UMM ADIYYAH CHAPTER 43 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 43 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 



Ya dade zaune cikin motar, yana kallon gilas din gaban motar, shi bai fita ba, shi bai
tada motar ya tafi ba, can kuma ya kwantar da kansa kan sitiyarin motar, ya runtse
idanu, Kwakwalwarsa ta rabe kashi daban-daban da har suke neman hautsina masa
lissafi, wayarsa da ke ajiye a gefe ya ji tana ruri.
Ta yi da farko, har ta katse. Aka sake bugowa, hannu ya sa zai aga, nan take wata
zuciyar ta tunasshe shi. “Zaid me ka ke yi? Me za ka koma a rayuwarka? Bayan duk
lokacin nan da ka diba, ka na neman gafarar

Ubangijinka, bayan alKawarin da ka dauka, me za ka yi da Kazantar nan?” Daga wayar ya yi, numfashinsa na fita da kyar Kasa-Rasa ya ce, “Go home. (Tafi gida.)” Meye? Yaya za ayi ka ce na zo na sameka, sannan kuma ka ce…”
Hancinsa ya hura cikin Kosawa, “Just… ki koma gida. Kar ki sake kirana kuma.” Yana kashe wayar ya dago idanunsa, dai-dai lokacin suka sauka a kan motarta da ta Karaso cikin filin adana motocin, daga inda yake yana hangota, duk kyan da ta yi


a cikin matsattsun dinkinta na atamfa da kyan surarta, ta madubin tare rana da suke
manne a fuskarta, ba su Kawata masa ita ba, kamar a lokaci na farko da ya afkawa
wannan rudi na shaidan. Amma ya zama lalle ya je ya sameta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Balle murfin motarsa ya yi ya bude (Glove Compartment), sannan ya isa inda ta
tsayar da motarta, bai damu da me ganinsa ba a harabar Guest-in din. Kai tsaye ya
nufi inda take, ya bude motarta.
“Baby, yaya za ka ce na koma gida, kuma ai na zaci ba za ka zo bane.”
Kau da kansa ya yi gefe sannan ya ce, “Kuskure ne, it was a mistake. Kuma wannan
ne karo na Karshe da zan miki magana a matsayin dan-uwanki musulmi, ki taimaka
ki bar wannan rayuwar. Ki na da darajar ki a matsayin “ya mace, ki na da abin yi, ba
abinda ki ka rasa, abinda muka yi a da, ki ajiye shi a matsayin kuskuren rayuwarki, ki
koma ga Allah ki tuba. Aiki ne ya ajiye ki a garin nan, ki yi shi, ki rike mutumcinki.
Don Allah, ba ki san gida nawa ki ka rusa ba, saboda I’am very sure, ba ni kadai
bane, amma ga wannan ki riKe, don Allah ki kama kanki, ki koma gida wurin
iyayenki, ki bar rayuwar nan. Za ki iya aiki, za ki iya kasuwancinki, amma ba sai kin
bar gaban iyayenki ba. Wannan ba mutumcin ki bane, a matsayinki ta “ya mace,
bare a matsayin musulma kuma. Idan ki ka mutu a wannan halin, me za ki ce da Allah?”
Fareeha ta hura hanci cikin takaici da jin haushi matuKa, ’Wa’azi na kiraka ka min
ne? Ai na san da Islamiyya a garinmu na baro can. Idan an bata maka rai a gida, za
ka zo ka sauke a kaina da wani wa’azinka, dama ina cike da kai, ranar da kayi min
wulakanci a ofis, na mayar yanzu hakuri ka zo ka ba ni, da alama wannan matar Www.bankinhausanovels.com.ng
taka ta gama kanannade ka a yatsunta, gaba daya babu kanka, tun da ka yi aure.”
Zaid ya cije hakoransa cikin KoKarin danne fushinsa, kar ya yiwa Fareeha illa. “Yes,
ta kanannadeni, saboda babu natsuwa da kwanciyar hankali da gamsuwar da ta kai
ko ta isa ta wuce ta alaKar aure. Shi ya sa na ke baki shawarar ki jarraba ki gani, ko
za ki amfana da shi.”
Mika mata takardar cek din hannunsa ya yi, “ki cire abunda kike so. Amma
Fisabilillahi ki koma gida gaban iyayenki, ki san me za ki yi da sauran rayuwarki. I’m very sorry.”
Yana juyawa, hawayen idanun Fareeha suna zulmiyowa daga idanunta. Take ta ji
wani abu ya jirkice daga rayuwarta, jikinta ya mutu murus! Lumshe idanunsa ya yi, ya koma cikin motarsa ya tayar ya tafi, daga rayuwar da
baya fatan ya sake waiwaya, ko yaya, bayan ya kasance yana da matarsa a gida.
Duk da rashintan ne ya nemi ya maida shi ruwa. Musulunci bai bar shi kara zube ba,
ya tanadar masa yadda ya kamata ya yi. Yana kuma iya KoKarinsa, amma yau idan
Umm Adiyya ba ta amince da buKatarsa ba, bai san yadda zai yi da rayuwarsa ba.

**********

Da Issha ta shiga ta dafa Indomie a kicin don yunwan da ke nukurkusanta, a nan ta
zauna ta ci, sannan ta dauraye abubuwan da ta yi amfani da su. Ta gama hadawa
ne, ta rufe windon kicin din ta kashe wuta, ta haura sama. Gabanta ne ya fadi ganinsa a tsaye a dakin.
“Me ka ke yi a nan?” Tambayar da ta zo mata kenan.
“Last I checked, nan gidana ne ai, ina da damar shiga duk inda na ke so.” Ya fada yana mata kallon tarr!
Wani abu ne ya toshe mata maKoshi. Ta yi Kwafa, “K! Yau kuma gorin gida ne ya tashi? Dadin abin ma dai ba daga jeji aka tsinto ni ba. Kuma ruwan da na sha, na rayu shi masu gidan suka…” Ba ta tashi sanin inda kalmar gaba ta maKale ba, saboda wata irin Www.bankinhausanovels.com.ng runguma da Yaya Zaid ya yi mata, ya hadata da jikin wardrobe din dakin nata. Yana mata magiya, tana yakice shi, cikin fushi. Har hawaye sai da ya yi.
Amma yanayinsa ya tsoratar da Umm Adiyya.
Ta razana sosai, saboda wannan wani bangarensa ne da ba ta taba gani ba. Gaba
Daya ya hautsine mata. Kuka ta shiga yi masa, tana roKonsa da ya bar ta. Amma
tamkar tana ingiza shi ne ma, don duk wani hakurinsa ya Kare. Ta kai shi bango.
Don haka yau ba daga Kafa. Sai da ya gama abinda zai yi da ita, ya fice daga dakin nata.
A nan dakin Umm Adiyya ta yi kuka har ta gode Allah. Ta yi da-na sani bila adadin kan sha’anin Yaya Zaid, daya bayan daya ta sare a kan al’amarinsa. Da mace na sakin kanta, a take a lokacin ko numfashi ba za ta Kara ja ba za ta yakice kanta
daga auren Zaid. Kila ma saki uku Kwarara za ta yi masa. Tashi ta yi ta kimtsa jikinta. Tafi awa guda a cikin shawa tana kuka. Daga Karshe ta yanke shawarar abin yi.

*******

Tun da ya bar dakinta ya wuce nasa dfakin, ya sulale a Kasa ya yi kuka kamar
Karamin yaro, bai taba tunanin zai iya yafewa kansa kan abinda ya faru dazu ba, bai san yaya aka yi ya sake har hankalinsa ya gushe ba, yana jin kukanta, yana tsaga masa zuciya, amma ya kasa tsayar da kansa. Abin takaicin, duk tsawon lokacin nan a dalilin kar ta sake shiga mawuyacin hali ya dage ya kafe, ta yi tsarin iyali, ta huta na dan lokaci tukuna, saboda kar mahaifarta, ta tagayyara ga shi shi da hannunsa ya sa ta a abinda ya wuce wancan halin muni,
sannan kuma ba tare da matakin tsarin iyalin ba ma.
Ya yi kaico da kansa, ya tsani kansa, ya ji ina ma Kasa ta tsage ya koma ciki. Yau ya Www.bankinhausanovels.com.ng
yiwa Umm Adiyya tambarin da zai dade bai gogu a tsakaninsu ba. Tashi ya yi ya wuce bandakin sa, ya saki ruwa a kansa, ya dade a cikin halin rudani,
kafin ya fito ya fara sallolin nafilfili. Can cikin dare yana jingine da jikin gadon dakin
sa, ya ji yana so ya je ya ga halin da take ciki, amma kuma yana taraddadin yanayin da zai sameta.
Ya san ba yanzu za ta huce ba, idan ta hucen ma kenan har abada. Akwai dogon
tafiya a gaba, kan a isa wurin, amma wata babbar buKatar son ya nuna mata cewa
ya damu da ita matuKa ne yake nukurkusarsa.
Wani kasalallen murmushi ya_ yi, cikin tausayin kansa, “Da ka damu da ita, da ka ba
ta abin da take so tun farko a gareka da hakan duka bai faru a tsakaninku ba.”
Sai yanzu ya auno girman abinda ya aikata, bayan ta rasa cikinta har sau biyu,
sannan ya zo ya Kara turmutsa mata rayuwa ta hanyar nuna mata fin Karfi.
Shiryawa ya yi ya fita daga gidan, don bai yi tsammanin zai iya fuskantarta a halin
yanzu ba. Bai yi tsammanin zai iya sake fuskantarta ba na iya tsawon rayuwarsa.

*********

BABI NA TALATIN

Tana gama shiryawa, ba ta jira komai ba ta wuce gidan Abba, ba ta dai san me za ta
ce ba, ba ta san me ya kai ta ba, amma ita dai ta ji gidan Yaya Zaid ya yi mata Kunci a ranar, ba ta san yadda aka yi suka iso wannan gabar ba, a iya tunaninta, amma yau a karo na farko, tun bayan da ya fayyace mata sonta da yake yi, a karo na farko
ta hango Karya a batunsa, a karo na farko ta yi tantamar soyayyar da yake iKirarin Www.bankinhausanovels.com.ng
yana mata. Domin yanzu ta tabbatar duka zancen karya ne. Zuwanta ta samu Maami ta riga ta fita, don haka share wuri ta yi ta zauna, su Fa’iz
duk ba sa gida, a taKaice ma dai da makullin hannunta ta yi amfani ta bude gidan,
gwamma ta yi nisa da Zaid, da duk wani abinda zai tuna mata da shi, sai dai kash!
Hatta gidan mahaifinta ko wane lungu da sako ta shiga, sai ta tuna wani abu na
Karya da yaudara da Yaya Zaid ya taba fada mata, ko ya yi mata a wurin na nuna soyayyarsa gareta.
Kuka ta ci, har ta gode Allah, kafin ta tuna da cewa Allah Ya ce lallai shi Yana kusa,
kuma Yana amsa addu’o’in bayinsa masu roKonsa.
Don haka ta yi alwala ta yi sallar nafila. Ta yi Addu’a mai yawa tare da sujjadarta ga
Allah. Da fatan Allah ya ba ta sa‘a a cikin Kudirinta.
Zuwa lokacin da Abba ya dawo gida, ta dan samu natsuwa, saboda haka ganin jan
fuskarta da ya yi, ya sa ya fahimci kamar ba ta da lafiya. Har ma ya tambayeta
abinda ke faruwa, sai ce masa ta yi ba ta jin dadi ne kawai. “Ki rinKa hutawa, ko zirga-zirga idan ya yi miki yawa a Karshen sati sai ki huta, ki na ji na?”
Muryar mahaifinta cike da kulawa a gareta ne, ya Karasa Dalle mata tafkin hawayen Www.bankinhausanovels.com.ng
da take ta tarewa. A wurin ta fashe masa da kuka mai shiga zucci. Ya-Salaam! Mamana me ya faru kuma? Lafiya dai ko?” Abba… Abba ba zan iya ba.”
“Subhanallah! Wani ne ya ce miki wani abu?” Kai ta girgiza masa, “Ba ki da lafiya ne? Kin je asibiti?”
Nan ma gunjin kukanta ne ya Karu, ta san yadda hankalin Abba ya yi Kololuwar
tashi, ba haka ta so ba, amma ba yadda ta iya.
Suna cikin wannan halin ne. Maami ta shigo ta tarar da su a haka.” Yau kuma Umm
Adiyya lafiya ki ke ta koke-koke ke da Abban naki?”
“Ka ji Khadija dai, ni kuma wani hawaye ki ka gani a idanuna? Shigo dai ki tambayi
‘yarki, ga ta nan tun dazu ake ta abu daya, sai fashewa da kuka take, ta ki fadar koma menene.”
Hankalinsa ya mayar kan Umm Adiyya, “Kin ga natsu, ki share hawaye, ki kuma kwantar da hankalinki, kin ji? Duk abinda yake damunki, bai fi Karfin Allah ba, ki yi shiru, ki fada masa damuwarki, idan mu ba za ki fada mana ba. Kin san komai dan hakuri ne ko?”
Don zuwa lokacin Abba ya fara hada daya da daya, ba tantama fada ta yi da mijin nata. Don kowa ya yi mata shaidar zurfin ciki, ba lallai bane ta fada masu menene. Umm Adiyya ta shiga kuka, tana girgiza masa kai. “Abba ba zan iya ba. Yaya Zaid ya haukace!”

********

Iyayen nata kallonta suke yi kamar wacce ta zare, take kuma shirin kai hari. Abba ne ke da Karfin halin nanata abin da ta fada “Hauka dai!”
Maami kam cewa ta yi, “Iya shegen naki har haka ya kai ga haka? Tozarcin da za ki mana kenan? MaKaryaciyar banza, maKaryaciyar wofi…”
Tana shirin kunno wasu abin fadin ne. Abba ya dakatar da ita, “Khadija dakata, kar
ki zarge ta, tunda har ta yi tattaki ta fadi haka, hala tana da hujja ko ba haka ba?”
“Haba Abba, yaya ma za ka bada Kofar ka ce a saurareta, bayan muna ji, muna gani Karya ce tsuburu take shirya mana. Zaid din ke hauka, duk tsawon shekarun da muka san shi, ba mu gan shi da ita ba, sai ita ce mai idon ganin haukar? In ce dai ko
ke ce mahaukaciyar?” Umm Adiiyya ta taKarKare ta shiga muzurai har da jan majina, “Allah Abba ba sharri

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *