UMM ADIYYAH CHAPTER 22 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 22 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA

Zaid yana daya daga cikin ‘yan sahun farko.
Musamman yadda Mama take kirarsa ‘Malam’, wasu kam ma a can Gombe sun zaci
da gaske shi din Malami ne na addini, saboda kamun kansa da kamala, ga ilimin ma
duk yana da shi.
Lokaci daya wannan surar da ta dade tana gi-nawa a ranta na soyayyar Dan-uwanta
kamili abin kwatance ya rushe, abin takaicin kuma matar da lullubinta na mayafi duk
da bai faye kauri da girma ba, amma dai alamu sun nuna misulma ce matar da take
manne a jikin sa tana kissing dinsa. Ko shi yake kissing din ma dai, oho? A lokacin
ba wanda ta tsana sai shi.
Amma kamar yadda ya fada ne, shi Dan-adam ajizi ne bai cika goma ba, ta iya
yiwuwa jarabawarsa kenan a rayuwa, wanda sai ya dage ya yaKa kafin ya samu
rahamar Ubangiji, domin wannan a idanun Allah babban alkaba’ira ne, koda ace ba

 ZAMU TASHI 

har zai iya aikata abinda zai kai shi gayin babban a cikin mutane. Cikin ofis dinsa, to ai tamkar yana aikata dayan kenan. Abinda an ce kan ka aikata shi, sai an zare maka imani na wannan lokacin da ka ke
cikin yi. Wannan abu ba Karamin girgiza mata duniya yayi ba. Ya ce ya daina, yaya aka yi ta san gaskiyarsa kenan? Ta yi nisa a saKe-saKen abubuwan da suka faru a tsakaninsu, ba ta san lokacin da
ya shigo gidan ba, sai sallamarsa ta ji a cikin falon sama, inda ta mayar wurin zamanta a gidan .
Zama ya yi a kujerar da take kallon tata, “Ke ba kya fita ne kullum a sama kamar tsuntsuwa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ta dan yi, “Ko a gida ba na fita ai, haka na saba.”
Kallon da ya yi mata ne ya sa ta jin kunya, saboda ta san ya san tana zama a Kasa, amma abin da bai sani ba, shi ne, don shi take zaman, don ta ga dawowarsa daga aiki ko ta ga giftawarsa a cikin gidan, saboda ba kasafai samarin gidan suke hawa
sama ba, sai ya zama dole, wannan tsarin gidan

Abba ne. Wataran dai ina dan zama, amma ba sosai ba. Kuma ban saba zama da kai ba.” Adiyya kenan, to yaya za ayi ki saba da ni, bayan ki na guduna? Ai sai kin zauna dani ne, za mu saba, ko ba haka ba?”
Gyada kanta ta yi, wani dadi ne ya ratsa zuciyar Zaid, bai dai bata tunani ba, dama hakan take da gaske, shi ya Konata har ta bayyana wancan bangaren nata mai fushi da tabara da tsiwa. Ba abinda yake jin dadin gani irin kyakkyawar fuskarta.
“To ba ni labarin abinda ki ke karantawar, tunda ni ba za ayi hirar da ni ba.” ‘Dago idanunta ta yi ta dan dube shi, “Ni ban ce ba zan yi hira da kai ba, me zan
fada maka to?” Shiru ya yi cikin alamar nazari, Www.bankinhausanovels.com.ng “Uhmm, kin ce ba kya so na, ban labarin samarinki   na da.” Gwalo idanu ta yi cikin tsoro da mamaki, “Samarina kuma?” “Eh mana, kar ki ce min kuma ba ki da su, ina ganin dogon layin da suke ta yi a Kofar gidan Abba, ba su san duk ke ba tasu bace.” Murda labbanta ta yi tana boye murmushin fuskarta, cikin alamar tsumewa.
Idanunsa suka kai kan labban nata kafin su koma kan idanunta. “Su hudu ne fa, amma dai duka ba su yi min ba.”
“Haba dai ki na nufin duk tara su da ki ke yi kawai ba wanda ya dan kwanta miki? A cikin su da za ki zabi wani, ki turo gida waye za ki tura?” Uhm… Akwai wani yana da hankali da kirki sosai, kuma yana sona kamar ba gobe…” Daga gira ya yi ya ce, “Yana sonki?’’ “Au, ya soni kai zan ce, kuma yana da Www.bankinhausanovels.com.ng hakuri…” Take Zaid ya yi da-na sanin dago wannan bangaren hirar tasu, sai yake ji kamar ita ma har yanzun son wancan din take yi. Wani Kullalen abu ne ya murda a Kirjinsa. Amma sai ya yi mata murmushi. “Yanzun yaya ya yi da ya ji labarin aurenki?” Yaya zai yi kuwa, banda ya yi haKuri, ni ban sake magana da shi ba.” “Meye ki ke kallona haka, ni ba ni nayi masa sakiya ba, da ya dage ya aureki kan na aureki shi kenan, amma tunda har na riga shi, anyi an gama kenan.” Kada idanunta ta yi ta yi fari da su.
“Adiiyya!” Zaid ya ambaci sunanta cikin wata siga mai shiga jiki. “Na’am?” “Kin san me ki ke min kuwa?”
“Me na yi kuma Yaya Zaid?” Ta tambaya cikin rashin fahimtar inda ya dosa da maganarsa Runtse idanunsa ya yi, ya dan saki hucin numfashi sannan yace, “Zo kiga wani abu.” Tashi ta yi ta bi bayansa zuwa Kofar da ya bi da ita, Kofar ta bulla zuwa waje ne, can farfajiyar na dauke da kujerun zama guda biyu da dan teburin gilas tsakiyarsu, sai furanni Kanana a jere masu kaloli daban-daban, gefe kadan kuma
kujerar lilo ce ta zaman mutum biyu mai rumfa. Filin yana kallon bayan gidan nasu. Suna fita, sauran jan hasken rana da ya rage ya sauka a kansu, tamkar an kunna Kwan gulob, idanunta ne suka kai kan rana, inda take daf da faduwa. Ta yi nisa cikin kallon ikon Allah, da yadda ya Kawata halittarsa cikin cika da haiba gami da kamala. Yake kuma juya al’amuransu yadda Ya so, har ma ba ta kula da lokacin da Zaid ya tsaya a bayanta ba, numfashinsa ta ji yana sauka kan wuyanta, a hankali, ga wani sansanyar Kamshin da ke fita daga jikin Sa. “Kin ga yadda ranar nan ta dauko gangarar faduwa? Abinda ki ke min kenan Adiyya. A hankali, son ki ya bi jikina, ya dauke hankalina, har ya kai ban san lokacin da ya
gama mamayeni ba, ya kasance ko wane motsina, ina yinsa ne tare da ke a cikin raina, ko a sani na ko a rashin sani na, ko a farke, ko a barci.” Shiru ya yi na ‘yan wasu daKiKai, yana kallon faduwar ranar ta saman kafadarta. Umm Adiyya kam, da mutum na narkewa ranar sai dai a kwashi ruwanta. Labbansa
ta ji daidai Kasan kunnenta, ya sumbaceta sama-sama, ya dan dauki lokaci a haka, abinda za ta kwatanta shi da ‘lingering kiss’, da a ce ta san rabe-raben sumba. I love you, my Twinkle.” Ya numfasa. Hawaye ne ta ji sun cika mata idanu, ba ta san daga ina su kuma suka zo ba. Hannu ya sa a kafadunta ya juyo da ita suna fuskantar juna, “Ina sonki Adiyya, ke a gareni ba hadi bace daga iyayenmu, ke shiryayyan al’amarine daga Allah gareni, ina sonki
tun ban san lokacin ba, na kasance ina hana kaina yarda da abinda yake gaba na, a tunanina bai kamata ba, a tunanina ba ke bace a raina. Na hana kaina yarda da hakan a lokuta bila adadin, saboda a Www.bankinhausanovels.com.ng tunanina zai kawo raini da KasKanci a tsakaninmu, a rashin sanina, shi wannan al’amari na zuciya, babu raini babu KasKanci. I’ve loved you forever, tun kan ki san meye kan ki, in fact lokacin da na hadu da su Femi, ana ta tunanin sunan kamfaninmu ke ce na farko da ki ka zo min raina, ADIYYAH! Hence, Adiyya Zubair ya bada AZ. You’re the bane of my existence, komai na ke yi da ke a raina.” Mamaki ne ya cika Umm Adiyya, ta yadda ba ta taba tsammani ba, wato tun ma kan ta fara haukarta na son Zaid, shi tuni ma yana sonta, amma son girmansa da jan ajinsa ya sa ya Kware su, tuntuni! Ba ta san me ya shiga kanta ba, ba ta san me zaiyi tunani a kanta ba, ita dai kawai abu daya ta ji ta yi, kuma ta yi shi a take a lokacin. Rungume shi ta yi, ta ma manta a waje suke, duk da a kebe ne saman balcony din da bishoyiyin mangwaron da ke bayan gidan, amma a lokacin ta ji ta a jikin mijinta kawai shi ne burinta. Hannu ya sa ya riKota jikin sa da kyau, ya rungume matarsa, kamar zai tsaga jikin sa ya maidata, don so. Ba shiri ya saketa, da ya ji wani radadii ya isa hannunsa, zare idanu ya yi yana kallonta a kidime. “KE! Wallahi zan hanaki karanta littafan vampires, L.J Smith din koya miki cizo tayi?” Oh Ashe yana lura da takardun da take karantawa. Wani dadi ne ya lullufe ta.
Juya idanunta ta yi ta ce, “Me ya sa tuntuni ba ka fada min ba, me ya sa kake ta ba ni wahala?”
“A’a ke da ki ke da mai sonki mai haKuri da hankali da kulawa, ni kuma meye a cikinsu da za a kalleni, bare a gane ina nawa son?” Kara make shi ta yi cikin salon so a kafadarsa, “Allah Yaya Zaid ka gama da ni.” Ta
fada a shagwabe. RiKo hanneyenta ya yi ya hada da nasa a saman Kirjinsa. “Ke ma kin gama da ni Adiyya. Allah ya bar min ke.” Fararen idanunta yake kallo da suka yi narainarai, gashin idanunta suka sake fita,
tana kiftasu, a hankali ya duKa daf fuskarta.
Ladanin masallacin unguwar ne ya kwada kiran sallar magariba, wannan ya sa ya tsaya cak! Umm Adiyya ta hadiyi wani abu, ta sadda idanunta Kasa, shi kuwa ya shafa gefen fuskarta. “Mu shiga mu yi shirin sallah ko?” Kai kawai ta iya gyada masa. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya-Salam! Ta rasa yadda za ta yi da bugun zuciyarta, ta tabbata ba tantama Yaya Zaid ya jiyo yadda Kirjinta ke bugawa dazu, amma a halin yanzu, ba ta damu ba da tonuwar asirin zuciyarta, tunda har shi ma hakan yakeji game da ita.

**********

Tana azkaar bayan ta idar da sallar maghriba ne, ya shigo gidan, a kan sallayar ya sameta. Wannan ya sa ya samu wuri ya zauna a gefenta, shi ma yana azkaar din harta idar. “Me ki ka roKa a sallarki?” Ya rada daf da kunnenta. Wannan ya sa ta yi saurin
sadda kanta Kasa, ta ga alama Yaya Zaid bai san me yake haddasa mata bane idan yana wannan shishige matan, ga wata sabuwar soyayya dal! Mai zaburarwa da take ji take Kara cika mata zuciya game da shi, idan yana irin wannan, sai take jin wani
irin sa’a take da shi har Allah ya juyo mata al’amura suka kasance haka? Ashe da duk shiririta take yi. “Ba komai, kawai azkaar na yi.” Ki rinKa mana addu’a a cikin sallarki. Allah yana son bayinsa masu roKonsa, kin ji ko?” Kai ta gyada masa, duk da tana yi din kawai ba ta jin fada masa hakan ne. Wace irin addu’a za ki mana to?” “Ta gamawa da duniya lafiya cikin imani, da kuma ta kariya daga rudiin rayuwa da
shaidian, sai kuma na samun nasara duniya da lahira ga mu da kuma iyayenmu.” Hmmm, addu’o’i ne masu kyau wadannan, sai dai kuma na gama gari ne, me Za ki roKarwa mijinki?” Ya-Salam. Allah Ya sa kar zuciyarta ta tarwatse, yaya za ayi muryar mutum ta kasance mai cike da ilhama, da zurfi da dadi ga kuma rashin gargada? Uhm, to ai kai ma ka na cikin wancan addu’o’in.””A’ah wai dai na ga mace ai tana yiwa mijinta wannan special addu’ar shi kadai ne,
me za ki roKa min?” “Allah ya dawwamar da ni a zuciyarka, ya ba ka ikon riKe ni cikin kyautatawa, ya
kareka daga dukkan wani sharri, ya kuma hadaka da zuri’‘arka a aljannah.” Hannu ya sa ya dago fuskarta da take ta faman boyewa saboda ita kanta ta ji nauyin maganganun. Matsawa ya yi kusa da ita ya sumbaci saman goshinta, hade da fadin,
“Allah ya amsa miki addu’o’inki, ya biya miki dukkan buKatunki na alkhairi, duniya da Www.bankinhausanovels.com.ng
lahira. Allah Yai miki albarka, Adiyyata.” Yanzu kam ba tantama ta ji zuciyarta ta kumbura a Kirjinta, saura kawai ta fashe, idan fashewar zuciya abu mai kyau ne.Dama da gaske haka amare suke da kunya ko kuwa dai tawa ce ta daban?” “Yaya Zaid, don Allah ka bari.” Ta fada a shagwahe hade da karya wuya.
Abu na gaba da ta ji kawai, shi ne fuskarta a tafukan hannun Yaya Zaid, inda ya shiga sumbatarta a hankali. Da farko numfashinta ne ya tsaya cak! A lokacin da numfashin ya dawo kuma ta kanta ya dawo, ba tantama saboda wani jiri da ta ji ya
kwasheta daga zaune, wani luuu! Ta ji kanta yana mata. Sai da aka dauki tsawon mintoci, sannan ta fado duniyar da suke. A hankali ya sake ta, inda wani numfashi ya kubuce mata, hada idanun da za su yi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *