NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 




MUN TSAYA 

Salma na kuka tace, “*Amma a gabanta naci alwashi na rantse fa Anti, zata dauke ni mai kuri.. Sa’a ta tare ta a fusace,“To dan kar ta dauke ki mai kuri, sai ki saka zare tsakaninki da dandaba ki janyo ya farde miki – ciki a gabanta, ko kuma maganar ta zo kunne Alhaji ya zo har gidan ya ci mutuncinki a gabanta ya kuma goyi bayan a gina mata kitchen din…Kawai sai Salma ta sake rafshewa da kuka.  Salma na ji tana gani Salmanu ya zo aka ginawa Husna kitchen da sabon kwanon rufi, aka yi ‘mata kantoci, bai bar gidan ba sai dab da magariba a gaban idonsa Husna ta shirya kitchen dinta sannan , yayi mata sallama ya tafi. Amma: kafin fitarsa sai da ya yar wa Salma magana a tsakar gida, ‘Idan mutum ya isa’ mai hukunci ina jiran . sarKar da zata daure ni ta kai Bamuda triangle ta jefa ni a hadiye”

*************

Washe gari da safe Salmanu ya kira Husna a sigar bokanta,Yau mijinki zai dawo”

ZAMU TASHI 

Yace mata. Muryarta a raunane zuciyarta na karkarwa tace masa, “Eh haka ne boka, wai zai dawo, amininsa ya sanar da ni”. Boka ya dan ja fasali sannan cikin muryar nasiha yace mata, “Ki yi hakuri ki ki sake karawa, in yayi abu ba daidai ba kar ki fusata, kuma kar ki bari kishiyarki ta gane damuwarki…” Cikin son fashewa da kuka tace, “Zan kwatanta Malam”. Bokan yace mata, “Har zuwa yanzu bai san da aurenku ba, duk yadda za’a yi ki dakatar da haduwarku in ya zo gida har sai ya neme ki da kansa, kar ki damu da kallon da kishiyarki zata yi miki ki yi hakuri wataran ita zaki kalla…”. Yanzu Husna ta sa kuka tace, “Wallahi ba ta da abin kallo Malam”. Salmanu ya ji dariya na neman kubce masa, wato ko Husna ta san Salma ba ta da abin kallo. Sai da yayi kokarin shanye

dariyarsa sannan ya tanka, “Ai bake zaki kalle ta ba, duniya ce zata kallar miki ita”. Husna ta share hawayenta don shirin fara sa wa zuciyarta dangana, ta ce, Www.bankinhausanovels.com.ng Shikenan Malain, ni babu abinda ba zan iya sadukarwa da Adamu ba”. Ya sake yi mata nasiha ita kuma ta yi masa godiya sannan suka yi sallama suka ajiye waya. Haka Salma ma ta kira tata bokar wato Sa’a, wadda ta taso almajirinta takanas ya kawo wa Salma tsubbace-tsubbacensu, ta turo mata bayanin ta waya. Adamu ya zama wani kayan gabas, kowa so yake ace shi ne da ragamarsa. Karfe sha biyun dare jirgin su Adamu ya sauka. Salmanu ne ya je dauko shi a mashin din Tanimu, karfe daya saura ya sauke shi a kofar gidansa ya juya, Adamun na zolayarsa, “Ka ga da na gyara wannan emtin dakin da kawai sai na sauke ka ka kwana a nan ka huta tafiyar daren Salmanu ya danka masa mukullin gidan da ya bashi’ajiya yana cewa, “Ka manta da alkawarin matarka Salma kenan, wadda tace kar na sake na je mata gida… ka shiga kawai, kana iya hutawarka gobe ma in yaso nabi kadin kayanka na karbo maka”. “Adamu yayi kasa da murya, “Sai kace gidan tsohonta ba”. Wani dadi ya mamayi Salmanu, ya hakikance ko ma meye sihirin Salma ya rage kaifi, ai addu’a ba karya bace. Da farin cikinsa yayi masa sallama ya Www.bankinhausanovels.com.ng tashi babur ya wuce shi ma zuciyarsa na bugawa, yana ta fatan Allah sa kar bugun farko Hauka ya sanya Adamu sakin Husna. Can cikin gida Husna ta gaji da fargaba taga in bata nemi tsari da ita ba, zuciyarta zata iya bugawa ta shiga uku, sai kawai ta fito don daura alwala _ta zo gaban Allah ta d’auke kewa. Fitowar Husna daga bandaki yayi daidai da shigowar Adamu cikin gidan yana sallama a nutse. Yayi turus ganin wata doguwar halitta ta fito daga ban daki sabanin `yar kumbubarsa. Husna ta dan tsorata amma lokaci daya jin muryarsa ya samar mata nutsuwa, sai dai maganar bokanta na fado mata sai tayi saurin amsa sallamarsa a firgice, kuma ta nufi dakinta da sauri ta rufe kofa. Wannan ne ya firgita shi kansa Adamu ya doshi Dakin Salma cikin azama ya bude ya shiga yana kiranta. Dama tana kwance a falo tana jinyar zuciyarta da take barazanar fashewa, in Adamu bai saki Husna yau ko gobe ba meye makomarta? Yau Husna wuni ta yi tana guma mata takaici, don kuwa kawayenta da yan unguwarsu sun wuni suna cika mata gida suna kuma warkajaminsu, kade-kade iri-iri tamkar a fadar Dujal. Dama ta dade da sanin Husna mutum ce ta mutane saboda fara’arta da kyautarta sannan da dalilin sana’ar dinkinta. Abinda ya kada Salma ta ji Www.bankinhausanovels.com.ng
Husnan na ccwa, to yanzu tunda ta yi muhallin kanta zata karbi tayin masu rokon ta koya musu saka da dinki. A razane Salina ta tashi zaune sakamakon kiran farautar da Adamu ya shigo yana yi mata, “Salma wacece na gani ta fito daga ban daki ta shiga can dakin”. Salma ta ji zuciyarta na neman kecewa amnia tana tattaro ta tana hadawa, “Wacce irin tambaya ce wannan?”. Ya tare ta cikin haki, “Kar ki yi wasa da numfashina Salma don Allah ki fada min. na ji abinda ban taba ji ba da ganinta, na ji zuciyata na shirin fadowa ta tarwatse duk da ban san ko wacece ba…”. Gigitarsa ya sa Salma ta fahimci aikin bokanta na tasiri a kansa, ta kebe baki tace “Amaryarka ce fa Husna, kwananta biyu a gidan nan yau, Alhaji ya ki yarda da ni cewa ka bar min sallahun ka fasa aurenta ya ki yarda da ni, dole so yake sai ka kyankyashe karamar bazawara”. Salma ba ta fahimci tunda ta ambaci sunan Husna Adamu ya fita daga hayyacinsa ba, sam bai ji wasu ragowar kalamanta na bayan sunan Husna ba, sai ganinsa ta yi yana wani irin numfarfashi ya doshi kofar fita daga falon nata, “Ina zuwa Sannan ya bace kamar walkiya. Salma ta tuma a kujera tana sakin ihun murnar an tafi sakin Husna, amma me? Ba ta dau wani dogon lokaci ba ta fahimci cewa Adamu gidan ya bari. Nan fa ta shiga tsoro da wasi-wasi, tun tana saka ran cewa tsabgogi ya tafi samowa ya zone amaryar tasa har samuwar awa daya ya tabbatar mata da babu lafiya, nan kuma idonta ya raina fata. Tun yamma salmanu ya cewa Tanimu, “Zai wahala yau ban kwana da Adamu a gidan nan ba”. Tanimu bai nemi ba’asi ba sai ya ce, “In haka ne yau a gidan nan zan kwana”. Adamu ba a hayyacinsa yake ba, don haka bai ga tsawon tafiyar ba yayi wa zawaciki tsinke a kafa cikin wannan talatainin daren a awa daya kacal. Bai damu da kwankwasa kofa ba ya kama katanga ya haura. Salmanu na jin motsi ya tashi Tanimu da ke bacci, “Kai tashi ka dauko mana ruwan sanyin nan da muka ajiye a kula, yau mu ne da fasa wa Adamu kankara a ka, ban ni na je na bude masa kofar falo”. Cikin tsananin mamaki Tanimu ya ce, “Kai wai ko da gaske ka zama bokan gaske ne? kace Adamu zai zo kuma gashi ya zo”. Salmanu ya wuce yana dariya yana cewa, “Ba wani bokanci, halin Adamu na sani sama da tafin hannuna” Adamu zai fara kwankwasa kofar kenan ya ji Salmanu na budewa, a rikice Adamu ya fara kokarin tara yawun da zai amsa tambaya idan Salmanu ya jefo masa, amma sai ya ga Salmanu na bude masa sai ya juya ba tare da yayi masa kwakkwaran kallo ba. Bayan sun shiga suka yi cirko cirko a tsakiyar dakin du su ukun. Daga bisani Salmanu ya doshi kula ya bude ya kamfato ruwan kankarar da ke ciki ya doshi Adamu yana cewa, “Adamu kanka hayaki yake kamar yana shirin kamawa da wuta, zo na kashe ma ita”. Adamu yayi kokarin yayi magana ya kasa, gaba daya harshensa ya sarke banda hawaye babu abinda ke zuba a idonsa, kawai sai ya durkushe gaban Salmanu, shi kuma ya kwara masa ruwan kankarar ya sake ciko kofi ya kuza . masa har sau uku, sannan ya ja shi gefe ya zaunar. Suka yi shiru har tsawon fiye da mintuna bakwai, dakin babu sautin komai sai sautin nishin Adamu wanda ke bayyana tsananin tashin hankalinsa. Ganin tsawon lokaci Adamu bai tanka ba ya sanya Salmanu cewa, “To ko zamu iya kwanciya in ya so da safe ma ji matsalarka?” Www.bankinhausanovels.com.ng Adamu ya taso masa da kuka da hayaniya, “Kana nufin ba ka san matsalata babe? ai tunda ka bude min kofa ba ka bi ba’asi ba na san ka san matsalata, ni gidan Radio ne da kake jiran sai na sake maimaita maka?” Salmanu ya daga hannu,  Na tuna, sorry na tuna, ka shiga ka tarar an aura maka yarinyar da ba ka so ko? Wannan ba sabon abu ba ne a wajenka, duk da wannan kuskurenka ne…” Adamu ya tare shi a fusace, “Kuskurena ne ta ina?”. Kai tsaye Salmanu ya amsa, “Da ka tafi ba ka sanar da Alliaji cewa ka fasa auren ba”. Ya sake tasowa Salmanu, “Kai ba ka san na fasa auren ba, in ba ma ka shirya min mugunta ba don me ba ka aureta ba?”. Salmanu ya kalle shi ido cikin ido yace masa, “Don ba ni take so ba kai ta ke so! in mace ta gwada min irin son da wannan yarinyar take gwada maka, na rantse maka da Allah sai na nuna mata hallaci na gatanta ta sama da da ko wacce mace da mijinta ke sonta… ni dan halak ne Adamu, komai kankantar alkhairi ba na manta shi…”. Hawaye suka sake wanke wa Adamu fuska, “Ni ne ba dan halak ba Salmanu, fadi ka Www.bankinhausanovels.com.ng kara-.
Salmanu ya basar yana cin magani yace, “Kuma dai”. Fuskar Adamu ta kara kwadancewa da damuwa, “Sannan in ma ba an so kuntatawa rayuwata ba, yanzun nan Salma ta fada min babu inn yadda ba ta yi da Alhaji ba tana sanar da shi cewa na fasa auren amma ya ki gaskata ta…”. Cikin tabe baki Salmanu ya ce “To wannan mutum ce da za’a karbi shaidarta? Wata agwagwa da ita kawai”. Adamu ba ya cikin hayyacinsa, kawai sai ya kundumawa Salmanu ashar, zai cigaba da surutai Salmanu ya tare shi, “Kai ji nan mana, kar ka cika ni da hayaniya, in auren dole ne ba bakonka ba ne, da wannan da wancan duk babu banbanci, ba ka so kuma ba ka nan aka yi maka„kuma in an maka kana rikewa da kyau, dalilin rikewar kai ka sani, mu dama haka muke so, amma dai yanzu ni ka sama min lafiya ka daina zagina, in ma zaka zage ni ka tafi bayan idona ka zage ni kamar yadda ka bar bayan idon Hajiya da Alhaji ka zo gabana ka zage su lokacin da suka aura maka Salma…”. Lokacin Tanimu ya sako baki “Gaskiyarka Salmanu, in ya wulakanta Husna Www.bankinhausanovels.com.ng ko ya tozarta ta duk dai Iyayensa ya tozartar tunda su suka ga kamar sun isa da shi baya nan suka yi masa aure, fakat!” Yaja bargo ya fara kokarin kwanciya, Salmanu ma haka yayi, sai suka bar Adamu yana ta faman zage—zage yana hayaniya, har dace musu ba zasu cika masu wa’azi ba sai ya gan su kan turmi a tsakiyar kasuwa. Babu wanda dai ya kula, illa Salmanu da ya himmaci Tsinewa Salma wadda ta sa kibiyar zalunci ta huda wa abokinsa ruhi kowa ya ga abin nan da yake an san ba ya tare da hankali. Kafin safiya zazzabi ya kwantar da shi, don haka a nan ya wuni, babu wanda ya damu da kora shi gidansa. A ranar ma aikin jummai ne babba a cikin ayyukan da suka yi. Wancan satin da suka ce ta dawo ta dawo din sai aka shirya mata yaudarar cewa, “Kafin ta gana da gwamnan aljanu mai neman aurenta, sai ta nemi wasu kayan saki da wani turare wanda zata sa ranar da zasu gamu da aljanin, kudin kayan da turaren yana kai wa dubu dari biyar zuwa bakwai, in ba ta sa wannan kayan ba to ko aljanin ya zo ganawar ba zai iya ba ta kudin auren nan da yayi mata alkawari har milyan hamsin ba. Jummai idonta a rufe ta ci aiwashin nemo Www.bankinhausanovels.com.ng kudin duk inda yake, in da ta bazama rance har da daga wani karamin gidanta ta siyar, shi ne a yau ta kawo kudi dubu dari bakwai cif wanda za’a siyo mata kayan gayun aljanu da turare. Salmanu bai bar ta haka ba sal da ya sake tsiro mata wata tsirfar, taje sati guda da kwana hudu zaki dawo, ki tabbatar kin ciko jakarki da kudi, wanda zaki rabawa yaran gwamna„ zaki kara kima a idonsa don kin san ko su ma Aljanun suna son manyan mutane, in an ce ke karamar macace jikinsa zai yi sanyi, kuma zai ji kamar bai cancanci azurta ki ba”. Jikin Jummai a sanyaye tace, “Haka ne kam Malam, don ko ni bana son karamar harka, matsalar kudin ne ba ni da su”. Salmanu yayi fuska ya ce, “Sake nemo rance zaki yi, ban da abinki ke da zaki yi arziki duk ba sai ki biya su ba”. Ta ji wani karfin gwiwa ya dake ta, da sauri ta mike tana cewa, “Tuni ma, ai ko da rufin baki sai na samo rancen, nima ba da rufe min bakin aka karbe min duk arzikina ba ba don Allah ya kawo ni wajenka. nake shirin farfadowa ba”. “Kike shirin macewa gabadaya dai”. Salmanu ya fada a ransa, amma a fili sai ya bita da ido har ta bace. Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu ya ga Adamu na gyara wajen kwanciya zai kwanta, ya ce masa, “Ni fa ban gane maka ba”. Adamu ya dago cikin rashin hayyaci ya dubeshi,
“To hayatu, ina fatan ba wani daga hankalin zaka yi min ba…” “Haba sai na sake daga maka wani hankalin ban da wanda kake ciki?” Adamu ya dan yi nishi, “Hnm!” Sannan ya mayar da kai ya kwanta. Salmanu yace, “Allah sarki, yanzu kiyayyar Husna ta shafi Salma kenan? Dalilin kin Husna ka zabi ka kauracewa Salma ma?”. Adamu yayi shiru bai tanka ba, amma fuskarsa tana nuna alamun rauni. Sun jima cikin shiru dukkansu, sannan babu zato babu tsanunani suka ji Adamu na shasshekar kuka. Tanimu da Salmanu suka dubi juna, cikin su babu wanda ya tanka. Sai da Adamu yayi abinsa ya ishe shi sannan ya dago ya dubi Salmanu, “Wai wa yace maka ba na son Husna ne?

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *