WALIJAAM CHAPTER 5 BY MAMAN TEDDY
*_Ga masu bukatar wannan littafi xasuna iya mgn dani ta wannan link din 👇_*
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
*_SADAUKARWA GA DUK KANIN FULANI🐄_*
*Alheri writers asso.📚*
_________________________
“Na shiga uku na ni Haula..!! Wannan wacce irin masifa ce Alhaji ya dauko mun ,lallai yau na yarda cewa Bayason farin ciki na dana Anwar ,aiko lallai baxan ta6a yarda da wannan lamarin ba ,yanda aka daura Aurennan a duniya haka zaa rabashi acan. Don ba a haufo wata diya da zata tako mun kafa ta shigo gidan mijina a matsayin suruka ta ba ,haka ba a haifo wata yarinya da xata Aurar mun d’a wai ta zauna mun dashi a matsayin mata ba ,nice kadai nake da za6i akan d’an dana haifa…ta karke maganan tana jan wani irin numfashi ma tattare da bacin rai da takaici ,tana mai dafe goshin ta .
Momy duk a yanxu ba lokacin mgn bace meye mafita a yanxu ko haka zamu saka idanu har abun da muke gudu ya faru?? Cewan Zabeena tana maganan hadi da matsar kwalllah”. Itakam Dr haula taakaici ne ya hanata bata amsa sai dai kawai ta mike tana barin komutsan da ta shigo dasu anan wurin hadi da nufar bedroom din ta ,don yanda zuciyar ta ke wani irin tafasa yana halba mata kamar xai tarwatse yayo waje .
Itakam Teema hawayen ne ke dada wanke mata ido kaman baxai dakata da zuba ba ,yyn da cikin sauri ta fice daga falon tana mai nufar gidan Mahaifin nata don neman Asma’u ta fidda mata da wata mafitan.
******
Bangaren shattu kuwa ganin irin Waaannan miyagun mutanen da ta hadu da su ,a cewan ta marasa imani ne yasata nufar rugar su tana komawa inda ta fito ,gab da xata isa Bukan su ne ta hango Hardo na tahowa daganin sakasan ba a hayyacin sa yake ba . Hango ta da yayi ne yasa shi tsayawa yana nisawa dama daga jiron su yake . Har tazo dab dashi bata nuna wani alama na tasan hardo ba illlah ma rabashi da tayi tana kewaya shi xata wuce .
Ke Ballagaza karuwa!!! Sunan da ya kira Shatu da shi kenan yana wannan numfarfashi kaman wanda yayi gudu ya gaji . Cak tajah ta tsaya ranta na suya sakamakon kirar sunan ta da hardo yayi da karuwa….Naam mijin karuwa inajin ka. Ta bashi amsaa a takaice tana murmushun bakin ciki .
A kufule Hardo yace waye mijin naki? , ni hardo Kuwa allah shi kyauta ai na dade da sakin ki ,kije ki nema fasikin da kukasaba fasikanci ki Aureshi.
Kasa basa amsa tayi sai binsa da wani irin kallo da take na mmmaki ,kamin lokaci daya kwallah yafara kwaranya mata yana gangarowa saman fuskan ta . Baki na rawa tace ” Hardo ni ka saka ? Ashe dama duk rantsuwar da kakeyi akaina na zaka zauna dani duk wuya duk dadi karya ne Hardo??. Ashe cewan da kakeyi tare zamu rayu zamu mutu duk karya ne?? Akan wannan abun ne xaka ce ka juya mun baya wai harda tukucin saki . Maganan nata ne ya harde sakamakon wani irin kuka da ya kubce mata .
Shikam Hardo juya mata baya yayi kamun ya cigaba da cewa ” eh ba sakeki shatu ,don nace xan rayu na mutu dake shine kkje kika dauko mun yar xina? Tom nafasa yanxu kowa na nemamawa yayan sa uwa ta gari ne ,kinga ko bana nemo masu mazinaciya ba…na sakeki Shatu bana sonki bana kaunar ki . Yana fadin haka ya juya fuuu yana cigaba da ta fiyar sa kaman xai fadi kasa saboda sauri fakakan² gashi babu kiba dan filinge kaman iska zai kada shi kasa .
Itakam Shatu anan wurin ta tsaya kamin ta zube kasa tana wani irin kuka ma gunji tsawon lokaci tana a haka ,kamin ta lalla6a ta tashi daga cikin wannan siyayin tana nufan jiron su hadi da isa buka .
Da shugarta ne Umma ta bita da wani irin kallo ,da yake nuni da abubuwa da dama ,Yawindo ne tayi saurin tarota tana kwance yarinyar bayan ta kana tace ” daga yau Shatu kar ki sake fita ko ina ,saboda ke matar Aure ce a halin yanxu ,Hardo ya sake ki a cikin dubbin jama’a kuma a daidai wannan lokacin ne wani bawn Allah ya roka a daura auren ki da d’ansa tunda baki da idda akan Hardo shi yasa aka daura Auren ki da wani mutumin na dabam .
Kirjin Shatu ne ya buga mata da karfi ,wanda saboda firgici sai da ta dafe wurin ,shikenan a yanxu na tashi a matar Hardo ,duk so da kaunar da nake masa ,kawai sai kuka hawaye na bun kuncin ta sharrr_sharrr.
Kwance yarinyar bayan Yawindo tayi tana zaunar da Shatun kamin ta zauna gyefen shatun tana kallon jaririyar tana fadin Mashaallh yarinyar kyakykyewa kamar diyar larabawa mene sunan ta ?. Jan hanci Shatu tayi cike da muryar kuka tace ” na sa mata sunan Umma na Fatima “. Aaaa mashallh ashe Nana ce….kai Yawindo wannan abun da kkyi tayi yawa banason a saka suna na sam wlh ta dai nima wani sunan tadabam ba suna na ba…Aiko baxa’a canja ba sunan diya Zahara. Cewan Yawindo tana murmushi hadi da mawa jaririyar wasa.
Itakam Shatu juyawa tayi tana kwantawa a hankali hadi da lunshe ido kwallahnna dada zubo mata ,ko wanni secon tunanin mgnan da Hardo yayi mata takeyi ,wanda zuciyarta kuwa kaman a wannan lokacin ne yake kara ingixa mata wutan soyayyar hardo .
********
Zaune suke Anwar da Abbas Sadeeq a dirning area suna lunch ,hankalin ko wannen su a kwance yake kowa na cin abuncin shi banda Abbas da yake dauke da fork ya kasa cin komai .
Anwar ne ya kallin Abbas kamin yace masa,” kai malam yadai kana ta rike da fork baka ci komai ba har yanxu kasan fa tafiya ce damu yanxu ,tun jiya Mom ta kirani tace na dawo gida tanason mgn dani ,kuma kai kana ta rike da Fork kaki cin komai yanxu fa xamu tafi.
Nisawa Abbas yayi yana lumshe makirarrun idon sa ,kamin ya taune la66an sa na kasa .
Murmushi Sadeeq yayi yana fadin bai wuce jarabarsa ce ta motsa ,tom oga Abbas ka kwantar da hankalin ka ,acan ma idan munje xaka samu hadaddun fine fine ladies . Just kaci abincin ka mu wuce kar ka 6ata mana lokaci plz.
A hankali Abbas ya furta ina son ta ne!! Ina son wannan yarinyar i really luv her .
Mamaki ne ya kamasu duka amma sai Anwar cike da miskilanci ya kawar da kai ,shikam.Sadeeq cewa yayi wace kenan..? Kai tsaye Abbs ya basa amsa da wannan bafullatanan ,a ina take aina xan sameta ? A ina xan ganta??. Karyar banza kanaso kayi iskanci da yar mutane tom bakaga da goyo a bayan t ba ,matar aure ce kayi wani abu da ita bulallai xaka shako ba haka ba Anwar ? Sadeeq yayi maganan yana duban Anwar da sai a sannan ya kalli inda suke .
Kwashewa da wani wawan dari su biyun sukayi suna kallon Abbs da yake kire da kwalin Exotic .
Hmmm kuna shirme ne cewan Abbas yana tsiyaya lemun a cup ,sai da ya kurba kadan sannan ya ajiye yana fadin ” ba son ta nake na lokaci daya ba ,wai nayi sex da ita shikenan ba ,Aaa son nake ta kasance dani har Abada ,tazama mun uwar y’ay’ana ba wasa ba yayi mgnan yana kallon su Anwar dasu ma shi suke kallo .
Cigaba yayi da cewa” kowaye mijin ta wlh indai ina lumfashi a duniya sai ya rabumun da ita na Aureta dani ta dace ba da wani ba.
Tsagaitawa yayi da mgnan yana kallon su . Murmushi Anwar yayi kurum kamin yace ” tom ai sai kabi kauyakun fulani ka nemo ta… Dariya s
adeeq ya hauyi kamin yace irin wannan fulanin ne da hausa basu iyaba sam….idan kaje da kanka zaka dawo mayaudari. Aa bazai dawo ba , kamin yafara neman ta sai yafara koyon fulatanci sannan kaga idn ya iya neman nata zai zo maasa da sauki….cewan Anwar yaana murmushi da hushiryar sa ta bayyana .
Kwarai kuwa hakane Anwar kaga sai ka fara zuwa ka koyo Fulatancin kasan meye WALIJAAM da imfinijaam…
Dariiya duka suka saka a wannan karon har da Abbas din kamin ya ajiye fork din da yake tsakarar ppr chicken yana daukar tissue hadi da goge la66an sa yana mikewa daga tsaye yana fadin kun kawo shawara kam mai kyau ,ku mu tashi haka mu dauki hanya .
Mikewa su duka sukayi suna ficewa daga falon hadi da fita fitowan da xasuyi ne naga ashe a barikin sojoji wannan gidan yake nufan daya daga cikin motocin su sukayi suna shiga kamin su dau hanyan zuwa gidan Mom Haula .
********
Ummie inaso idan na samu hutu naje Garin kaduna gidan Momyn Abbas acan zanyi hutu ,kinga na dade banje ba ummie . Diyanan tayi magana tana kallon Ummien nata da hankalin ta ke akan laptop din dake gaban ta . Idon kuwa na ta sanya masa siririn gewayayyan Eyeglass wanda yakasance fari ne mai launin trnsferent medical.
_________________________
_FREE page na dab da karewa masu bukata zasuna iya magana dani ta link din dake saman page ,Don Allah kar kimun mgn kiga ban baki amsa ba , kwana biyu ina busy sosai ,idan biyan littafin zakiyi ga hanyoyin biya nan nasa a kasan wannan page din ,idan kin biya kimun screen short na evidence dinki ,idan kati ne kk turo zan gani kuma xan saki a paid grp 2 inshaallh… Masu tambayar grp link na comment wlh ya cika ,idan biyan littafin xakiyi sai ki biya kaawai ngd…_
_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_
_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
_Normal grp 200_
_Vip grp 500_
_Spc group 1k👌_
_Idan kati xaki turo MTN ne ._
_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_
_0028799846_
_Farida Hashim stanbic bank_
_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_
_+22797780373_
_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._
*_Taku mai kaunar ku tare da nuna mawa masoyan ta soyayya da kauna ,kulawa duka wato_*
*MAMAN TEDDY🧸*