yayi min casting spell kawai nace masa sunanan Fadima, yana murmushi yace

“Nasan zaki ce me yasa yake haka, just give me your digit kinji?”

Nanma babu musu na bashi. Crap! That’s the beginning of everything, mafarin bude sabuwar chapter cikin kundin rayuwa ta. Seda yayiwa me napep kashedin ya tafi dani a hankali sannan yayi min murmushi tareda waving hannun shi. Tunda muka tafi me napep din ke min zancen mutumin da bansan sunan shi ba. Bance masa ci kanka ba har ya hakura ganin bana kula shi. Har kofar hostel ya kaini sannan nace zan bada kudin yace min ai an riga an biya kudin.

Lokaci sosae na dauka inata gyara kayan da na siyo, lokaci zuwa lokaci ina tuna fuskar wannan mutumin a haka na gama inata tsaki duk lokacin da idanuna sukai min picturing dinsa. Chocolate na ciro na fara ci ina kallon wani film danai downloading. Wajen maghrib na tashi na daura noodles sannan naci na dakko books dina ina dan dubawa amma kuma bana gane ko kalma daya da nake karantawa kamar dai hankalina baya kan abinda nakeyi. Se nakai page ban gane ba se na tiso baya amma still hakan ce ke kasancewa. Ihu na saki tareda runtse idanuna dake ni daya ce a dakin na wullar da littafin nace

“Meke damu na ne?”

Na tambayi kaina ba tareda nasan amsar da zan bawa kaina ba. Tashi nayi na duba wayata naga tara ta wuce, bazan iya fita ba se na kunna kallo na fara yi with the hope kilan zan daidaita amma hakan bai samu ba zuciyata da hankalina suna wata duniyar da bansan ina ba. Kashe kallon nayi na kwanta tareda lumshe idona se kawai dazun a kofar sufi ya dawo min, nake tunanin ko ya sunanshi? Ko meye aikin shi? Ko zai kirani? Can kuma se na fara mamakin kaina, yaushe na
fara damuwa da alamuran mutanen da suka nuna interest dinsu akaina? Shi bai ma ce yana sona ba fa.

Kamar yasan tunanin me nakeyi se naji ringing din wayata dake gefena haka nasa hannu na janyo tunanina bazai wuce Hibba ko kuma sisters dina ba, tunda Daddy na kira na fada masa na dawo daga shopping din. Sabuwar number ce, shiru nayi ina karewa screen din kallo a haka nayi missing call din babu jimawa aka kara kira wannan karan ban barshi ya katse ba nayi swiping tareda karawa a kunne na. Yana min sallama na fahimci da wani nake magana, se naji kamar an tsoma ni cikin ruwan sanyi, for no reason se naji hankalina ya kwanta.

“Fadima ya kikaje?”

Ya tambaya yana murmushin da nake jiyo sautin shi, a hankali nace

“Alhamdulillah!”

Se mukai shiru na wasu dakiku kafin ya sauke ajiyar zuciya yace

“Fadima bansan ta ina zan fara miki bayani ba, amma nasan kamar waya ta min kadan na miki bayani”

Bance komai ba amma muryar shi kadai se naji tana fitar da wani abu a cikin zuciyata tana cikata guraban dana barsu babu komai.

“Fadima!”

Ya kira softly dake ban saba ana kirana da sunan ba se nake jin kamar dan ya furta Daddy ya saka min sunan. Ya iya fadan sunan har seda naji inama Fadima kowa ke cemin ba Nanah ba.

“Sunana Aliyu, I’m married, yes inada aure inada yara uku, dukkansu maza ne, ni asalina dan Gombe ne amma zan iya ce miki ko haihuwa na a kano akai so ni kano ta bude min idanuna. Anan nayi karatu kuma nan nake zaune da iyayena da matata da yayana.”

Idanuna na lumshe jin harda mata yake da ita, ko dan dama na ayyana hakan duba da shekarun sa idan baida aure zaa samu matsala kenan.

“Bakice komai ba? Ni kadai nake ta magana”

Dan murmushi nayi nace

“Ai naga kana kokarin fahimtar dani kai waye shiyasa nake sauraran ka”

Haka ya cigaba da fada min har abinda ban saka ran zai fada min ba, munyi magana na kusan mintina talatin sannan yace min

“Fadima i need to go, to ten yanzun se munyi magana da safe”

“Allah ya bamu alkhairi”

Na fada sannan mukai hanging na kwanta shiru ina tunano dukkan maganar shi, yana da aure yana da yara anya kuwan zan iya? Na ayyana a raina idanuna na lumshe wata zuciyar tana ayyana har nayi accepting dinsa kenan? Na watsar da dukkan makamai na kenan? A wannan daren banyi karatu ba, banyi kallo ba, se reminiscing nake akan maganar da mukayi dashi ko nace yayi danni i was just attentively listening.

Cikin bacci naji wayata na vibration, juyi nayi ina jin an takura min kuma bana son ma picking call din, amma jin kiran yaki katsewa yasa na laluba wayar nayi picking ba tareda na kalla screen din ba balle nasan wanda yake kira.+

“Nanah Fadima!”

Se naji na wartsake idanuna sun bude tar, daga jin muryar Aliyu, dukda haka banyi magana ba seda ya kara cemin

“Nanah lokacin sallah yayi, ki tashi kinji?”

Mikewa nayi nace

“Tohm”

Daga haka ya kashe wayar nima se na mike na dauki kettle na tafi bayi, na dawo nayi karatun quran sannan nayi sallah. Ina nan zaune da casbaha hannuna ina ja seda nayi azkhar sannan na koma na kwanta tunda lectures din se 8am nake da ita. Bacci nayi sosae lokacin dana tashi bakwai da rabi, a gigice nayi wanka ko mai ban shafa ba na dauki carton color abaya na zura na murza oil perf dina sannan na dauki wayata da papers din na fita a 360. Ina zuwa kofar hall din tuntuni madam ta shiga na tarar da wasu a tsaye bata barsu ba balle ni da nazo yanzun. Baifi mintina goma muka kara ba kowa ya kama gaban shi dama munsan ba zata barmu ba. Daki na koma na hau gado na fara bacci can cikin baccin naji ana bubbuga min gefen katifa, idanuna na bude naga Hibba tsaye a kaina, tashi nayi na zauna ina kokarin kare kaina nace

“Wallahi Hibba bacci nayi da yawa! Shiyasa na makara”

“Meye amfanin alarm, kunyi saa batayi komai ba”

Dadi naji sannan ta ciro lecture note dinta tana min bayanin abinda nayi missing, mun kusan awa sannan muka gama bayan na fahimci me aka tattauna a class din and i was very proud of Hibba. Muna gama wannan na dakko mata popcorn da chocolate na aje mata, tana ci tana danna wayarta tana murmushi anan tawa wayar ta fara ringing, tunda naga me kiran naji gabana ya fadi na kalla Hibba naga hankalinta baya kaina, kawai se nai picking, ni na fara gaishe dashi ya amsa cikin murmushi kamar ko da yaushe.

“I thought of kiran ki tuntuni amma se nake ganin kilan kina lecture ne”

Kamar yana gabana na marairaice fuska nace

“Nifa banje ba!”

“As in? Me ya faru?”

“Makara nayi kuma ta hanani shiga shiyasa”

Dariya ya danyi yace

“To ai laifin naki ne madam, yanzun yadda zaayi ki tura min time table dinki se ina notifying dinki”

Murmushi nayi cikin jin dadi nace

“Nagode zan tura maka. Ya office?”

“Gamu a office”

Daga nan muka shiga random talks wanda nima kaina ina mamakin kwana daya tak na saki jikina dashi, Jabir da kusan muaki shekara ban taba bashi koda quarter of my time ba, kalla hashir dashi ko picking calls dinsa bana yi amma Aliyu kamar wanda yayi casting spell akaina , abin da mamaki. Mun kusan thirty minutes muna hira inata murmushi da dariya wanda ni kaina bansan na iya su ba, ji nake kamar lokaci ya tsaya kada ya wuce. Kiran sallar zuhr yasa yace

“Nanah ki rike ni da yawa fa, muyi sallah ko and make sure kinci wani abun kafin ki fita class”

Kamar yana gabana na gyada masa kai tareda fadin

“I’ll do that inshaaa Allah”

Se yace min

“Bye for now!”

Aje wayar nayi tareda sakin wani kwantaccen murmushi na lumshe idona, bansan me nake ji ba amma da nasan ko meye yana da dadi Kamar ZUMA haka yake. Mikewa nayi da niyyar yin alwala se lokacin na hadu da idanun Hibba da alamun she has been starring for a while. Hade fuskata nayi in embarrassment na dauki buta na fita, inata dariya a haka Nayi na dawo tana zaune inda na barta amma duk inda nayi idanunta na yimin rakiya da alamar tambayoyi ne fal bakinta, da kuma mamaki. Na idar na kalleta nace

“Yunwa nake ji, ki tashi mu tafi”

Ba tace min komai ba ta mike muka shirya muka fita, bata cemin komai ba nima ban shirya bude bakina ba haka muka ci abinci muka wuce lecture. Wasawasa se abu ya fara karfi tsakanina da Aliyu, munyi sati biyu da sanin junan mu a cikin satin biyun babu abinda na tsinta zamana dashi se farin ciki, dukda har lokacin bai cemin yana sona ba amma nasan kokari yake ya gama clearing ma kanshi matsugunni, daya tabbatar ya samu gurin zama zai bude bakin shi.

Ranar Friday inata shirin tafiya Dutse saboda na samu break din mid semester, Hibba tazo itama tana zaune tana waya  ta gama ta kalleni tace

“Nanah!”

Dagowa nayi na dubeta sannan na zipping trolley nace

“Yes Hibba!”

Ina jiran karin bayani, se kuma tace min

“Yaushe ne ma bikin su yaya Rahma”

Nasan bashi zata tambaya ba, for all this while nasan jira take na mata bayani, nima ina son nayi mata amma not when Aliyu bai furta ba, nafi son na bata genuine labari me kuma dadi bawai hasashe na ba.

“Karshen week dinnan ne,amma kinsan iya yaya rahama ce an fasa na yaya Mariya fa”

Idanunta da mamaki tace

“Kai subhannallah me ya faru? Amma babu dadi”

“Walalhi fa, to ya zaayi haka kaddarar ta take, kinga cewa sukai wai bata da uwa shiyasa bazai aure ta ba, wai mu ba mace ta rike mu ba, bamuda tarbiyya, zaman kanmu muke….”

Kawai se na fara kuka, bansan me yasa nake kukan ba amma nasan ina tuna
halin da ya Mariya ke ciki ne, ban taba tunanin auri sakin Daddy zaiyi affecting dinmu haka ba. Lalalshina Hibba ta dinga yu har nayi shiru se nayi murmushi nace

“I’m sorry to disturb you”

Hararata tayi tace

“At least zakiji relief tunda kin fada, to amma sau nawa uwa tana fita tana barin yayanta, mutuwar aure ai is common a yanzun.”

Dan murmushi nayi me ciwo nace

“Hibba ba zaki gane ba, idan da sakin da ake nufi ne da sauki, kinga gidan mu mu 12 ne mu takwas a ciki kowa maman shi daban, yaya rahma da ya Mariya maman su daya, Lubna da Nawwara maman su daya, ban taba ganin mamata ba, bansan ya take ba, yar ina ce ke ko sunanta ban sani ba se daga baya, Daddy yayi aure kalakala shiyasa abin ya faru ahaka”

Nasan kwakwalwar kan Hibba kasa dauka tayi saboda mamaki, tafi mintina uku in deep silence kafin ta riko hannuna tace

“I’m sorry Nanah, Ayya Nanah haka kika rayu?”

Dariya nayi nace

“Eh mana, gani kuwan kina gani na, dukkanmu haka muka rayu babu uwa se daga baya kowa ke sanin tashi amma banda ni, kowa tashi uwar ta neme shi ni bansan tawa ba  ko ta manta dani bane, ina fatan duk inda take alkhairin Allah ya kai mata!”

Se naji zuciyata tana karyewa kwanakinnan so nake naji daga gurin mamana, ban taba gaskata zancen Aminatu ba seda na koma naga hatta Ummu tayi reuniting da maman ta amma banda ni,kowa dangin shi sun neme shi amma ni ko oho, kullum ina zuba idanu har na gaji.

Sosae Hibba ta tasauya min sannan ta rakoni na hau napep ita kuma ta tafi gida, muna zuwa tasha napep din daya kawo Aliyu na sauke shi, yau ma manyan kaya ne a jikin shi sede ba tazarce ba, wani soft yadi ne brown a jikin shi, yayi kyau ga hula da yasa hannunsa daure da agogo dake sheki saboda hasken rana. Karasowa yayi yana fadin

“Nanah fadima”

Ina ganin sunana na mishi dadi ne sosae shiyasa bama taba waya bai fada ba, wannan shi ne karo na biyu da muka hadu dadhi se waya da mukeyi. Shi ya samo min mota aka saka kayana sannan ya tsaya ta window yana min hira, kafin wani lokaci mota ta cika yayi min sallama ya tafi. Ina isa na tarar an gyara gidan ko ina anyi sabon paint anyi mana furnishing ko ina da sabbin kaya, gidan yayi kyau karshe ma kuwa, yan rahoto sun fada min duk yadda Amal ta iya zuzuta abu se naga yafi yadda ta fada min.Kowa yayi murna kamar yadda muka saba mukaci abinci sannan aka dakko lefen yaya Rahma na gani sannan kuma aka dakko kayan da zamuyi fitar biki dasu.

Bayan kwana biu da dawowa ta gida, munata shirye shirye yawancin bamu zama munata kokarin ganin taron ya tafi yadda muke so, dadin abin Anty hauwa dasu yaya nasiba duk sun zo se abin yazo mana da sauki. Ina daki mun dawo daga ganin hall din da zaai kamu, nida Anty Sumayya muka je, muna dawowa na sauke Arfat daga baya na na shiga wanka saboda zafin da akeyi. Amal ta kawo min wayata bayan na fito tace+
“Ya Nanah tun dazun ake kiranki fa, nadai ce kin shiga wanka”
Karba nayi na duba as expected Aliyu ne, seda na gama komai sannan nayi returning call din.
“Ya mutanen gida dasu Umma?”
“Duk suna lafiya”
Na bashi amsa ina daidaita kwanciyata, se yace
“I wanted to come in fada miki muhimmin abu, but jiya aka aikani Niger wani official assignment”
Kaina na gyada nace
“It’s ok, ya hanya?”
“Alhamdulillah!” Ya bani amsa sannan yace “Nanah, ina sonki, ina son na aureki na zauna dake har karshen rayuwata, banso na fada miki ta waya ba, naso nazo gida na sameki, amma tafiyar nan ta min shigar sauri, kuma I can’t hide it anymore ina jin gwara na fada miki kisan halin da nake ciki. Amma bazan takura miki ba ina son na baki lokaci so that you can think about us been together, na dai fada miki inada aure yayana biyu, ina son na aureki saboda ina sonki. Amma nafi son muyi rubbing mind dake kiji ko halaye na sunyi miki.”
Abinda nake ta jira kenan, shi ne ya fada yace yana sona, yau din daya fada se naji ba yadda nake expecting ba zanji ba, na zata zanji irin immense feeling dinnan amma se naji ni so empty se ma kamar tsoro da nake ji, se zuciyata ta fara tambayata zan iya? Zan iya zama da matar shi kuwan? Ya yaran shi? Amma yace yana sona kuma nasan da gaske ne? He’ll protect me, amma idan na kare da saki fa? Nima…..
“Are you there? Karki damu ba yanzun zaki bani amsa ba. You need time to sort everything out, ki dauki lokacin ki. Bansani ba ko second daya, minti daya, awa daya, kwana daya ko kuma sati daya amma dan Allah banda shekara daya!”
Ya fada yana marairaice wa and wannan yanayin yasa bansan lokacin da na saki murmushi ba nace
“Shekara nake so fa”
Na fada muryata cikeda zolaya, dariya yayi yace
“Bazaan iya jira har shekara ba, nida nake fata zuwa shekarar ace kin kusa haihuwa, naga product of love dinmu”
Fuskata na rufe ina kyalkyala dariya a hankali me shiga rai, wannan moment din yana daya daga cikin wanda bazan manta ba, dariyar da nake was so genuine. A haka jana da magana har muka dauki lokaci seda karshe yace
“Amma kiyi shawara da Umma kiji me zata ce”
Na fahimci uwata nake nufi se nace masa
“I don’t have one”
Da tausayi cikin muryar shi yace
“Ayya Allah ya jikanta”
Se naji ko da gaske ta mutu na ayyana a raina, se idanuna suka ciko da kwalla and da sauri na masa sallama dan bana son yaji  wannan kukan. Bayan na kashe wayar na tsaya ina ta kallon wayar tareda jujjuya ta a hannu ina ayyana dukkan words din da suka fita a bakin shi, they were so genuine, banji glimpse na karya ba. Da sauri na mike tare da fadawa kan gado ina dariya ian jin tamkar ina kan gajimare ne, wani irin feeling me karfi yana shiga cikin zuciya da ruhi na. Pillow na janyo na rungume tare da lumshe idanuna but wannan maganganun nashi su kadai ke min amsa kuwwa a kunne na.
STORY CONTINUES BELOW
Na jima a wannan halin har yaya Rahama ta shigo, ashe tuntuni take nema na, tafi mintina uku tsaye tana kallona se rolling nake akan gadon duk nayi tubutbu da spread din dake gadon, inata kuma murmushi, ganin kamar na zauce yasa ta kai min duka, ina dagowa na rungume ta ina saki dariya, aa se ta tsaya tana kallona da mamaki tace
“Ke aljanu ne suka hau kanki!”
Dariya nayi nace
“Ko daya ZUMA ce kawai”
Tsaki tayi dan bata fahimci me nake fada ba, ta bani sakon Anty Hauwa akan naje tana dakinta tana kirana, mikewa nayi na daura dan kwali na fita amma duk yadda nake kokarin danne murmushi dake fuskata na gagara, it’s obviously all over my face. Tana zaune itada Anty Sumayya suna zuzzuba turaren wuta cikin containers dinsu, dakin banda kamshi babu abinda yake.
“Mom gani”
Dagowa tayi tana dubana tareda tsura min idanu kamar tana son karanta abinda yake akwai a tare dani. Zama nayi ina rufe fuskata ina murmushi wayaga farin shiga, kada kuga laifi na fa, soyayya ce.
“Wani yace yana son ki ne?”
Ta fada tana kallona, dauke kaina nayi ina gyada mata kai, se ta fara dariya tana cewa Anty Sumayya
“Maman Munib kina jin yar gidan ki, ikon Allah Nanah ashe kin dawo hanya”
Duk se kunya ta kamani, Anty Sumayya tayi tsaki tace
“Ki dai bi a hankali kinata wani rawar kafa maza yan iska ne”
Se naji banji dadi ba me yasa zata ce haka, Aliyu daban yake nasan bazai taba yaudarata ba. Bata rai nayi ganin haka tace
“Nanah
bata rai kikai, ya hakuri ai ba duka haka suke ba, fada mana me yace?”
Se naji sanyi a cikin raina, na bude baki na fada musu komai. Mom cikeda gamsuwa tace
“Da alama he’s a gentleman, amma yace gida daya zaku zauna da matar tashi”
Bakina na turo nace
“Yau fa yace yana sona! Ni ban tambaye shi ba”
Shawarawari suka bani sosae sannan na kama musu aikin muka gama inata jina wata daban. A hankali ranaku suna tafiya aka shigo biki munyi biki kayatacce kamar yadda muke so, an gama an kai amarya dakin ta anan Dutse cikin famous Danmassara quarters. Tafiyata da Aliyu smoothly take tafiya, bai kara furta kalmar nan ta so ba amma a aikace yana nuna min soyayya zalla ma kuwa.
Ina gama mid semester break na koma school, duk lokacin da mukai waya da Mom zata cemin ya Aliyu zan ce mata Aliyu is fine muna nan tare dashi. Ranar dana koma nasha gyara saboda ni mutum ce me tsafta , ko lecture banje ba da mukai waya da Aliyu ya dinga fada wai saboda shara nayi missing class sede nayi dariya kawai nace yayi hakuri.
Bayan kwana biyu ina daki ina duba wani sabon handout dana karbo wajen Hibba ina dubawa sega kiran Aliyu ya shigo, tattara papers din nayi na aje gefe tateda picking call din
“Nanah ya school?”
“Alhamdulillah” na bashi amsa sannan na gaida shi ya amsa nace
“Ina su Muneef?”
“Suna lafiya lau, Nanah baki nema na ma, irin kice min se yaushe zan zo ko?”
Dariya na danyi kadan nace
“Yanzun fa zan tambaye ka yaushe zaka zo?”
Se yayi dariya yace
“Oyah ask me”
Se na tambayeshi yace min da daddare zai zo, daga haka mukai sallam cikin sauri nayi dialing numbers din Hibba, tana picking nace
“Hibba Aliyu zai zo anjima”
“Who’s that?”
Ta tambaya, se na tuna ashe bata sanshi ba, na zauna na fara bata labarin Aliyu da kaomai ban boye mata ba wani mugun zagi ta sakar min bayan na gama
“Shi ne se yau zaki fada min”
Na marairaice nace
“Come on Hibba kiyi hakuri inata jira ya fada ne yace yana sona”
Tsaki tayi tace
“Ya miki kyau, kice kina son shi kenan. Ni fa ban yarda da soyayya ba! Ni fa banga namijin da zan bata lokaci na akan shi ba…”
Ta fada tana kwaikwayon muryata, dariya nayi nace
“Hibba baki mantuwa, naga lokacin ni yarinya ce, i was few months younger yanzun kuma I’m older!”
“To Alhamdulillah naji dadi zaki ji me mutane keji. Ina son ki bi komai a Sannu don’t rush things Nanah kiyi addua Allah ya muku zabi mafi alkhairi, Allah ya daidaita zaman ki da matar shi da yaran shi, ya bawa dangin shi ikon accepting dinki”
“Amin Amin Hibba, what will life be without you?”
“Without Aliyu dai!”
Ta fada tana dariya, ni kuma nayi pouting, ita ta tsara min yadda zan tarbe shi, wajen biyar da rabi ya kirani ya zo, na gama shiryawa cikin bakar abaya me flowers ja da silver, nayi kyau ba laifi. Fita nayi hannuna da wayata da kuma karamar wallet, a eatery din da nace masa anan yake jirana, ina zuwa ya kashe min fuska da wani murmushi wanda seda naji butterflies a cikin cikina……soyayya ZUMA ce!
In the dark of night the stars light up the sky, we see them flying free just like you and me! Everyone is lonely sometimes but I’ll walk a thousand miles to see your eyes❤️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *