RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Hafsat ta yi murmushi tana ci gaba da ninke kaya, “Umma sai you kika kula’? Ai hatta idanun Nasreen irin naki ne. Ki dubi Naufal da kyau ki dubi Yaya Haidar kamanninsu ya baci. Abin ya .dade yana bani mamaki, amma da yake zama wuri daya yana sauya kamanni sai ban damu ba.” Umma ta dafe kirji da karfi tana cewa, “Ko dai Abbanku ne yayi cikin yaran nan? Wallahi ban yarda da shi ba.” Hafsat ta dubeta da mamaki, tace, “Umma me ya kawo irin maganar nan kuma? Ai ba da zuri’ar Abba suke kama ba, da zuri’arki suke kama.- Umma ta zazzaro mata manyan idanunta tana dubanta, “Kaf zuri’ata basu san komai ba, in banda Alqur’ani da Hadisai, me yasa za ki ce da zuri’ata suke kama? Kai bana son maganar nan abarta kawai.” Umma ta fada zuciyarta cike da tunani. Washcgari suka tattara suka koma Abuja, suka bar Umma cikin tunani da tarin damuwa. Kwanaki biyar ta dauka tana amfani da magungunan ta ji sauki sosai kamar bata taba yin wata lalura ba. Zakiyya kuwa ta rantse in dai
ZAMU TASHI
tana raye ba za ta taba barin Nasreen su kebance da Sultan ba. Shi ma kuma bai sake nemanta ba, yana matuKar jin tausayinta yana son sai ta sake Warwarewa Sosa.
A Katon dakin taron wanda yake mallakin Ashmaan ne, a cikin katafaren kamfanin su. Dukka jaruman ne zazzaune, suna Sauraren irin ruwan masifar da Sultan yake zuba masu babu ji babu gani. Sai yanzu ya dan tsagaita tare da sake kallon su daya bayan daya, ya ci gaba da cewa, “Abin ya ishe ni haka! Dukkanku nan hukumomi ne masu zaman kansu, akan me matsalata za ta gayareku fitarwa? Me ya sa za ku ci gaba da jan abin da tsawo? Ina Kara roKonku da ku janye ku bar ni in yi abubuwana da kaina, a kwanaki biyu rak! Zan samo wanda ake nema.”
Dukkansu suka dubi juna, = sannan BarristerTajuddeen Abdulsalam yace, “Fushin nan ya yi yawa, duk wurin nan babu wanda bai yi nasa lokacin ba, in dai a kan fushi da zuciya ce. Amma da yayin mu ya Kare dukkanmu nan mata su suka sauya mu daga irin yanayin da muke, kai me yasa ba zaka canzu ba? Soja ma ya canza tasa rayuwar bare wani dan sanda?”’
Sultan ya dube shi ido cikin ido ya ce, “Kayi kadan ka raina dan sanda ina wannan wurin.”
Muhbub ya hada rai ya ce, “To ya ishe ka Tajjud, ka kama kanka tun wuri, dan sanda ya wuce saninka.”
Khamis ya dube su ya tabe baki yana ci gaba da latsa wayarsa. Yace “Kanku ake ji.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya fizge wayar hannunsa yana dubansa rai a bace, “Me zai sa ka dinga latsa waya ana magana mai mahimmanci?” Sai a lokacin ya dubi wayar yaga an rubuta Alhaji Na kan titi. Ya jujjuya wayar yana tunanin inda ya taba jin sunan.
Khamis ya fizge wayarsa yana aika masa da mugun kallo, “Malam ina ruwanka da wayata? Ni nan aiki aka bani kuma gashi ina yi, amma ka tsaya sai hayaniya kake yi mana. Zafin kanka yana gab da sauka, in dai da ‘yar mutan Borno ka zabi tafiya.”
Yamutsa fuska ya yi yi yace, “Ku kuka dauki ‘yar mutan Bornon wata abar yabawa, ni ba ita ke gabana ba, mahaifin Nasreen nake son in hukunta shi.”Ashman da yake ta latse-latsen Laptop ya dago yana dubansa, sannan ya ce, “Ka dai bi a hankali tun kafin tauraronka ya sauka daga gun ‘yar mutan Borno. Wai ma da kake cewa zaka hukunta mahaifin Nasreen, ka mance surukinka ne?” Sultan ya furzar da huci mai zafi, yace, ‘““Nayi rantsuwa ko jinina na kama da laifin nan sai na hukunta shi, dai-dai da laifinsa. Ni cinnaka ne, wanda bai san na gida ba.”
Dukkan su suka kafe shi da idanun su kamar masu jin tausayinsa. Shi kansa yasha jinin jikinsa irin kallon da suke yi masa. Duk cikin su aka rasa mai Karfin halin da zai yi masa bayani, dole suka daga tattaunawar zuwa jibi. A gajiye Sultan ya dawo gida, a falo ya sami Nasreen ta ci kuka idanunta sun kumbura. Tana ganinsa ta dago dara-daran idanunta ta sauke su a bisa nasa. Mamaki ya kama shi, ya tabbata babu wanda zai aikata mata hakan sai Zakiyya.
Babu tambaya ya mike cikin zafin nama zai wuce dakin Zakiyya. Nasreen ta kamo hannunsa cikin sanyin jiki, wanda yasa dawowa da baya yana dubanta. Wasu sabbin hawaye suka wanke mata fuska. ““Nasreen raina yana baci idan kina Zubar da hawayen nan. Ki daina kuka na gaya maki yana daya daga cikin abinda na tsana in ga kina yi Www.bankinhausanovels.com.ng
Sharce hawayen fuskarta ta yi ta fara magana cikin rawar baki, “Dee. Su waye iyayena? Ka gaya min da gaske cikin shege mahaifiyata ta yi ta haifeni? Yanzu ni da Naufal ‘ya’yan shegu ne? Baka sona Dee, baka sona! Da har na _ tambayeka~ gaskiyar kasancewar mahaifiyata mara addini, ka Karyata hakan, har kayi min rantsuwa mahaifiyata ta bar gidan duniya tana rike da addinin Allah. Kuma yau dinnan ba sai gobe ba, zan bar maku gidanku, zan bar zuri’arku, zan daina jin gori daga bakunan ‘yan uwanka.”A lokaci guda ta saki hannunsa tare da dire maganarta cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa.”
Maganar ta zo masa a bazata, a kuma irin lokacin da bai taba zato ba. Sunkuyawa ya yi kusa da ita yana dubanta cike da mamakin furucinta, ‘““Nasreen kika ce bana sonki? Kin yi gaskiya da kika iya kallon Kwayar idanuna har kika gaya min Kalmar bana sonki. Nasreen na fara sonki ne tun kina cikin mahaifiyarki, a lokacin da baki zo duniya ba, bare kisan wahalar
zaman duniyar. A_ sanadiyyar in tsamo mahaifiyarki daga halin da take, har yau dinnan ban sake zama inuwa daya da mahaifiyata ba, a lokacin ne kyakkyawan ginin da mahaifina ya dade yana yi domin inganta rayuwar iyalansa ya wargaje. Ginin da har yau ba a sake tada gininsa ba, domin kuwa gyaransa sai Allah.
“Muna rayuwa cikin son juna, wanda har ta kai dangi suna alfahari da mu, suna yaba mana, suna kwatance da hadin kan mutanen gidanmu, rana guda, ranar da na hadu da mahaifiyarki wannan kwatance ya rushe. Tun daga ranar na zama bare a cikin gidanmu, tun daga ranar ‘yan uwana Hafsat da Haidar suka ware ni kamar ba dan uwansu ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haka na taso cikin maraicin ‘yan uwa. Mahaifina kadai ke bani goyon baya. Duk kina nufin hakan ba so ba ne? Tun zuwanku gidanmu ke da dan uwanki, mahaifina da matarsa Umman mu, suka raba hanya, ya kasance mahaifiyata tana yawan saba masa. Duk ni ne sanadi saboda na kawo ku cikin rayuwar gidanmu. Ra’ayina ba aikin dan sanda bane, amma saboda in sami daman aiwatar da bincike akan wanda ya yi sanadin zuwanku duniya, na sauya ra’ayina zuwa
aikin dan sanda. Duk kina nufin ba sonki nake ba? Ban taba yi wa iyayena gardama ba, haka sun jima basu ga hawaye a idanun dan su ba, sai a dalilin mahaifiyarki. Har gobe ina kallon Anti Saudat a idanuna, har gobe ban daina kai goshina Kasa ina yi mata addu’a ba, haka na kasa kallon tarin hotunanta da suka jima a hannuna, sai dai na ba abokaina domin su nemo abubuwa akanta. Mahaifiyarki musulunta ta yi, kuma har ta bar gidan duniya tana riKe da addinin gaskiya. Yanzu za ki ji dukkan abinda kike son ji akan rayuwarki.” Ya Karashe maganar cikin raunin murya, wanda za ta iya rantsewa bata taba jinsa da irin muryar ba. .
Nasreen ta dago cikin wasu hawaye masu tsananin zafi, tana girgiza kai. Idan da a ce bakinta zai iya furta magana a yanzu, da ta roki Sultan ya yi shiru da labarin da yake son bata, domin wannan ma kadai ya gigitata, ya tafi da dukkan sauran Karfin halin da ya rage mata. Tausayin kanta, tausayin Naufal, tausayin Sultan, su suka fara buga tsere a cikin zuciyarta, suna Kara sa mata damuwa.
A yau ta Kara yarda, duk duniya babu mai son su da gaskiya irin Sultan. Kunyarsa ta Www.bankinhausanovels.com.ng
lullubBeta, saidai kuma me mahaifinta ya yi da har Sultan zai yi aikin dan sanda saboda shi? Tana da buKatar amsoshi masu tarin yawa daga bakinsa. Wannan karon hawaye da majina suke sauka daya idanunta zuwa hancinta, ga wanii irin gumi da ke tsattsafo mata, ta jiKe ta yi sharkaf. Sultan ya mike tsaye ya kwashe yadda aka yi har ya taimaka wa Saudat zuwa haihuwarsu da ta yi, har ya gangaro kan renon su da ya sha cikin wahala. Duk ya yarda ya sadaukar da farin cikinsa saboda nasu farin cikin.
.Tun Nasreen tana iya fahimtarsa har ta daina fahimtar komai, numfashinta yana kaiwa yana komowa. Ta tabbata sun gama tozarta a duniya, tunda har ya kasance aka yi wa mahaifiyarsu fyade aka samar da su a duniya. Haka babu wanda ya san waye mahaifin su. Tabbas sun tabbata ‘ya’yan shegu kamar yadda Zakiyya take ta nanata mata a kullum, wanda hakan yasa ta haddace sunan shegu, saboda yawan ambata mata da ake yi. Da Karfi ta riKe kanta, hakan bai taimaka mata da komai ba, domin kuwa a take ta zube a sume.
Sultan ya tsaya kawai yana kallonta, ya rasa ma me zai fara yi mata domin bata taimakon
gaggawa. Sosai yasa natsuwa a zuciyarsa hakan yasa ya tuna da ruwa, ya je ya dibo yana shafa mata a fuska. Da Karfi ta saki ajiyar zuciya, ta ware idanunta tana dubansa_ dishi-dishi. Hannunsa ta kama ta mayar bisa kanta da ke sara mata.
Cak ya dauke ta ya kai cikin dakinta ya kwantar bisa gado.
Zakiyya da ta gama leKen su ta saki dariyar jin dadi ta shige abinta.
Nasreen tana riKe da hannunsa, ta Ki saki, gani take idan ta saki zai tafi ya barta ne. A hankali take magana, “Dee, na yi mugun Www.bankinhausanovels.com.ng
– mafarki, wal… Wai… Wai… Mu shegu ne, an yi wa Mamana fyade, ta yi rayuwa a Karkashin mota, ta yi bara a titi, sannan wai, wai kakannina ba musulmai bane.. Mafarkin babu dadi Dee, babu abin sha’awa a cikin rayuwar mu, bana son mafarkin, kayi min addu’a kada in sake yin irinsa.” Wasu surutai take yi tana kuka.
Sultan ya yi danasanin gaya mata wadannan maganganun, bai taba tunanin Nasreen za ta tashi hankalinta kamar yadda ta tasa a yanzu ba, bai taba tunanin Nasreen za ta: fita hayyacinta haka ba. Yana nan zaune bai iya cewa komai ba. Kafin yasan abin yi zazzabi mai zafi ya shiga jikinta sai rawar sanyi take yi.
Hankalin Sultan ya sake tashi, ya kira Aslaf a waya ya gaya masa duk abinda ya faru, Aslaf ya ce, “Amma da ka sani da ka dinga gaya mata a hankali ne, domin yarinya ce Kwakwalwarta ta yi Karama da daukar irin wannan tashin hankalin. Bari Yumnah ta zo yanzu ta dubata.”
Sultan ya sauke wayar yana sake kai dubansa gareta, har yanzu ta Ki sakin hannun, duk da irin karkarwar da jikinta ke yi. Shafo kanta ya yi da dayan hannunsa yana tofa mata addu’a, “Baby za ki ji sauki kin ji? Ki yi hakuri ki rage damuwar nan kin ga kin tada min hankali. Wannan Kaddarar ba a kanki aka fara ta ba, haka agun Allah kin fi wasu wadanda suke cikin musuluncin, amma basu yin aiki da abinda addinin ya fada. Ke baki da laifi, mahaifiyarki ma bata da laifi, mahaifinki shi ne mai laifin. A wurina kinfi wadanda aka Haifa ta hanyar halas. Babu wanda ya isa ya tambayi Allah dalilin aiko da Kaddara. Sai dai ma mu gode masa a dukkan yanayin da muka tsinci kanmu.” Haka ya dinga yi mata kalaman lallashi, kuma yana cin nasarar wargaza dukkan damuwar da suka taru suka hanata zaman lafiya. Yumnah da kanta ta tuko mota ta zo har gidan, ta dubata tare da bata allurai.
A falo suka fito suna tattaunawa da Sultan, ta sake tabbatar masa kada ya yi nisa da Nasreen, saboda su samu jininta ya sauka. A zahiri ta yi hakan ne domin ta nesanta Zakiyya da Sultan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kwanan Nasreen biyu ta wartsake, a lokacin kuma sunan da Sultan ya gani a cikin wayar Khamis ya tsaya masa a rai. Tunani yake yi waye Na kan titi? Domin tabbas ya taba jin sunan amma ya rasa a in da ya ji. Wannan zaman da suka yi shi suka kira da zama na Karshe, sun tabbatar za su yi Kundunbala su gaya masa komai, haka dole ya ba su hadin kai wajen zartar da hukuncin da ya dace. Sai dai fa duk taron su a cikin dakin taron, babu wanda ya iya furta komai. Yadda suka yi shiru haka Sultan ya yi shiru, ya yi alKawarin ba zai ce masu komai ba, don wulakancin ya ishe shi hakannan. Wayarsa yake latsawa, sai ga kiran wayar Alhaji Mu’azzam yayan Umma. Cikin girmamawa ya dauka ba tare da ya nemi izinin kowa daga cikin dakin ba, kamar yadda ya saba. Daga cikin wayar yake magana, “Sultan ina son nemanka,
ana son a lalata min suna, kuma antabbatar min masu KoKarin aikata hakan, suna da kusanci da kai, Ashmaaan, wani mara kunyar yaron nan dan jarida, da wasu dai haka. Ina son ganinka gobe insha Allahu.”
‘ Daga kai ya yi yana kallon su Ashmaan, zufa na karyo masa, a lokaci guda mamakin fuskarsa ta Karu da Ashmaan ya amshe wayar ya bude muryar gaba daya sannan ya fara magana, “Ashmaan ba mara kunya ba ne, domin yana girmama na sama da shi, idan suka kasance masu girmama kansu. Ba za ka sami ganin Sultan kamar yadda ka buKata ba, haka kai baka da laifi + ko alama a cikin maganar nan, masu laifin dai suna nan zagaye da kai, wanda kai baka san suna » aikata barna da sunanka bane. Muna fatan zaka yi hakuri ka barmu muyi aiki a kan Alhaji Kabir ba akanka ba. Mun gode.” Sultan ya rasa abin cewa sai kallon-kallo ake yi. Al-ameen ya yi alKawarin zai cire dukkan wata kunya da shakkar yadda maganar za ta iso cikin kunnen Sultan, ya yi maganarsa, ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.”
Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.”
Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG