UMM ADIYYAH CHAPTER 21 BY AZIZA IDRIS GOMBE
                Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA
Ba ta son dagowa ta dube shi, amma sai dai kafin ta hana kanta, ta riga ta yi garajen
kallon idanunsa, kallon da Yaya Zaid ya ke
mata na daban ne, ta san kallon da yake
mata idan yana zolayarta, ko yana son ta fada wasu tarko nasa, amma yau sai take
ganin alamun gaskiya a maganganunsa.
“Ka san an ce idan mutum ya saba yin Karya, duk randa ya fadi gaskiya, zai yi wuya
a yarda da shi kuma, saboda ya riga ya yi wa kansa mummunar shaida.”
“Fada min me zan yi miki na nuna miki cewa babu Karya a cikin batuna?”
“Ka rabu da ni.”
Kallonta ya yi tamkar me neman ya karanto wani abu a can cikin ruhinta, sannan ya
sa daya hannunsa ya shafo saman kansa cikin damuwa. “Don Allah ki daina fadan
wadannan kalaman, saboda aje-aje za su zamo normal a KwalKwalwata. Ba na son
hakan ya kasance.”
*************
Kallonta yake yi cikin sauraren abin da za tace, ganin ta yi shiru ba ta Kara fadin
komai ba, ya sa ya dan murza yatsun hannunta
ZAMU TASHI
da suke cikin nasa hannun, sannan 
ya ce. “Twinkle, ina so ki fada min tsakani da Allah, ranar da ki ka ganni a ofis, 
haushina ki ka ji don kin ganni da abinda ba ki taba tsammani ba a matsayina na 
yayanki ko kuma haushina ki ka ji, don na karya miki zuciya?” 
A take ta crag° idanunta tana dubansa cikin kaduwa, “Me ya sa za ka yi tunanin wani 
abu daban, dole raina ya baci, saboda abinda na dade ina yarda da shi shi ne, kai 
ne babba. Sawunka muke bi, domin gina tamu rayuwar, amma na kama ka da
 
babban laifi irin wancan. Ka fada min idan kai ne, ranka ba zai baci ba, ganin abin da 
ka ,,,,,, ka na yarda da shi, duk Karya ne ba hakan bane?” 
Runtse idanu ya yi, ya hadiyi wani abu, sannan ya budesu a kanta. “Na ji Twinkle, 
amma ina so ki san da cewa mutum ajizi ne, na amince na tafka kuskure babba a 
baya, wanda maimakon na kalle shi, kuma sai na zabi hanya mafi sauKi wajen Www.bankinhausanovels.com.ng zulmiyewa hakan, har ta kai na tabo rayuwarki a sanadin Decisions dina. 
Amma ina son a karo na farko ki dubi abin nan, ki min uzuri ki mance da shi, domin 
na yi miki alKawarin tun wancan lokacin ban sake kamarta hakan ba, kuma ba na 
tsammani ko fatan zan sake aikatawa koda a gaba ne. 
Domin kin bude min idanuna akan abin da na hana kaina gani don son kai. Yadda 
na ke roKon Allah gafara. Ina fatan Ya karba. Haka na ke so ki yi haKuri ki ba ni 
damar gwada miki na yi nadama. Ki ba ni dama na gwada miki matsayinki a raina. 
Za ki iya min wannan?” 
Yana kallon yadda labbanta da habar ta suke rawa, alamun tana shirin yin kuka, 
daga fuskarta ta yi ta kalli gefe. Hade da hadiye hawayen da ta ji ya taso mata 
kumatunta ya loba ciki. 
“Kar ki damu, let it all out. Ba zan yi judging dinki ba, ba laifi bane abin da ki ke ji a cikin ranki, haka ba laifi bane nuna shi a zahiri. Ko ki 
yarda, ko kar ki yarda, yadda ki 
ke ji a halin yanzu, haka na ke ji ni ma. Hakan yana nufin wani abu ko?” 
Tana juyowa suka hada idanu, ta ga kyakkyawan murmushin da ke maKale a 
fuskarsa, duk da kasancewar yana cikin jin Kuna, wannan ya sa ta kasa riKe kanta, 
nan da nan hawayen suka balle. Komawa gefenta ya yi ya zauna, ji yake yi kamar ya 
riKota, ya rarrasheta, amma haka ya saurara mata, ta sha kukanta har sai da ya ji ta 
lafa, sannan ya ce. “Kin ji sassauci yanzu?” 
Kai ta gyada masa. “Ka yi haKuri Yaya Zaid, ban san me ya hau kaina ba, ni dai 
kawai na ji kamar ma na bace na bar komai da kowa ne, ban san wani irin fushi 
bane ya zo min a wannan lokacin, wanda har ya girmama na ke jin zafinsa tamkar 
tsana. Na san gaba ba kyau, haka rashin da’a, amma duk lokacin da na… …Ganka, 
abinda kawai na ke gani Www.bankinhausanovels.com.ng 
Murmushi ya yi ya ce, “Hakan na faruwa. Musamman idan abin da ka ke so ya karya 
maka zuciya.” 
Harara ta kai masa, tana jan hanci ta ce. “Haka na ce maka?” 
“Ban haKurin naki dai bai je inda ya kamata ya je ba, kar ki sa ayi rejecting 
application dinki. Ki daina min wannan kallon, ko kuma duk abinda ya faru, ki kuka da kanki.” 
Tura bald ta yi tana kifta gashin idanunta da suka jiKe da hawaye. “To kuma kallon 
ma sai ka fada min yadda zan yi?” Ba ta ankara ba, ta ji ya matsa daf da ita, hannu 
ya sa ya zagayeta cikin kyakkyawar runguma, dumin jikin sa na shigewa cikin nata, 
yayin da take jin bugun zuciyarsa a jikinta. Gaba daya jikinta ya gama yin lakwas! 
Wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki da ba ta taba tsinta ba. Ya dauki lokaci a 
hakan, ba tare da ya sake ta ba. 
A hankali cikin Karfin hali ta sa hannu ta dan ture shi daga jikinta. Yaya Zaid…” Ta fara fada, amma har yanzu wata Karamar kyarma ta ji jikinta na yi. 
“Na’am Adiyyata?” Yanayin da ya kira sunanta, ya sa ta dago idanu ta kalle shi, 
wanda ba tantama shi ne kuskuren da ta soma yi. Domin ba ta taba tsammanin za ta 
ga wannan irin lallausar kallo mai haddasa bu-gun zuciyar mutum ya Kara gudu ba 
daga Zaid, wanda bai damu da komai ba, bai damu da take mutum ba, ya juya shi 
son ransa, yau ta ga wani abu a idanunsa da soyayyar Komfuta ba ta isa ta saka 
masa a tare da shi ba. Shin sonta ta hango a idanunsa? 
“Ina rokon alfarma daya.” Ta fada a sanyaye, don gaba faya jikinta ya mutu murus! 
“Ina sauraronki. Twinkle na.” Shiru ta yi tana wasa da yatsunta cikin tauna abinda 
ke bakinta, kafin ta furta, nan da nan gudun kar ta kasa fada. “Uhmm… za ka 
saurara min? Kar ka min gurguwar fahimta kawai dai…” Wasa ta shiga yi da habar 
gyalenta kanta a Kasa, cikin matsananciyar jin 
Www.bankinhausanovels.com.ng kunya ta ce, “Uhm, ban shirya ba.” 
Shiru ya yi yana duban rudanin da ke tattare da ita. “Na sani, shi ya sa zan bi da ke 
a hankali har mu isa wurin, ni ma wannan abinda ki ke ji, haka ne a wurina kuma 
sabon al’amari ne, muna da sauran rayuwarmu, don mu kammala fahimtar juna.” 
“Ba haka bane nufina.” 
Yanzu kam rudani ne Karara fuskar Zaid. “Menene manufarki?” 
“Ba zan zauna da kai ba alhali ka na shiga hakkin wata.” 
“Ban gane ba?” “Fatima…” **** *** 
“Twinkle, ban rabu da Fatima ba, haka nan babu komai a tsakaninmu, ba komai face 
taimakonmu da ta yi.” 
Kallonsa take yi kamar kansa ya juye. “Ban gane ba ka na fafin haka ne, kuma ba 
haka ba?” Kusan hakan na ke nufi.” 
“Yaya Zaid ka na rudani, me ka ke nufi?” 
“Ki kwantar da hankalinki, babu abin tada han-kali a nan, Fatima ba matata bace.” 
Wani jiri ne ta ji yana kwasarta, ta fara tan-gadi, ba ta san me take ciki ba, domin ji ta 
yi kamar tana mummunar mafarki a farke. 
Kamar an nausheta da mugun Karfi, tsabar fir-gicin da kalaman Zaid suka haddasa 
mata. Yaya za ayi ta gagara gane komai? 
“karya kayi min? Dukkanku kun min Karya. Don me?” Ta fada, idanunta a cike taf
Da hawaye. “Me ya sa za ku min haka?” 
“Shhh, Adiyya ki kwantar da hankalinki.” Ya matso kusa da ita da niyyar yi mata 
bayanin komai, amma ta sa hannu ta dakatar da shi. “Ba na son jin komai, ka riKe 
bayaninka. Na gaji da komai.” 
Tana fadin haka ta wuce sama da sauri, kamar za ta kife a hanya. Numfashinta ne 
ta ji yana fita sama-sama. Tana zuwa dakinta ta kullo Kofar daga inda yake tsaye, sai da ya ji Karar buga Kofar. Shafo kansa ya yi cikin damuwa. 
Ba haka ya so ta fahimci komai ba, yanzu da hakan ta faru kuwa Allah kadai ya san 
irin aikin da ke gabansa. 
Umm Adiyya ta sha kuka har ta gode Allah, ta gagara yarda da cewa kowa zai 
rufeta, har Maaminta, har Fatiman ma da ta yarda aka hada wannan shirin da ita. 
Sai lokacin abubuwan suka ci-gaba da dawo mata yadda tun bayan bikin nasu, aka 
ce Fatima ta koma makaranta, sai dai ta ji Zaid can ya ce zai je dubota, amma cikin 
kwanakin, ita ba ta taba zuwa ba. 
Sannan ko tafiyarsu Gombe, wato shi ya sa ba wanda ya tambayesu Fatiman. Ji ta 
yi ba wacce ta kai ta wauta da dolonci duk duniya, yadda har suka iya dabaibayeta 
da kalamansu na wayo. Amma suna waya da Yaya Zaid, koda yake ta hakan suke 
shirya plan dinsu. 
Haka ta kwana ido tangararau! Tana saKa tana warwara, tana kuka, ganin gabaki 
Daya danginsu sun juya mata baya. Can kusan Asuba ta tashi ta yi nafifilunta yadda 
ta saba, sannan ta jira aka kira sallah. A nan wurin barci ya yi awon gaba da ita. 
Cikin barci-barci ta ji ana KwanKwasa Kofar dakin, ta san waye ne, don haka ta ce 
“Kar ka bata lokacinka, ka tafi ba abinda ya sameni, lafiyata Kalau, idan abinda ka 
zo gani kenan, idan kuma ka zo ka ga gawata ne, to da saura na tukuna, tsirarun 
mutane ba za su hargitsa min rayuwa, su saka min baKin-cikin da zai kasheni ba.” 
“Come on, Adiyya, don’t be stubborn, ki bude Kofar nan.” 
Kifa kanta ta yi kan gwiwowinta, ta lumshe idanunta, ba ta tsammanin barcin ma zai 
dawo yanzu da aka lalata mata tunani ma. 
Tana jin muryarsa, yana ta magana, wannan ya zaburar da ita ta isa wurin Kofar, ja 
ta yi ta bude cikin zafin nama. Www.bankinhausanovels.com.ng 
*********** 
BABI NA GOMA SHA TAKWAS 
“Me ya saura kai min Yaya Zaid? Don Allah ka fada min me ya yi saura kai min a 
rayuwa? Ka yi amfani da fin Karfi da barazana ka sa iyayena sun aura maka ni a 
dole, don ka boye abinda na gani a wurin aikinka, ka yaudareni da cewa ka na min 
so na gaskiya, ka sa na Kara fara…” Hannu ta sa ta goge hawayenta, “Kai min 
Karya, ka ha’inci zamanmu, me ya yi saura kai min yanzu? Don Allah na roKeka ka 
bar ni haka na ji da kaina, na gaji ba zan iya ba, kuma, ka ji?” 
Tausayinta ne ya matuKar kama Zaid, take ya ji wani abu ya tokare masa zuciya. 
“Umm Adiyya… ki tsaya na yi miki bayanin komai.” 
“Ya isa Yaya Zaid, don Allah ka bar ni haka nan.” 
Hannu ya sa ya riKota, “Na san ba kya son ki ji komai daga gareni, to na yi miki 
alKawarin ba zan dago maganar ba, amma don Allah ki yi haKuri, ki zo mu je ki ci abinci, tun jiya da rana rabonki da ki ci ko-mai.” 
“Ni ba inda zan je, ka bar ni kawai.” Yana jin yadda ta yi magana da muryarta mai 
cike da shagwaba. 
“Ummu da dai basu Fa’iz, sai na rantse Maami ta bata autarta da shagwaba.” 
Ta gaza yarda a cikin zance mai muhimmanci irin haka Yaya Zaid zai sako maganar 
wasa. “Za ki iya sauka ko na kawo miki abincin nan? Ko kuwa na kai ki inda abincin 
yake?” Ya Karasa cikin zolaya. 
Harararsa ta yi, sai kuma ta tuna ya ce mata babu kyau. Ya san yadda ake yi ya 
Daureta da hujjoji, yadda ba abinda za tayi masa ta ji 
“Na fasa.” “Meye?” 
“Na fasa auren, gida zan koma yau. Ba zan iya ba,” 
“Adiyya, please ki yi shiru, babu kyau wannan furucin. Allah yana fushi da mata Www.bankinhausanovels.com.ng masu irin furucinki. Na san ranki ya yi matuKar baci, amma na dorawa kaina laifin, 
duk ni na jawo komai, amma tunda ga halin da muka samu kanmu a ciki, don Allah 
ki yi haKuri ki daina wannan furucin, kin ji? 
Ki na tsammaninsu Abba za su ji dadi idan wani abu ya faru a wannan tafiyar, duk 
irin jajircewar da suka yi don ganin yiwuwar aurenmu?” 
Shiru ya yi yana nazarinta, tabbas ya san kala-mansa sun shigeta. Fata yake yi kar ta 
tubure akan kafiyarta. 
“Za ki cutar da mu muddin hakan ta faru. Please, give us a chance.” 
Kai ta gyada masa, sannan ta sa kai ta bi ta gefensa, don fita daga dakin. Bin 
bayanta ya yi har suka sauka Kasan, suna shiga kicin, ya sa hannu ya ja mata 
kujera daya. “Me za ki ci?” 
Nazarinsa ta dan yi kadan, ba ta son zaKewa ya zama duk a tunaninta ne abubuwan da suke faruwar nan, daga da-wowarsa daga Amurka zuwa yanzu. 
“Cornflakes.” 
‘Cornflakes? Akan cornflakes ne, sai kin yi do-gon nazari?” 
“Ka tambeyeni me na ke so, shi ne na fada maka.” 
“Na ji maida wuKar, cornflakes it is.” Yana ajiye kwalin, tana ajiye `yan kwanoni 
masu zurfi guda biyu kan teburin kicin share hawayenta ta yi, bayan ta koma ta 
zauna. Shi dai mamaki yake yi, yadda mutum zai sha cornflakes a matsayin abinci. 
“Amma ki na Koshi kuwa?” Dole ya tambaya. 
Ganin kallon da ta watso masa, ya san dole ya bi a hankali, tunda lallami yake yi. 
Tana zaune ya hada mata ya miKo mata. Da sauri take sha, dama yunwa ta gama 
nuKurKusarta, don haka lokacin da ta daga kai, ta ga ya sa hannunsa a habarsa 
yana Kare mata kallo, sai ta ji wata kunya ta kamata, ta sauke idanunta Kasa, ta 
koma tauna a hankali, kamar mai tsoron haKo-ranta. 
“Ki mance ina nan, ki ci abincinki. Yanzu zan fita, ki na son wani abu a gari?” 
Kada kai ta yi alamar a’a. Zaid ya miKe bayan ya ajiye kwanonsa a gefe, 
kasancewar shi bai sha ba, tissue paper ya sa a gefen bakinta ya goge mata 
madarar da ya taba gefe da gefen lebenta na sama. Yau kam ta kusa ta nitse cikin 
Kasa, karbar tissue din ta yi, ta Karasa gogewa. 
“A dawo lafiya.” 
Ta fada lokacin da ya isa Kofar kicin din, juy-owa ya yi, ya ga ta ba shi baya, ba ta 
kallon inda yake. Murmushi ya yi ya ce, “Na gode.” ************ 
Bai dawo da wuri ba a ranar, koda ya dawo abinci kawai ya ci, ya samu ta riga ta 
kimtsa ko ina ta shiga ciki, KwanKwasa Ko-farta ya yi kawai ya sanar da ita 
dawowarsa hade da mata sai da safe.
********** 
Haka suka shafe kwanaki biyu a gidan, ba fada, ba tashin hankali, yanzu Umm 
Adiyya dai ta koma Ummunta, ba ta cewa uf-fam, asali ma daki ko falon sama ne 
suka koma wurin zamanta, da zarar ta dawo daga aiki, saboda ba ta san me za ta ce 
masa ba, idan ta yi la’akari da irin rashin mu-tuncin da ta yi ta zuba masa. 
Ga shi ya zo ya ba ta haKuri. Amma ai batun gaskiya ne, sun mata ba daidai ba, don 
haka fushinta yana kan hanya, sai dai kawai dole ne ta saduda, tunda abinda ya faru 
ya riga ya faru. Ba ta dai sake tambayarsa yadda aka yi komai ba, a ganinta babu amfanin sanin ma. 
A haKiKanin gaskiya lokacin da ta ga Zaid da wancan matar a ofis dinsa manne jikin 
juna, Karamar hauka ce ta kamata, ta rasa inda za ta sa kanta ta ji dadi, abu ne da 
ba ta taba kawowa ranta ba, a cikin dangi, idan akwai wandanda ake girmamawa 
ake ganin sun kama kansu to Zaid yana daya daga cikin ‘yan sahun farko. 
Musamman yadda Mama take kirarsa ‘Malam’, wasu kam ma a can Gombe sun zaci 
da gaske shi din Malami ne na addini, saboda kamun kansa da kamala, ga ilimin ma 
duk yana da shi. 
Lokaci daya wannan surar da ta dade tana gi-nawa a ranta na soyayyar Dan-uwanta 
kamili abin kwatance ya rushe, abin takaicin kuma matar da lullubinta na mayafi duk 
da bai faye kauri da girma ba, amma dai alamu sun nuna misulma ce matar da take 
manne a jikin sa tana kissing dinsa. Ko shi yake kissing din ma dai, oho? A lokacin 
ba wanda ta tsana sai shi. 
Amma kamar yadda ya fada ne, shi Dan-adam ajizi ne bai cika goma ba, ta iya 
yiwuwa jarabawarsa kenan a rayuwa, wanda sai ya dage ya yaKa kafin ya samu 
rahamar Ubangiji, domin wannan a idanun Allah babban alkaba’ira ne, koda ace ba
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG